saki Hajja Fannah har suka fice. Gaba d’aya ta gaza katab’us. Ita a halin yanzu ta fara tantama idan Mahaifiyar Ummul na cikin hayyacinta. Girgiza kai tai cikeda tausayin Ummul tana mai ayyanawa lallai tana cikin jarabawa.
**
Khulsum da dawowarta kenan daga makaranta taji k’urin miya na k’una kan wuta duk ya cika gidan. Ga hayak’i na fitowa daga kitchen. Da sauri sauri ta shigo a tunaninta babu kowa ne amma sai ta hangi Mama zaune tsakar gidan tana gyaran k’umbarta.
Bata ce komai tasa kai zata shige muryar Mama ya dakatar da ita “Toh shafaffiya maras kunya. Kin shigo kina kallo na dan rashin mutunci ko sannun fatar baki ta gagareki. Toh ai sai ki shige ki aje jakarki kije ki gaida tukunyar miyan dake k’auri kan wuta idan ba haka ba tuwon dare ya haramceku. Ahtoh dan a banza azumin da ba lada zai hau kanku daga ku har uwarku dan nikam raina guda inada gidajen ‘ya’ya ‘yan albarka da suke kame gidan mazajensu da zasu bani tuwo. Saima gidan da na zab’a naci. Banda asara har yaushe za’a ce manyan budare da suka rik’a suka rik’e a gida ana saka masu kwanon tuwo gidan mahaifinsu. Yo sadaka kuke ci sa’anninku masu mutunci dai suna d’aunansu suna aikin lada suna girka ma mazajensu tuwo.” Ta mik’e tana buge zaninta “Idan Kinga dama kar ki duba miyan girkin uwarki Suwaiba ne dan nikam na gama girka ma k’artai irinku tuwo a gidan nan. Dan dai cikina d’aya da Malam bazai gagara ba. Amma bazai yuwu da girmana a ganni ina zama bakin murhu ina girka ma gandama gandaman ‘yanmata irinku tuwo ba. Daga me yawo da sunan karatu sai mai yawo da sunan koyon san’a..” Tasa kai ta nufi d’aki “Tani ta daina girka ma k’artai tuwo wacce duk tai zuciya cikinku ta tafi nata d’akin mijin ta girka.” Ta k’arashe tana rangad’a gud’a da shewa.
Khulsum ta girgiza kai kurum kafin ta aje jakar makarantarta nan tsakar gidan ta cire hijab ta nufi kitchen d’in. Shigarta keda wuya ta soma jiyo muryar Umma ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba.
“Ko labari na sakeji kinje gidan matar can da sunan koyon San’a Ummul saidai ki nemi wata mahaifiyar amma bani Suwaiba ba. Banda salo da fitina ke da ake gab da saka miki rana yo wacce sana’a zaki koya ya wuce zaman aure dake gabanki.”
Da mugun mamaki Khulsum ke duban mahaifiyarsu “Umma.. Yanzu d’an koyon sana’ar ma hanata kikayi. Umma itafa sana’a dogaro da kai ne…”
“Ki rufe mun baki Khulsum, aure shine babban sana’ar dake gaba gareta.. Shine daraja da cikan mutuncin ‘ya mace.”
Khulsum ta saki baki da mamaki “ Umma a wann zamanin da akasarin wasu mazan basu sauk’e nauyin d’awainiyar matansu da Allah ya hukunta masu wann san’ar ba ita zata rufa masu asiri ba. Umma ko za’a baka Shi fah abu naka dad’i ne dashi.”
“Idan bakiyi shiru ba Khulsum zanzo wajen naci miki mutunci.. Hanshak’iya ana fad’a kina fad’a.”
Muryar Mama da fitowarta daga d’aki waya manne kunnenta ya katse Umma. Cikin d’aga murya Mama Ke ci gaba da fad’in “Hellaww ina jinki Badidi na Badi’atu ‘yar albarka.. Wai shi Tasi’un ya kawo miki Kaji kika soye mun.. Kaji D’an albark. lallai Tasi’u ya cika Surki na k’warai.. Allah dai ya maku albarka ya k’ara zaunar daku lafiya a gidajenku ya rabamu da sharrin mahassada masu san ganinmu a rana.”
Kuka ya kuma zuwa ma Umma bata iya sauraron wayar da Mama keyi ba ta shige d’aki.
