Share this page
bazata bari Mommy ta tafi prison saboda ita ba. Sauri sauri ta isa k’ofa ta murda makullin ta soma k’ok’arin fitowa a hankali cikin sand’a. Tana tafe tana waige waige ga tsoro da Ya cikata. Saidai tana zuwa k’ofan da zai fitar da ita waje taji gam an rik’e hannunta. K’iris Ya rage bata saki k’ara ba amma sai taji an toshe bakinta. Ta d’ago idonta masu cikeda tsoro tana duban Haidar dake huci yana dubanta. A matuk’ar tsare yace “Are you trying to escape.? Where do you think you are going.? Answer me.! Guduwa kike so kiyi..?” Girgiza kai take hawaye naci gaba da gangaro mata. Haidar yaci gaba da janyota yana fad’in bazata bar wann gidan ba Har sai tayi abinda ya umarceta. Da k’arfin gaske Ya tura k’ofan d’akin Ya jefata ciki. Cikin rawar jiki Ummul ra soma k’ok’arin rarrafowa tana fad’in “Dan Allah kar ka sake rufeni.. Dan Allah Kaji tausayi na ka kyaleni na tafi.. Na maka alk’awari bazan zauna cikin rayuwarka ba.. Dan..!” “Shiiii..!” Ya mata alama da yatsarsa saman labb’ansa. Ya duk’a gabanta yanda take nan duke tana hawaye cikin rawar jiki. Sai ta soma k’ok’arin matsawa baya ganin Ya duk’o gabanta suna fuskantar juna. Ga zuciyarta da bai daina tsinkewa ba. Haidar ya dan d’auki lokaci yana dubanta kafin ya kauda kansa gefe. Hannu yasa ya kamo hannunta cikin k’ok’arin hanata ci gaba da matsawa. Tsoro Ya hango sosai saman fuskarta. Sai ya soma sassauta rikon da yai mata a hankali. D’ankwalinta da ya fad’i gefe ya d’auko. Ummul taga Ya kuma nufota taci gaba da k’ok’arin matsawa Har saida ta isa jikin gado. Ga mamakinta bai mata komai ba sai rufa mata D’ankwalin da yai. Ya kuma duk’awa gabanta suna fuskantar juna. Ta sadda kanta kasa tsoron dake fuskarta bai gushe ba. A hankali ya soma fad’in “Look, you can call me a monster, but I don’t hate you… And..that doesn’t mean I like you either.. Kuma idan har kikayi abinda na sakaki.. Believe me, I’ll let you go..” Ta dago raunannun idanunta tana dubansa. Sai Ya jinjina mata kai a hankali alamun tabbatarwa. Dubansa take shima ita yake duba. Sai ta sadda nata idon a hankali tana mai girgiza masa kai alamun a’a. Cikin sanyin murya mai gauraye da rauni take furta “Ubangijina Ya bani umarni da nai maka biyayya cikin abinda bai sab’a masa ba. An shar’anta wa mace neman al’jannah a k’ark’ashin mijinta. Kaman yanda shima namiji nashi aljannar yana k’ark’ashin mahaifiyarsa. Ka sani Mommy da kake k’ok’arin turawa kurkuku naka aljannan ta wajenta aka ce ka nema.?” Shiru baice komai ba. Ummul ta goge hawayen da suka gangaro mata kafin taci gaba “Shin akwai D’an Adam din da zai wasa da aljannarsa.?” Cikin k’arfin hali Tai maganar dukda zuciyarta dake bugawa. Katseta Haidar yai da fad’in “Shut up.!” Ya katseta yana mai nunata da yatsa kafin yaci gaba “Who do you think you are.?” Ya kuma girgiza Kai yana rage muryarsa cikeda gargad’i “You don’t have the right to speak to me that way.?” Sai ta tsinci zuciyarta da ba ma Haidar amsa da fad’in ‘Ni matarka ce.!’ Kaman Wanda yaji amsar da Zuciyar nata ta bayar sai yaci gaba da jinjina Kai had’ida furta “Kiyi gaggawan yin abinda na umarceki for your own freedom. You don’t want to live with a monster as a husband.!” Ya k’arashe yana tsareta da ido. Girgiza masa kai tai “Kai ba mugu bane. Kana kuma da zuciya mai kyau.. Wanda har zaiji tausayin dabba Ya bata abinci bana jin zaik’i jin tausayin mahaifiyarsa wacce tai sanadiyar zuwansa wann duniyar, ta rainesa har kawo girma..” Katseta yai da fad’in “Enough.! Ya isheki haka.. You don’t know anything..! Ke baki san komai ba gameda wann matar.!” Sosai Ummul ta razana da yanayinsa. Haidar yaci gaba cikin tsananin huci “Yes you might be right.! Watak’ila tayi sanadiyan zuwana wann duniyar. Amma naso ace ta barni na Mutu ina yaro da rayuwar k’unci da ta bani.! Yes. Watak’ila ta raine ni kaman yanda kikace. But I was sacred the whole time!” Yaci gaba da jinina Kai yana duban Ummul da idanunsa da suka kad’a sukai jazir “She raised me while degrading me.. While insulting me.. She raised me locking me up in a dark room. Forcing me to eat papers. She raised me punishing me for her sins.!” Yaci gaba “Because of her.. I grew up feeling low self esteem, feeling insignificant… I had a hard time living in myself..!” Yaci gaba da huci yana jinjina akai “And for years… It took me years to overcome the fear and the trauma..!” Ya matso da fuskarsa kusan nata “Did you know na girma ina shakku da kokonto if she’s really my real mother.? Do you know how it feels ka girma cikin shakku da kokonton sanin wanene kai.?!” Suka dauki lokaci a haka suna duban juna hawaye na gangaro ma Ummul. Haidar ya matso kusanta had’ida sassauta murya “So don’t act like you know everything.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice ba tareda ya kuma yunk’urin rufeta ba. Tana jin sautin tashin motarsa. Tai saurin Lek’awa nan taga Ya fuzgi motar ya bar wajen a guje. Tabi bayan motar da kallo Har ya b’ace ma ganinta. Sai ta tsinci kanta da masa addu’an kasancewa cikin aminci. Jiki a sanyaye ta dawo da baya ta zauna saman gado had’ida rapka tagumi. Ta rasa mai zuciyarta ke ji gameda al’amarin Haidar. Idan ta fahimcesa kaman dai ya amo da abinda ke masa ciwo a zuciya ne. Har k’asan zuciyarta bata jin shid’in mugu ne. Sai ta stinci zuciyarta da tausaya ma rayuwar Haidar d’in. Dan bayan abinda ya gama amo mata ta fahimci alak’arsa da mahaifyarsa ya samo nakasu ne tun yarintarsa. Sosai taji tana son sanin asalin wanene Haidar. A wata fuskar sai tana ganin kaman shida ita sunada k’addara mai kamanceceniya musamman a b’angaren abinda ya shafi alak’arsu da iyayensu. Tunanin Umma da irin rabuwar da sukai ya fad’o mata.. A hankali ta lumshe idonta hawaye na gangaro mata. Ranan har dare bata kuma saka shi a idonta ba. ** Hisham yai tsaki a karo na ba adadi. Da alama amfanin Dareen ya k’are cikin rayuwar Haidar. Da alama Anisa ce kawai yanzu zatai masa amfani wajen cimma burinsa. Idan kuwa har amfanin Dareen ya k’are baiga amfanin zamanta da Haidar ba. Watak’ila idan asirin da Dareen tai masa ya karye Haidar zai fito da Ummul daga yanda ya b’oye ta. Bazai iya jure rashin sanin ina Haidar yakai Ummul ya b’oye ba. He knows Haidar so well. Idan zai Mutu bazai tab’a sanar da kowa ga yanda ya b’oye Ummul ba. Shi mutum ne da ke aiwatar da abubuwansa ba tareda shawarin kowa ba. Shi mutum ne da baida kusanci da kowa face zuciyarsa da abinda ta raya masa. Idan kuwa har