Share this page
Anisa… I hope kaima na Sami goyon bayanka D’anuwa.” Murmushin takaici ne ya kufce ma Haidar “You are unbelievable.! You really have no shame.! Ta nan ka b’ullo..? Zaka auri Anisa..Just what are you up to this time around.? Mai kake shiryawa Hisham.?!” Daddy ya dakatar da Haidar “Haidar ya isa haka.. Kar ka fara.” Girgiza Kai Haidar yake yana duban Daddy “Daddy don’t tell me har yanzu baka gane wann makaryaci mai fuska biyun ba..! Daddy I’m sure idan ya shirya Auren Anisa wata manufa yake dashi amma ba don yana son Anisa ko yana so ya fiddata daga situation da take ciki ba Wanda shi ya jefata.. Daddy this monster here only think of himself.. If he says he wants to marry Anisa that’s because yanada wata manufa da yake so ya cimma.! I’m very sure he’s up to no good.!” “Enough Haidar.!” Daddy ya dakatar dashi kafin yaci gaba “Kai a rayuwa ba’a yafiya aka yafe maka.? Meyasa kullum kakeda negative thought Akan D’anuwanka Wanda ba abinda yai maka face alkhairi..! Ka fad’a mun abu d’aya da yayi na cutar dakai..! Idan aka Ummulkhair ne ya maka bayani ya kuma janye idon shi Akan iyalinka a lokacin da ya fahimci Kai take aure. Sann na d’auka an rufe wann babin a jiya da aka maida aurenka da iyalinka.! Yanzu yazo da batun yana Neman Auren Anisa kace ba haka ba.! Toh mai kake so yayi Haidar.? Ka sanar Dani mai kake so ya aikata kuma.!” Shiru Haidar yai ba tareda ya kuma cewa komai ba. Yayinda Hisham ya soma bama Daddy hakuri cikin kwantar da murya da k’ok’arin kwantar masa da hankali. Ya dubi Haidar da idanunsa suka kad’a sosai. Ya sassauta murya “Haidar, ina fata mu samu daidaiton fahimta watarana. I hope a day will come.. Ranan da zaka sake amincewa Dani. Ka amince bani nufinka da komai face alkhairi.” Ya dan numfasa “Ka yarda Dani, da kyakkyawan manufa nace zan nemi Auren Anisa. Amma idan kanaga bata cancanci miji kaman ni ba.. Ba matsala sai na hakura.After all, ba yau ne rana na farko da na fara neman Aure ana rejecting dina ba.” Kalamansa sai ya tuno ma Daddy labarin da Hisham d’in ya basu lokacin da yaita Neman aure ana rejecting d’insa sabida rashin cikakken asali. Wanda Daddyn yake ganin hakan kaman laifinsa ne. Now is the right time for him to be a father to his son. Daddy ya dubi Hisham yace “Ya isa haka Son. Just don’t mind your brother. A hankali wataran zai fahimceka. Idan Kana so ka auri Anisa zan nema maka Aurenta. Ba Anisa kawai ba. Kai Ko ina kake so kaje neman Aure ni mahaifinka Aliyu Maitama zan tsaya maka.. Ko ‘Yar gidan waye kuwa. Ba Wanda zai sake maka gorin asali.” Hisham ya murmusa cikeda Jin dadi. Kaman zai kuka yake furta “Thank you Daddy..! For the first time in my life.. Naji a raina Nima inada mahaifi kaman ko wani D’a.” “Ya kamata kaji haka koda yaushe. Because your Dad will always be here for you kaji koh.” Girgiza Kai kurum Haidar keyi kafin yasa kai ya fice daga parlorn dan bazai jure kallon Kayan bak’in ciki irin wann ba. Mommy ta mik’e tabi bayansa. Daddy ya dubi Hisham yace “Amma wani hanzari ba gudu ba.. Kanaga za’a bada belin Anisa cikin sauk’i musamman yanzu da iyayen yarinyar can Dareen suka bayyana kuma suke Neman hakkin Ran ‘yarsu.?” Hisham ya jinjina Kai “K’warai Daddy. Da ace Anisa bata amsa cewa da ganganci tabi kan Dareen da mota ba Tabbas da abin yafi zuwa da sauk’i. Babban abinda zaisa a bada belin Anisa a halin yanzu shine rashin ganin gawar Dareen Wanda ganin gawar Dareen ne kad’ai zai tabbatar da mutuwar ta. Kaga zamuyi amfani da hakan a court. Da taimakon k’wararren Lauya kotu zata amince ta bada beli koda za’a ci gaba da Shari’ar. Daddy ita kanta Anisa da ta bige Dareen batada tabbacin Dareen ta Mutu ko bata Mutu ba tinda bataga gawar ta ba balle ta tabbatar kaman yanda ta fad’i a statement dinta. So bazai yuwu a yanke ma Anisa hukunci ba tareda k’wakk’waran dalili ba. Anisa ta cancanci second chance kaman kowa a rayuwa Daddy. Kuskuren da ta aikata bazai zama dalili da zaisa a juya mata baya ba. Daddy idan ka amince min zan tsaya tsayin daka har sai na tabbata Anisa ta Sami freedom din data cancanta. Dan rashin adalci ne a barta a rufe ba tareda an tabbatar da ta aikata laifin kisan ba. Idan har daga baya wani abu ya bayyana.. Ina nufin aka samu gawan Dareen ko wani k’wakk’waran dalili da zai tabbatar da mutuwar Dareen.. Ka yarda dani Daddy ni da hannuna zan mik’a Anisa ma hukuma, Alk’ali yai hukunci koda bayan ta zama matata. Zan kuma d’auki hakan matsayin k’addara Daddy dan D’anadam bazai wuce k’addararsa ba. Daddy I believe Anisa ta cancanci Rayuwar farin ciki mai cikeda ‘yanci a Gidan Aurenta koda na dan lokaci kad’an ne. Ina fata ta Sami wann opportunity d’in a rayuwa ta samu wann experience din koda na dan lokaci kad’an ne.. Balle ma in sha Allah baza’a sameta da laifin kisan ba.” Ya k’arashe cikeda kulawa. Mommy dake tsaye bayan parlorn duk sai jikinta yai sanyi. Sai ta rasa tausayin waye zataji. Anisa dake tsare ne ko kuwa Hisham d’in ne dake kokarin nema mata ‘yanci Wanda take ji kaman dukkansu sunyi failing Anisar sai Hisham ne zai sadaukarwa mai girma ga d’iyar ‘Yaruwar tata. Daddy ya dafa kafad’an Hisham “I’m proud of you Son. Kanada zuciya mai kyau kuma mai yalwa. Allah ya maka albarka da wann sadaukarwa mai girma da kake k’ok’arin yi. Amma ina so ka fara tuntubar mahaifyarka da batun. Munyi waya ta kuma sanar Dani gobe ‘yanuwanta zasu mata rakiya zuwa nan Abuja. Yanada kyau kaji nata ra’ayin da shawarin.” Hisham ya amsa da “Shikenan Daddy zanyi kaman yanda kace in sha Allah.” Daddy ya amsa da “Maddallah. Allah yayi jagora.” Hisham ya sake amsawa da Ameen kafin yai Sallama ma Daddyn ya fice zuciyarsa wasai. Washe gari kuwa Hajja ta samu tarewa zuwa gidan mijinta Engr Aliyu Maitama a nan birnin tarayya tareda rakiyan tsirarun ‘yanuwanta. Daddy yaso ya raba musu gida ita da Mommy amma sai Mommyn harma da Hajjan suka zab’i zaman tare a gida d’aya. Hakan yasa tuni aka gyara ma Hajjan nata sashen a nan cikin gidan. ** Anisa bataji mamakin ganin Haidar ya kawo mata ziyara ba dan tasan izuwa wann lokacin labari ya isa masa cewa Hisham naso ya aureta. Haidar ya tsareta sosai da ido kafin ya gyara zamansa yace “Tell me, is it true… Da gaske ne wann D’aniskan ya miki tayin aurensa.?” Ta furzar da huci kad’an had’ida rausayar da ido “Believe me I couldn’t believe it either.. I mean how shameless of him. Ta ya zai soma cewa zai aureni