gidansu suna duban masu shigo da lefe.
Tin suna k’irga akwatuna har dai suka hak’ura da k’irge suka zuba ma sarautar Allah idanu.
Azeema ta tab’a Salima tace “Yaya Salima anya wann ba kwari suka saya gaba d’aya ba..!”
Salima ta sauk’e ajiyan zuciya “Ni na ma rasa abin fad’i.”
Gajeren tsaki Badia tai “Mtseww aikin banza.. Wann da gani kasan kayan haya ne ba lefe ba..” Tana ida fad’in haka ta d’age labulen d’aki ta shige.
Azeema ta dubi Salima tace “Kin ganni nan wallhi baza’ayi hidimar nan babu ni ba.. Gwara na shiga a dama Dani dan nasan duk rintsi sai an sallameni da atampa da jaka da takalmi na samu na yak’an dangin Habibu.
Salima ta tab’e baki “Amma Azeema matsalarki kad’an ce..!” Tana ida fad’in haka itama ta fad’a d’akin mahaifiyarsu. Duk suka zuba tagumi suna Jin yanda hayaniya ke ci gaba da tashi. Zancen guda d’aya ne Ummul tayi dace.
Azeema kaw tuni ta nufi bakin farandar Umma yanda ake baje kolin kayan lefen Ummul. Sai zuzuta kyaun kayan take tana fad’in ‘yaruwarta tayi goshi..
Umma ta dubeta tace “Kar ki damu Azeema dake za’a tafi kai amarya.”
Azeema ta daka tsalle tana fad’in “Wllhi Umma ni har zaman d’aki ma sai na mata ai.. Irin wann kayan bajinta kayan alatu haka. Kai ina ma nice mai sa’a irin Ummul..”
Anzo yanda Umma take so. Taji ana ambaton Ummul d’inta da mai sa’a.. Umma ta shiga washe baki tana jin yanda mutane ke fad’in K’warai Ummul tayi goshi ita d’in mai sa’a ce.
Haka akaita shigo da zuk’a zuk’an akwatina da sunan lefen Ummulkhairi. Kan kace me labari Ya karad’e unguwa.
Umma naku fah ba’a sama ba’a k’asa, uwar amarya da kanta. Duk magulmatan unguwar masu tsegumin Ummulkhairi ta kasa auruwa Sun dawo b’angaren Umma. Mama taga tijara a wann ranan, dan tuni Umma ta amshe girman nata kama daga cikin gida har zuwa wajen mutanen unguwa Wanda a baya suke aibata su.
Uwa uba da sukaga su Hajja Asshe matsayin iyayen mijin da zai auri Ummulkhairi dan tuni d’aya daga cikin kawayen Asshe ta soma bada bayanin ko su waye su. Hakan ya kuma sanyar ma kowa gwiwa dan mijin Asshe dai ba b’oyayyen mutum bane a birnin Kano da kewaye. Hakan Ya kuma tabbatar masu Umma dai ba hark’ar shan jini ta fad’a ba kaman yanda duk sukai zato a baya. Allah ne ya kashe ya basu. Lokacin su ne yayi.
Azeema sai kallon Hajja Asshe take sanda taji tana yabon surkarsu Ummul. Sai duban dank’ara dank’aran gwal d’in dake zube wuyarta da awarwaron dake hannunta take. Ga wani k’amshin ‘yan gayu na musamman da matan suke. Dan Asshe ita da K’awayenta suka kawo lefen.
**
Yanda Mama taga rana haka taga dare. Ko asibiti wajen mijinta ta kasa komawa tinda taga an kawo lefen Ummulkhairi. Ta mik’e ta shiga safa da marwa a d’an tsukikin d’akinta tana neman hanyar da zatabi ta hana yuwan wann aure.
Wani tunani ya fad’o mata. A fili ta furta Dije. Dije ce kawai zata sa wann aure Ya watse.
Cikin sauri ta isa tana bubbuga k’afar Badia wacce tinda Tasi’u Ya b’ace ta dawo kwanan gida.
“Badia, ke Badia.. Tashi mana..!”
Badia ta mik’e tana mutsuka idanu da kyar “An fara shagalin bikin ne..?”
“Shagalin bikin Ubanki..!” Mama tace tana danna mata dak’uwa.