haka ne Dareen batada wani amfani. Da ita da dodon nata k’arya suke. Tinda asiri baiyi wani aiki ba ya kamata ya gwada tactics d’in Anisa. Watak’ila ta haka zai samu ya mallaki Ummul. Shi Akan ya rasa Ummul ya yarda zai iya abandoning mission d’insa na ganin bayan mahaifinsa wato Engr Aliyu Maitama da ahalinsa. Da wann tunanin ya mik’e yana huci yana ayyana a cikin zuciyarsa bazai tab’a bari ma Haidar Ummul ba. Soyayyarsa ga Ummul ne last abu da ya kamata ya tabba bai bari Haidar ya rigasa samu ba. Hajja ta saka masu albarka dashi da ita. Ummul bata cancanci miji irin Haidar ba. Bata cancanci zama cikin ahali irin na Maitama ba. Akan ya mallaketa ya yarda ya rasa komai. Ya isa ya janyo wani drawer. K’asan drawer d’in ya daga tile guda sai ga wani bak’in tulu an rufe samansa da jan kyalle. Dama shi yake ajiye da wann tulun Wanda hakan yasa ya rik’e Dareen a tafin hannunsa. Dareen batada say sai abinda Hisham ya fad’i dukda da ita da sunanta da sumarta da na Haidar aka had’a akai asirin amma batada say dan bata san ina Hisham ya b’oye tulun ba. Shiyasa a kullum take bin Hisham a sannu dan Dodon tsafi ya sanar dasu duk randa wann tulun ta fashe asirin zai karye sann Haidar zai rabu da ita zai nuna bai ma tab’a saninta ba. Koda Hisham yaji haka sai yai wuf ya d’auke tulun ya b’oye dan ya samu ya rik’e Dareen cikin hannunsa ta dinga yin duk abinda ya Umarceta. Wann dalili yasa Dareen batada say sai abinda Hisham ya fad’i sabida Tulun na wajensa ya masa b’oyo mai nisa kaman yanda Dodo ya sanar da ita. Hakan yasa Dareen ke bin Hisham a sannu gudun kar ya fasa wann tulun ya karya asirinta na kasancewa matar Haidar. Sauri sauri ya fito daga gidan nasa tulun rungume cikin hannunsa. Dareen na tsaye haraban gidan tana faman safa da marwa ta hangi Hisham na zuwa. Tai tsaye Cak tana dubansa k’irjinta na bugawa. Bata Ida razana ba saida ta hangi hannun Hisham rungume da bakin tulun da Dodo ya k’ulla aurensu da sumarta da sumar Haidar ya rufe cikin wann tulun ya kuma tabbatar mata matuk’a wann tulun na nan yanda yake aurensu da Haidar babu abinda zai samesa sai mutuwa ce zata raba. Ta nufo Hisham cikin rawar jiki tana fad’in “Finally ka zab’i ka dank’a min ajiyan makullin aurena da Haidar.!” Tai maganar murmushi saman fuskarta. Dakatar da ita Hisham yai da fad’in “Stay right there.!” Dareen taja ta tsaya zuciyarta naci gaba da tsinkewa. Cikin rawar murya take furta “Hi….Hisham.. What’s going on..?” Murmushi Hisham yake da gefen baki “You are no longer useful to me.. Kuma kinsan abinda nake da mutanen da basuda sauran amfani wajena.. I dispose them.. Just like this..” Ya k’arashe yana k’ok’arin sakin tulun. Dareen ta zaburo tana k’ok’arin yowa Kansa “No Hisham don’t do this.. Please kar ka aikata min haka.. Kar ka tsinka igiyan aurena da Haidar.. Wllhi I truly love him..!” Dariyar rainin hankali Hisham yai “Love.? Did you just say love.. How is that relevant.? Ta ya zakiyi soyayya da mutumin da bashi a hayyacinsa. bai san dake ba ko ince baisan da Aurenki ba.? Ko kuma nace idan ma ya sani auren na fluctuating cikin kansa.” Dareen ta girgiza Kai tana hawaye “Watak’ila baisan ya akai Aurenmu ba amma nayi alk’awarin kare wann auren till my last