kiyi zarra a zuciyar Kabiruna, ya zamana babu mace mai iya kamoki a zuciyarsa da idanuwansa". Maganartata ta saka naji kunya, mu kai sallama da ita cike da kewarta ina daɗa jin ƙaunarta acikin raina. na kira Alhassan ma muka sha hira da shi, yana ce min wai idan zai zo nayi masa girki sama da kala goma dan so yake ya tabbatar da ingancin girkina, nayi dariya nace da shi aikuwa sai dai kar yaci. Shamsiyya Sani ma mu kai waya da ita, tana ta tsokanata da wannan iskancin nata, ƙarshe dai ba dan mun gama hiran ba na kashe wayan, dan idan na biye mata sai ta lalata min kunnena. na kira Yagana na sanar mata mun sauka, sai da za muyi sallama nake tsokanarta yace ko ta fara lissafin, tayi dariya sosai tana ce min shaƙiya tare da cewar za tayi kewarmu.
bayan sallar isha'i nayi shirina cikin wasu riga da skirt na english wears da Yaya ya lodasu akwatu huɗu, kaman me shirin buɗe kanti. kayan sun min kyau sosai dan har sai da na bawa Nawwara tayi min hotuna, na duƙa ina rufe drowern da na maida humra sai jin mutum nayi ya kwantar da kansa a bayana ya kuma zuro hannayensa saman cikina, cikin wata iriyar muryar da ban taɓa jinsa da ita ba yace,"i love you Maryam". sai naji ƙafafuna sun shiga ruwa, na ɗago ina juyowa gare shi tare da dafa kafaɗunsa gudun karna faɗi, sai ya rungumeni tsam irin rungumar da ta banbanta da sauran da yake min, dan har ƙashin bayana sai da yay ƙara. a hankali naji yana shinshinar wuyana kafin muryarsa ta fito can ƙasa yayin da yake murza hannuna cikin nasa,"Maryam wannan ƙamshin fa?...wane irin turare ne kika saka haka?, wayyooo Maryam kinji yanda yake motsa min jikina kuwa". kaɗan ya rage yawun da ke zarcewa zuwa maƙogorona ya haɗo tare da zuciyata su fito, na motsa jikina ina so na zame daga jikinsa sai ya kuma ƙanƙameni, fuskarsa kwance kan kafaɗata yay shiru kaman wanda yay bacci, sai numfashinsa da ke fita a hankali a hankali...shirun da naji yay yawa yasa nace,"Yaya". har ga Allah a irin yanda yay shirun nan da yanayin yanda yake sauke nunfashi zaka rantse kace ko bacci yake, amma da mamakina sai naji ya amsa da,"ummm". sai nayi shiru ban ƙara cewa komai, kafin na ƙara jinsa ya kira sunana."Maryam". a hankali na amsa da,"na'am". "ina sonki, ina sonki da yawa, dan Allah kinji...". kamar wani ƙaramin yaro me neman wani abu a yanda yay roƙon, naga kaman yana neman faɗuwa sai na ruƙo shi ina tambayansa,"dan Allah me?". bai ce komai ba har tsawon sakanni uku, kafin nan ya ɗago da kansa ya haɗani da jikin bango, sannan ya duƙo da kansa saitin bakina a ƙoƙarinsa na ya haɗe bakinmu wuri ɗaya, haɗuwar leɓensa da nawa yay daidai da bugawar wayarsa, sai kawai yaja wani dogon tsaki na ƙorafi ya saki ƙuguna da yake riƙe da shi sannan ya ɗaga wayan yana magana murya a ɗage. "Abdurrahim kana da matsala". ban san me Abdurrahim ɗin yace da shi ba naji ya ƙara jan dogon tsaki kamin yace,"su jirani ina zuwa". ya kashe wayan yana zurawa a aljihu, ya tsareni da idanuwansa da suka fara ƙanƙacewa tare da ce min kiyi alwala ki jirani yanzu zan dawo, just some minutes kinji. gyaɗa masa kai kawai nayi, kuma sai da na ɗauki tsawon wasu sakanni tsaye a wurin kamin na iya jan ƙafafuna cikin mutuwar jiki na shiga toilet nayi alwala na dawo bakin gado ina zaman jiran dawowarsa.
