Share this page
Ummulkhair juna biyu ke gareta.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Duk abinda ke faruwa da Ummul tono mata nata bayan yake.. Tamkar dai reputation ne na abubuwan da suka faru da ita shekarun baya.. Dama a yan kwanakin taso ta fahimci hakan saidai tayita kore tunanin abin dan guje ma tono nata bayan. Sabida duk abinda zaisa ta waiwayi baya guje masa take. Saidai ga dukkan alamu duk yanda kaso guje ma wani abin sai Ya tono kansa a wasu lokutan.. Hajja ta fad’a duniyar tunanin abinda Ya faru da ita shekarun baya. Auren ta da Mahaifin Uban cikin Ummulkhair wato Aliyu Maitama kuma mahaifi ga tilon D’anta Hisham.. Sai kuka da muryar Ummul ta sinkayo tana fad’in “Dan Allah Hajja nikam bani son wann cikin.. Dan Allah kar ki bari na haifosa.. Dan Allah kisa likitocin nan su ciresa.. Ki taimake…” Batakai aya ba Hajja Tai k’arfin halin tattaro k’arfinta ta rufe bakin Ummul da k’arfin gaske “Kul. Ko da wasa kar na sake jin kalamai masu kama da wann daga bakinki Ummulkhair.. Da iliminki da karatunki.. Da addinininki..? Haba Ummul this is not like you.. Ba haka Ummul d’in da na sani take tunani ba.. Mai hak’uri a duk halinda ta tsinci kanta ciki.. Kinyi hak’uri a lokacin da kika fuskanci k’alubale na JINKIRIN Aure da fashe fashen Aure. Kin karb’i k’addararki kuma in sha Allah kin dace da jarabawa. Toh ki sani yin Aure ba yana nufin k’alubale da jarabawa Sun k’are bane. A’a wani sabon babi na karatu da jarabawa ne rayuwa ta kuma bud’e miki.. Shi kansa zaman auren karatu ne kaman yanda mutuwar Auren zai iya zama jarabawa a gareki. Ki sani ba akanki aka fara mutuwar Aure ba haka zalika ba akanki za’a daina ba… Kowa da yanda rayuwa take zuwa masa.. Kowa da irin k’addararsa a rayuwa. Kowa akwai abinda aka sanya masa jarabawarsa da k’alubalen sa cikinsa.” Ta dan numfasa sai Ta kamo hannayen Ummul cikin nata wacce Har lokacin hawaye ke kwaranya mata “Duk abinda kikaga Allah Ya hukunta ma bawa, Allah yasan dalilin da Ya k’addari aukuwar hakan.. Taho nan..” Ta k’arashe tana rungumo Ummulkhairin daga zaune.. Sosai Hajja ta rungumeta zuciyarta fal tausayinta. Cikin zuciyar nata take fad’in ‘Ko ni da suka sheganta nawa cikin ban ciresa ba.. Dan haka Bazan tab’a bari makamanciyar tunani irin wann yayi tasiri a zuciyarki ba.’ A fili kuwa murmushi take tana rungume da Ummul d’in “ ‘Ya’ya rahama ne.. Kyauta ne mai girma Wanda Allah kad’ai ke bama wanda yaso cikin bayinsa.. Insha Allahu zaki haifo abinda ke cikinki lafiya kuma zai zamto mabudin alkhairi da sauyin rayuwa mai inganci a garemu baki d’aya..” Cak Hisham dake daga bakin k’ofa hannunsa rik’eda ledan maganin da Dr yai prescribing ma Ummul yaja Ya tsaya sakamakon kalaman da yaji na fita daga bakin mahaifiyarsa.. K’iris Ya rage ledan dake hannunsa bai sunce Ya fad’i k’asa ba… Mai hakan yake nufi..? Ummulkhair ciki ne da ita..? No.. No way.. Allah yasa ba Daidai yaji ba. Babu wani ciki tattare da ita.. Haidar bazai masa haka ba..! Watanni uku Sun cika ta fita daga iddan Haidar bazai yuwu ace ciki ne da ita ba.. It can’t be… It definitely cannot be. Bai sadaukar da komai dan ya rasata daga k’arshe