breath. You can’t break our marriage Hisham.” Ya kuma murmusawa har lokacin bak’in kwaskon na cikin hannunsa “Na tuna miki yanda akai kuka hadu ne.?” Ta kasa cewa komai sai hawaye dake gangaro mata. Hisham yaci gaba “Wani rana ne a airport. Zamu tafi wani construction work Lagos muka hadu dake a jirgi. Tinda naga yanda kike kallon Haidar na tabbata kin kamu da sonsa. Kinyi ta k’ok’arin shige masa amma sai kika lura bazaki samu chance dashi ba. Har dai kaman kinyi giving up. Ni na sameki nai Miki proposing idan kina son Abokina da gaske. Kika kuma tabbatar min zaki iya komai dan kawai ki mallakesa. Na baki zab’i cewa zaki mallakesa amma zaki min aiki a jikinsa. Zaki zame min tamkar spy wacce zata dinga nado min komai na duk abinda yake ciki a rayuwarsa domin Nima na cimma burina Kansa. Dani dake muka had’a k’arfi da k’arfe. Ni na nemo Miki sumar Haidar muka had’a da naki sumar muka Kai gaban dodon tsafinku aka k’ulla aurenku da Haidar kaman yanda Dodon ya buk’ata. Ya kuma tabbatar mana duk yanda Haidar yake zai bayyana matsayin mijinki.. Zaki bayyana masa matsayin matarsa.. Haka ne.?” Taci gaba da girgiza Kai tana hawaye. Hisham yaci gaba da murmusawa “Kiyi gaggawan b’acewa daga cikin rayuwar Haidar. Dan idan kika jira na fasa kwaskwon nan Haidar sai ya kusa kashe ki da hannayensa kafin ya mik’a ki ga hukuma.” Dareen na huci take dubansa “Na ranste da Allah baka isa ba Hisham. Baka isa ka rabani da abin kaunata Haidar ba.!” Ta k’arashe tana kokawan k’wace bakin kwaskon daga hannun Hisham. A daidai lokacin Haidar ya k’araso. Hisham na hangosa yaci gaba da kokawan k’wace kwaskon daga hannun Dareen yana fadin “Allah ne ya toni asirinki mushirika. Ni dama na jima da fahimtar ba tsakani da Allah kike zaune da abokina ba. Kuma yau sharrinki zai koma kanki dan sai na fasa wann kwaskon da na ganki dashi. Yau Haidar zai fahimci gaskiyar abinda naita nusar dashi akanki.!” Aikaw garin kokawan k’wace kwasko ya fad’i k’asa ji kake tasss ya fashe. Sai ga bak’in hayak’i na tashi. Dareen ta saki k’ara tana soshe soshe yayinda Haidar ya Kama Kansa da yai wani irin sara masa. Ya duk’a nan wajen yana rik’e Kansa had’ida sakin k’ara da bai san yana yi ba. Nan ya kwanta wajen tamkar sumamme. Hisham yayo Kansa a guje yana jijjigasa yayinda Dareen ta k’araso tana haki ta dubi Hisham dake jijjiga Haidar Wanda da alama ya sume. Ta nuna Hisham da yatsa “This is far from over Hisham. Ko ince shadow ka tsammaci dawowa ta dan nice zan dawo maka a matsayin Shadow.!” Murmushi Hisham yai mata da gefen baki “Kafin ki dawo na Miki alk’awarin na d’auke abinda nake son d’aukewa daga wajen Haidar. Bazaki sameni cikin rayuwarsa ba.!” Ya k’arashe yana mai kashe mata ido guda. Da baya da baya ta dinga tafiya har ta shiga gidan a guje ta soma tattara ya nata ya nata. Hisham ya d’auki Haidar ya shigar dashi cikin gidan ya kwantar sa saman kujera. Bayan ficewar Dareen. Bayan shud’ewar wasu mintoci Haidar ya soma bud’e idonsa da sukai masa nauyi yana jin kaman abin da a kullum yake ji ya masa nauyi a k’irjinsa anyi lifting masa. Wani cunkushewa da yake ji zuciyarsa da kwanyarsa suna masa sai yaji kaman an d’aga masa Abu mai nauyi da aka ajiye cikin k’irjinsa. Tilon