Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Kabiru ido wanda motsinsa kawai nake so na gani ko na sami ƴar natsuwa a tare da ruhina. "goge fuskarki". Ya Amadu yace da ni a sanda ya ƙaraso wurin yana tsaye daga gefen gadon, hannunsa kuma daya miƙo min handkerchif ɗinsa ne, na miƙa hannu na amsa sai naji shi da damshin ruwa, na ɗago idona na dube shi naga ya kafeni da ido da irin kallon da ban taɓa ganin ya min shi ba a ƙwayar idonsa. kallon daya haifar da jin wani abu ajikina, ba shiri na haɗiye guntun yawun dake maƙogorona na haƙura da jin ba'asin dalilin daya sa zan goge fuskana, kuma ban fahimci dalilin hakan ba sai dana ɗora Handky ɗin ina goge fuskar, ashe a bushe ta ke, bushewar ruwan hawayen da nake zubarwa tun tasowarmu daga Qatar har saukarmu ƙasar nan. "amsar guda ɗaya ce, ƙanwa! daga wannan matsayin so na ƙanwa, daga wannan matsayin karki yarda ki baiwa wani abu me tasiri damar shiga cikin kanki ya sauya tunaninki". tabbas banda kallonsa nake a sanda yake maganar, zan rantse da Allah ba Ya Amadu ne yay maganar ba, saboda yanda bakinsa yake a gimtse, haka kuma laɓɓansa basu motsa ba, kuma yanda yay maganar kamar bada ni yake ba, dan idonsa sam ba'a kaina yake ba, yana kallon wani wuri na dabanne, sai dai saɓanin tunanin cewar hankalinsa ma ba'a kaina yake ba yasha banban a sanda na kusa zamewa daga kan kujera zan faɗi yay saurin saka ƙafarsa ya riƙe kujerar da kuma hannunsa guda wajen riƙoni. na rufe idona sai dai kamin na buɗe har ya bar kusa da gadon, sai kawai nabi bayansa da kallo a sanda yake daf da fita daga room ɗin, da tarin wasu abubuwa fal da ban san ma'anarsu ba a cikin kaina. bayan fitarsa na kasa hana hannuna daga riƙo na Ya Kabiru da yake ta sonyi tun ɗazu, ɗumin tafin hannuna da nasa suka haɗe, na lumshe ido tare da jinginar da kaina ga gefen ƙarfen gadon, tunani nake, tunanin da ban san na mene ba, har zuwa sanda idona ya kai kan jakar Mami na ɗauko na zuge zip ɗin na zaro tab ɗinta. da security ajiki, kuma duk abinda yazo kaina idan nasa sai taƙi buɗewa, haka na tsurawa hoton Ummi dake kan screen ɗin wayar tata ido ina kallo, tunanin saka sunana a password ɗin yazo kaina duk da banda tabbacin zata iya sakawar, dan gani nake Mami tafi son Alhassan akaina, ni kawai dai na amsa sunan ƴane a wurinta, amma banda wani matsayi a zuciyarta, amma kuma ko dana saka har sunan Alhassan ɗin bai buɗe ba, hakan kuma yasa ni mamaki, sai dai mamakin daya haska cikin ƙwayar idona da cikin kaina a yanzu yafi na lokacin dana saka sunan Alhassan yaƙi buɗewa, _Maryam._ ina rubuta sunana wayar ta buɗe, kuma da buɗewarta hoton jarirai biyu ya bayyana akan wallpeper, hoton dana tabbatar da mune time ɗin da muna jarirai, dan haka ban san lokacin da na kai hannu ina shafa hoton ba tare da haɗewar saukar murmushi a fuskata. ƙaunar Mamina, Soyayyar Mamina, Bigen mahaifiyata, wannan Mahaifiyar, Uwa, Uwata da ta ɗauki cikina tsawon wata tara tana rainonsa, ta kuma haifeni bayan mawuyaciyar naƙudar da Allah kaɗai yasan adadin azabar dake cikinta, wadda ita kaɗai ce zata ƙaunace ni, ƙauna ta haƙiƙa a duk yanda nake, da duk yanda na kasance. *5:00am.