Ita kuwa Mama tana ganin Umma da yaranta sun shige d’aki ta sauk’e nannauyan ajiyan Zuciya tana datse wayan Badi’a wacce ita kanta Badi’an ta rasa gane wasu surkulle mahaifiyarta Ke mata cikin waya. Ita da take sana’ar da ita irin uk’ubar da Tasi’u Ke bata a ‘yan kwanakin wanda ta gaza jurewa tana ce mata ita ta gaji da auren gida zata dawo sai taji tana mata wasu sunbatu wai Tasi’u ya kawo Kaji a gyare mata.
Mama ta koma d’aki ta kuma danna kiran Badi’a. Kaman jira Badi’a take ta d’aga kiran “Mama wani irin abu ne inace miki Tasi’u ya dawo da hallayansa na baya yau bugun tsiya ya min saida mak’ota suka k’waceni kina kira mun wasu kaji.”
Mama ta yarfe gumi “Ke Badi’a saurareni. Idan Tasi’u tsire naman jikinki yake haka zakiyi hak’uri ki zauna.. Zanzo gidan na sameki nasan yanda zamu b’ullo masa amma koda wasa kar kiyi tunanin dawowa gida.” Daga haka bata kuma tsayawa sauraron Badi’a da tuni ta fashe mata da kuka tana fad’in ita dai ta gaji.
Mama kaw ta mik’e tana tunanin yanda zasu b’ullowa al’amarin Tasu’u mijin Badi’a.
**
Abuja.
Maitama Builders (MB).
Zauren tattaunawar ta cika da ‘yan jarida abinda ya shafi b’angaren kasuwanci. Kowa shirye yake da tambayoyin da zai Engr AA. Maitama yake. Hisham ya shafi goshinsa dan interview d’in zai kasance live ne sakamakon yanda kowa ya k’agu yaji gaskiyar al’amarin bayan video da yai trending a manyan shafuka musamman shafukan watsa labarai na kasuwanci.
Hisham sai kai komo yake yana duba lokaci yana add’uan Allah sa kar Haidar ya badasu. Wann shine kad’ai damarsu ta k’arshe da zata d’aga darajan Kampanin ta kuma wanketa daga daud’an da aka shafa masu.
Masu gabatar da interview sun cire rai da zuwan Haidar. Sun mik’e da zummar tafiya Hisham yai saurin dakatar dasu yana sanar dasu Lallai Haidar zai zo shi.
A can gidan Daddy kuwa suna zaune shida Alhaji Gimba a parlor suna duban live event d’in yanda Daddy Ke girgiza kai. Ko janye idanunsa daga screen bayayi “I told you he’s not capable of anything good..”
Alhaji Gimba ya girgiza kai “Inada yak’ini akanshi, Zai bayyana, kuma zai abinda ya dace.. Na tabbata bazai bamu kunya ba.”
Daddy ya soma k’ok’arin mik’ewa da zummar haurawa sama yana furta “This is a complete waste of time Gimba. Ni zan shige ciki..”
Alhaji Gimba yai saurin dakatar dashi “A’a Abokina.. D’an Dakata, kalli nan..!” Yai masa nuni da screen yanda aka hasko Haidar yana k’arasowa cikin hall d’in. Yayi kyau cikin shiga irinta cikakkun ‘yan kasuwa masu huld’a ciki da wajen k’asa. K’warjininsa ya cika wajen.
Bakin Alhaji Gimba ya gaza rufuwa sabida farin ciki.
Daddy ya jinjina Kai “I hope it doesn’t turn out to be another scandal.” Ya fad’i idanunsa akan Haidar da ake haskowa.
A can Company Hisham ya murmusa yana duban abokin nasa harda d’aga masa yatsa guda alamun jinjina. Wani duba Haidar ya aika masa kafin ya wuce yanda aka tanadar masa domin zama.
Yana k’arasawa mai gabatarwan ya mik’e had’ida mik’a masa hannu sukai misabiha kafin Haidar ya gyara zaman suit d’insa ya Zauna attentively.
Nan da nan aka soma gudanar da interview d’in. Yana jefo ma Haidar tambaya yana amsa sa daki daki cikeda k’warewa da sanin aikinsa nan ya jefa floor ma audiences wani ya d’aga hannu ya soma jefo ma Haidar nasa tambayar “Yallab’ai, munga wani hoto na yawo a kafafen sadarwa har wani gidan jarida ya wallafa wani labari cewa fad’a ya kaure tsakaninka da mahaifinka sabida gazawarka da kuma banbancin ra’ayi da kuke dashi. Shin menene gaskiyan al’amarin..?”.
