Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tata tace, "Ma! Yanzu ba ki duba yanayin damuwar da nake ciki ba sai ɗan dukan da naima jikanki...ke kenan duk sanda ɗanki ya ƙunsa min kema sai kin ƙunsa min, shikenan ai". Ta ƙarashe maganar tana tasowa ta wuce ta gabansu har tana bangaje Joseph. Ya kalli Kakarsa da damuwa yace,"Granny...". Bai faɗi abunda zai ce ba tasa yatsa a leɓensa, "Shhhh dont stress your self kaji...indai akan banbancin addini ne Mominka ba zata taɓa sauyawa ba, saboda haka kaima kake daina zuwar mata da zancen da ya danganci hakan". Ya ɗaga mata kai, suka maida hankali kan Kukun gida da ke sanar musu cewar Lunch is ready. Nan suka sauka ƙasa inda suka wuce dining section, har tsawon wucewar rabin awa Dad da Mom basu fito ba, dan haka sai su uku suka yi lunch ɗin, su na kammalawa kuma Joseph da Obi suka fita ɗauko Yayansu Emanuel a airpot wanda jirginsu zai sauka da ƙarfe huɗu. **** A ɓangaren Dad kuwa zaune yake bakin gado, yana shafa kamfutar da ke gabansa, wayarsa a gefe tayi ƙara, ya miƙa hannu ya ɗauka ba tare daya duba sunan me kiran ba, sai da ya kara a kunne daga can ɓangaren aka kira sunansa da, "Major naga kiranka ina bakin aiki shi yasa ban ɗaga ba". Jin muryar amininsa ne yasa shi dakatawa da shafa kamfutar da yake sannan yace, "yayi kyau, nayi tsammanin ma ko kana gida kana hutawa ne". Daga can ɓangaren Major Josiah yace da shi, "ina babu hutu ai, yanzu haka fitowarmu babu jimawa daga meeting da President". Dad ya sauke numfashi yace, "Kuna sane kuwa da garkuwar da akayi ta mutanen da ke kan hanyarsu ta zuwa zamfara state?". Josiah yace,"ƙwarai mun sani". "to amma kuma babu wani mataki da za ku ɗauka akan hakan kenan?". Daga ɓangaren Josiah shi ma nunfashin ya sauke sannan yace,"bamu da ikon ɗaukan wani mataki, saboda ko a yanzu da aka zauna meeting na miƙa wannan issue ɗin, amma shugaban ƙasa yace bai yarda da mu kai farmaki wurin ba...hasalima duk wata magana da muke kawowa akan bada tsaro ga ƙasa sai ya daƙile hakan". "to amma zaman naku akan menene ku ka yi?". "akan basu tsaro ne iyaka yasu bada sauran al'umma ba". Cike da takaici Dad ya girgiza kai sannan yace,"Allah ya kyauta...yanzu abunda nake so da kai Emanuel zai dawo yau, shi ne ina so a haɗa shi da gwarazan securities da zasu raka shi amso mutanen da akayi garkuwa da su". Josiah yace,"babu matsala, we will talk letter yanzu zan shiga office ne". Daga haka suka yi sallama. Dad yaci gaba da scrolling ɗin hotunan waɗanda akayi garkuwa da su ta cikin kamfutar, mata sunfi maza yawa, sai dai abunda ko da yaushe yake ɗaure masa kai shi ne me yasa ba'a garkuwa da christians sai musulmai?, kuma me yasa abun kullum ke ƙarewa akan talaka? Da dukkan hannunsa biyu ya shafi sumar kansa tare da kwanciya saman gadon fuskarsa na fuskantar POP...ya lumshe ido yayin da hoton wata rayuwa can baya ta shiga haskawa acikin idonsa. *Bichi.