inata jera hamma ya dawo ɗakin yana aje leda a bakin drower, tukunna ya shiga yayo alwala ya dawo yace na tashi muyi sallah, munyi sallah raka'a biyu kaman yanda sunnah ta koyar, sai kuma naji ya shiga koro adu'oi wanda zan iya cewa adu'ace da ke cikin kansa gaba ɗaya yake yinta, yayinda ni kuma nake binsa da amin har lokacin da shima yace amin muka shafa tare. ya juyo ya fuskanceni ya dafa kaina yay min adu'ar da sunnah ta koyar sannan ya matso kusa da ni, yasa duka hannayensa ya tallafo gefen fuskata yace. "doll". da wannan muryar tasa mai zurfi ya kirani da sunan da shi yasani saurin ɗago ido na dube shi, ƙwayar idonmu ta sarƙe wuri guda. "kina jin yunwa?". na girgiza kaina acikin tafukan hannunsa alamar a'a, bai janye hannunsa ba ya ƙara cewa. "amma ai yought zai iya shiga wannan shamulallan cikin ko?". ya faɗa with full of smile on his face. shiru nayi bance komai ba, dan ni gaba ɗaya gani nake kaman ba Ya Kabir ba, kuma komai ganinsa nake kaman a mafarki. sai ya ƙara cewa,"wannan yought din ba irin sauran bane, kisha ko kaɗanne kinji". ya faɗa yana buɗe roban yought ɗin yana kawowa bakina, na buɗe baki na sha ba wani da yawa can ba. sai naji ya matso da fuskarsa jikin tawa sose sannan ya haɗe bakina da nasa, nayi saurin runtse ido da naji yana zuba min yought ɗin da ke bakinsa cikin nawa, wanda sai bayan da ɗanɗanonsa ya hau kan harshena tukunna na tantance yought ɗinne amma da farko nayi zaton ko yawunsa ne me daɗi haka. lokaci ɗaya naji wani abu ya tsarga tun daga tafin ƙafata har tsakiyar kaina, wani abu da ke neman hargitsa min ƙwaƙwalwa...take duk wata jijiya ta jikina ta shiga juyawa, a san da naji tafukan hannunsa masu sanyi a saman cikina, yatsansa ɗaya cikin cibiyata, sai nayi saurin riƙe yatsan zuciyata na wani irin bugu acikin kunnena.
a zaune na ke amma jina nake kamar zan faɗi, kawai sai naji kansa a saman ƙirjina, muryarsa na fitowa da wani irin sauti da yasa idanuwana rufewa lokaci guda, muryarsa ta fito a hankali kaman mai jin bacci da cewan, "Doll ba zan miki komai ba sai da yardarki". sai nayi ƙarfin halin ɗago da kansa da ɗan sauran kuzarin da nake da shi, a wannan lokaci idanuwansa sun ƙanƙance sun sauya launi, yanayinsa na komawa kaman wanda yay maye. sai naga yay wani irin murmushi yana cewa, "Doll ko na haƙura mu wuce wannan part ɗin?". sai kawai na tsinci kaina da saurin girgiza masa akai alaman a'a ina mai miƙa hannayena na riƙo kansa sosai na haɗa goshinmu wuri ɗaya. sannan muryata ta fito a hankali da kiran sunansa wanda zan iya cewa ya amsa minne da ƙyar, kafin nayi shiru na gaza cewa komai dan ban san me zance da shi ba, ni dai na kira sunan nasa ne kawai, sai naji yana cewa da ni.
"Doll ba ki bani amsa ba, mu tsallake wannan part ɗinne? ba zan miki dole ba, ba zan miki komai ba har sai kin yarda da ni, zan iya haƙuri insha'Allah". yay maganar da yanayi na ban tausayi, sai na ƙara kamo kansa muryata a hankali nace,"a'a Yaya, kar mu wuce, indai wannan part ɗinne kar mu tsallake shi...na yarda da kai, Allah Yaya na gama yarda da kai thousand percent". sai kawai naji ya saki wata nauyayyar ajiyar zuciya yana motsa yatsansa babba acikin kunnena tare da yin hamdala ga Allah.