ba..! Jikin Hisham yaci gaba da rawa a daidai sanda ya kuma sinkayo muryar mahaifiyarsa tana tabbatar da juna biyun dake jikin Ummulkhair.. Zufa yaci gaba da karyo masa ta ko ina.. Da baya ya soma komawa ba tareda ya iya shiga d’akin ba. A nan cikin d’akin kuwa Hajja duk ta zak’u sai d’auki take. Bata san dalili ba amma sai ta tsinci kanta cikin matsanancin farin ciki gameda samuwar cikin. Ji take tamkar zatayi jika nata na kanta dan ‘ya ta d’auki Ummulkhair koda a zahiri abinda ke cikin nata Ya kasance tsatso kuma jika ga mutanen da suka zamto silan durk’ushewar rayuwarta. A b’angaren Hisham kuwa tashin hankali maras misaltuwa Ya shiga. Bayan dawowarsu gida can k’uryar d’aki Ya k’ule ya shiga dunk’ule hannunsa yana sakin huci.. Ya bigi garu da hannun nasa yana furtawa a hankali cikin karaji “Damn you..! Damn you Haidar..! How dare you..!How could you do this to me.!” Yaci gaba da sakin huci gumi na tsartsafo masa. Ji yake da zaiga Haidar gabansa da Ya shak’esa da iyaka k’arfinsa. Yana nan a haka wayar Ania Ya shigo masa.. Ya dubi wayar yana ci gaba da sakin huci kaman bazai d’aga ba. Sai Ya koma ya zauna ya janyo wayar ya daga ba tareda Ya daina sakin huci ba. Yana d’agawa daga d’aya b’angaren Anisa tace dashi “Ango ka sha k’amshi.. I know by now ka fayyace ma Ummulkhair irin soyayyarta dake lullub’e cikin zuciyarka.. Watak’ila Har an fara zancen saka muku rana. Toh nima dai Albishir na kira na maka dukda nasan kace ya kamata mu daina kiran juna tinda hak’armu na raba tsakanin Ummul da Haidar ya cimma ruwa.. Na kiraka ne na sanar dakai cewa Aunty Kwaise taje Har Kano ta d’aukoni ta dawo Dani gidanta.. Kuma kasan mai yanzu treating dina take da kyau har wani respect naga tana bani da kula na musamman.. Yanzu bata min kallon shashasha kaman yanda take min a baya.. Na tabbata bazai jima ba zan saye zuciyarta kamar yanda Ummul ta lashe zuciyarta. In no time zata aura min d’anta dan wllhi sosai ta d’aukeni da mahimmanci wann karon.. Finally burina zai cika Hisham.!” Ta k’arashe tana ‘yar tsallan murna. “Shut up.! Shut the hell up.!!” Hisham ya daka mata tsawa kafin yaci gaba cikin huci “Kina jina idona idon tsinannen Haidar d’in nan sai kashesa..!” A d’an tsorace Anisa ta waro ido waje kaman Hisham d’in na kallonta tace “Excuse me.. Mai kake cewa.. Kan wane dalili zaka kashe Haidar dina..?” “Shut up Neesa..! Kar ki sake ambato min sunansa..! That Imbecile made sure ya bar wani babban dalili da zai hana k’arewar alak’a tsakaninsa da Ummul..!” Anisa ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Ban fahimceka ba.. Alak’a kamar ya..?” “He made sure ya bar gudan jininsa tattareda ita..! He ruined all my plans.. All our plans. Duk abinda muka jima muna shiryawa zai zama aikin banza..!” Anisa da taji maganar a bazata cikin rashin fahimta tace “What do you mean..? Mai kake nufi ya bar gudan jininsa… So kake.. Kace min like.. Ummul is pregnant..?” Hisham ya furzar da huci “So kike na maimaita miki.. He made sure he impregnated her kafin ya rabu da ita.. I hate him..!” Anisa ta soma girgiza kai “A’a.. We can’t let this happen.. Haidar can’t find out about