Share this page
you free?” Shiru kaman bazai amsa ba Ya soma yan kame kame Haidar Ya katse sa “You know me. I don’t take no as an answer. Ina jiranka.” Daga haka katse kiran yai. Duban Anisa yai yana huci. Cikin zuciyarsa yake ayyana Ya tsani yanda Haidar keyi kaman wani boss d’insa bayan cewa ko a haife ne shine gaba da Haidar d’in.. Anisa ta katse shirun da fad’in “See Kai gashi yana nemanka amma ni cewa yake anyi restricting zuwan visitors.” Hisham Ya furzar da huci “Kinsan meye matsalar?” Anisa ta girgiza kai alamun a’a. “Bazai yuwu Ummul ta ganni wajen Haidar ba all our plans zasu lalace ne. No Ummul bazata ganni wajen Haidar ba. It will be a disaster.” Anisa ta murmusa “But this is the perfect time da ya kamata ka visiting Haidar because Ummul bata wajensa ta tafi gida. I believe ma Shiyasa ya samu chance na kiranka. Hisham yace “You sure.?” “Hundred percent.!” Ta basa amsa tana mai jinjina kai. “Perfect! Yanzu abinda zaayi kiyi maza ki tafi gida ki rik’eta ki hanata barin gida Har sai nayi alerting naki. Ma’ana sai na bar wajen Haidar.” Anisa tace “An gama Barinyi sauri na tafi kafin ta fito nasan sai ta tsaya tayi wanka tayi wasu abubuwan.” Daga haka sukai sallama da Hisham. Shi Ya nufi asibiti wajen Haidar ita kuma ta nufi gida wajen Ummul. A can gida kuwa Mommy sai nan nan da Ummul take tana fad’in maza maza ta gama shiryawa driver ya maidata. Mijinta majinyaci ne bai kamata ta barosa shi kad’ai ba. Asshe kanta sai mamaki take ganin yanda Mommy keyida Ummul. Lallai Anisa tayi gaskiya da tace idon Mommy ya rufe akan Ummul. Gani take kaman an canza mata ‘yaruwar tata da gaske ne. Gaba d’aya Mommy ta tashi daga Aunty Kwaise da ta sani ta koma wata abu daban. Ita kanta Asshe lamarin tsoro Ya fara bata. Ta zuba ma sarautar Allah ido ta kasa katab’us. A haka Anisa ta iso gidan ta taddasu sai karantar Mommy take tana ganin yanda take ingiza Ummul tayi ta tafi wajen mijinta. Makirin Murmushi Anisa tai tana jinjina kai dan har ta hasasho ta yanda zata tarwatsa Auren Haidar da Ummul. Muddin ta fayyace ma Ummul komai zata fahimci Hajiya Kwaise Maitama azzalumar mace ce ba soyayyan gaskiya take nuna mata ba. Kawai tana mata duk abubuwan da take ne don amfanin kanta da D’anta. Tabbas Ummul zata tsani Kwaise da tsinann auren da tai ma da d’anta Wanda boka Ya had’a. Ta k’arashe tunanin tana mai kecewa da Makirin murmushi. A k’ofan fita daga sashen Mommy Anisa ta cimma Ummul. Suka sakar ma juna murmushi had’ida gaisuwa. Anisa ta k’arada “Ba dai har zaki wuce ba.?” Kafin Ummul ta kaiga bata amsa ta kuma sakin murmushi tana mai dafa kafad’an Ummul d’in “It’s fine, Ya kamata ki tafi kin baro mijinki shi kad’ai… I Miss having you around Ummul.. Kinsan bahaushe yace sabo turken wawa” Suka murmusa a tare kafin Anisa ta mik’a mata jakan hannunta “Ga wann kar na rik’eki da surutu.” Ummul ta d’an girgiza kai kad’an cikin rashin fahimta “Ta mecece.?” “Kayanki ne a ciki. Nayi tunanin na kai miki su asibiti sanin cewa zaki buk’ata amma sai mijinki Ya koreni dasu.. Kamar dai ko yaushe.” Ta k’arashe tana mai k’ak’aro murmushi. Jikin Ummul Ya d’anyi sanyi “Kiyi hak’uri Anisa…” Saurin dakatar da ita Anisar tai “No no.. You don’t have to apologise for his behaviour. Kar ki samu damuwa.. Nasan