* ƙarfe biyar ɗin asuba agogo ya buga a washegarin abinda ya faru, kuma kaɗawar agogon ta haɗe da buɗe idon Kabir a wannan lokacin, ya shiga wurga idanuwansa da sukai masa nauyi akan kowanne bango na ɗakin, inda ganin nasa ya tabbatar masa da cewar a asibiti yake, kuma kwance akan gadon asibiti, sai ya maida murfin idon ya rufe na sakan ɗaya sannan ya kuma buɗewa ya saukesu a saman ɗakin. Yagana dake zaune bisa darduma a wannan lokacin tana lazimi, wadda ta kafa ta tsare da jiran farkawarsa, dan ko bacci bata iya yi ba, kwana tai tana roƙarwa Kabiru sauƙi a wurin Allah, haka kuma zuciyarta bata bar taraddadin farkawar tasa ba, dan ita gani ma ta ke kamar ko likitocin ƙarya sukai musu an ɓoye musu ne amma Kabiru ya mutu, shi yasa ko a daren jiyan da akai-akai taje gida Amadu zai kwana da shi taƙi yarda ta tafi, domin tana ganin kamar sai da safe ne za'ace ma ta harma an kaishi ƙabarinsa. tun buɗewar idanuwansa na farko idonta ya kai kansa, kuma sai taga abin kamar a mafarki saboda haka ne batai magana ba sai a yanzu da ta kalla ya buɗesu tangararau ya zubesu a sama, a lokacin ta ƙarashe laziminta da faɗin,"Alhamdulillah". sannan ta yunƙura ta miƙe tana kiran sunan nasa,"Kabiru ka farka." ya juyar da ƙwayar idonsa zuwa kanta sannan ya ɗaga ma ta kai. sai tai murmushi tana saka hannu ta shafa sumar kansa. "Yagana tsautsayi ne amma ban bige shi da gangan ba, nayi iyakar yina wajen ganin na kauce masa amma sai ya dinƙa ƙara shiga gabana...ina fatan bai mutu ba Yagana, bana so zunubin kisa ya hau kaina, ban san wane shi ba, amma jikina ya bani dama ya shiryawa faruwar hatsarin namu". Muryarsa ta fito a hankali yana kallonta, kuma muryar ta fito da ƙoƙarin dawo da ita cikin hayyacinta daga tunanin wacca tai silar faruwar hatsarin nasa. jin shirun amsarsa daga bakinta lokaci guda jikinsa yay sanyi, daga yanzu kuma wannan lokacin ya ɗaura niyyar azumin kaffara. "babur ɗin shima ya mutu ko kuma ya tsira?, na Anas ne na ara ya kuma jadadda min kar wani abu ya taɓa lafiyar machine ɗinsa". Yagana ta sauke numfashi kamin tace,"daga wanda ya bigeka har machine ɗin suna lafiya babu wanda ya mutu acikinsu, Anas ɗinma ya karɓi babur ɗin nasa daya zo dubaka, shi kuma wanda ya bugeka yana can a hannun hukuma." nan ta ke ya sauke wata ajiyar zuciya ta farinciki, ba murnar tsiran babur ɗin ba, murnar tsiran rai ne, dan idan babur ne yana da kuɗin biyan sabo bama gyara ba. "Maryam fa?". wannan karan muryar tasa ta fito ne da wani irin amo da ita Kanta Yagana ta kasa tantanceta, kuma sautin muryar daya fito a hankali ta cikin shirun ɗakin shi ya farkar dani daga baccin da nake, kuma acikin tunanina na ƙoƙarin tantance inda na jiyo kiran sunan, aciki ne na tsinci maganar Yagana na cewa. "ta dawo, sunzo tare da mahaifiyarta ta ainihi". da mamakin Yagana sai ta kalla yay murmushi haɗe da cewar. "na san komai Yagana, babu abinda Akila ta ɓoye min dangane da ita, tun a lokacin da tasa ni yi ma ta bincike ta gama buɗe min cikinta...ina Maryam