asiri na a rufe a kula da ita idon masu ido bai ganta bakin masu baki bai tofa ba.”
Asshe ta jinjina kai “Cikin kwanaki k’alilan komai zai kammala da yardar Ubangiji Ummul d’inki ta shige d’akin aurenta mafarkin ki ya zama gaskiya.”
Umma sai ta fara hawayen farin ciki tana fad’in shikenan burinta yana gab da cika. Allah zai cika mata wann buri nata daga k’arshe.
Asshe ta girgiza kai kafin ta fice ta bawa Umma waje tai mai isarta.
A haka Ummul ta k’araso ta tadda Umma wacce itama hawaye ne kwance saman fuskarta.
Ta k’urawa mahaifiyarta ido. Sai kuma tasa bayan hannunta ta share hawayen dan taji kaf tattaunawar da su Umma sukai.
“Alfarma d’aya zan rok’eki Umma.” Ta fad’i cikin rawar murya.
Umma ta dubeta wann karon hawaye ne saman k’uncinta.
Ummul taci gaba “Ki kaini wajen Abba na gansa nai masa Sallama kafin ku killaceni a wann gidan.”
Umma ta jinina mata kai tana sakin murmushi ta kamo hannayen Ummulkhairi “Zamuje Ummul. Zamuje kiga mahaifinki. Sann zan baki labarin duk abubuwan da suka faru dalla dalla tin daga lokacin da Tani ta fatattake ni naje na nemo kud’ad’den jinyar mahaifinku.”
Bayan Umma ta labarta komai dangane da had’uwarsu da Asshe da irin duk wani taimako da Asshe Tai mata. Da buk’atan Asshen na nema ma d’ansu aurenta. Jinina kai Ummul tai ba tareda tace komai ba dan kalamai sun k’are saman harshenta. Abinda yai mata saura hawaye ne Wanda suma d’in batada tabbaci idan basu kusan k’arewa ba.
Driver ne ya d’aukesu Ya kaisu Har asibiti wajen Abba.
Mama dake zaune a haraba tana hangosu ta mik’e cikin sauri ta nemi wajen b’oyo ta b’uya yayinda Ummul da Umma suka shige d’akin.
Umma ta dubi Ummulkhairy tace “Zan barki ki gana da mahaifinki Ummul. Ku biyu.”
Ummul ta jinjina mata mai tana goge hawayen da suka kwararo mata.
Ummul zaune gaban gadon mahaifinsu Wanda idanunsa ke lumshe, ta saka bayan hannunta ta share hawayen da suka gangaro mata, abubuwan da suke faruwa da ahalinsu sai gifta mata suke a k’wayar idanu. Ta d’aura hannunta guda saman na Abba. Cikin rawar murya take furta “Abba tinda ka kwanta komai bai k’ara daidaita ba.. Umma ta canza Abba..” Sai kuma tai shiru tana share hawayenta “Abba koda bana nan… Ban sani ba ko zamu sake had’uwa ba ko bazamu sake had’uwa ba. Abba ka yafe wa mahaifiyata a bayana. Dan Allah ka yafe ma Umma.!” Kuka ya hanta ci gaba da magana.
Da k’yar kukan nata Ya tsagaita kafin taci gaba “Abba bazanso wani wanda ba kai ba ya aurar dani. Watak’ila Umma ta hana maka wann damar ne domin ceto naka rayuwar.”
Muryarta yaci gaba da rawa “Abba banida wani zab’i.. Rayuwarka na kan gab’a a nan.. Watak’ila wann shine maslahan ahalinmu. Watak’ila komai zaizo k’arshe. Watak’ila ni ce matsalar. Watak’ila idan nayi nesa daku zaman lafiya da kwanciyar hankali zai wanzu tsakanin ahalin. Abba zanyi duk wata sadaukarwa sabida ahalina. Ka yafe mun Abba. Kuma ka yafe wa mahaifiyata .” Ta k’arashe tana mai kifa kanta gefen Abba hawaye na kuma kwararo mata.
