waiwayowa gida ba aure ma can yayi. Ya auri baturiya ‘yar k’asar Poland. Suna can da yaransu har biyu saidai shi Alhaji Gimban yaje Ya duba su idan yaji kewa amma sam basu zuwa Nigeria Shiyasa a lokacin da Daddy yake nuna halin ko inkula akan Haidar Alhaji Gimba yake ganin kuskuren abokin nasa. Mu zamto masu godiya ga d’imbin rahamar Ubangijinmu garemu domin abinda kake rainawa wani shi kawai yake fata da burin Allah Ya basa. Bamu gane mahimmancin wani ni’ima da Allah yai mana sai mun rasa wann abin. Allah kasa mu zamto bayinka masu godiya a gareka da kuma karban k’addara a duk yanda tazo mana.
**
Khulsum ta rok’i alfarmar iyayenta da su bari ta tafi can Jigawa wajen Dije. Koda aka fara bikin ma Abba da Umma basu nemi ta dawo ba sai Inna Dije Tai mata nata bikin a can. Aure kawai aka d’aura a Kano amma tana can wajen Inna Dije. Sosai Inna Dije taji dadin hakan Har saida tai hawaye sabida farin ciki. Hak’ik’a Khulsum ta girmamata ta bata darajan uwa taji dadin wann karramawa sosai. Taita godiya ma abba da Umma tana hawaye. Umma tace ta daina godiya Hak’ik’a ita d’in ta zamto uwa ga Khulsum a lokacin da ta gaza zama uwa gareta. Abin farin cikin shine Allah Ya dad’a had’e kan ahalinsu kuma ya cikasu da alkhairi.
Umma da Mama Tani suka had’e kawunansu suna kukan farin ciki. Yau yaransu gaba d’aya sunyi aure. A baya lokacin da sukaci musu buri na ganin sunyi ko wani irin aure ko ta halin k’ak’a sai Allah Ya barsu da wayonsu. Yanzu da suka fawwala masa al’amarinsu sai Ya zamto majib’icin al’amarinsu. Ya kawo ma ‘ya’yansu mazajen aure na gari a lokaci guda. Lallai Ubangiji Ya cika abin godiya.
An sha biki lafiya a lokacin cikin Ummul Ya tsufa Baba Ali nada shekara d’aya da wata uku a duniya.
Tai zaune a playing room d’in Baba Ali tana duban yanda Haidar Ya baje ma yaron kayan wasa dangin building block da motoci irin na construction.. Harda helmet ya d’aura masa yana fad’in “Da kyau my little Engr let’s build a house for Maama..”
Ummul ta kuma dubansu tana sakin sassanyar murmushi.
Wayan Haidar ne ta soma ruri Ya daga yana amsawa. Da alama wayar nasa aiko ya Shafa. Tinda Ummul taga haka sai ta d’anyi kicin kicin da fuska dan tasan bazai wuce kira na gaggawa Ya samu daga Lagos ba sabida taji sanda ya ida wayan Ya kira Sadis yace ya masa shatan PJ a ranan zai tafi Lagos d’in bazai jira jirgin safe ba.
Ya k’araso gabanta ya dan langab’e kai yana duban yanda ta cika Tai fam. Ya duka gabanta hadida d’aura hannayensa saman laps dinta “Maman Biyu.. What’s wrong.. Why the long face.?”
Ya dan hararesa kad’an bakinta a ture, kaman zatai kuka tace “Nasan tafiya zaka kumayi.. Bayan duka duka yaushe kazo.”
Haidar ya dan murmusa yana mai kamo yatsun hannayenta cikin nasa “Duk sabida haka ake fushi ana bata kwalliyan da aka mun.?”
Sai Ya bata dariya ta dan murmusa tana mai kuma turo baki “Amma ai baka jima da zuwa ba.. Kuma kace wann karon zaka jima kafin ka koma.”
Jinjina mata kai yai “Kiyi hak’uri.. Dole ce tasa zanje suna buk’atana a can. But I’ll only be there for a while.. Bazan jima ba In sha Allah. Da zaran na gama abinda yakaini zaki ganni.. Tashi muje ki tayani i shirya jaka.” Ya k’arashe yana mai taimaka mata ta mik’e da kyar. K’arasawa yai Ya d’auki Baba Ali suka nufi dakinsa gaba d’aya dan shirya jaka.