ɗin?". ya ƙara tambaya a karo na biyu, kuma kafin Yagana tace wani abu na taso daga inda nake, ina takowa kamar wadda ƙwai ya fashewa aciki, irin takun tafiyar marasa gaskiya, irin takun tafiyar wadda ke tsoron amsar ɗanyan hukunci, kuma a lokacin dana ƙaraso bakin gadon, zan iya kiran kallo ɗayan da yay min da kallon tsautsayi, dan bada niyya yay ba, yay kallon ne bisa rashin sanin cewar ƙwayar idonsa zata sauka akaina ne. "Ya Kabiru sannu". na faɗa muryarta na fitowa a hankali, da kuma rawar jikin da ban san ta mece ba, kuma sai naji sam babu daɗi da rashin amsa mini ɗin da yay, shin bai san a halin da nake ciki ba ne akan ciwon nasa? da har zai nuna halin ko in kula akaina, banfa iya bacci ba sai da Yagana tasa nurse ta min allurar bacci ta dole, amma har sanda aka min allurar ina zaune a gefensa, gefen wannan hannun nasa da nawa ke riƙe da shi da ban san lokacin da aka rabani da shi ba. "naga kamar ruwan ya ƙare, ki cire masa tunda likita ya nuna miki yanda za kiyi ɗazu". Yagana ta faɗa a sanda ta juya tana faɗin,"Allah baka lafiya ya kuma bi maka hakkinka Kabiru, ba kai kaɗai ba dukanmu sai Allah yay mana sakayya tsakaninmu da waccan algunhumar matar Amarya, ƴar banza me kama da ƴaƴan birinya, tsinanna makirar mace, zamanta dai acikinmu kam ya ƙare, ƙwarai ta shammacemu kuma ta ɓata wayonta. wallah da muka je naso ofishin ƴan sanda nan naso an bani kulki na mummuƙawa ƴar banza a kafaɗa... kai bari nayi sallah naji masallaci na tayarwa". na zagaya ta gefen inda aka saka masa ruwan, sai dai sam na kasa zare masa allurar da jininsa ya fara biyowa ta ciki kasantuwar ruwan drip ɗin ya ƙare, ba wai dan ba zan iya cirewar ba ne, a'a sai dan kawai ina jin ba zan iya cire masa ba, kaman zanji masa rauni ne, kuma bana so yaji zafin cirewar. ganin jinin na ƙara fita da yawa na kai hannuna dake rawa kan butterfly ɗin, kuma kamin na kai ga ɗaga bandage ɗin sai naji ya riƙe hannuna ya ɗauke daga kai, ya juyo ya zare da kansa. sannan ya yunƙura zai miƙe daga kan gadon ya sauka ƙasa, sai nai saurin dawowa ta gaban nasa ina dakatar da shi cikin saurin muryar da ban taɓa yi ba wajen faɗin,"Ya Kabiru ƙafarka akwai ciwo, Dr yace karka taka". gaba ɗaya a wani kiɗime nayi maganar ina riƙe ƙafafun nasa na maida kan gadon. ban kalle shi ba, amma a jikina nake jin irin kallon da yake bina da shi, kuma a wannan durƙusawar da nai sai naji ƙafafuna kamar an riƙe su, sam na kasa ɗagowa, sai kaina dake kallon ƙasan tiles ɗin, idona na zubar da hawayen da ban san dalilin zubarsu ba, abu guda da na sa ni shine ba zan taɓa yafewa kaina ba idan har na zama silar wanzar da ɓacin rai akan wannan fuskar ta Ya Kabiru. wucewar kusan rabin sa'a kafin maganar Yagana ta haifar da kuzarin da ya gushe min lokaci baya kaɗan. "ke ba kya sallah ne?". sai dana saka hannu na goge hawayen fuskata kan nace ma ta. "zanyi Yagana." tukunna miƙe na shiga banɗaki dan yin alwala. ƙarfe goma saura su Ummi suka zo, kamin shigowarsu drivern Mami ne ya fara shigowa da manyan basket guda biyu kowanne shaƙe da manyan coolers na