"Yaya nima wannan jaririyar zuciyar da ke dashe a ƙirjina tana sonka tana ƙaunarka, Yaya zan zauna da kai muddin rayuwata...zan zame maka baiwa a komai, dan kai ne muradina, kai ne walwalata, kai ne farin cikina, kai ne annashuwata...Yaya duniya kanta shaida ce da cewar kai kafi cancanta da ka zama abokin rayuwata, kayi min halacci, kana da ƙima da daraja a wajena fiye da tunaninka....Yaya kai ne, only you, only you na ke so ka zama uban ƴaƴana". yaja wani numfashi bayan nayi shiru yace,"nima haka Doll". kuma daga hakan bai jira komai ba ya haɗe laɓɓana da nasa a hankali, a hankali cikin wani salo nasa na daban shi kaɗai, salon da ya sakani damƙe hannayensa saboda yanda nake jina tamkar ana jana zuwa sama, kuma a wannan lokacin ji nake dama mu tashi zuwa wata duniyar da ta ke tamu mu biyu kacal...tsawon wasu daƙiƙu muna haka kamin ya janye daga jikina ya kamoni mu miƙe tsaye a tare, har wannan lokacin ban buɗe idanuna ba, a rufe suke tun sanda ya haɗe laɓɓanmu, bakinsa a kunnena naji ya zura harshensa ciki, yay wani irin zuƙa a ciki da ya sa numfashina ya shiga kakkatsewa sannan dukkan jikina kuma ya ɗauki rawa. akan ƙafafunsa nake tafiya har muka iso bakin gado yasa hannu ya kashe light, ɗakin ya gauraye da wani irin duhu da acikinsa babu abin da nake ji sai numfashinsa.
jikina ya hau ɓari da naji yana ɓalle min buttons ɗin rigata, sannu a hankali bakinsa ya sauka akan ƙirjina tsakiyar breast ɗina, a hankali yake kissing wurin tasirinsa na bin kowacce jijiya ta jikina, kawai sai naji yana bin kunnena da wasu irin kalamai, wasu kalamai da saƙonni da a lokaci guda su kai kacakaca da dukkan lissafina da tunanina.
duk wani rawar jikinsa da kakkarwarsa sai naga ina nema na fishi, nema nake na fishi zaƙuwa da zalama, ban san lokacin da muka hau gado ba, ban lokacin da ya rufemu da bargo mai ɗumi ba, ban san lokacin da duhun ɗakin ya daɗa bayyana ba, haka ban san lokacin da labule ya ɗaga wata lumsashshiyar iska ta shigo ɗakin ta gauraye shi ba. abun da kawai na sa ni, a wannan gadon, cikin wannan ɗumin bargon, cikin wannan duhun mai haɗe da ni'imtacciyar iska, da ƙyar Yaya ya iya gamsar da ni, shikenan tushen wata sabuwar rayuwa ta wanzu a tsakaninmu, muka tabbata abu guda, sunanmu na *MK* ya tabbata.
sanyin iskar da ke shiga hancina ne ya farkar da ni, na buɗe idanuwana a hankali cikin hasken alfijir ɗin da ya ratso ta labulen windon ɗakin, asuba ce a wannan lokacin a yanda na fahimta, sai na lumshe idona a hankali kamin na sake buɗe shi a hankali, cikin sakan ɗaya, biyu sannan idona ya sauka akan fuskar Yaya da ke kwance akan ƙirjina, hannayensa na kewaye dani. murmushi ya ɓalle min, na kai hannu na ƙara rufemu da bargon ina mai tusa hancina acikin sumar kansa da wani sanyayyan ƙamshi ke tashi.
