Share this page
sabida kwanakina k’ayaddu ne a halin yanzu. Kwanaki k’alilan suka rage mun kaman yanda Likita yace sabida ciwon daji na huhu da nake fama dashi. Watak’ila wann hukuncin abinda nai ma mahaifiyarka ce. Had’a baki da akai dani aka ci amanarta. Ni tawa ta riga ta k’are kuma na girbi abinda na shuka. Saura Ya rage naka Hisham.. Ka tafi ka dauki fansa. Ka dauki fansa wa mahaifiyarka.. Ka tarwatsa ahalin da suka zalunceta.. Kasa su biya abinda suka aikata mata..! Wasiyata a gareka kenan..! Fansa..! Ka d’au wa mahaifiyarka da kai kanka Fansa..!’ Yana ida fad’in haka ya soma tari sosai yana kame k’irjinsa.. Ba’a jima ba yace ga garinku ya mutu. Tin daga wann lokacin, tinda wann mutumin ya bani labarin abinda Mahaifina da matarsa sukai ma mahaifiyata sai naji a duniya banida sauran buri da ya wuce d’aukar Fansa.. Sai naji kaman amfani na kawai na girma na d’auki fansa ne.. Fansar duk abinda akaima mahaifyata da irin rayuwa na k’ask’anci da muka fuskanta ta dalilin wann k’age da aka mata. Nayi rantsuwa sai na tarwatsa wann ahalin koda shi kad’ai ne abinda zanyi a rayuwata. Shekaru biyu na rayuwata na b’ata a gidan yari kafin daga bisani aka fiddo ni. Koda na fito ban nuna ma Hajja na san wani abu dangane da baya ba. Ban nuna mata na san asalina ba. Saima na daina tanbayarta gameda asalina da dangin mahaifina. Daga nan sai na maida hankali kan aikin k’arfi da karatuna fafa. A lokacin Hajja ma ta soma sana’ar d’inki. Sai muka bar k’asar Borno gaba d’aya muka dawo makwabciyarta Yobe. Mun jima a yobe kafin muka dawo Kano. A nan na maida hankali na karanci b’angaren Architecture sabida mutumin can ya sanar Dani mahaifina Engr ne na gine gine sann sana’arsa kenan. Sai na fuskanci idan ina so na kutsa cikin ahalin na musu lahani kwatankwacin Wanda suka mana nida mahaifiyata dole ya zama inada wani makami da zanyi amfani da shiga jikinsu dashi. Nayi dedicated lokaci sosai ganin na zama mai kwazo a fannin. Ban huta ba har saida na zama cikakken Architect kuma kwararre. Duk wani labarai da ya danganci Kampanin Mahaifina wato Maitama Builders baya wuceni. A nan ne na fahimci ta hanyarka ne zanfi samun saukin shiga cikin kampanin harma da ahalin.I became Woolf in Sheep’s clothing and befriended you in order achieve my goal.” Ya kuma duban Haidar yana jinjina kai “Kaji dalilin da yasa na kutsa cikin ahalinku. Sann na kawo Dareen cikin rayuwarka dan ta zame mun kaman spy. Ta dinga sanar Dani duk wani hali da kake ciki musamman tsakaninka da iyayenka.. Dareen ita ta jefeka da asiri Haidar dan ta kasance da kai saidai na goya mata baya sabida k’udirin da nake dashi akanka da ahalinka.. Na amshi tukunyar da Tai maka asiri na b’oye a wajena ne sabida nasan duk daren dad’ewa wataran zan karya wann asirin da hannuna. Kuma hakan ce ta kasance na fasa wann tulun da ta d’aure kurkwarka ciki bayan da na fahimci ka auri Ummulkhair..!” Haidar na hawaye yake huci yana dubansa “Don’t you dare mention my wife you psycho.!” Hisham ma hawaye yake yana jinina kai “Dole na ambaceta Haidar..! Kasan dalili..?” A fusace Haidar yace “You are obsessed with her.!” Hisham ya girgiza kai “No Haidar.. Na Sani na so Ummulkhair Tun kafin ka aureta.. Amma a baya ne..! I’m not capable of loving..!” Hisham ya basu labarin had’uwarsu