abinci, sannan Alhassan ya mara masa baya shima hannunsa riƙe da madaidaicin kwandon kaba da tarin fruites aciki. daga baya kuma saiga Mami da Ummi sun shigo, na miƙe da saurina naje na rungume Mamina ina ma ta sannu da zuwa, sai Ummi ta tsaya tana kallona a sanda ta harɗe hannayent tana jinjina kai, sai naji nauyinta ya kamani dan haka na sa ki Mami na tafi gareta ina murmushin dake bayyanar da haƙorana gaba ɗaya na rungumeta itama. "a'a Maryam ki dai nuna min wariyar launin fatar kawai, na yarda zan ɗauka a hakan, ai daɗin abinma ina da Alhassan bake ɗaya bace". sai na ƙunshe fuskata ajikinta ina cewa,"to ai Ummi kece kika shigo daga baya, amma dake ne kika fara shigowa ke zan fara rungumewa kamin ita". tana murmushin itama tace,"ba wani nan ni ban tsaru ba". da haka muka kama hannun juna zuwa kujerar da zata zauna, na duƙa na gaisheta ita da Mami, Alhassan ɗin kuma dake hararata na murguɗa masa baki...Baba ma yace ai yaga alamar yanzu idona baya ganin kowa sai Mami kawai, dan yaga alama shima tun jiya na manta da shi, duk sai naji kunya ta kamani, dan cikinsu babu wanda ya faɗi ba dai-dai ba, yanzu hankalina gaba ɗaya na kan Mamina ne. Alhassan ya yunƙuro zai ƙwalo min jarkar hannunsa akan murguɗa masa bakin da nai karaf idon Mami akansa tace,"ka buga ma ta sau ɗaya, ni kuma naita buga maka har sai kanka ya zama ƙwalele". gaba ɗaya akasa dariya har da Ya Kabiru dake amsar magani daga hannun Yagana. dariyar tasa kuma tasa ni jin daɗi, daɗin da har saida na motsa laɓɓana, sai dai kuma jikina yay sanyi sanda muka haɗa ido da shi naga ya ɗaure fuska. karo na huɗu kenan tun daga farkawarsa, idan na gama fahimta a yanzu Ya Kabiru sam bai son ganina, fushi yake da ni, to laifin me na masa?, tambayar da bani da amsarta, kuma nai ƙoƙarin na sameta tun sanda ya zamana daga ni sai shi a ɗakin amma yaƙi bani dama, lokacin nan da Yagana ta fita nace masa. "Ya Kabiru inata maka sannu baka amsa ba". bai responding nawa ba har sai dana tambaye shi sau uku tukunna yace da ni,"sannu indai daga bakinki ne bana sonta, ba sannunki kaɗai ba, ganinki ma ba so nake ba". furucin nasa kuma daya sani a damuwa ya ɗaga hankalina a lokaci ɗaya. "ki tashi kuje gida ki wanka, zuwa anjima sai ku dawo bayan kun huta". maganar Ummi ta dawo dani daga duniyar tunani, nace da ita,"Ummi ni ba sai naje ba, Yaganan dai ta tafi". "haka za ki zauna kina tsami da warin asibiti?". sai Mami tace,"barta zuwa anjima ma tafi tare, zanje ganin gwamna nan da 12". Ummi tayi knodding kanta kawai tana ci gaba da karanta takardar da suka amso daga wurin likita akan ciwon Ya Kabiru. kuma barin kallona da zanyi daga kanta muka haɗa ido da Mami wacce ke magana a wayar da ke kare a kunnenta, tayi min nuni da cinyarta na tafi na zauna akai inata farin ciki, zaman nawa ya zama lokaci ɗaya da gama wayartata, tasa hannu ta juyo da fuskata tana goge min wani abu da ban san mene shi ba, a yayinda a gefe guda gangar jikina da ruhina ke daɗa tsargawa da so da ƙaunar mahaifiyata. "dilla tashi, sai kin karya ma ta ƙafa". Alhassan yay maganar cikin ɗagowa