Haidar ya kafesa da idanu kafin yai clearing throat d’insa.
“A ko wace ma’aikata I believe ana samun sauye sauye da banbancin ra’ayi tsakanin shugaba da ma’aikatansa. Which is what makes the company stand firm on its feet..”
Babu wanda zaice bai zama impressed da yanda Haidar ke amsa tambayoyin da ake masa with so much courage and determination.
Mutumin ya jinjina kai “So does that mean da gaske ne kenan kaida Mahaifinka baku samun jituwa har a wajen aiki..?”
Haidar yai masa k’uri dan ya gane turosa akai yai masa tambayoyin da zasu tunzurashi. Tafukan hannayensa ya d’an had’e waje guda “I’m not here to tell a story about my personal life. But Being the son of the president of this company doesn’t make me different from others. If I don’t receive any VIP treatment it’s because that’s the company’s policy. And I believe this is why the company remains on track despite all the challenges.”
Ya kuma jinjina kai. “One more question Engr. “Is it true that your company is going bankrupt.. And the economy is at the state of crisis.?”
Haidar ya d’an rage girman idanunsa kad’an yana duban mutumin, lokeci guda ya d’an gyara zaman suit d’insa “Let’s call this a business perspective. Some times failures lead to future successes. I can assure you, MB (Maitama Builders) does not… and will never fear challenges..” Ya k’arashe yana mai mik’ewa lokaci guda mai gabatarwan ma ya mik’e yana mai mik’awa Haidar d’in hannu alamun musabiha “Mun gode da bamu lokacinka da kai Rankayadade.
Alhaji Gimba ya dubi Daddy “Look, duba kaga yanda yake amsa tambayoyin with so much focus and determination. He has all the potentials and skills to take this company to a greater heights. I’m super optimistic about him.”
Daddy dai baice komai saima mik’ewa da yake k’ok’arinyi.
Alhaji Gimba ya rakashi da kallo yana mamakin Allah yai baiwa wa mutum da samun d’a irin Haidar Wanda yake d’aya tamkar ga dubu amma ya kasa gani ya kuma kasa appreciating. Sosai lamarin abokin nasa ke d’aure masa kai yanaji inama nasa d’an ya kasance kaman Haidar.
**
Hisham ya kuma duban Haidar had’ida girgiza kai “Ban fahimceka ba Haidar.”
“Meye baka fahimta ba..?” Haidar yace yana duban Hisham d’in.
D’an gyara tsayuwarsa Hisham yai “Kanaso kace min gadar zare yaso k’ulla maka da ya shirya wann interview d’in..? Kanaso kace min ya shirya hakan ne just for you to fall into his trap and create more scandals.? Kana so kace min shi kake zargi da yi ma Kampani zagon k’asa.?”
“He gave me all the reasons to suspect him.”
Hisham ya kuma jinjina Kai “Amma zanji mamaki idan haka ya kasance duba da kusancin shi da mahaifinka.. So what are you planning now..?”
“Of course I’ll play his little game. Shiyasa ma na halarci interview d’in.” Ya k’arshe yana k’ok’arin mik’ewa.
Hisham ma ya mik’e suka soma takawa.
“If that’s the case, I’ll support you Haidar har gaskiya ta bayyana.”
Ba tareda ya dubi Hisham ba yace “I’d rather do it alone. This is my battle and I’ll fight it alone.. I’ll make my Dad swallow all his words a lokacin da zan kamo wuyan mutumin da ya aminta dashi matsayin babban mak’iyinsa. Each and every insult da ya jefeni dashi sai na sashi ya cinye kalamansa. And hakan zai faru ne kawai idan ya d’aurani Akan project d’in nan. So I’ll do whatever it takes to make sure ya mallaka min ragamar wann project din.”
Hisham yai still yana duban Haidar d’in “Haidar kana magana kaman fansa kake so akan mahaifinka. Haidar.. Anya lafiya kake.. Mahaifi fah ya wuce wasa.?”
“Wani mahaifin kenan.. Amma wani suna ya tara..!” Yana ida fad’in haka ya bud’e motarsa ya shige.
