ta fita da shi. sai kawai ganinsa nayi ya shigo sanye cikin ƙananun kayan da idan nace bai yi kyau acikinsu ba ma nayi ƙarya, muna haɗa ido na ɓata rai. ya ƙarasa bakin table ɗin ya zubo abinci a plate sannan ya ijje akan carpet ya umarceni da na sakko muci. nayi masa shiru na kauda kai. ya ƙara cewa,"yanzu fa Ummi ta kirani tana tambayan kinci abinci". nace,"to ni ba zanci ba na ƙoshi...kuma ka gama ka bani takardata na tafi gidanmu yanzu, dan naga da gaske ne kai ɗin aka aura min kuma ni ba zan zauna da wanda baya so na ba". sai ya sa ki wani killer smiling mai ƙarfin sauti da cewan. "ahh tunda ma dai ke kina sona ai da sauƙi, a hankali kya koya min son naki". da sauri nace,"ni nace maka ina sonka, Allah sauƙa na so wanda ba ya so na, yake ƙaurace min saboda ƙaddarar da ta samar da ni". yay shiru bai ce min komai ba, sai na ɗago ido ina dubansa da yanda ya tsareni da ido, na tsuke baki na murguɗa shi gefe sannan nace masa. "ko baka ji ba, nace bana sonka, idan kaji haushi ka ɗauka mataki". ai rufe bakina ke da wuya sai jin hannunsa nayi saman bakina ya matse da ƙarfi, kafn nan yasa haƙori ya gantsara min cizo a leɓe, na kuwa daddage na kurma uban ihu, ihun da ya ja Yagana zambaɗa salatin da bata shirya ba.
a lokacin kaman na fita parlon na sameta na bibbigeta dan takaici, salati ta ke zabgawa tana faɗin wai. "shikenan Abunda nake gudu ya faru...yanzu Kabiru haƙurin da nace maka shi ne ka gaza yinsa, yanzu shikenan akan gadon nawa...ni Rakiya Manniru naga ta kaina, haihuwar ƴaƴa da jikoki iya shegen da ba'a taɓa min ba sai akanku". ihun da na kuma saki ya ƙara sakata zabga salati tana cewa,"Kabiru kana jina ina salati da salallami shi ne ba zaka barta haka ba, dole dai sai an fara lissafin kwanakin ciki daga ɗakina...Kabiru nace ka ƙyaleta haka kuzo ku wuce Habujan a yanzu ku ƙarasa acan, ko kuma ga ɗakinka can ku ƙarata amma ni wannan ihu ƙara yinsa ba a ɗakina ba".
[7/18, 16:14] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*(52)*
Yagana na tsaye na sababi Zulai ta faɗo parlon da sauri, tambayarta ta ke lapia amma ko sauraronta bata yi ba, salati kawai ta ke zabgawa tana kambaba zancen da ba shikenan ba. Zulai ta juya ga su Basma da ke zaune kan kujera hankulansu na kan tv su na kallo, ta kira sunan Sadiya, ta juyo a sanda ta ke kai mango baki tana sha. "wannan ai shashashanci ne Sadiya, kuna jin Yagana na salati ba ku tashi kuga meke faruwa da ita ba". kamar Sadiya ba zata ce komai ba can ta nisa sannan tace. "Inna ki yiwa Allah ki ƙyale wannan rikitacciyar tsohuwar". lokacin Yagana ta juyo tace da Sadiyan. "wannan kuma da wadda ke tsaye kusa da ni kike ba ni ba". Sadiya ta ƙara kaiwa wuya amma bata ce mata komai ba. Zulai ta