Mama dake lab’e bayan window ta waje taji duk abinda Ummul tace. Wato Suwaiba ta shirya aurar da Ummulkhairi ne a sirrance..? Shin wann shine dalilin canzawan Suwaiba..? Aiko idan haka ne sai taga ta yanda za’ayi wann aure.. Idan Suwaiba tasan wata bata San wata ba. Toh amma ta ya zata b’ata auren tinda Suwaiba bata nuna masu mijin Ummul d’in ba.? Kar dai Suwaiba ta samo attajiri ne ma Ummul d’inta.. Idan har al’amra sukaci gaba da tafiya a haka kenan fah Suwaiba zata zamto sarauniya a gidan. Sai abinda tace. Harta ‘ya’yan cikinta su Azeema sai Sun gagareta. Tin yanzu ma komai ya canza balle abubuwa suci gaba da tafiya a haka.. Uwa uba Har kawo wann lokacin basu saka Tasi’u a idonsu ba... Dawowan Suwaiba dik shi ya karkata masu hankali ta kasa aiwatar da komai gameda b’cewan Tasi’u. Toh inaga Abubuwa sunci gaba da tafiya a haka.? Yanzu ita fah zata tashi a tutan babu kenan ga Suwaiba ta dawo da sabon sauyi..
Mama ta koma gefe saman benci ta zauna had’ida buga uban tagumi. Kallo d’aya zaka mata ka fahimci duniyar tai mata atishawan tsaki. Sai faman sauk’e tagwayen ajiyan zuciya take tana canza salon tagumin ta. Babu babban abinda ya bata takaici kaman da ya kasance yanzu dik abinda suke ci daga wajen Suwaiba ya fito.. Shikenan Suwaiba fah ta amshe girman nata. Abinda yai saura kawai shine Suwaiba ta umarceta ta soma kiranta da Yaya.
Saiga Mama na hawaye tana fad’in har abada bazata bari Suwaiba tai nasara akanta ba. Idan abinda zata aiwatar k’arshe shine hana yuwan auren Ummulkhairi ta shirya yi. Da dai ta bari Suwaiba tai galaba akanta gwara tai komai dan nasara nata ne da yaranta ba na Suwaiba da nata ‘ya’yan ba. Da wann tunani ta mik’e tagajan magajan domin kaw zama bai ganta ba.
*
Kan Ummul na kife gefen mahaifinta tana ci gaba da cazgan kuka mai ban taisayi.
Umma ta k’araso ta dafata.
Ummul batace komai ba Har Umma ta ta k’araso wajen.
“Tashi kije Ummul direba yana jiranki. Ki sani bazan bari ki koma gidan mahaifinki ba har sai ranan Aure gudun kar wani abu ya gifta. Kindai san matsalarki da abubuwan da mukaita fuskanta a baya na fashe fashen Aurenki. Wann karon ban shirya ba ma wani k’ofa ya lalata Aurenki ba. Naga Tani bata nan a nan, zan zauna wajen Abbanku Har Tani ta dawo. kuma zan karanto masa komai koda bazai bud’e idonsa ba na tabbata kunnuwansa da zuciyarsa zasu saurareni.”
Ta murmusa tana duban Ummul “Na tabbata a yau mahaifinki ya farka ya ganki a d’akin Aurenki zaifi kowa farin ciki sann wann kad’ai Ya isa ya zama silan yaye damuwar dake k’unshe cikin zuciyarsa.”
Dubanta kurum Ummul Tai ba tareda ta iya cewa komai ba. Har yanzu dai a idon Umma itace matsalar ahalinsu da k’addararta.
Ta kuma juyowa ta dubi Abba hawaye suka kuma gangaro mata. A hankali ta isa ta tofa masa addu’o’i kafin tasa kai ta fice jiki a mace.
**
Abuja..
Zaune suke gaba d’aya a nan lambun dake farfajiyan gidan. Mommy Daddy harma da Anisa.
Mommy dai bata sama bata k’asa gaba d’aya kana ganinta zaka hango tsantsan farin cikin da take ciki.
Ta dubi Anisa tace maza ta sami one of the mades su shirya wajen cin abincin mutum guda.
Daddy ya dubeta “Are you expecting someone.?”
Mik’ewar da Anisa zatai ta hango shi ya nufo garden d’in. Looking handsome as always. Zuciyarta yai wani irin yankewa.