Har ya bace ma ganin Hisham bai daina mamaki ba. Al’amarin Haidar da mahaifinsa ya soma zarce tunaninsa.
***
Kano.
Tinda Abba ya shigo gidan hannunsa na hagu ke dafe da b’angaren k’irjinsa. Ya kuma duban Umma dake zaune gefensa ta rapka uban tagumi tana masa sannu.
Ya amsa yana mai gyara zamansa bayan yasha maganin da ta kawo masa.
Saida ya daidaita zamansa sosai kafin Ya soma magana “Suwaiba” Ya kirawo sunanta.
“Na’am Abban Ummul.” Ta amsa duk jiki a mace ganin yanayin Abban.
Abba yaci gaba “Magana nake so muyi amma ina so ki kwantar da hankalinki.”
“Toh Abban Ummul.. In sha Allah zan kwantar da hankalina.. Nidai burina ka samu lafiya..”
Abba ya d’an b’ata lokaci kad’an kafin yace “Ai na sanar dake yanda mukai da manemin auren Ummulkhairy. Wato Alhaji Kamilu mak’ocina a kasuwa.”
Umma ta jinjina kai “Eh kwarai anyi haka..”
Abba ya kuma jinjina kai “Wato Suwaiba bayan shi Alhaji Kamilu yazo yaga Ummul kwanaki uku da suka shige. Washe gari da safe kaman yanda kika sani sun taho har nan k’ofar gidana shi da wani abokinsa sun bada sadaki.. Alhaji Kamilu ya bada sadaki naira dubu d’ari a matsayin sadakin ita Ummulkhairy lakadan”
Umma kam tsaban farin ciki bata tsaya taji k’arshen zance ba ta shiga gud’a tana fad’in Ummul dinta tayi goshi ‘yan bak’in ciki saidai su Mutu.
Abba ya lumshe idanunsa kad’an yana jin zafin k’irjinsa na k’aruwa. Daurewa yai ya d’an bud’e murya yai mata tsawa kad’an data saurare shi.
Umma ta kuma wahse baki tana gyara zama “Yi hakuri Abban Ummul.. Farin ciki na ne ya gaza b’uya. Ummul d’ina lokaci yayi. Ai ni dama tin a nan wajen ka kirawo yan uwanka a nan cikin gida suka zama shaidu aka d’aura.”
“Suwaiba ki dubi girman Allah ki saurareni.” Ya kuma fad’i cikin tsarewa.
Ta saka hannayenta biyu ta kame bakinta “Na tuba.. Nayi shiru Abban Ummul.. Ina sauraronka yaushe suka nema a saka lokacin biki..? Ni wllhi na ma basu wuk’a da nama su saka ko gobe ne.”
Abba ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yana girgiza kai kafin yaci gaba “Toh kinsan kwanakin baya kasuwa ta d’an ja mun baya har na amso bashin hatsi a nan cikin kasuwa..”
Jikin Umma ya soma sanyi amma sai tace “Kasan mutane yanzu idan Sun bika bashi sunyita korortoto kenan kai kace duniya ka amsa wajensu.. Su kwantar da hankulansu lokacin biyansu yayi in sha Allah..”
“Ki saurare ni Suwaiba.”
“Toh Ina sauraronka Abban Ummul..” Tace tana gyara zamanta.
Abba yaci gaba “Toh shekaran jiyan da suka kawo sadakin sai shi Wanda yake bina bashin hatsi Ya taho mun da buk’atan kudinsa. Lallai Lallai shima yana neman kudinsa zai amfani dasu. Kuma nima nasan yanda Kasuwa ta koma a halin yanzu. Wasu lokutan Har ka fita ka dawo ba’a zuwa saye. Godiyan Ubangiji ne kawai amma al’amarin k’asar sai addu’a. Hakan yasa na d’auka cikin sadakin Ummulkhairy na biya tinda gadarana sadakin ‘yatace. Banida hanyan biya sai wann sadakin. Na cira ciki na biya.. Yau kwatsam da naje Kasuwa Alhaji Kamilu ya tareni da batu mai tada hankali.”
Ai bai kai aya ba Umma ta soma girgiza kai tana fad’in “Dan Allah. Dan tsarkin mulkinsa da buwayarsa Abban Ummul ka rufa mun asiri ka mun sutura.. Kar kace min shima ya amshe sadakinsa.. Wayyo ni Suwaiba na shiga uku na Mutu na lalace..”
