Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *AUREN WATA UKU.!* *01* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* _Rayuwa tana zuwa ma bawa ta fuskoki daban daban cikeda jarabawa had’ida K’alubale. Ashe wasu mutanen Akan k’addarosu cikin rayuwan bawa ne matsayin jarabawa. Ashe Akan jarabci ‘ya’ya da nasu iyayen kaman yanda wasu ‘ya’yan ke zamtowa jarabawa ga iyayensu. Shin su waye ka tashi ka sani matsayin ahali.? Shin a ina k’alubalen take.? A ina gwagwarmayar take..? Tabbas wasu mutane da suka zamto jigo na rayuwar d’an Adam ka iya zama babban jarabawa a gareshi. Shin muna hak’uri da jarabawarmu ko kuwa dai bijirewa muke ga d’inbin rahamar Ubangijinmu garemu..? Bari mu tsunduma cikin labarin AUREN WATA UKU dan jin yanda ta kaya tsakani wasu ahali_ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.! Kano State, Nigeria. Gida ne da za’a iya kiransa da gidan gandu sakamakon ahali guda dake rayuwa cikin gidan. K’ofofi ak’alla kuwa zasu kai takwas koma sufi. Yayye da k’anne dama makusanta na kusa wanda sukeda hakkin mallaka suke rayuwa cikin gidan. D’aya daga cikin k’ofofin anyi cincirindo ana kallon abinda ke wakana. Dama dai abin kallo, magana harma da tsegumi basa kad’an a gidan yawa. Ba komai akai cincirindo ana kallo ba sai akwatunan da ake fita dasu sahu sahu matan da sukazo kwasan kayan suna tofin Allah tsine. D’aya matar ta kuma janyo k’aramar akwatin da k’arfin gaske kaman zata tsinke hannun jakan. Fad’i take “Alhamdulillah Allah Ya tsami d’anmu daga k’angin gori.. Me za’ayi da gayyan tsiya. Wllhi d’anmu yafi k’arfin wann sharan. Yaro d’an dangi, inyi.. Ina dalili.? Yarinyar da kowa Ya kwana da sanin sau babu adadi kenan ana amshe sadakinta. Kawai sai shi Zubairu sabida baida mafad’i mu bari Ya aureta.. Toh wllhi sam bazata saku ba wai bindiga a ruwa ehe.. Banda ma dai bani k’asa ina can birnin Saudiya da ina zan bari wann zancen banzan yayi nisa har akaiga kawo lefe..?” Ta d’anyi fasali tana kuma wangale bakinta yanda hakwaran makka har biyu suka bayyana cikin bakin nata, ta ko wani angle walwali yake. “Aure dai mun fasa shi bama gayyan tsiya cikin zuri’armu..” Ta k’arashe d’aya matar da suke tafe tare tana tayata da fad’in “Wann gaskiya ne Hajjaju. Ai dama cewa nai kina dawowa za’a wargaza komai dama ganin babu idonki ne.” Hajiya Dudu ta cab’e “Toh na dawo sai naga uban da zai d’aura wann gantalallen auren..!” Ta k’arashe k’iiii tana janyo trolley guda. Wata mata ce da tin shigowan matan take sharb’an kuka an rasa mai bata baki ta isa da sauri ta rik’o hannun wann gabjejiyar matar. Cikin muryarta dake fita da kyar sabida kukan da taci take fad’in “Hajiya Dudu dan Allah dan Alfrman manzo Sallallahu alaihi wasallama ki rufa min asiri.. Kar ki bari a fasa auren nan.. Ki ceci d’iyata dan Allah..” Bata kai aya ba matar ta fincike hannunta tana ci gaba da huci had’ida aika mata muguwar harara ta gyara zaman mayafinta “Ke Suwaiba bari kiji na fad’a Miki