joy take maganan.
Shid’inma dauriya kawai yake amma ji yake kaman yayi kukan musamman da Mommy tace “Na kasa yarda rana irin wann zaizo Haidar… Zanga D’anka.. Ma sha Allah. TabarakAllah…! Alhamdulillah is all I can say..” Ta d’anyi still kafin taci gaba “What about Ummul..? How is she.. How is my daughter Haidar..?”
Sai sann Haidar Ya dan waiga ya dubi Ummul wacce ke kwance ta basa baya hawaye naci gaba da gangaro mata.
“She’s fine Mommy.. I mean.. She will be fine..”
Mommy tace “What do you mean she will be fine.. Ina take..? Can I talk to her.. please put her through.. I want hear her voice.. I want to know how she’s doing.?”
Haidar ya dan furzar da huci lokacin da jaririn Ya fara yan k’anan kuka. mommy ta sinkayo sautin yaron daga cikin waya. Annurinta ya ninku, yayinda k’walla ta kuma ciko idonta “Is that my grandson.. Is that his voice..?”
Haidar ma murmushin yake yana duban yaron “Yes Mommy.. It’s your grandson.. He wants to hear your voice I guess. I’m putting you on speaker.”
Yasa Mommy a speaker yana yana duban yaron yake fad’in “Guess who’s on the line Son.? It’s Grandma. Say hi to granny.!” Cikeda farin ciki yake maganan gwanin ban sha’awa.
Mommy tace “Hello my cutie.. Is that you..? Is that your tiny voice.? How’s my little love doing..? Oh c’mon don’t cry.. Is the little one hungry..?” Cikeda farin ciki da ya gaza b’uya take maganganun. Haidar sai murmushi yake yayinda Ummul ke saurarensu daga nan yanda take kwance har lokacin hawaye ke gangaro mata musamman da ta sinkayo muryar Mommy tana magana ma jaririn.
Mommy tace da Haidar Ya bata Ummul. Sai Haidar Ya d’an waigo kadan yana duban Ummul da ta basu baya. Kuka take maras sauti. Ya d’anyi gyaran murya yace “She’s.. still asleep Mommy..”
Mommy ta jinjina kai “Kyaleta tana buk’atan hutun.” Ta k’ara da “Haidar, nace ya batun aurenku.. Mecece makomar aurenku da Ummul.?” Jikinta duk a sanyaye Tai tambayar cikeda shakkun amsar da zata samu daga gare shi.
Lumshe idonsa yai kad’an had’ida furzar da huci daidai lokacin wata mata mai sanye da kayan nurses ta dan manyanta matar ta shigo. Ta dubi Haidar dake rik’eda jariri ta kuma dubi Ummul. Kallon na mamaki ko tuhuma take ma Haidar ganin bataga mutanen da suka taho da Ummul ba. Kafin tai magana Haidar yai saurin furta “I’m the father.” Sai ta saki murmushi matar tace “Ba shakka naga kama.. Congratulations to you.” Ya jinjina mata kai had’ida mata godiya kafin ya sumbaci yaron Ya mik’a mata. Ta amshi yaron tana nufan Ummul.
Ficewa waje Haidar yai yana amsa kiran Mommy. Mommy ta sake nanata masa tambayar da Tai masa.
Furzar da huci Ya kuma yi yana shafa kansa kad’an “All that I’m sure Mommy.. Shi ne I won’t give up my wife.. I’ll never give up Khairy.. I won’t give up my little family.. I will do everything I could to make sure ahalina bai tarwatse ba.” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “If Khairy is the architect of our love Mommy.. Then I’ll be the Engr.. If she’s the one that designed our love.. Then I’d make sure it is well built.. I will be the protector of that love.. I know it won’t be easy.. It will be difficult.. But then, I won’t give up.. Never..!”
Mommy ta goge hawayen da suka gangaro mata. Murmushi ne saman fuskarta amma can k’asan zuciyarta zallan tausayin D’an nata ne. Ta shiga jinjina kai tana fad’in “May Allah be with you Son… Ina rok’on Allah ya had’e maka ahalinka kaman yanda Ya had’e mun nawa.”
Haidar Ya amsa da Ameen Mommy. Yai mata godiya Tai masa fatan alkhairi da nufin washe gari idan Allah yakai rai jirgin sassafe zasu biyo itada mahaifinsa.