maida hankalinta ga Yagana da ke faɗin,"ki kalle min nan fa Uwar Amadu, wai yaron nan Kabiru daga yi masa halacci nace ya shiga su ci abinci da matarsa shikenan sai ya tafi aikata abunda ba haka mu kai da shi ba". Zulai tace,"me ya faru Yagana?". Yagana tayi guntun tsaki sannan tace,"kema Zulai wataran dai akwai ki da duhun kai...matsa ki ban wuri nan kiga na shiga na fito da shi". sai a yanzu Zulai ta fuskaci inda maganar Yagana ta dosa, dan haka ta dakatar da ita daga shiga ɗakin tana cewa,"yi haƙuri Yagana". "nayi haƙuri kamar ya Uwar Amadu...ba ki lura da ta'asa ake aikawa ba akan gadona ba ne". "bai zama lallai hakan ba Yagana". "ke kinji uban ihun da yarinyar nan ta kurma kuwa da kike faɗar wai ba farketa yay ba...ta ina za ki sa ni, haka fa yaron can Lamiɗo yay mana da bikinsa, daga shiga ɗaki a barsa ya keɓe da matarsa sai fito mana yay kayan jikinsa duk sun ɓaci da dilkar da ake shafa mata, to yanzu tsakani da Allah ki faɗa min a wanne irin yanayi Kabiru zai fito, kai kai ni Rakiya Manniru ina ganin abinda ya isheni bai ishi Allah na ba....akan gadona, kan gadona fa akai kwanciyar aure, wannan ɗiban alhaki da me yay kama". tayi zancen tana neman kujera ta zauna haɗe da rafka tagumi. Sadiya taja dogon tsaki tace,"wallah Yagana kayan haushinki da yawa yake...ta ya mutumin da baifi minti biyar da shiga ɗaki ba za ki ce ya farke matarsa?, sai kace wanda zai yi fyaɗe ko kuma wanda aka aura masa wacce ba ya so...dan Allah ki rage zuzuta abu". Yagana dai bata ce ma ta kanzil ba tayi kunnen uwar shegu da ita.
ni kuwa tunda Ya Kabir ya sakar min baki daga matsar da yay masa nake aikin matsar hawaye, naja hancina da ya cika da majina ina ƙara kumbura da irin tunanin sharrin da zan ƙala masa wurin Daddy a raba wannan auren. yasa hannu ya gyarani akan cinyarsa da nake a zaune, zaman da yay min ta dole dan kawai zai yi forcing ɗina naci abinci. ya kawo spoon bakina wanda ya ɗebo eba da ya sha miyan egusi busashshen kifi. "oya haa". na kasa yi masa garda saboda yanda naga ya ɓata rai, irin ɓacin ran da tun tasowarmu tare ban taɓa gani a fuskarsa ba, haka ya dinƙa feeding nawa har sai da ya tabbatar da cikina ya cika kafin ya ƙyaleni.
kuma abunda nake ta tsoro tun shigowarsa shi ya faru, idonsa ya ƙyalla kan wedding card gift ɗin da ke aje gefen pillow ɗin da na ɓoye. a ɗazu da ina sallar isha'i Ya Ahmad ya shigo, lokacin tayarwata kenan dan haka bai iya zaman jiran na idar ba ya sunkuya har ƙasa ya aje min card ɗin sannan ya juya ya fita, ya fita ya barni da bugun zuciyar da har yanzu bai tsaya ba, kuma harga Allah a lokacin ko da ace nayi sallama ne ba zan iya ɗaga kai na dube shi ba balle na iya yi masa magana, dan ban san da me zance masa ba.