wllhi idan ‘yarki itace autan mata Zubairu bazai kwashe ta ba.. Uban wa yasan abinda yasa ko wani manemi ke gudun ‘yarki.. Haka kawai a tashi a lik’a ma namu d’an.. Toh gari da yawa ga ‘yammata birjit masu jini a jika ba irin ‘yarki da ta girma ta rik’a ta tsofe gida ba.. Ke bari ma kiji cikin dangi zamu samar wa Zubairu matar aure dan gida bai k’oshi ba baza’a kai waje ba. Wajen ma ma bola shara irin ‘yarki..!” Tana ida fad’in haka ta fincike hannunta tana fad’in “Zinaru muje kinji kafin tsautsayi Ya hau kan kayan nan dan wllhi abu d’aya yayi ciwo tass sai an lale an biya.! Daga nan ma gidan Hajiya Atine muka nufa da kayan nan.. Ayyiriri D’anmu zai angwance da ‘yar dangi ba ‘yar bakin ruwa ba..” Haka suka fice suna guda suna watsa habaice habaice. Matar da suka ambata da Suwaiba ta duk’a nan wajen tana cazgan kuka hannayenta biyu aka fad’i take “Na shiga uku ni Suwaiba Ina zan saka raina inji sanyi da wann bala’ai..” Wata mata da ta d’an data dan ga dukkan alamu tafi ta tsugunnen a haife itace tai karaf ta cab’i zancen nata “Ohni Tani naga ikon Allah.. Aure ace ak’alla goma kenan ana karban sadaki ana anshewa idan ban b’ata lissafi ba.” “Yaya bai Kai goma ba..!” Suwaiba dake duk’e wajen ta fad’i cikin gunjin kuka. Tsaki Tani tai “Kayi magana ace kishi, na baki shawari ki d’auki yarinyar nan ki kaita baki ruwan Aljanun ruwa ne suka aureta amma kink’i ji kink’i d’aukan shawarina Suwaiba.. Waima har zigaki ake ana ce Miki ni ce nan nai ma ‘yarki asiri na hanata aure.. Toh ai idan ma asirin nai mata yazo gidan sauk’i sai ki d’auki k’afa kije gidan malamai a kwance miki sammun..” Ta kece da dariya had’ida rangad’a gud’a “Ayyyiriri nanaye Ayi dai mu gani.. Mun zuba ido mun baje kunnuwa..” Ta k’arashe tana gyara d’aurin zaninta da Ya karkace. Su kaw sauran al’umman gidan dake tsaye suna bama idanunsu abinci tuni Sun soma tsegunta lamarin. * Cikin tsanaki ‘Yanmatan guda biyu ke takunsu gefen kwalta. Kallo guda zakai masu ka fahimci ‘yanuwan juna ne sakamakon kamanni ta fuskan halitta da su biyu din suke dashi. Babban zata Kai kimanin shekaru 31 a duniya amma bazaka fahimci hakan ba sabida kyaun kira da Allah yayi mata. Sama bazakai zaton ta girme ma k’aramar wacce keda kimanin shekaru 20 a duniya har sai ka kula sosai. Sun karyo kwanan layinsu kenan suka hango wasu mata guda biyu jikin ginin wani gida Wanda garun baida tsawo sann duk ya murmushe abinka da ginin bani bani, idan da zakai tsalle d’aya zaka iya kamo katangar. Wata mata ce da d’aurin k’irji daga nan cikin gidan ta dafe katangar ta lek’o suna tattaunawa da matan nan guda biyu dake daga waje. Aiko matar dake lek’en katangar da d’aurin k’irji tana hango ‘Yanmatan ta soma yima sauran biyun magana a hankali tanai masu nuni da ‘yanmatan da idanu. Tanai masu zindensu. Gaba d’aya suka juyo suna duban ‘Yanmatan. Sun kusan cimmasu k’arama daga cikin ‘Yanmatan tace “Adda Kinga magulmatan matan nan wllhi nasan bazai wuce zancenmu suke