kaman zai fizgoni, na turo bakina gaba kamin nace wani abu Mami ta rigani da cewar,"sai kasa ta tashi ai tun da ƙafar taka ce". ban san lokacin da dariyar ta suɓuce min ba ina kallonsa tare da haɗa masa da gwalo. Mami kuma tace,"gyara zamanki da kyau Autata, cinya taki ce bata kowa ba". Yagana da ke yafa mayafi za su tafi ta taɓe baki da cewar,"goɗe goɗe da ke akan cinya ko kunya". nace,"Yagana bafa a taki na zauna ba". "yo kice ma za ki zauna akan tawa ki gani". sai kuma ta juya kan Mami da cewa,"wannan ƴa taki dai ba halin ƙwarai gareta ba, dan haka kar ki nuna ma ta son da zai sa ta sangarce, wahala za ki sha wurin tanƙwarata, ko da yake anan dai albasa tayi halin ruwa". na kalli Yagana na ɓalla ma ta harara saboda jin haushin maganarta ta ƙarshe, sai ta murmusa kunci da cewa,"Allah na kaɗai na ke tsoro, dan haka Maryama dai-dai na ke da hararki wallahi, ni Rakiya ba, da ni kike zancen, ai akwai ranar ƙin dillanci". harar tata dai na kuma yi bance ma ta komai, su na gabanin fita a ɗakin tace da Ya Kabiru,"kai kuma Malami ka daure ka zama namiji ka tashi haka, ni ba zai yiwu na dinga zaman jinyar asibiti ba, jiya haka naita faman tsartar da yawu kamar wata me ƙaramin ciki. saboda haka ka warware dan tafiyar nan tawa da ka ga nayi ba zan dawo ba, iyakaci na ke maka aiken sannu...idan kuma na biya Amarya ta zo ta dinƙa jinyarka ne to?." ta ƙarasa zancen nata tana ƙunshe dariyar da ke neman fitowa, shi kuma yace,"in dai kin shirya yin takaba ki aikota ai ba wani matsala bace Hajiya Yagana". sai ta dawo daga baya tana cewa,"au kai na manta ban faɗa maka ba, wannan ja'irar yarinyar ta min alƙawarin kujerar makkah fa, ka ma ta godiya idan ka gama ciwon bakin akanta." da haka ta juya ta fita, har ta fita kuma ta dawo tambayar yace ko dai shi direban ba irinsu Mami bane shi ma ba ya jin hausa, dan indai shi ma irinsu ne to gwara a haɗata da dutse ta tafi ta san ta tafi da wanda bai san me ta ke ba da hujjah. Ya Amadu da ke tsaye ya girgiza kai da cewa,"muje dan Allah kar ki cika mutane da magana". "ah toh Amadu idan ba za ka iya da maganar tawa ba ka toshe kunnenka mana ina dalili anan, haka kawai Allah ya tsagan baki kace ba zanyi magana ba...ni dai wannan hali naka na ba ni takaici, banda cuta ce da ba'a ƙaunarta ai sai nace dama kaine a maimakon Kabirun, haba sai kake takura min kamar wani Babana". shi dai tafiyarsa yay ya barta a wurin, bayan yace da Alhassan ya taso su tafi tare, kuma Alhassan ɗin na zuwa wucewa ta gabanta ta riƙo rigarsa da cewar,"kai zagalo tsaya, Allah ya sa ni wannan tsayin naka tsoro yake bani, bari nayi gaba sai ka biyoni a baya". daga ƙarshe dai gaba ɗaya har ni akai tafiyar. kuma abin da bamu sa ni ba da ni da Yagana da Ya Kabiru da ke kwance, shi ne, Mami ta saya mana sabon gida anan Saye ɓangaren masu kuɗin anguwar, ashe tun bayan saukarmu a ƙasar tasa aka nema ma ta gidan, kuma abin da ta bari su Baba suka kwasa a tsohon gidanmu ƙalilan ne duka ƴan abin da ba'a rasa bane da suka zama na amfanin dole. gidan flat ne me kyau da part daban daban, dan ɓangaren