Share this page
tsaneka Haidar.!” Ta kuma lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. ** A can gidan Hisham kaw cikin huci Ya mik’e kaman zai shak’o Dareen dake tsaye gabansa yake fad’in “You damn fool.. Na fada miki so nake ki sheganta wann tsinannen cikin jikin naki, kan wani dalili zaki jingina kanki da kalmar Aure tareda Haidar.. Auren da Boka ya Miki alwali… Auren da akai Haidar bashi a hayyacinsa. Tsakaninki da Haidar babu wani kalma mai sunan Aure a tsarina.! Wann shegen dake cikinki shege ne shid’in shege ne dole ki sheganta shi kaman yanda Kwaise Maitama ta shegantani ina jariri d’an wata uku a ciki.. Ina so tarihi ya maimaita mata Kansa cikin ahalin Maitama Akan jikan Kwaise Maitama. Taji zafin samun jika shege kaman dai yanda ta shegantani. Kin fahimtaaa..!” Ya k’arashe kaman zai shak’e wuyanta sai wani irin tururi yake. Girgiza kai Dareen take tana huci tana Shafa cikinta “No.. No way Hisham.. Bazan tab’a abinda kake fad’I ba, bazan tab’a sheganta D’a na da Haidar ba.. Koda ace Aurenmu bai kasance kaman ko wani Aure ba wann cikin da Aure aka same shi.. Kuma shine abu kad’ai da zai maida Aurenmu da Haidar.. Ka cire wann a ranka.. Duk abinda zai faru Babu abinda zai hanani komawa ga masoyi na Haidar tareda D’anmu dake cikina. Zamu Gina ahalinmu as it should be.!” Kaman daga suka sinkayo muryar Anisa “Wann kuma k’arya kenan.. Zancen banza kenan. Ban aikata komai ba ban sadaukar da komai dan wata kucaka irinki ta mallaki Haidar ba.!” Dareen ta juyo cikin tsananin mamaki tana duban wacce Tai maganar “And you.. Ke kuma wacece..?!” Anisa taci gaba da takowa “Ki kirani masoyiyar Haidar da ta sadaukar da komai tayi duk wani fad’i tashi dan ta mallakesa..!” Dareen ta juyo tana duban Hisham da mamaki “Hisham.. Wacece wann.. And what is she saying.?” Anisa ta katseta “Kar ki tambayesa. I am his accomplice.. Mu biyun tare muka shirya dawowarki cikin rayuwar Haidar dan kawai mu raba Haidar da matar da Mahaifiyarsa ta aura masa. Ki kirani masoyiyar Haidar sann ki kira Hisham da masoyin Matar Haidar. Mu biyun are team.” Ta murmusa “Ki yarda dani amfaninki Ya k’are kinyi abinda muka kawo kiyi Dikda naji wani babban kwafsi.. Ki sani koda ace cikin jikinki na Haidar ne bakida wajen zama cikin rayuwarsa. Haidar nawa ne ni kad’ai.!” Dareen ta juyo tana wani irin duba na cin amana ma Hisham dan batasan da zancen wata Anisa ba sai kawo wann lokacin. Ta soma girgiza kai tana jada baya “Lallai ka cika shed’ani Hisham.! Ka cika babban mayaudari.. You are a Demon.! Na kasa yarda na Barka kayi amfani dani dan cimma bak’in burinka akan Haidar a karo na biyu..! Amma ka sani wann shine zai zama na k’arshe.. Zan tafi yanzu.. Zan sanar da Haidar komai duk wani mugun k’ullinka akansa ko dan D’ansa dake cikina.. Bazan tab’a bari ka sake cutar da Haidar ba.. Zan sanar dashi komai koda zan rasa shi..!” Tana ida fad’in haka ta fice a guje. Hisham Ya soma k’ok’arin binta a guje yana kiran sunanta yana fad’in ta dakata.. Anisa tuni ta take masa baya. Koda suka fito Sun tadda Dareen Har ta bud’e gate ta fice.. Anisa ta shige mota tace da Hisham maza Ya shige su bi bayanta. Hisham Ya shige suka soma bin bayan Dareen dake gudu a k’afa tana saka hannu tana neman abun hawa. Saidai akai rashin sa’a babu alamun mutane a layin balle abun hawa. Dareen taci gaba da gudu a galabaice tana k’ok’arin tsere musu.. SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!