Mommy ta fad’ad’a murmushinta tana nuni da Haidar dake k’arasowa “Oh! He’s here already.” Ta maido da dubanta ga mijinta “Ya kamata mu rinka samun lokaci irin haka na musamman domin ahali. After all, amarya za’a kawo mana very soon.”
Baice komai ba yaci gaba da abinda yake. Dan yanzu ya kula Kwaise batada zance sai na auren D’anta.
Haidar ya k’araso Mommy na masa sannu da zuwa. Sai nan nan dashi take. Wani sabon kula da soyayya take nuna masa abinda bata masa a baya ba. Kaman tayi ma wofi haka ya d’auki abun tinda yasan ba dan Allah take ba.
Koda Anisa ta kawo plate karb’a Mommy tai tana k’ok’arin serving d’insa sai haba haba dashi take tana tambayarsa me za’a zuba masa.
Cikeda k’osawa Haidar Ya rik’e hannunta Ya amshi plate d’in “Mommy please that’s enough, I can do it myself. I’ve been doing it since childhood.”
Jikinta ya d’anyi sanyi ta soma Tina ita dai tin tasowarsa tin yarinta bata tab’a tambayarsa yunwan cikinsa ko lafiyarsa ba. Masu aiki da Nannies Sune suka San lafiyarsa, cinsa ko shan sa. Har yayi ciwo ya gama bata san yayi ba kuma ba matsalar ta bane. The only abu da take tambaya ta kuma tada hankali akai shine karatunsa na boko da sakamakon da zai birge mahaifinsa. Idan kuwa bai kawo sakamakon da zai birge mahaifinsa ba ranan zai wuni ne a d’aki mai duhu kuma a kulle cikin tsananin horo.
Mommy ta gyara zama ganin table d’in Ya b’ata shiru sai sautin cutlery dake tashi cikin plates.
Ta d’an murmusa tana duban Haidar “Ya labarin aiki.. Ina nufin sabon project d’in naku.. Kun fara ne.?”
Yasan so take tai creating hiran da zai had’asa magana da mahaifinsa. Ya d’an girgiza kai kad’an “Still ironing out the details..” Ya d’ago yana dubanta sosai tinda yasan tasan komai “In a couple of months, Mommy. Let’s say two to three months.”
K’arasowar wata mai aiki rik’eda k’aton frame a rufe Ya katse Mommy. Mai aikin ta k’araso cikeda ladabi ta tsaya nan bayan Mommy rik’eda frame d’in tana sanar da ita security ne Ya shigo dashi.
Mommy ta jinjina Kai tana mai nuna mata yanda zata ajiye.
Ta maidoda dubanta ga Ahalinta tana kuma fad’ad’a murmushinta “Na had’a mana wann cin abincin ne a tare domin na gabatar mana da wani mihimmin abu. Musamman gareka Haidar.” Ta k’arashe tana mai isa jikin frame d’in.
Ta shiga bud’ewa sannu a hankali tana mai furta “Kyakkyawar Amaryar mu. Matar D’anmu Haidar. Sirkarmu wacce zata zamto silan dunk’ulewar ahalinmu.”
Cak ya tsaya da abinda yake. Lokaci guda yana mai matse fork and knife dake rik’e cikin hannunsa. Bai iya janye idanunsa daga saman plate d’in ba haka nan bai dubi hoton da mommy ke nuna masa ba wacce ta ambaceta da matarsa.
Girgiza kai Daddy yai yana tunanin matarsa ta zauce da wann auren da take yunk’urin yima d’ansu. Ya d’auki tissue had’ida goge bakinsa. Ya dubi Mommy kafin yace “Are you in your right state of mind. What’s the meaning of this Kwaise.?”
Mommy tace “Gani ya kori ji Engr. Matar Haidar ce. Idan ba a hoto ba nasan bazaije ya ganta ba har sai Randa aka kawo mana ita gidan. So kafin a kawota yak’i amincewa yace gaibu na auro masa. Gwara na samu dalilin kafa hujja. Look kalla kaga, zasu dace da Haidar.. Asshe ta iya zab’e.” Ta k’arashe sai duban hoton take tana murmushi.
Daddy dai kallon wacce ta samu matsala yake mata. Lokaci guda ya girgiza Kansa “I’m done here.” Yai maganar yana mai barin wajen.
