nayi maganar ni da ita mu ka ƙaraso kan tabarmar ina ajiye botikin kokon ita kuma tana ajiye kofunan zuba kokon, ta ke ce min,"wallahi zan fita ne ina so naje jigawa, kin san Babanku kuma ba ya son tafiya da rana, shi yasa nayi himmar gama komai da wuri tun da ke yanzu ba zaman gidan kike ba balle na bar miki aikin". "aikuwa dai kinyi dabara, dan kina kaiwa sha biyu Baba zai ce ba za ki ba. Inna amma dai ba bikin gidan Umman Abbas za'ai ba ko?". "ba shi bane, ita ɗince dai ta kirani kuma ina tsammanin ba zai wuce akan bikin zamu tattauna ba". na ɗan ɓata fuska ina cewa,"Inna kin ce fa idan za kije zamu tafi tare". "kiyi haƙuri sai gaba idan zan koma tukunna...shiga ɗakin Zulai kice ta ba da kwanon abincinta, idan Adawiyya ta tashi ta fito kuci na ku, Sadiya ma tazo ta ɗau nata".
Na shiga falon Inna Zulai da sallama, du ka basa nan su na cikin ƙuryar ɗaki, daga can ɗin na jiyo muryar Adawiyya na faɗin,"Inna yanzu shikenan inaji ina gani sai ta rigani aure ban fara cimma muradina ba, kina ji fa abin da Baba yace wai yau zai ɗaura ma ta aure". Sadiya ta amshe da cewa,"ni gaba ɗaya Adawiyya na rasa gane kanki a al'amarin kishin da kike da Mairo, ina ce dama shi ɗan gidan Sarakan kike so kuma an shiga an fita kin gama samunsa, to mene kuma za ki ɗaga hankalinki akan batun aurenta tun da ba da shi za'ai ba, ke ba dama kika samu na goranta ma ta ba ta auri mutumin da yake kafiri a ada". Adawiyyan ta kuma cewa,"ni fa duk in da za'ace Mairo zata ji daɗi baso nake ba, shi ɗin fa da zata aura ba ƙananan mutane bane, babba ne shi ma dan ubansa shi ne major general na ƙasa ba ki ɗaya kamin yayi retire, wallahi inaji Ya Amadu na faɗar mahaukatan kuɗi ne da su, hatta gidan da suke zaune idan kaje zaka rantse ba'a ƙasar kake ba..me kike tunani idan Mairo ta koma rayuwar can gaba ɗaya?, wallahi sai tafi yanda ta ke ɗin nan kyan gani, kuma bada jimawa ba kiga ana haskata a gidan talabijin, ai ke kin gani ma a vediyon da Ya Amadu ya nuna mana san da tana kafira". a wannan karan da tayi shiru kuma Inna Zulai ce ta amshe da cewa,"Adawiyya idan kika kaini bango zan fita a lamarinki, na faɗa miki ki bar asarar hawayenki ki zuba ido ki gani idan auren zai tabbata, na faɗa miki muddin ina raye rayuwar yarinyar nan a wahala zata ƙare, bana faɗar abin da ba zan cika ba, ba kuma na tunkarar abin da ba zai kaini ga nasara ba, a wanne dalili zan zuba ido ina ganin su na ci gaba ni kuma rayuwar tawa ƴaƴan a dakushe kullum, ƴaƴana su ƙare a auren manomi, ai ba zai yiwu ba...wannan kuɗin da ku ka ga na karɓa wurin Amadu naira dubu hamsin ƙar ya nayi masa da cewar zanja jari, boka zan kaiwa ya magance mana komai, yanzu nan zan shirya na wuce dan a kammala aiki da wuri, yau ai sai dai Malam yaji kunya a idon jama'a, dan sai jama'a sun gama taruwa yaron zai zo yace ya fasa, ban damu da duk ƙananun maganar mutane da za su biyo baya ba tunda ba akan ƴaƴana bane". naja numfashi nai tattaki na ƙarasa bakin ƙofar ɗakin, sannan na buɗe baki na kwarara sallama, hakan kuma yasa su kai tsit da abin da suke son ƙara cewa.