**
A can waje kuwa Sadis bai fasa bin bayan motan Hisham ba har saida ya cimmasa. A dole Hisham yai birki yai parking.
Hajja ta soma karanto salati tana waige waige ganin Mota ta sha gabansu ba shiri.
“Hisham meke faruwa.. Waye wann meyasa yake bibiyanmu.?”
Hisham da k’irjinsa bai daina bugawa ba girgiza kai yake yama kasa ficewa daga cikin motan. Fad’i yake cikin rawar murya “I.. Ya.. Yaron Ogana ne a wajen aiki.. Ogana da nake aiki k’ark’ashin Kampanin sa.. Engr Aliyu Maitama mahaifin Abokina Haidar.!”
Cikin wane irin shock Hajja ta d’ago tana duban Hisham fiyeda Wanda ta shiga lokacin da taga Haidar.
“A..Aliyu Maitama.. K’ark’ashin sa kake aiki..?!” Ta fad’i cikin birkicewa.
Hisham Ya jinjina kai “Eh Hajja k’ark’ashinsa nake aiki kuma na tabbata shi Ya turo a kamani a tunaninsu ni macuci ne kaman yanda Haidar yai zato.. Hajja abun is complicated amma na tabbata komai zai fito fili idan suka tabbatar banida laifi kuma ni taimakon Abokina kawai nake.”
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un shine abinda take nanatawa cikin zuciyarta. Bata sake fahimtar komai ba sai tsintar kanta da Tai a station dan tuni an kama Hisham anyi dashi ofishin yansanda.
Hisham Ya kamo hannayen Hajja cikin nasa daga nan yanda yake rufe cikin cell. Ya kwantar da murya sosai “Hajja I’m innocent.. Ban sace Ummul ba.. Ban kuma raba Haidar da Ummul ba.. Hasalima ban tab’a sanin Ummul abokina Haidar take aure ba har sai bayan da suka rabu.. Sann a wann lokacin na san ‘yaruwarsa Anisa tana neman rayuwar Ummul da abinda ke cikinta kaman yanda tayi ajalin rayuwar tsohuwar matar Haidar da abinda ke cikinta..!”
Hajja bata fahimtar komai sai hawaye dake gangaro mata tana duban D’an nata cikeda tausayawa. Ta ya fara aiki k’ark’ashin kampanin mahaifinsa ba tareda saninsa ba.? Ta ya D’anuwansa ya zama abokinsa ba tareda saninsa ba.? Ta ya D’anta ya fad’a gidan da taita k’ok’arin nisanta shi dashi ya fad’a cikinsa tsamo tsamo..? Ta ya duka wad’annan abubuwan suka faru. This a too much of a coincidence.
Muryar Hisham ta sinkayo yana fad’in “Hajja ki daina kuka.. Banida laifin komai Hajja ta.. Your son is innocent.. I’m sure Haidar would understand so as his father. Su d’in mutane ne masu nagarta.”
Hajja ta kuma lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. Silalewa Tai nan wajen tana kuka sosai. Kuka mai tab’a zuciya.
**
Washe gari jirgin safe su Mommy suka biyo zuwa Bauchi. Haidar kuwa asubahin fari Ya baro masaukinsa Ya nufo asibitin dan dama bai yarda ya bar asibitin ba saida ya samar ma Ummul da jaririnsu room nurse da zata kula dasu dan ko nawa zai kashe a kular masa dasu tinda shi dai bazai yuwu Ya kwana dasu ba.
Cikin tsananin damuwa mai tattareda tashin hankali Ummul ta kuma tambayar nurse din “Ina Hajja.. ina Hisham meyasa ban sake ganinsu ba tin jiya..? Ki fad’a mun.. Haidar ne yace ki rufe ni a nan Ki hanani fita..? Dan Allah Ki sanar Dani.. Ina Hajja da Hisham..?”
“Suna yanda Ya kamata ace nan suke.!” Haidar da shigowarsa kenan da kaya nik’i nik’i na jaririn da na mahaifiyar jaririn Ya fad’i haka.
Nurse din ta sauk’e ajiyan zuciya tana ma Haidar sannu da zuwa. K’ok’ari taketayi Ummul ta saka ruwan tea a cikinta ko jariri zai samu ruwan nono amma tak’i sai tambayarta take ina Hajja da Hisham.