Zuciyar Anisa yaci gaba da bugawa tana mai duban hoton. Cewa da Mommy tai Asshe ta iya zab’e shine keta yawo cikin kumnuwanta. Mai kenan hakan ke nufi.? Amminta ce ta zab’o wa Haidar mata.? Mahaifiyarta ta turota gidan ne dan taci amanarta ta nema ma Haidar auren wata daban a garin Kano.? Ko kuwa mai Ammi take nufi da ita.?
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*18*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Haidar ya k’arisa gaban mahaifiyarsa yana mata duban mamaki. Ya jinjina Kansa kad’an har lokacin dubanta yake “Had I known, akan wann abun kika kirawoni nan. I wouldn’t have wasted my time coming here.” Yai maganar yana nuni da hoton Wanda ko kalla baiba. Daga haka sa Kai yai zai shige amma sai yaji kaman Wanda aka ce ya juya ya dubi hoton.
Bazai iya ce ga kamanninta ba ko wani abu mai Kama da wann. The only thing he noticed cikin hoton shine k’wayar idanunta masu cikeda rauni ga kwantattun hawaye ciki. Yanda kasan magen dake cikeda tsoro. Ya janye idanunsa ba tareda ya kuma ceda Mommy komai ba yasa kai ya fice.
Mommy tai saurin bin bayansa cikin k’ok’arin dakatar dashi.
Anisa kaw kasa janye idanu tai daga barin duban hoton. Ita wann d’in wacece.? A ina Amminta ta samota.? Maiyasa Mommy ke yunk’rin had’a aurensu da Haidar Dikda cewa Haidar d’in baya so. Cikin azama ta mik’e tana Jin kuka na zuwa mata. Ta gaji ta gama zaman gidan, bazata zauna a kawo wata cikin gidan da sunan matar Haidar ba. Gwara ta tafi ta koma gida dik abinda Ammi zata k’ulla ta k’ulla Akan idonta dan tayi imani bazata bari wann auren ya tabbata ba. Idan ma anyi it won’t last long. She promised. Table knife d’in dake hannunta ta jefa jikin hoton Ummul Ya kuwa samu daidai tsakiyar fuskar hoton. Sai sakin huci take ta mik’e ta shige cikin gida kaman zata fashe.
Tana shiga ta soma kiran layin mahaifiyarta. A zuciya take had’a kayanta cikin suitcases. Ammi tana d’agawa Anisa taci gaba “Wow congratulations Ammi. Aikinki yana kyau. So wann shine dalilinki na turo ni gidan nan..? Ki nemar wa Haidar auren wata can garin Kano.. Wato baki so na zame Miki matsala cikin abinda kike shiryawa shisa kika tarkaso ni kika turo ni nan..?” Ta jinjina Kai tana mai ci gaba da huci “Ammi I thought plan d’in shine nazo nan dan na Sami kusance da Haidar da kuma ahalinsa.? But what did you do Ammi.. You sent me here for you to carry out whatsoever your plan might be. Zan dawo gobe goben nan.. Zan dawo garin Kano. Kuma ina mai tabbatar Miki na shirya b’ata dik wani shirinki Ammi.” Ta k’arashe cikin huci.
Daga d’aya b’angaren Asshe ta katseta “Idan ke shashasha ce ki dawo Anisa. Abinda baki sani ba shine wann auren da kikaga na dage ina nemar ma Haidar ba ji ba gani ma ke nake Anisa.”
Baki sake Anisa ta girgiza Kai “Wane irin ma ni kike Ammi bayan gashi na gani da idona kin turo picture d’in yarinyar da kike nemar ma Haidar Aurenta. C’mon Ammi mai kike nufi.?”
Asshe ta murmusa kad’an “Bazaki fahimci komai ba sai nan gaba kad’an Anisa. Amma wann auren kaman fansar Haidar nake nemar Miki dashi. Idan har ba’ayi wann auren ba bazaki tab’a iya samun Haidar ba Anisa. Har abada.”
Anisa ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Ammi auren da kike nemar ma Haidar fansa kaman ya.? Ammi mai hakan yake nufi.? Ni fah ban fahimci komai ba.”