Inna ta taso ta fito tana washe min baki da murmushin makirci, na tsuguna na gaisheta. "yau da sassafe haka, ko kun yi halin da ƙawar taki ne?". nace da ita,"a'a Inna ai anan gida na kwana. dama Inna ce tace ki bada kwanon abincinki tana sauri zata fita ne". "to shikenan bari na ɗauko miki". ta faɗa tana komawa cikin ɗakin, na ƙara cewa da ita, "Inna su Adawiyya sun je makaranta ne?". "a'a kin ganta anan tana aikin kukanta na gaira babu dalili, na rasa uwar da akai ma ta". na saki murmushin da ya fitar da sauti ina cewa,"ke dai Adawiyya kin shiga uku da damuwa, to idan kin gama kukan ki fito muyi break fast...Sadiya kema Inna tace kije ki ɗauki naki". Adawiyya ta fito jikinta a sanyaye, fuska duk ta kumbura saboda kuka. "ai gwara ni sau dubu akanki, idan ina ciwo bana kwakwazo". a wannan karan dariya nayi bayan na amshi kwanon abincin da Inna ta miƙon, na yi gaba ina ce ma ta,"ai kuka yanzu kika soma indai ba za kisawa zuciyarki haƙuri da salama ba...kuma ki sauri ki fito dan tafiya zanyi gidan Yagana".
abincin muke ci amma gaba ɗaya na lura cin dole ta ke yi masa, damuwarta ta fito fili ƙarara ta kasa ɓoyuwa. bata san tawa damuwar taci uwar tata ba, hasalima ni ƙatuwar matsala ce dani da ban san ta inda zan tunkari al'amarin ba, al'amarin shirinsu na kunyatar da Baba akan fasuwar ɗaurin aurena. tabbas nasan duka zuciyoyinsu babu imani, musamman Inna da idan tace zatayi abu to sai ta aiwatar hankalinta ke kwanciya, tunani nake kamar naje na sami Baba na faɗa masa ko kuma na faɗawa Innata, to amma kuma idan na faɗa ɗinma babu amfani, dan babu me yarda da maganar da babu shaida.
a can gidan Yagana tun da na shiga na sameta tana bacci na kwaso kayan wankinmu na fito da su, a cikin kayayyakin da Ya Kabiru ya siyo min na ɗauko wani sabulun wanki me ƙamshi, ina wankina ina sauraron karatun ƙur'anin da aka saka a gidan radio ina binsa, da yake izu talatin ɗin ƙasa ne kuma mun sauke a makarantar allo, sai naji zuciyata ta fara washewa daga dukkan damuwarta da fargaba.
na gama shara na fito daga wanka sai ga Saddiqa ta shigo, na tafi da ɗan saurina na rugumeta ina yi ma ta oyoyo. Saddiqa sabuwar ƙawar da nayi ne a lokacin rasuwar Gwaggona, jika ce a wurin Baba Lami a kano su ke tazo hutu ne gidan Malam Liman. mun sha hira sose da ita kafin ta tafi, sallama dama tazo min akan zata koma gida hutunsu ya ƙare, hirar da mu kai da ita duk sai ta ɗebe min kewa, tana ta bani labarin makarantar bokonsu me su na turkish international school, kuma naji makarantar ta burgeni sosai har na ƙudurta a raina zance Ya Kabiru can za'a kaini, tun da dama har yanzu yana tunanin wadda za'a kaini ne, shi da Ya Amadu sun ce sun fi son private school me kyau da inganci, wadda ba za'ayi dana sanin biyan kuɗinta ba, kamar dai irin ta su Adawiyya, amma ni basa so nayi bording saboda matsalar idona da kuma firgita da nake yawan yi cikin dare.