su Inna Zulai daban, na Baba daban, ni da Yagana a ɓangare ɗaya, sai mazan gidan ma aka haɗasu ɓangare ɗaya kowa da ɗakinsa, Ya Kabiru da Ya Amadu kawai part nasu daban daban, tsohon gidan kuma tasa an bige shi ana gyarawa tace Baba sai ya zuba ƴan haya a ciki. duk wannan bayanin sai a yanzu da muka taho Ya Amadu ke bamu shi, adu'a da sa albarka kuwa da Yagana keyi ma ba zai faɗu ba, dan tun kamin mu ƙarasa gida tace da Alhassan,"kai Zagalo kira min gyatumarka na ma ta godiya". shi da bai san me tace ba sai ni na karɓa wayar na kira ma ta ita. nima sai da muka ƙarasa gidan na shiga godewa Mamina da naga haɗaɗɗan ɗakina da yanda aka ƙawata shi, komai anyi shi da favorite colour ena white and blue, ɗakina na kallon na Basma sai na Yagana dake daga can ɓangrenmu, tamfatsetsen parlonmu kuwa ba'a magana. dan haka ina fitowa daga wanka na baje akan lafiyayyan gadona dan huta gajiya, sanyin Ac sai ratsani yake, maimakom baccin da na ke saka ran zanyi sai na kasa, wani tunanin na daban ya shiga cikin kwanyata, tunanin da ke neman hargitsa min lissafi. _shikenan komai yazo ƙarshe, sirrikan sun bayyana, komai ya warware, sabuwar rayuwa ta fara..._ *Bayan Wani Lokaci, Qatar, Turakar Mai Martaba.* Almustapha da Imam(Joseph) tare da Ibrahmi(Obi) su ka shigo cikin turakar. su ka ƙarasa har gaban Mai Martaba inda suka zube a ƙasa gaba ɗayansu su ka kwashi gaisuwa, Mai Martaba ya amsa tare da sanya masu albarka, da kuma ƙarayi musu adu'ar tabbatuwa acikin musuluncin da suka karɓa a kwanakin baya da suka shuɗe, a wancan ranar da Almustapha da Major suka je asibiti, bayan dawowarsu gida ne an gama bikin mutuwar Madam Gloria da Madam Merry, Almustapha yazo har kano ya ɗauki Malam da Malam Liman suka je can abuja, su ka riske Major inda Malam Liman yay masa wa'azi me ratsa jiki, kuma da ya ke yana da rabo, a washe gari ya kwashi ƴaƴansa da jagorancin Malam Liman su ka zo har nan Qatar ya karɓi musulunci daga hannun Sarki Shaik Samim bin Hamad wato sarkin Qatar mahaifi a wurin su Aaliya. yanzu haka Major yaje ƙasa mai tsarki inda ya fara ɗaukan darasi na ilimin addini a wajen Shaik Mufti Mahek, sai muyi musu fatan Allah yasa rabon ya kai su har aljannah. Hirar da Mai Martaba ke yi tasa ce shi da Almustapha, sai Ibrahim da ke sako baki jefi-jefi, kuma su na tattaunawa ne musamman akan wata ma'aikata da Mai Martaba yake son mallakawa Alhassan ita, yake so Almustapha ya shige masa gaba a harkar, tun da shi Alhassan ƙaramin yaro ne, har yanzu da sauransa, duk da cewa idan ka ganshi ba zaka ce masa mai shekara goma sha takwas ba, zaka ce ya bawa shekaru ashirin baya, kuma yaron akwai hankali dan halinsa ma na manya ne, zai iya yin abin da ba ma lallai wani babban yayi ba. gaba ɗaya cikinmu babu wanda ya san da musuluntar Daddy da sauran ƴan'uwana, sai bayan da aka sallami Ya Kabiru daga asibiti, ranar da Mami da Ummi su ka dawo Qatar, a wayar da suka yo ne suke shaida mana da duk abin da ya faru, daga baya kuma Alhassan ke tsegunta min zaman sulhun da Abi yaywa Mami da Daddy, sai dai ko kusa Mami tace