ba. Jibi yanda suke kallon mutane kaman mayu. Su ko kunya ma basa ji da girmansu da aurensu suna halin banza. Mtsw Allah ya kyauta halin matan unguwan nan. Mazajensu suna ficewa suma suke tafiya yawon gulma.” Babbar ta murmusa tace “Ke wa yace miki gulmarmu suke.. Nidai dan Allah bana san tashin hankali Khulsum, nasan halinki sarai.. Gaisuwar fatan baki ya wadatar..” Khulsum tace “Wllhi Adda ko kaffara bazanyi ba zancenmu suke. Tinda muka karyo layin nan suke mana kallon k’asa k’asa kuma wllhi mata tai mana zancen banza zataji babu dad’i tinda dai matan unguwan nan basu San su rik’e girmansu ba.” Babban ta d’an tsare fuska “Ya isa Khulsumu. Kar ki sake cewa komai. Na san halinki sarai.. Kar ki ma wata mata magana cikinsu balle su samu abin tofawa.” Khulsum tace “Ahaf wllhi Adda kema kinsan halina ba yanda za’ayi mata ta gaya mun bak’a na shanye ban rama ba. Ai sai nayi ciwo ma.. Tab.!” Ita dai babbar bata kuma cewa komai ba sai girgiza kai da tai dan haka nan take ba mai yawan hayaniya bace. Koda suka iso daidai yanda matan suke Babbar ce ta bud’e murya ta soma gaishesu cikeda girmamawa. Suka amsa yayinda Khulsum ta bisu da idanu. Har sun wuce d’aya matar ta bud’e murya tace “UMMULKHAIRY..” Daidai lokacin babba daga cikin ‘Yanmatan ta juyo tana dubanta “Na’am Maman Sahal..” Matar ta murmusa tace “Ya batun aure ne wai.. Shiru shiru har yanzu ga Ummikhulsum har ta taddoki kodai tare za’a had’aku ne.?” Kafin Ummulkhairy ta kaiga bata amsa suka sinkayo muryar Khulsum tana fad’in “Maman Sahal nace ba, idan gadon katako kikayi, to dan Allah ki canza kiyi na k’arfe kar ruma ya kama ko tsari da gara suci..” Maman Sahal sai tai murmushi tana neman maida abun barkwanci “Oh su Khulsumu ba’aji ayi shiru.. Ai tambayan Alheri nai ba sai kin fad’a mun bak’a ba.” D’aya matar dake lek’en Katanga tai karaf tace “Aff Lallai maman Sahal jaridu suna wuce ki kwanan nan, bakida labari har lefenta fah an kai kwanaki uku da suka shige.” Ummulkhairy ta had’iyi abinda ya tokare mata mak’oshi had’ida aika ma ‘yaruwarta ummukhulsum mugun kallo. Ta shiga janyo hannun Khulsum zasu shige Khulsum ta kuma dogewa dan bataji bata mayar ba kaman dai yanda Maman Sahal tace. Khulsumu ta murmusa tace “Kinji abokiyar gulmar taki ta baki amsa.. Ina kika makara baki sai jaridar ba.? Ko kudin sayan ne bakida shi na ranta Miki..?” Nan fah Maman Sahal taja da baya ta Ware idanu tana nuna Khulsum da d’an yatsa “Ke kul wllhi ahir d’inki.. Koda wasa kar kimin rashin kunya ni ba sa’arki bace..” D’aya matar ta bud’e murya tace “Wai dama Maman Sahal wa ya aikeki dogon hira da wann maras kunyar yarinyar.. Yarinyar da sam batada ta ido, ba ganin kowa take da gashin ido ba. Tanaji tana gani mata masu hankali ma yanzu ba auruwa suke ba ballantana ita maras kunya wacce bata mutunta kowa. Bazata d’auki darasi akan Yayarta ba. Kowa yayi shaidan Ummul a unguwar nan batada abokin fad’a tun tasowarta amma gashi nan ta kasa auruwa.. Sai