Badia taja tsaki tana turo baki gaba “Haba Mama ni wllhi na zata shagali aka soma inata mafarkin mun tafi Kai amarya an raba mana motoci matsayin tukwici kin wani kama kin tashen.”
Mama ta kuma danna mata harara “Dan ubanki murna kike wann annobar zatai aure bayan ke ga naki auren yana sama yana k’asa. Allah kad’ai yasan yanda wann macucin mijin naki ya gudu.. Ba abun muyi k’ararsa ba mu tona ma kanmu asiri…”
Badia tace “Mama Tasi fah ba guduwa yai ba. Ni na tabbata yana can yana juya mana kud’ad’enmu sai yayi arziki kaman mijin da zai auri Ummul kafin ya dawo. Na fad’a Miki ko jiya fah Munyi waya dashi.”
Katseta Mama tai tana mai kuma danna mata wani ashar d’in “Ashe ke babbar shashasha ce. Yacce kika san Suwaiba ce ta haifeki.. Ba dan ina tsoron tonuwar asirina ba ace na saida gadon mijina tun kafin ya mutu wllhi da na maka k’arar wann d’an iskan mijin naki a Kotu..”
Badia ta shek’e da dariya “Toh ai saidai ki maka k’arar wofi Mama. Dan Tasi dai ba ganinsa zakiyi ba sai Ya zama hamshak’in Mai arziki ya dawo mana da kud’ad’en mu.. Wai baki so muyi arziki kaman nasu Ummul ne..”
“Idan kika sake kira mun Ummul a nan zan zagi gawa ka k’i kabarin uban nan naki dake kwance. wann aure kuma ba yinsa za’ayi ba dan alwashi na d’auka. Bani wayarki..” Ta k’arashe tana mik’a mata hannu.
Badia ta dubeta sai kuma ta mik’a mata “Mama me zakiyi da wayata, ni dai dan Allah kar ki kira Tasi ki zagesa dan nasan halinki..”
Bata amsata ba sai ta mik’a mata nata wayar “Ungo nemo min lambar Dije.. Allah Sa dai bata canza layi ba..”
Badia ta dubeta galala “Mama Inna Dije kike nufi ko wa..?”
“Dije k’anwar Ubanku Isubu kira mun ita..”
Badia tace “Mama me zaki fad’a mata a tsohon daren nan.. Sanin kanki ne Inna Dije da Abba harma da ahalinsa sun raba gari tun da jimawa..”
Mama ta jinjina kai “Waye sila..?”
Badia tai k’uri tana dubanta.
Mama taci gaba “Suwaiba da bakinta ta fad’a cewa ‘Yarta Ummul ita tai sanadin barin Fa’iz duniya dan haka zan kira Dije na sanar da ita komai na kuma kunna mata recording d’in da kikai a wayarki lokacin da Suwaiba ke fad’in Ummul ce tai Sanadin Fa’iz.. Sai muga ta yanda za’ayi ai wann aure tinda naga su ‘yan uwan mahaifin naku an rufe bakinsu da kud’i.. Dije ita kad’ai ce zata saka birki ma wann aure..” Ta k’arashe tana kecewa da dariyar cin nasara. Tana ayyana yanda za’a wayi gari da labarin an fasa auren Ummulkhairi.
Saidai duk Neman wayar Inna Dije da suke basu samu ba cikin daren. Akan dole Mama ta hak’ura da niyyan washe gari idan Allah ya kai rai zata nemi wani hanyar dan bazata hak’ura ba. Duk rintsi sai ta cimma Dije an wargaza shirin wann auren.
**
Khulsum ita kad’ai ta kwana wajen Abba. Tana zaune gefensa hawaye na gangaro mata. Hannunta saman nasa “Abba.. Abba na Kai hak’uri. Allah ya jarabceka da cuta kaman yanda ya jarabceka da ahalinka. Abba Allah masu imani yake jarabta. Ina rok’onsa da ya baka lafiya ya kuma baka ikon cin jarabawa.” Taci gaba da kuka tana mai kwantar da kanta gefe da mahaifinta. A hankali taji kaman Abba na motsi. Khulsum tai saurin d’agowa tana dubansa, sai taga kaman bakinsa na motsi. Ta matsa kusa dashi cikin sauri tana kai kunnenta saitin bakinsa dan jin abinda yake son fad’i.
Tai saurin d’aura hannayenta saman nashi “Abba gani a nan. Khulsum ce Abba.”