*AFTER 1 YEAR...MK*
"Hellowww Daddyn Urnborn". nayi whispering softly acikin kunnensa. "It looks like someone will be late for work today". na ƙara faɗa ina ba shi kiss a kowanne eyes nasa, that made him open his eyes lazily yana kallona da murmushin da ke talewa a leɓensa.
"Morning to you Baby Doll". ya faɗa yana janyoni jikinsa. "morning sarkin bacci". na faɗa ina kama tsinin hancinsa. "Doll wannan ɗumin jikinne bana gajiya da shi shi yasa kullum nake kusan yin late a work". sai na ƙara sakin wani murmushin na kwanta lamo ajikinsa ina jin yanda zuciyarsa ke bugawa. ya kai hannu kan ƙaton cikina yana faɗin,"1 week remaining ko?". na gyaɗa masa kai kawai ina tura hannuna cikin singlet nasa na shiga wasa da nimple ɗinsa. "i have to be at the office by now shi ne za ki tsokanoni ko". shiru nayi masa, dole ce take sawa nake barinsa fita office, amma ba dan son raina ba, ina son mijina, ina matuƙar sonsa, kuma ina godiya ga Allah da ya mallaka mani shi, haka ina godiya ga wannan ƙaddarar da ta sauya komai.
duk sanda nake tare da shi, sai naji inama akwai wata hanya da zan sanya lokaci ya tsaya cak, so i could cherished our moment together forever, or if my life was a dream zan yi fatan naita baccin ba tare da na farka ba. ya bani kiss a saman kumatuna da forehead ena, duk da cikin jikina ya tokareshi amma haka ya san yanda yay ya haɗe hancinmu wuri guda yana gogawa, shaƙar numfashin juna kawai muke, kuma tuni na gama kashe masa jiki da shafa hannuna da nake a saman mararsa, sai ya ƙanƙameni yana lumshe idanu, sai na saki murmushin da ya haɗe da dariya ina janyewa daga jikinsa. sai yay saurin buɗe shanyayyun idanuwansa yana ƙara janyoni yace,"Allah ba ki isa ba". kuma ba tare da ɓata wani lokaci ba muka fara nunawa junanmu soyayya har zuwa lokacin da muka gama samun natsuwa sannan mu kai wanka...na shirya shi muka fita mu kai break fast tukunna ya wuce office ina cewa da shi,"Jay plss be at home in time for dinner".
ko da na dawo ɗakin Nawwara na wuce, na sameta tana shafa icing a jikin cake ɗin munafurcin da ta gama haɗawa. yawuna ya tsinke na zauna kusa da ita, tsabar walaƙanci tana jina amma saboda abinda ta ke ya fini bata kula da ni ba. bata ankara ba kuwa na kaiwa cake ɗin damƙa nayi ƙatuwar gutsira na kai baki, tsananin baƙin ciki da takaici ya hanata cewa da ni komai sai sakin baki da tayi tana kallona, kaman ta kurma ihu ta rufeni da duka. haka na janyo cake ɗin gabana naci iya cina bata ce da ni ƙala ba, sai da nayi hani'an tukunna na dubeta ina dariya nace. "sorry ba laifina ba ne". "dama ai haka za ki ce". ta faɗa kaman tasa kuka. na shafe ma ta icing ɗin a fuska har lokacin ban bar dariya ba saboda yanda ta cukule. "dilla can Allah na tuba dan dai cake, me akai akayi shi...sai a tura driver ya sayo masa wani". tace,"ai nasan da na sayarwa naƙi saya na zauna nayi da kaina saboda bana so hubbina yake cin kayan waje". na taɓe baki nace,"oho dai, tun jiya nake cewa ki rakani kawai ai min operation a ciro waɗannan yaran kika ƙi, da yanzu ai cake