Haidar since childhood.. He’s rude, arrogant, short tempered.. and sometimes unpleasant to be around.. Ki yarda dani, idan da sabo na saba da halin d’anuwana..” Da mamaki Ummul ke dubanta dan ko ba auren soyya sukai da Haidar ba sosai taji zafin kalaman da take fad’i kansa. Amma sai ta danni zuciyarta ta murmusa “Baki tunanin kalaman da kike sunfi kama da cin fuska.?” Shiru Anisa batace da ita komai ba. Ummul ta murmusa had’ida dafa kafad’ar Anisa “Kar ki damu banyi fushi ba. Dan dik abinda kika lissafo gameda shi kwalliya na d’aukesu. Domin kaw sosai suke k’ara masa k’warjini da birgewa.” Ta k’arashe murmushin nan nata dake tunzura Anisa saman fuskarta. Murmushin da yafi kama da yak’e Anisa ta k’ak’aro “Of course. Haka ne.. Let me walk you to the car..” Ta k’arashe tana mai kamo hannun Ummul d’in suka nufi mota. A hanya Anisa ke ci gaba da fad’in “Mutanen gidan nan sunyi kama da mutanen kirki koda ahalin ya kasance birkitaccen ahali mai tarin gib’i.. Haka ne.?” Ummul ta dubeta cikin rashin fahimta. Anisa ta murmusa “Ko wani d’an adam yanada sirrikansa.. Amma akwai wasu abubuwan da sirri baida muhalli cikinsu. Kamar dai Aure. Haka ne.?” Ummul ta kuma girgiza kai tana karantar yanayin Anisa. Tana danganta maganganun Anisa da tunanin kodai Anisa tana so ta sanar da ita cewa tasan yanda akayi aurenta ne.? Amma batada wani sirri da ta b’oye ma Haidar gameda aurensu face iyaka da Umma tai mata da d’aukacin ahalinta Har na tsawon watanni uku ciki harda mahaifinta dake kwance yana jinya. Bata Ida tunanin ba ta kuma sinkayo muryar Anisa daidai sanda suka isa jikin mota. “Kina tunanin kinsan ahalin gidan nan ne Ummul.? Ko kina tunanin kinsan mijin da aka aura Miki ne.? Ina shawartar ki kar ki zak’e da yawa.. Don’t get too attached. Be warned.!” Cikeda gargadi tai maganar kafin ta murmusa “Akwai abubuwa da dama dake cikin duhu. Ina fatan a lokacin da duhun nan zai yaye miki Ummul bazaki sameni cikin wad’anda suka ci amanarki ba. And you can count on me dan ciwon ‘ya mace ta ‘ya mace ce.” Ta k’arshe tana murmushi had’ida bud’e mata marfin mota “A cikin gidan nan trust no one but yourself Ummulkhair. Tabbas Wani Auren nasara ne. Amma Wani Auren halak’a zai kaika.! Allah Ya tsare hanya.” Ta k’arashe da murmushi. Tana ida fad’in haka ta juya ta shige cikin gida zuciyarta na mata fari k’al. Dan ta tabbata ko ba komai ta cika shakku cikin zuciyar Ummul. Wani abu ma sai randa k’wai Ya fashe gaba d’aya. Tabbas Anisa tayi nasaran jefa mata waswasi da shakku cikin zuciyarta. Shin da gaske ne ita d’in ta zak’e da yawa.? Batasan mai Anisa take son sanar da ita ba. Sann koda wann auren tun usul bata tsammaci farin ciki ko wani abunda yai kama da wann cikinsa tun farko ba. ta tsinci kanta cikin tsananin shakku da rud’ani Wanda bataji irinsa a baya ba. Sann sosai taji tana buk’atan sanin mai Anisa take son sanar da ita musamman gameda mijinta Haidar. Haka har ta isa asibiti tunanin da take kenan jikinta duk a sanyaye. * Asshe bata iya kwanaki garin ba ta tarkasa ta dawo Kano dan sosai ta firgita da lamarin ‘yaruwarta dole ta dawo gida ta samu ta shawo kan matsalar kafin komai Ya ida kwance mata musamman da idonta ya tabbatar mata idan ‘yarta Anisa bata k’arashi rayuwarta gidan yari ba