nai watsi dasu daga farko.” Ta kuma murmusawa kafin tace “Tinda inada ke Ammi, I know I’m not fighting a losing battle.”
Suka sakar ma juna murmushi a tare kafin Anisa tasa kai ta fice zuciyarta na mata sanyi. Zatai whatsoever it takes dan ta tabbata yarinyar nan ta fita daga rayuwar Haidar duk tsananin son da Mommy ke mata kuwa. Ta kuma rausayar da ido kafin ta shige.
Asshe ta janyo ma Inne Dije k’ofa kafin ta fito daga b’angaren bak’in ta nufi wajen ‘yaruwarta daketa faman neman layin Haidar bata samu.
Zama tai gefenta ganin damuwa ya nuna k’arara saman fuskar Mommy.
“Aunty Kwaise, ya na ganki haka. Allah sa dai lafiya.?”
Mommy ta furzar da huci kad’an “Na gaza samun layin Haidar Har yanzu. Ga amaryarsa ta iso.”
Asshe ta jinina kai kad’an “Relax Aunty Kwaise. Ki kwantar da hankalinki.. Yarinyar nan tana nan a gidan nan har tsawon watanni uku. Ki basa space kar ki tak’ura masa da batun a yanzu. Tinda an samu Ya amince kuma yarjejeniya akai dashi so I believe zai zo Har nan kan k’afafunsa.”
Mommy da har lokacin ta gaza samun sukuni girgiza kai take “What if ya janye fah Asshe.? What if wancan makirar ta kuma jifansa da wani mugun asirin fah..? Asshe what if Malaminta yafi namu..? Asshe I’m scared.. Tsoro nake kar duk efforts d’ina su tafi a banza.”
Asshe ta kamo hannun Mommy ta zaunarta saman gado “A’a Aunty Kwaise ke uwa ce. Da izinin Allah k’ok’arin ki bazai tafi a banza ba. Haidar zai dawo gareki. D’anki zai dawo gareki. Munyi komai kaman yanda Malam yace. Inada yak’inin hak’armu zata cimma ruwa. Just relax, ki zama calm kuma ki tunk’ari Haidar a tsanake. Yanda kike ta rawar k’afa akan yarinyar zai k’ara tunzura Haidar ne. Kinsan halinsa hasalima kinfi kowa sani tinda ke kika haifesa. Ki bashi gobe zuwa jibi koma satin nan. A hankali sai ki tunk’aresa da batun.”
Mommy ta girgiza kai “Sati Asshe..? Toh me zaman me yarinyar zatai a gidan nan idan Har babu wanda tazo domin shi.. Asshe no sati yayi yawa. Kema uwa ce ya kamata kifi kowa fahimtar mai nake ji.”
Asshe ta jinjina kai “Na fahimceki Aunty Kwaise. Shiyasa nake k’ok’arin fahimtar dake abinda na hango.”
Mommy ta jinjina kai a hankali tana duban Asshe wacce gaba d’aya batada wani kuzari “Asshe.” Ta kirawo sunanta in a serious tune.
Zuciyar Asshe Ya tsinke. Kai da ganinta kaga maras gaskiya.
Mommy taci gaba “Akwai abinda ya kamata na sani ne..? Ina nufin, tinda kuka kawo yarinyar nan kin canza. Kaman akwai abinda ke damunki ba kaman lokacin da muka soma shirya auren nan ba. Tell me, is there something I should know.?”
Asshe tai Shiru zuciyarta naci gaba da yankewa sai tanajin tamkar ‘yaruwar tata ta riga ta fahimci komai abinka da maras gaskiya.
“Asshe.!” Mommy ta kuma ambato sunanta su duka biyun suna duban juna.
Sai Asshe ta fashe da kuka tana girgiza kai.
Hakan yai mugun tada hankalin Mommy. Bata San sanda ta mik’e ta k’araso wajen ‘Yaruwar tata ba. Ta dafata tana tambayarta meke faruwa.
Asshe na hawaye take bama Mommy hak’uri tana girgiza kai.
Cikin rashin Hajiya Kwaise ke girgiza kai “Asshe meyasa kike kuka irin haka. Kuma meyasa kike bani hak’uri.. Wani laifi ne kika min..?”
Cikin zuban hawaye Asshe taci gaba “Na miki laifi mai girma Aunty Kwaise..”
Mommy ta girgiza kai “Laifi.. Wane irin laifi..?”