Amma sai taji kaman yana ambaton Ummulkhairi cikin maganan da bai iya fita sosai.
“Ummulkhairi.!” Khulsum ta nanata a hankali. Cikin sauri ta dubi Abba “Abba zanyi k’ok’arin dakatar da ita. Bazan bari Umma ta cimma makahon burinta Akan ‘Yaruwata ba. Abba zan dakatar Adda Ummul kaji..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin mik’ewa. Sai kuma ta juyo ta dubi mahaifin nasu Wanda babu kowa wajensa sai ita. Toh idan ta fice wani abun ya taso fah,.? Ko ma wani abu ya samu Abba.? Kasa ficewa tai sai komawa da tai ta zauna tana tinanin taje ta dakatar da ‘yaruwarta ne ko kuwa ta zauna da Abbanta ne.? A hankali ta lumshe idanunta tana jin wani abu mai ciwo na tasowa daga cikin k’irjinta. Batajin har abada zata kuma iya kiran ahalinta da sunan ahali. Nan taci gaba da sak’awa tana warwarewa taje ta sanar da Ummul Abba ya ambaci sunanta ne kokuwa ta k’yaleta da makauniyar biyayyan da take k’ok’arin yima Umma.
**
Asshe da gogaggun k’awayenta Sun samu hallarowa da Kayan lalle nik’i nik’i. Dan dama sassafe aka taho da Ummul d’in gidan. Umma tace saidai azo gidan mahaifinta a d’auketa kaman yanda yake a al’ada bayan an d’aura aure.
Mama ta zuba ma sarautar Allah ido ganin matan nan harda masu algaita suke tafe suna masu rakiya. Sai Asshe ta isa ta kamo hannun Umma suna tik’an rawa tare ta b’alle bandir ‘yan dubu dubu ta shiga lik’a ma Umma. Su Maman Sahal magulmata Unguwa da sauran ‘yan cikin gidansu Ummul kaw fitowa sukai suna tayasu tik’an rawa sai damben kwasan kud’ad’en da Asshe ke lik’awa suke tsakaninsu da masu algaita.
Mama ta kuma rapka uban tagumi. Ikon Allah yanzu Isubu na kwance gadon asibiti Suwaiba take wann bariki a cikin gidansa. Idan sunanta Tani wann aure baza’ayi ba. Ta mik’e ta cikin k’ok’arin dakatar da masu algaita tana fad’in irin fashe fashen auren Ummul da bak’in k’addara da yake biyeda rayuwarta. Idan har suna nema ma d’ansu lafiya kar su had’asa da annoba. Sai aka maida Tani Mahaukaciya dan babu Wanda ya d’auki zancenta. Iyayen ango kam ma ko kallo bata ishesu ba suka sa aka fito masu da Amarya Ummul Asshe na shafa mata lalle da kanta da turare iri daban daban, harda wasu tufafi irin na al’adansu da suka zo dasu aka rufa ma Amarya Ummul.
Bayan komai ya kammala Asshe ta juyo ta dubi Tani “Munyi abinda ya kawo mu a yanzu. Sai kuma mun zo tafiya da Amaryar mu..!” Har zata shige ta kuma juyowa ta dubi Tani “Sai hak’uri haka zakiyi ta cin karo damu cikin gidan nan idan ba amaryarmu muka d’auke muka ba.!”Daga haka sa kai sukai suka fice k’awayen Asshe na raka Tani da wulak’antaccen kallo.
Su Baba Dauda da Baballe k’annen mahaifin Ummul suka take ma Asshe baya kaman zasu bangaji Tani. Nan suke sanar da Asshen indai Ummulkhairi ce Sun bawa D’ansu duniya da lahira Allah basu zaman lafiya Ya kad’e fitina.
Asshe ta murmusa tana gyara mayafinta kana ta dubi Baba Dauda tace “Ma sha Allah. Alhamdulillah, naji dadin wann batu kuma akwai sauran aikenku na nan tafe..”
Baba Dauda suka dubi juna suna washe baki.
Asshe taci gaba “Iyayen Aliyu zasu iso nan bada jimawa ba. Zasu kawo kudin aure da duk wani abinda ake buk’ata na Al’ada. Babu b’ata lokaci nake so a d’aura auren nan..”