* *50* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* Wasa wasa an shafe sati uku da mutuwar Auren Ummul da kuma Haidar. A wann lokacin Daddy ya shafe a k’alla sati guda da dawo daga SouthAfrica, kuma labarin scandal din da yai erupting wajen bikin tariyar Haidar d’in Ya cimmasa. Hankalin Mommy duk ba’a kwance yake ba sanin mijinta mutum ne da ko kad’an baiso wani abu ya shafi Kasuwancinsa. Yanda rayuwar ahalinta Ya soma daidaita bata fatan abinda zai kawo musu wani mishkila ko sab’ani. Ga mamakinta sai Daddy ya tari abun bisa lumana ba kaman yanda Ya saba a baya ba. Dan ko zancen bai bata k’ofan ta masa ba dikda taso yi masa. Bai canza ko kad’an daga irin kulan da yake bata ba tin bayan da suka daidaita tsakaninsu. Hasalima k’ara janta jiki yai yana fad’in irin kewarta da yai. Ta d’an dubesa a sanyaye tana so suyi zancen sai Ya kuma janyo hannayenta yace “Kwaise na gaji da tafiye tafiyen nan. Inaga lokaci yayi da zan mik’a ma yaron nan ragamar kasuwancin.. Koda wani portion ne. We are not getting any younger.. Shekaru k’aruwa suke..” Mommy ta jinjina kai duk jikinta a sanyaye. Alamun shigowar mota sukaji. Daddy ya lek’a window sai Ya murmusa yace “Ina tunanin Yaronnan ne … Na kira shi yana company.. Na sanar dashi Ya bar aikin da yake yazo gida magana zamuyi.” K’irjinta ya bada dam.! Dan tuni jikinta Ya bata ba magana mai k’aramin mahimmanci bane zaisa ya kirawo Haidar ya bar aikinsa yazo gida dan kawai suyi magana. “Let’s go downstairs..” Ta sinkayo muryar Daddy yana k’ok’arin nufan k’ofa. Jikinta babu wani k’wari tabi bayansa. A parlor suka iske Haidar Har ya k’araso yana jiran sauk’owa mahaifin nasa. Haidar ya risina ya gaida iyayensa. Duk suka amsa masa da sakin fuska saidai kallo guda zakai ma Mommy ka fahimci tana cikin damuwa. Daddy ya dubi Haidar cikeda kulawa “Aliyu.” Ya kirasa da asalin sunansa. Haidar ya amsa cikeda girmamawa. Daddy yaci gaba “Na dawo na taradda abubuwa marassa dad’in gani da kuma sauraro. Garin yaya al’amra suka lalace har haka.?” Haidar ya jinjina Kansa a hankali sai yace “Daddy Kai hak’uri.. Ban.. san abubuwa zasu zama haka ba.. Amma tuni nasa jam’ian bincike su binciko yanda Dareen take.. Kai hak’uri Daddy.. Idan duka wann ya saka Kasuwancinka cikin had’ari..” Daddy ya sauk’e ajiyan zuciya kad’an sai ya girgiza kai yace “Ba wann nake son ji ba.” Mommy ta dubesa da mamaki. Sai Daddy yaci gaba “Ba batun Kasuwancina da abinda zai shafesa nake son ji ba.. A’a naka batun nake son ji.. Al’amarinka da iyalinka. Because you matters to me more than any business.” Haidar yaji wani abu can k’asar zuciyarsa. Yau Daddy ya zab’i ya fifita al’amarinsa sama da Kasuwancinsa da a baya yake d’aukakawa. Jikin Mommy yai sanyi musamman da taga Haidar yayi shiru. Duka laifin nata ne. Gwara ta sanar da Daddy yanda al’amarin ya kasance. Jiki a sanyaye Mommy tace “Dama..” Haidar bai bari takai aya ba yai karaf yace “Daddy scandal din da ya faru ya.. janyo sab’ani tsakanina da Ummulkhair.. Kuma har ta kaiga na mata saki.. d’aya.” Sai Mommy ta dubi Haidar cikeda tausayawa.. Ta