Asshe ta kuma jinjina Kai “Bazaki fahimci komai a halin yanzu ba Anisa. Amma nan gaba kad’an zaki gane duk abubuwan da nake fad’a miki. Idan har kina so Haidar ya zama naki sai kin bada goyon baya d’ari bisa d’ari ma wann auren. Ki bawa Aunt d’inki k’warin gwiwa akan auren d’ari bisa d’ari. Idan har kina son D’anta sai kinso wann auren Anisa. Ke idan an kawo matar ma ki shiga jikinta sosai ki tabbata ta samu kusanci da Haidar.”
“Ammi kin kuwa ji abinda kike fad’i. Ammi how can I possibly do that.? Maganar mutumin da nake so the most fah ake a nan. Ta ya zan so ya samu kusanci da wata bani ba.?”
Asshe ta murmusa kad’an “Ni mahaifiyarki ce, kuma nafi kowa so ki kasance cikin farin ciki Anisa dan haka kiyi abinda nace idan har da gaske kina sonsa. Nan bada jimawa ba zai zama naki. Amma fah sai kin tabbata wann auren nasa ya yuwu.”
Anisa ta girgiza Kai kad’an “Ammi wai meyasa dole sai anyi auren. Can’t he just marry me instead.?”
“Ke bana son shashanci kika auresa yanzu kashe kanki zakiyi.. Na fad’a Miki Fansar Miki shi zanyi da wann auren wai meyasa mik’ewa shashanci ne.?!”
Da mamaki Anisa tace “Kashe kaina kuma Ammi dan na auresa.?”
Asshe Jin ta kusan yin b’aranb’arma ya sata sassauta murya tace “Anisa ni mahaifiyarki ce, kuma ki yarda dani I want nothing but the best for you. So idan nace ki yarda dani ma ke nake wann yak’in ki yarda kawai. Zaki mallaki Haidar. Zai zama naki Watak’ila nan da watanni k’alilan kinji koh. So ki kwantar da hankali ki and trust your Ammi.”
A hankali Anisa ta sauk’e ajiyan zuciya “Shikenan Ammi, if you say so. I trust you, hundred percent.”
Bayan sun Ida wayar zama Anisa tai tana tunanin maganganun mahaifiyarta. Ta ya zata goyi bayan wann auren.? Abun da kamar wuya. Ta mik’e jiki babu wani k’wari ta shiga unpacking kayanta.
**
Yana tsaye k’asan shower ruwan na sauk’owa tin daga cikin sumarsa har zuwa jikinsa, saurin bud’e idanunsa yai Wanda suke a lumshe sakamakon hoton fuskar yarinyar da ya gaza b’acewa a kwanyarsa da kuma k’wayar idanunsa. Ba wai fuskar nata yake gani cikin k’wayan idanunsa ba. Dan bazaice ga kamanninta ba. A’a kwantattun hawayen da shi kad’ai ne yai noticing a hoton yake gani. Sau d’aya tak ya kalla, maiyasa ya kasa cire hoton cikin idanunsa, meyasa duk rufe idanun da zai sai yaga idonta masu d’auke da hawaye.. Maiyasa ta amince da aurensa.. Meyasa hawayenta kawai ya iya noticing.? Shin dole aka mata.? Shin Wacece ita ma.? Shin tasan shirin Mommy Akan auren cewa AUREN WATA UKU zasuyi kuma dalilin auren shine mahaifinsa ya mallaka masa project. Shin tasan duka wad’ann ta amince da aurensa.? Is she that lowlife.? Wacece zata amince da irin wann wulak’antaccen auren. Does she have any idea who he really is.? Does she even know what she’s getting herself into.? Tambayoyi da yawa Wanda idan ba ita ba babu mai amsa masa. Take yaji zuciyarsa ta soma raya masa ‘Maybe she’s aware of everything.. Maybe kaman yanda Mommy tai deal dakai Akan auren haka itama tai deal da ita.. Mommy zatayi komai dan abinda take so. He knows his mother har cinikin auren zatayi. What if wann yarinyar cinikin aurenka tayi da Mommy.? Take yaji zuciyarsa na masa wani irin zafi. Ji yai ya kuma tsanarta. Ya tsani mutumin da zaiyi komai sabida kud’i da abin duniya. Sauri sauri ya fito daga shower d’in dan baiso yaci gaba da tunanin.