"ke ƙaro mana radiyon nan". Yagana ce ta faɗa tana daga zaune tana karin kumallon da Saleh ya kawo ma ta yanzu, babu yanda banyi da ita ba ta ɗauki sabon brush ɗina ta ke amfani da shi taƙi, wai ita tafi ganewa gawi ko kuma tasa ruwa ta kurkure bakinta, ita bata yarda da wannan abin me yaji na bature ba, haka kawai ya ɗaɗe ma ta dasashi, ko kuma shi brush ɗin ya karya ma ta ƴan haƙoranta da Allah ya bar ma ta.
"ku guji munafurci domin yana daga cikin manyan kaba'irai, wanda Allah SWT yaywa masu yinsa tanadin wutar jahannama. a littafinsa me tsarki yana cewa,"innalmunafikina fil darkil asfali minannar, fabashshirhum bi'azabin azim". munafurci yana nufin cin naman mutane, ka ɗauki zancen wani ka kaiwa wani, ka haɗa husuma a tsakanin mutane da kuma zama da mutum da zuciya biyu...". wa'azin da ke ta shi ta cikin radion kenan daga bakin wani Malami, kuma jiyo sallamar Ya Amadu daga waje yasa na rage sautin radiyon ina amsa sallamarsa, dan Yagana tuni ta tada sallar wadha sallar da bata wuceta, ni kuma kasancewar cikin jini shi yasa banyi ba domin nima bata wuceni, dan na koya daga wurin Gwaggona. "tsohuwar gidan nan sai ki dinga wani ƙunshe kanki a ɗaka kamar wadda taiwa kishiya laifi, aita kwaɗa sallama ba ki sa ni ba, ranar da wani ya shigo yayi wuff da turken awakinki naga ta tsiyar ƙunshe kai kamar daddawar ɗaƙa". maganar yake yana sanyo kansa cikin ɗakin, tun da yay maganar za'ai wuff da awaki Yagana ke tai masa gyaran murya, sarai yasan da shi ɗin ta ke, dan har ya zauna dariya yake ƙasa-ƙasa. na duƙa na gaishe shi kamar wata munafuka, dan ni Allah ya gani ina matuƙar shayin wannan bawa nasa, ya amsa min a daƙile, ban damu ba inda sabo mun saba.
"za kiyi baƙo zuwa anjima, ai na zai zo ya sameki?, danni yanzu kano zan je". maganar a ƙasaƙasa yayi, na fahimci ba ya so Yagana taji, na haɗiye wani yawu a maƙoshina da ya wuce min da ƙyar, kamin na ba shi amsa da cewar,"ya sameni a can gida". Yagana ta sallame daga sallar lokacin ta juyo tana shafa adu'a, adu'ar da ko yinta ba ai ba saboda sababi na cinta. "Amadu fata na gari lamiri, kuma insha'Allahu babu abin da zai sami awakina, in dai ba so kake mu sami saɓani da kai ba to ka daina ja musu jafa'i...na rasa wannan abu duk abi a sawa al'amuranka ido, alhalin kai baka damu da bawa ba, ni acikin jikokina ma mantawa nake da kai, dama kai ba mutumin da za'a iya zama da shi ba ne, Uwarka ma ban da ƴar kanta ce ai da tuni kasa ma ta hawan jini da wannan tsinannan miskilancin naka da na rasa aina ka gado shi, kana ganin ɗan'uwanka Kabiru fuskarsa kullum a sake duk wurin da ya shiga faran faran da shi, amma kai duk wanda ya zauna tare da kai sai zaman ya gundure shi, sai kayi wani gumm kamar wanda ke fama da cutar warin baki...Allah ya gyaraka, amma ka sauya hali ni shawara nake baka, idan kayi aure a haka Matarka yaji zata dinga yi".
yay murmushi yana cewa,"Hajiya Yagana ikon Allah, ai daɗi da ke a tsiya da ke". sai da ta gama jan carbi kan tace,"ka rabani da tsiya dan wannan kalmar a gindin Zulai ta ƙare, ahh tou".