abokinsa Hisham ya gani zaune gefensa yana danna masa towel saman goshinsa. Hisham na ganin Haidar ya bud’e ido ya sakar masa murmushi yana hamdala “Alhamdulillah Haidar ka tashi.!” Sosai Haidar ya mik’e yana k’are ma Hisham kallo “Meke faruwa Hisham. What just happened.?” Hisham bai Kai ga basa amsa ba ya hangi hotonsa da na Dareen mak’ale a parlorn ta mak’alk’ale cikin jikinsa. Ya juyo yana duban Hisham zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri. Sai ya mik’e ya isa jikin hoton yana kallo sosai. A hankali komai yake dawo masa. Tin daga had’uwarsu a airport da irin shige masa da taso yi bata samu k’ofa ba. Dan har wajen aikinsu a Lagos ta bisu. Da tsanar da yai mata. Ya kuma tuna Tabbas yayi zaman aure da ita auren da bazai ce ga yanda aka k’ulla ba. Auren da wani lokaci Ya tuna da ita wani lokaci Ya mance da ita. Idonsa naga hoton yake furta “Ya akai na k’are da auren yarinyar nan Hisham.?” Hisham ya mik’e yana mai furzar da huci. Ya dan tako kusan Haidar d’in su duka biyu suna kallon hoton kafin Hisham yai gyaran murya “Tambayar da na jima ina maka Haidar. Ka mance.?” Hisham yaci gaba “Tun a fari ban San ya akai haka ta kasance ba Haidar. Sanin irin k’iyayyar da Kai ma yarinyar a haduwarku ta farko a airport. Ka tuna.? Ganinka kawai da ita nai matsayin matarka bansan ya akai k’iyayyar da Kai mata ya rikid’a ya koma soyayya ba. Soyayyar da har ta kaiku ga aure. Auren da bayan ni ko iyayenka baka sanar masu ba kuma nima ka haneni na sanar masu.” Haidar yai shiru kaman mai nazari dan yasan duk anyi haka. Idonsa ya kada sosai yake duban hotonsu da Dareen yana tuna irin rayuwar da sukai Wanda sai gashi yana son tuno Abu ko tambayarta wani Abu sai ya kasa ko ya mance “How is this possible Hisham.?” Hisham ya girgiza Kai kad’an “Baka a hayyacinka ne Haidar.. Kaga wann..” Ya k’arashe yana nuna masa bakin tukunyar da ya fasa. Haidar ya tako yana duban abun da mamaki. Abun da shi bai tab’a believing ma anayi ma mutane ba balle yayi tasiri akansa. Hisham yaci gaba “Kwanaki uku kenan bamu hadu da Kai ba. Naje asibiti wajen d’aya matarka dake kwance asibiti a tunanina zan sameka can ban sameka can ba. Hasalima Likita ya sanar Dani ka d’auki matarka kun tafi babu Wanda yasan ina kuke. So sai nayi tunanin nan gidanka ka kawota maybe ka had’ata da matarka Dareen. So da nazo sai na tadda Dareen rik’eda wann kwasko da kake gani tanata wasu sunbatu more like rituals, kaman ma yare take dan ban fahimci mai take cewa ba. So sai jikina ya bani wani Abu ba daidai bane. Musamman yanda taketa ambaton sunanka ga yare tanayi ga kuma wann tukunyar cikin hannunta. Koda ta ganni ta razana sosai nan na fahimci my hunch was right. Shine kaga ina kokawan fasawa har Allah ya taimakeni nai nasaran fasa wann kwaskon Wanda ko shakka babu na tsafin ta ne.” Hisham ya numfasa dan har lokacin Haidar bai iya cewa komai “ Ka gode ma Allah Haidar da ya maida mata sharrinta kanta.” Yai maganar yana mai dafa Haidar d’in. Haidar baice komai ba sai komawa parlor da yai ya zauna saman kujera ya k’ura ma waje guda ido. Har lokacin bai dawo daidai ba da alama. Hisham ya dafasa kad’an “Is not easy.. Abinda kake going through ba abu bane mai sauk’i Haidar. Ace ka