"wancan card ɗin fa?". tambayar Ya Kabir ta katse min gajeran tunanin da nake, ƙirjina ya fara yin fat-fat, ban san me aka rubuta ajikin card ɗin ba, dan tunda na ɗauko aje shi kawai nayi da zummar idan zan kwanta zan karanta, abu ɗaya kawai da nake tunani nasan ba zai wuce marriage wish ba. ban san me zance masa dan haka nayi tsilli tsilli da idanuwa bakina a gimtse. hannunsa na zagayowa kan cikina ya ƙara tambayata, da irin sautin da ayanzu na gagara yin shiru na amsa masa da. "Card ne". "ehh ai nasan card ɗin ne...na mene shi ne abunda na ke tambaya". na haɗiye wani guntun yawu sannan nace. "nima ban sa ni ba". na amsa mishi a ɗarɗarce saboda yanda yake tambayar cike da tuhuma, cikin kausashshiyar muryarsa yace,"tashi ki ɗauko min". nayi ƙumm na kasa tashi, a tsawace ya ƙara cewa,"nace ki tashi ki ɗauko min ko". muryana a ƙasa nace,"to ai ka matse ƙafan nawa". sai a yanzu ma ya tuna da cewar ƙafafuna na tsakanin cinyarsa ne da ya maƙalesu, ya ware ƙafar na miƙe kamar munafuka naje na ɗauko, abunda ya ban mamaki ina miƙa masa kallo ɗaya yaywa card ɗin sannan ya ɗago ya dubeni fuska babu annuri yace,"me ya kawo Ahmad wurinki?". sai nayi kaman ban gane me yake nufi ba. "wai ba za ki bar min shiru ba idan ina tambayarki". "to ai kai ne da wata negative tambaya, me zai kawo Ya Ahmad ɗakin nan bayan yasan ni matar wani ce". a harzuƙe cikin tsananin ɓacin rai yace,"zan ɗaukeki da mari wallah, ni za ki rainawa hankali...ƙamshin turarensa da naji shigowata naki ne? ko kuma wannan hand writing ɗin naki ne?...kin faɗa uban me ya kawo shi wurinki ko sai na miƙe kinga ainihin tsayina tukunna". jikina na shaking nace,"wallah ni ban san me yazo yi ba, kawai ya shigo ya aje min wannan ya fita amma Allah ka yarda da ni ko kallonsa ban ba". ya galla min wani banzan kallo kamin yasa hannu ya keta card ɗin, sai da yayi gutsi gutsi da shi tukunna yay watsi da su gefe sai wani irin huci yake. sannan ya miƙe tsaye ya tsaya a tsakiyar kaina yana cewa,"daga yau ko wuta Ahmad ya aje kikai gigin ɗauketa gudun karta ƙona ki Maryam abin da zan miki sai kin ƙwammaci mutuwa ki kai...stupid kawai". yay maganar kamar zai rufeni da duka sannan ya bar ɗakin fuuuu kawa guguwa. ya fita ina jiyo Yagana na cewa da shi,"Ta faru ta ƙare, da gasken dai lissafin daga ɗakina zai soma...ai shikenan Kabiru kanka ka yiwa". abinda yasa ta faɗa masa haka ganin yana gyara zaman belt ɗin da ke jikinsa ne, dan da kamar zai cire belt ɗin ne ya dukeni sai kuma yay saurin ficewa.
na miƙe ƙafafuna a sanyaye na shiga toilet ɗin Yagana na wanko fuskata na dawo na kwanta ko cire kayan jikina banyi ba, bacci yay ƙaura daga idona tunda na kwanta, tunaninsa da tunanin abunda yay min kawai na ke, sai ƙwafa nake saki a raina. haka har Yagana ta shigo ɗakin, ina jinta sanda ta kunna fitila ta kashe tana faɗin,"ni Rakiya Allah yasa bai jiwa ƴar mutane ciwo ba...dan yanda naga ya fito fuskar nan kamar hadarin da ya haɗe a gabas nasan bata daɗin rai akai ba, ni dai Kabiru bai kyautan ba, dan da ya san amana na karɓa ba zai aikata hakan ba". ta hayo gadon tana taɓa jikina, cikin fushi na bige hannun nata. ta hau surutanta har taga ji kuma ta dawo tana yabona da yabon Ya Kabir, har da kukanta na zata rabu da shi gobe, wai tasan yanda yay auren nan in ya tafi sai ranar da ta ganshi...ina kallonta tana haɗa wasu kayansa da ta ke faɗin ta wanke masa tasa an goge, tana haɗawa kuma tana goge hawaye, duk sai naji ta bani tausayi, na sauko na ɗora kaina saman cinyarta, nan ta shiga yi min kalar nata nasihar da faɗan duk akan zamantakewar aure.