* "goben ƙarfe nawa zaka wuce?". Baba ke maganar da Amadu wanda ke zaune a gefen mahaifin nasa. "jirgin ƙarfe bakwai zai tashi, saboda haka fitar asuba zanyi inda tsawancin kwana". Baba ya jinjina Kai sannan ya kuma ce masa,"zaka yi kamar watanni nawa kamin ka leƙomu?". "wallah ban sani ba Baba, a yanda nake so dai ace duk wata biyu zanke zuwa, to amma sai abunda ma'aikatar tace". Baba ya numfasa kana yace,"shikenan Allah ubangiji yayi jagora, Allah ya tsare hanya...sai dai idan ka sauka bamu san taya zamu sani ba tunda ba waya a gidan". Ya ɗago da kai ya dubi mahaifinsa cike da tausayawa, yana jin kamar ma yace ya fasa tafiyar, dan tun a ɗazu da suka taru su na masa nasiha sai duk jikinsa yayi sanyi, sai dai babu yanda zaiyi ya san hanyar arziƙi ce ke kiransa. "Baba karka damu dana sauka zan kira wayar Auwalu ɗan gidan Malam Ladan sai ya kawo muku, na faɗa masa zan dinga kiransa yana kawo muku har zuwa lokacin da Allah zai sa ai min albashi na siya muku wayar, ga Lukman sai ya nuna muku yanda ake sarrafata duk da shi ma ba wayewa yayi akanta ba sosai". Na buɗa baki nace,"tabɗi Ya Amadu Allah kam karka wani sa wannan mara mutuncin yaro ya dinƙa zuwar mana gida, gaskiya ƙwamma ba muyi wayar da kai ba indai haka ne, ranar nan fa ya gama zaginmu a waje wai ƴaƴan me faskaran icce". Mu'azzam ya dokan tsawa da cewar, "dilla can rufewa mutane baki, manya na magana kina sako baki". Na turo baki gaba nace,"Baba fa ya zaga". Yana jifana da mugun kallo yace,"nace ki mana shiru ko, indai ba ki rama ba ai nasa uban ya zaga". Inna Amarya tace, "rabu da ita dan yace Ƴaƴan Me faskare da ba ƴaƴan nasa bane?". Nace, "to ai Inna ba iyaka nan ya tsaya ba, ni dai sai dai idan bai shigo gidan nan ba Allah saina rotsa wayar tasa dan na tsane shi". Ban ida rufe baki ba Inna ta gwaɓe min laɓɓana, zafi yasa ni sosa wajen ina yarfe hannu. Gwaggona wadda ke zaune daga can ƙofar ɗakinta tace da Ya Amadu, "ni dai na faɗa maka, idan kaje ka ƙara riƙe addininka karka yi wasa da shi tunda kaga dai kai ɗaya ne musulmi acikinsu karsu dulmiyar da kai, kuma kayi taka tsan-tsan dasu domin basu da amana macuta ne, ni wallahi da ace na isa da kai Amadu wannan tafiyar ba zaka yi ta ba, hanyar arziƙi ai da yawa take, baka san ta inda Allah zai kuma ɓullo maka da wata ba...shawarata ka kula da mutuncin kanka". Ya Amadu ya dubeta yana amsawa da, "insha'Allahu Gwaggo zan yi kamar yanda kika ce". Inna Zulai tace,"tafiya ce dai tunda ni dana haife shi na amince to sai yayi ta, babu batun wani da kin isa, ko kin isa ɗin idan nace a'a wannan isar taki bata isa ba...saboda haka ni dai ki rabar min da ɗa da wannan maganganun naki na jafa'i da kike jifansa da su, Ba komai ne ke damunki ba sai baƙinciki da arziƙin da ya same shi saboda ke Allah bai ba ki ɗa namijin da zai hidimta miki ba". Cikin ɗaga murya Baba ya dakatar da maganarta, "Ke Zulai bana son shirmen banza, wannan wanne irin magana ce, Ke ko kunya ma ba kya ji a gaban ƴaƴanki kike wannan sokiburutsun, to ki rufe min baki tun kamin na saɓa miki, shashancin banza kawai". To haka dai Baba yay ta bawa Ya Amadu shawarwari da kuma nasihohi akan zaman da zaiyi idan yaje can, ya jima yana jaddada masa akan yayi ruƙo da gaskiya akan aikinsa, domin ita kaɗai ce zata ba