anzo kaman za’ayi aure zance ya lalace. Ita wann kam inaga ba jinga ba saidai tayi bandaro ma.. Dan idan Har ba’a d’auki mai hankali ba banji za’a d’auki fitsararriya..” Khulsumu kaw kafin matar nan ta rufe baki ta bata amsa da fad’in “Ai tinda mata gantalallu irinku basu rasa masu kwasan su ba bana Jin akwai kalar macen da bazata samu mijin aure ba.!” Haba Nan fah Maman Sahal da gang d’inta suka nufo Khulsum Ummul na tsakiya tana janye Khulsum tana bawa su Maman Sahal hak’uri Wanda kaman zugasu take. Fad’i suke sai sun cire ma Khulsumu rashin kunyarta. Itama Khulsum d’in sai tsalle take tana fad’in dik matar da ta fasa dukanta ta raina Wanda take zaman aure k’ark’ashinsa. Ana tsaka da wann kacaniya suka hango mata da akwatina nik’i nik’i aka sun dososu sahu sahu sai bala’i suke suna fad’in d’ansu bazai auri annoba ba. Aiko nan suka ja wani wawan birki sakamo hango su Maman Sahal da k’awayenta d’aya da d’aurin k’irji sai tsalle suke yunk’urin cakumo Khulsum ga Ummulkhairy a tsakiya sai kuka take tana rok’onsu suyi hak’uri.. Garin janye Khulsum akaI watsi ma Ummulkhairy da mayafi ya fad’i gefe had’ida fincike mata d’ankwali tuni sumarta ya bayyana. Salallami suka fara Hajiya Dudu tana masu nuni da su Ummulkhairy tana fad’in “Kunga abinda nake fad’a maku ko. Allah dai ya ceci Zubairu bazai yanka kazar wahala ba balle ya fige. wann ba matar aure bace. Sauran matan suka shiga salati suna fad’in Sun shaida. Hajiya Dudu ta kuma danna wayarta a kunne tana fad’in “Halo kai Zubairu nace wai kana ina ne haka da ka kasa k’arasowa..? Toh maza maza ka iso.. Alhamdulillahi tinda kana kusa ka gane ma idanunka. Kai sauri nace Jarababben banza..!” Tana Ida wayan taci gaba da fad’in “Alhamdulillahi ai ni naji dad’i gwara dai yazo ya gane ma idanunsa.. Da banyi da gaske ba bazai bari azo a amshe kayan nan ba.. Toh gwara ya k’araso ya gane ma idanunsa. Me za’ayi da mace mai dambe a titi..!” D’aya daga cikin k’awayen Maman Sahal kaw tana hango su Hajiya Dudu da akwatuna ta saki shewa tana gud’a tana jero baitukan ayye mama ayye mama har zuwa da aure yana raka aure da na biki mun tafi tare. Haba nan fah waje ya kuma kacamewa kan kace mai anyi caa a wajen. Mota ce k’irar Civic 2000 ta karyo layin hakan yai daidai da juyowan Ummulkhairy wacce idanunta ke zubda ruwa. Karaf idanunta suka kafe cikin na Zaubair dake rolling glass din mota. SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU.!* *02* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* Zubair yai parking idanunsa kan Ummulkhairy da tun isowar motarsa wajen ta kasa komai sai hawaye dake bin k’uncinta. Ba yau ne rana na farko da aka kawo sadakinta aka amshe ba balle wani Kayan lefe saidai a yau d’in taji wani irin abu da bata tab’a ji ba a baya. Ta sani ba wai son Zubair take ba sabida zata iya cewa zuciyarta ta k’ek’ashe da batun wani aba mai suna soyayya. Batajin ko a gaba zatayi wani abu wai shi soyayya. Tayi na’am da aurensa ne dan