Nurse din Suka gaisa kafin Haidar Ya shiga aje kayayyakin dake hannunsa matar tana sanar dashi Sun sha fama da ‘yar rigimarsa daren jiya dan cewa Tai saidai a barta ta fice. Ta dubi Ummul murmushi saman fuskarta ta kuma dubi kofin tea dake aje gefe sai ta dubi Haidar tace “Kuma tak’i ta saka komai cikinta balle wann babban mutum din ya samu isasshen abinci.” Ta mik’a mata mug din “Ya kamata ki shanye wann.. Mu a Likitance ruwan nono shine farkon rigakafi ko wane jariri ke buk’ata.”
Ummul ta galla mata harara. Dariya taso bama nurse din amma ta gimtse tace “Daure dai ki shanye wann.. Ni kinga ma tafiyata.” Ta mik’e tana ma Haidar Sallama.
Bayan ficewarta Haidar ya maidoda da dubansa ga Ummul wacce ta nannad’e jikinta cikin mayafi. Ya dan furzar da huci kad’an kafin yace “Kiyi hak’uri ki sha.. Take one more sip.. Please.!”
Kauda fuskarta gefe ba tareda ta dubi yanda yake ba. Ga jaririn tuni ya soma mutsu mutsu yana cilla k’afafu sai tsotsan hannunsa yake alamun yunwa.
Haidar ya kuma furzar da huci yana shafe fuskarsa “Look Khairy.! Idan baki sha ba zan tako har wajen na baki da kaina kuma kinsan zan aikata..!”
Ta dube shi a dak’ile “Ni kuma sai na tsaya wani k’ato ya bani abinci a baki.. Allah ya sawak’e mun. Idan ka mance ne dai na sake tuna maka.. Ni Ummulkhair ba matarka bace. AUREN WATA UKU mukayi kuma ya k’are.!”
Haidar ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa had’ida furzar da huci. Yasan dole zai sha fama ba kad’an ba. Yakai dubansa ga yaron da tuni ya b’ige da kukan yunwa ga Ummul ta had’e rai sosai ta kauda fuska gefe. Dik yanda take son ta d’auki D’anta ta basa abincinsa ta lallashesa yai shiru ta kasa sabida tsananin k’iyayyar mahaifinsa dake kuma tunzurata. Sosai kukan jaririn ke mata zafi amma ta kasa koda motsawa sabida Haidar dake wajen.
K’arasowa yai ya d’auki yaron ya shiga jijjigasa yana lallashinsa. Sai ya saka ma yaron lip d’insa na k’asa aiko tuni ya capke ya soma tsotsa kaman ya samu abinci. Ummul ta saci kallonsu yanda Haidar ya saka bakinsa ma yaron sai jijjigasa yake. Hawaye suka gangaro mata.
Daidai nan sukaji Sallama a k’ofa. Haidar ya bada izinin shigowa.
Wa zata gani.? Mama Tani ce da ‘yanuwanta guda biyu Azeema da Badia. Suka tafi a guje suka rungume Ummul suna kuka. Yayinda Haidar ke gaisawa da Mama Tani ya mik’a mata jaririn yana musu sannu da hanya. Dan dama Tun a daren jiya ya tura Sadis ya tafi Kano d’aukosu. Asuba Sun kamo hanya shisa sukayi isowan safiya.
Haidar ya fice wajen Sadis ya basu waje.
Sosai Ummul ke kuka tana tambayan sauran ahalinta. Ta dubi Azeema tace “Ina Khulsum..? Maiyasa bata biyoku ba..? Itama tana fushi dani ko.? Umma da Abba duk fushi suke dani ko.?” Hawaye suka ci gaba da gangaro mata tana girgiza kai take fad’in “Bazan iya dubansu cikin ido ba.” Cikin tsananin rawar murya take maganar.
Azeema ta murmusa tana share ma Ummul d’in hawayen da suka gangaro mata “Dukanmu muna fushi dake ‘yaruwa.. Shin wak’e gudun danginsa a lokaci mai mahimmanci irin wann…? Amma Kar ki damu zamu iya yafe Miki ko dan zuwan Sabon D’anmu.!” Ta k’arada “Kinga d’ago ki gani.. D’ago kiga da wa muke tare.” Ta k’arashe da murmushi saman fuskarta.
