Share this page
a k’irji “Na shiga uku ni Asshe mai Hilal yake a Kotu.?!” Batasan sanda ta finciki marfin mota ba tabi bayansu a fusace. SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..! *40* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* “Ke Suwaiba dakata.!” Ta furta da k’arfin gaske daga nan yanda take tsaye bayansu. Gaban Umma ya yanke ya fad’i. Ta kasa juyowa sai furtawa da Tai cikin zuciyarta ‘Asshe.!’ Shi kaw Hilal da tsananin mamaki Ya juyo yana dubanta “Ammi.!” Ya furta cikeda mamaki. Asshe taci gaba da jinjina kai tana huci “Baka tsammace ganina ba koh..? Nace baka tsammaci ganina ba koh..?” Hilal Ya d’an lumshe ido kad’an ya k’araso yana k’ok’arin janye mahaifiyarsa “Ammi please don’t make a scene here.” A hankali yake maganar yana k’ok’arin janye ta. Ta funcuke hannunta tana nunasa Umma da d’an yatsa “Kina jina Suwaiba kurwar zuri’ata kur..! Idan na sake ganinki kusada d’a nah.. Kinga nan.” Ta nuna mata kotu dake gaba garesu “Wllhi a nan za’a rabamu.!” Hilal yai saurin katseta “Ammi Umma bata tilasta mun zuwa wajen nan ba.. Nazo ne da rad’in kaina..” “Rufe mun baki kai kuma kafin na Sallamaka da gaske kabi daji.!” Umma ta k’araso cikin sauri tana girgiza kai “A’a Asshe dan Allah kar kice haka.. Wllhi Hilal yaron kirki ne mai biyayya.” Da mugun mamaki take duban Umma “Kul.! Ahir d’inki kar ki sake ki sake saka mun baki ina magana da D’ahna. Suwaiba ke har zakiyi magana akan biyayya..?!” Umma ta sadda kai k’asa a sanyaye. Asshe taci gaba “Kina jina idan har baki sakar mun kurwan D’ah ba wllhi sai na maidake abin kwatance a garin nan.! Ban haifo muku D’ah dan yaji da matsalolinku da gurguntaccen ahalinku ba ehe.!” Ta dubi Hilal “Kai kuma idan ni ce na haifeka ka saka k’afarka a kotun nan.!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige mota fuuu kaman zata tashi sama. Hilal Ya dubi Umma yace “Kiyi hak’uri Umma bansan Ammi na biyedamu ba..” Umma tai saurin girgiza masa kai alamun a’a “Kar ka damu Hilal kabi umarnin mahaifiyarka. Ni zan shiga na saurari k’aran Yaya Tani. Idan bata ganni a kotun ba zatai tunanin na kuma watsar da ita ne.. Inada yak’inin Allah zai kawo yanda za’a biya mutumin nan kudinsa Tani ta dawo gida.” Hilal Ya jinjina Kai a hankali “Umma biyan kudin bazai zama matsala ba in sha Allah.. Na Miki alk’awarin baza’a sake zaman Kotu akan wann batun ba.” Kaman daga sama suka sinkayo murya “Zaman Kotu da Tani yanzu aka fara dan sai na karb’ar ma D’anuwana hakkinsa rabon gadonsa da Tani tai yana raye. Idan banci taran Tani ba ba sunana Dije ba.!” Tsaf Hilal ya gane Inna Dije ita ce dai Kanwar Abbansu Khulsum dake wajensa a asibiti sann koda aka sallame su Khulsum d’in ta tabbatar masa gidan Inna Dije dake Dutse zasu wuce da Abba yanda zaici gaba da jinya. Gaisar da Inna Dije yai yana mai k’arasowa gareta “Ni zan biya taron Innah.. A kashe wutan maganar nan kowa ya huta.. Kar ki manta ku ahali ne kai juna Kotu ba naku bane musamman yanzu da Abba yake cikin wann yanayi.. Inna Idan Abba ya farfado daga jinyarsa yaga ahalinsa suna fad’a da juna irin haka mai kike tunanin zai kuma samunsa.?” Shiru Babu Wanda yace komai daga Inna Dije har Umma. Hilal ya samu k’warin gwiwan ci gaba “Rashin lafiya irin na Abba baya buk’atan tashin hankali irin haka. Salama da