Ummul tana fiddo masa kayan yana shiryasu a suitcase ta d’an dubesa. Kaman bazatai magana ba sai kuma tace “Dazu Munyi magana da Anisa a waya take ce mun basu ganka ba har yanzu.. Yau kuma satinsu guda kenan da dawowa daga Germany.. Kowa yaje Ya duba Hisham saura kai..”
Haidar Ya katseta “K’arata ta kawo miki banje na duba mijinta ba..?”
Saurin girgiza kai Ummul Tai “A’a ba haka bane” Ta bar abinda take ta matso yanda yake “Dan Allah ka yafe ma D’anuwanka.”
Ya dubeta kad’an sai Ya girgiza kai “Na yafe masa tuntuni.”
Ta jinjina kai “Kai kokari ka mance komai ku gyara alak’arku.. Haka ne kawai zai tabbatar da yafiyarka a gareshi.. Ina so ka min wann alfarmar mijina, kaje ka duba D’anuwanka kafin ka wuce Lagos.. Please mijina.!” Ta k’arashe cikin sigan lallashi tana kuma kamo hannayensa.
Haidar Ya dan furzar da huci kad’an “Fine, zan biya na duba shi.. Yayi miki..?”
Ta murmusa cikeda jin dadi tana jinjina kai “Yayi min.. Na gode sosai.”
Tsareta yai da ido. Sai Ya tallafo fuskarta da tafukan hannayensa.. Ya kannare ido sosai yana dubanta “What have you done to me Khairy..? You convince me on most impossible things..”
Ta murmusa tana kashesa da wani irin kallo mai kashe masa jiki. Ta sakala hannayenta saman kafad’unsa, ta langab’e kai “You love me so much that you can’t say no to me.” Tai maganar tana kashe masa ido.. Sai Ya janyota jikinsa Ya lumshe ido “Of course I do.. I do love you..!” K’arshe duk’awa yai saitin zungureren cikinta ya soma zance da cikin “Hey twins, Papa is going on a short trip.. While I’m away, be good kids and don’t give too much stress to Maama… I love you.” Ya k’arashe yana sunbatan cikin. Ummul kaw sai dariya take dan so tari idan Haidar na zance da cikin jikinta sosai abin ke bata dariya. Sai ka rantse da wani cikakken mutum yake magana. Ba wai taga banbancin rainon cikinta na farko lokacin bata tareda Haidar da wann da take tare dashi. Taga gata da soyayya irin wana batai zaton na faruwa da gaske ba. Ita kam ba abinda zatace ma Ubangijinta sai godiya. Fad’insa ne tsanani yana tareda sauk’i sann duk Wanda ya dogara gareshi toh ya isar masa. Tafiyan Haidar da kwanakin da basu shige biyu ba ta fara labour. Ai kaw koda aka tafi asibiti cikin ikon Allah bata d’auki dogon lokaci tana labour din ba ta haifo d’iyarta ma sha Allah. Ba’a kuma jimawa ba namiji Ya biyo baya. Ma sha Allah tabarakallah. Allah mai kyauta da k’ari, buwayi gagara misali.
Zo kaga farin ciki wajen d’aukacin ahalin. Abin baa cewa komai sai son Barka. Shi kansa Uban gayyan wato Haidar kai kace ba’a tab’a masa haihuwa bane. Kowa na farin ciki da son Barka. Wann karon Umma da kanta saida ta wanko k’afa tazo Abuja. Tsaban farin cikin da Abba ya shiga ma tuni yace Umma da Mama Tani duk su shirya su tafi. Yara biyu lokaci guda ba k’aramin kyauta bane. Taron suna yaga jama’a . Harta da Inna Dije saida tazo.. Su Badia da Azeema dake a nan Abuja gidajen su yake tuni akai komai dasu. Khulsum ce dai aka sha fama da Hilal dan ciki gareta kuma karami irin mai saka laulayin nan. Da kyar dai saida Aunty Asshe ta saka baki Ya amince suka biyo jirgi suka taho gaba d’aya. Gaba d’aya dangi duk sun hallara. Abin fah ba’a cewa komai sai son barka.
Ranan suna da safe Hajja ta had’e kan ‘Yanmatan gaba d’aya dan d’abbaka wani al’ada na ahalinsu. ‘Yanmatan a gida da sirakai sukan hadu su girka ma mai jego abinci wana zata ci.
Aka had’a Anisa da yanke Albasa. Idon Anisa sai hawaye yake sai mita take tana fad’in ita bata saba da wann aikin wahalan ba. Fad’i take “Wayyo idona yaji.. I can’t open my eyes.. Wai dole dai sai mu zamuyi aikin nan gida cikeda ma’aikata.”
