Share this page
Ki kasheni idan kina so.. Ni na miki laifi.. But please sapere my child..! Let the child live please.. Kiji tausayin jaririn dake ciki Wanda baida hakki..!” Wani kafurin dariya Dareen ta kece dashi tana duban Hisham “Unbelievable..! Ban iso kanka ba cikakken D’aniska.! Ni zaka duba kace I should spare your child.?! Did you spare my own child Hisham..?!” Ta kuma kecewa da dariya kafin taci gaba “Wai ni kake ce na tausaya ma jaririn cikinka da baida hakki..? Ka mance lokacin da kai da wann k’aramar doluwar kuka murk’ushe nawa jaririn da tayun mota.?! Ka gaya min Hisham nawa jaririn shi hakkin uban wa yaci cikinku.?!” Taci gaba da jinjina Kai tana dubansa “Gwara ma wann shegen dake cikinta iyayensa tsinannu ne azzalumai Watak’ila zunubinku Ya shafe shi.. Amma ni nawa jaririn fah.? Cikin innocent Haidar ne Hisham..! Haidar shine uban jariri na..! mutumin da ka tarwatsa masa rayuwa kai destroying d’insa from the root..! Uban cikina is innocent..! shi aka zalunta cikin gaba d’aya labarin.!” Taci gaba da jinjin kai tana duban Hisham “Kamar yanda zan k’araci rayuwata saman wheelchair sabida murkushe mun k’afafu da kukai da mota, kaman haka zan tabbata ka zama paralyzed for the rest of your miserable life Hisham..! Kaman yanda kuka kashe D’ana da Haidar yana watanni uku kacal a ciki..! Kaman haka zan kashe wann cikin naku mai watanni uku a ciki..! Haidar zai k’araso nan Hisham.. Zaka bud’e baki ka sanar dashi komai..! Ina nufin komai..! Duk abubuwan da kai masa a rayuwa..! Duk shiga rayuwarsa da kai..! Duk tarwatsa masa rayuwa da kai.. Zaka bud’e baki ka karanto zunubanka gaban Haidar..! Ko d’aya bazaka bari ba sai ka fad’a taryan taryan..!” Ta k’arashe tana mai kiran d’aya gardin tace Ya sake mana ma Hisham igiyan shocking. ** Cikin zuban hawaye take duban Hajja, da kyar take furta “Dan Allah Hajja kice mun bai kai kansa ma ‘Yantadda kaman yanda suka nema ba..” Ta rintse idonta hawaye na gangaro mata “Yau Aurenmu yake cika watanni uku cif a karo na biyu.. Hajja dan Allah kice mun zai dawo gareni kice mun ba AUREN WATA UKU muka sakeyi ba..! Ya mun alk’awari wann karon Aure mukai na Har abada.. Dan Allah kice zai dawo gareni.. Idan na rasashi nima mutuwa zanyi Hajja..!” Ta k’arashe tana kame k’irjinta tana kuma rintse idonta dake ci gaba da zuban hawaye.! Hajja Tai k’ok’arin maida nata hawayen tana jijjiga Ummul take fad’in “Ki daina maganganu irin haka Ummul. Ba abinda zai samu Haidar.. Ba abinda zai samesu gaba d’aya da izinin Allah. Haidar zai dawo gareki Babu zancen AUREN WATA UKU tsakaninku.. Zakuyi rayuwa mai tsawo tare in sha Allah kinji koh.. Kici gaba da ambaton Allah kinji koh. Da sannu zai kawo mana sauki cikin al’amarin.!” Ta k’arashe hawayen da take ta k’ok’arin dannewa na zubo mata itama. Mommy da Aunty Asshe ma an rasa mai bama wani baki Hilal na tsakiyansu Ya rungumesu dukansu biyu shima hawayen yake Ya kasa jurewa. Aunty Asshe fad’i take “Ina yawan kiran Anisa shashasha kun sani..? Amma lokacin da akai Aurenta sanda zasu tafi SouthAfrica.. Kun san mai tace min da muka keb’e a d’aki.? Ce min Tai Ammi ki yafe min.. Nasan na sakaki bak’in ciki da dama because of my stupidity..!” Asshe yaci gaba da hawaye tana jinjina kai “Sai tace min I’ll make it up to you Ammi..! You will be proud