cikan burin mahaifiyarta kaman dai sauran aurarrakin da ake saka mata ana fasawa. Dikda hakan bazata bataji ciwon abinda ya faru cikin zuciyarta ba. Ta zaci wann shine na k’arshe. Ta zaci komai zaizo k’arshe. Ta zaci burin mahaifiyarta zai cika daga k’arshe. Sann kowa zai salama saidai abun ba haka bane. Da alama ita dai wann shine k’addararta bazata tab’a aure ba kaman yanda mutane ke fad’i akanta. Lumshe idanunta tai hawaye masu tsananin dumi suka gangaro mata. Shin yaushe ne komai zai kare.. Yaushene komai zaizo k’arshe.? Tambayar da ita kanta bata da amsar sa. Khulsum kaw ko tsayawa kula su Hajiya Dudu batai ba balle ta kula da Zubair Wanda bai jima da k’arasowa wajen ba. Sai zuba ruwan masifa take tana nuna su Maman Sahal tana fad’in duk macen da bata fasa kokawa da ita bata haifu ba. K’arasowan wasu matasa sukai k’ok’arin raba fad’an. Sai huci Khulsum take tana gyara mayafinta. Ta d’auki mayafin Ummul da akai jifa dashi can gefe ta rufa mata. Ta shiga janyo hannunta tana fad’in “Adda Ummul muje aurenki kuma in sha Allah ba fashi Akan idanunsu za’ayi saidai mata ta mutu..” Kaman daga sama suka sinkayo muryar Hajiya Dudu tana fad’in “Aure ba fashi a gidan uwarki.? Mai za’ayi da mace mai dambe a titi..” Ta jiyo tana duban Zubair da ya kasa koda bud’e k’ofar mota balle ya fito “Ka daiga abinda nake fad’a maka ko.. Ka gani da idanunka.. Allah ya ceceka bazakai asaran sadaki ba.. Yo wann ai asaran sadaki ne.. Dama da na fada maka wann yarinyar ballagaza ce. Yanzu zaka yarda da batu na. Aure kaida wann ballagazar ko a k’iyama ehe..!” Ta k’arashe tana jefa kit d’in hannunta cikin boot d’in motar da tuni sauran matan sun dire akwatunan hannayensu ciki. Har lokacin idanun Ummulkhairy a k’asa suke hawaye d’aya na bin d’aya. Gaba d’aya sai jikin Khulsum yai sanyi musamman da taga yanda Zubair ke aikama Ummul wani irin kallo da ta gaza tantance na tsana ne ko na mamaki. Sunaji suna gani Hajiya Dudu ta k’arashe maganganun ta suka shige mota da sauran matan. Tuni Zubair yaja mota Sun bar wajen saima k’ura da ya bud’e su Ummulkhairy dashi. Jiki a matuk’ar sanyaye Khulsum ta kamo hannun Ummul. Saidai kafin tace wani abu Ummul ta janye hannunta ta nufi gida cikin saurin wani kukan na kuma b’alle mata. Jiki a sanyaye Khulsum ta take mata baya. Suna shigowa gidan suka tadda mahaifiyarsu zaune dirshan tsakar gidan sai cazgan kuka take. Ga Mama Tani wato kishiyar mahaifiyarsu kuma uwar gida a wajen mahaifinsu tayi bak’e bak’e a tsakar gidan sai ‘yan wak’e wak’enta na habaici take. Ummul ta k’araso a sanyaye ta duk’a gaban mahaifiyarsu dake cazagan kuka. Jiki a sanyaye, murya na tsananin rawa Khairy ke fad’in “Umm..Umma.. Umma..” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Umma ta d’ago idanunta masu zuban ruwa. Cikin kuka take duban Ummulkhairy tana nunata da d’an yatsa take fad’in “Ummul na gaji.. Wllhi na gaji.. Na gaji dake.. Na gaji da wann fashe fashen auren da ake akanki.. Ummul na amso Miki rubutu.. Na Kai sunanki gaban Malamai an baki rubutu an miki addu’o’i.. Ke k’arewa har ruk’iya an miki.. Ummul anya ke ‘yaradam ce..” Ta k’arashe tana kuma fashewa da kuka. Yayinda Kan Ummulkhairi ke duk’e kukanta na k’aruwa da Jin kalaman mahaifiyarta. Khulsum kaw girgiza Kai kurum take tana duban mahaifiyar tasu cikeda mamaki Jin irin kalaman dake fitowa daga bakinta. Ita kaw Mama shewa tai harda tafi kaman ta samu tv haka take dubansu. Sai dariya take cikeda nishad’i. Khulsum ta aika mata mugun kallo kafin ta maido da dubanta ga mahaifiyarta da kuma ‘yaruwarta. “Umma dan girman Allah ki daina irin wann kalaman Akan ‘yarki.. Ke fah uwa ce Umma..” Khulsum tace ranta na tsananin sosuwa. A hasale mahaifiyarsu ta d’ago tana fad’in “Ke dalla can rufe min baki.. Mai kika sani..? Ki bari randa kika zama mahaifiya irin k’addarar da ya samu ‘Yaruwar ki ya samu d’iyarki sann ne zakiji ciwon da nake ji.. Wayyo Allah.. Wayyo ni Suwaiba laifin mi nayi aka jarabceni da ‘ya irinki Ummul.. Ke ba wani tawaya bane tattare dake d’an hasken nan baki rasa ba. Ke duk wani abin da mace zatai tink’aho dashi daidai gwargwado Allah ya baki amma a rasa Wanda zai aureki kowa da yazo sai Ya gudu.. Haba Ummul..!” Ta kuma fashewa da wani kukan.. Idan da sabo sun Saba da dramar mahaifiyarsu. Khulsum ta girgiza Kai. Tinda aka soma amsan kud’in auren ‘yar uwarta Ummulkhairy ana fasawa cikin damuwa da tashin hankali mahaifiyarsu take. Batada da burin da ya wuce taga Ummulkhairy tayi aure ta bar gidan ko ba dan komai ba sai ko dan gori da maganganu da take fuskanta Kama daga kan Abokiyar zamanta har izuwa kan ahalin gidan dama sauran jama’an unguwa. Mahaifiyar Ummulkhairy ta kasance irin mutanen nan ne masu saka damuwan maganganun mutane a ransu. A akasarin lokuta mutane suna mata kallon sakarya wacce batada wani wayo ko cikakken hankali. Sann tin Ummulkhairy tana k’arama taci burin ta aurar da ita da k’anan shekaru saidai Allah bai nufa hakan ba. Haka zatai mata wanka tai mata ado tin tanada k’ananan shekaru taita mata wak’e tana karanto baitika tana mata rawa tana fad’in saura k’iris ta aurar da ita saura k’iris ta kaita d’akin miji. Koda Mama kishiyarta zataita yab’a mata maganganu da fad’in ta jira dai taga girman ‘yar tata sam bazata tab’a tankata ba. Umma Ta kasance irin mutanen nan ne masu san Barkwanci Wanda kowa ya mata wann shaidar Wanda hakan kesa wasu ke mata kallan shashasha a akasarin lokuta. Ko fad’a Abokiyar zamanta ta tareta dashi wasa take maidashi Sam batada abokin fad’a kaf unguwar balle gidan. Hakan yasa halinsu itada Khulsum yasha bam bam. Domin kaw albasa batai halin ruwa ba. Dukda kuwa cewa Ummulkhairi ma bata dauko barkwancin ba. Sai sanyi wann kuma wajen mahaifinta ta dauko. Burin Ummulkhairi shine cikan burin mahaifiyarta. ta samu mijin da zai aureta koda bata sonsa zatai hak’uri ta zauna dashi dan burin mahaifiyarta ya cika. Burin mahaifiyarta shine Ummul d’inta tai