Azeema ta harareta “Ni fah gaskiya duk kin cika mana kunne. Masu abin mita ma basuyi mita ba sai ke.?” Tai maganar tana nuni da Khulsum da Badia dan dukansu biyu juna garesu.
Anisa ta galla mata harara da idonta da yai jazir Ya jik’e da hawaye “Ina ruwanki dake nake.? Ai duk laifinki ne. Sabida kinajin haushina kika sa aka hadani da yanka albasa. Toh ai sai kizo ki karisa.. I’m not doing it again..!” Ta k’arashe tana aje wukar had’ida goge ido.
Azeema ta tabe baki “Toh ke me zaki iya ma idan ba yanka albasa ba. Ba iya girkin kikayi ba balle ace kiyi. Dan haka dole ki yanka albasa.”
Badia ta lallashi Anisa da fad’in kar ta biye ma Azeema k’ila itama fitinar masu k’aramin ciki take bata sani ba.
Azeema ta zaro ido tana fad’in ita batada komai.
Aunty Asshe ce ta lek’o tana musu sannu da aiki. Ta dubi Khulsum tace kar tayi stressing kanta musamman da yake cikin jikinta na sakata laulayi sosai.
Kawai sai Anisa ta fashe da kuka tana fad’in “Wayyo Ammi idona.. Wayyo yaji..”
Aunty Asshe ta galla mata harara “Meye haka ke kuma.. banson sakarcin banza.”
Anisa ta kuma turo baki tana fad’in “Ammi wllhi bakiji ba kaman idona zasu fice.”
“Toh su fice din mana. Haka dai zakiyi.”
Ta kuma fashewa da kuka tana fad’in “Why are we torturing ourselves.. Is there not a machine for doing this..?”
Aunty Asshe tace “Machine din kenan hannunki..” Ta dubi su Azeema tace su karo mata lawashin duk ta yanka. Kuma Mijinta na ida jin k’arfi zasu tattara su tafi gidansu kuma zata hana ya d’aukar mata wata mai aiki.
Anisa tace “Ammi kawai kice baki sona.. Dama Hilal kikafi so gashi kin hana matarsa aiki.”
Aunty Asshe tace eh d’in ba’a sonta d’in. Ta dubi Khulsum tace maza ta fito kitchen din haka Anisa ta had’e aikin Khulsum d’in da nata duk tayi.
Khulsum tana fad’in zata iya Azeema na turota waje tana fad’in “Wllhi Ammi dazu ma bakiga ba yanda take tangad’i kaman zata fad’i k’asa saida na tarota.”
Aiko nan Aunty Asshe tace maza maza ta fito haka ta huta.
Anisa sai ta kuma fashewa da kuka tana ma Azeema Allah ya isa data sa aka had’ata da wahala. Dan ko bayan aurensu da Hisham a SouthAfrica ba girki take ba. Sann da suka tafi Germany jinya ma ba girki take ba. Yanzu da suka dawo ma gidan Daddy suke.
Azeema da baki baya shiru ta galla mata harara ta karo tulin albasa ta dangwala gabanta tana fad’in “Allah dai yasa surkarki ce ta sakamu. Kuma baa isa ace baza’a ayi aikin sirka ba.” Ta kekace da dariya tana fad’in “Maza ayi biyayya aci gaba da yanka albasa aci gaba da murza ido aci gaba da hawaye.” Gaba d’aya saida ta basu dariya. Kawai sai Anisa ma ta fashe da dariyar ga ido jazir fuska sharkaf da hawaye.
Yara sunci sunan Mommy da Abba. Ta ko wani b’angare farin ciki ke circulating. Da yamma aka sha walima na alfarma a nan gidan Daddy. Bak’i maza da mata. B’angaren mata daban na maza daban. Musamman aka d’auko babban malami yai wa’azi sosai kan mahimmanci tarbiya da kula da yara. ‘Ya’ya rahama ne kuma kyauta ce da babu mai yinta sai Allah. Sann duk Wanda aka danka masa kiwon d’a Tabbas amana aka dank’a masa Wanda Allah zai tsayar dashi Ya tambayesa gameda wann amana da aka basa. Yaya ya tafiyar da amanar.? Ya sauk’e nauyi da hakkoki da suke kansa.? Mu sani kafin mu samu nagartattun ‘ya’ya Tabbas sai mun zama iyaye masu nagarta kuma ababen koyi. K’addarar mu tana tafiya da jarabawar mu. A lokacin da muka kamanta namu k’ok’arin muka kuma had’a da neman taimakon Allah sai kuma mukaci karo da jarabawa, toh fah mu sani wasu mutanen Allah yakan k’addarosu cikin rayuwarmu ne matsayin jarabawa. Ya Allah kasa mu zama ‘ya’ya masu biyayya ga iyayenmu sann ka sanya mu cikin iyaye masu nagarta. Ka azurta Al’umman Mamzonka (SAW) da samun ‘ya’ya na gari wad’anda zasu zamto sanyin idaniya kuma sadak’atuljariya a garemu baki d’aya. Allah ka iyar mana abinda mu bamu iyawa. Ya Allah duk wata uwa da take nema ma ‘ya’yanta shiriya Allah ka shirya mata su. Masu neman haihuwa Allah ka azurtasu da salihan ‘ya’ya wad’anda zasuyi alfahari dasu dama Al’umma baki d’aya. Ameen thumma Ameen.!