shi nasara a aikinsa ta kuma ɗaukaka shi harta ba shi kariya, shi kuma yana amsawa da insha'Allahu, muma ƙannensa duk muka bishi da adu'a, ni dai harda guntun hawayena alokacin da Ya Amadu ya miƙe zai wuce ɗakinsu, yake cewa mu yafe shi kuma muyi masa adu'a dan ba lallai mu gana ba gobe tunda daga masallaci zai wuce, sai naji kamar yana mana sallamar ban kwana ne ba zamu ƙara ganawa da shi ba. Sai ƙarfe kusan goma sannan kowa ya wuce ɗaki dan kwanciya, har na kwanta naji shiru shiru Adawiyya bata shigo ba, na sauko daga kan gado zan fita, Inna da ke sauya kaya tace ina zani, nace mata,"naga Adawiyya bata shigo bane". tace min, "ki ƙyaleta kawai ba lallai uwarta yau ta barta kwana nan ba". Nace,"a'a bari dai naje na gani, dan naji tace min kanta na ciwo ɗazu". Da sallama na ɗaga labulen ɗakinsu, Inna Zulai na zaune tana jina amma bata amsa min ba, na shiga daga ciki ina cewa, "Inna ina Adawiyya?". Ta ɗago ta kalleni da masifarta tace,"uwar me za ki yi mata da wannan daren, yarinya sai shegen kinibibi irin na uwarta". Lallai ayau na tabbatar da cewar wani na cin darajar wani, banda haka tun a furucinta kan Gwaggona a ɗazu naso na yaɓa mata magana ba ruwana da girmanta, to sai taci darajar mahaifina da kuma ɗanta da ya maida uwata tamkar ita tayi naƙudarsa. "Inna naji tace ne kanta nna ciwo shi ne nazo dubata". Cikin ɗaga murya ta kuma cewa dani, "to da kika zo nan lafiyar za ki bata ne uwar iyayi, to lafiyarta ƙalau kwana ne dai na haramta mata shi a ɗakinku, tun itama baku asirce min ita ba kamar Amadu, saboda haka zo ki fice min a ɗaki kamin ranki ya ɓaci, idan ma barbaɗe aka turoki yi aniyarku ta biku". Ni dai ganin haukarta na daɗa yin yawa na bar gabanta na wuce wajen shimfiɗarsu Sadiya, tabbas akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanina da Adawiyya, duk da cewar sun rufe kawunansu da zanen rufa hakan baisa na kasa ganeta ba, na yaye zanen daga saman kanta, haka kawai na saki murmushi saboda kallon fuskarta da nayi, nasa hannu na taɓa goshinta naji sanyi ƙalau, sai naji daɗi a raina kenan ta rabu da ciwon kan. A hankali na shiga tashinta ina kiran sunanta, sai da aka daɗe sannan ta amsa min, na kamo tafin hannunta nasa a nawa na riƙe, na kai bakina saitin kunnenta nace,"tashi mu tafi ɗakinmu". Daga irin yanda take motsa idonta nasan cewar ba bacci take ba tana jina. Nasa hannu ina girgizata da salon wasa, cikin hargowa tace dani,"dilla Malama ni ki ƙyaleni". Sai na ɗanyi dariya na daɗa girgizata ina cewa, "to ki tashi mu tafi saina ƙyaleki, ai kan naki ya daina ciwo, kin san dai ba zan iya bacci ba kya kusa dani ba". Taja tsaki ta juya kwanciyarta tana cewa, "Ni dama ba wani ciwon kai da nake...kuma idan ba ki kwana tare dani ba ki mutu, kinga ma wallahi idan ba ki rabu dani ba zan tashi na shaƙeki har sai kin bar numfashi, ko lallai ne saina kwana a ɗakin uwar kareren naki". Sosai naji ba daɗin kalamanta, na saki baki ina duban gefen fuskarta da mamaki, ban san me nayi mata ba yau, dan tun bayan dawowarmu daga masarautar bichi ta sauya min, ko magana nayi mata bata amsa min