da Anisa da yanda akai suka tabbata AUREN WATA UKU na Ummul da Haidar yazo k’arshe, yanda Ya d’auki Ummul Ya kaita ma Hajja har stabbing kansa da yai da duk wani k’ulli da yai dan ya tabbata Ummul bata koma wajen Haidar ba. Yaci gaba da jinjina kai yana duban Haidar “Na fahimci ba Ummul nake so ba. You are the one I’m obsessed with Haidar. You are like my trigger.. Kaidin kana tuna min duk wani abu da nai going through ne a rayuwa Wanda iyayenka sukai sanadiyan jefani da mahaifiyata ciki. Na fahimci duk abubuwan da nakeyi inayinsu ne kawai dan na k’untata maka..! Amma bayan da na fahimci Anisa na d’aukeda juna biyu.. Bayan da na fahimci zan zama mahaifi.. Sai ya zama ba abinda nake so irin wann D’an.. Wann cikin dake jikin Anisa.. Haidar Allah shine shaidana na zubar da makaman yak’ina da kai tun a SouthAfrica.. Na kuma dawo gida Nigeria da zuciya d’aya.. Da niyyan na Gina rayuwa mai kyau da ahalina.. Ina nufin Anisa da abinda ke cikinta.. Koda Anisa bata sona.. Na saka ma raina a hankali zan koya mata sona.. Sann Watak’ila zuwan wann D’an dake cikinta zai iya canza k’iyayyar da take mun.. Amma like they say abinda ka shuka shi zaka girbe.. Na yarda abinda na shuka shine nake girbewa.. Na yarda ba komai a cikin fansa face tarin nadama da danasani. I lost the child..! I lost my child.. Kuma na sani.. Idan Hajja taji abubuwan da na aikata In the name of revenge bazata tab’a yafe mun ba. And she will despise me.. Zata tsaneni.. Koma na rasa mahaifyata gaba d’aya kaman yanda na rasa D’ana..!” Ya juya ya dubi Anisa wacce ta fice a hayyacinta sabida galabaita. Ya dawo da dubansa ga Haidar “Please save my child Haidar.. Please he’s your nephew.. Save him please..! Ban damu ba idan Dareen ta kashe ni a nan.. But please you need to save Anisa and the child..!” Kafin Haidar yai wani motsi sai gani sukai Dareen ta zaro bindiga. Tai pointing Anisa dashi tana fad’in “Da ita da abinda ke cikinta zasu mutu Hisham..! I don’t give a damn about you or your wife.. And much less your unborn child.. Dukanku uku ina nufin your little family.. Matarka da D’anka dake ciki zaku Mutu yanzu a nan.. Ka zaba da waye zai fara tafiya cikinku..?” Haidar Ya soma girgiza kai yana duban Dareen “No Dareen.. Please don’t do this.. Just let them go please.. It is me that you want.. I’m right in front of you.. And I’m not going anywhere.. I’m coming with you.. Just let them go please..!” Dareen ta harba harsashi sama ta saki k’ara tana fad’in “No Haidar.. These two destroyed our own little family.. Sun kashe mana D’anmu kuma sun tarwatsa mu.. Basu cancanci rayuwa ba..!” Ana haka suka soma jiyo sautin motar ‘yansanda tana nufo wajen. Dareen ta waigo ta dubi Haidar da mamaki “Did You call the police..? You betrayed me Haidar..!” Ta soma kuka tana girgiza kai yayinda kartan guda biyun suka soma k’ok’arin janye wheelchair d’in Dareen suna fad’in “Ma’am we need to leave right away.. The police are heading our direction.. We can’t afford to get caught..!” Dareen ta saki kara tana tarjewa take fad’in “No..! I’m not leaving.. I’m not going anywhere without Haidar..! No.. Bazan tab’a barin Haidar ba.. He’s mine..! Shi din nawa ne..!” Daidai lokacin ‘Yansanda sukai masu kawanya suna fad’in Dareen da yaranta suyi surrender.. Girgiza kai Dareen