fahimci yasan duk abinda tai amma ya zab’i ya rufa asirinta. Bazai bari mahaifinsa yaji ga abinda ta aikata ba gameda AUREN WATA UKU. Allah sarki D’a da uwa. Sai taji girma , k’ima da soyayyan d’an nata ya k’aru a kwayan idonta. Fatan ta Allah ya albarkaci rayuwarsa Ya daidaita al’amarinsa da iyalinsa. Daddy ya dan numfasa sai ya dubi Mommy yace “Rankidad’e, can I have a moment with my son.?” Ya k’arashe yana dan mata alama da ido. Mommy tace “Badai cireni akai daga cikin ahalin ba.” Ya dan murmusa kad’an “Waye ya isa ya cire ran gida cikin ahalinta. Magana ce tamu. Men talk.” Ta d’an murmusa “Kace dai kawai wariya. Toh bara na baku waje dama inada abinyi.” Ta k’arashe tana mik’ewa. Daddy yai gyaran murya kad’an yace “Haidar banji dad’in abinda kai ba dukda sanin saki a musulunci ba haramun bane amma sai idan Ya zama dole akeyi. Idan akace daga samu sab’ani za’a dinga saki da ko mu nan iyayenka bamu kawo har wann lokacin muna tare ba. Kai shaida ne.. Kaga k’alubale da iftila’i na rayuwa da mukaita fuskanta. Amma dukda haka muka jajirce. Har hakuri ta kawo mu yanda muke yau. All marriages have ups and downs but this decision should not arrive easily.” Sai Daddy ya mik’e tsaye kaman Wanda ya tuna wani abu “Kaga tashi muje.. Akwai yanda nake so ka rakani.” Haidar ya jinjina Kai yana amsawa. Suka jera suna tafe shida mahaifinsa. Ta window Mommy ta hangesu sun jera Sun fice. A ranta tace ko ina D’a da mahaifin suka nufa sai Allah. Ta murmusa tana jin dad’in yanda sabo ya fara shiga tsakaninsu. Koda suka fito Haidar ya tambayi Daddy ko Yai masa kiran driver d’insa amma sai Daddy yace a’a shi Haidar d’in zai tuk’a motar. Nan ma cikeda girmamawa Haidar ya amsa masa. Daddy ya shige mazaunin mai zaman banza yayinda Haidar ya shige wajen driver. Suna tafe Daddy yace dashi gidan Alhaji Gimba suka nufa. Kai tsaye Haidar ya d’auki hanyar gidan aminin mahaifin nasa. Koda suka isa Daddy yace da Haidar yai parking daga waje. Nan ma yabi umarnin mahaifinsa. Suka fito Daddy na d’an gaba kad’an yayinda Haidar ke take masa baya. Sai Haidar yaga Daddy ya nufi masallacin k’ofan gidan Alhaji Gimba. Suka gaggaisa da mutane ya tambayesu Ya Sheikh bai fito ba. D’aya daga cikin mutanen yace “Ai zai wahala Ya Sheikh ya fito yau sabida tun jiya yake cewa bai gane jikin ba.” Daddy yai masa fatan samun lafiya. Ya kuma yi ma mutanen Sallama Wanda kusan dukansu Dattijai ne kaman sa da ma Wanda suka fisa. Da alama duk sun saba dashi dan tare suke d’aukan karatu a nan masallacin tsakanin sallar magrib da isha wajen Imam ya Sheikh. Sun fito tareda Haidar kenan saiga Alhaji Gimba. Nan suka tsaya suna gaisawa. Haidar ya dan matsa gefe ya basu waje. Alhaji Gimba ya dubi Daddy ya dan girgiza kai “Lafiya dai naga ka taho tareda Haidar..?” Daddy ya dan sauk’e ajiyan zuciya yace “Lafiyan zance ba lafiya ba tinda kanada masaniyar abinda ya faru lokacin bikin tariyarsa da iyalinsa.. Tinda Har business competitors dinmu sun so suyi amfani da wann su sokemu.” Alhaji Gimba ya jinina Kai “Haka ne.” Daddy yaci gaba “Toh Wato abinda ke faruwa shine.. Wann abu da ya faru har ya haifar da matsala tsakanin shi Haidar d’in da iyalinsa.. Kuma kaga abu da yara tashi d’aya yayi saki.. Kasan da yawan samarin nan ba’a