yace,"Yagana wai ba kya kara ne?". sai ta ɗaga murya tana faɗin,"har Uwarka fa ta gama cin amarcinta bata taɓa kawo min farantin shinkafa da sunan abinci ba, ƙarshe ma sai cewa tayi ita ba zata iya girki da uwar miji ba...da labarin yazo kunnena naje har gidan na cashe ma ta, sai da taga ina da iko da igiyoyin da ta ke taƙama da su sannan tasha jinin jikinta dani ta hankalta...Amadu ba wannan ba ma, yanzu me ya kawoka gidana da sanyin safiya haka ko gama wartsakewa ban ba?". na dubi agogo naga har ƙarfe sha ɗaya da rabi amma ta ke kiran sanyin sassafe.
ya ciro kuɗi a aljihu ya miƙa ma ta,"gashi kici goro, sallama dama nazo yi miki dan gobe jirgin sassafe zan bi". "to kuma sai a kace maka babu rana babu dare da ba zaka iya biyo wannan lokacin ba tunda sallamar ta zama dole a wurinka". ta karɓi kuɗin,"to an gode Allah ya shi albarka, yasa afi haka. dawowa ta gaba dai sai a dawo da himmar aure, zaman ya isa haka in ba so kuke ku shiga sahun tuzurai ba, sa'anninku duk sun tara ƴaƴa jiyama sai da naje sunan matar Saddiqu". yace,"Yagana ai mu da sauranmu har yanzu yara ne, shekara 33 fa kacal". ta kwaɗa wani salati tana riƙe haɓa da cewa,"ina zancen yara anan, kana ganin yanda Kabiru jin daɗi da hutu ya maida shi wani babban mutum, jiya fa da na dawo daga unguwa na shigo ɗakin nan na tarar da shi sai na zube ina kwasar gaisuwa ce nake wani babban me faɗa aji ne a ƙasar nan, ko fa fitila ban kunna ba jiya a ɗakin nan saboda yanda hasken fatarsa ya gauraye ɗakin nan, ƙamshi kuwa kace shi ne kamfanin turaren, baka ji ba daka shigo?...to shi matsalarsa ɗaya hannun ɓera gare shi, shi yasa ban cika son zuwansa gidana ba". bani kaɗai ba, hatta Ya Amadu sai da yay dariya, dariyar da ta lotsa dimple ɗinsa har ciki, ita kuwa kamar ba ita tai maganar ba, tana ɗaure kuɗin da ya bata a gefen zani ta ƙara cewa,"ba batun dariya bane Amadu, in dai Kabiru ne yana da halin ɓeraye shi yasa ma yau zanje wajen Malam Kabiru ai masa rubutu ya samu yasha kamin ya koma, kar yaje can ya ɓallo mana wani ɓallin...jiya fa da zan fita Zannira ta min aiken tuwon masara da lafiyayyar miyar kuka taji man shanu, na tura abuna ƙasan buhun can saboda ma kar Yarinyar nan ta shigo ta ganshi, ashe ajiyar banza nayi, dan ina dawowa na tarar da ɗan banzan yaron nan ya gama aikawa da shi cikinsa, kai kuwa Amadu kace min Kabiru bai kamu da cutar ɓeraye ba, dan su ne masu zaƙulo ajiyar da ba tasu ba...kuma fa saboda rashin kirkinsa ya kai intaha ko haƙuri bai bani ba, sai ma mita da yake min wai nayi shiru kansa na ciwo. ni kam Rakiya ai na gaji da zaman Kabiru, lokaci yayi ya koma can dama ni bamu samu haɗuwar jini da shi ba". na buɗe ba ki nace,"Kai Yagana, da Ya Kabirun ne ba kwa jituwa?, ranar fa da ya kawo miki gasashshiyar kaza kika ce kaf jikokinki kinfi ƙaunarsa". ta waigo ta ɓalla min harara,"aku uwar magana wa ya saka da ke?...wannan ai haɗa fitina ne baccin yanzu kika gama jin wa'azi, irinku ne masu ji basa aiki da shi. ni Kabirun ma ya shigo ya san yanda zai yi a haɗa da ke a tafiyar su Adawiyya ku koma tare, ba zai yiwu ki dinga haɗani da mutane ba...fisabilillahi yanzu ai sai kisa Amadu yaga baƙina, ya ɗau kuɗinsa dubu biyu ya ban kuma kina wani batu na daban, ke dai sam baki da hali kina da ƙatuwar matsala". dariya kawai Ya Amadu keyi, kan ya bata labarin musuluntar Emanuel, ta kuwa bushe da dariya har da kifawa,"shegiya ƙaniya! ɗan banza duk yanda akai mafarki yay ana cin ubansa a ƙabari har aka hasko masa zurfin gidansu shi yasa ya karɓe kalmar Shahada da wuri...to na masa barka, idan ka koma ka miƙan gaisuwa kace ina gaishe shi tunda yanzu ya zama namu".