Baba Dauda yace “Alhamdulillahi.. Shikenan, komai ta kankama.. Allahu Akabar.. Oh ashe dai yarinyar nan zamu ga ranan aurenta.. Isubu dai Allah yayi yana kwance yana jinya za’a aurar da d’iyarsa.. Allah Ya k’ara rufa mana asiri. Ai shi auren shine mafi a’ala a gareta.”
Baballe sai gyada kai yake yawa k’adangare “Wann gaskiya ne.. An samu maslaha kan matsalar yarinyar nan daga k’arshe. Yau ko farkawa Yaya Isubu yai yaga Ummulkhairi bata gidan zaifi kowa farin ciki. Musamman idan yaji d’akin mijinta ta tafi.”
Asshe ta jinina kai tana kuma bud’e handbag d’inta. Nan ta ciro kud’ad’e ta mik’a masu “Ga wann kuyi amfani dasu ku canza tufafin jikinku. Dan Allah ko ready made sai ku saya dan wllhi duk wari kuke. Kun San Manyan mutane ne zasu taho amsar auren D’anmu. Bai kamata aga sirakanmu cikin daud’a ba.
Baballe yana wage baki yake fad’in “Wann na jikina ai sabuwa ce Hajiya. Fitar sallah ce..” Yana maganar yana d’ago rigar jikinsa.
Kaman zasu kwanta gaban Asshe haka suka sa hannu suka amshe kud’ad’en suna mata godiya.
Akan idon Mama komai ya auku. Ta dubi Badia dake gefenta “Ki shige muje dan ubanki.. Wllhi bazan zuba idanu a aurar da Ummul ba. Tinda mutanen nan basu jin bari ko da k’afa ne zan tafi garin Dutse na sami Dije da wann labari tinda na gaza samun wayarta.. Wllhi idan ina numfashi baza’ayi wann aure ba..!”
Badia ta kuma riketa “Mama na yaushe, baki alk’alami fah ya Riga ya bushe. Mutanen nan babu abinda zaisa su fasa aura ma D’ansu Ummul.. Kina ganin yanda Hajiyar can ta gwasaleki dan girman Allah kawai ki hak’ura aci hidiman biki damu..”
Mama ta kuma danna mata ashar “Bazan bari Suwaiba da munafukan k’annen mahaifinku Su aurar da Ummul ba.. Dije kuma idan taji recoding din da zan kai mata zata waiwayi gida ko dan ta amsar ma D’anta hakkinsa.. Kinga dole wann aure Ya watse kaman yanda sauran suka watse.!”
Badia tace “Idan kuma kika kira Inna Dije reshe ya juye da mujiya fah Mama..? Ina nufin idan Inna Dije tazo ta fahimci kin saida kaf abinda D’anuwanta ya mallaka kin ci gadonsa tin yana raye fah.. Um um fah Mama.”
Mama ta kuma harzuka “A gidan uwar naci gadon nasa bayan wann shegen mijin naki ya gudu da kud’ad’en. Ai saidai a kama mijinki..”
“Ta Ina za’a kamasa tinda babu Wanda yasan yanda yake yanzu. Ke fah za’a kama Mama..” Badia ta fad’i haka cikeda gargad’in mahaifiyar tata.
Mama na huci take fad’in “Dije bazata san wann batu idan ba kece da shegen bakinki kaman ta’adin wuk’a zaki sanar da Dije ba. Ki zuba min idanu kiga yanda zan kassara auren Ummulkhairi, idan na gama da wann sai naji da D’aniskan mijin nan naki maras mutunci. Dik yanda zai gudu wllhi sai na nemo sa na amshe kud’ad’e na idan yaso auren naki ya mutu..!” Tana ida fad’in haka tasa kai fuu ta koma cikin gida tana sakin huci. Bataga ta zama ba dole tayi shirin tafiya garin Dutse. Ameen
Badia kaw tab’e baki tai had’ida koma cikin gida akaci gaba da hidima da ita.
**
Misalin k’arfe 4:30pm ‘Yanuwan Mommy Maza masu karb’an auren suka samu isowa gidan su Ummulkhairi ciki harda mijin Asshe. Ba tareda wani b’ata lokaci ba suka soma gudanar da abinda Ya had’asu. A yammacin wann rana aka d’aura auren Ummulkhairi Yusuf tareda angon ta Aliyu Aliyu Maitama bayan cika cikan k’ulla aure sun tabbata. A nan k’ofar gidan mahaifinta.