D’agowar da Ummul zatai sukai ido hud’u da Khulsum. Rabon su da su saka juna a ido Tun lokacin Auren Ummul d’in a gidan Hajiya Asshe ranan da mahaifiyarsu tai ma ‘yanuwan Farrak’u a k’ok’arinta na ganin Auren Ummul Ya tabbata.
Hawaye suka ci gaba da kwaranya musu.. Khulsum tana k’arasowa gaban Ummul kukan Ummul d’in Ya k’aru sosai. Murya na rawa Khulsum ta furta “Adda Ummul..!” Sai sukai bursting cikin kuka sosai su duka biyun. Suka rungume juna suna yin mai isansu. Har saida Mama Tani tace zasu tasa mata sabon maigida da kukan da suke dan tuni bacci ya d’auke jaririn cikin hannunta.
Ana haka su Mommy harma da Daddy sukai sallama tareda jagorancin Haidar.
Gaishe gaishe aka soma kan Ummul na kife k’asa tin shigowar Mommy da Daddy. Mama Tani ta mik’a ma Mommy yaron tana fad’in ta rigata ganin angon nasu. Sukaita ‘yar bankwanci a tsakani Mommy tana fad’in ma sha Allah ta sumbaci goshin yaron. Sak Haidar dinta sanda yake jariri. Su Azeema kaw ficewa sukai bayan Sun gaisar da iyayen Haidar.
Mommy ta mik’a ma Daddy dake zaune saman farar kujera yaron. Ya amsa yaron kyakkyawan murmushi bisa fuskar Daddy. Haidar yana gani Daddy na ma yaron addu’a ya tofa masa. Ya mik’a ma Mommy yaron bayan ya jero ma jaririn da mahaifyarsa add’u’o’i. Har kawo wann lokacin Ummul bata iya d’ago fuskarta ba.
Daddy ya dubi Haidar yace suje daga waje. Ba musu Haidar yabi bayan mahaifinsa.
Bayan ficewar su Mama Tani ma ta zame jiki ta fice tana ce da Mommy bari ta barta ta gana da sabon Angonta dan gashi da alama har ya kori Daddy.
Mommy ta murmusa tana jinjina barkwancin Mama Tani.
Mik’ewa Mommy tai rungume da yaron cikin hannunta ta dawo kusan Ummul wacce tinda Mommy ta nufota k’irjinta ya tsananta bugu. Ta kasa koda motsawa balle ta dubi Mommy tin bayan gaisuwa Wanda shima da kyar ta iya. Ta sani tana fara magana kuka ne zai biyo baya.
Mommy ta kwantar da jaririn cikin baby crib d’insa dake gefe. Ta kuma matsowa sosai kusan Ummul. Sai Mommy ta d’aura hannayenta saman na Ummul. Ummul na ganin hannun Mommy saman nata hawaye suka shiga gangaro mata.
Mommy ma kuka ne taji na zuwa mata. Sai kawai ta rungumo Ummul cikin jikinta tana fad’in “Taho nan ‘Yata..!” Mommy ta rungumeta sosai cikin jikinta yayinda Kukan Ummul ya k’aru, Mommy na ci gaba da lallashinta.
**
A can waje kuwa taryan taryan Haidar ya karanto ma Daddy komai gameda Abokinsa Hisham da irin cin amanar da yai masa bayan ya aminta dashi. Sann ya sanar da Daddy baida haufin duk wani scandals da failures da Kampaninsu ta fuskanta da saka hannunsa ciki. Daddy yaita jinjina lamarin domin kuwa zai iya cewa bai tab’a tsayawa ya tantance kamannin matashin ba cikin employees d’insa dukda kuwa cewa suna tareda Haidar kusan ko Yaushe a company. Ya dubi Haidar yace ai sai su wuce police station din snn ya kuma ce da Haidar d’in ya kirawo company lawyer d’insu cikin gaggawa. Dole Hisham nada Ubannin gidan da suka turosa kampaninsu domin Ya musu zagon k’asa.
Tuni Sadis ya jasu suka nufi station yanda Hisham ke gark’ame.
*
Hajja na gaban Kanta tana magiya ma ‘yansanda da su saki D’anta dan bata fata Aliyu Maitama ya tadda su a station d’in. Alk’awari tai ma kanta bazata tab’a jingina ma D’anta sunan Aliyu Maitama ba koda kuwa shine abu na k’arshe da zatai a rayuwarta. Ba yanda batai su bata belin Hisham ba amma sunk’i sunce sai Wanda yai filing complaint akansa yazo idan D’anta nada lawyer yana iya kiransa.