sai dai tayi ta jan tsaki, dana lura da wannan ne ma na tambayeta menene tace min kanta ke ciwo, ashe ba hakan bane, to ko dai nayi mata wani laifin ban sani ba?, tun tasowarmu wani abu bai taɓa shiga tsakaninmu ba akan rigima, dan faɗanmu ma na wasa ne, ko abinci ɗazu ma da aka zuba mana raba mana tayi kowa yaci nasa, bayan bamu taɓa cin abinci daban ni da ita ba, ko da an zuba mana idan ɗaya baya nan to sai ɗaya ya jira ɗaya, dalilin da yasa ma Baba wani lokacin ka kiramu da tagwaye. Na kuma kamo hannunta nace, "Adawiyya wani abun nayi miki?". Sai ta fizge taja tsaki tana daɗa rufe kanta da zane, na miƙe na fita jiki a saɓule, Inna Zulai ma da nake mata sai da safe ci kanki bata ce min ba. Shigata ɗakin Inna tace, "kije Gwaggonki na kiranki, idan kin dawo karki manta ki rufe mana ƙofa bacci zai iya ɗaukeni kamin ki dawo". Na amsa da to sannan na nufa ɗakin Gwaggona, ina shiga na tarar da ita ta gama wanke allo, na zauna gefanta kamar mara lafiya, zuciyata cike fal da tunanin laifin da nayiwa Adawiyya wanda ban san shi ba. Bayan Gwaggo ta gama bawa Basma rubutu sannan nima ta miƙo min sai aikin kauda fuskarta take daga gareni, na miƙa hannu na amsa nayi bismillah sannan na kafa baki na sha kaɗan, ina ajiyewa ta jefeni da wawan kallo, "ɗauki ki ƙarasa shanye shi". Ba shiri na ɗauka na rumtse ido kace maɗaci aka bani, ina kuma shanyewa kawai sai na fashe da kuka ina kifa kai da gwiwa. "me aka yi miki kuma?, idan har akan rubutun nanne to kuwa tabbas yau zan fara sa miki waya ajiki". Nai saurin girgiza mata kai ina cewa,"a'a Gwaggo ba rubutu bane, Adawiyya ce take jin haushina ko magana bata son yi min". Gwaggo taja guntun tsaki ta miƙe tana nufar gadon ta da cewa, "a halinki na rashin kyautawa kika yi mata wani abun". Nace,"Allah Gwaggo ni ba abunda nayi mata". Ta ɗan murmusa sannan tace, "to ni yanzu me kike so nayi miki, faɗanku ne dai wanda ya shiga tsakani kunya kuke ba shi...kuma wata ƙila saboda faɗan da Malam yaywa Uwarta ne take tayata kishi". "a'a Gwaggo tunfa dawowarmu a ɗazu ne". Bayan ta kwanta tace, "to kin gani kuwa dole kin mata wani abun, ai shariya ba halinta bane, ke kuma halinki sai ke...ki kwana anan ba sai kin koma ɗakin Innarki ba". Na miƙe kamar wadda ƙwai ya fashewa aciki na hau kan gadon, sai da na maƙalƙale Gwaggona sannan na samu bacci ya ɗaukeni sakamakon faɗuwar gaba da naji ya tsananta garen. Can cikin dare na farka dan gabatar da sallar dare wadda a yanzu ta zame min jiki, idan ban riga Gwaggona tashi ba to ita zata rigani, dama ita kusan kullum cikin raya dare take, na murza idona dan wartsakar da baccin da ke cikinsa sannan na zuro ƙafata na ɗan ƙaro hasken fitila. A tunanina Gwaggona ce ke sallah sai da na ƙaro hasken fitila na ganta kwance tana bacci. Na ƙaro hasken fitilar sosai sannan na kai dubana ga Kulu wadda ta ɗaga hannaye sama tana roƙon ubangijinta, na zuba mata ido sosai kamin nayi la'akari da kukan da takeyi, kana iya jiyo kalamanta da take cikin yarenta, da sautin muryar kuka da ke neman cin ƙarfinta, tun muryar nata na fita a hankali har ta bayyana