take tana dubansu. Cikin huci take furtawa a hankali “If I can’t have you Haidar.. Then no one will have you.. Zan kashe ka kuma na kashe kaina.. Zamu kasance a eternity tare da D’anmu gaba d’aya.. Zamuyi forming ahalinmu a can..!” Tana ida fad’in haka Tai saitin Haidar da bindiga tana fad’i da k’arfin gaske “I love you Haidar..!” Tauuu.!!! Ta saki harsashi. Hisham Ya saki k’ara yana ambato sunan Haidar da k’arfin gaske..! Daidai lokacin signal d’in Ya d’auke daga nan yanda suke kallo cikin parlorn Daddy. Bayan labari mai firgitarwa had’ida tsoratarwa da suka gama saurara. Tabbas harsashin kaman ta hudo cikin camera d’in ne ta samesu gaba d’aya.! SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!* *65* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* *END* Haidar ya tallafo Hisham Wanda tuni Ya mik’e dukda k’afafunsa dake masa rawa Ya tare ma Haidar harsashi a lokacin da Dareen ta harba. Harsashin ta samu Hisham a bayansa maimakon ta Sami Haidar. Tuni jini ya soma ambaliya. Girgiza kai Haidar yake yana duban Hisham dake furtawa cikin galabaita “I’m a failure… A worthless son and a cruel brother… Forgive me Haidar… Ka yafe mun.. Kace ma Hajja ta yafe mun..! Ka rokar mun gafaran iyayena Wanda na zamto jarabtu a garesu.. Dan Allah ka yafe mun brother..!” Girgiza kai Haidar yake “What have you done Hisham..? Mai ka aikata.. Mai ka aikata ma kanka..?” Ya k’arashe yana girgiza kai yana kuma ce ma police d’in suyi maza su kirawo ambulance. Dan tuni Hisham Ya fice hayyacinsa. Haidar na rik’e da Hisham ga Anisa ma can kwance unconscious. Su duka biyun Sun fice hayyacinsu a haka ambulance ta k’araso aka sakasu ciki. Ya waiga Ya dubi Dareen dake kwance kasa jini na bin kanta dan a lokacin da ta harba harsashin da nufin Ya samu Haidar take ta D’ana ma kanta. Aka rufeta da farin k’yalle dan tuni tace ga garinku su kuwa yaran nata ‘yansanda tuni Sun kama su. Ana isowa asibiti aka wuce da Hisham da Anisa zuwa ER dan ceto rayuwarsu. Haidar na zaune wajen Daddy ya k’araso. Ya tsaya daga nesa yana duban Haidar d’in ga wasu kwantattun hawaye saman fuskarsa. Juyowar da Haidar zai sukai ido hud’u da Daddy. Sai Ya mik’e tsaye yana jin hawaye na k’ok’arin ciko idonsa shima. Daddy na k’arasowa suka rungume juna shida Haidar sai kawai Daddy yai bursting cikin kuka. Fad’i yake “I’m sorry.. I doubted you… I’m sorry son.. Please forgive me..! Ka yafe ma Babanka..! For he’s not perfect..!” Haidar ya rik’e hannayen Daddy suna duban juna. Ya girgiza kai kad’an “No Daddy, ka daina rokona gafara..” Sai ya d’anyi shiru yana duban Daddy “I just wanted the truth to come out.. amma ban rik’e ba Daddy.. Kasan dalili..? Sabida kai din mahaifina ne..!” Daddy sai Ya kuma rungume Haidar hawaye na kuma gangaro masa. Haidar ya dan shafe fuskarsa da tafukan hannaye yace “Hisham da Anisa suna ciki.. Hisham is undergoing a surgery.. He took a bullet for me Daddy..” Katsesa Daddy yai da fad’in “I don’t know Haidar.. Ban sani ba idan ina so na sake ganinsa bayan abubuwan da naji ya aikata maka.. Meyasa zai cutar dakai.. You haven’t wronged him in any way.. Ni nai masa laifi why would he take it out on you..! Meyasa bai hukuntani ba ya zab’i ya hukuntaka..? Meyasa zai shiga rayuwarka Ya tarwatsa maka..!” Girgiza kai Haidar yai “No