zama a fahimtar dasu menene ma Auren kansa kafin su shigesa which is wrong.. As a parent musamman ma Uba inaga yanada kyau idan D’anka yakai munzanin Aure ya kuma zo maka da batu na Aure idan Har zaka nemar masa Auren ‘yar wani. Ko dai kai ka zaunar dashi ka fahimtar dashi menene Auren kokuma ka kaisa yanda za’a zaunar dashi a sanar dashi Auren tareda hakkokinta da hukunce hukuncenta.. Dan nima har yau ina nadaman wasu kurakuren da nayi a baya kuma bana fata irin haka ya faru da D’a na. Idan ka duba da yawa yanzu Shiyasa zakaga mace macen Aure yayi yawa dan shiga cikin Auren kawai ake ba karatun sanin hukunce hukuncenta.. Shine kaga na kawo shi nan dan Sheikh Imam ya fahimtar dashi wasu abubuwa. Sai kuma akai rashin sa’a Sheikh yau bai fito majalisi ba.” Alhaji Gimba ya jinjina Kai “Wann gaskiya ne Abokina. Ina ma iyaye da yawa zasuyi yanda kayi da an rage wasu mace macen Auren da babu gaira babu dalili. Amma tinda yanzu Sheikh baya nan ni zan zaunar dashi mu d’an yi magana ta fahimta.. Kasan kai zai iya jin nauyinka a wasu abubuwan.. Sann idan son samu shima kasa ya dinga zuwa d’aukan karatu ko ba lokacin da muke ba.. Akwai lokacin da aka Ware dan samari kaman shi. Lallai yanzu Babu mai zama da jahiltan addini sai Wanda yaso.” Daddy ya jinjina Kai “Wann haka ne.. Toh zan bar maka shi. Zan kira driver yazo ni ya d’aukeni.” Alhaji Gimba yace “Akwai driver na ai sai ya kaika.” Nan sukai sallama Daddy ya sanar da Haidar shi zai tafi A d’an wani hut dake haraban gidan suka zauna yayinda Alhaji Gimba ya soma jan Haidar d’in da hiran Kasuwanci kafin ya d’anyi gyaran murya yace “Haidar, ni aminin mahaifinka ne nasan kasan da wann.” Haidar ya jinjina Kansa a hankali. Alhaji Gimba yaci gaba “Kaman yanda musulunci yace abokan iyayen mu iyayen mu ne. Idan sunga munyi wani abu ba daidai ba zasu iya kiranmu su mana gyara.. Idan ma ta kama su tsawatar mana duk zasuyi.. Haka ne.” Nan ma jinjina kai Haidar yai. Alhaji Gimba yace “Ma sha Allah. wato Haidar, mahaifinka ya sanar Dani abinda ke faruwa, ba wai dan ya bud’e min sirrinka ba sai dan so da yake a samo maslaha.” Haidar yai shiru yana sauraronsa. Alhaji Gimba yaci gaba “Wato shi Aure wani abu ne da yakeda mahimmanci Haidar a rayuwar Al’umma gaba d’aya. Dalilai da dama suna sawa ayi aure haka dalilai da dama Suna sawa Aure ya mutu Wanda ba’a so. Daga cikin dalilan mun sani Aure ibadah ne bautan Allah ne kuma d’abbaka sunnnar Ma’aiki (SAW) sann duk Wanda ya d’auki aure matsayin ibada bautan Allah zai samu dacewa da tsira harma da farin ciki a cikinta. Hakan nan Aure yana sa kamewa daga fad’awa tarkon zinace zinace. Kaman yanda yazo a hadisin Abdullahi Dan Umar Allah ya kara yarda a garesu. Yanda Manzo (SAW) yace yaku taron samari ga Wanda ya samu iko daga cikinku yayi aure. Shi aure yana tsare gani sann yana kame al’aura. Har yake cewa ga Wanda bai samu hali ba toh yayi azumi. Shi azumi garkuwa ne.. Sann dalili na gaba samun nagartacciyar Al’umma. Ta hanyar Aure ake haihuwa a samu Al’umma nagartacciya. Bazamu fad’ad’a ba amma kaga ko wad’ann muka d’auka Sun ishemu dalili. Haka zalika shi Auren nan ba’a barmu kara zube ba saida aka koyar damu yanda zamu zauna cikinta ta fuskar shari’a da koyarwar addini. Ta yanda d’aya bazai