of me..! Ammi Ina sonki..! Kice ma Abba ya yafe min.. Kuma kice ma Hilal ina son shi.. And I thank him for always having my back.!” Ta k’arashe cikin kuka yayinda Hilal ma ta matse hawayen da suka gangaro masa. Mommy kam bata iya cewa komai ba sai hawaye dake ci gaba da gangaro mata tana tuna randa ya dage sai an basa matarsa da D’ansa Sun tafi.. Ta tuna irin draman da akai kafin ta amince Ya d’auki iyalinsa su tafi.. Ta tuna saida ta aje masa mata na tsawon watanni uku kafin ta basa matarsa.. Ta tuna sanda ya shigo ya mata Sallama da kalamansa na soyayya a gareta. Ta tuna yanda yaita bata hakuri yana fadin bazai tafi ba sai ya daina fushi dashi kuma sai ta saka masa albarka. Sai Mommy ta rintse ido hawaye masu tsananin zafi suna gangaro mata “My prayers are with you Son.. Allah bazai basu dama akanka ba.!” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka. Daddy kuwa yana daga waje bakin parlorn shida Alhaji Gimba yanda Alhajin Gimban keta k’ok’arin kwantar ma abokin nasa hankali. Duk k’arfin hali na Daddy saiga hawaye na gangarowa daga idonsa. Ya kuma d’agowa yana duban Alhaji Gimba. Cikin zuban hawaye Daddy yaci gaba “Gimba my two Sons.. Yarana guda biyu wanda nai failing dinsu tin suna yara ko ince Tun suna ciki basu zo duniya ba..! Wad’anda Allah ya bani su cikin tausayinsa da jin k’ansa da kuma rahamarsa amma sai nai masa butulci ban nuna godiya a gareshi ba.! Guda d’aya na sheganta shi da harshena na koreshi tin yana ciki.. Ya girma babu mahaifi..! Guda d’ayan kuma.. Ya girma gaba na amma banyi appreciating d’insa ba. Ya girma tamkar Babu mahaifi sabida wofantar dashi da nai akan idona..! Yau gashi dukansu biyu suna hannun barayin Daji Gimba.. Su biyun sunyi abota tin basu san sud’in ‘yanuwa bane. Amma abotan Ya koma k’iyayya a lokacin da Ya kamata sufi son junansu bayan sun fahimci Sun had’a mahaifi guda.. Gimba inaji kaman ni na haifar da conflict d’in dake tsakanin yarana guda biyu.. I failed them both.. And now.. Ban sani ba.. Ko dai na sake ganinsu ko ba na sake ganinsu ba..! Gimba kana ganin Har yanzu Ubangijina hukunta ni yake akan laifuka na na baya.?!” Ya k’arashe yana girgiza cikin zuban hawaye. Alhaji Gimba Ya girgiza kai “Kar kayi magana irin haka abokina. Duk abinda Ubangiji Yayi daidai ne. Ba’a saka ayar tambaya. Tsarki ya tabbata gareshi mai mulkin sammai da k’assai mai juya al’amara yanda yake so. Idan yaso Yayi mana rahama idan yaso Ya azabtar damu duka iko nashi ne akan halittunsa. Sann duk halinda muka tsinci kanmu ciki rahamarsa ne.” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “Ka daina dawo da kurakuren da kai baya kana azabtar da kanka dasu. Mu dukanmu ‘yanadam ne kuma masu kuskure sann mafiya kyawun masu kuskure cikinmu sune masu tuba. Wanda mukai tuba na gaskiya dominsa Ya sani sann shi d’in mai yawan gafara ne mai jin k’ai.” Ya dan dafa hannun Daddy “Tabbas idan Munyi imani za’a jarabce mu.! Kai hakuri abokina kai tawakkali. Ka saka ma ranka wann rajabawa ce daga Allah.. Muyi addu’an Allah Ya kub’utar dasu Ya dawo mana dasu lafiya..” Daddy ya amsa da Ameen yana mai waigawa ko zaiga Sadis amma bai gansa nan wajen ba. Alhaji Gimba Ya gyara zama yace “Kuma Haidar kawai suka nema yakai kansa.? Sann meyasa baayi gaggawan sanar da jami’an tsaro ba dan a samu a shawo