kwanciyar hankali yafi buk’ata ta. Na tabbata idan Abba ya tashi yaga ahalinsa sun had’e. Suna k’aunar juna sun mance duk abinda Ya faru a baya. Sun kuma yafi juna wann kad’ai sai yafi maganin da Likita zai bashi.” Ya k’arashe yana duban Inna Dije. Sai kuma ya soma saka hannu a aljihu “Zan biya ko nawa ne idan hakan zai kawo maslaha da zaman lafiya cikin ahalin.” Inna Dije na murmushi ta dakatar dashi “A’a haba.. Idan na karbi kudi hannun surki na mai na zama kuma.” Tai maganar tana fad’ad’a murmushinta. Sai ta soma mutsuke ido tana janyo bakin mayafi tana share hawayen da suka soma zubo mata bagatatan “Na jima banji kalaman da suka ratsa zucuyata irinta yau ba. Tabbas Babu komai cikin k’iyayya da gaba. Tabbas D’an uwana ya farka yaga ahalinsa sun dunk’ule waje guda shine babban maganin da yake buk’ata. Laidai kam bakai halin mahaifiyarka ba. Al basa batai halin ruwa ba. Ubangiji ya maka albarka. Lallai ka cika D’ah na gari da kowa su iyaye zasuyi buri da mafarkin samu. Da ace duniyar zata cika da mutane irinka masu k’ok’arin ganin Sun wanzartar da zaman lafiya tsakanin Al’umma da rayuwa ta canza. Haka Inna Dije taita sharb’an kuka tana fad’in ta tuba ta canza halinta. Taita saka ma Hilal albarka har ya bar wajen. Mamaki ne ya cika Umma matuk’a da al’amarin Inna Dije dare d’aya dai kokuwa rana d’aya tak Inna Dije ta sauya. Ta ya za’a ce kalaman Hilal da basu shige a k’irga ba Sun karkata Zuciyar Dije. Kai abun da mamaki matuk’a. Har Umma ta dawo gida mamakin wann kayan al’ajabi take. A nan tsakargida ta yada zango ta kwab’e hijabinta ta lank’aye saman gajeren katanga dake tsakargidan. A haka Badia da Azeema suka shigo tsakar gidan suka taddata. Duban Umma sukai a tare suka dubi juna da mamaki ganin sunata Sallama bata amsasu ba. Suka k’araso a tare cikin sauri suka zube gabanta. Badia ta kamo hannun Umma cikin nata a dan firgice “Umma Mama ta Miki wani abin ko.? Umma saida muka fad’a Miki Mama tuban d’an muzuru tai.” Azeema ta cab’e “Umma mun fad’a Miki gaskiya Mama bazata tab’a saduda ba.. Mun santa kuma munsan halinta tinda ita ta haifemu ta kuma rainemu.. Duk abinda Mama take acting kawai take dan ta samu a fiddata ta shak’i iskan ‘yanci ta fito taci gaba daga yanda ta tsaya.” Badi’a tace “Umma fad’a mana, Mama ta miki wani abu ne..? Ki fad’a mana Umma idan ta Miki wani abu ne zamu fuskanci Mama koda ta kasance mahaifiyarmu. Dan munyi alk’awari bazamu sake bari wani ya cutar dake muna kallo ba. Koda baki haifemu ba mun Miki alk’awari zamu kasance ‘ya’ya masu biyayya a gareki.” Ta k’arashe tana duban Umman cikeda kulawa hannunta cikin na Umman. Umma ta murmusa hawayen farin ciki na gangaro mata. Ta dubi Azeema ta kuma duban Badi’a. Hannayensu su duka biyun ta kamo ta rik’e cikin nata. Ta girgiza Kai a hankali “A’a yarana, Yaya Tani bata mun komai ba.. Kuma ina nan Akan bakata in sha Allahu. Zanyi iyaka k’ok’arina wajen ganin ta dawo garemu. Wani al’amari da ya d’aure mun Kai ya faru.” Badia da Azeema suka dubi juna da mamaki “Wani al’amari kuma Umma.? Wane irin al’amari kenan. Mai ya faru.?” Cewar Azeema tana duban Umman cikeda kulawa. Umma ta jinjina Kai tace “Yau da na tafi sauraron k’aran Yaya na gamu da Innarku Dije.” Suka kuma duban juna da mamaki “Inna Dije.?” Azeema ta nanata. Umma ta