Anisa da isowarta jikin k’ofan kenan nan tai tsaye ta kasa kunne tana sauraron wani laifi ne mahaifiyarta ta aikata ma Mommy. Cikin zuciyarta Addu’a take Allah yasa taji amsoshin duk tambayoyin da takewa mahaifiyarta gameda wann murd’add’en aure da sukai ma Haidar.
Muryar Amminta ta sinkayo tana fad’in “An sace komai Aunty Kwaise. Kayan lefe na gani na fad’a da kika sa akai ma yarinyar. A lokacin da kayan ya dawo gidana bayan an kai gidansu yarinyar.. A lokacin b’arayi suka biyo dare suka kwashe komai.. Maganar millions of Naira ake.. Shiyasa kikaga dik jikina yayi sanyi ko zarafin fad’a ma yarinyar ma ban samu ba balle danginta.”
Shiru Mommy tai tana dubanta. Sai ta jinjina kai a hankali “Kan haka kika tada hankalinki.. Idan dan wann ne Babu wani matsala tinda kwalliya ta biya kud’in sabulu yarinyar ta riga ta shigo hannunmu. Akan auren nan har property na na d’aga na sayar a garin nan.. Kwabon Aliyu Maitama baiyi ciwon kai cikin yak’in neman auren nan ba. So ko nawa zan kashe akan yarinyar nan bazan Ji ciwo ba Asshe because it worth it. Gobe idan Allah Ya kaimu sai ita yarinyar su fita da Anisa ta tayata da shopping kafin mu shawo kan shi gogan. Kinga fitan nasu da Anisa ma zai d’an sa ta kuma sakin jiki sann Anisa ta koya mata wasu abubuwan yanda zamu samun daman shawo kan Haidar Ya amince ya zauna da yarinyar matsayin mata a sauk’ak’e.
Jin haka yasa Anisa sakin tsaki tana juya idanu cikeda takaici tasa kai ta shige dan batai tsammanin abinda za’a ce ba kenan. Ji yanda Mommy keta rawar k’afa kan wann yarinyar. Ita taji ta tafi taje ta k’are mata kallo taga me take dashi haka da Har Mommy ta kasa hangowa tattareda ita.
A b’angaren Asshe kuwa sauk’e ajiyan zuciya Tai dan dama kaya hayansu ta karb’o ta coge kud’ad’e. Dan a wann auren Ummul da Haidar da ta had’a ba k’aramin jari taja ba tinda a halin yanzu mijinta baya yayinta amaryarsa yarinyar Sa’ar Anisa ke cinye kud’in harta da yawon k’asashen waje ya daina yi da ita da amaryarsa yake. Abin sosai yake mata ciwo musamman idan ta tuna yanda tayi nata zamanin kafin ya auro yarinyar. Da alama bokan yarinyar da iyayenta yafi nata aiki ne inji Asshe. Hakan yasa ta buga business d’inta da auren d’an ‘yar Uwar nata. Dan haka koda wasa bazata tab’a bari Kwaise tasan gaskiyan al’amari ba.
Sanda Anisa ta tafi sashen Haidar sai cika take tana batsewa ita kad’ai. Ji take tamkar cin fuska ake mata da matar Haidar. Ta ya ma za’a kawo wata kucakaa ajiye gidan da sunan matar Haidar. Gidan da ita da kanta ta shirya komai to her taste wanda takeda tabbacin Haidar d’inta zaiso. Bata hango Haidar tareda wata cikin gidan ba. Gida ne data shirya masu su biyu take kuma hangosu da kalolin soyayyar da zasu sha a cikin gidan harma da yaran da zasu haifa. Ta kuma rausayar da ido tana furzar da huci kad’an kafin ta nufi sama.
Ga mamakin Anisa zaune ta tadda Ummul a parlor har lokacin kanta rufe cikin mayafi. Ta saki baki tana kallon ikon Allah kafin ta girgiza kai had’ida juya ido “Seriously.! Da gaske kina nan kina k’unk’ume a wajen. Kina jiran miji yazo ya bud’e fuskarki.. Lallai kuwa zaki jima kina rufe kaman kwab’in cincin dan ba mijin da zai bud’e wann fuskar naki.!” Ta k’arashe tana fincike rufin fuskan Ummul.
Damm! Haka k’irjin Ummul ya buga sanda taji mai maganar ta finciki mayafin da Mommy ta rufa mata bayan sun kawota sashen.