this.. No one should find out bout this.. She can’t be pregnant.. She can’t give Haidar a child do you understand Hisham.. Dole muyi komai domin kawar da wann cikin.. No matter the cost..!” Hisham baice komai ba sai huci da yake ci gaba da furzarwa. Anisa cikin tsananin damuwa da tashin hankali taci gaba “Hisham wann cikin shi zai sake k’ulla igiyoyin Auren Haidar da Ummul da mukayi komai domin tsinkasu. Idan har muka bari wann ciki ya tabbata har aka haifosa kashinmu ya bushe.. Dan zamu rasa komai.. Dole muyi komai domin kawar dashi kuma kaine zakayi dan kaine kake tareda ita..” “Mai kike nufi..?” “Ina nufin duk yanda za’ai mu cire wann cikin.. Bazai yuwu a haifosa ba..” “How..? Ta ya hakan zai kasance.?” Anisa tace “Kawai ka kaita asibiti a cire ko ka saka mata magani cikin wani abin sha ta sha Ya fice.. Is as simple as this.” Wann karon murmushi Hisham yai kafin yace “Lallai na yarda kin cika mai k’wak’walwar kifi Anisa. Ta ya kike zaton zanyi duk abinda kika ce ba tareda Sun zargeni ba.. You must be stupid.!” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “Look, Daga mahaifyata har Ummul sunyi matuk’ar yarda dani bazanyi wani abu da zai rusa wann yarda nasu da na samu ba..” Anisa ta furzar da huci “Toh idan ba haka ba ya zamuyi..? Ai gwara mu markade wann cikin ma fiyeda shegen can dake cikin Dareen Wanda muka markade. Dan wann shine babban barazana a garemu.. Hisham duk yanda za’ai cikin nan bazai zo duniya Ya tarwatsa mana farin cikinmu ba.!” Hisham Ya furzar da huci “I need to think of something.. Amma banda zubar da cikin.” Cikeda k’osawa Anisa tace “Har kanada wani abinda zakai tunani akai bayan wann cikin threat ne a garemu..” Ta girgiza kai cikin tashin hankali “Hisham, we can’t afford any further miscalculation… We need to act now tun munada dama akan cikin nan.. Tun yana k’arami.. Yanzu ya kamata mu b’arar dashi. Idan ta kama na taho yanda kake ne zan taho just to carry out the job.” A zuciye yace da ita “I love Ummulkhair kin fahimta.. I want to build my relationship with her based on trust.. Bazan tab’a bata wani room da zata zargeni ba.. So tinda nace ki bar min komai ki bar min nasan abinda zanyi.. The bottom line shine Ummul bazata tab’a komawa ga Haidar ba..!” Bai jira cewarta ba ya katse kiran yana ci gaba da sakin huci. Ya jima zaune wajen yana sak’e sak’e cikin zuciyarsa da yanda zai b’ullo ma al’amarin. Ya shafe fuskarsa yana jin tsanan Haidar na ninkuwa cikin zuciyarsa. A b’angaren Ummul kuwa wani kula na musamman take samu daga Hajja wacce takeji tamkar dai jika zata samu. Duk yanda Ummul ke nuna bata son cikin bai hana Hajja d’aukin cikin ba. Sann dukda samuwar cikin ya haifar mata da tuno nata bayan bai canza yanda take ji gameda cikin a zuciyarta ba. Duk wani abinda tasan yanada kyau ga mata masu juna biyu sauri take taima Ummul. Haka zalika duk abinda tasan mata masu juna biyu naso kokari take ta mata koda Ummul d’in tana nuna bata so. ** A parlor Hajja ta tsinci magungunan da aka bama Ummul ko d’aya bata sha ba ta ajesu. Hajja ta girgiza Kai ta d’auki ledar maganin ta nufi d’aki yanda takeda tabbacin Ummul na kwance nan dan