toh kuwa ba shakka zata k’are a turu ganin irin abinda take wanda yafi kama da hauka tuburan duk dan akan Haidar. Da fari ta saka ma Ummulkhair guba a turare sann ta d’aura alhakin kan Mommy har ta tafi jail tai kwanaki dik akan haka. Yanzu ga had’arin mota da ta shirya ma Haidar wanda k’iris bai rasa ransa ciki ba. Lallai ya zama dole tasan abinyi.. Dole ta raba wann jarabebben aure na Ummulkhair da Haidar wanda ta zamto silarsa a farko ko dan ta ceto ‘yarta Anisa. * Kano.. Sun had’e su uku a parlorn Hajiya Asshe. Mama Tani wacce bata jima da shak’an iskan ‘yanci ba, Inna Dije sai kaw Uwar gayya Hajiya Asshe. Tani ta girgiza kai cikin rashin fahimta tana duban Inna Dije “Dije kina nufin kice wann matar ita tayi belina ba sirakan Suwaiba ba.? Sann so kike kice mun duk zaman dad’I da naga kinayi da Suwaiba a halin yanzu dama ba na gaskiya bane.? Dije wai meke faruwa ne.?” Inna Dije ta murmusa tana duban Tani “Tani banda abinki.. Wann ma ai sirkar Suwaiba ce. Kuma ke a tunaninki ni Tani zan tab’a yafe ma Suwaiba da ‘yarta Ummulkhair ne. Kar ki mance a dalilin bak’in k’addarar Ummulkhairi na rasa tilon D’ana Fa’izu.! Kuma ke kinfi kowa sani Tani. Dije bata yafiya sai d’aukar fansa.! Yau d’in nan zan sanar dake wace kalan Aure Suwaiba taima ‘yar D’anuwana dake kwance yana jinya wanda zai zamto Miki makami da zaki kori Suwaiba da Auren cin amana da tai miki. Tani na san komai Suwaiba zata Miki a halin yanzu. Duk wani halacci na k’arya da zata Miki bazaki tab’a mance bak’in cin amana da ta miki na aure Miki miji bayan kin aminta da ita da tayi ba. Haka ne?!” Tani tai shiru tana duban Inna Dije wacce ke sakin huci. Tani sai ta girgiza kai a hankali “A’a Dije. Yo ni a halin yanzu wani makami nakeda shi Wanda zan yak’i Suwaiba dashi bayan yarana da a kullum nake goranta mata cewa sunyi aure suna d’akin mazajensu gasu nan duka sun dawo gida daga wacce miji Ya koroto sai wacce miji Ya gudu Ya barta. K’arewa ma Suwaibar ke kula dasu a lokacin da nake gark’ame gidan gyaran hali. Na sani abinda Suwaiba ta min bazan tab’a yafe mata ba ko mutuwa Malam yayi amma a halin yanzu banida abinda zan yak’i Suwaiba dashi kina gani yarana ma sun koma k’ark’ashin tutar Suwaiba.. Toh mai yai saura.?” “Malam Isubu Yayana shine kad’ai ya miki saura Tani. Dan Dikda kasncewarki ‘yar ta’adda mai saida hakkin miji da ransa da sunan gado ta’addacin da Suwaiba tayi yafi naki kuma dik randa D’anuwana yasan mai Suwaiba ta aikata a lokacin da yake kwance ya rabu da ita kenan rabuwa ta Har abada.. Kuma idan mutuwar auren yaranki ne Ya tsaya Miki ki taya Suwaiba sharan d’aki yanda Ummul zata zauna dan nan da wata d’aya jal Ummul zata dawo gida ta jone da naki yaran.!” Tani ta girgiza kai “ban fahimceki ba Dije.? Mai kike nufi.? Wane irin Aure Suwaiba taima Ummul.?” Carab Asshe ta cab’e “Auren mutuwa.! Auren warware sihiri.! Auren WATA UKU.!” Take Tani ta mik’e a zabure tana dafe k’irji “Na shiga uku ni Tani. Auren mutuwa..?!” SameenaAleeyou*AUREN WATA UKU..!