Cak Hajja Fannah tai tsaye daga waje tana sinkayo sunan mijin da ya auri Ummul wanda masu algaita keta faman nanatawa. Aliyu Aliyu Maitama. Sunan da har abada bazai tab’a shafewa a duniyarta da na d’anta ba koda kuwa tayi k’ok’arin kauda sunan. “Aliyu Maitama.” Ta nanata a hankali. Sai kuma ta sake fad’in “Aliyu Aliyu Maitama.?” Shin Aliyu da ta sani ne ya Auri Ummul ko kuma d’ansa ne.? Ko kuma wasu daban ne basu ba. Take rayuwar ta na baya ya soma dawo mata. Rayuwarsu a gida Maiduguri. AUREN WATA UKU da tayi da Aliyu Maitama. Rabon da suka samu a tsakanin WATA UKU Wanda yak’i aminta da wann rabon tin yana ciki baizo duniya ba. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Meke shirin faruwa.? Bata Ida tunanin ba ta hango motoci ‘yan d’aukan amarya Sun samu k’arasowa. Zuciyarta ne ya kuma yankewa. Koda ace shekaru sunja bazata mance kamannin K’anwar kishiyarta Kwaise ba wacce da ita aka k’ulla komai. Bakinta na rawa ta furta “Asshe..!” Ji tai k’afafunta na Neman gaza d’aukarta. Da gaske Asshe k’anwar Kwaise take gani ana mata kirari da uwar ango Aliyu Haidar Maitama. Kenan Ummul d’an Kwaise ne ya aureta.? Kenan Ummul D’anuwan D’anta Hisham da suka had’a uba d’aya ta aura.? Ta ya zata soma sanar da Hisham Ummul d’an Uwansa da baisan dashi ba ta aura.? Bata kuma sanin meke faruwa ba.? Bata kuma sanin ina take jefa k’afafunta ba sai ganin kanta da tai cikin gidanta.
Zama dirshan tai wani irin kuka na taso mata. Meke shirin faruwa da ita. Badai baya ne ke k’ok’arin dawowa cikin rayuwarta ba. Ta jima da binne bayanta. Ta kumayi alk’awari bazata waiwayi baya ba. Sann uwa uba bata shirya sanar da D’anta Hisham asalinsa ba.
Sosai jikinta ke rawa sanda ta soma tuno rayuwarsu na baya.
**
Mama da Tunda taga manyan mutane da sunan sunzo shaida auren Ummulkhairi bata iya jura zama ba. Nan tai azaman tafiya garin Dutse dan ta sanar ma Dije abinda ke faruwa. Koda an d’aura auren tasan idan ta isa ga Dije ta kuma kunna mata rikodin d’in nan dole a warware auren koda kuwa an d’aura. Sann a yanda tasan zafin Dije ko birnin Sin aka Kai Ummulkhairi sai ta bita ta fanshi mutuwar tilon d’anta. Tashan mota ta nufa.
Tana tafe tana tsaka da wann tunani ta hangi Mutumin k’auye da akai cinikin shagon Malam dashi ya kuma saya shagon. Cikin Mama ya bada wani irin sauti na tsoro.
“Yauwa Yallab’ai gatan can.. Itace Tani Uwar gidan Malam Isubu. Kuma itace ta saida mun shago.”
Mama taja wani irin wawan birki tana duban ‘yansanda da suka nufota. Zuciyarta sai tsinkewa. Ta yunk’ura zata gudu saidai babu hali.
Mutumi ya k’araso yana fad’in babu yanda zata gudu sai ta masa kashin kud’ad’ensa.
Mama ta fara kururuwa tana fad’in ita wllhi bataci kudi ba Tasi’u ne ya gudu da kud’ad’en. Bakauye yace baisan wann zance ba shidai kawai a tafi ofishin ‘yansanda.
**
Sauri Khulsum take kan faman zabgawa gashi ko taro batashi balle sisi, da k’afa taketa nik’owa ga uban nisa. Alla alla take ta isa ta dakatar da wann aure. Ji rai Sam bazata bari Umma ta salwantar da rayuwar ‘yaruwarta sabida san zuciya irin nata. Burinta kawai ta cimma Ummul kafin Umma ta aurar da ita.