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*24*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Zuciyarta yaci gaba da tsinkewa. Ta sani bata tsammaci farin ciki cikin Auren ba. Kaman yanda bata tab’a mafarkin akwai wani rayuwa mai dad’i gaba gareta ba. Saidai tafi zaton tashin hankalin daga wajen mijin. Tinda mutum ne da ko saninsa batai ba. Sann shima bata tunanin ya santa.
Ta d’ago a sanyaye tana duban Anisa dake ci gaba da aika mata mugun kallo.
Anisa bata daina sakin huci ba ta finciko Ummul ta tadata tsaye “Tashi makira. Sai wani sanne fuska kike tinda kikazo. Irinku kunfi kowa iya makirci.” Ta shiga zagaye Ummulkhairi dake tsaye tana k’are mata kallo. Sai ta tab’e baki dan ido ba mudu ba yasan kima. Dukda nad’e take cikin lafaya tasan ko kusa bazasu zo d’aya ba. Hasalima Anisar bazata nuna mata komai ba face farin fata.
Anisa ta rausayar da ido cikeda takaici. Tai tsaye gaban Ummul wacce Har lokacin ko motsawa batai ba “Kar kiyi tunanin zaki tadda farin ciki a wann gidan dan kinyi nasaran saye zuciyar Mommy. Bariki ji na fad’a Miki wani abu. Mommy mace ce da take tamkar Hawainiya.. Babu wuya ta canza launi. And Haidar.?” Ta kuma sakin murmushi tana ci gaba da zagaye Ummul “Hello, I’m sorry to say sai kin gwammaci mutuwa da auren wann miskilin. Bansan dalilinki na amince ma aurensa ba amma ina mai tabbatar Miki Kinyi babban ganganci. You’ve made a grave mistake, because Haidar Maitama would never ever fall for someone like you.!” Ta k’arashe muguwar murmushi saman fuskarta ga wani wulak’antaccen kallo da take bin Ummul d’in dashi.
Saida ta gama juye ma Ummulkhairi buhu buhun wulak’anci kafin tasa kai zata fice.
Ummul ta sakar mata murmushi tace cikin sanyin muryarta “Baki sanar Dani sunanki ba.”
Anisa ta kalleta a dak’ile “Mai sanin sunana zai miki.?”
Ummul ta kuma murmusawa “Sanin suna nada mahimmanci ko dan hakkin zamantakewa. Allah yasa hakan ba matsala bane.”
Anisa ta tsareta da ido tana kallon salon makirci daga wajen wann bagidajiyar. sai kuma ta girgiza kai tana rolling eyes “I don’t have your time.”
Har tasa kai zata fice ta sinkayo muryar Ummul “Ina tunanin tinda har kika tako yanda nake kinada lokaci na.” Tai maganar murmushi saman pale face d’inta da taci kuka.
Anisa ta kuma dubanta da mamaki. Wanda mamakin Ya hanata magana. Bata tsammaci maganganu irin wad’ann daga bakin bagidajiyar Amaryar Haidar ba.
Ganin tayi sakare yasa Ummul kuma murmusawa ta k’araso kusanta “Ni sunana Ummulkhairi.. Watak’ila nasan kin sani Shiyasa baki tambaya ba.” Har lokacin sassanyar murmushi ne saman fuskarta Wanda ba k’aramin tunzura Anisa ya kuma yi ba.
Ganin Anisa tayi Shiru yasa Ummul katse shirun da fad’in “Yauwa gwara da Allah yasa kika shigo.. Dan Allah ina ne band’aki wllhi tun d’azu nake so na tashi nayi sallan isha amma bansan ta ina zan shiga ba.”
Hararta Anisa tai daga sama zuwa k’asa “Ina Miki kashedi, kar ki kuskura ki shiga d’akin cen. Dan wann d’akin d’akin Haidar ne.” Ta k’arashe tana nuni da d’akin.
Ummul ta murmusa kad’an “Ok haka na nufin wancan kenan zan shiga.” Tai nuni da d’aya k’ofar.
Takaici ya kuma cika Anisa ganin da gaske Ummul bata d’auketa da zafi ba. Taja tsaki tana juya ido kafin tasa kai zata fice.
Ummul Tai saurin dakatar da ita “Kinga.” Anisa ta juyo tana dubanta a dak’ile.