bayan ukuban da ya jefani ciki..! Ka yarda dani, Ya b’ullo ta wann salon ne bayan da yaji an maida Aurenka da Ummulkhair. Na tabbata wani abun yake son shiryawa.” Haidar yai shiru kaman mai nazari “And you.? What are you suggesting.?” Anisa taci gaba da jinjina Kai tana dubansa “Zan amince da Tayinsa. Zan aure shi.” Da tsananin mamaki Haidar ke dubanta “Did you hear yourself. Kin kuwa ji mai kika fad’a.? Zaki amince ki amshi tayinsa.? Zaki amince ki aure shi..? Are you going to let him use you for the second time.?!” Murmusawa tai kad’an “You might know Hisham as a friend.. Amma ni na sanshi ne a matsayin mugu. Hisham is a very coning person. Idan yace zai Aureni kaman ya sadaukar da wani portion ne na soyayyar da yake ma Ummulkhair. Knowing Hisham bazai tab’a sadaukarwa mai girma irin wann ba ba tareda ya samu wani babban outcome ba. Idan har yace zai Aureni ka yarda dani akwai wani shiri babba da yake kullawa ta k’ark’ashin k’asa. Kar ka mance Hisham ya kawo mace cikin rayuwarka har ta aureka kukai rayuwar aure ba tareda ka ankare ba. Wanda duk zai aikata abu makamancin wann ba k’aramin shed’ani bane. So na sani Hisham ba mutum bane da za’ayi under estimating d’insa. Duk abinda yake yi is well calculated. Amma ka yarda dani aurena da yace zai yi wann karon shine babban miscalculation mafi muni da zai tapka a rayuwarsa. Ni ba wann shashashar Anisa da ka sani a baya bane. Bazan Auri Hisham dan na bashi dama yai amfani Dani ba. Saidai ni nayi amfani dashi. Wann karon zai tone ramin da zai rupta ne a ciki da Kansa ba tareda ya ankare ba. Zan tabbatar mishi da cewa ni mace ce kuma yayi kuskuren underestimating dina. Ni yafi cancanta na bayyana asalin waye Hisham sabida Dani yai amfani. Kuma aurensa da zanyi shi zai bani dama na samu duk wani kusanci dashi sann na yaye rufin fuskarsa kowa yasan waye shi. Ka yarda dani Hisham bazai tab’a barinku ku samu peace ba kaida Ummulkhair matuk’a yana nan a kura lullub’e da fatan akuya.” Haidar ya girgiza Kai kad’an “No.. No Anisa. I won’t let this happen. Ina nufin bazan bari ki jefa rayuwarki cikin had’ari ba dan kawai asirin Hisham ya tonu. Kin kuwa san mai ake nufi da kalmar Aure.? Ta ya zaki amince ki auri mutumin da ke kanki kinsan ba mutum bane. Anisa Aure is a life time commitment.. Ke ‘Yaruwata ce kuma k’anwata. Koda ace bamu had’a alak’a ta jini ba bazan bari wann devil d’in ya kusanceki ba balle har akai ga maganar Aure. Aure is serious commitment. Na d’auki al’amarin Aure da wasa a farko naga yanda ya juya mun. Bazan barki ki d’auki wann path din ba. Bazan bari kiyi gambling da rayuwarki ba dan kawai kina so ki tona asirin Hisham.” Ya dan furzar da huci yana jinjina Kai kad’an “Akwai ways da yawa da za’a Kama shi. Yanzu haka nasa ana bincike kan iyayen Dareen.I believe a hankali through wad’ann mutanen zamu samu wani haske gameda gaskiyar al’amarin mutuwar Dareen ko nace b’acewarta. If she’s alive ita kad’ai ce zata iya kawo k’arshen yaudarar Hisham.” Anisa ta murmusa “And what if she’s dead.? Zan tabbata ne kawai a nan gidan yari babu ranar fita. Sann Hisham bazai tab’a biyan duk abubuwan da ya aikata ba. Uwa uba bazai tab’a bari ku Sami kwanciyar hankali