jinjina Kai “K’warai Dije dai k’anwar mahaifinku.” Badia tace “Allah yasa dai ba wani abin tai Miki ba Umma.” Umma ta girgiza Kai “A’a ko kad’an bata mun komai ba.” Nan take ta labarta musu taryan taryan yanda sukai da Inna Dije. Ta k’arada “Har cewa tai ina iya zuwa naga mahaifinku a Dutse dik sanda nake buk’atan hakan..” Daga Azeema har Bad’ia ido suka zuba mata. Azeema ta mik’e k’afa tana girgiza Kai cikin yanayin salon da take idan bata gamsu da abu ba “Aaaa haba Umma. Wllhi matan nan wasa kawai da hankalinki suke. Wai Mama da Inna Dije ne dare d’aya suka zama salihan bayi.. Kaji ‘yan rainin hankali. Kut wllhi k’arya suke.” Duban da Umma tai mata yasa ta kame bakinta kad’an “Ai afuwan Ashe munce zamu k’ok’arta mu rage wasu abun. Yo baki ya saba aita sorry damu Umma in sha Allahu munata k’ok’arin saita halayyan namu koda salihanci baya mana dad’i. Amma dai wllhi idan bindiga za’a saka mun bazan yarda mata guda biyun nan tuban k’warai sukai ba. Haba Mama ce fah da Inna Dije ake magana a nan.” Badi’a ma girgiza Kai tai “Gaskiya Umma Nima zuciyata bata amince da wann canzawa da Inna Dije tai tashi guda ba. Kaman yanda har yau na kasa amincewa da tuban Mama. Umma suna amfani ne kawai da Zuciyar ki mai kyau dan su cimma wani buri nasu.” Umma tai shiru tana tunani. Ta sani Dije tanada masaniya kan abinda Tani batada masaniya akai tinda Akan idon Dije akai auren Ummul. Babban fargabanta shine kar Dije tai amfani da abinda ta sani gameda auren Ummul ta tarwatsa sabon alak’an dake tsakaninta da abokiyar zamanta Tani. Kaf fad’in danginsu Dije ce kad’ai takeda masaniya kan cewa Ummul AUREN WATA UKU tai. Mai zai faru idan tai amfani da wann damar ta tarwatsa mata ahalin da take k’ok’arin had’ewa kaman yanda tai alk’awari a baya. Fargabarta d’aya dik randa Ummul tasan da saninta tai mata AUREN WATA UKU ‘Yarta zata tsaneta sann zatayi danasanin duk wani biyayya da tai mata matsayinta na mahaifiyarta. Ta lumshe idonta tana addu’an Allah ya kawo mata mafita ya daidaita komai kafin komai ya lalace. Azeema ta d’an tab’ata “Umma kar ki damu. Idan ma Inna Dije wasa take bugawa ki bita a haka. Kinada manyan ‘yan wasa tareda dake. Kinada goalkeeper kinda defender. mu nan zamu tayaki buga wasanta. Umma alk’awari muka Miki bazamu tab’a barinki ke kad’ai ba. Mu ‘ya’yanki zamu tare Miki duk wani fad’a.. Umma a d’an zaman nan da mukai dake kinyi hak’uri damu. Kinyi mana abubuwa da mahaifiyarmu batai mana ba.. Kin zama uwa ta gari a garemu nida ‘Yaruwata. Umma mu kuma munyi miki alk’awarin zama ‘ya’ya masu biyayya a gareki.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. Umma ta dubi Azeema ta kuma dubi Badi’a. Sai taji k’walla Sun ciko idonta. Allah sarki rayuwa, tayi addu’a Allah ya bata ikon gyara kuskuren da tai kan ‘ya’yanta guda biyu Ummulkhairi da Ummukhulsum. Ya kuma bata ikon zama uwa ta gari ga ‘ya’yan mijinta guda biyu Azeema da Badi’a. Sai ga hawaye na gangaro mata. Badi’a ta kamo hannun Umma “Umma Watak’ila tunanin ‘yanuwan mu kike Ummul da Khulsum. Haka ne.?” Sai Umma ta lumshe idonta hawaye na kuma gangaro mata. Azeema ta kamo d’aya hannun Umman, murmushi saman fuskarta “Umma, nasan kina hango fuskokin Ummul da Khulsum cikin namu fuskokin.. In sha Allahu watarana ‘yanuwanmu zasu rik’e hannayenki