zauna da mace ak’alla tsawon watanni shida ba tareda sanin ya akai ka aureta ba akwai tashin hankali… Amma na maka alk’awari zata biya abinda ta aikata maka abokina. I’ll look for her yanda ta shiga ta fita.. we can’t let her get away with what she did to you..!” Ya mik’e yana jinjina Kai alamun tabbatarwa. Lokaci guda yasa kai ya fice da zummar neman Dareen. Kai kace da gaske Har zuciyarsa ya damu da Haidar d’in ne. Haidar ya bisa da kallo har ya bace masa ba tareda yace komai ba. Ya jima zaune wajen yanata kallon hotonsu shida Dareen. Bazai ce ga abinda yake ji ba. Saidai wann nauyin da a kullum k’irjinsa ke masa yaji kaman anyi lifting abu mai nauyin. Like he’s free from captivity. Amma freedom da bazaice ga makomarsa ba. Jiki babu k’wari ya mik’e ya fice daga gidan ba tareda ya jira dawowar Hisham ba. A b’angaren Hisham kaw ficewa yai cikin k’ok’arin cimma Dareen dan yasan ta yanda zai bullo mata kafin tai gangancin b’ata masa shirinsa. Saidai koda ya fita bai cimma Dareen ba ga wayarta bata shiga. Yaita buga tsaki yai saurin dawowa ga Haidar dan ya samu yaji ina yakai Ummul ya b’oye. Saidai yana dawowa yaga wayam babu Haidar babu dalilinsa. Ya buga tsaki yana naushin kujera da hannunsa “Damn you Haidar.! Damn you.!” Yayi duk abinda zaiyi ne dan ya gano yanda Haidar ya b’oye Ummul amma da alama Haidar ya fice ya tafi ba tareda ya jira dawowarsa ba. Bayan duk abinda yai ma Haidar d’in still yai zab’i yaita yin abubuwansa ba tareda ya sanar dashi ba. Haka ya dinga tsaki shi bai cimma Dareen ba bai kuma tadda Haidar ba. Ficewa yai yana dialing layin Anisa. ** A b’angaren Haidar kaw koda ya k’araso gidan zama yai a veranda dake nan wajen gidan. Bai bi takanta ba bai nemeta ba sai zama da yai ya daura hannayensa saman k’afafunsa Kansa kife tamkar maras lafiya ko Wanda ke cikin yanayin damuwa. Ta window ta hangi motarsa. Tai mamaki Jin bataji shigowarsa ba yau d’in. Tai saurin mik’ewa ta yafa mayafin doguwar rigarta ta nufo waje. Nan ta gansa zaune ya kifa Kansa ga tsuntsayen da yake basu abinci Sun kewayesa amma ba abincin yake basu ba. Sosai taji mamakin ganinsa haka sai ta soma takowa cikin sand’a kaman mai tsoro ta k’araso Sallama saman bakinta. Amma sai taji shiru bai amsa ba. Ta d’anyi gyaran murya tace “Ka mun izinin…. Zama.?” Nan ma shiru bai amsa ta ba. Sai dai kawai tai ta maza ta zauna daga can gefe dashi tana satan kallonsa ganin bazai amsata ba. Har lokacin Kansa a kife yake. Bai d’ago ba bai ce da ita komai ba. Ta dan sha jinin jikinta sai ta soma kallon yanda tsuntsayen suketa kewayesa alamun suna jira ya basu abinci. Ta saki murmushi a hankali tace “Kaman dai… Kai suke jira..” Yanda tai maganar zaka fahimci k’ok’ari take ta had’a kalaman saman harshenta. Nan ma shiru bai ce komai ba. Ta d’an k’ara satan kallonsa still yana nan yanda yake. Ta maida kallonta ga tsuntsayen “Bari ni na baku…. idan zakuci nawa.” Tai maganar murmushi saman fuskarta. Har lokacin yana nan yanda yake. Mik’ewa tai tana satan kallonsa har lokacin yana nan yanda yake. Ta tafi ta dauko sauran abincin da Haidar ya kawo mata na ranan da ya gabata. Ta k’araso a d’arare tana watsa masu sai suka fara tashi sama suna guduwa. Ta d’anyi rau rau da