****ɓangaren Kabir kuwa yana fita direct ya zagaya ta ƙofar baya, inda ɗakinsu Nawwara yake, dama ƙofa biyu ce, ko ka shiga ta kitchen ɗin Yagana ko kabi ta baya wajen flowers ɗin gidan. da farko da ya shiga ɗakin bai lura da kowa ba dan ko sallama bai yi ba bare a amsa yasan da wani a ɗakin, sai Iya ce da ta kula da shi ta yunƙura ta miƙe daga kwancen da ta ke tana gaishe shi. ya shafi bayan wuyansa ya amsa sannan ya tambayeta ina Nawwara. tace da shi ta shiga wanka ne da yake yau ta wuni da zazzaɓi sai yanzu taji daɗin jikinta. sai ya juya ya fice bayan yace da ita,"iya idan ta fito kice ta sameni a ɗakina". ta amsa mishi da "to" tana ƙara yi masa Allah sanya alkhairi dan jiya gaba ɗaya ma bata ganshi a gidan ba.
bai yi minti goma sha biyar da shiga ɗakinsa ba yaji knocking ƙofa. ya ƙarasa saka button na rigarsa sannan ya bata izinin shigowa ɗakin. ta sanyo siraran ƙafafunta ciki bakinta ɗauke da sallama kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta. "Ya Kabir gani". ba tare da ya dubeta ba yace,"na ganki, idan kin gaji da tsayuwar kya iya hawa kaina ki tsaya". daga yanda yay maganar tasan ransa babu daɗi, dan da sauri ta ɗago ta dube shi, kamin nan ta durƙushe a wurin tana fuskantarsa. "ɗauki wannan abincin ki cinye". ta buɗi baki zata yi magana ya dakatar da ita da cewa,"bana son musu". saboda haka ba dan taso ba ta shiga cin abincin, bata wani ci da yawa ba tace da shi ta ƙoshi. sannan ya ƙara cewa da ita,"ɓalli wannan maganin kisha". ta kalli inda wani ƙaramin box yake ta ɗauki maganin da ya mata nuni da shi ta ɓalla tasha, ya taso yace ta miƙe yay mata allura, lokaci guda ta shiga matse hawayen da ke shirin sakko mata, tana cewa da shi. "Ya Kabir na warke wallah". bai bi ta kanta ba ya janyota jikinsa ya tsira ma ta allurar a sanda ta ke ruƙunƙume shi tana sakin ɗan ƙaramin kuka. sanin cewar ba iya lailayawa zatayi ba ya lailaya mata sosai kan muryarsa ta fito a sanyaye yana cewa. "kin gama haɗa kayan naki?". ta ɗaga masa kai alamar ehhh. ya sauke numfashi sannan yace,"ɗazu naje wurin Baba". sai tayi saurin zamewa daga jikinsa tana ɗago kai da ido ta kalle shi. shima ya kalli ƙwayar idonta da ta ciko da hawaye tukunna yace,"ba na son kuka". ya faɗa yana saka hannu ya goge ma ta su da suka sami damar sakkowa.
"munyi magamar Kabirun da kika ce an ba ki, yace sun neme shi tunda jimawa kuma an tabbatar musu da ya rasu, basu faɗa miki ba ne kawai...ashe almajirin Ummanki ne da yay musu halacci, kuma shi ya nuna yana biɗar aurenki tun kina tsumma...na faɗawa Baba cewar zan tafi da ke can ƙasar da nake zaune za ki ci gaba da karatunki acan...na basu haƙuri na ƙurewar lokaci da aka samu wurin sanar da su, amma nayi musu alƙawarin ko shekara ba za kiyi ba zan kawo ki kona sa akawoki ki gaida su...hakan yayi miki?". ta ɗaga kai tana cewa,"na gode da kulawanka gareni". sai taji yasa yatsunsa ya ɗago haɓarta yana cewa. "idan waɗan nan ƙafafun ba su daina rawa ba idan suka ganni next time ɓallasu zanyi, kin san dai ba zasu yi wuyar ɓallewa ba yanda suke kamar sillan karan nan". bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. "kin dai gama shirya komai ko?". "ehh na gama". "kar ki haɗa da tsaffin kayanki, na saya maki wasu su na wurin tailor sai zamu wuce zamu tsaya a karɓa". "tom na gode, Allah ya ƙara arziƙi". "amin amin..kije ki kwanta Allah ya ƙara sauƙi...amma ki tabbata ban fito ina cewa Nawwara fito ba, ko kuma ki fito kina ce min kinyi mantuwa". "insha'Allahu". daga haka tayi masa sallama ta fita yana bin bayan da kallo, zuciyarsa na lissafa masa wani abu da yake ganin da wuya ya yiwu...amma yana roƙon Allah yasa hakan ta kasance.