kaman yanda nida Badi’a muka rik’e hannayenki yanzu..” Umma ta murmusa hawaye na kuma gangaro mata. Ta shiga jinjina Kai a hankali “In sha Allahu yarana. Wataran ahalinmu zai cika da alkhairi.. Wataran zamu had’u gaba d’aya cikin alkhairi. Wataran komai zai wuce ya zama labari.” Suka jinjina mata Kai a tare murmushi saman fuskokin su. Umma ta janyosu ta rungume tana mai lumshe idonta. Addu’anta d’aya Allah ya had’e kan ahalin mijinta ya kuma bashi lafiya. Suna a haka suka sinkayo Sallamar Inna Dije. A tare Badia da Azeema suka mik’e zaune suna duban Inna Dije dake shigowa haraban tsakar gidan cikin yanayin da zasu ce bata tab’a ganinta ciki ba. Idan ma Sun tab’a Watak’ila tun kafin ta rasa farin cikinta tilon D’anta Fa’iz. Mik’ewa Baida tai cikin huci “Da wanne kika zo Innah.?” Umma tai saurin kamo Badia ta zaunar cikin k’ok’arin dakatar da ita. Azeema tace “Ai dai gwara mu tambayeta Umma dan idan da tashin hankali tazo bamu maraba da ita. Kaf fad’in gidan nan a halin yanzu babu k’ofan da yakai k’ofan nan zaman Lumana dan haka bazamu bari a kawo mana tashin hankali ba.” Ta k’arashe tana watsa ma Inna Dije mugun kallo. Umma ta girgiza Kai kurum ganin irin kallon da Azeema ke yi ma k’anwar mahaifin nasu. Ta sani Sun canza sosai Sun rage wasu abubuwan sosai. Amma wasu abubuwan sai a hankali su daina dan haka ga duk Wanda ya san su waye su a baya dole yai masu uzuri. Umma ta murmusa tana mai janyo Azeema kusanta “K’warai d’iyata k’ofan mu ya zama k’ofan zaman lafiya da lumana cikin yardar Ubangiji. Hakan yasa Innarku shigowa cikin lumana.” Ta k’arashe tana duban Inna Dije wacce ta koma tamkar salihar mage “Haka ne Dije.?” Inna Dije tai saurin d’agowa ta dubi Umma sai ta jinjina Kai a hankali “K’warai Suwaiba. Babu abinda yafi yafiya, zaman lafiya da lumana.” Umma ta jinjina Kai kafin ta maido da dubanta ga Badia da Azeema “Ku gaisar da k’anwar mahaifinku.” Suka dubi juna suna yatsina fuska. Umma ta tsare sosai tana dubansu alamun tana jira su aiwatar da abinda ta umarcesu. Murya can k’asa Badia tace “Wllhi darajan Umma kikaci.!” Zuciyar Dije yai wani irin tsinkewa jin wai yau ita ake ce ma taci darajan Suwaiba shashashar matar D’anuwanta. Ta had’iyi abinda ya tsaya mata sanda ta sinkayo muryoyin yaran D’anuwan nata suna gaidata da k’yar. Ta amsa masu a Mutunce da sakin fuska kaman dai ba Inna Dije ba. Umma tace Badia ta kawo ma Inna Dije abinci sann Salima ta gyara mata d’akinsu ta kwana ciki tinda tace washe gari take komawa Dutse. Sosai Inna Dije ta saki jiki ta nuna musu komai ya shige. An bud’e sabon shafin rayuwa na zaman lafiya da k’aunan juna tsakani da Allah. Harda ba ma Umma zab’i tai idan tana so a dawo da Abba gida cikin ahalinsa. Umma ta murmusa had’ida girgiza Kai kad’an “A’a Dije zamansa a can yafi. Kinga har yanzu akwai abubuwan da bai sani ba. Kaman auren Ummul da Tani dake tsare. Kuma kinga shi mutum ne majinyaci shiga damuwa ko tashin hankali ba nasa bane.” Muryarta ya soma rawa sanda taci gaba da fad’in “Yau a k’alla watan Ummul guda da aure harda ‘yan kwanaki.. Dije kinfi kowa sanin auren Ummul mai k’ayyadadden wa’adi ne.. Nafi so idan wa’adin ya cika Ummul ta dawo garemu kaman yanda Hajiya Asshe ta tabbatar mana sann a lokacin Tani ta dawo sai mu fuskanci Malam gaba d’aya matsayin