zalunci d’aya ba a cikin zamantakewar. Domin kuwa addinin musulunci addini ne mai kyau da tsari da kuma adalci. Haka zalika idan rabuwar Aure ta kama dole, Wanda ba’a fata toh nan ma saida aka koyar damu yanda zamu rabu bisa kyautatawa da mutuntawa.” Ya dan gyara zamansa kafin yaci gaba “In Islam, it is believed that married life should be filled with mercy, compassion and tranquility. Sann Zaman aure zo mu zauna ne zo mu sab’a.. Ko harshe da hakori watarana ana samun mishkila.. Toh idan an samu sab’ani ba haka kawai ake saki ba sabida girman al’amarin.. Akwai hikima da musulunci ya saka saki hannun namiji. Dan idan mace ne zakuyi fad’a sau d’aya amma tana iya cewa ka saketa sau dubu. Kaga tunaninta da naka ba d’aya bane.. Hangen nesanka da nata ba d’aya bane.. Kai ko a halitta ta fuskar k’iran jiki kaida ita ba d’aya bane. Ita haka Allah ya halicceta mai rauni kai kuma mai jurewa. So idan al’amara irin wann suka taso endurance dinka da tolerance d’inka ya kamata yafi nata. Idan an samu rashin fahimta ko matsala a zamantakewa a tsakanin. Kuyi k’ok’arin samo maslaha tsakaninku ba sai third party ya shigo ba, idan kukai trying a tsakaninku still ba’a samu maslaha ba sai a saka manya ciki dan amfani manyan kenan. Bama a fata har takaiga zuwa gaban manya toh amma idan ya zama ba mafita sai a mik’a matsalar gaban magabata. Idan ya gagara a mik’a matsalar gaban jagororin Al’umma wato malamai. Idan shima baiyi working ba toh fah ka sani duk yanda ake son wani Auren rabuwan shi yafi alkhairi. Sann idan Allah ya k’addari ba sauran zama dole za’a rabu.. Toh sai a rabu cikin mutuntawa da kyautatawa..” Ya dan gyara zamansa “Shin ya ma ake sakin.? Saki yana nufin furtawa. Intention na saki ba saki bane. Idan kace ma matarka zan sakeki, wann ba saki bane.. I intend to divorce you, this is not a divorce. I think we should get separated, this is not a divorce either.. It has to be a statement or a verb. In the sense that Na sakeki, .. Or you are divorced. Shikenan ta saku. Shi da yayi sakin yanada chances na kome guda biyu, idan yayi na uku babu kome Har sai ta auri wani mijin bashi ba. Idan miji ya saki matarsa sau d’aya, meaning one down two to go. Sann Anfi so matar ta zauna gidan mijin tayi iddarta. Akwai hikima da musulunci yace ayi hakan. Dan a wann zaman zai iya maida matarsa kuma ta maidu ba sai anje ana biko da sauransu ba. Menene Iddah.? Shine waiting period after the divorce. Ga macen da batada juna biyu iddah period dinta shine 3 monthly cycles.. If she’s too old like If she’s in her menopause ma’ana wacce ta daina Al’ada ko kuma yarinya k’arama wacce bata fara ba their iddah period is 3 months.. Idan mata mai juna biyu ce kuma iddarta shine ta haihu.. And this may be 2 months, 3months, 7months.. Depending on her pregnancy.” Sai ya dan gyara zamansa “Now, it is prohibited for a man to divorce his wife a lokacin da take al’ada, or when she’s in the state of purity yet he had intercourse with her in that state of purity. An hana saki a wad’an nan lokutan. Wann shine saki na bidi’a. Innovated divorce. Mafi rinjaye Sun tafi akan it is sinful but valid. Ma’ana kuskure ne hakan amma matar ta saku. Idan mutum zai saki matarsa. God forbid, yet they had intimacy few days, few