Abba ya kifa kansa yana girgizawa yana jin yanda Umma ke fad’in ta shiga uku ta Mutu ta lalace. Takaici da ya cika shi ganin tak’i sauraronsa sai kuka take tana jefa kanta a uku. Abba yace “Aima baki gama jefa kanki a uku ba Suwaiba sai kinji irin wulak’anci da kwance zanin da bawan Allahn nan ya mun a cikin kasuwa.!”
Umma ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansa hannayenta duka biyu dafe da k’irji yayinda Abba yaci gaba da fad’in “Tinda nake a rayuwata ba’a tab’a min irin tozarci da wulak’ancin da bawan Allahn nan ya min ba. Suwaiba, Alhaji Kamilu dai ya amshe sadakinsa ba yanda banyi ba ya bini bashin sauran kud’ad’ensa amma sai cewa yai bazai iya jira ba dan haka yasa yaran shagonsa suka kwaso kaya a nawa shagon darajan kud’ad’ensa makotanmu a kasuwa masu burin su ganmu a rana duk suna kallo. Wann wulak’anci da mai yai kama Suwaiba..”
Kukan Umma ya k’aru mik’ewa tai ta fice tana rera kuka tana fad’in Ummul zatayi ajalinta.
Daga Ummulkhairy har Khulsum a tsorace suka nufo waje jin Umma na ambaton zata fad’a rijiya.
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*08*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Yaran Umma suna kuka suna rok’onta ta sauk’o daga saman rijiya Mama na kuma ingizata “Suwaiba ko ki fad’a ko kar ki fad’a da alama dai bak’in cikin wann ‘yar naki shi zai ajalinki.. Wayyo ni Tani zanyi kewarki Suwaiba. Ashe tafiya zakiyi ki barni.. Na yafeki duniya da lahira Suwaiba.” Ta shiga rangad’a ma Badi’a da bata jima da zuwa gidan ba kira tana fad’in ta fito tayi bankwana da Suwaiba tafiya zatayi ta barsu.
Suwaiba ta dena kururwar da take tana duban Mama da mamaki “Yaya bazaki hanani fad’awa ba.. Rijiya fah zan fad’a..”
Mama ta kamo bakin zani tana goge hawayen da babu su “Yo ko na hanaki ko ban hanaki ba wancan ‘yar taki mai bak’in k’addara zatayi ajalinki Suwaiba. Ta shiga doka kiran Badi’a wacce bata jima da zuwa gidan ba.
“Badiatu.. Badiatu! Badiatu..!! fito kiyi sallama da Suwaiba.. Suwaiba dai lokaci yayi..!”
Badi’a ta d’age labule fuska a yatsine tana kuma turo kallabi gaban goshi “Toh Mama ki barta ta fad’a mana.. Idan bata fad’a ba ai bata tabbata shashasha ba.!”
Khulsum ta harzuk’a “Uwa bata fi uwa ba Anty Badi’a kar ki sake gangancin zagar min mahaifiya..”
Badi’a ta malamalo ashar had’ida zame d’aurin kanta tai d’amara dashi tayo kan Khulsum tana fad’in kafin uwarta Suwaiba ta fad’a rijiya sai ta fara jefata ciki taga uban da ya tsaya mata.
Ai sai Umma tai tsalle ta duro daga saman rijiya ta shiga janye Khulsum wacce Baid’ia Ke k’ok’arin janyota Mama na tayata. Abu sai ya koma kaman dambe Mama ta shige ma ‘yarta Umma ma ta shige ma nata ‘yar wacce taga haik’an rijiya za’a jefata.
Ummul kaw fashewa tai da wani irin kuka sosai ganin wann tashin hankalin dik sabida ita ake.
Tana tsaka da kuka tana rok’onsu suyi hak’uri su daina ta hangi Abba na rarrafowa daga d’akinsa hannunsa guda dafe da b’angaren k’irjinsa. Ta kirawo sunansa cikin kid’ima tana mai nufansa.
Hakan yaja hankulansu. Nan take suma sukai Kan Abba suna ambato sunansa. Tuni idanunsa sun kafe suna kallon sama baka iya ganin bak’in k’wayan idon.
Sai kuma suka koma kururuwa suna neman agaji.