matsalar da wuri.” Daddy yai saurin girgiza kai “A’a Gimba rayuwar yarana are at stake here.. Kaga ita Anisa ma cewa sukai juna gareta kaga dole abisu yanda suka buk’ata kasan yanda wad’ann azzaluman mutane suke gudanar da al’amaransu sam babu Allah a ransu Gimba. Yanzu mistake kad’an zaayi su hallak’a min yara gaba d’aya. Watak’ila idan Haidar yaje su nemi Ransom mai tsoka.. Ni ko rayuwata suka nema ba Kampanina da abinda na mallaka ba zan basu dan su sako yaran nan Gimba.” Alhaji Gimba Ya tsare Daddy cikeda tausayawa. Sai yana tuna lokutan baya da Daddy ke cewa kampanin sa Ya fiye masa Haidar. Yau gashi yana ce zai sadaukar da komai nasa dan ya ceci Haidar ciki harda rayuwarsa. Ya dan numfasa sai kuma yace “Amma akwai alaman tambaya a nan Abokina.. Meyasa zasu buk’aci Haidar Ya kai kansa..? Meyasa Kai tsaye basu nemi Ransom ba.? I’m sorry to say this.. Abokina Anya baza’a duba maganar Haidar ba.? Banso na saka maka zargi ko shakku akan D’anka musamman da shike baku jima da kasancewa da juna ba.. Amma..” Daddy yai saurin dakatar da Alhaji Gimba yana girgiza Kai “Haba Gimba kar kace kaima ka yarda da shirmen Haidar. Haidar zafin kishi kawai ke d’awainiya dashi amma d’an uwansa bai nufinsa da komai face alkhairi. Masu garkuwa su suka sacesu. Kasan mutanen nan da salo salo na yaudara.. Kar ka mance sukan sace mutum su nemi kud’in fansa Wanda yakai kudin ma suyi garkuwa dashi..” Sai ya d’anyi shiru kaman Wanda Ya tuna wani abu “Haidar shine in charge na sabon kwangilan titi da mukeyi a jihar Lagos.. Kasan Kampani da dama sun nemi kwangilar basu samu ba.. Kanaga garkuwa da akai da yaran nan nada alak’a da wann kwangilar tinda gashi basu nemi ransom ba sai Haidar..!” Alhaji Gimba yai shiru sai kuma ya jinjina kai kad’an “Everything is possible here.. Amma Kai tsaye bazamuyi saurin yanke hukunci ba.. Saidai dole mu saka abinda kace into consideration. Allah dai ya bayyana mana su cikin aminci.. Daddy ya amsa da Ameen yana jinjina kai. ** Kutsawa yake cikin dajin yayi tafiya da baida wani nisa daga bakin kwalta. Kasancewar ba daji bane sosai hakan yasa Sadis bai sha wahalan samun layin Haidar ba. Bakin kwalta Haidar ya bar motarsa Ya sauk’a d Ya fara tafiyar k’afa. Nan yake sanar da Sadis ya kunna tablet d’in da sukai connecting spy camera din dake button din wuyar rigar Haidar d’in dashi. Akwai app da sukai installing cikin tablet d’in yanda kowa zaiga live streaming abinda ke faruwa. Spy Camera d’in dake jikin button d’in wuyar rigar Haidar zata dinga nade komai yanda su kuma zasuke gani cikin tablet d’in. Lokaci guda Sadis ke fad’in an gama. Daddy yana gefe nan cikin parlorn yana amsa waya bayan Alhaji Gimba Ya fice zuwaga majalisunsu zai sanar dan a tayasu da addu’a. Ga security ya kuma zama very tied a gidan. Har lokacin su Mommy jigum jigum suke. A haka Sadis ya shigo parlorn rik’eda tablet d’in yace dasu gaba d’aya Haidar yana so suga abinda zai kunna musu. Take hankulansu ya dawo ga Sadis. Daddy ya katse wayan da yake ya k’araso yana tambayar Sadis meke faruwa.? Mai Haidar yake so su gani.? Take Sadis ya kunna tablet d’in ya kam video na sirri da Haidar ke nad’a Wanda ke mak’ale gaban rigarsa kaman button. A haka Haidar yaci gaba da kutsawa. A daidai jikin wata bishiya yaji alamun fito. Yaja Ya tsaya