**
Haihuwan ‘yan biyu yazo ma Haidar da tarin nasarori na rayuwa. A lokacin Daddy yai stepping down daga matsayinsa na kasancewa shugaban kampani kuma mai jagoranci kampanin. Yanda Ya d’aura D’ansa Aliyu ya zamto shugaba kuma mai jagorancin Kampanin. Sann Ya bar zab’i hannun Haidar gameda aikin Hisham under his company. Idan har Haidar ya amince zai iya barin Hisham yai aiki a company, idan kuma bai amince ba Hisham bazai koma company ba. A Cewar Daddy bayan yafe masa da yai wann shine hukuncinsa.
Gagarumin taro aka gudanar yanda Haidar ya karbi lambobin yabo da karramawa dama. Ciki harda aikin da ya gudanar na bridge project da ya jagoranta a lokacin da yai yarjejeniyar AUREN WATA UKU da Ummul. Wann gadar ta zamto kaman itace mafarin komai. Sanda ya fito domin bada speech d’insa bai k’asa a gwiwa ba har saida ya fad’i mahimmancin wann project d’in a garesa da yanda Ya zamto silan canza direction na rayuwarsa harma da Company’s future. Wann project d’in zai tabbata na musamman cikin jerin ayyukan da yayi.
Daddy ya k’araso sukai masabaha bayan zauren taron ya kacame da tafi da fatan alkhairi.
Murmushi saman fuskar Daddy yake furta “Congratulations Son, ina tayaka murnan d’imbin nasarori da ka samu. Ka cancanci fin haka. Nasan bazanyi danasanin dank’a maka ragamar company ba. Inada yak’inin zaka kai Company zuwa matsayi mai girma cikin yardar Ubangiji.” Ya kuma duban Haidar sosai yana jin k’walla na ciko idonsa. Sai ya kuma tuno lokutan baya yanda yaita nuna gazawar Haidar d’in da kasawarsa. Muryar Daddy yaci gaba da rawa sanda yake furta “Today I want to tell you this Son. I am so proud of you.. Ina alfaharin zama mahaifinka Aliyu..! Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.
Haidar ma murmushin yake sai yai hugging Daddy “Thank you Daddy.. Thank you for trusting and believing in me. In sha Allah bazan baka kunya ba.”
Daga nan manema labarai sukaci gaba da hasko Haidar as the New President of Maitama Builders suna neman ji ta bakinsa.
Daga bayansa Ya sinkayo murya na fad’in “Congratulations brother..! Ka cancanci wann matsayin.!”
Juyowar da zai sukai ido hud’u da Hisham dake dogara sanda alamun ya fara takawa da sanda bayan da Ya dawo jinya daga Germany.
Murmushi Haidar Ya saki sai ya mik’a Hisham hannu suka gaisa “Thank you… Brother.!” Haidar yace hannunsa cikin na Hisham. Hawayen farin ciki suka gangaro ma Hisham dan wann shine rana na farko da Haidar Ya kirasa da D’anuwa Tun bayan da suka san cewa sud’in ‘yanuwan juna ne.
Hisham yaci gaba da murmushi yana jinina kai “Ina rok’on Allah yai rik’o da hannayenka sann yai maka jagoranci… D’anuwana.”
Haidar ya kuma murmusawa had’ida jinjina kai “Na gode D’anuwa.. I hope very soon zaka samu lafiya sann ka dawo bakin aiki. Muyi aiki hand in hand.. like before.. cikin aminci da yarda.”
Hisham Ya d’ago da mamaki yana dubansa “Does that mean zaka barni naci gaba da aiki k’ark’ashin ka, Mr President.?”