Kaf mutanen gidan aka rasa mai kawo masu d’auki dan dik a nasu zaton wasan kwaiwayo ne da suka saba.
Sukai masa caa akai kowa yana ambato Sunansa suna rok’onsa ya tashi. Umma sai masa fifita take da bakin zani yayinda Mama ta kawo ruwa cikin kofi tana mik’awa Umman. Fad’i take “Suwaiba duba mana kiga yana numfashi.”
Umma na kuka take fad’in “Haba Yaya kar kiyi tunani haka. Abban Ummul na numfashi..” Taci gaba da rera kuka tana rok’onsa ya tashi kar ya tafi ya barsu.
Kaf ‘yanuwansa maza dake zama cikin gidan aka rasa mai zuwa ya dubasa balle a kaisa asibiti. Dama gidan Sun gaji gaba na ‘yanubanci tin daga iyaye da kakanni. Yan wann d’akin babu ruwansu da yan wancan d’akin. Shi Abba kusan shine babba cikin mazan dake rayuwa a gidan sauran yeyyen nasu duk mata ne suna gidajensu. Shi a d’akin mahaifiyarsa shi kad’ai ne namiji. Hasalima su biyu mahaifiyar tasa ta haifesu. Daga shi sai kaw ‘yaruwarsa k’anwarsa mai suna Inna Dije. Inna Dije da mijinta basu jima da komawa garin Dutse na jihar Jigawa ba yanda mijinta ke aiki. Hasalima mijin nata d’an asalin jihar Jigawa ne amma yayi zaman Kano yanda yaga Inna Dije k’anwa ga Abba ya aureta. Sun zauna tsawon lokaci a Kano kafin iftila’in rashin tilon d’ansu ya samesu. Tin bayan rasuwar D’ansu basu kuma zaman Kano ba hakan kuma yai daidai da canjin wajen aiki da mijin Inna Dije ya samu. Sann tin bayan wann lokacin Inna Dije bata kuma saka k’afarta a garin Kano ba.
Wasu dattawan unguwar masu ganin mutincin Abba su suka Kaisa wani k’aramin asibitin gwabnati mafi kusa. Mama da Umma sukai masu godiya.
Jigum jigum sukai gaba d’aya suna jiran ba’asi daga wajen likitoci.
Daga yanda suke zaune Mama ta kafe Umma da yaranta dake zaune daga d’aya b’angaren suna hawaye. Sai cika take tana huci dan wann dik dalilin Suwaiba da ‘yarta ke faruwa. Ta sauk’e idanunta kan Ummul wacce ta kasa daina kuka maras sauti. Kaman wacce aka sinkara ta soma furta “Wann duk laifinki ne Ummul.. Idan Abbanku ya rasa ransa ki sani alhakin mutuwarsa zai ratayu ne a wuyanki.. Kece nan kikai silan mutuwar mahaifinku..!”
Umma ta d’ago tana duban Mama shaye da mamaki “Yaya ya zaki ce haka.? Ta ina Ummul ta zama Sila..?”
“K’warai kuwa ita ce Sila dan bak’in cikinta da abunda ke faruwa da ita su suka taru suka haddasawa mijin mu ciwo ehe.!”
Badia dake koke Koke tana ambato sunan mahaifinta ta k’arasa a guje ta shiga janyo Ummulkhairy tana fad’in shegiya mai bak’in k’addara kafin ki kashe mana uba sai and fara kasheki kowa ya huta. Daidai lokacin su Azeema da Salima sauran yaran Mama dake gidajen aurensu suka iso ai nan suma suka aukawa su Khulsum. Fad’a dai yaci gaba a asibiti. Har saida ma’aikatan asibitin suka tasamma koransu.
Da kyar dai aka raba bangarorin guda biyu fada. Kowa suka koma gefe suna aika ma juna mugun kallo.
Can da jimawa wani Likita ya fito. Suka mik’e gaba d’aya suka nufesa.
Sukai ma likitan caaa da tambayoyi kowa naso a soma amsa nasa. Mama da yaranta su Salima na yi Umma da Khulsum na yi. Ita dai Ummul ita kad’ai ce baka Jin bakinta.