Yana fitowa ya tadda Dareen har ta kwanta. Ya k’arasa shirinsa kafin ya isa gefe ya kwanta. Saidai kwanciyar sa da kad’an ya soma sinkayo sautin Dareen a hankali kaman na mai kuka.
Ya d’an mirgino yana dubanta, nan yaga har kaman shesshek’a take. Side lamp ya kunna ya mik’e daga kwamcen da yake “Hey.” Ya furta a hankali.
Jin bata amsa ba ya sanya shi matsawa kusanta ya mirgino da ita, nan yaga hawaye Sun wanke mata fuska. Baison ganin hawaye tin yana yaro. Watak’ila hoton yarinyar can da ya gaza b’ace masa a k’wayar ido ma sabida hawayen da ya hango ne cikin idonta. He hates to see people cry.. A nashi tunanin ba abu k’arami bane zaisa mutum kuka. A lokacin yarinta duk irin abubuwan da yai going through baya iya kuka koda yana son yi. So he believes idan har baiyi kuka lokacin yarinta lokacin da ya kamata ace yayi ba dukda irin abubuwan da ya fuskanta a rayuwa Lallai ba Abu k’arami bane zaisa mutum kuka.
“What’s wrong.?” Ya tambaya cikin kwantar da murya idanunsa tar kanta.
Dubansa tai sai kuma ta girgiza Kai “Haidar I don’t know.. Ban sani ba, I.. I just feel like I’m losing you somehow..”
Zuba mata ido yai tausayin ta fal k’irjinsa. She’s right, a kwanakin kaman ya nesanta Kansa da ita. Above all, wann auren shirin ko yace auren yarjejeniya da Mommy ke yunk’urin yi masa yasa ya d’auke masa hankali da tunani.. He feels like he’s not being fair to her.. Koda ace bai mata irin son da take mishi. She’s still his wife kuma ta cancanci kula na musamman daga wajensa. Hannayenta ya rik’e cikin nasa suna fuskantar juna. Yayinda Dareen taketa addu’an Allah yasa tarkonta ya d’anu. Bata isa tace ga weak point d’insa ba tinda tasan shi mutum ne da ba kasafai ake iya karantar yanayinsa ba. What she’s sure about shine shi Mutum ne mai tausayi wanda ta fahimci haka from his actions, especially towards mutane masu rauni. Yanada tsananin zafi saidai a wasu lokutan tausayin masu rauni da yake dashi yakan rinjayi zafin sa. Da wann takanyi amfani ta tatsa duk wani information gameda rayuwarsa. Ta kula yanzu kaman ya daina sanar da ita abubuwa da dama. Ya fara komawa kaman dai Haidar d’in da ta soma sani daga farko kafin aikin aisiri yai tasiri akansa. Muryarsa ta sinkayo yana fad’in.
“I have been dealing with so many things lately… That I even lost sight of what’s more important.. I mean you..!” Gajeren murmushi saman fuskarsa ya kuma rik’e hannayenta cikin nasa yaci gaba da fad’in “But I’ll make it up to you.. Just choose a place from the map.. Let’s go for a vacation.”
Surprisingly take dubansa “Really, vacation..? Na zab’a duk yanda nake so from the map.?”
Murmushin bai bar saman fuskarsa ba yake jinjina mata kai “Just mention the place.. Any place you have in mind.”
“OMG.! I love you.. I love you so much..” Ta fad’i tana mai fad’awa jikinsa sabida murna.
“I’ve never been to Cuba. Let’s go to Cuba. Zan duba mana best Resort da sukeda shi.” Ta fad’i murmushi saman fuskarta.
Shid’inma murmushin yai kafin ya jinin Kai “Alright Cuba, Lets explore Cuba then.”
Rungumesa ta kumayi zuciyarta na raya mata ta mance komai ta daina binciken komai tabi mijinta suje su sha soyayyarsu.
A b’angaren Haidar kaw cikin zuciyarsa yake ayyana wann shine maslaha. A daidai lokacin da Mommy zata kawo masa yarinyar can matsayin mata zata shafa ne taji baya nan.. Bazai dawo ba sai bayan wani lokaci, zai timing lokacin da zasu fara gudanar da project d’in kafin ya dawo k’asar.