Murmushi Haidar Ya kuma “It’s your company Hisham. Kasancewana shugaba bazai canza matsayinka ba matuk’a zakayi aiki bisa gaskiya da amana.”
Hisham sai Ya rungume Haidar yana hawaye yake furta “Thank you brother.. Thank you for accepting me back in the company. Na gode maka matuk’a.”
Haidar ya rik’e hannayen Hisham cikin nasa “Together we will take the company to greater heights… Together we will make Daddy proud.!”
Hisham yaci gaba da jinjina Kai murmushi saman fuskarsa “Together brother.!” Sai suka rungume juna.
Daddy dake gefe yana kallonsu sai Ya goge hawayen da suka gangaro masa kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Who would’ve thought wad’ann yaran nasa guda biyu zasu sake zama k’ark’ashin Inuwa guda.? Godiya ta tabbata ga mahaliccinsa da Ya cika ahalinsa da alkhairi bayan sun fuskanci tarin k’alubali da jarabawa. Tabbas when there is life there is hope. Mai rai kada ya zamto mai d’ebe tsammani ga rahamar Ubangijinsa. Domin shi d’in shine mai sauya al’amara a lokacin da yaso.
**
Tsaye yake gaban makeken hoton bridge d’in Wanda akayisa cikeda kwarewa da kuma fasaha. Da yawan mutane suna masa lak’abi da ‘heart shaped bridge’ sabida unique shape da wann gadar ke dashi kaman shape din heart. A zuciyarsa yake furta ‘It started with this da alk’awarin cikin watanni uku da alk’awarin AUREN WATA UKU. She came into his life and everything changed. Ya gina bridge d’in with so much love. Kaman yanda wann bridge d’in Tai linking Manyan hanyoyi guda biyu kaman haka Tai linking zukatansu. And that’s why he named the bridge in his heart ‘Bridge of Love.’ Ya waigo yana duban Baba Ali dake guje guje tsakanin ‘yanuwansa twins dake zaune cikin toys dinsu suna wasa. Ummul ce ta k’araso tana k’ok’arin hana Baba Ali guje guje tsakanin yaran gudun kar ya fad’i kansu dan already yaja k’afan wann yaja kunnen wancan.
Muryar Haidar ta sinkayo yana fadin “Let him be love… So yake su tashi suyi wasan tare.”
Ta dan dubesa “Amma idan Ya fad’i kansu fah. Gaba d’aya sakalta yaron nan kake.”
Murmushi Haidar yai yana janyota jikinsa “What do you expect.? He’s my namesake, after all.”
Ta dan dubesa “kuma sai na bari yaci min zalin iyaye..? Ina nufin yarana manyan sunane dasu. Abba ne da Mommy guda a wajen.”
Ya jinjina Kai kad’an “Haka kuma.. Toh amma kinga shi suna biyu yaci. Shifa takwaran Daddy ne kuma takwaran Babansu..”
Ta d’an tsaresa da ido “Wait, what are you implying here.? So kake kace ni kad’ai ce bare a tsakani.?”
D’an tabe baki Haidar yai yana jinjina kai “Kind of..” Sai ya rad’a mata “If you don’t want us to gang up on you kawai Ki haifo naki takwarar..”
Zaro ido waje Tai tana turasa “No way.. Nak’i takwarar..” ta k’arashe tana jifa masa teddy. Su duka biyun dariya suke. A haka Baba Ali ya k’araso da gudu ya haye wuyan Haidar. Ai kuwa sai Ya shiga cillasa yana masa kalan wasan da shi kad’ai yake masa. Yaron Ya shiga k’ek’yata dariya yayinda Haidar Ya kwanta da baya Ya d’aura Baba Ali saman k’afansa ya janyo twins zuwa cikinsa.
Ummul Tai zaune tana dubansu zuciyarta fari tas. A hankali ta furta “Alhamdulillah.!”
*TAMMAT BI HAMDILLAH.!*
*A nan na kawo k’arshen wann littafi mai take AUREN WATA UKU. Fad’akarwar dake ciki ina rok’on Allah Ya had’amu daku baki d’aya wajen lada. Kurakuren dake ciki Ubangiji Ya yafe mana.*
*Masoyan Sameena masu bibiyan labarnta, duk yanda kuke ku sani Sameena tana sonku kuma tana ji daku. SAIDAKU masoyan Sameena. Ubangiji ya bar k’auna. Taku Har kullum..*
SameenaAleeyou📚
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 64 Chapter of 64