Hajja ta kuma marairaice fuska “Rankaidade ka dubi girman Allah ka min alfarmar nan.. Ka dubi soyayyar dake tsakanin D’a da mahaifiya ka bani belin D’ana.. Ko nawa zan kokarta na biya in sha Allah.”
Shi kaw Hisham addu’a yake daga nan cikin cell yanda yake gark’ame kar a bada belinsa har sai mahaifinsa Aliyu Maitama yazo station d’in. Aiko kaman daga sama ya hango Haidar da Sadis ga Daddy na biye dasu. Hisham ya saki murmushi da gefen bakinsa. Cikin zuciyarsa yake furta ‘Bingo.! Daga k’arshe dai, korarren D’an zai had’e da mahaifinsa. Bari dai mu gani Aliyu Maitama.. Ya zakai da wann D’an naka da ka sheganta… The Son you never noticed dikda jimawansa yana aiki k’ark’ashinka.!’
A haka suka k’araso cikin station d’in waya manne kunnen Daddy dake magana da company lawyer dinsu.
Cak Hajja ta had’iyi kalamanta. Tai mutuwar tsaye nan wajen. Ta ina zata mance wann murya dukda muryar ta manyanta a halin yanzu.. Ta tuno muryar a lokacin da ya jajanta mata rashin mahaifinta kuma leburansa a Kampaninsa. Ta tuno muryar a lokacin da yai alk’awarin Aurenta bayan rashin mahaifinta. Ta kuma tuno muryar a lokacin da ya furta mata kalman saki ya kuma sheganta jaririn cikinta. Ta tuna sanda ya turata kurkuku har ta haife D’anta a gidan yari. Yau gashi nan zai kuma tura D’an da yai sanadin haihuwarsa a gidan kasu zuwa gidan kasu. Ta lumshe idanunta tana jin zuciyarta na bugawa cikin sauri.
Cak Daddy ya ja ya tsaya, ya dakata da wayan da yake a daidai sanda ya shigo cikin ofishin yana jin bugun zuciyarsa na k’aruwa ba tareda yasan dalili ba.
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*55*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Officer yana hango su Haidar yace “Yauwa Hajiya.. Ki adana duk wann magiya da kike. Gasu nan sun iso su yafi cancanta ki roka ba mu ba.” Ya k’arada barkanku da isowa.”
Zuciyar Hajja yaci gaba da harbawa daga nan yanda take tsaye gaban kanta.
A hankali Daddy ke takowa kusan matar yana jin bugun zuciyarsa na k’aruwa. A b’angaren Hajja ma hakan ce ta kasance. Ta kasa koda motsawa balle ta waigo. Addu’a kawai take cikin zuciyarta Allah Ya kawo mata da sauk’i. Ji take tamkar numfashinta zai bar gangan cikinta haka nan k’afafunta tamkar bazasu iya d’aukanta ba. Tana jin officer yana fad’in “Ga mahaifyarsa nan tun safe take mana magiya a nan.. Tak’i barinmu mu huta.. Cewa take lallai lallai sai mun bata belin D’anta.”
Haidar ne ya katse D’ansandan da fad’in “Idan D’anki nada lauya kuna iya gabatar dashi k’arshen gata da zaki masa kenan. Dan sai nayi sharia da D’anki with every means and resources da nake dashi.!” Ya k’arashe yana aika ma Hisham dake tsare cikin cell mugun kallo kaman zai shak’o sa.
Har lokacin jikin Daddy a matuk’ar sanyaye yake dan matar tak’i juyowa ta dubesu Har wann lokacin. Sai Ya d’anyi gyaran murya yace “Sannu Baiwar Allah.!”
Zuciyarta taci gaba da harbawa tana sanar da ita ‘Bakida sauran zab’i da Ya wuce ki fuskanci baya Fannah. Komai yazo k’arshe.. Yau dai gaki ga Aliyu Maitama.. Ki juya ki fuskance shi.. Dole ki juya koda zaki tuna masa bayansa da ya k’yamata. Just turn and face the reality.!’ Lumshe idanunta Tai hawaye suka gangaro mata kafin ta soma k’ok’arin waigowa cikin wane irin yanayi.