* *43* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* Inna Dije ta jinjina kai “K’warai kuwa kaman yanda kika ji.” Wata ‘yar bazawarar dariya Mama Tani tai irin Wanda bai kai ko ina ba “Haba haba Dije. Dani dake munsan Suwaiba.. Koda ace shashasha ce lamba d’aya bazata tab’a abinda kike fad’a mun ba. Koda ace mafarkin Suwaiba da cikan burinta shine taga Ummul dinta a d’akin aure ko wane iri ne. Dije munsan Suwaiba bazata tab’a gigin jefa ‘yarta a halak’a Har haka ba.!” Asshe ta murmusa tana duban Tani “K’warai kuwa da saninta bazata jefa ‘yarta a auren halak’a kaman yanda tayi ba. Burin Suwaiba shine ‘yarta Ummul tayi aure ko ta halin k’ak’a ko wani iri ne matuk’a sunansa Aure. Tabbas da ace Suwaiba tasan wani irin Aure ta jefa ‘yarta ciki da nadaman da zatayi sai tafi wanda take ciki yanzu.” Ta numfasa kafin taci gaba “A Yarjejeniyar da mukai da nida Suwaiba shine ‘yarta Ummulkhair Auren Kwangila tayi mai k’ayyadadden wa’adi Wanda wa’adinsa watanni uku ne. Sam ban sanar da Suwaiba ga asalin sahihin manufar Auren ba. Hasalima ban sanar da kowa bayan ‘Yaruwata da muka shirya Auren tare sai ku da Ya zama dole na bude maku cikina dan bazan iya wann yak’in ni kad’ai ba. A halin yanzu Babu abinda nake so kaman Ummul ta fice daga rayuwar ‘Yaruwata tinda na kula Ummul ta riga tayi tasiri a zuciyarta. Ba haka na shirya abun ba.. Domin kuwa a halin yanzu ‘Yaruwata mahaifiyar mijin Ummul Auren gaskiya take son D’anta yayi da Ummulkhair ba AUREN WATA UKU kaman yanda muka faro daga farko ba.” Tani ta dubeta da mamaki sai ta girgiza kai “Toh mai kike so muyi a nan.? Ta yaya zamu raba auren da bamu muka k’ulla ba.?” Inna Dije ta murmusa “Mu kad’ai ne zamu iya datsen Auren sabida mu keda kusanci da Ummul da kuma Mahaifyarta Suwaiba. Hajiya Asshe batada abokin tarayya domin kuwa ‘yaruwar tata da tai komai domin ita asirin Suwaiba yayi tasiri akanta tinda gashi ta makance da soyayyar Ummul ma d’anta. A halin yanzu Suwaiba ta aminta da mu Tani. Da wann aminci mu kuma zamu yi amfani mu tsinke Auren ‘yarta sann mu d’au fansar duk wasu abubuwan da tai mana.!” Tani tai shiru kaman mai tunani sai kuma ta girgiza kai kad’an “Amma idan Har Ummulkhair Auren mutuwa tayi mai zai hana mu kyaleta ta Mutu cikin wann aure kinga Babu babban fansa da zamu d’auka kan Suwaiba tamkar ta rasa ‘yarta da ta k’wallafa rai akanta tin haihuwarta. Musamman ma ke da kika rasa tilon D’anki ta dalilin bak’in k’addararta.” Dije tai ‘yar bazawarar dariya wann karon “Idan dan wann ne da na jima dayi Tani. Idan kashe jinin Suwaiba shine fansar ran Fa’izu ai Khulsum tana nan gabana da tuni na b’atar da ita. Kar ki mance ‘ya’yan Suwaiba duk yanda naje nazo ‘ya’ya na ne.. Sann ai mutuwar Ummul bazai mata ciwo ba musamman idan a gidan Aurenta ta Mutu. Hakan na nufin burin Suwaiba na aurar da Ummul Ya cika kenan. Ai bari kiji Tani Ummul ta dawo gida sann tasan duk wani badak’ala da mahaifiyarta ta tafka da sunan Aurar da ita sai yafi komai yi ma Suwaiba ciwo. Dik randa Ummulkhairi tasan cewa Mahaifiyarta ta siyar da ita ne domin ta zamto makarin asiri da sunan Aure zata tsani Suwaiba, zatayi danasanin kasancewarta mahaifyarta sann zatayi nadaman duk wani biyayya da ta jima tana mata. Ba a nan kawai ba, Mijinki Yayana zai tsani Suwaiba zai guje ta Ya rabu da ita rabuwa ta Har abada kai kowa nata sai Ya guje ta. Dan babu Wanda zaiji abinda Suwaiba ta tapka bai kyamaceta ba. Yanzu kin fahimci manufata.?” Ta k’arashe tana tsare Tani da ido. Makirin Murmushi Tani ta saki