ɗinki na nan lafiya". ta buɗi baki za tayi magana wayarta tayi ƙara da ringtone ɗin i love you my baby boy. tana ɗagawa sai cewa tayi da Abdurrahim "Habibi kaga Yaya ko?". ta faɗa masa da kukan shagwaɓa, ina jiyo shi ta cikin speakern wayan yana tambayanta me nayi mata, tace da shi. "na gama haɗa maka birthday cake ɗinka tazo ta cinye tana wani ƙalawa unborn". ina jinsa ya saki ƙwafa yana faɗin,"yanzu duk wahalan da kika shiga bata tausaya maki ba ta zauna ta cinye, ina ce ma ko sannu bata maki ba ko?". tace da shi,"ina tace min sannu kuwa tana can ɗaki liƙe da miji bata ma san nayi aikin ba, sai iya zuwa ta cinye". "rabu da ita, zan rama ne akan mijinta...kuma zan zo na ɗaukeki ai sai naga yanda zata yi da zaman wannan ƙaton gidan". na ƙyalƙyale da dariya na warci wayar ina cewa da shi,"ka ɗauketa ka kai ta ina ƙaton gwauro?". "ina ruwanki, ke da mijinki ya ɗaukoki daga gidanku ina ya kai ki, Allah kina shigar mana hanci da ƙundundune...sa'arki ɗaya ma ɗanmu ne yaci da sai dai kiji sammaci yanzun nan". "oho dai cake ne na cinye kuma ko yanzu akai wani naji ina so sai naci ehe...kuma wallah Abdurrahim kar na sake naji kaima Jay wani abun in ba haka ba sai na shiga na fita na lalata wannan auren naku". sai ya bushe da dariya yana cewa,"yasin munfi ƙarfinki, munsha li'ilafi da tabbatyada, dan haka munfi ƙarfin muguntar mutum". kashe wayar nayi na jefa mata kayarta ajiki, na dafata na miƙe ina roƙonta akan ta yiwa Allah ta zo muje asibiti ai min operation ai yanzu ya isa acire twins ɗin da ke cikina duk da Edd ɗina sai nan da 7days, danni nace ban haihuwa da kaina sai dai a yankani. dan walaƙancin Nawwara sai ce min tayi bata ƙi ganin ma na fara naƙuda yanzu ba ta miƙe ta bar min gidan bama ɗakin ba. ta fice ta barni tana jarabar ɓata ma ta cake ɗin da nayi, sauranma sai mage ta bawa ta cinye akan ta ban na ƙarasa shi...nace zan haɗa mata sharri wurin Jay tace na manta itama tana da Habibi, yarinyar nan tunda Ya Kabir ya haɗasu da Abdurrahim ta fitsare kamar shi. ashe dalilin tahowarmu da ita kenan, yace tausayin yarinyar da yake ji ne yasa shi ganin babu wanda ya dace da ya aureta kamar Abdurrahim, kuma kasancewar munbi duk da wata hanya da Nawwara zata ja hankalinsa nan da nan kuwa Abdurrahim ya amince da ita. yanzu haka bikinsu wata uku ya rage dan zuwanmu da wata bakwai muka je can inda har iyayen Abdurrahim ɗin muka tafi suka nema masa aurenta.
*After 2days.*
"ina kika maida wan nan kayan?* yana tsaye daga bakin closet ya kama ƙugu yake tambayana. nace da shi,"yanzu dan Allah kaya nawa gareka da zaka ce min ina na kai maka wannan kayan". sai yay murmushi ya wurgo min singlet ɗin hannunsa yana cewa,"to sarkin dalla dalla...kayan da Ishaq ke ɗinka min nake nufi". har yanzu hankalina na kan kayan Babies ena da nake ninkewa ina zubawa a riyo ɗinsu, haka nake kullum banda aikinyi sai na fito da su na ƙara ninkewa, takaicin hakan na ƙume Nawwara dalilin da ya sa ma kenan idan taga ban fito parlo ba zata kira wayana tace wai ina fama da rashin aikinyi.