Daddy ya daskare nan wajen. Ya kasa gaskgata abinda yake gani. It’s her.. It’s really her… Ta ya zai mance kamanninta bayan ya shafe tsawon shekaru yana nemanta.? Ta Ya zai mance wann fuskar nata koda ace sanin k’uruciya yai mata. Fannah..! Fannah ce.. Fannah matarsa da ya d’aukar ma Marigayin mahaifinta alk’awarin rik’eta bisa amana. Fannah da Ya datse igiyan Aurensu da jaririn cikinsa cikin jikinta. Cikin da Ya fidda shi daga cikin ahalinsa tun kafin ya shak’i iskan duniya. Fannah da Ya tura fursuna da jaririn cikinsa. Cikin tsananin rawar murya Daddy ya furta “Fann.. Fannah..!”
Sai tai bursting cikin kuka ba tareda ta iya furta komai ba.
Haidar ya dubi Daddy cikin tsananin shock sai ya kuma dubi matar. Ya sake duban Daddy da mamaki “Fannah kuma..?! Daddy… Fannah naji kace..?!” Ya kuma girgiza kai kad’an cikin rashin fahimta ko rashin aminta “Fannah.. Your exwife.. Matar da.. Matar da Mommy ta jima tana nema..? Daddy ita ce wann..?!” Ya k’arashe yana nuna Hajja cikin tsananin shock.
Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta. Har lokacin cikin tsananin shock shima yake “Eh Haidar..! Ita ce.. Ita ce Fannah.. Matata..! Matata da muka rabu tsawon shekaru na kuma nemeta ban sameta ba.!”
Daga nan cikin cell Hisham ke girgiza kai fuskarsa na nuni da tsananin mamaki yake furta “Hajja.. Hajja meye nake ji haka..? Meye suke cewa haka..?!” Ya dubi Haidar Har lokacin da mamaki samar fuskarsa tamkar gaske “Meye nake ji haka..? Ta Ya mahaifiyata ta zama matar mahaifinka..?!”
Sai sann Daddy yakai dubansa ga Hisham zuciyarsa na tsananta bugu. Bai san sanda ta soma takawa ya isa har gaban k’arafunan cell da Hisham ke rufe ciki. Daddy ya k’ura masa ido without saying a word. Su duka biyu shida Hisham kallon juna suke cikin ido.. A hankali Daddy ke bin Hisham da kallo k’walla tab idanunsa tin daga fuskarsa har izuwa k’afafunsa yanda yaga k’afafun Hisham d’in Sun jeru da nasa k’afafun suna kallon juna. Sai Daddy ya k’ura ma yatsun k’afafunsu kallo. Babu abinda ya raba k’irar halittar k’afafunsa da na matashin. K’wallan dake kwance cikin idanun Daddy suka d’igo suka sauk’a saman k’afan Hisham. Sai Daddy ya juyo yana duban Hajja dake kuka sosai shid’in ma hawaye ke gangaro masa. Yana dubanta yake nuni da Hisham yatsarsa Har rawa take “Is.. Is he my son..? Shi ne D’ana.. da kika tafi yana ciki..!”
Sai Hajja ta kuma fashewa da kuka ba tareda tace komai ba.
Cikin wane irin yanayi Hisham ke girgiza kai yana duban Hajja. Ya tamke k’arafan cell sosai yana kuma girgiza kai mai cikeda nuna rashin amincewa “Hajjah.. Mai nake ji haka..! Mai haka yake nufi..? Mai Mahaifin Haidar yake cewa..? Hajja mahaifin Haidar .. Shine mahaifina..?
Har lokacin ta kasa cewa komai sai kuka yayinda Daddy yaci gaba da duban Hisham hawaye naci gaba da gangaro masa.
Haidar da yai mutuwar tsaye yana duban abin al’ajabi cikin wane irin yanayi yake girgiza kai “No.. No.. No way.. This can’t be.. No this can’t be happening..?”
Hawaye suka ci gaba da gangaro ma Hisham. Cikin wane irin yanayi yake furta “Hajja please answer me.. Is he my father..? Da gaske shine mahaifina..? Hajja shekara da shekaru ina tambayarki ina mahaifina..? Ina danginsa.. Ce min kike ya mutu all these years.. Ce min kike baida kowa baida dangi.. Hajjah.. Ta Ya mahaifin Abokina Ya zama mahaifina..? Hajja ki sanar Dani dan Allah.. Hajja zuciyata tana nauyi.. Dan Allah Ki sanar Dani bazan iya d’auka ba.!”