irin Wanda ta jima batayi ba tin kafin a gark’ame ta a gidan gyaran hali “Lallai dole na jinjina Miki Dije. Wann shiri naki Ya shiryu Ya kumayi daidai da fansar da na jima ina so na daukan kan Suwaiba amanata da taji ta aure min miji bayan na aminta da ita.! Har na hango idon Suwaiba a lokacin da Malam zaiji cewa Matar sonsa Suwaiba ta mik’a yarsa mafi soyuwa ayi tsafi da ita.!” Ta kece da wata iriyar muguwar dariya Dije na tayata. Asshe ta dubesu tana murmushi “Toh ni babu abinda zance sai hamdala tinda dukkanmu mun samu matsaya guda shine mukai Suwaiba k’asa warwas. Abinda zamu maida hankali yanzu akai shine ku kuje kuci gaba da shashantar da Suwiaba kuna nuna mata cewa Lallai kuna tareda ita dan taji dadin sakin jiki daku ta yarda cewa tuba na gaskiya kukayi. Nima kuma zan maida hankali ga ‘Yaruwata da shirye shiryen da take na tariyar Ummul da Haidar da zaran an sallami Haidar d’in daga asibiti. Bazamu bari ayi wann bikin tariyar ba. A daidai wann lokacin zamu k’addamar da duk wani shirin mu sann mu lalata komai. Zan raba D’an ‘Yaruwata da zuri’ata da annobar da na kawo mana cikin zuri’a. Sann ku kuma zaku d’auki fansar ku akan Suwaiba. Duk kun amince da haka.?” Gaba d’aya suka jinjina kai suna masu jaddada k’udirorinsu. ** Abuja… A hankali yake takowa cikin parlorn bayan kiran da Ya samu daga Hajiya Kwaise Maitama cewa tana nemansa. Koda Hisham yaji sak’on nemansa da Hajiya kwaise keyi baiji ko d’ar ba cikin zuciyarsa sann baiyi k’asa a gwiwa ba ya amsa gayyatar nata. Cak Ya tsaya tsakiyar katafaren parlorn na alfarma bayan one of the maids ta masa iso. Wann shine ya kamata ace Ya kasance rayuwarsa amma Hajiya Kwaise ta masa denying. Ta koresa a gidan mahaifinsa tin yana ciki baizo duniya ba. Ya d’aga kai yana kallon wani hoton Haidar da ba’a jima da kafawa a parlorn ba. Shi kansa Haidar baisan da hoton ba dan yana asibiti Mommy tasa aka saka hoton. A Office aka masa hoton bayan ya gama gudanar da wani presentation. Yayi kyau sosai k’warjininsa sosai ya bayyana cikin hoton. Wani irin k’atutun bak’in ciki ya tokari Hisham. Wann duka rayuwarsa ne amma ta sace komai daga gare shi ta baiwa D’anta shi kad’ai. Ya tsane su gaba d’aya. Kuma babu Wanda zai ragar masa cikinsu. Yana nan tsaye wata maid din ta k’araso ta k’araso ta cika centre table da kayan motsa baki. Ta kuma tanbayesa ko yana son tea ko coffe. Ya girgiza mata kai had’ida fad’in kar ta damu abinda ta kawo ya wadatar. Tai excusing kanta ta fice. Har lokacin Hisham na nan tsaye gaban hoton Haidar ya had’e hannayensa ta baya yana kallon hoton. Sallaman Mommy yasa shi kaikaitowa yana dubanta. Kaman ko yaushe Hajiya Kwaise Maitama ta sauk’o zuwa parlorn cikin shigarta ta alfarma. A da saidai ka hango izza da isa a tattare da ita amma a halin yanzu annuri fari’a da walwala kake hangowa a kyakkyawar fuskarta. A sanda take takowar nan Hisham kaw cikin zuciyarsa cewa yake ‘Kece sila.. Kece silar komai.. Baki cancanci yafiyana ba Kwaise Maitama.’ Ta k’araso da murmushinta tana nuna ma Hisham wajen zama “Bismillah zauna mana.” Shid’inma murmushi ne saman fuskarsa ga kwantar da kai da yake irinta girmamawa Wanda zaka ranste Har cikin ransa ne. Saida ya duk’a Har k’asa ya gaida Mommy cikeda risinawa da girmamawa Wanda hakan sosai ya kuma birge Mommy ta kuma jin ta aminta sosai da tarayyarsa da D’anta. Ta amsa da sakin fuska tana fad’in Ya tashi ya hau kujera ya zauna. Hisham yai yanda Mommy tace cikeda girmamawa ba. Mommy ta dubesa bayan ta tambayarsa mutanen gida da aiki. Hisham yace “Kowa lafiya Mommy. Aiki kuma mun gode Allah.” Ya k’arashe da murmushi saman fuskarsa. Mommy ta murmusa tana fad’in Masha Allah. Dak’ik’a ya dan gifta kafin tace “Arc. Hisham ko.?” Hisham ya murmusa “Hisham d’in dai Mommy.” Itama murmushin tayi “A’a gwara dai na baka title dinka. I heard that you are one of our best architects a nan M&M Builders.” Cikin raha da k’ok’arin sako barkwanci take maganar wanda a baya ba d’abi’arta bace. Hisham Ya dan murmusa “K’ok’ari kawai muke Hajiya.” Itama ta murmusa “Toh ma sha Allah. Allah ya taimaka.” Hisham Ya amsa da Ameen. Mommy ta dan gyara zama kafin tace “Hisham wata ‘yar alfarma nake buk’ata daga wajenka.” Ya d’ago Ya d’an dubeta sai Ya girgiza Kai “Alfarma kuma Mommy.. Wace iri kenan.?” Wani folder ta dauko gefenta ta mik’a masa tana fad’in ya duba ya gani. Hisham ya saka hannu biyu ya amsa. Mommy taci gaba a sanda yake warware folder d’in “Plan ne na gida. Ina so ka duba kai nazari akai.” Hisham Ya ida warware folder d’in yana dage takardun yana gani. Mommy taci gaba “I want to surprise your friend.. My son.” Hisham ya dago ya dubeta “You mean Haidar.?” Mommy ta jinjina masa kai “He’s my only son.. Our only son nida mahaifinsa.” Tai maganar da murmushi saman fuskarta Wanda yake nuni da tsananin k’aunar da take ma D’an nata. A cikin zuciyarsa Hisham yace ‘Sabida kinyi sanadin raba d’ayan d’ansa da ahalinsa.’ Amma a fili sai Ya murmusa “Okay.. And mai za’ayi da wann.?” “Nasan kanada masaniyar cewa tsawon lokaci alak’an Haidar da halinsa akwai babban tangarda ciki since you are his best friend and possibly his only friend nasan kanada masaniya kan wann.” Hisham ya jinjina kai a hankali “Haka ne Mommy.. And believe me burina shine Haidar ya shirya da ahalinsa.” Mommy ta kuma jinjina kai “Hakan yasa na gayyato ka domin ka min wann aikin. After all, layinka ne.” Hisham Ya kuma jinjina kai kafin Mommy taci gaba “Wann plan na gidan da na dank’a maka shine gidan da muka fara zama cikinsa nida Mahaifin Haidar wato Engr Aliyu Maitama a lokacin da muka dawo Abuja.. Ina so Haidar da matarsa Ummul su tare a wann gidan da zaran an sallamesa daga asibiti. Na dank’a maka ragamar komai duk wasu gyare gyare da sauye sauye Wanda yayi daidai da ra’ayin Haidar ayisu kafin bikin tariyarsu da zaran an sallamesa daga asibiti. Kai abokinsa ne nasan kasan ra’ayinsa tsare tsarensa. Inaso ayi komai to his taste ta yanda zaiji dadin bazatan. Duk wani abinda ake buk’ata don’t hesitate to let me know. Kar ka mance na sanar da kai wann din Bazata ne. So ko Boss dinka a Office ina nufin Mahaifin Haidar banso ya sani.. Is our little secret for your dearest friend.