Daddy.. Please don’t talk like that.. Dan Allah kayi ma Hisham uzuri ka yafe mishi… He’s gone through a lot in life.. As they say zuciya batada kashi.. Mu duka mun hukunta sashi da kurakuren sashe. Mu d’auki hakan matsayin k’addara da jarabawar ahalinmu..” Ya dan jinjina Kai kad’an yana duban Daddy “Koda mantuwa ya kasance mai wahala.. Mu yafe ma juna.. At the end, we are all family.. And that’s what matters..” Ya k’arashe yana k’ak’aro murmushi. Daddy ya share hawayen da suka gangaro masa yana duban Haidar d’in. Kyakkyawan murmushi saman fuskarsa “Kanada zuciya mai kyau Haidar.. Madallah da D’a irinka..! Madallah da kyauta irinka..! Hak’ik’a nayi kuskure da na kasa ganinka a gabana..? Hak’ik’a samun D’a irinka babban kyauta ce Aliyu.. A lokacin da wasu ‘ya’yan suka zamo jarabawa ga iyayensu wasu kuma sanyin idaniya ne.. Nayi zaton kaine jarabawa na.. Nayi zaton D’an da na rasa a baya shi zai zamto sanyin idaniya a gareni. Ashe ba haka bane.. Ashe wasu kyautan basuda farashi a duniyar nan..! Allah ya maka albarka Aliyu..! Allah ya haskaka rayuwarka da d’imbin alkhairai..! Kaman yanda ka zamto D’a na gari a gareni ina fata ka zamto Uba na gari ga ‘ya’yanka wad’anda zasuyi alfahari dakai sann su zamto sanyin idaniya a gareka..” Ya k’arashe yana kuma hugging Haidar. Haidar ya share k’wallan da suka gangaro masa yana mai rungume Daddy. * A b’angaren su Mommy kaw tuni anyi rushing Hajja zuwa asibitin sabida jininta da Ya hau har ta rasa consciousness. Farkawan da Hajja zatai sai ganin Mommy tai zaune gefenta. Mommy ta matso tana mata sannu. Hawaye na gangaro mata take girgiza kai “Ta ina na ragesa..? Nayi iyaka kokarina ganin na tayar da D’a na gari.. Na sadaukar da komai nawa wajen inganta rayuwarsa.. Na zata na basa duk wani tarbiya da kulawa.. Ashe ni din na gaza… Ni ba uwa ta gari bace..!” Ta k’arashe cikin rawar murya kuka na cin k’arfinta. Hannayenta Mommy ta kamo tana girgiza kai “Kar kiyi magana irin haka Fannah..! Tabbas ke uwa ce ta gari.. Sann kin bama Hisham duk wani kulawa.. Kin sauk’e nauyi da hakki da Ya rataya a wuyanki irin Wanda ni ban sauk’e akan nawa D’an ba..” Hajja na hawaye tace “Meyasa zai min irin wann sakayyar..? Ta ina na tauye shi.? Tsawon rayuwata nayi zaton mutumin kirki na raina.” Mommy ta jinina kai “Wann shi ake kira jarabawa.. Haka Allah yaso Ya sanya sashe cikinmu matsayin jarabawa ma junanmu.. A baya ban kasance uwa ta gari ba amma an jarabci D’a na Haidar da samun uwa irina… Sann yayinda ke kika zamto uwa ta gari sai aka jarabceki da samun D’a irin Hisham Wanda Ya girma da burin fansa Ya kuma rufe Miki k’udirinsa.. Amma dukda haka ba yana nufin Hisham ba yaron kirki bane.. Shi d’in d’a ne mai biyayya ga mahaifiyarsa.. Kaman dai yanda yai defending mahaifyarsa Har ya tafi kurkuku a sabida haka. Rashin sa’a akayi Ya hadu da Wanda Ya karkata masa zuciya zuwa burin fansa a gidan kasu. Kuma kuskurenki d’aya ne a nan rashin sanar da Hisham asalinsa da bakiyi ba da bakinki har dai wani mugu Ya rigaki sanar dashi Ya kuma daurasa akan tarbiyar yanda zai fuskanci al’amarin. Shiyasa a duk wani abinda Ya shige ma yaranmu duhu musamman idan wann abun mukeda hakkin sanar dasu. Lallai mu Ya kamata mu sanar dasu domin tarbiya namu ne hakkinmu ne.. Nauyi ne da ta rataya a