ba kaida Ummulkhai.” Ta dan numfasa “Na gode da kulawarka a gareni D’anuwa. Amma Hisham ya wuce tunanin mutum.. Bana tunanin akwai wani bincike da zaisa a Kama Hisham dumu dumu dan shi d’in k’wararre ne. Sann baya barin wani shaida da zai tracing back to him. Abu d’aya da zaisa a Kama Hisham shine abi ta hanyarsa. Ina nufin makirci.! Aurensa ne kawai zaisa na samu kusanci dashi.” Taci gaba da jinjina Kai a hankali “I might not be innocent. Kuma nasan in one way or the other dole zan biya abubuwan da na aikata a rayuwa. Tabbas ni nake driving motar. Ni na bige Dareen da Mota but under the influence of Hisham. Ka yarda dani bansan ina hankalina yake ba lokacin da na bige Dareen maganganun Hisham ne kawai suke yawo a kwanyata. K’ok’ari kawai nake na dakatar da ita kar isa gareka kaman yanda Hisham keta tunzura ni da na dakatar da ita. Dan idan ta isa ta sanar dakai komai zaka tsaneni koma ka hukunta ni. Ashe amfani kawai yake Dani dan na zame masa garkuwa na aikata laifin da zai amfani ya rufe bakina dashi. While I’m stuck here Hisham bazai tab’a biyan abubuwan da ya aikata ba. Ina buk’atan ficewa a nan dan na tabbata ya biya duk abubuwan da ya aikata.” Haidar ya furzar da huci kad’an yana jinjina Kai “Idan haka kika zaba. Fine.! Kowa yanada ‘yancin yin yanda yaso da rayuwarsa. Amma bana so ki saka ma ranki sabida ni Haidar zaki sadaukar da farin cikinki da rayuwarki ki auri mutum irin Hisham. Idan duk abinda kike fad’a gaskiya ne Anisa. Then Do it for yourself.. For your own freedom.. For you to clear your name...!” Yana ida fad’in haka ya mik’e yai ficewarsa. Anisa ta bisa da kallo har ya bace mata. Ta lumshe idanunta hawayen nadama suka gangaro mata. ** A cikin satin maganan Auren Anisa da Hisham ya kankama. A b’angaren Hajja sai bata kawo komai a ranta ba tafi alak’anta hakan da Jin k’ai da taimako da D’anta ya saba tsakanin Al’umma tinda d’abi’ar taimako shaidarsa ce. Sann hankalinta ya kwanta da maganan Ummulkhair musamman da yake an maida Auren Ummul d’in da D’anuwan Hisham d’in wato Haidar. Ga Hisham ma zai nasa auren ya samu natsuwa. Itakam maganar Auren sosai tai na’am dashi dukda can cikin zuciyarta bata Jin wani abu mai Kama da farin ciki gameda auren. Sann Sam bata samu natsuwa hundred percent ba sai kawai tai k’ok’arin kawar da tunanin dan tasan bazai shige aikin shed’an ba tinda shi Sam baya fatan a k’ulla alkhairi musamman a batu irin na Aure. Bugu da k’ari bayan series of Aure da D’an nata yake nema a baya ana hanasa idan tak’i wann sai ya zama kaman tayi butulci ne ma Allah. Tuni ta bar ma Allah lamarin ta kuma nema zab’insa ciki. Ko wane aure yana zuwa da nasa k’alubalen. Waye zai tab’a tunanin wai ita Fannah D’anta zai auri d’iyar Asshe k’anwar Hajiya Kwaise.? Waye zai tab’a tunanin zata dawo gidan Aliyu Maitama suyi rayuwa mai tsafta da Hajiya Kwaise.? Lallai rayuwa cike yake da sauye shayen lamra. Allah ka sauya mana sharri zuwa alkhairi. Ameen. Cikin k’ank’anin lokaci aka aiwatar da komai dan tinda akazo da batun auren sai Anisa ta samu sassauci daga wajen iyayenta musamman Abbanta Wanda dama shi yaima Amminta iyaka da ita matuk’a tana tsare a police station. A cewarsa bai haifi ‘yar da zata d’aga masa hankali ba. Ba kaman da Abban Anisar yaga D’an Aliyu Maitama ne mijin Anisar. Abun duka gida ne.. Hakan yasa babu wani dogon bincike balle jan lokaci. Balle ma shi ina ruwansa baijin ko kashi Anisa ta kawo zai fasa aura mata da dai ta zame masa masifa da tashin hankali cikin gidansa. Can Kano gidansu Anisa akaje ka d’auro Aure ko gida Abbanta bai bari taje ba daga cell yace a wuce da ita d’akin mijinta. Taron biki ma bai bari an masa a gida ba. Mommy ce ta had’a yar k’aramar biki can Abuja. Da kyar Abban Anisa ya bari Asshe ta halarta bikin yar nata. Bayan biki da kwanaki biyu Daddy yace da Hisham wann karon shi zai tafi SouthAfrica dan ya kula da kasuwancinsu na can. Ya d’auki matarsa su tafi can musamman da yake an dage sauraron k’aran Anisar har sai bayan watanni hud’u masu zuwa. Sam Hisham bai k’i tayin Daddy ba. Sati guda kawai sukai a Nigeria ba tareda Anisar ta tare da angon nata ba tinda sud’in ma tafiya ne. bayan bikin suka tattara suka nufi southAfrica. Tafiyar da zai d’auke su tsawon watanni uku. Da wutsiyar ido yake duban Anisa sanda suka zauna saman kujerun jirgin. Ya saki wann muguwar murmushin nasa kafin ya rank’wafo kad’an cikin k’ok’arinsa na d’aura mata seatbelt “Babe, I can’t wait jirgin nan tai landing. A hannu zan sureki na fara nuna miki soyayyar da ban samu daman nuna miki a Nigeria ba.” Banbarakwai haka taji abun. Ta watsa masa wani irin mugun kallo kafin tai ‘yar bazawarar murmushi na nuni da takaici “Kar mu raina ma kanmu hankali Hisham. Nida Kai munsan babu komai cikin auren nan face k’arya. So we shouldn’t expect anything from this marriage. Dan ina mai tabbatar maka ni Anisa bazan tab’a barinka ka tab’a koda d’an yatsana ba cikin watanni uku da zamuyi tare. Kuma ka saka ma ranka.! AUREN WATA UKU shi mukayi. Ina cika watanni uku a lokacin da muka dawo Nigeria zan rabu da k’addararren aurenka.!” Hisham ya tsareta da ido. Sai ya murmusa yana daidaita zamansa saman seat din. Irin Wanda ya kware a shed’ana yake fad’in “A naki wauwautan Anisa kinyi zaton wasa da hankalina kike..! Kinyi zaton kin Aureni ne dan Ki samu dama akaina ki bankado duk wasu sirrika na. Haka ne..? Kina tunanin a watanni uku da zamuyi matsayin mata da miji zaki iya samun dama akaina ki bankad’o duk wasu sirrika nawa.? Har haka kike son Haidar.? Dan na tabbata sabida shi kikai sadaukarwa mai girma kika amince da aurena.!” Yai maganar yana shafe hab’arsa yana mata wane irin duba. Har lokacin murmushi ne saman fuskarsa “Lallai kin tabbata sokuwa Anisa idan har kikai tunanin zaki iya outsmarting dina by marrying me.!” Ya k’arashe yana kamo hab’arta suna fuskantar juna. Murmushin itama ta sakar masa dan bazata bari ya gane ta karaya ko abu mai Kama da haka ba. Ya dan girgiza Kai yana dubanta “Bazaki tab’a yin hankali ba balle wayo Anisa. Idan amfani dake a karo na farko ya fi min sauki a lokacin da ban Miki farar sani ba. Meyasa amfani dake a karo na biyu lokacin da na sanki kaman tafin hannuna zai min wahala.” Ya d’anyi gajeren tsaki had’ida yin ‘yar bazaurar dariya irin Wanda ake ma Wanda aka raina masa wayau kafin yace “Ki yarda dani daga k’arshe kece zaki kasance da Haidar ba Ummul