weeks ago. Musulunci yace he waits until she gets her menses. Idan tai tsarki ba’a samu intimacy ba sann sai ya saketa. Kaga zai wahala ma yayi sakin idan har zai jira wann lokacin. Amma da yawa hakan baya faruwa sabida mafiya yawan sake sake cikin b’acin rai akeyi. Akwai hikima cikin duk abinda musulunci yayi umarni ko yayi hani..” Yaci gaba da bayani kan hukunce hukunce da hakkoki Haidar na saurarensa.. Har ya fara tuna nashi sakin da matarsa Wanda sun samu intimacy kafin ya saketa. Ya lumshe idonsa kad’an yana karanto istigfari. Har saida ya sinkayo muryar Alhaji Gimba yana tambayarsa “Be open with me Haidar. Shin kana son matarka.?” Haidar ya jinjina masa kai “I love her with my life Uncle… But..” “There’s no but if you truly love her..” Jiki a sanyaye Haidar ya girgiza Kai yace “I choose to be the problem Uncle.. I choose to carry the burden..” Ya dan girgiza kai a hankali “Mahaifiyata ta wahala sosai.. Tanada kurakurenta, but.. I can’t let her carry it all alone.. Bazan iya barinta ita kad’ai ta fuskanci matsalar ba sabida ita din ta fahimci kuskuren ta kuma ta tuba.” Yaci gaba da jinjina Kai “I choose to be her shield in this.. Idan hakan na nufin sitirta kuskurenta, even if it would destroy me.!” Ya k’arashe cikin yanayi mai ban tausayi. Alhaji Gimba ya dubesa cikeda tausayawa. Yanada masaniya gameda family issue da ahalin Aminin nasa suka fuskanta. Yau Haidar ne yake sacrificing farin cikinsa sabida mahaifyarsa lallai rayuwa ta sauya kuma Haidar ya cika D’an da za’ayi alfahari dashi. Sai yaci gaba da jinjina Kai a hankali murmushin saman fuskarsa yake duban Haidar d’in. “Idan na fahimceka Haidar, kayi komai ne sabida mahaifiyarka. Kuma duk d’a nagari irin haka zaiyi.. Ba ina nufin sakin ba.” Ya d’anyi gyaran murya “Ka zab’i ka sadaukar da farin cikinka sabida mahaifyarka.. Amma rabuwa da iyalinka bazai zama mafita ba. Bansan menene wann kuskure na mahaifyarka da Kake son sitirtawa ba, ka sani duk Wanda Ya rufa asirin wani musulmi Allah zai rufa nasa ranar gobe balle Mahaifiya. Saidai akwai hanyoyi da dama da ake bi dan shawo kan matsala. You can’t let yourself be destroyed in the process.. Because Destruction is not the solution and it will never be. Mahaifyarka sai tafi shiga tashin hankalin idan har hakan yai destroying d’inka. You are a man, and you supposed to act like one.. Be brave enough to face your problems..Kar ka guje ma matsalolinka dan idan ka guje masu zasu bibiyeka ne har k’arshen rayuwarka.” Ya dan numfasa “I’ll ask you this question again, do you love your wife.?” Dubansa kurum Haidar keyi, ya shiga jinjina Kai ba tareda ya iya furta koda kalma ba. Alhaji Gimba ya jinjina Kai “Then what are you waiting for, go and reconcile with your wife. Kaje ka dawo da iyalinka.” Sai Haidar ya d’anyi shiru yana tunanin irin k’iyayyar da ya hango a kwayar idanun Ummul. Ya sani a halin yanzu Babu abinda tafi tsana Watak’ila sama dashi. Jin yayi shiru yasa Alhaji Gimba murmusawa yace “Bansan Aliyu da rashin k’warin gwiwa ba dukda ance rauni na cikin soyayya.” Ya k’arashe cikeda barkwanci. Sai Haidar ya d’an k’ak’aro murmushi yana jinjina Kansa “In sha Allah Uncle, zan dawo da ita. Kuma bazan tab’a sarewa ba. Na gode k’warai.. Allah ya saka da alkhairi ya