*Plsss Comment and vote*.
*SIRRIN ƁOYE*
*_Abbas Haruna, Muhammad Kareem, Hussain ATK, Sdeen, Mukhtar, Muhammad Kamji, Surajo Salman, Hassan Basiru, Abubakar Saraki, Mariam Jumare, Amina Musa Galadima, Kherdeejer, Amina Kabir Caps, Maryam kd, Mum Syyid and Noor, Ummu Ashfat, Hajara Usman Aboki, Ummee Imam .Ina maku fatan nasara a rayuwaku tare da adu'an alkhairin Allah da kariyarsa su isa gareku a duk inda kuke._*
*(53)*
6:00am.
akan dining muke, ina fuskantar Ya Kabir shima yana fuskantata, sai Nawwara da ke daga ɗayan kujeran ta gefensa. na cika nayi fam da abunda ban san menene ba, wannan ƙullutun abun da ya tsaya min a wuya na rasa na menene, dan ta ƙarfi da yaji nake kora shi da abincin da nake ci amma yaƙi wucewa.
"wai ke ba ki gama ci ba ne?". bakina ya furta maganar da ban shirya mata ba ga Nawwaran da idona ke kanta tun ɗazu ina banka mata wata uwar harara, ban san dalilin da ya sa nake jin mugun haushinta ba haka kawai babu gaira babu dalili, kuma jin haushin daga jiya ne zuwa yau amma lokacin da nake gidan kaman Basma na ɗauketa. sai naga ta tsorata da maganar da nayi mata har cokalin hannunta yana neman ya faɗi. "dilla Malama da ke fa nake kina wani muzurai kaman baƙar munafuka". na ƙara yin maganar a tsawace, sai kawai Ya Kabir ya tsaya yana kallona kafin ya maida kallonsa gareta. sannan saboda wani rainin wayo nasa da ya kusa sawa na kaiwa bakinsa duka yake tambayana wai dawa nake. naja dogon tsaki na miƙe ina tura kujera baya zan wuce ɗaki ya riƙo hannuna. "wai ke meke damunki ne...na faɗa miki fa ba zamu tafi haka ba ki ci abinci ba...kin san tafiyan awa nawa zamuyi? ko bana ce miki mun fasa zuwa abujan ba ne direct Ethiopia zamu wuce". na warce hannuna a nasa ina binsa da harara kafin nace,"idan damuwa kayi da cina ka biyoni da abincin ɗaki...amma ba zan zauna da mijina muna cin abinci tare da ƴar aiki ba, for what reason?...kuma ma indai da gaske da ita zamu tafi sai dai ku tafi tare amma ba zan bika ba, ai na faɗa maka bana son ƴar aiki".
"to dama waya ce miki aiki zata je miki? ita ma nata personal zaman ne zai kaita". ban tanka masa ba nayi wucewata ɗakin Yagana ina sakin kuka mara dalili, kawai dai nasan idan nayi zan huce takaicin wani abu da ke ƙasan raina.