sose inda nake jiyo maganganun nata raɗau ba tare da sanin me take cewa ba tunda bada yaren da nake ji bane, hawaye gaba ɗaya ya wanke mata fuska, Fatarta ta koma ja. A hankali kuma sautin kukanta da na muryarta ya ragu, ta kifa fuska a tafukan hannunta tana mai ci gaba da kuka a hankali. Tsananin tausayinta ya kamani, nasa hannu na goge hawayen da nima suka sauko min, Lallai a duniya babu marasa tausayi irin iyayen Kulu, babu abunda zuciyata ta ƙissima min akan wannan kukan nata face rashin iyayenta, waɗanda suka manta da ita da rayuwarta tun tsawon shekarun da naji Ya Amadu ya labarta min. Na sauka daga saman gadon cike da tausayi da jin ƙanta na isa gabanta, nasa hannu na ɗago da fuskarta, na sanya ƙwayar idona cikin nata wanda haskensa ya cika min idanu, lokaci ɗaya ruwan hawayen da ya kuma saukowa daga idonta nima ya sauka a nawa, nasa hannu na goge mata, ban ankara ba naji ta rungumoni jikinta ta matseni tsam a ƙirjinta har ina iya jiyo bugun zuciyarta. *Comment&Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *MissAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maki hajarki cikin farashi mai rahusa, ke dai tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *12)* Mun ɗauki tsawon lokaci rungume da junanmu, tun shashsheƙar kukan Kulu na fita har ta daina, ni kuma a nutsuwar dana samu daga wannan jikin nata ne bacci ya soma ɗaukana, sai can kamar kuma tsikarin allura naji ta tureni daga jikinta har ƙeyata ta bugi da bango, ta kauda fuska gefe saboda kar ta haɗa ido dani, lallai acikin ɗabi'un Gwaggona dana Kulu akaina zan iya cewa babu banbanci, dan ko a ɓangaren Gwaggona sau tari ta kan kauda kai daga gareni musamman lokacin da ta san ina buƙatar kulawarta tamkar ba ita ta tsuguna ta haifeni ba, ni kuma hakan na damuna, yana min ciwo, yana kuma sani zubar hawaye, domin banda shaƙuwa irin ta uwa da ƴa da har Gwaggona zata iya jin sirrina, ko kuma na faɗa mata matsalata, Duk sanda na kaiwa Inna Amarya wannan kukan nawa sai tace nayi haƙuri kunya ce tsakanin Ɗan fari, sai dai ni kuma na ɗauki hakan a matsayin cutarwa, dan tabbas ina cutuwa matuƙa, ita Kulu nasan ba dan komai yasa take yakice ni daga jikinta ba sai dan iyaka da Gwaggo tayi mata da ƴaƴanta, amma banda haka tabbas zan iya cewa Kulu zata iya zame min Uwa kamar Inna Amarya. Ganin yanda na tsareta da idanu yasa ta tashi ta bar min wajen, ta koma gun shimfiɗarta ta kwanta. Nima na tashi na fita dan ɗauro alwala, sai dai me kuma!, ina fita tsakar gida naja na tsaya saboda abunda idanuna suka yi tozali da shi, tsoro ya kamani, jikina ya hau kyarma, nayi dakiyar dana hana kaina gaggawar kurma ihu, na shiga jero adu'oin neman tsari da halittar dana gani a tsaye daga can wurin banɗaki ta juyan baya, hannu a kunne da alama waya ake, dan ina iya jiyo sautin fitar murya ƙasa-ƙasa amma bana jin me ake cewa, gaba ɗaya jikinsa lulluɓe yake da ƙaton zane, hakan yasa ba zaka tantance mace bace ko namiji, kuma a duk iyaka ƙoƙarina na son in gano zanin wane acikin gidan na kasa saboda na manta a ɗakin wa na taɓa ganinsa, sanin zanin