Hilal daketa faman zabga gudu dan ya samu ya cimma kwatancen da Amminsa ta masa, bai fata a d’aura auren bai isa location d’in ba. Auren d’anuwansa Haidar wanda shi kanshi Haidar d’in bai samu halarta ba. Bai fata ace shima ya rasa auren ko dan ya samu abun goranta ma Haidar cewa shi ya karb’ar masa aure.
Kaman daga sama Khulsum taji a wanketa da tab’o. Taja tai birki tana duban jikinta yayinda Hilal ya buga uban tsaki ya bud’e motar ya fito yana duba yanda tayun motarsa suka b’aci da tab’o. Allah ya gani ya tsani datti ya b’ata masa mota. Da datti ya tab’a masa Mota gwara ya b’ata masa kaya. Hilal irin wad’ann mutanen ne da zasu iya yini maka suna aikin k’alk’ale abin hawansu dan shi bai yarda car wash sun iya wanke mota ba.
“Whattt.!” Ya furta da k’arfin gaske yana zagaye motar daga duk’e yana duban yanda duk tab’o ya wanke tayun Motar zuwa fuskar mota.
“C’mon this is not happening.. I spent half of the day ina wanke motar nan.. What the hell..”
Muryar Khulsum dake tsananin huci ne ya dakatar dashi “Malam kai ta mota ma Kake.!” Tai maganar cikin sakin huci.
Hilal ya d’ago yana duban mai maganar kasancewar idanunsa rufe suke cikin bak’in gilashi hakan yasa bata hangi k’wayar idanunsa ba.
“You again.?” Ya furta yana mai nunata.
Sai ya zame glasses d’in dake idanunsa Wanda hakan ya bawa Khulsum daman ganesa.
Da gaske wann d’an rainin hankalin take sake gani gabanta Wanda ya kirata da mai aiki a gidan da Umma ta Kai Ummul.
“Makaho ne kai.. Ko bakaga aika aikan da ka mun bane.?!”
Ya shiga binta da kallo sama da k’asa dan tsaf ya ganeta tun a kallon farko. Ita ce dai intruder d’in da ya kama a b’angarensa 2 days back.
“Kece zan tambaya ko makauniya ce ke.. Why do you keep on getting on my way.? Are you stalking me..?” Har lokacin idanunsa akanta.
Khulsum ta kuma tunzura. Ta soma takowa kusansa tana sakin huci kai kace rufesa da duka zatai. Hilal sai ya soma matsawa da baya. Khulsum ta nunasa da yatsa bata daina sakin huci ba “Kayi sa’a sauri nake banida lokacinka balle na fad’a.!”
Kafin ta rufe baki suka soma sinkayo wata murya tana rok’on ‘yansandan da suka tasata Gaba tana fad’in su mata rai wllhi ta tuba kar su tafi da ita. Tasi’u zasu nemo shine b’arawo shine ya gudu da kud’d’en.
Khulsum ta juyo da mamaki had’ida furta “Mama.!”
Aiko Mama tana Jin haka ta bud’e murya sosai tana fad’in “Khulsumu ki ceceni kar ‘yansandan nan su tafi dani.. Wllhi ba guduwa zanyi ba ba tashan mota zan tafi ba.. Wllhi banci dukiyar mahaifinku ba.. Ke shaida ce Khulsum ni ce nan ke kula da mahaifinku.. Kar ki bari a tafi dani babu mai kula da Abbanku bayan ni..!”
‘Yansandan suka tasa k’eyarta cikin mota suna fad’in ta shige suje station. Ta Adana duka bayananta tai masu a can..
Mama na kururwa tana duban Khulsum tana fad’in ta ceceta aka jefata cikin motar ‘yansanda.
Khulsum ta yunk’ura zata bi bayansu tana fad’in su dakata amma inaa Sun wuce. Ta nufi kwalta a guje tana yunk’urin tare abin hawa saidai babu Wanda yai yunk’urin tsaya mata.
Kaman daga sama taga motan d’an rainin hankalin nan yaja ya tsaya gabanta “Shiga muje.. shiga mubi bayansu kafin su b’ace mana..”
Tai tsaye tana dubansa kaman mai tunanin shiga. Hilal ya kuma danna mata horn alamun tai sauri ta shiga kar su rasa motar ‘yansandan.
Sauri sauri ta bud’e marfin motar ta shige tana fad’in subi bayansu. Nan da nan Hilal ya kwashi motar suka bi hanyar da motar ‘yansandan tabi.