wuyanmu.. Baza mu so wani daban waje yaje Ya basu nasa tarbiyar ba.” Ta kuma kamo hannayen Hajja “Kar kiyi ma Hisham baki.. Kar ki hana masa yafiyarki da albarkanki.. Ke d’in uwa ce kuma babban jigo na rayuwarsa. Hisham ya tuba ya kuma gane kuskurensa. Muyi fatan Allah Ya yafe mana baki d’aya ya kuma iya mana abinda mu bamu iyawa. Allah yasa iyaye da dama su d’auki darasi cikin irin rayuwar da mukayi da namu yaran.” Hajja ta amsa da Ameen tana jinjina kai cikin matuk’ar sanyin jiki. * Bayan da Anisa ta farfado ne su Aunty Asshe harma da Ummul da Hilal suka k’araso. Kai tsaye d’akin hutu da Anisa take Aunty Asshe da Hilal suka nufa yayinda Ummul Tai tsaye tana dubansa Ya basu baya yana amsa waya. K’walla tab idanunta. Juyowar da zai sai sukai ido hudu.. Ji take kaman ta tafi a guje ta haye jikinsa sabida farin ciki.. Ya kaste wayar da yake Ya tsareta da ido sihirtaccen murmushi saman fuskarsa. Sai Ya bud’e mata hannaye alamun ta taho. Ta soma waige waige dan ta tabbatar ba mai ganinsu. Haidar ya kuma murmusawa yana tayata waige waigen “Taho mana.. There’s no one here..” Ya fad’i yana daga mata gira. Ai bata san sanda ta tafi a guje ta rungumesa kaman ma ta mance Baba Ali dake cikin hannunta. Ya had’esu duka Ya rungume.. Ummul kam sai ta saki kukan da taketa k’ok’arin dannewa. Haidar Ya kuma matsesu gaba d’aya had’ida lumshe idanunsa “It’s over.. It’s finally over.!” Ya Baba Ali dake cikin hannunta “Come here Little Lion.. Come to Paapa..!” Ya k’arashe yana daga yaron sama tuni yaron Ya shiga kyalkyale dariya alamun yayi kewan Babansa. Ummul ta tsare su da ido tana jin shauk’in k’aunarsu gaba d’aya. A can d’aki kuwa wajen Anisa Hilal Ya sakata gaba ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba Kai kace ba ‘yan biyu suke ba. Kace Ya girme mata ne. “Kinsan me kin tabbata mai kwakwalwar kifi Anisa.. Why would you get married to that psychopath.. Are you that stupid..? Bansan shashashancinki yakai wann peak din ba.!” Anisa ta juya ido da kyar had’ida furzar da huci “Ammi please… tell him to leave..” Aunty Asshe ta hararesa “Bakada hankali ko Hilal.. Baka ganin halinda ‘Yaruwarka ke ciki ne.. Idan bazaka iya taimakawa da komai ba ka wuce ka fita.. Kar ka sake stressing dinta.” Hilal Ya furzar da huci “Amma Ammi ni fah gaskiya kawai nake fad’i..” A fusace tace “Rik’e gaskiyar taka bamu so..” Ta k’arashe tana k’ok’arin kai spoon din oath bakin Anisa. Sai lallaba Anisar take tana fad’in tasha ko kadan Likita yace ba abinci a system dinta. A haka su Mommy da Hajja suka shigo. Mommy ta k’arasa ta d’anyi hugging Anisa daga nan yanda take kwance saman gado Tai mata sannu da jiki da fatan samun sauk’i. Sai suka fice gaba d’aya su ka bama Anisa da Hajja waje. Bayan Hajja ta mata sannu da jiki. Hannaun Anisa ta rik’e cikin nata “Ina mai baki hakuri on behalf of Hisham.. He manipulated you and made you go through a lot… Kiyi hak’uri Anisa.. Kuma idan baki son zama dashi ki sani kinada goyon bayana.. Allah ya baki lafiya..” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin janye jiki. Har ta kai k’ofa ta sinkayo muryar Anisa “Hajja..!” Juyowa Hajja Tai tana dubanta. Anisa tasa hannu ta share hawayen da suka zubo mata “Im not innocent.. I’m also being punished for my sins… Abinda na shuka nima nake girbewa.. Wad’anda sukafi cancanta a nemi yafiyarsu sune Ummul da Haidar… Ina fata su yafe mana kuma Ina fata Allah Ya yafe mana gaba d’aya.!” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka. Hajja ta dawo da baya ta rungume Anisa daga nan yanda take kwance. Sai Anisa ta shige jikinta tana matsan hawaye. Ta d’ago ta dan dubi Hajjan “How’s… he doing..?” Tai tambayar tana mai janye jikinta daga na Hajja. Ganin Hajja ta mata k’uri sai yasa ta dan sadda kai ta k’arada “I mean.. Hisham.. What’s his condition.. What did the Doctors say..?” Hajja ta sauk’e ajiyan zuciya “Sunyi nasaran cire harsashin sann aikin yayi kyau according to them.. But they insist something might remain irreversible in his life.. Sabida harsashin ta kuskuri k’ashin bayansa... Hakan na nufin zai iya zama saman wheelchair har k’arshen rayuwarsa.. sunce a jira farkawarsa.. Sann a shirya ma aukuwar komai.” Ta jinina kanta kad’an ba tareda ta kuma furta komai ba. Jikinta duk a mace. Hajja ta d’auko oath d’in taci gaba da bama Anisa tana fad’in Tai kokari ta shanye. ** Koda Hisham Ya farfado kuwa iyayensa guda biyu basu tunk’ar d’akin da yake ba. Haidar ne yaita basu baki yana fadin suyi hakuri su yafe ma Hisham su kuma shiga su dubasa. Dik da shima Haidar d’in bai iya shiga Ya duba Hisham d’in ba. Ya yafe masa amma baijin su biyun zasu iya zama in good terms like before. Daddy kaw darajan Haidar Hisham yaci Shiyasa zai shiga ya duba halinda yake ciki. Kwance Daddy ya hangi Hisham saman gado, Ya jima sosai yana dubana yana tuno farkon had’uwarsu matsayin d’a da mahaifi. Ya tuna yanda yaita k’aryata Haidar akan Hisham d’in. Ya tuna irin yardar da Ya basa had’uwarsu ta farko cikin k’ok’arinsa na gyara kuskuren da yai ma Hisham d’in da mahaifiyarsa a baya. Juyowar da Hisham zai ya hangi Daddy tsaye yana dubansa cikin yanayi da zai iya cewa bai tab’a ganin fuskarsa ciki ba. Sai Hisham yaji Daddy ya furta “SON.!” Hisham ya d’ago da mamaki yana duban Daddy. Gashi dai ya ambacesa da D’a amma fuskarsa a matuk’ar daure. Hisham yaci gaba da hawaye yana duban Daddy. Yayinda Daddy yaci gaba “Kasan na baka wann title d’in a karon farko da na d’aura ido akanka matsayin D’ana.?” Hisham ya jinjina Kai a hankali yana mai ci gaba da hawaye. Hawaye suka gangaro ma Daddy har lokacin fuskarsa a matuk’ar daure. Daddy yaci gaba “Shin kasan Haidar shekara nawa yayi ina kallonsa a gabana amma ban tab’a basa wann title d’in ba..?” Muryar Daddy ta soma rawa “Kasan shekara nawa na kwashe ina hukunta Haidar a sabida rashinka..? Kasan shekara nawa nayi ina denying masa sunan da shi ya cancanta fiyeda kai..?! Did you know that I never doubted you.. Not even once.. Ka san na yarda da kai a karon farko.?” Yaci gaba da girgiza kai yana duban Hisham “Why..? Meyasa..?” Kuka ya hana muryar Daddy fita. A haka ya silale wajen yana dafe fuskarsa da tafukan hannayensa yana jin zuciyarsa na masa nauyi. Hisham ma kuka yake yana fad’in Daddy ya yafe masa. Saida sukai mai isansu su duka biyu Hisham naci gaba da rok’on Daddy gafara kafin Daddy ya mik’e ya daidaita tsayuwarsa yana duban Hisham d’in with a straight face “Duk abubuwan da ka mun a Company.. All the damages you’ve caused… All the scandals.. All the setbacks zan iya yafe maka kuma zan d’auki hakan matsayin hukunci