“Na gode.” Tai maganar har lokacin kyakkyawan murmushin ne saman fuskarta wanda ko shakka babu k’ok’arin b’oye tashin hankalin dake saman sa take.
Wani tsakin Anisa ta kumayi kafin tasa kai ta fice a fusace.
Sauk’e ajiyan zuciya Ummul tai tana mai hamdala cikin zuciyarta. Dan da dai tai tozali da mijin da aka aura mata, gwara taita karo da wann figaggiyar. Dan idan fad’a da tashin hankali ne zata iya cewa cikinsa ta girma. Amma miji bata san mai zata tarar ba. Bata san wani irin k’alubale zata fuskanta tare da shi ba. Haka zalik’a zuciyarta Sam ya gaza natsuwa dukda kwantar mata da hankali da mahaifiyarsa tai. Ta kuma sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin tasa kai ta nufi d’aya d’akin hagu da wanda Anisa tai nuni dashi matsayin na Haidar.
Kaman mai tsoron shiga haka ta tura k’ofar. Zuciyarta bai daina tsinkewa ba. Sai addu’an neman samun salama had’ida natsuwa take cikin zuciyarta take. D’aki ne mai matuk’ar kyau da tsari komai na ciki sabo ne dal da alama. Tai tsaye sororo tana duban d’akin dan ita dai bata San ta ina zata fara ba. Abinda ta soma tunowa shine gadon baccinsu ita da ‘yaruwarta Khulsum. Shikenan Sun rabu. Ta rabu da kowa nata kenan kaman yanda Umma ta umarceta. Shikenan ba ita ba danginta. Wani hali Abba yake ciki.? Yaya yanayin k’arfin jikinsa.? Umma ta mata iyaka dasu gaba d’aya tace ko a waya kar ta nemesu idan har ita ta haifeta. Sai taji k’afafunta Sun gaza d’aukarta. Nan ta silale wajen kuka na zuwa mata gadan gadan.
**
Kano…
Har ta kwanta wajajen misalin k’arfe shad’aya na dare taji ana buga mata k’ofa. Ta mik’e da kyar tana mamakin waye haka cikin daren nan. Bata kawo kowa ba sai Khulsum tinda ita ce tazo mata cikin dare irin haka a kwanan baya.
Ta k’araso tana tambayar wanene lokaci guda tana ci gaba da fad’in Khulsum kece nan wajen.
Ga tsananin mamakinta muryar D’anta Hisham taji. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa.
“Hisham.!” Ta furta a hankali
Hisham yace “Hajja ni ne.”
Ta bud’e k’ofan tana dubansa da mamaki “Lafiya kai kuma cikin daren nan.. Watau bazaka daina irin wann tafiyar naka ba ko.”
Murmushi Hisham keyi yana duban mahaifiyar tasa “Haba Hajjata tarban da za’a min kenan. Hajja ko shigowa gidan banyi ba fah balle na sha ruwa balle mujega gaisuwa.”
K’wafa tai tana dubansa kafin tasa kai ta shige tana ci gaba da sababin yanda ya maida tafiyan dare d’abi’arsa.
Hisham ya maida k’ofan ya rufe kafin ya take mata baya yana fad’in Allah ya huci Zuciyar Mamanshi tuba yake.
Sukai zaune a parlor suna gaisawa bayan ta gama sillesa tas kan yanda ya maida tafiyar dare jiki musamman duba da yanayin hanoyin a yanzu.
Hisham ya tsareta da ido. Shi sai lokacin yake hango rama tattare da ita.
Ta d’an kuma dubansa “Waima mai Ya dawo dakai ne.? Inji baka jima da komawa bakin aikin ba. Kai da kanka kace kunada babban project a kampanin ku zaka tara hankalinka waje d’aya. Toh me ka dawo yi.?”
“Hajjah..” Ya kira sunanta a hankali.
Sai ta d’ago ta dubesa ganin sosai ya tara hankalinsa.
“Wani abu ya faru ne da bana nan.?”
Tambayar da yai mata sai taji tamkar yana sane da cewa Ummul tayi aure ne kuma ba kowa ta aura ba face D’anuwansa da suke Uba d’aya. Ji tayi kaman d’an nata Ya riga yasan sirrin da ta jima tana b’oye masa.