**
A can gidansu Ummul kaw Sanda aka soma buga algaita ana shelan an d’aura auren Ummulkhairi sai jikin Umma ya d’auki rawa. Duniyar ta shiga juya mata. Gani take kaman ba gaskiya bane. Kaman d’aya ne daga cikin mafarkan da ta saba. Wai yau an d’aura auren Ummul d’inta.. Ummul tayi aure. Sai Umma ta yanki jiki ta fad’i hankulan mutane suka yo kan Umma.
SameenaAleeyou…📚*AUREN WATA UKU.!*
*19*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Ruwa aka kawo za’a yayyafa ma Umma Asshe ta dakatar dasu ta bud’e bakin jaka ta shiga lik’a ma Umma kud’i had’ida umartan matan da ke gefe da su rangad’a ma Umma gud’a cikin kunne.
Aiko firgit Umma ta mik’e tana tambayan da gaske ne an d’aura auren Ummul, Ummul d’inta dai. Sai kuma ta fashe da kuka tana fad’in bata tab’a tsammanin zataga wann rana nan kusa ba.
Masu lallashi nayi masu tausayi nayi masu murna nayi harma da masu takaici.
Toh komai akace d’an lokaci ne, shi kuma aure baka tab’a yinsa sai lokacin da Allah Yace. No matter how hard you try or how many relationships make. Zai faru ne kawai a lokacin da Allah ya nufa. Yau dai Allah ya k’addari za’a d’aura auren Ummulkhairi bayan tulin fad’i tashi da mahaifiyarta taitayi dan dai taga ‘yar tata tayi aure. Dukda irin kawo sadaki ana janyewa saka rana ana d’agawa harma da amshe lefe yau Allah ya nufa ya kuma k’addari za’a d’aura auren.
‘Ya’ya musamman mata tamkar k’wai suke hannun iyayensu. Babu Iyayen da zasu so wani abu na k’i bisa tsautsayi ko tilastawa ya fasa wann k’wai da suke rik’e dashi cikin kula da kaffa kaffa. Tabbas burin ko wata uwa koma iyaye in general shine da zaran ‘yarsu ta Kai gab’an aure su kaita d’akin mijinta cikin salama da aminci. Saidai wasu lokutan insecurity yakan rinjayi confidence da muke dashi akan yaranmu Wanda hakan ka iya zama babban threat a garemu. Tsoron zamansu a gabanmu babu aure, tsoron maganganun mutane da abinda ka iya zuwa yazo yakan sa mu mance wani b’angare mai mahimmanci Wanda yake tamkar foundation idan babu shi tamkar anyi gini bisa iska ne . Shine neman zab’in Allah da fawwala masa lamra. Idan tsoron ya rinjayi raunin har aka mance wann gab’a mai mahimmanci hakan ka iya jefa rayuwar yaran cikin had’arin da yafi zamansu gaban Iyayen. Wani auren death sentence ne iyaye suka jefa yaransu ciki ba tareda sunyi la’akari ba. Da yawa auren yayi ajalinsu. Wasu ma anyi tsafi dasu sabida ba’a nemi zab’in Allah ciki ba tun farko.
‘Ya’ya amana ne hannun iyaye sann sunada hakkoki Akan iyayensu kaman yanda iyaye keda hakkoki Akan nasu ‘ya’yan. Mu fara k’ok’arin sauk’e nauyi da hakkokin yaranmu Wanda shine tarbiya na farko da zamu basu ko dan nan gaba su sauk’e namu nauyin hakkin dake kansu. Bazai yuwu ka haifi d’a ka wofantar dashi ba kai tsammanin zai girma da tausayinka. Da yawan yaran da muke ji muke gani suna zama abin gudu cikin Al’umma mu bincika yaya tarbiyansu ya samo asali. Wasu tun suna yara iyayen sun d’ebe masu albarka da harsunansu. Wasu iyayen basu san cin yaran ba basu san karatunsu ba balle maganinsu Wanda duk nauyi ne da ya rataya kan iyaye. Ko a d’abi’ance Yaron da ya taso cikin kula da soyayya ba daidai yake da yaron da aka wofantar dashi ba. Akwai jarabawa. Idan kayi iya naka Allah ya jarabceka wann kuma jarabawa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 64