bayan kusan minti ashirin sai gashi ya shigo ɗakin Yagana, ya zauna bakin gadon kusa da ni, na juyar da kaina daga kusa da shi na koma fuskantar Yagana da ke juye min wani rubutu a jarka da Baba ya bayar ɗazu da asuba. "to gashi nan Babanku yace kar ta yi wasa da sha...har kaima zaku ke sha tare kaji ko". ya amsata da cewan,"tom Yagana an gode Allah bada lada". bayan ta kamalla komai ta taso ta kamo hannunsa da nawa ta haɗe wuri guda tana cewa da ni,"Mairo kike ko Maryam, ni dai dan girman Allah ki kula da marayan nan, ba shi da uwa dan haka na roƙeki ki zama uwa a gare shi, tun yana ƙarami ya rasa mahaifiyarsa dan haka dan Allah ki zame masa farinciki uwa ga ɗanta...tun bayan mutuwar mahaifiyarsa ni na zame masa uwa, ban taɓa bari yayi wani nisa da ni ba sai da karatunsa ya riske shi, yanzu gashi yayi aure kuma ba lallai wannan tafiyar me nisan zamani da zai yi ba mu ƙara samun damar ganawa ido da ido". sai kawai naji wani mugu mugun tausayinsa ya kamani, na kalle shi ta gefen ido naga yana goge ƙwallar idonsa. sannan na kalla Yagana da itama ke goge hawaye, sai naji nima hawayen na sakko min, muryana a hankali nace da ita. "insha'Allahu Yagana". sai tayi murmushi tana ƙara damƙe hannunwanmu anata tana cewa,"kin min alƙawari?". na ɗaga mata kai da cewan,"ehh Yagana nayi miki, haƙiƙa babu abin da za ki nema daga gareni na kasa yi miki shi, dan kinyi min komai a rayuwata... kuma insha'Allahu duk tsayin lokacin da zamu ɗauka acan zamu dawo mu sameki da rai da lafiyarki, da yardar Allah sai kin ɗauki ɗan jikanki da hannunki". a tare suka kalle ni, tana shafo fuskata da cewan,"Allah ya amsa min Mairo...au ashe fa Baba Kabiru ya hanani faɗin wannan sunan". sai na ɗan cukule fuska da muka haɗa ido da shi nace mata."to amma Yagana shima kiyi masa faɗa kar yake min ƙiriniyansa, dan ba ya jin maganata". nayi maganar a kumbure. tace da shi,"Baba Kabiru kaji dai...ka rage ƙiriniyanka tunda Mama Mairo tace bata so, in ba haka ba kuma duk hukuncin da tayi maka babu ruwana ko ƙara kar ka kawo min". yana murmushi yace,"za'ai yanda kika ce Hajiya Yagana". ta gyaɗa kai sau biyu sannan tace,"Maryam amanar Allah ce tsakaninmu Kabir, na ba ka amanarta, dan darajan Allah ka kula da ita, Kabiru idan ka cutar da ita kai da Allah". "insha'Allahu Yagana ba zan ba ki kunya ba". ta saki hannunmu tana miƙewa da cewar,"bari naga Iya ko ta gama dakan waccen daddawar da kace a haɗa maku da ita...sai daren jiya Zannira ta aiko da ita". ta ƙarasa ficewa a sanda ta ke ƙara cewa,"ita Nawwaran ta gama shiryawa to?". shi kuma yana bata amsa da ehh.
ya jinginar da gefen fuskarsa atawa yana cewa da ni,"Ya ya dai?". ban ce masa komai ba sai ɗan murguɗa baki da nayi. sannan ya miƙar da ni tsaye, ya ɗauko vail ɗin abayata ya min rolling, sannan ya kama hannuna muka fice daga ɗakin, ina ta cewa ya cikani amma yaƙi har sanda muka ƙarasa bakin mota, kunya duk ta dabaibayeni ganin Baba a tsaye a wurin, amma shi ko a jikinsa, ganin Ya Ahmad ma yasa sai ƙara wani janyoni jikinsa yake yi.
munsha adu'a daga ƴan gidanmu, har sai da suka sakani kuka sosai, musamman Inna Zulai da duk ta kashe min jiki a da ta ke ƙara roƙata yafiyar abunda tayi min. babu kowa a gidan sai Ya Ahmad, kuma shi ya kaimu airpot, muna tafe su na hirarsu da Ya Kabir ni dai da Nawwara munyi tsit. sai da muka hau jirgi tukunna shima ya bar airpot ɗin, da zamu hau jirgi kuwa raina ya washe da dariyar Nawwara dana ci, wadda ta kasa hawa jirgin sai da Yaya ya riƙeta tukunna.