Ta girgiza kai a d’an daburce “Mai ka gani.. Kaga ni bacci nake ka katse min. Ko ma meye mayi magana da safe. Tashi kaje ga abinci a kitchen sai kai warming kaci tinda kai ka so zuwa cikin dare. Idan bai maka ba kasha ruwan shayi dama abinda ka Saba kenan.”
Hisham Ya girgiza kai. Tana k’ok’arin mik’ewa yai saurin k’arasawa Ya rik’e hannunta “Hajjah you look sick. Kinyi ciwo ne sanda bana nan..?”
Ta sauk’e ajiyan zuciya jin ba Ummul ya tambayeta ba wanda ba grin Allah da zai waye suyi waya bai tambayeta ita ba. Yaso karb’an lambar wayarta ma sai Hajjan ta sanar dashi Ummul batada waya. Yaita mamakin ya za’ace budurwa kaman Ummul ba waya a hannunta.
“Eh.. eh nayi dan zazzabin nan da ake fama dashi. Amma bai wani tsanani ba. Shiyasa ma ban sanar dakai ba gudun kar ka tashin hankalinka ka d’ago k’afa kazo. naji sauk’i Alhamdulillah.”
Hisham Ya girgiza kai “Haba Hajjah. Har kiyi ciwo ban sani ba.. Hajja a duniyar nan sabida wa nake neman duk abinda nake nema. Hajja sabida kece.. Lafiyarki na gaba da komai da kuma kowa. You are my number one priority kin sani..” ya kuma girgiza kai “Da ace wani abu ya faru dake da bazan tab’a yafe ma kaina ba.” Ya k’arashe fuskarsa fal damuwa.
Sai ta k’ura ma d’an nata ido ganin yanda hankalinsa ya matuk’ar tashi a sabida ita. Koda duka duniya zasuyi rejecting d’insa zata so shi ta k’aunace shi domin kuwa Hisham d’inta definition ne na d’a na gari a idonta.
Ta d’an dungureshi “Silly. Ba abinda zai sameni da izinin Allah sai naga ‘ya’yanka.”
Ya murmusa yana duban mahaifiyar tasa cikeda so da k’auna “And very soon zaki gansu in sha Allah. Dan wann karon na d’au d’amaran neman aure da gaske. Bazan koma ba sai na tabbata an bani ita.” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.
Zuciyarta yai wani irin tsinkewa. Take annurin fuskarta ya d’auke cak. Ta soma k’ok’arin kauda fuskarta dan bata so su had’a ido. Hasalima bata san ta yanda zata soma sanar dashi labarin Auren Ummul ba. Shin da wanne zata fara.? Cewa Ummul tayi aure ko kuma D’anuwansa da baisan yana dashi ba ta aura. Shin mahaifinsa tasowa yai daga kabari kokuwa dai yana raye tintinin.
Zata mik’e Hisham yai saurin dakatar da ita ganin gaba d’aya yanayinta Ya sauya tashi guda “Hajja na fad’i wani abu ne da bai dace ba.?”
Girgiza masa kai tai “Hisham kaje ka kwanta dare yayi.” Tana fad’in haka ta mik’e ta shige d’aki ta barsa nan wajen yana sak’e sak’e. Fatansa Allah sa dai lafiya ba wani abun bane ya faru. Jiki babu wani kuzari Ya mik’e Ya nufi nasa d’akin.
**
Washe gari Inna Dije bata Ida warwarewa ba sai a cikin mota bayan Sun d’auki hanya sunyi nisa. Ita kad’ai sai layi take dan baccin bai saketa ba. Haka Asshe da Anisa suka turata cikin mota. Ko zarafin Sallama da Ummul basu barta tayi ba.
Saida sukai nisa Abadan kafin Inna Dije ta ida warwarewa. Ta dubi Asshe dake gefenta da mamaki tana kuma duban cikin motar.
Asshe ta karyi goron dake hannunta dan galibi idan zatai tafiya mai tsawo da goronta cikin jaka. Ta murmusa tana duban Inna Dije “Barka da safiya K’awalliya.”
Inna Dije ta kuma dubanta da mamaki sai lokacin take tuno duk abubuwan da suka faru.
Asshe ta murmusa had’ida mik’a mata goro “Karb’i ki karya kumallo.”
Inna Dije kallon mamaki kurum take ma Asshe Har lokacin. Ta dubi goron da take mik’a mata “Kin bani k’waya cikin dare yanzu zaki had’a min da goro ki k’arasa kasheni. Makira algunguma.!”