yana waige waige. Can ya hangi wasu k’artai guda biyu Sun fito daga bayan wata k’atuwar bishiya. Daga nesa sukai masa umarni da “Hands in the air.” Haidar ya d’aga hannayensa sama alamun surrender. Kartan suka k’araso guda d’aya yai searching Haidar dan ya tabbatar bai d’auke da makami. Yayinda guda d’aya yake lek’en bayan Haidar d’in dan ya tabbata shi kad’ai yake babu jami’an tsaro. Ya dubi Haidar yace “Are you sure you are alone.?” Haidar ya jinjina Kai “You can be sure I’m alone.!” Suka amshi cell phone d’insa kafin sukai blindfolding d’insa. Tafiya kad’an sukai idanun Haidar suna rufe. Sai yaji alamun kaman ba mutanen wajen. Abinda kunnuwarsa suka soma sinkayowa shine gurnani da kuka kaman na mutanen dake cikin azaba. Anisa wacce ita ta soma hangosa fad’i take “Haidar..! Haidar please help.. Help me.. Zasu kashe ni…!” Cak Haidar yaja Ya tsaya ga idanunsa a rufe.. A hankali Ya furta “Anisa..!” Cikin sauri Ya zame abinda suka rufe masa ido dashi. Ya nufo Anisa dake kwance jini na bin k’afarta. Cikin tsananin shock yake furta “What happened to you..? Mai Hisham ya aikata Miki..? Ina Hisham yake..? Su waye wad’ann..? Come.. I’ll save you.. We need to leave this place..” Ya k’arashe yana k’ok’arin d’agota. Saidai bai rufe baki ba ya sinkayo muryar Hisham dake baje cikin chakwabi na laka. Sam bai ma zata mutum bane wajen Ya zata curin k’asa ne ko wani abin. Da kyar Hisham Ya d’ago hannu yana fadin “Brother please don’t leave me here.. Dan Allah kar ka barni a nan.. Zasu kashe ni wllhi..!” Girgiza kai Haidar yake yana duban Hisham cikin rashin yarda “Wai meke faruwa ne haka a nan..? Meye kake shiryawa ne Hisham..? Meye ka aikata ma kanka.. Mai ka aikata muku.. Mai zakai gaining cikin duka wann wasan.?” Cikin murya irinta mai kuka Hisham ke fad’in “Ka yafe mun Haidar..! Ka tausaya mun ka fitar Dani a nan.. Wllhi kasheni zatayi..?” “Zata kasheka..? Ita wa..?” Daga bayansa Ya sinkayo murya tana fad’in “Banyi alk’awarin kashe ka ba Hisham Har sai kayi confessing duk wasu abubuwa da kayi ma Haidar da ahalinsa.!” Cikin wane irin yanayi Haidar ke juyowa Har ya sauk’e idanunsa tsaf akanta. “Dareen.!” Ya furta cikin tsananin shock yana duban Dareen dake zaune bisa wheelchair. “You.. you are alive.?” Haidar ya kuma fad’i yana dubanta. Dareen ta saki murmushi “Im alive Haidar my love.. I am very much alive.. Burin wad’ann azzaluman na ganin sun kashe ni sun rufe baki na bai cika ba.! Sunyi k’ok’arin takeni da mota dan kar na isa gareka na tona asirinsu wajenka.. Sunyi nasaran takeni da mota amma basuyi nasaran kasheni ba kaman yanda sukai nasaran kashe mana jaririnmu mai watanni uku a ciki..! Haidar I was carrying your child.. Our child.. The fruit of our love.. The only abu da zan dinga gani na tuna soyayyarmu.. Wad’ann azzaluman Sun kashe min shi.. Kaman haka nayi alk’awarin tatse tsinannen D’ansu dake cikin Anisa dan su d’in basu cancanci zama iyaye ba.!” Girgiza kai Haidar yake yana dubanta tashin hankali k’arara saman fuskarsa. Lokaci guda Ya daga hannaye sama a hankali kaman mai surrender. Fad’i yake “You don’t need to do this Dareen..! You don’t need to torture them like this.. You don’t need to kill their child.. Just let them go please.. Let Anisa go.. She’s bleeding..!” A fusace Dareen ta katsesa da fad’in “No