ahali.!” Ta k’arashe cikin murya irinta mai kuka. Inna Dije ta matso gareta ta dafata kad’an “Suwaiba Hak’ik’a kurakurai mun riga mun taptapka a baya. Gyaran da zamu masu kenan shine mu gyara gaba.” Umma ta jinjina Kai a hankali tana duban Inna Dije itama Inna Dijen Umma take duba ko wanne da abinda yake sak’awa cikin zuciyarsa. ** Hilal yana isa gida kaman jira take ta soma kiransa. Ya murmusa kad’an yana mai lumshe ido dukda jikinsa Ya basa ba kalamai masu dad’i zaiji cikin wayar ba. Ya d’aga yana jiran da mai zata fara. “Wai Kai dan Allah a sau nawa zance maka ka daina shiga al’amarin ahalina..? Shin bakada wani abin yi ne? Ko kuma dai ka zama wakilin wanzar da zaman lafiya ne.?!” Ya murmusa kad’an yana mai relaxing cikin kujerar motar “I’d rather become a Peacemaker and a unifier da ace na zama mafad’aci..” Kafin yakai aya yaji an finciki marfin motar an fuzge wayar. Ba kowa bace face mahaifiyarsa. Khulsum wacce batasan meke faruwa ba daga d’aya b’angaren taci gaba “Ni Khulsum Ina maka gargadi na k’arshe da ka daina shiga hidiman ahalina dan zaman lafiyarka da naka ahalin.!” Asshe dake huci ta katseta “ Ke mai kika ce.?!” Ta fad’a da mamaki tana duban Hilal da Ya zuba ma sarautar Allah ido. Khulsum kaw tinda taji muryar mahaifiyar Hilal cikin wayar sai ta katse kiran a daburce zuciyarta na tsinkewa. Asshe ta dubi Hilal da tuni ya fito daga cikin motar “Mai ya had’aka da yarinyar nan Hilal.? Nace mai ya had’aka da ita.?” Ta shiga salati tana dafe k’irji “Na shiga uku ni Asshe Sun ranste sai Sun lasheka.! Ka amsa min Hilal!” Ta k’arashe kaman zata rufesa da duka. Daidai lokacin Motar mahaifin Hilal Ya shigo gidan. Yanda sukaga yanayinsa daga ita Har Hilal d’in Ya d’aga masu hankali. Musamman yanda sukaga Ya nufosu a zafafe ga wane irin kallo da yake bin Hilal d’in dashi. Yana k’arasowa yace su biyosa parlornsa. Asshe ta dubi Hilal Wanda shima ita ya duba cikin tunanin yanayin da yaga mahaifinsa ciki. Suna shiga ya nuna ma Hilal saman carpet gabansa “Zauna nan.!” Ba musu ya isa ya zauna yana kokarin gaida mahaifin nasa Wanda ko amsawa bai ba. Abinda bai tab’a masa ba tun tasowarsa. Mamaki ya kuma cika Asshe dan tasan Hilal dan gaban goshin mahaifinsa ne Tun tasowarsa. A Cewar sauran ahalin gidan baya laifi idon mahaifinsa. Jiki a sanyaye tace “Alhaji lafiya.. Meke faruwa.?” “Ki tambayi wann D’an naki.!” Ya k’arashe cikin huci yana nuni da Hilal. Ta girgiza kai cikin rashin fahimta tana duban Hilal. Asshe ta kuma duban mijinta duk hankalinta a tashe da yanayinsa. Ta kuma duban Hilal. “Hilal.? Meke faruwa ne wai..?” Kafin Hilal yakaiga bude bakinsa mahaifinsa ya katsesa “Meye dalilin da yasa ka bar karatunka.? Meye dalilin da yasa ka bar makaranta wann karon.?!” Salati Asshe ta soma cikin tashin hankali tana girgiza kai “Hilal.! Makarantar ka kuma bari wann karon ma..? Na shiga Uku ni Asshe.. Hilal asirina kake so ka tona.. Meke damun rayuwarka ne.. Abubuwan da bakai a k’uruciya ba kake so kayi yanzu.?” “Gwara ki tambayesa idan ma shaye shaye Ya fara. Dan wann karon idan ya watsar da karatunsa sisin kobona bazai sake ciwo akansa da sunan karatu ba. Makaranta na nawa aka canza masa.? Sa’anninsa daga masu aure sai masu ‘ya’ya shi Har yanzu baima san ina nasa rayuwar ta dosa ba. Shi ba kasuwa ba