tinda suka komo daga asibiti da labarin cikin yau kusan kwanaki uku kullum zama take a d’aki tana aikin kuka abinci ma sai Hajja tayi da gaske take ci. Hajja ta turo k’ofan d’akin tana juya magungunan kaman mai k’irgensu take fad’in “Ummulkhair wai baki sha maganin nan ko d’aya ba tinda aka baki su..?” Da kyar Ummul dake ta kwance lamo hannunta guda saman cikinta ta mik’e tana goge ragowar hawayen da suka gangaro mata tanayi tana avoiding idon Hajja dan tasan bata son kuka da shiga damuwar da take. A hankali ta furta “Hajja ni wari suke min bana so.” D’an girgiza Kai Hajja tai kafin ta zauna gefenta kad’an “Banda abinki Ummul magani ai ba’a shansa dan dad’i.. Shi wann maganin folic acid ne kuma magani ne mai amfani sosai ga mata masu juna biyu wanda ake so su fara shansa tin ciki na k’arami sabida matuk’ar amfaninsa ga jaririn dake cikinsu. Da yawan mata masu juna biyu idan an basu magunguna makamancin wann sai su aje bazasu sha ba Wanda haka barazana ne ga lafiyar jaririn dake cikinsu.” Cikin murya irinta mai kuka ta katse Hajja “Amma ni bana son jaririn Hajja… Bana so na haifosa dan Allah..” Ta k’arashe cikin rawar murya Hajja ta girgiza Kai had’ida kamo hannayen Ummul “Na haneki da fad’in kalmar nan Ummul.. Ke din nan bada jimawa ba zaki zama mahaifiya da izinin Allah. Duk abinda kike furtawa ki sani na tasiri Akan D’anki. Zama iyaye ba abu bane mai sauk’i. Daga zaran ance yau Kin zama uwa toh ki sani rayuwarki ta canza, dole ki zama mai kula da taka tsantsan kan abubuwan da kike furtawa musamman kalaman da suka danganci ‘ya’yanki dan bakin mahaifiya sosai yake tasiri. Sann duk wani decision da zakiyi making da ya danganci rayuwarki ki sani dole wann D’an nada wani kaso na hakki a cikinsa.. Ke din wani nauyi ne da amana yake gab da hawa kanki wanda yasa nake tunanin lokaci yayi da zaki waiwayi gida Ummulkhair.” Ummul ta d’ago a d’an razane tana dubanta. Sai ta soma girgiza Kai “A’a.. Dan Allah a’a Hajja.. Bazan iya ba.. Bazan iya tunk’aransu a haka ba.. Wllhi bazan iya ba.. Dan Allah ki barni a nan nidai bani so su ganni da wann cikin..” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka. Hisham da fitowarsa kenan da niyyan yima Hajja Sallama dan a ranan yake son komawa Abuja kafin ya ida shirya yanda zaiyi da cikin Ummul nan ya lab’e bakin k’ofa yana sauraronsu. Cikin zuciyarsa yake fad’in wato Hajja ta shirya mayar da Ummul gaban iyayenta kenan. Komawan Ummul gida kuma na nufin Haidar zai sameta. Ai kuwa bazai tab’a bari hakan ya kasance ba. Bazai tab’a bari Ummul da Haidar su sake crossing path ba tareda ya samo solution d’in yanda zaiyi da D’an Haidar dake cikinta ba.. He needs to make his move fast kafin Hajja ta b’ata masa komai.. Komawa Abuja bata gansa ba har sai ya samo ma Kansa mafita. Sai ya samo makomar cikin Haidar dan bazai tab’a bari duk sadaukarwar da yai su tafi a banza ba. Komawa da baya yai yana tunanin abun yi. Dole ya dakatar da Hajja. Kai tsaye waje ya fice yana kiran Anisa a waya. Nan yake la barta mata zancen Hajja da Ummul da ya sinkaya. Anisa ta mik’e tsaye a firgice tana girgiza Kai “No… No way Hisham… We can’t let this