gameda kuskuren da na aikata maku kaida mahaifiyarka a baya, musamman kai.. Koda rayuwana ka nema duka zan d’auki hakan matsayin hukunci na.. But not at the expense of my Son’s life.. Ran Haidar yafi mun duk abinda na lissafo maka ciki harda nawa rayuwar. Da ace na rasa Haidar a wann had’arin motar da ka shirya masa da bazan tab’a yafe maka ba.” Cikin zuban hawaye yake fad’in “Nasan ban canci yafiyarku ba.. And I know I’ll have to earn for it..” “Is that why you took a bullet for him..? Kana tunanin hakan da kai ya wadatar.?” Daddy ya katsesa. Kafin yaci gaba “Koda bakayi hakan ba Haidar zai yafe maka. Kasan dalili.?” Daddy yaci gaba da jinjina Kai “Sabida yanada zuciya mai kyau Wanda babu k’udirin fansa cikinta sai d’imbin alkhairi.” Hawaye suka kuma gangaro ma Hisham kansa kife a k’asa. Girgiza kai kurum Daddy yai kana yasa kai ya fice cikin sauri dan bai fata zuciya ta debesa Ya furta wani kalma out of anger. A k’ofa suka had’uda Hajja tana shigowa. Suka dubi juna duk jikkunansu a mace musamman Hajja. Sai kawai tasa kai ta shige dan bayan abinda Hisham Ya aikata gaba d’aya nauyin kowa take cikin ahalin. Kasa duban mahaifyarsa a k’wayan ido yai. He failed her as a son.. Bayan duk wani fad’i tashi da Tai akansa. Bayan duk wani sadaukarwa irin sakayyan da zai mata kenan.? Hajja kuka Hisham kuka. Sai taji bazata iya jure tsayuwa kusansa a d’akin ba. Tasa kai zata fice amma sai ta tuna kalaman Mommy a gareta da wann Hisham ya samu sassauci wajen mahaifiyarsa. ** Kishingide suke saman sofa ta shige jikinsa sosai. Hannunsa zagaye da ita yana shafa sumarta kaman mai k’irga kitson dake kanta. A hankali ta furta “Ka yafe mun..! Na maka kuskuren fahimta.” Mik’ewa yai zaune had’ida cireta daga jikinsa. Ummul ta bisa da kallon mamaki yanda ya tsare sosai yasha mur. Sai ta d’an girgiza kai kad’an “Bazaka yafe mun ba ko..?” Tai maganar kaman mai shirin kuka. Ya jima sosai yana dubanta sai ya tabe baki kad’an “No.” Yai maganar yana mai gyara zamansa cikin kujera harda hard’e hannayensa a k’irji. Sosai ya sha mur fuskarsa babu alaman walwala. Tai rau rau da ido “Toh ka fad’a mun mai zanyi ka yafe mun..” Ya dan saci kallonta da wutsiyar ido yanda ya hango damuwa k’arara saman fuskarta. Ya saki murmushi kad’an. Bata ankara ba sai jinsa Tai cikin jikinta. ya shigar da fuskarsa cikin wuyanta sosai. Cikin sigan rad’a yake furta “Maybe I can forgive you..” Ta dan fito da ido waje “Da gaske.?” Ya jinjina Kai kad’an “But only If you tell me… You love me.. like hundred times.. That’s the only way.” A hankali take sakin sihirtaccen murmushi tana kashesa da wani irin duba “That’s just it.. Shikenan.?” Haidar ya jinjina mata kai yana fadin “Umhum..!” Sai ta matso sosai saitin kunnensa ta rada masa “But I love you more than love itself..And when I tell you I love you.. I’m not saying it out of habit.. I’m reminding you that… You are my life..!” Baisan sanda ya rufe bakinsa da nata suka lula wata duniyar. ** Months later… An fara shirye shiryen auren Hilal da Kulsum, Azeema da Sadis da kuma Badia da Alhaji Gimba. Dan Alhaji Gimba bai k’asa a gwiwa ba har saida ya tabbata ya samu soyayyar Badia da amincewar ta. Matarsa ta jima da rasuwa kuma d’a d’aya gareshi Wanda tinda Ya tafi turai karatu bai kuma

Chapter 63 of 64