Haidar.! They killed our child..! These two monsters killed our child.. Na kiraka ne kaga fansar d’aukan ran D’anmu da sukayi sann wann Devil din yai confessing duk abubuwan da Ya maka. Wanda ya hana na sanar dakai ta hanyar amfani da Anisa ta bigeni da mota..! A yau shi da bakinsa zai fad’i komai akan fuskarka Haidar. Zai fad’i duk abinda yai maka da ahalinka..!” Ta mik’a hannu ta cakumo Hisham dake layin azaba “It is game over for you.! Start talking Bastard.! Ka fad’a masa yanda ka kawoni cikin rayuwarsa ta hanyar sihiri dan ka tarwatsa tsakaninsa da iyayensa.. Talk.!” Ta k’arashe tana turasa gaban Haidar yanda Hisham Ya zube gaban Haidar yana nishi. Zamu iya cewa ba D’anadam guda dake motsi parlorn Daddy. SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!* *64* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* Har lokacin duk’e Hisham yake gaban Haidar yana fidda numfashi da kyar. Ya kaikaito yana duban Dareen dake zaune saman wheelchair gefensa. A hankali yake jinjina kai yana dubanta “So this is your plan..? To exact revenge.?” Cakumosa Dareen ta kumayi tana huci “No, this is not revenge but a Karma.. This is exactly what Karma looks like..! When you feel you are at the lowest of your life..?” Ta murmusa “You think you are Smart Hisham.? Well I’m ten steps ahead of you.. Filthy Bastard..! Tell him now.. Tell him everything.! And when I said everything.. I mean every.. Thing..!” Haidar yaci gaba da duban Hisham yana girgiza kai da idanunsa da tuni Sun kuma kad’awa “I know you’ve always known… Ka jima da sanin cewa kai din.. d’an mahaifina..? Sann dalilin da Yasa ka shigo rayuwata kenan.. Haka ne..?” Hisham Ya jinjina masa kai yana dubansa. Murmushi saman fuskarsa “That’s right Haidar.” Haidar ya jinin kai kad’an “But why me.. Meyasa ni..? What have I done to you..?” “Because ta hanyarka ne kawai zan kutsa cikin ahalin ka na kuma tarwatsa ku..! Nayi rantsuwa matuk’a ina numfashi your family will never be whole.. I vowed to be shadowing each and every step you take in life.! Nayi rantsuwa sai na tarwatsa ku.!” Yaci gaba da jinina kai yana duban Haidar “Na kawo Dareen cikin rayuwarka dan na samu saukin tarwatsa ku.!” A fusace Haidar Ya katsesa “But that family you tried so hard to break has already been broken.. Wann ahalin Ya riga Ya tarwatse tin kafin zuwanka.. Kuma kasan mai..? I’ve paid the price..! Na girma Ina biyan wann farashin.. Ka sani.?!” Hisham yai saurin katsesa“No Haidar baka biya komai ba..! Baka biya komai ba kan irin rayuwar da na fuskanta..!” Hisham yaci gaba da hawaye yana duban Haidar d’in “I grew up in a misery..! I grew up watching my Mom suffering.. Suffering from the misery your parents inflicted on her..! Before you judge me.. Ina so ka saurari nawa b’angaren labarin.!” Cikin huci Haidar ke dubansa “Nothing justifies what you did Hisham.. Kai dan adam ne kaman kowa and you had your chance to do what’s right..!” Hisham ya girgiza Kai “Mai zakace ga D’an da aka haifesa a kurkuku..? Mai zaka ce ga yaron da Ya taso cikin kyama da tsangwama..? Mai zakace ga yaron da Ya taso ba tareda yasan mahaifinsa ba.. Mai zaka ce ga yaron da aka turasa kurkuku sabida rashin galihu sann a wann kurkukun yasan cewa a nan aka haifesa..? Mahaifinsa shi ya jefa mahaifiyarsa a wann kurkukun