Likita ya zuba ma sarautar Allah idanu yana duban wann ahali Wanda majinyacin da suka kawo baya buk’atan irin wann hayaniya da tashin hankali nasu. Ya d’an girgiza kai yana k’ok’arin kwantar masu da hankali amma sai yaga kaman basa gane wann yaren. Tsawa ya daka masu yace duk suyi shiru ko su fice su bar masu asibiti.
Bayan Likitan ya kebe da Mama da Umma Ya dubesu yace “Ku sani yanzu ba lokacin tashin hankali bane. Lokaci ne da mijinku ke tsananin buk’atar kwanciyar hankali. Ko kunsan mijinku na d’aukeda matsanancin ciwon zuciya mai haifar da Kumburin zuciya.!”
Ai sai suka rikice Umma kuka Mama kaw mik’ewa tai dafe da k’irji “Likita kumburin zuciya fah kace.?!”
Likita ya jinjina mata Kai “K’warai Hajiya.. Kuma ciwonsa ya wuce matakin farko.. Hasalima zamuyi k’ok’ari ne mu turasa can babban asibitin koyarwa dan a can ne zaifi samun kula sunada k’wararrun likitoci da ya shafi ciwon zuciya..”
Umma ta share hawayen da suka zubo mata tana tuna ranan da mijin nasu yai masu wasiya da hak’uri da zaman lafiya “Likita yanzu mai zai faru da mijinmu..?” Tai maganar cikin tsananin rawar murya mai cikeda rauni.
Sauk’e ajiyan zuciya yai yace “Kwararrun Likitocin da suka shafi b’angaren ciwon zuciya ne kad’ai zasu iya sanar daku abinda zai faru.. A halin yanzu bazan iya ce da ku komai ba.. Zuwa gobe da yardar Allah zaa tafi dashi can asibitin koyawar sai Likitocin zuciya su dubasa. Amma ku kwantar da hankulanku ba wani abin tashin hankali ana warkewa cikin k’udarar Ubangiji. Kuyi hak’uri na fad’a maku gatsau sabida Kun Kai hak’urina bango ne shiyasa. Ku kwantar da hankulanku ku had’e kan ahalinku ko dan samun lafiyan mijinku.. Please do this for your husband.” Ya k’arashe yana dubansu su duka biyu.
Mama tace “Sunan maganin ka fad’a Likita.?”
Ya d’an murmusa kad’an had’ida girgiza Kai “Cewa nai kuyi hakan domin mijinku.”
Suka jinjina Kai a tare Likitan ya k’arada “Kar ku damu babu abinda zaku biya mutanen da suka kawo sa nan sun biya komai. Saidai idan an kaisa can babban asibitin koyarwa dole zaa bukaci kud’i ko nace kudade masu yawa.”
Daga haka Sallama likitan yai masu suka fito jikkunansu duk a sanyaye.
**
Abuja.
Hisham ya dubi Haidar wanda ya bada hankalinsa sosai ga laptop d’in dake gabansa wanda da gani ko ba’ace kasan aiki tuk’uri yake domin achieving goals dinsa. Ya d’an Sauke ajiyan zuciya “I hope he approves the new proposal.”
Shiru Haidar yai idanunsa kan computer din har lokacin. Yeci gaba da juya pen d’in dake mak’ale cikin yatsunsa guda biyu “I know my Dad, he’s so meticulous… So everything should be done carefully..”
Hisham ya jinina kai yana mai mik’ewa “Alright, with your permission Sir, zan koma bakin aiki na.”
“Dama ban rik’eka ba.” Haidar yace yana d’an juyi cikin kujeran da yake.
Kafin Hisham yakaiga ficewa wayarsa tai ruri. Mahaifiyarsa ce mai kira. Ya fad’ad’a murmushinsa yana mai d’aga kiran.
Sosai yake hira da ita cikeda so da k’auna da alamun kewan juna daga duka b’angarorin nasu. Haidar na iya sinkayo muryar mahaifiyar Hisham yanda take ta binsa da addu’o’i nagartattu yana amsa mata da ameen. Baya kasa kunne ya saurari abinda bai shafesa ba amma sai ya tsinta kansa da sauraron wayan Hisham da mahaifiyarsa. Har dai Hisham d’in suka ida waya da mahaifiyarsa Hisham na sanar da ita bazai jesa Kano anytime soon ba she shouldn’t expect him bayan bai jima da sanar da Haidar yana son daukan hutu yaje ya duba gida cikin kwanakin.
Haidar ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 64