"ka manta kai kace na tattarasu gaba ɗaya na bawa Abubakar...kai Jay wai me yasa kake da mantuwa tun baka tsufa ba". yasa hannu yana shafo bayan wuyansa, ba tare da ya ce komai ba ya ƙaraso inda nake shima ya zauna a ƙasa kusa da ni, sai kallon cikina yake kafin nace da shi. "lafiya? kafa daina kallan mun yara dan kyauna nake so suyi ba naka ba". "ni dama ai nafi so suyi kyanki, kawai dai ina mamaki ne idan na tuna yanda da cikin nan ke a shamule". sai kuma ya tankwashe ƙafa ya kuma matsowa kusa da ni yana faɗin,"Preety wai nayi ƙoƙari kuwa ranar first night enmu?, har yanzu ji nake kaman a maido shi baya". na sauke masa ɓawon ayaban da na gama ci a fuska, ina cewa,"idan kwaɗayin ayaba ne ya kawoka ba baka zanba...gwara ka tashi kaje ka haɗa kayan wankinka dan ni daga nan har na haihu kayan ƴaƴana kawai zanke taɓawa". sai kawai naji hannunsa cikin rigana ya fito da breast ena yana faɗin,"ni ai ba mayen ayaba bane...kema kin san da wannan". na taɓe baki nace,"kasha iya shanka, twins na zuwa ya zama ƙwalelenka, tsakaninka da shi kallo daga nesa".
*_Fashin Baƙi._*
Na haifi kyawawan ƴaƴanna twins Mace dana miji, ranar suna kuma da aka sha shagalin da ko biki albarka suka ci sunayensu masu albarka, Namijin akasa masa Adam(sunan Baba) mu ke kiransa da Ramadhan, macen kuma Hajara wadda muke kiranta da Nihla. aiko munsha sababi wurin Yagana akan ba'a saka sunanta ba, wai dama ba son tsakani da Allah muke mata ba, da muna sonta har zuciyarmu sai muyi mata kara. Jay yace tasha kuruminta haihuwa ai yanzu aka fara, ta rubuta ta aje haihuwa ta gaba sunanta ne, tace daga baya kenan nan da shekara uku ko biyu ai tana gidanta na gaskiya.
Anyi auren Abdurrahim da Nawwara inda suma suka tare nan kusa damu babu nisa, dan abotarsu da Yaya da gaske ne, kusan kullum kuma Nihla na wurin Nawwara acewata ni kam nafi son Ramadhan me sunan Babana, yaron da na ɗora dukkan so da ƙaunata akansa, ɗaukansa ma ban fiya so ayi ba, har faɗa mu kanyi da Jay wani lokacin dan idan na tattara hankalinta akan Ramadhan bana fuskantar kowa da komai. shima kuma duk sanda yaso ya rama idan ya ɗauki Nihla sai na kusan kuka sannan yake saurarona, dan shima yafi son mai sunan Mamansa.
Ya Ahmad yayi aure shima, ya auri wata ma'aikaciyarsu me suna Ngozi ada, lokacin da ta zo wurinsa ta faɗa masa tana so ta shiga addininsu yaji duk duniyarsa babu macen da yake so sama da ita, kuma ta amsa kalmar shahada ta tashi daga Ngozi ta koma Nusaiba, su na nan zaune a lagos.
Adawiyya ma tayi aure, ta auri tsohon saurayinta na farko da ta wulaƙanta shi akan Suhail.
Inna Amarya kuwa ta kamu da paralize, inda aka maida ita gidansu taci gaba da jinyarta acan, ni dai tun ranar farko da muka je dubata ban ƙara sanin a halin da take ciki ba yanzu, ta zama bar tausayi maganarta sam bata fita, kamar me gwaranci, duk tabi ta ƙare ta lalace, ranar da muka je tana ta miƙo hannu wai zata taɓa su Nihla na doka ma ta tsawa nace "kull ɗinki, har yanzu ban mata da ke ki kai ajalin Gwaggona ba, ganina ma da kika yi anan darajar Mijina kika ci, amma ni ko a lahira ban fatan haɗuwa da ke, kuma har ki mutu ban yafe miki da abubuwan da kika mana ba".
da zamu taho kuwa sai kuka take, Allah masanin abunda ta ke son cewa damu, ni kuwa a raina cewa nake dama ta mutu bata nemi yafiyar waɗanda ta cuta ba taji daɗin cin ubanta a ƙabari. shi kuwa sai wani jimami yake yana tausaya ma ta, haushi ma yasa har muka isa gida ban ƙara kula shi ba.