ba. Idan kika bi plan dina daga karshe Haidar zai tabbata naki.” Ya k’ank’ance idanunsa yana dubanta kaman zai sumbaceta “Mai zai faru idan na saka Miki rigar bomb. Zaki kira Haidar ki nemi taimakonsa.. Sann shi kuma zaizo ya ceceki like a real hero.?” Murmushi yaci gaba da yi yana dubanta yayinda Anisa ke ci gaba da masa kallon mamaki tama rasa a wani aji zata aje Hisham. Hisham yaci gaba “Zaku kasance a wann d’akin da na kulleki da rigar bomb ku biyu. Bomb din zai tashi daku biyun. Zaku k’one tare.. Ku biyun zaku Mutu tare kaman dai asalin masoya.. Sann ni kuma, Zan Auri matar K’anina sann na kula da bayansa ina nufin marayan D’ansa da bzawarar matarsa kaman dai D’anuwa na gari..!” Ya k’arashe yana murmushi mai bayyana hakwara. Matsawa ta soma k’ok’arin yi daga gefensa yai saurin rik’o hannunta ya matseta cikin jikinsa. Ya rank’wafo da bakinsa saitin kunnenta. A hankali yake furta “Kaman haka inada hanyoyi da dama da zanyi amfani dasu dan cikan burina. So I’m warning you Anisa, do not teste my patience.!” A hankali kuma ya soma sakin hannun nata yana sakar mata murmushi. Saima ya shiga k’ok’arin gyara mata mayafinta yana fadin “Hey wifey.. Did I scare you..? Im just kidding.” Yai mata rad’a a kunne da fad’in “bazan kasheki ba.. Zan barki kiyi rayuwa mai tsawo da Haidar d’inki.. Happy.?” Ya k’arashe yana kashe mata ido guda da murmushi saman fuskarsa. Anisa batace komai ba sai tsaresa da ido da tai dan dama Tabbas tasan Aurenta da Hisham yayi yanada shiri fiyeda Wanda yafi wann ma. Ta shirya ma aukuwar komai. Alk’awari tai bazata sake bari Hisham ya kuma samun damar cutar da Haidar da Ummul ba. Even if it will cost her her life. ** Tin bayan tafiyan Hisham da Anisa k’asar SouthAfrica Haidar bai kuma bi takan Ummul ba. Mommy dai ta sanar dashi idan Ummul d’in tayi Arba’in zata tare nan Abuja. Abinda Ya bama Mommy mamaki shine sam bai wani nuna d’okinsa ba balle damuwarsa. Sai bata kawo komai a ranta ba tinda tasan Watak’ila yayi d’okin ne har ya gaji. Sosai Ummul ta damu da halin ko in kula da Haidar yai da ita tin bayan aurensu a karo na biyu. Tanaji zaizo gidan Ya gaida su Umma yaga D’ansa Ya tafi amma ko sunanta bai ambata balle Ya buk’aci ganinta. Ranar wata juma’a ma haka tanaji su Azeema suna shelan zuwansa. Tana daga d’aki tana jinsa Har hira suke yana wasa ma D’ansa amma koda Azeema tace bari ayi masa kiranta sai Ya mik’e abinsa yana fadin Azeema ta shige cikin gidan Tai masa kiran ‘yan samari Wanda zasu shigo da aike. Hankalin Ummul idan yayi dubu Ya tashi. Wai ita Haidar yake basarwa irin haka.. Toh mai Tai masa ne da tsanani.. Kodai Ya daina sonta ne.? Tambayar da taji ya haifar mata da fad’uwan gaba. Sai taji k’walla na yunk’urin ciko idonta. A nan d’aki Mama Tani ta shigo ta isketa tana rera kuka dan dama duk idan Haidar yazo gidan sai iyayen mata su shige k’ofan Abba su bar masu filin tsakar gidan. Mama Tani ta dubeta da mamaki “A’ah! ke kuma kukan me kike..? Ina Haidar d’in.. Wai Har ya tafi ne.?” “Nima ban sani ba Mama.” Ta bama Mama Tani amsa cikin kuka. “Ban gane baki sani ba.” Cikin kuka taci gaba “Mama Haidar ya daina sona ko yazo gidan nan wajen D’ansa kawai yake zuwa amma ko