**
Kano
Da tsananin mamaki Hajjah Fannah ta dubi agogo Jin da gaske buga mata k’ofa ake. K’arfe shad’aya na dare har ta gota. Ta fito da kyar dan har kawo lokacin bata wani Jin k’arfin jikinta.
Khulsum ta gani tsaye k’ofar gidan ga alamun hawaye saman fuskarta.
“A’ah! Khulsum. Lafiya? Ina kika fito cikin Daren nan..?”
Khulsum bata iya amsa mata ba sai ma wani sabon kukan da ta fashe mata dashi. Hajja Fannah tai saurin kamo hannun Khulsum suka shige cikin gidan.
Ruwa ta soma kawo mata tace ta sha ta samu natsuwa. Ta d’an dubeta “Khulsum ina Ummul..? Meke faruwa ne wai.. Inji ba wani Abu bane ya kuma faruwa.?”
Khulsum ta saka bayan hannunta ta share hawayen “Hajja Adda Ummul ta tafi.. Umma ta saida ita.. Tabi Umma.. Ta amince da auren da Umma ta shirya mata.. Ta zab’i tayi biyayya ma Umma bisa auren da ta shirya mata a bayan idon mahaifinmu.. Su d’in basuda wani banbanci da Mama da yaranta masu burin ganin bayan Abba..!” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka.
Hajja Fannah ta dubeta da mamaki “Aure kuma Khulsum. Aure Ummul zatayi.?”
Khulsum ta jinjina mata Kai har lokacin jikinta a mace yake.
Sai Hajja Fannah ta nemi duk wani ciwon da takeji ta rasa. Taci buri ma d’anta Wanda ko shakka babu shima ya auka ma soyayyar Ummulkhairin. Saidai kana naka Allah na nashi kuma na Allah shine daidai.
Jiki a sanyaye ta dubi Khulsum “Wanene mijin da zai auri Ummul.?”
Khulsum ta girgiza mata Kai tana mai tab’e baki “Bana tsammanin ko ita kanta Umma da ta had’a auren ta sansa.”
Sauk’e ajiyan zuciya Hajja Fannah tai, wani irin batu ne ita kanta Umman nasu bata san mijin da ta nemo ma Ummul ba. Ta yaya haka zai kasance.? Ummul ta wahala a rayuwa bazataso ta kuma fad’awa wani wahalar ba. Lokaci yayi da za’a dakatar da mahaifiyar Ummul. Idan ahalin su Ummul bazasu iya dakatar da Suwaiba ba zata nemi taimakon manyan Unguwa musamman mai Unguwa da commette d’insa asan halinda ahalin Malam Isubu ke ciki ayi k’ok’arin dakatar da Suwaiba tun kafin mai aukuwa ya auku.
Ta dubi Khulsum tace “Kici abinci ki kwanta ki huta na Miki alk’awari in sha Allah zanyi iyaka abinda zan iya dan naga mahaifiyarku bata salwantar da rayuwar Ummul ba da izinin Allah.
Khulsum ta jinjina mata Kai ba tareda ta iya cewa komai ba.
Hajja Fannah dai mamaki ne ya kasa saketa. Sai sak’awa da warwarewa take tana tinanin toh waye mijin da Suwaiba ta kawo ma Ummul Wanda ita kanta bata sanshi ba. A haka ta kwana cikin daren tareda zullumin idn har auren Ummul ya tabbata batasan ta yanda zata soma sanar da tilon d’anta Wanda ta jima tana binsa da batun aure yana kaucewa sakamon k’azafi da mahaifinsa ya jefasa dashi tin yana d’an watanni uku a ciki. Daga k’arshe Hisham ya samu macen da take tunanin zasu samu daidaito sai ga kuma abinda ke shirin faruwa. Tabbas Zuciyar D’anta zai karaya.
Washe gari ma Khulsum wajen mahaifinta ta yini dan ko ta kan ahalinta bata kuma bi. A cewarta dukansu basuda banbanci da juna.
*
Washe gari masu kawo lefe Sun samu isowa gidansu Ummulkhairi. Tin daga bakin layin ake k’irga motocin dake shigowa domin kawo lefen Ummulkhairi.
Su Azeema sukai layi suka jeru nan tsakar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 64