shi ba wani sana’an hannu ba shi ba karatun ba. Sanin kanki ne sauran yarana sai Sunyi zaman yaran shago kafin na barsu suyi wani karatu amma shi da yake gata Ya masa yawa gashi nan bai san mai yake ciki ba.!” Cikin tashin hankali Asshe take duban Hilal “Kace mun hutu kake Har yanzu.!” “Makarantar su sun jima da soma karatun wann zangon. Daga gidan Alhaji Halilu nake akwai nasa yaran a makarantar nasu. Muna labari yara sunata hutu yake sanar Dani ai Sun tsufa can Cyprus. Gashi nan ki tambayeshi.!” Ya k’arashe yana nuni da Hilal d’in cikin b’acin rai. Asshe ta fashe da kuka ta mik’e tana nuna Hilal da yatsa tana fad’in bayanta yake son gani. Sai sann Hilal ya katseta “Ammi I didn’t dropout.. Ok.. Ni bar makaranta ba..” “Idan ba bari kai ba mai ya hanaka komawa.?!” Ta tambaya tana kuka. Ya dubi mahaifinsa cikin kwantar da kai “Abba ba makarantar na bari ba.. I Only take.. half a semester off..” Mahaifinsa ya katsesa “Akan mai zaka jingine karatunka na wani lokaci.. Akan mai..? Mai kake yi a nan d’in.?!” Zuciyar Asshe ya kuma tsinkewa kar dai sabida matsalolin zuriyan Suwaiba Hilal ya shashantar da karatunsa. “Tambayarka nake.?!” Mahaifinsa Ya kuma katsesa. “Abba.. Aure nake so a nema min kafin na koma.” Daga Asshe Har Mahaifin nasa da mamaki suke dubansa. Asshe baki sake tace “Aure.? Aure Hilal.? ‘Yar wa kake nema.?” Muryar Mahaifin Hilal d’in ne ya katsesu “ ‘Yar waye yake nema ba shi bane matsalar. Matsalar shine bazan masa aure bai koyi komai a rayuwarsa ba. Kodai ya koyi san’a na basa jari yayi aurensa ko kuma yayi karatu. Amma bazan nema masa auren ‘yar kowa baida sana’a ko aiki ba. Son da nake masa bai kai na sangartasa Har haka ba. Nima nawa iyayen ba haka suka mun ba. Dan haka bazanyi ma nawa d’an kisan gwani ba. He must learn to take responsibilities. Kuyi shawari da D’anki. Kodai ya kama Sana’a ya hakura da karatun yayi auren ko kuma ya ci gaba da karatu kafin yayi auren.!” Yana ida fad’in haka ya mik’e zai fice. Sai kuma ya juyo ya dubi Hilal “Kana jina, ka dawo da duka kud’ad’en da na baka da sunan makaranta. K’wandala ban yarda ka bari wajenka ba. Kar ka bari na sake maimaita maka ka dawo mun da kud’ad’ena.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice. Asshe taji duniyar na juya mata. Ta k’araso gaban Hilal dake duk’e wajen “Ina jinka.. Wace yarinyar ce ta d’auke maka hankali haka..? ‘Yar waye.. Waye mahaifinta a garin nan.?!” Ya d’ago yana murmushi mai ciwo yana duban mahaifyarsa “Ammi is that really what matters now.? Kar ki damu kinfi kowa sanin ko wacece ita da kuma ahalinta..!” Yana ida fad’in haka ta mik’e ya fice cikin sassarfa. Zuciyarsa fal damuwan yanda zaiyi Ya maidama mahaifinsa kud’ad’ensa kafin wa’adin da ya basa Ya cika. Yana ficewa Asshe ta mik’e tana tunanin abun yi. Wacece ta d’auke mata hankalin D’a haka.? Khulsum.! Sunan da zuciyarta ya raya mata kenan. Ta soma girgiza kai tana zagaya parlorn. Suwaiba ta gama da ita da halinta dole ta nemo hanyar da zata raba Hilal da wad’ann harababbun mutane kafin su gama da ita. Dije.! Ita ce ta fad’o ranta. Dije ce kawai zata zamto makamin da zata yak’i Suwaiba da ita. Saurin ficewa tai ta nufi nata sashen. Saidai tana isa ta tadda wayar Anisa na shigo mata. Labarin hadarin su Haidar da Anisa ta sanar da ita ya kuma