Asshe ta dara kad’an “Haba K’awalliya wasa fah ake bugawa. Da sauran lokaci ai ba’a gama ba. Kika sani ko anjima ki lallasa ni.”
Inna Dije tace “Ina muke..?”
Asshe ta kuma karyar goronta “Kar ki damu mun kusa isa gida nasa a shirya Miki karin kumammalo mai kyau gudun kar kiyi mutuwar bakin al’muru.”
Inna Dije ta girgiza kanta Wanda Har lokacin nauyi Ya mata “Yanzu sabida rashin imani naki Asshe shine kika bugar dani ko sallan asuba banyi ba kika nad’oni kika saka cikin mota.. Toh ina jakan kayana.?”
Asshe ta tab’e baki “Buhun tsummokaranki zakice. Wari suke min a mota nai watsi dasu. Kar ki damu sabbi suna jiranki idan mun isa. Yanzu bari a samu waje a tsaya kiyi sallah tinda kin dawo hayyacinki.”
Inna Dije sai kallon mamaki take ma Asshe dan ta fara zarce tunaninta.
Koda suka iso Kano kai tsaye gidan Asshe suka nufa. Inna Dije ta samu ta saka abu cikinta sann tai wanka aka bata tufafi ta canza.
Asshe ta k’araso tana dubanta lokaci guda tana tinda ransa Suwaiba ta soma zuwa gidan.
Murmushi ta sakar mata ganin ta shirya tsaf “Ko kefa K’awalliya. Kin ganki kuwa..”
Inna Dije ta d’aga mata hannu alamun dakatarwa “Ke ni fah ba Suwaiba bace. Babu wani makircinki da zai bani tsoro. Bazan bari na sake fad’awa tarkonki ba. Mijina baisan nayi tafiya ba a nasa tunanin ina tare ne da d’a uwana. Ni ba ballagaza bace kaman Suwaiba.”
Asshe ta murmusa “Ashe duk kanwar ja ce.”
“Mai kika ce.?” Inna Dije ta katseta.
Asshe ta kuma murmusawa “A’a K’awalliya cewa nai idan kin gama Hilal sai ya kaiki masaukin ki.”
Zata fice kenan Inna Dije ta janyota. Saitin kunnenta take rad’a mata “Kinyi kuskure tinda kika kaini naga gidan. Watak’ila kin lashe wasan a wann karon. Amma ki kiyayi karawa na gaba. Abun bazai miki da kyau ba. K’walliya.” Ta k’arashe harda kashe ma Asshe ido.
Sai Asshe ta murmusa su duka biyun suna k’are ma juna kallo.
“Kar ki damu na Miki alkawarin babu had’uwa na gaba. Dan kafin wann lokacin zan tabbata ‘yarku ta fice daga rayuwar D’anmu. K’awalliya.” Asshe tace tana mai ficewa. Lokaci guda ta kira Hilal Tai masa umarni da yakai Inna Dije Asibitin koyarwa.
**
Cikin sand’a Umma ke takowa ta nufi k’ofan d’akin Abba tana addu’an Allah yasa kar ta tadda Dije.
Ai kaw tana tura k’ofan a hankali taga Babu kowa sai Abba dake kwance shi kad’ansa.
Tai k’uri tana dubansa sai taji hawaye na neman ciko idonta. Rayuwarsu na baya taketa tunowa da yanda burin son ganin ta aurar da Ummul ko ta halin k’ak’a ya rufe mata ido. Ta share hawayen da suka zubo mata tana neman afuwan mahaliccinta cikin zuciyarta. Cikin sand’a tamkar mai tsoron kar wani ya ganta ta shigo d’akin. A d’arare ta zaune gefe dashi. Tana hawaye take furta “Abban Ummul ka yafe mun. Na tapka kuskure mai girma. Kuma nasan ni ban cancanci yafiya ba.. Amma..” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Saida tai mai isarta kukan da ba sauti kafin taci gaba “Bazan gushe ba Ina maka addu’an samun lafiya mijina.. Hak’ik’a duniya makaranta ce kuma naga izna akan hakan. Duk abubuwan da na aikata Sun dawo gareni harda tukuici. Kaico na.. Kaicon irin wann rayuwa. Kaiconki Suwaiba.!” Ta k’arashe tana toshe bakinta dan kuka ne na gaske ke zuwa mata.