ita dai abin da ake tunanin zai faru tsakaninsu ba zai taɓa yiwuwa ba. damuwa ta haska ƙarara a saman fuskata na buɗa baki nace da shi,"amma kai mene view ɗinka akan hukuncin Mami na ƙin amincewa auren Daddy?, ni dai gaskiya zan so ace ta haƙura suyi aurensu, ko dan Allah ya ƙara rufa mana asiri". da ya ke Alhassan A ne, ya saki wata siririyar dariya kamin yace,"ke ki kwantar da hankalinki, batun cewan ma Mami bata son auren Daddy daga baya ne, dan ba kya wurinne, amma da tsab idonki zai hango miki kwantacciyar soyayya a idanun junansu". ban san lokacin da na saki dariya ba, har ina kifawa akan kafaɗar Yagana da ke kusa da ni, nace da shi,"kai dai baka da kunya, iyayenka ma baka bari ba". dariyar ya ke shi ma yace,"hmm to ai bari kiji na ba ki labari, ranar da Daddy zai tafi saudia ina kallonsa da yamma ya tarfa Mami yana lallashinta, na faɗa miki ya koma kaman ƙaramin yaro fa a gabanta, ita kuma sai wani yauƙi ta ke tana cewa wai ita sai ta rama wahalar da rayuwarta da yay, ke ba ki kalla a yanda ta ke maganar ba sak ke idan kina shagwaɓa, ni kuwa na riƙe haɓa nace ikon Allah, ni da Ummi da Akhy Almustapha muna gefe muna musu dariya". a wannan karan dariyar da nayi har da dukan Yagana, ba kuma wai ina sa ni ba, amma ƴar tahalikar nan sai ji nayi ta ɗale min gadon baya babu shiri na miƙe daga kusa da ita. still ban bar dariyar ba nace,"ina jinka ci gaba da bani ina sha". yace,"gulmawuya to naƙi na ƙarasa". "ah yi haƙuri Yayana na kaina". a wannan lokacin murmushi yay mai sauti, yaci gaba da bani labari cikin nishaɗin da muke ciki. "ba ki san me ba, da naga Mami na neman wahalar min da gyatumi ta sa shi kuka sai naje na kutsa a tsakaninsu, ke ba ki kalla wani abin dariya ba lokacin da suka ganni, sai ga Daddy na susar ƙeya wai naje na ɗauko clipper nayi masa aski ance masa na iya aski ni ke yiwa Abi ma, ni kuwa nace masa ai Mami ce uwar ɗakina, ita ta koya min dan haka idan da gaske me kyau yake so to su sulhunta kansu a daren nan gobe a ɗaura musu aure, a tare su ka sakar min ranƙwashi fa, Mami har da murɗe min kunne saboda nace idan ba tsayuwar sulhu su ke ba to a faɗa min gaskiya...ina faɗa maki ma Abi yace da Daddy ya dawo daga umara za'a ɗaura aurensu, ita kuma Mami tace bata yarda ba, ya za'ai sai da za'ai bikin ƴarta kuma ayi nata, Ammi kam tace to ki zauna idan anyi na ƴar taki ta sami ciki ta haihu ayi naki...ni dai ina cin dariyar drama, Malama ki baro wannan ƙauyen kawai kizo a dinƙa yi a gabanki ba kike kirana ina ba ki labari kuma ba kya biyana ko sisi". na kai hannu na goge ƙwallar da ke neman sauko min kamin nace,"ka faɗawa Mami ramuwar gayya da ɗaukan fansa aiki ne na yahudu da nasara, saboda haka ba su dace da ɗan musulmi ba ko kaɗan, manzon Allah da kansa yace kada muyi koyi da su. saboda haka ina roƙonta da tayi haƙuri ta yafewa Daddy nah...ai abin da ya faru a tsakanin rayuwarsu zuwa rayuwar Alhassan da Maryam ɗin da suka haifa wannan tsananin rabo ne da ƙaddara, ƙaddarar da babu wanda ya isa ya kauce ma ta, amma dan Allah tayi masa afuwa kar mu

Chapter 37 of 52