da Ya zamto tushensa.. Sann.. Sann Matarsa ita ce silar aukuwar komai..!” Yaci gaba da jinjina kai yana duban Haidar “Yes Haidar a kurkuku nasan cewa a nan ne aka haifeni.. A nan nasan labarina.. Da asalina da aka rufe tun kafin nazo duniya..!” Ya share hawayen da suka gangaro masa kafin yaci gaba “Kaman yanda ka sani sunana Hisham..! Na taso na tsinci kaina ni kad’ai wajen mahaifiyata, babu mahaifi, babu D’anuwa ko ‘Yaruwa… Babu tak’amaimen ahali… Mu biyu ne tak.. Daga ita sai ni.. Na taso cikin kyara da tsangwama daga wajen mutane da dama.. Tin ina yaro tin bani fahimtar kalaman da mutane ke jifarmu nida mahaifiyata dasu Har dai nakai munzanin da na soma gane abubuwa. Babban kalma na aibu da ake jifana dashi shine rashin Uba.. Wanda har ta Kai na soma jefa ma Hajja tambayoyi gameda nawa mahaifin. Amma sai ta ce mun Ya rasu.. Idan nace ina danginsa sai tace mun baidasu.. Idan na tambayeta nata dangin sai ta ce mun na daina yawan tambayoyi inada ita kuma tana k’aunata. Daga baya na fahimci Ahalinta Sun koreta ne sann suna gudunta.. Tabbas ita d’in korarriya ce cikin danginta dan nima lokacin da naso tunk’ararsu sun koreni tin kafin na tunk’aresu. Babu mai so ace ya rab’e mu balle Har ya samu wata alaka damu.. Duk yanda na shiga korata ake ana jifana da kalamai na aibu.. Na shiga rud’ani da damuwa musamman idan na daga ido na kalli mahaifiyata sai naga mutumiyar kirki.. Nayita jefa ma kaina tambayoyi meyasa muka zama abin gudu abin kyama bayan kyawawan D’abi’u da mahaifiyata take dasu Wanda take k’ok’arin d’aurani akai.. Zan iya cewa kaf cikin mutanen da suke hantaranmu suke kyaranmu babu Wanda bazai so ace Ya samu D’a mai natsuwa irina ba.. Duk yanda mukaje korarmu ake.. We had nowhere to go.. Mahaifiyata tana iya k’ok’arinta taga ta samar mana abinda zamu rufa asirinmu dashi.. But it was not easy.. Tayi ko wani irin aikatau dan ta turani makaranta.. Ta hana kanta abinci dan rayuwana Ya inganta.. Ita d’in uwa ce kuma uba a wajena… A wani gida da take aikatau yanda muka samu saukin tsangwaman da muke fuskanta a nan ta turani boarding school da dan kudin da take samu a wann gidan.. Wani rana na dawo hutu na tadda Maigidan yana kokarin yaci zarafinta… Da yaga haikan bazata bashi kanta ba sai Ya soma zage zage yana jifanta da kalamai masu muni yana cewa waye a gari baisan wann D’an nata ma ta hanyar banza ta same sa ba.. Dan haka Dole ta basa kanta dan ya mata sutura ita da D’anta..! I was only 16 then.. Zuciya ta debeni ganin yana kokarin nufo mahaifiyata dake neman hanyar tsira.. Nai jifa da jakar makaranta na na rarumi wani katako a wajen na kwada masa akai.. Take jini Ya balle yai kwance wajen tamkar maras numfashi.. Ganin haka yasa hankalin Hajja Ya Tashi.. Jikinta na matuk’ar rawa take furta Hisham ka kashe shi.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Ka tashi ka gudu kafin wani Ya cimmaka.. Ka fita daga nan ka gudu.. Na soma girgiza Kai ina hawaye fad’i nake A’a Hajja bazan tafi na k’yaleki ba.! A dole Hajja tasa na fice daga gidan. Koda matan mai gida suka shigo suka tadda mijinsu haka sai suka kira ‘yan sanda suka sanar dasu cewa mai masu aikatau wato Hajja ta ita tayi yunk’urin kashe masu maigida bayan tayi k’ok’arin seducing d’insa bata samu yanda take so ba. Dama Sun jima da sanin ita