waye ba shi ya dameni ba, waye a tsayen shi na damu da na sani, na dai baro su Gwaggona a ɗaki, ƙofar ɗakin Inna Amarya kuma a rufe yake, Inna Zulai kuwa nasan ko karan hauka ne ya cijeta ba zata fito da wannan tsakiyar daren ba, na tabbatarwa da kaina hakan akanta, saboda ita tana da tsoro sosai, ko fitsarin dare bata fitowa sai dai ta tsula abunta a fo wanda ta siya saboda tashin dare, to kar da ace ɓarawo ne ya shigo mana gida?, Na daddage na buɗe bakina na kurma ihun "Ɓarawo". da siririyar muryar da Allah ya bani, har sai da nayi ihun sau biyu tukunna Baba ya buɗe ƙofa ya fito, sai gasu Ya Amadu da Ya Kabiru ma a tare, kowa kuma ya shiga jefo min tambayar ina ɓarawon yake?, ashe tuni ma ya bar wajen, murya na rawa nace da Baba, "a wajen banɗaki na ganshi". Aiko nan mazan gidanmu suka yi wajen, wasu kuma suka fita ƙofar gida ko zasu tarfa shi ta bayan katanga. "ikon Allah, amma me ɓarawo zai shigo yi cikin gidan nan mu da bamu aje komai ba?". Baba yay maganar da Matansa da ke tsatstsaye kowacce acikin taraddadi, Inna Zulai tace, "shi ne abun tambayar ai...kuma ke Mairo kin tabbatar mutum kika gani kuwa ba a ƴan barci kike ba?". "ehh wallahi Innah, ai banma yi ihun ba sai dana tabbatar shi ne ɗin". Baba ya kuma girgiza kai, "Ɓarawo acikin gidan nan, ikon Allah!". Gwaggona ta sauke numfashi bata ce komai ba sai wajen banɗaki da ta ƙurawa ido, dan ita macece irina me yin nazari da zurfin tunani akan abun da ya bata mamaki. "ni nama kasa cewa komai". Inna Amarya ta faɗa wadda ke tsaye daga ƙofar ɗakinta. Na kuma cewa, "Baba kuma fa waya yake yi lokacin dana gansa". Kan kowa yace wani abun sai ga su Ya Kabiru sun shigo kowa na maida numfashi. "Baba babu fa kowa a wajen nan wallahi, babu ma alamar an dira ta baya gaskiya, dan Malam Yakubu da Ƴaƴansa har kan kwana suka bi". Ya Kabiru ke wannan bayanin, Mu'azzam ya ɗora da cewar,"nan ciki ma fa babu wata alama tasa, saboda ko yane da za'a ga alama ta neman wajen ɓuyarsa ko kuma fita". Kowa yay shiru wucewar sakanni kamin Baba yace, "to Allah ya tsare...kowa ya koma yaje ya kwanta". Sadiya da ke tsaye kusa da Inna Amarya tace, "yanda Mairo ke da hargitsewa wallahi ma nasan bai zama lallai ɓarawo ta gani ba, magagin barcinta ne kawai". "ai da ban gani ba babu yadda za'ai nayi ihu a wannan daren". Daga haka kuma kowa ya juya ya wuce ɗakinsa, tunda muka shiga ɗaki ni dai na kasa bacci saboda tsoro, nayi lamo kwance ƙirjina sai bugawa yake, kuma dana rufe ido sai hoton wancan mutumin yake haskawa cikin idona, hakan yasa na gagara rufe shi na bar shi a buɗe, kuma ko a duhunma hakan take, nayi yunƙurin kunna haske saina tuna Gwaggo bata iya bacci da haske hakan yasa na koma na ƙudundune. Can naji motsin an buɗe ƙofa an fita, nayi zumbur kuwa na miƙe nabi bayan Kulu da ta fice, ban sanya ƙafata a tsakar gidan ba sai da na tabbatar da ta shige ɗakin Baba, na tafi saɗaf saɗaf na ɓoye a inda ko fitowa akai ba za'a iya ganin ko da inuwata ba. Na jiyo muryar Baba na fita da cewar, "da ina da ikon tsaida hawaye, da na jima da tsaida zubar hawayenki Kulu". Banji