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. K’ak’aro murmushi Hisham yai dukda mutuwar zaune da yai yana sauraron Hajiya Kwaise kafin ya shiga jinjina kai “Bakida matsala Mommy. Haidar tamkar D’anuwa na d’aukesa ba aboki kawai ba. Zanyi komai to the best of my ability in sha Allah.” Mommy ta murmusa tana dubansa. Yanda yace D’anuwa Ya d’auki Haidar ba aboki kawai ba sosai Ya hakan Ya haifar mata da sanyin jiki. Bata san dalili ba amma sai taji tunanin Fannah da abinda ke cikinta yazo mata. Watak’ila da ace Fannah ta haife abinda ke cikinta idan Ya fito namiji da yanzu Sun taso tare haka da D’anuwansa Haidar tamkar dai abokan. Sai ta tsinci kanta da addu’an Allah Ya bayyana mata Fannah Ya kuma sa ta haifi abinda ke cikinta ko Haidar d’inta zai samu D’anuwa ko ‘yar uwa. Daga bisani mik’ewa tai tana ce ma Hisham Ya saki jikinsa kaman a gida yake Yaci abubuwan da aka kawo masa. A haka Mommy ta bar parlorn duk jikinta a mace sakamakon tuno Fannah da abindake cikinta da tayi. Yayinda Hisham yai mutuwar zaune yana jin shirin Kwaise Maitama. Wai shi Hisham shine zai gyara ma Haidar gidan da zai zaman aure da Ummul d’insa sann gidan ma ba ko wane gida ba. Gidan Mahaifinsa da ya fara zama ciki lokacin da yazo garin. Idan akwai Wanda yafi kowa cancanta da zaman aure tareda Ummul a wann gidan ba kowa bane face shi. Shine babban d’an mahaifinsa sann shine ya fara son Ummulkhair tun kafin Kwaise tai mata k’adararren auren nan da D’anta. She’s so selfish. Ta ya zai fara wann aikin ma.. Just how.? Muryar Anisa yaji a kansa wacce mamaki ya cika sai waige waige take “What are you doing here.? Who invited you.?” Duban Anisa yai sai Ya murmusa “Mu gaisa mana kafin duka wad’ann..” Anisa taci gaba da ‘yan waige waige kafin tai k’asa da murya tace “Is this also part of your games.?” CCTV camera dake mak’ale a parlorn Ya kalla sai Ya murmusa Yace “Neesa long time no see. Ko dan dik rashin lafiyar abokina ne ya b’oyeki kema..?” Mamaki Ya cika Anisa tana duban Hisham dake kurb’an drink din dake hannunsa. Lokaci guda Ya mik’e yai k’asa da murya “Zan iya samun rakiyarki..? To my ride.?” Anisa ta murmusa ta biye wasan Hisham “Sure.. Of course.” Hisham ya nuna mata hanya “After you.” Sa kai sukai suka fice a tare. Suna isa jikin motar Hisham yace “Get in.” Ta dubesa da mamaki “Ban gane ba.. Are you a kidnapper now.?” “Just get in Neesa.. We need to talk.. Somewhere else.” Ba musu ta bud’e motar ta shige kafin Hisham ya shige mazaunin driver ya tada motar suka fice daga gidan. Tinda suka fice daga Hisham ke zabga gudu saman kwalta zuciyarsa na tafarfasa musamman idan Ya tuna aikin da Kwaise Maitama ta basa wai shi Hisham sai zai renovating gidan da Haidar da Ummul d’insa wai zasu zauna. Anisa ganin gudu ba na k’arau ba Hisham na yunk’urin hallak’asu cikin motar ta soma k’ok’arin dakatar dashi “Ka dakata Hisham.! Wai meke faruwa ne.? Why are you so furious.? Where are you taking me to.?!” A harzuk’e ya buga kan steering wheel ya dubeta yace “I don’t know Neesa.! I just don’t know maybe to hell.!” Yanda Yai maganar yana huci gashi bai daina gudu ba yasa Anisa kuma razana ga wata mota gaba garesu Wanda k’iris Ya rage Hisham bai daki bayan motar ba “Hishaamm.!” Ta k’arashe tana daka masa tsawa daidai sanda Hisham ke taka birki a tsakiyar titi. Rufin asirin Allah Babu wata mota bayansu. Ya d’ago yana dubanta cikin huci. Itama d’in hucin take tana dubansa “Just what do you think you are doing.? What’s gotten into you.? Are you trying to kill us or something.?! Meye haka.? Kaga saidai tafi hell d’inka

Chapter 40 of 64