ido tana kallonsu “Kaga ni basa son na basu.. dan Allah ka amsa ka basu.. Kaga guduwa suke..” Tai maganar kaman zatai kuka tana duban Haidar Wanda sai a lokacin ya dago fuskarsa yana dubanta. Gabanta yai wani irin yankewa ya fad’i gani da tai fuskar nasa cikin wane irin yanayi da zatace bata tab’a ganinsa ciki ba. Ga idanuwansa Sun kad’a sunyi ja sosai. Duk sai jikinta yai sanyi. Ta sadda nata idon a hankali tana tuhumar kanta mai ma ya kawota yanda yake.? Wata zuciya tace ta haka ne kawai zaki iya fahimtarsa idan har kina son sanin wanene shi. Wata Zuciyar ta gargad’eta ‘Anya baki tafi da nisa ba Ummul.?’ Sai ta soma k’ok’arin janye jikinta da nufin barin wajen amma sai taga hannayensa saman nata. Ta d’ago a d’an razane tana dubansa. Shid’inma ita yake duba. Wann karon fuskarsa ya zama pale sosai tamkar ta marassa lafiya. Batasan ya akai ba sai ji tai ya rungumeta sosai cikin jikinsa had’ida kwanto da Kansa saman kafad’arta. Zuciyarta yaci gaba da harbawa. Har lokacin Haidar na nan rik’eda ita idanunsa a lumshe. Yayinda jikin Ummul ya gama yin sanyi. Kaf nauyinsa ya d’aura mata saman kafad’arta. Ta kasa katab’us ta kasa koda motsawa Haidar kaw bai saketa ba. Sun jima sosai a haka kafin taji yana sassauta rik’on da yai mata. Ya soma k’ok’arin mik’ewa tsaye fuskarsa a matuk’ar tsare kaman ba shine ya gama rungumarta ba. Kauda kansa gefe yai kad’an yayinda Ummul tai k’asa da fuskarta cikin sanyin jiki. Saida ya mik’e tsaye sosai ya zira hannayensa cikin aljihun jeans d’insa kafin ya dubeta “Let’s go.” “Na’am.!” Ta fad’a a dan daburce had’ida dagowa tana dubansa. “Pack your things we are leaving..” ya fad’i yana nufan mota. Mamaki ya cika Ummul. Allah mai iko.. Toh kodai Addu’arta ne suka fara karbuwa.. Allah yasa haka ne. Allah yasa Zuciyar Haidar ne ta karkata ga mahaifyarsa kaman yanda take ta addu’a. Cikin sauri ta mik’e tai yanda yace. Tana karasowa yasa hannu ya bud’e mata front Seat ta shige a d’arare. Tana addu’an Allah yasa ba wani wajen zai kaita ba. Ita dai addu’a kawai take cikin zuciyarta tinda suka baro wann gida dake tsakiyan daji a cewarta. Ganin sun nufi gari yasa hankalinta ya soma kwanciya. Bata Ida mamaki ba saida taga sun doso wani dogon gini mai d’aukeda ‘yansanda tin daga waje. Suna isowa yace ta fito. Tai yanda yace tana biye dashi suka shige cikin ginin. Haidar ya nuna mata wajen zama kafin ya k’arasa yai magana da wasu ‘yansanda. Dawowa yai yanda take ya zauna daga gefe. Sai faman rabe raben ido take tana duban wajen. Can ta hango Mommy tafe ta nufo yanda suke. Cak Ummul ta mik’e k’walla na ciko idonta yayinda idon Mommy ma ke k’ok’arin zubda k’walla. A hankali Ummul ta furta “Mommy.!” Tuni Ummul ta soma takowa zuwaga Mommy su duka biyun hawaye ke zubo masu. A yayinda suka cimma juna kuwa sai suka rungume juna suna masu bursting cikin kuka. Mommy ta tallafo fuskan Ummul tana duba murmushi saman fuskarta “I knew you’d come…” Shiru tai tana duban Ummul d’in kaman wacce ta tuna wani abu. Dan ita dai Mommy har kawo wann lokacin gani take turaren da boka ya basu ne mai guba ciki Wanda ya tassama ajalin Ummul. Hannayen Ummul ta kamo, tana mai kuma k’ak’aro murmushi “Are.. You here to withdraw

Chapter 33 of 64