Shigowar Khulsum kenan ta hangi Umma zaune gaban gadon Abba tana shesshek’ar kuka.
Khulsum Tai saurin k’arasowa ta raba tsakanin mahaifinta da mahaifiyarta.
Umma ta d’ago jiki a sanyaye tana duban Khulsum wacce itama d’in ita take duba saidai babu d’igon annuri a fuskarta.
“Khulsum..!” Umma tace cikin tsananin rawar murya.
Khulsum ta girgiza mata kai “Umma me kikeyi a nan.. Dan Allah ki tashi ki fita kafin Inna Dije ta shigo ta taddaki. Dan yau ta sanar Dani zasu dawo tareda ‘Yaruwata wacce kikai mata auren rashin galiho. Inna Dije tace bazata bari aci amanan mahaifinmu dake kwance ba. Tace bazata dawo ba sai tareda ‘Yaruwata wacce kika rabamu da ita sabida son zuciya irin naki Umma.” Khulsum ta k’arashe hawaye na gangaro mata yayinda Umma ma ke hawaye tana jinjina kai. Dan a halin yanzu ita dai kam tasan batada wani hujja ko kalamai da zatai amfani dasu dan ta wanke kanta. Ta kuma san sai yanda k’arfin Dije ya k’are wajen ganin ta rabata da ahalinta.
“Umma dan Allah ki tashi ki fice.. Bamu neman wani tashin hankali a nan..” Khulsum ta sake fad’i cikin rawar murya.
Jiki a sanyaye Umma ta mik’e sai ta ajiye ‘yar kular da ta shigo dashi na abinci Wanda ta kawo ne ma Khulsum d’in.
Duban foodflask d’in Khulsum Tai ganin Umma takai k’ofa tai saurin dakatar da Umma kafin ta d’auki kular ta mik’a mata “Kin mance wann Umma. Idan dan Abba kika kawo baici.. Idan kuma sabida ni kika kawo kiyi hak’uri nima bana buk’ata. Ci na ko shana bai tab’a damunki ba Umma. Abu d’aya ne damuwarki a gidan duniyar nan shine ki aurar da ‘Yaruwata.” Tai murmushi mai ciwo “Auren da kikai ikirarin kin rabu dani akan shi Umma.. Wacce Har zaki mata irin wann kalami bana tunanin akwai sauran damuwar da zakiyi da ita Umma.. Haka ne.?” Ta k’arashe tana duban mahaifiyar tata.
Har lokacin Umma bata iya cewa komai ba sai hawaye.
Khulsum ta share hawayen da suka zubo mata kafin ta kuma nuna ma Umma k’ofa “Idan Inna Dije tazo nan ta sameki Umma kinsan abin bazai kyau ba. Ki dubi girman Allah ki duba jinyan da mahaifina ke ciki dan Allah ki fita ki tafi Umma..”
Umma ta jinjina kai tana hawaye ta nufo waje. Khulsum tai saurin bin bayanta rik’eda kulan abincin tana k’ok’arin dakatar da ita.
Daidai lokacin motar Hilal tai parking..
Aiko Inna Dije tana hango Umma da Khulsum tai saurin fitowa ta nufosu.
Ta yanda take shiga bata nan take fita ba. Saida tai ma Umma tas kafin ta janyo Khulsum tace maza su shige wajen Abba.
Khulsum ta kaikaito ta dubi Umma tana kuma sharan k’walla.
Haka Umma taci gaba da tafiya kaman kazar da k’wai ya fashe ma.
Hilal da akai komai gabansa bayan Umma yabi da mota dan sosai ta basa tausayi. Ya fito ya gaida Umma bayan yayi parking gefen kwalta. Umma ta ganesa d’an wajen Hajiya Asshe ne da ba yau suka fara had’uwa ba. Hilal Ya rok’eta ta shiga mota ya kaita gida. Da fari k’in amincewa Umma tai saida Hilal yai da gaske dan ta kula idan har bata shigan ba bazai k’yaleta ba.
Yai saurin bud’e mata backseat ta shige kafin ya dawo mazauninsa Ya shige had’ida tada motar.
Har k’ofan gida yakai Umma kafin Ya juya. Maimakon ya koma gida sai ya koma asibitin.
Room number d’in Abba ya tambaya a reception suka sanar dashi. Ya isa yai knocking. Har lokacin Khulsum kuka take
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 64