jagula mata lissafi. Asshe ta shafe goshinta tace “How’s my sister doing Anisa..? Yaya ‘yaruwata take.?” Anisa takai dubanta ga Mommy wacce Daddy ke rik’e da ita Sun nufi mota. Da kyar ya shawo kanta zai kaita gida ta dan huta Tai sallah. Saida yai mata alk’awarin dawowa da ita asibitin ma kafin ta amince ta bisa. Ta numfasa daga nan yanda take tsaye tana wayar “Your sister needs you Ammi.. Gata nan ta kasa barin asibiti. Ta kasa cewa komai ta kasa cin komai sai kuka da kiran sunan Haidar take. Ammi ya kamata ko mai kike ki bari ki zo Abuja.. Ki raba Haidar da annobar da kika lik’a masa kafin tai ajalinsa.. Dan tinda ta shigo ahalin tashin hankali ne ke kunno kai na yau daban na gobe daban. And worse part d’in shine ta lashe Zuciyar Mommy bata ganin laifinta. Tana mata wani irin soyayya da bazai bari ta bud’e idonta ta gane cewa ita d’in annoba ce kuma had’ari ce ga rayuwar Haidar.. Ammi only you.. Ke kad’ai ce zaki iya raba wann jarabbabben aure da kika nemar ma Haidar. Dan idan ba kece kika bud’i baki kikace Ummul annoba ce Mommy bazata tab’a yarda ba.!” Zufa yaci gaba da karyo ma Asshe dan yanzu wani masifan da ya b’ullo mata ya wuce gaban tasa k’afa ta tsallake. A halin yanzu ba rayuwar Haidar bane kawai akan layi harda rayuwar nata d’an Hilal. Dan tayi imani tsautsayi da masifa ke bibiyan Suwaiba da ahalinta.. Bazata tab’a bari Hilal dinta Ya fad’a cikin wann bala’i ba. Nan take ta sanar da Anisa zata kira Mommy amma bata jin zata samu zuwa duba Haidar a daidai wann lokacin domin kuwa wani wutan zata kashe. Dole ta saka ma Suwaiba birki. Anisa tace da mamaki “Ammi yanzu ita Ummul d’in Har tanada ‘yaruwa da Hilal ya k’yalla ido kanta.? Ammi wai mai kika gani so special gameda mutanen nan ne kam da kika jajibo mana su..? Ammi yanzu kina so kice mun Abba yace Hilal ya maida masa kud’ad’ensa.?” Asshe tace “Wann ba matsala ta bace Anisa. Tinda nasan D’anuwanki kobon mahaifinku bazai ciwo ba zai maida masa. Da ace kece sai na damu.” Anisa ta katseta “Ammi you are wrong.!” Asshe tace da mamaki “Mai kike nufi.?” Anisa taci gaba “Ammi.. Bana jin Hilal yanada kud’ad’en maida ma Abba yanzu.” Tai maganar kanta staye. Da mamaki Asshe tace “Kan mai zaki ce haka.. Kinsan wani abu ne..?” “Ammi Hilal ya tura mun kud’ad’en dake account d’insa.!” Da mamaki Asshe tace “Ke ban fahimceki ba mai kike nufi..?” Take Anisa ta labarta komai yanda Leenah taita karb’an kud’ad’e wajenta ita kuma tana tambayar Hilal. Asshe ta koma ta zauna gijif saman gado tana dafe kai “Kin kashe ni Anisa..!” Take zuciyarta ta soma ayyana mata Yanzu idan Hilal bai maida masa kud’ad’en ba dole k’arshe zai fad’i gaskiya cewa ma Anisa ya bada. Idan aka isa nan.. Magana zai fito fili.. Komai zai bayyana. Mijinta zai San ta tafi gidan boka. Aunty Kwaise zata San ta ha’inceta akan auren Haidar da Ummul. Wani b’angare na auren da ‘yaruwarta bata san dashi ba zai bayyana. Snn ‘yarta Anisa zata shiga uku. Gaskiya zai bayyana cewa ita ce sanadin rufe Aunty Kwaise da akai. Ahalin zai tarwatse .. Bazata bari hakan ta kasance ba.. Bazata bari ba. Gaba d’aya Asshe ta daburce ta susuce. Ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba. Daga ita Har Anisar kuka suke. Ko wanne na jingine laifi ga d’aya b’angaren. Anisa na kuka

Chapter 36 of 64