me tace masa ba, haka kuma shi ma banji abunda yace mata ba, na kuma rumtse ido tare da ƙara kasa kunne sosai dan kar wata maganar ta kuma wuce kunnena, domin a yau dai na tabbatar da akwai wani sirrin ɓoye da ke tsakanin Kulu da mahaifana. Sautin muryar Baba ya ɗan ɗaga yaci gaba da cewa da Kulu, "Kulu ina so ki gane rayuwa kowa da irin tasa. kamar yanda labarin rayuwar kowanne bawa dabanne, To haka kowacce rayuwa na cike ne da tarin ƙaddarori masu yawan gaske, haka ma kowacce ƙaddara da fuskar da take zuwarma mutum, kuma kowanne bawa da kika gani yana taka sawu ne akan ƙaddararsa kuma duk inda ta nufa da kai dole sai ka bita baka isa ka guje mata ba domin rubutacciya ce, amma karɓarta ta kowacce irin fuska shi ke nuna ƙarfin imanin mutum. Kuma kowanne bawa da kalar irin tasa ƙaddarar, wani zai tsinceta da kyau wani kuma zata zo masa da muni kuma dole ya karɓa in har ya yarda yayi imanin da Mahallicinsa, Allah ya kan jarabci bawansa ne domin gwada ƙarfin imaninsa ya gani shin zai iya cinye jarabawar, idan har kuma yayi riƙo da wannan ƙaddarar to zaki kalla ko akan wanne Al'amari ne ƙarshensa yazo masa ta yanda bai yi tsammani ba. Saboda haka ki sani Allah da kansa yana faɗa a Alqur'ani cewa "Ahsiban-nasu an yutraku an ya quluu amanna wahum la yuftanun". Mutane su na tsammanin zamu bar su barkatai alhalin sun ce haƙiƙa mu munyi imani?. To kinga kenan tabbas mumini ake jarrabawa, wannan kuma jarrabawar taki ce, ki roƙi ubangiji ya baki ikon cinyeta ba wai ki zama ko da yaushe cikin kuka ba, wannan kukan babu abunda zai yi miki. Suwaiba ta faɗa miki abunda kike tunanin faruwarsa anan gaba muddin tana raye ba zata bari hakan ta faru ba, nima kuma nayi miki wannan alƙawarin, matuƙar ina raye babu mai sanin wannan sirrin naki, na ɗauke ki ne tamkar ƴar cikina...Suwaiba kuma ta ɗaukeki ne matsayin ƴar'uwar da kuka fito ciki guda, Ko wani ya nemi ya tozartaki wallahi sai inda ƙarfin Suwaiba ya ƙare, ba zata bari ba ko da ace hakan zai zama silar rayuwarta ne". Wucewar sakanni kamin na jiyo muryar Kulu na cewa, "Malam gani nake kaman ƙaddarar zata iya juyawa, ina tunawa da maganar Kakata da take cewa Barewa bata gudu ɗanta yayi rarrafe...haka kuma mahaifina ya taɓa ce mana abunda iyaye suka aikata a ƙuruciyarsu to shi ƴaƴansu suke aikatawa idan sun taso...Malam kayi haƙuri, waɗannan kalamai biyun da nake tunawa su ne suke sakani zubar hawaye su kuma ɗaga hankalina sannan zuciyata ta ƙara yin rauni, ayanzu haka ina mai dana sanin sunan dana raɗa mata, ina gudun karta tashi akan turbar me wannan sunan, Dama ace sunana na raɗa mata da ba zan kasance a fargabar rayuwarta ba a duk inda zata tsinci kanta kuwa, sai dai kuma idan itama ta gamu da irin tawa ƙaddarar". Kukan da ya ci ƙarfinta yasa ta yin shiru, kamin taci gaba da cewa, "wallahi ina jin tamkar na kashe kawunanmu ko dan saboda na huta da ɗanɗanar wannan baƙin cikin rayuwar da nake yi, itama kuma ta huta da fuskantar baƙin ciki anan gaba". Kuka yaci ƙarfinta sosai tana kuma cewa, "gwara ita na kanji tana bina da kyakykyawar adu'a

Chapter 9 of 52