aure ta tafi d’akin mijinta. Mahaifiyar su Ummulkhairy ta kasance itace mace ta biyu a gidan mahaifinsu. Matarsa ta fari itace Mama Tani yara uku gareta kuma duk sunyi aure suna d’akin mazajensu. Badi’a itace babba sai Salima sann autarta wacce Ummulkhairy ta girme mata da shekaru uku itama tuni tayi aure tana d’akinta. Autar Mama tani sunanta Azeema. Mama ta kasance d’aya daga cikin matan unguwar Wanda basu da aiki sai aibata duk macen da Allah ya jarabceta da JINKIRIN aure ko mutuwar aure. Nan zakaji bakin Mama tana alfahari tana fad’in ita nata yaran kaf suna d’akin mazajensu kai kace wayonta ne ya kawo hakan ko dabararta. Mahaifinsu baida wani karfi saidai basu rasa abinda zasu saka bakin salati, saida manja da mangyada yake a kasuwa dukda dai jarin ba wani mai yawa bane amma sunfi k’arfin abinda zasu saka a bakin salati daidai talaka. JINKIRIN auren Ummulkhairy ba shine ke tada hankalin mahaifinsu ba kaman yanda ake maganan aure magana yabi iska. Dukda ya kasance Dattijo kuma mai k’ok’arin danne damuwarsa ya fawwala wa Ubangijinsa lamuransa can k’asan zuciyarsa na damuwa da al’amarin ‘yarsa Ummulkhairy saidai Sam baya nuna hakan. Kullum cikin cewa yake Allah ne bai nufa ba. Ga manema Sam basu fasa nemanta ba domin kaw d’iyarsa tubarkallah ce batada makusa saidai ace d’anadam tara yake dama bai cika goma ba. Yayi imani lokacinta ne kawai baiyi ba. Gyara zamansa yai yana sauraron kukan da Umma ke ci gaba da yi tana fad’in “Abban Ummul dan girman Allah ka nemo min mafita wllhi bansan ya za’ayi na sake fuskantar mutanen unguwar nan ba. Toh ma da wani fuska zan sake fita ana nunani ana k’irga fashin auren Ummul da akai.. Dan Allah ka nemo min mafita Wayyo ni Suwaiba..” Ta k’arashe tana kuma rusa wani kukan. Abba ya girgiza Kansa, ya kasance mutum maras San hayaniya kaman dai ‘yarsa Ummulkhairy. Shi irin mutanen nan ne da zakai abu su kauda idanu suyi kaman basu gani ba sann irin mutanen nan ne masu nuna kulawa da k’auna kan duk Wanda Allah ya hukunta kasancewarsu tare Kama daga iyalansa har zuwa kan ‘Ya’yansa da danginsa dukda kuwa k’annensa dake zaune cikin gidan basu d’aukesa bakin komai ba hasalima gaba suke dashi. Hakan baisa ya fasa masu nasiha da wasilci da zumunci ba. Cikin b’acin rai ya tsame hannunsa daga cikin kwanon tuwon dake gabansa ya katse Umma da fad’in “Haba Suwaiba! Ya isa haka nan.. Shin yau ne aka fara amsar lefen Ummulkhairy ko sadakinta..?” Batace komai ba sai gunjin kuka da take ci gaba. Ya kuma girgiza Kai “Toh tinda ba yau bane na farko sai ki kwantar da hankali dan na tabbata bazai zama na k’arshe ba tinda dai kink’i amincewa ‘yarki ta koma makaranta tai karatu kaman yanda ita Ummul d’in ke so.” Cikin zuban hawaye ta d’ago tana duban mijin nata “Yo wani karatu fisabilillahi .. Aima shekarun ta Sun wuce shekarun zaman aji.” “A ina kika tab’a ji an girma ma neman ilimi Suwaiba..? Waima dakata Suwaiba. Da kika damu kika daga hankali duka

Chapter 1 of 64