Bross Almustapha ma yay aurensa, yana zaune da matarsa acan London.
bayan tsawon wani lokaci, ina ɗauke da cikin wata tara Allah yayiwa Yagana rasuwa, bayan tayi fama da rashin lafiya, jinyar da ta zama ajalinta. mutuwar da ta kusa zautar da ni da mijina, ba mutane kaɗai da suka kasa gane kanmu ba, hatta mu ɗin mun kasa gane kanmu, dan har akai adu'ar bakwai bamu dawo hayyacinmu ba, haka kuma tun zuwanmu washe garin rasuwar bamu ƙara haɗuwa da juna ba sai ranar da zamu tafi, shima dan Baba ya takura ne akan mu shirya mu bi su Mami abuja washegari sai mu wuce gida, tunda dai zaman namu ba shi zai dawo da Yaganan ba.
kuma daren ranar da muka isa abuja na haihu, na haifi yarinyata mai kama da Yagana sak, tana dirowa duniya ni da babanta muka kirata da suna Ruƙayya, bamu ɓoye ma ta suna ba kaman yanda Yaganan ta roƙa.
Matar Ya Ahmad ma ta haihu, itama sunan Yagana ɗin ya saka, ƴarsa ta biyu kuma ya saka ma ta Maryam wai mai sunana.
yanzu haka anata shirin bikin Basma da Alhassan nan da kwanaki ƙalilan da suka rage, abu ya zama tuwona maina, auren Yayana da Ƙanwata, sai shiri nake kamar wadda zata aurar da ƴar fari.
Yarana kuwa duk sunyi wayo ma sha Allah, duk in da aka gansu yabo da tofa albarkacin baki akan kyan su ba a magana. soyayya kuwa tsakanina da mijina sai son barka, kullum sabuwa ke ƙaruwa, ji muke da ace da damar da zamu hana mutuwa rabamu tabbas da mun yi.
______________________________
*TAMMAT BIHAMDULILLAH!*
*Alhamdulillah, Alhamdulillah.*
*ina roƙon Allah ya haɗamu a alkhairin da ke cikin wannan littafi, sannan yayi mana gafara a kuskuren da ke cikinsa...amin y Rahman*
*_Finally zan tsaya anan😥...and its time to say good bye to you my people😍😥. thank you very very much for your love and support😘...thanks to all of you that took your time to read, comment, and vote for each and every chapter💋....and most crucial; thank you very much for all the prayers and well wishes that you guyz have sent my way since the starting point to the ending point💋❤...i will forever be grateful to all my wattpad family, Halima hz Palace and Fitattu Biyar Novels, i feel loved and i love you to the moon and back💖....kuna da yawan da ba zan iya lissafo ku one by one ba, akwai sunayen da idan ban lissafo su ba zan iya cewa SIRRIN ƁOYE bai kammala ba, to amma a kaɗan ɗinsu idan nace zan jero waɗannan sunayen zamu ƙara ɗaukan wasu chapters enne😅, amma dai kowanne makarancin littafin nan ya sa ni wannan page ɗin nasa ne sukutum guda na bahi🙌._*
*My headech, matar Awwaluuu, jikar Yagana and my pracetamol nace ba😂😂...bari dai nayi quite kafin na fara ɓallo sunaye😅*....ina yi mana fatan alkhairi
*Start:-15 October 2021.*
*End:-25 february 2022.*
_Please for those following youtube channel kindly search for my Channel NISHADI MULTIMEDIA, do subscribe and press the bell icon for vedio update._
_Ku tsumayi zuwan sabon labarina wanda zai fito a team FITATTU BIYAR, na kuɗi akan farashin #500, ina fatan za ku nuna min ƙauna wajen mallakarsa, a nuna min zunzurutun ƙauna don Allah a siya😍 tabbas ba za ku yi nadamar siya da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 51 Chapter of 52