gaisawa baya tsayawa muyi.” Maganganun ta suka so bama Mama Tani dariya amma sai ta gimtse tace “Toh ke ba haka kike so ba. Inji a nan kike kumfan bakin ke ba don kina sonsa kika amince da komen gidansa ba. Ke bari kiji na fad’a Miki maza irin Aliyu ba’a ja musu aji dama kad’an k’adangarun nan na bariki masu d’ingilallun buje ke jira akansu. Ahtoh.!” Badia dake daga parlor ta dage labule ta lek’o tace “Ahtoh Mama fad’a mata dai. Tana nan tana wauwauta taji ana shafe Fatiha a Abuja.!” Ummul ta kuma tunzura da kalaman Badia. Sai ta kuma fashewa da kuka. Mama Tani ta aika ma Badia dak’uwa “Kinci gidanku Badia. Ke bakinki bazai fad’i alkhairi ba. Kiji da naki matsalan wann gantalallen mijin naki ya gudu Ya barki ba tsuntsu balle tarko. Ke ba mai aure ba ke ba sakakkiya ba.” “Haba Mama Aure ni da Tasi’u kuma ai ko a k’iyama.!” Cewar Badia. Mayafi Mama Tani da dauka tana fad’in zata dubiya layin bayansu. Badia tace da ita a dawo lafiya. Mama Tani na tafe can k’asan babban kwalta ta hango ana ihun b’arawo sai jibgan mutumin ake ana masa ihun b’arawo mutane kaw sai tururuwa suke. Kaman Wanda aka ce Mama Tani ta kutsa nan ta hangi Wanda ake ma ihun b’arawo ba kowa bane face Tasi’u mijin Badia. Tasi’u dai da Ya gudu da kudin Bakauye da takardun bogi na shagon Abba ya kuma jefata a uku. Mama Tani ta dafe k’irji tana salallami “Na shiga uku mai zan gani ni Tani.?! Tasu’u.!” Tasi yaji muryar da Ya sani yana tunanin samun rahama daga jibgan da yake sha sai Ya soma k’ok’arin rarrafowa ga Mama Tani yana fadin “Mamana Mamana takaina kimin rai wllhi akasi aka samu ba ni ne b’arawon ba.!” Samarin dake wajen suka dubi Mama Tani sukace “Baaba D’anki ne.?” Mama Tani ta zaro ido waje tana dafe k’irji “Ni Tani haramiya.! Allah shaida ban haifi b’arawo ba. Wllhi ba D’ana bane nima nan a sanadiyan wann kafuri na tafi gidan kasu bada hakki ba.! Kucimin uwarsa da kyau amma kafin nan ku dakata.!” Ta waiga gefe ta dubi yaran da aka tasosu daga makaranta ta amshi paper da pencil hannunsu ta mik’a ma Tasi’u tace “Rubuta.! Rubuta ma ‘yatsa rasidi dan ubanka!.” Tasi yana haki yake girgiza kai “Mama kimin rai wllhi ina son Matata hasalima abinda Ya shigo dani layin nan kenan dan na maida matata kawai tsautsayi Ya hau kaina aka soma ihun b’arawo ni kuma na karyo kwana kenan na taka sawun b’arawon amma wllhi bani ne b’arawon ba.!” Mama Tani ta jinjina kai “Sanin gaskiyanka sai Allah Tasu’u. Amma ko hakan d’in ne ba abinda zance sai Alhamdulillahi.! kaji yanda akeji. Kaman yanda ka gudu da kud’i ka barni a tsaka mai wuya banci nanin ba nanin ta cini. Ba kunya ba tsoron Allah ina Uwar matarka. Da tsufa na geme geme na tafi kurkuku k’anun yara suka shassahata ma wann fuska tawa Mari sabida Kai. Toh kaman haka kaima yau ka taka sawun b’arawo. Wann sai Ya zama wa’azi gareka damu baki d’aya Tasu’u.!” Samarin sukaci gaba da girgiza kai suna fad’in “Karya yake bakinsu d’aya da b’arawon wllhi sai munyi ajalinsa a nan ehe.!” Mama Tani tace ku dakata kar kuyi ajalinsa. ‘Yata ta shafe shekara da watanni tana zaman gaibu da aurensa ba tareda ansan yanda yake ba. Bazata kuma yin takabansa ba bayan tsawon lokacin da ta diba babu sanin

Chapter 57 of 64