kuma tunda muka hau jirgin haka kawai sai nake jin wani mixed feeling da duk ya ɗauke wani ɓacin rai nawa, naji na wanzu a wani sabon yanayi da jin daɗi, dan haka kawai naji zuciyata na washewa, Ya Kabir na min hira wadda duk akan company ɗin da yake son buɗewa ne, wata maganar na tsoma baki wata kuma nabi zanen ginin company ɗin da kallo ba tare da nace komai ba...tashinmu da awa biyu naji idona ya fara rufewa, dan jiya ban wani samu nai bacci sosai ba saboda miskilanci, na zura hannuna ana Yaya na kwantar da kaina a kafaɗarsa daga nan kuma bacci ya ɗaukeni, ban farka ba sai buɗe ido nayi na ganni akan gado, wai ashe time ɗin da muka sauka ba ya so ya tasheni sai kawai ya ɗaukoni a hannu.
time ɗin da na tashi baya gidan, sai Nawwara ce ke faɗa min wai sun fita shi da wani abokinsa, ina ji kuma nasan Abdurrahim ne...da yamma muna zaune ni da Nawwara a living room muna kallo muka ji ƙaran bell, Nawwara ta tashi taje ta karɓi abincin da Yaya yay taking mana order...kallo nake amma gaba ɗaya hankalina na kan Mamina, tun jiya rabona da jin muryarta, gashi wayana na hannun Ummi ina ga mantawa tayi bata bani ba.
na shiga bedroom ɗin da yake mallakinsa ne wanda na tashi a bacci ɗazu. akan dressing mirrow na kalla ƙaraman wayansa a ijje, nasan kuma ba ya aje dan ya manta bane sai dan saboda yasan zan buƙata. fuskata ta washe da murmushin jin daɗi a lokaci ɗaya, na ɗauko wayan na zauna bakin gado tare da danna kiran wayan Mamina.
"Autana". na amsa a sanda ta kira sunan nawa, ina jin kaman na shiga ta cikin wayan na rungumeta. "ya akai? kun sauka?". kaman ina gabanta na ɗaga kaina alaman ehh tare da cewan,"ehh Mamina tun ɗazu ma". "to masha'Allahu...babu dai wata matsala ko?". "ehh Mami babu...sai dai Mamina ina kewanki". tai murmushi mai sautin da ya motsa min zuciya sannan tace,"tun yanzu Autana, jiya ne fa kawai". na turo baki a shagwaɓe ina cewa,"Mami kawai fa kike cewa, to Allah Mami jina nake kaman na shekara dubu bana tare da ke". mun ɗau tsawon lokaci muna waya da ita kafin muyi sallama. daga nan kuma na kira Ummi, ita kuma ta maida ni kaman wata ƙawarta sai tsiya ta ke min, har nake ce mata aini na daina kulata, tace ai dama tuni tasan da cewan na daina yinta, itama mun daɗe muna waya daga ƙarshe take ce min,"Maryam nasha gaya miki Kabir na matuƙar sonki, dan haka yau sai kinyi haƙuri da yanda zai zo miki, ta salon da za ki sameshi...kiyi dauriya da juriya, dan wannan ruɓaɓɓan son da ya ɗauki tsawon shekaru masu yawa yana yi miki yau zai nuna miki shi, kema ki zage ki zama mace ta gari Maryam, a wannn daren ki faranta masa rai, dan Allah a daren yau ba sai an kai da nisa ba ina so ki ɗauko min jika, tunda ni dai ba zan yarda ƴata na haihuwa nima ina haihuwa ba, zan dai ta rainon jikokina...yauwa sannan idan kin shirya wannan humrar da na bashi ya kawo miki, ki tabbata kin shafe duk ilahirin jikinki da ita, dan so nake
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 50 Chapter of 52