Ya Amadu zai tafi Ya Kabiru ya shigo, tun daga tsakar gida da Yagana ta jiyo sallamarsa ta ke kiran,"ɗan halak kaƙi ambato, ɗan albarka shigo ka ganni da baƙin asuba kamar korarru". ya shigo ɗakin yana amsheta da tasa tsiyar shi ma. sanye yake cikin coffee ɗin yadi me ƙaramar riga, yay kyau sosai a cikin ɗinkin, sai zuba ƙamshin da Yagana ke faɗi yake, yana sanye da baƙin glass ɗin da ke ƙara ƙawata kyawun halittar fuskarsa. ya ƙaraso ciki yana sawa Ya Amadu ƙafa kamin ya wuce inda Yagana ke masa nuni da kusa da ita. "Matar ya dai?". ya faɗa yana taɓa kumatunta. ita ma ta shafo fuskarsa tana koɗa kyan da yayi, har da cewa ba zata bawa yarinyar ƙauye shi ba, idan ya koma yaga ta aure a can ya aure kawai. sai kuma tace na shiga ɗaki na ɗauko mata ƙwaryar zuma, na kawo ta karɓa ta dire a gabansa tana faɗin,"Zuma ce farar saƙa, jiya bayan fitarka Mujibu yay min aikenta, ko sha banyi ba nace sai ka fara sha tun da nasan kai ma'abocinta ne, sha kaji me kyan ce". ta faɗa tana gutsurowa ta kai bakinsa ya karɓa, ni dai kallonsu kawai na ke ina murmushi, kuma kallon bana Yagana bane na Ya Kabiruna ne, da kallon na sa ke hadda tasirin wanzuwar wani abu a tare dani da ban san ko menene shi ba. ban san lokacin da wata dariya ta suɓuce min ba har da ƙwalla, lokacin da Yagana ta tura ƙwaryar zumar gaban Ya Amadu tana faɗin,"ga shi nan uban kwazazzafa sai ka gutsira, in faɗa maka Kabiru tun da ya shigo ya dameni wai dole sai na ba shi ai kai ba sai kasha ba, naƙi nace kai na ajiyewa, shi ne fa dalilin wannan uwar harar daka ga yana watsa min...dama tun kuna yara haka yake sai a zuba muku abinci ya wawashe ya barka da ƴar ƙaramar murya kana kuka, ƴaƴan Zulai ai akwai cin tsiya cikinsu a buɗe yake".