d’in ba mutumiyar arziki bace sann tanada criminal record. Hajja batai wata wata ba ta amasa laifin da fad’in ita ta illata mutumin Wanda Ya kwashe watanni kwance asibiti baisan yanda kansa yake ba. Da naga za’a tura Hajjata kurkuku sai na fito na amsa laifin aka turani gidan yari da k’anan shekaru.” Hisham yaci gaba da jinina kai yana duban Haidar “Hajja ta shiga cikin yanayi na tashin hankali da d’imauta. Bamuda kowa bamu da komai bamuda mai tsaya mana. Allah ne gatanmu. A kurku na hadu da wani mutumi wanda Ya kwashe shekaru da dama a kurkukun. K’alilan ne suka fisa jimawa cikin kurkukun. Bansan dalili ba amma Allah Ya jefa kaunata Zuciyar mutumin. D’abi’a ce a kurkuku duk sabon zuwa dole a masa sannu da zuwa. Sann wann sannu da zuwa d’in ba komai bane face bugu na fitan hankali wasu lokutan Har stabbing mutum ake. Na bugu iyaka buguwa a hannun sauran inmates d’in. Toh bayan naci bugu ne hankalin wann mutumin Wanda yana d’aya daga cikin masu fad’a aji tsakanin prisoners Ya kai kaina. Ya kirawo ni ya bani abinci naci ya kuma ce daga wann bugun na farko da aka mun kar Wanda ta sake tab’a koda d’an yatsa na. Da wann na samu saukin gwale gwalen azaban gidan kasu. Mutumin ya tanbayeni labarina na sanar dashi cewa k’ok’arin kare mahaifiyata nake shine dalilin shigowata gidan kasu. Koda yaji abinda Ya faru sai naga ya jinina Kai yace mun nayi daidai. Bansan wani tunani yake cikin zuciyarsa ba sai naga ya ciro wani hoto cikin aljihunsa yana kallo. Idona yakai kan abinda yake kallo sai naji k’irjina yayi wani irin bugawa. Dan koda kuruciya Ya nuna a fuskar Hajjata Tabbas na gane ita ce. Hannuna na rawa nake nuna hoton nace ‘Ina kasan Hajjata.?’ Sai Ya dubeni da mamaki Ya girgiza kai ‘Hajjarka.?’ Na kuma jinjina masa kai ‘K’warai Hajjata.. Mamata.. Mahaifiyata..’ Sai naga mutumin ya tashi sosai yana dubana ‘Kai.. Kai D’an Fannah ne..?’ Sai na jinina masa kai nace k’warai ni D’anta ne.’ Sai mutumin yace dani ‘Ina mahaifinka.?’ Sai na girgiza masa kai nace ‘Mutanen gari suna cewa bani dashi.. Amma Hajjata ta sanar Dani Ya rasu Tun kafin a haifeni..’ Sai naga mutumin yana jinina kai. Ni kuma sai na tambayesa ya akai yasan Hajjata sann me hotonta yake wajensa.? Ya gyara zama yana dubana sai Ya sanar Dani shi tsohon masoyinta ne da wasu masu k’arfin iko suka rabasu. Ya kuma dubana yace ‘Mahaifinka na nan Hisham.. Mahaifinka bai Mutu ba.. Sann kaga wann gidan Yarin a nan aka haifeka.. Kaidin tamkar ka dawo Tushenka ne ko ince k’addara ta kuma kawoka ciki wann kurkukun dan kasan bak’in zaluncin da aka muku kaida mahaifiyarka Tun kafin kazo duniya.!” Hisham yasa hannu Ya share hawayen da suka zubo masa yayinda hawaye sukaci gaba da zarya a fuskan Haidar. Lokaci gida Hisham yaci gaba “A nan ne wann mutumin Ya bani labarin duk abubuwan da suka faru baya.. Auren Aliyu Maitama da Mahaifiyata da yanda Matarsa Hajiya Kwaise Tai amfani da shi wann mutumin wato tsohon masoyin mahaifiyata ta tarwatsa auren mahaifyata da Aliyu Maitama ta kuma sa Ya koreni daga cikin ahalinsa tun ina ciki banzo duniya ba sann Ya daure mahaifiyata Har ta haifoni a gidan Kasu.. Mutumin yaci gaba da sanar Dani ‘Ni na biya kurakuraina tsawon zaman da nayi a gidan yarin nan.. Sann ni da ka gani bazan tab’a fita daga gidan yarin nan ba

Chapter 62 of 64