k’ara girma.” Alhaji Gimba ya murmusa “Yanzu naji Zaki na magana. Allah ya maka albarka ya mana jagora.” Haidar ya amsa da Ameen had’ida k’ara godiya ma Alhaji Gimba. Alhaji Gimba ya mik’e suka jera zuwa motan Haidar a tare tamkar yana ma Haidar d’in rakiya. Haidar bai tab’a tsammanin rana irin wann zata zo ba. Mutumin da a baya yake masa kallon tarayyarsa da mahaifinsa babu wani alfanu. Mutumin da yai masa mummunar fahimta a baya. Sai gashi yau wann mutumin ya zamto tamkar mutumin da ya jefa masa igiya cikin rijiya mai duhuwa yace ya kama ya fito. Tabbas zaka k’i wani abu wann abun alkhairi ne a gareka, zaka so wani abu wann abun sharri ne a gareka. Fatan alkhairi Alhaji Gimba ya kuma yi ma Haidar d’in. Ya kuma ce a duk lokacin da wani abu ya shige masa duhu ko yake nema shawari his door is always open yazo ya samesa matsayin Uba a wajensa. Godiya Haidar ya kuma masa cikeda girmamawa kafin ya wuce. Tinda ya fito daga gidan Alhaji Gimba yake ji kaman ya k’ara masa k’warin gwiwa ne.. Yayi alk’awarin zai jira Ummul Har tayi healing koda zai d’aukesa tsawon shekaru ne.. Amma yau da Alhaji Gimba ya nusar dashi zai iya wasa da damarsa sai yaji bazai iya jira ba. Zai tafi yayi yak’in dawo da Ummul cikin rayuwarsa da taimakon Allah. Washe gari sassafe yai shiri da zummar d’aukan hanya garin Kano. Ya shigo ya gaida iyayensa sann ya k’arada “Daddy, Mommy.. Ina so zan tafi garin Kano yanzu.. Zanje na dawo da Khairy.” Farin cikin Mommy ya gaza b’uya. Duk a ‘yan kwanakin ta kula ko zancen Haidar baiso a masa sai gashi yau yace zaije ya dawo da matarsa. Suka saka masa albarka tareda fatan alkhairi. Daddy ya dakatar dashi. Mommy ta dubesa da mamaki. Sai Daddy yace da Haidar ya jirasa a mota yana nan fitowa. Mommy tace “Engr. Ya naga ka tsayar dashi..?” Ya murmus “With your permission Rankidad’e, I’m going with him.. I want to be a father to my son..” Har k’walla saida suka ciko idon Mommy. Ta tuna farkon Auren Haidar da Ummul d’in Daddy cewa yai ba hannunsa ba ruwansa tayi yanda take so da rayuwar D’anta. Yau sai gashi ya saka kansa tsamo tsamo a al’amarin Haidar d’in. Ta murmusa tace “Toh kodai nima nayo muku rakiyar ne.?” Daddy ya girgiza Kai yana d’aura wristwatch d’insa “A’a wann tafiya ce tamu ta maza. Daga baya sai kiyi naki.” Murmushi kawai Mommy tai ta musu fatan sauk’a lafiya baida dacewa. ** Koda suka isa garin Kano sun samu an kaisu Har k’ofar gidan Malam Isubu mai Manja kaman yanda aka fi saninsa. A farfajiyan gidan aka saka masu tabarma daga nan k’ofan su Ummul d’in dan Tani bata bari ‘yanuwan Mahaifin Ummul da suke uba d’aya Wanda suka amshe kudi hannun Asshe farkon Auren Ummul d’in sun shiga cikin maganar ba, sanin abinda ka iya zuwa yazo. Dukda maganan na maza ne amma kamawa take Shiyasa tazo wajen tinda tasan da cewa akan kudi ba abinda su d’in bazasuyi ba. Sann basu san da mutuwar Auren Ummul d’in ba. Bayan sun gaisa Nan take sanar dasu Daddy har kawo wann ranan basu saka Ummulkhairi a idonsu ba. Sun bincika duk yanda ya kamata amma babu labarinta. Haidar ya dubeta cikin shock “Khairy bata nan..? Toh ina take.?” Tani ta sauk’e ajiyan zuciya “Duk yanda ya kamata mu bincika gidan ‘yanuwa da zuri’a mun bincika amma Babu labarinta. Tin a lokacin

Chapter 46 of 64