tabbas Yagana sai ta kashe auren da ke da soyayya ma, ba mara soyayyar ba, yanka sharri a wurinta ba ya da wani wahala, kuma idan tana yi sai ta ɗaure fuska ka rantse da gaske ta ke, duk tabi ta ɗaure mutum da jijiyoyinsa. da taga yanda Ya Amadu yay kicin kicin sai ta bushe da dariya tana faɗin,"Allah sarki Amadu, Allah ya jiƙanka ba dan ka mutu ba...kai Kabiru da wasa nake yi, kar naje ya ƙullaceni idan ya koma garin arna yasa su ɗaure min baki na shiga uku". kiran sallar azahar ɗin da akai ita tada su Ya Amadu suka fita zuwa masallaci, sai can Ya Kabiru ya dawo shi ɗaya lokacin na gama kwashe shanyarmu zan shige ɗaki, na rasa dalili, na rasa me yasa yanzu indai na gansa sai na ke jin ina faɗawa cikin wani irin yanayi me wuyar fassaruwa, gabana yayta faɗuwa. har ya iso gabana ban sani ba, dan nayi nisa a zuzzurfan kallon da nakewa bakinsa da ke motsawa da salon murmushi, ya lakuce min hancin yana faɗin,"kallon fa?". nace,"Ya Kabiru nima ka sammin abin da kake sawa kana ƙara kyau". murmushi yay ya kama hannuna da ba kayan, mu kai ɗakin Yagana. "duk kyauna ai ban kai Balarabiyar da Gwaggo ta haifa ba". a san da nake ajiye kayan nace,"tab ana cewa yanzu nafi kama da inyamurai kana haɗani da larabawa". "inji uban wa?". ya faɗa yana ɗaure fuska kuma yana tsareni da ido. su Sadiyya naji su na zancen, yanzu kuwa idan na faɗa masa ai babu wanda zai hana shi ɓaɓɓala ƙasusuwan yarinya a yau, dan haka sai na fizge da faɗin,"a jikina kawai nake jin kamar mutane za su ke faɗan hakan". har yanzu bai saki fuska ba, kuma bai bani amsa ba, sai ya kamo hannuna ya zaunar da ni a kusa da shi kamar wanda zai ɗorani a saman cinyarsa, kafin ya ɗora bayan hannayena akan tafukan hannunsa yana bin su da kallo.
"wancan ranar na faɗa miki fatarki bata son wanki karki ƙara, ashe baki ji ba, shi ne har da yin wanki me yawa haka". muryar tasa ta fito cikin sautin faɗa yana me shafa fatar wurin da ta kusa ɗaɗewa, ƙwarai an jima ana faɗa fatar jikina bata son wahala, shi yasa ko lokacin da Gwaggona na raye ban fiya aikin ruwa ba, aiki ma ko da Ya Amadu ya raba mana shara aka bani, idan kuma za'ai wankin yara ni na ke shanya, aikin taɓa ruwa ba ya wuce irin ɗan kaɗan ɗin nan. Yagana ta sako baki,"to kai an faɗa maka wannan yarinyar tana jin magana ne bayan ta zuciyarta". sai ya ɗago ido ya dubeni, ni kuwa Allah yaji ya gani ina cikin wani hali, dan yanzu ko ido bana son haɗawa da shi, tun da Ya Kabiru ya soma shafa fatata da tai ja ta ɗaɗe naji numfashina ya katse a ƙirjina.
"kin yi amfani da Sol de Janeiro Coco Cabana?". sai da nayi ƙoƙarin saita tunanina kan na kaɗa kai na amsa masa,"a'a, wanda na buɗe ma ai bai ƙare ba". a yanzu cikin ƙwayar idona yake kallo kamar me son karanto wani abin, sannan yace,"je ki ɗauko". na miƙe jiki kamar mara laka na shiga uwar ɗakin Yagana, na ɗauko akwatin da ya shaƙo min ita da tsaraba da zai dawo, na buɗe na ɗauko cream ɗin da yake nufi, sannan na fito na ba shi. ya ɓare robar sannan ya shafa min man a hannuna. "yau ta zama rana ta ƙarshe da zan ƙara ganin kinyi wanki da kanki. idan ke ba kya ƙaunar lafiyarki to akwai wanda ya damu da ke, ya kuma damu da lafiyarki, ya kuma ƙi jinin duk abin da zai taɓa masa lafiyarki". a wannan karan muryar tasa a hankali ta fita, murya da ta shiga bin kowacce jijiya ta