Hawaye ne ke ci gaba da gangaro ma Daddy yai saurin shigar da hannunsa cikin k’arafan cell d’in Ya tallafi fuskar Hisham dake kuka sosai. Cikin rawar murya Daddy ke furta “My son.. My son.. You really are my son.. I’m your father.. Your father is alive.. He’s very much alive.. Mahaifinka na raye D’anah.!”
Sai Hisham yai bursting cikin kuka yayinda Haidar yaci gaba da dubansu cikin tsananin shock.
‘Yansandan ma duk mamaki da al’ajabi ne Ya cikasu. Kowa a wajen mamaki yake. Sai babba cikin ‘yansandan ya fito yana gyara d’amararsa yace “Inaga an sami rashin fahimta a nan..! Da alama rikicin na cikin gida ne.. Inaga bai kamata mu bar wann k’araffan su zama shamak’i tsakanin D’a da mahaifi da suka shafe shekaru basu tare.” Ya k’arashe yana mai bud’e cell.
Kaman jira Daddy yake sai Ya shige Har cikin cell d’in Ya rungume Hisham sosai cikin jikinsa.
Girgiza kai kurum Haidar yake yana duban Daddy da Hisham yana jin tamkar dai duniyar na juya masa. Ya kasa yarda da abinda idonsa ke gani.. Ta Ya mutumin da yaci amanarsa zai zama D’an mahaifinsa.. Ta Ya zai soma kiran wann bak’in k’umurcin D’anuwa. Just what is this.? Meye yake faruwa haka.? Bazai iya jure tsayuwa nan wajen ba. Bai san sanda Ya fice daga wajen cikin wane irin yanayi ba.
**
A can asibiti kuwa an rasa gwani wajen tarairayar sabon jariri da mahaifiyarsa tsakanin Mommy da Mama Tani. Dr ne Ya shigo ya duba jariri da mahaifiyarsa nan yake sanar dasu a ranar zaayi Sallama. Mommy ta kuma daukan jaririn ta mak’ale shi cikin hannunta tana fad’in zasu fice lambun dake bayan d’akin Ya samu vitamin d’in dake cikin hasken ranar hantsi a cewarta.
A wasa Mama Tani ke fad’in su dai basu saba da jegon turawa ba. Jariri a d’aki yake har yai kwanaki bakwai.
Mommy ta murmusa tace gwara dai su fice taji dumin mai gidanta koda na dan lokaci ne tinda gashi har zaayi Sallama.
Sai jikin Mama Tani Ya d’anyi sanyi Har taji ba dadi dan ta kula sosai yaron ya shiga ran Kakar tasa gashi Haidar da Ummu basu tare balle ta Sami kusanci da yaron. Sauken ajiyan Zuciya Mama Tani tai tana addu’an samun maslaha a al’amarin ma’auratan cikin zuciyarta. Musamman idan ta tuno wani rikicin da suka baro gida wato Abba. Ta maido da dubanta ga Ummul bayan Mommy ta fice tace “Yauwa Ke Ummu, nace ba.. Kinga dai a halin yanzu ke uwa ce.. Abinda aka sani ga uwa kuma shine sadaukarwa.. Ummul inaga tinda Allah yasa kin haihu lafiya sann yanzu rabo Ya tsaga tsakaninki da yaron nan Aliyu.. Bakiga yanda Ya shiga damuwa da tashin hankali ba sanda baki nan, yaro mai k’aunarki ga dattaku da sanin yakamata ba irinsu mijin Badia Tasi’u barawo da mijin Azeema Habibu gantalalle. Ni inaga zaifi kyau a maida aurenku tinda ga rabo a tsakani.. Yaro Ya girma tsakanin iyayensa biyu yafi.. rabuwar sai dole. Idan Har ke d’in kika sauko daga dokin fushi kika amince a maida auren Abbanku mai sauki ne..” Bata Kai aya ba ta soma sinkayo kukan Ummul.
Taci gaba da girgiza kai “Ni dai a’a dan Allah Mama. Wllhi bani son komawa gidan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 52 Chapter of 64