jikina tana neman ƙassara ɗan sauran kuzarin da ya rage min. yawu kawai na haɗiya na kaɗa kai wajen ba shi amsa. har yanzu dai bai saki fuskarsa ba, sai ma ƙara tamketa da yay, ya ɗauke wuta kamar babu shi a wurin, nima na kasa wani ƙwaƙwƙwaran motsi, sai bugun zuciyata da ke ƙara tsananta, na kai yatsa zan goge ƙwallar da ke neman saukowa, sai dai kamin na kai ga hakan hannun Ya Kabiru me ɗauke da hanky ya goge min. na kalle shi naga yana kallon wani gefe na daban. a raina faɗi nake na shiga uku, wai zuciyata wacce iriyar zuciyata da bata da lissafi, Yayana ne fa, Yayana da mu ke uba guda, amma ta ke wani ƙazamin tunani akansa. na zuƙi wata iska me ɗumi sannan nayi ƙoƙarin ture dukkan wani abu da tunani ke haddasa min shi a raina, na gyara zamana na saƙala hannuna ta cikin hannunsa, ina leƙen wayar da yake shafawa. "lectures ku ke?". "umm". ya bani amsa a taƙaice, ni kuwa nan duk neman shiri nake yi. a lokacin sai na tuna da lambar wayar Saddiqa da ta bani ɗazu, na ɗauko ina ce masa,"Ya Please save this number for me, ta ƙawata ce ina so na kirata zuwa anjima naji if she arrives home safe and sound". wayar kawai ya miƙo min bai tankani ba, na karɓa nayi dialling sannan nayi saving na miƙa masa. "taki ce ai". jin abin da yace na gyara zama babu shiri, na kai hannu na juyo da fuskarsa da ya kauda gefe, bakina yaƙi rufuwa saboda murna. "you say what?, Ya cewa fa kai tawa ce?". na tambaya ina jujjuya wayar da nasan tasa ce, mamaki ya lulluɓeni a san da ya fito da wata daga aljihunsa, iri guda exactly da ta hannuna, sai yanzu na lura ta hannuna tafi tasa sabunta, sai na saki baki nama rasa wanne irin farin ciki zanyi. na shiga kwararo masa adu'a kamar yawun bakina zai ƙafe, sai kawai ya miƙe yay ƙofa yana faɗin,"ban siya dan ayi shirmen banza ba. research only". "an gama Yayana na kaina, Allah ya jiƙan mahaifiya yasa afi haka". daga haka kuma ya fita.
*Abuja, 12:00pm.*
tun zamansu a dining dan yin break fast idon Madam Gloria ke kan Emanuel, da dukkanin tunaninta na son gano abin da ke damunsa a kwanaki biyun nan, wani abu na damunsa, kuma yana ɓoye wani abu, tabbas tasan da hakan domin ba haka yake ba, shi mutum ne me walwala amma a cikin kwanakin da suka shuɗe taga duk ya sauya, koma ta kira canjin nasa da tun ranar da shegiyar yarinyar nan ta bar gidan, alƙawari ne tayiwa kanta in dai ɗanta ya sami matsalar damuwa akan yarinyar to tabbas sai ta shafe rayuwarta da rayuwar ahalinta sun zama tarihi.
ta ƙara tabbatar da akwai matsala tare da shi tun san da aka zauna don cin abincin, amma shi ya kasa ci, illa aukin juya fork ɗin da yake akan wainar ƙwan. tayi gyaran murya hakan yasa duka yaran suka karkata hankalinsu kanta hatta kuwa Granny, yau babu Dad ya tafi wata seminer a can india.
"baka da lafiya ne?". ta tambaye shi idonta a kansa, sai ya girgiza ma ta amsar a'a. "to mene ka tasa abinci a gaba kaƙi ci?". ya shafi gashin kansa ta baya yace,"ina tunanin meeting ɗin da zamuyi a gobe ne". ya faɗa yana miƙewa yaja kujerar baya, agogon hannunsa ya kalla yaga ƙarfe sha biyu an kusa sallar azahar ma kenan, cikin dabara yace da Mom ɗin,"i want to rest, zan kulle ɗakina kar a dameni". baki kawai ta taɓe ta bishi da ido har ya haura sama. tunda ya shiga ɗakin yasa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 52