happen.. Kaga abinda nake fad’a maka ko.. Wann shine abinda nake tsoro.. Idan har Ummul ta koma gida toh kuwa shakka babu tamkar ta koma hannun Haidar ne dan a halin yanzu Haidar baida wani aiki sai zarya tsakanin Abuja to Kano. Bazaka bar Ummul ta isa Kano da wann cikin ba. Do whatsoever it takes ka dakatar da aukuwar hakan.. Hisham dole cikin nan ya salwanta dan cikan burinmu. Bamu tafi da nisa har zuwa nan da wani d’an tayi ya ruguza mana shiri ba.” Hisham ya bud’e marfin motarsa ya shige yana shafa Kai had’ida furzar da huci “Kaina ya k’ulle Neesa.. I don’t know what to do anymore.. Knowing Hajja bazatai k’asa a gwiwa ba har sai ta damk’a Ummul ga iyayenta.” Ya kuma furzar da huci yayinda Anisa taci gaba cikin hasala “Toh ai duka laifinka ne. Da ace ka d’auki shawarina ka tistiyesa da bamu kawo wann gab’ar ba.. Da ba wann zancen muke yanzu ba.” “Are you insane Neesa. Bakisan had’arurrukan dake tareda abortion bane ko me.? Ta ya zan jefa rayuwar Ummul cikin had’ari bayan duka abinda nake dan na mallaketa ne. Wann banzan Haidar d’in ne ya b’ata komai da ya kasa hak’uri har saida ya tabbata ya d’irka mata ciki. Idona idonsa sai na shak’esa tinda ya keta gonata dan Ummul tawa ce ni na fara saninta tun kafin ya santa. Ni na fara sonta tun kafin ya sota. Ni na fara niyyan Gina rayuwar Aure mai tsafta tareda ita kafin shi da uwarsa su k’ulla Auren yaudarar da yai da ita.. Idan sunana Hisham Haidar ya gama rayuwar Aure da Ummulkhair.!” Anisa ta furzar da huci “Duka wad’ann bazasu taimakemu ba Hisham. We are running out of time. We need to act now kafin Ummul ta isa Kano.!” Hisham yai shiru yana sakin huci yana fidda tururi shi kad’ai. Idonsa naga kallon gabansa daga nan yanda yake zaune cikin motar. Bai kuma ceda Anisa komai ba sai huci da yake fiddawa har saida Anisa tai tunanin ko ya aje wayar ne. Anisa ta kuma ce “Hello.. You there.?” Gungun matasa rik’eda makamai dangin dogayen wuk’ak’e da Hisham ya hanga ya sanyasa sakin murmushi. Duk abinda matasan suka gani sai Sun saresa da makami ba mutum ba dabba. Kai ko abin hawa suka gani a layin sai sun rabza masa makaman hannuwansu. Lokaci guda yace da Anisa “I have a plan.” Ya fad’i yana mai sakin murmushi kafin yaci gaba “I will surely ruin Hajja’s plan of taking Ummul back to her parents.” Cikeda k’osawa Anisa tace “Meye shirin naka.?” Hisham ya murmusa “‘Yan sara suka.!” Cikin rashin fahimta Anisa tace “Yan sara suka kuma.?” Hisham Ya kuma murmusawa “Just wish me well..!” Yana ida fad’in haka ya katse kiran ya mik’e da sauri ya fice daga motarsa. Aiko yana ficewa daga motar matasan nan suka k’araso a guje suka dinga dukan motar da makamai har saida suka farfasa glass. Shi ko Hisham a guje ya shige gida dan kar su saresa ko suyi ajalinsa. Yana shigewa ya sad’ad’a a hankali ya shige kitchen. Wuk’a ya d’auka zuciyarsa na bugawa da sauri. Ya rintse idanunsa yana bama kansa k’warin gwiwar abinda yai niyyan yi “I have no other option. Bazan iya barinki ma Haidar ba Ummul..!” Ya fad’i yana mai dab’a ma Kansa wuk’ar a gefen cikinsa. Ya rintse idonsa da k’arfin gaske sabida azaban zogin da yaji. Ya tafi da sauri cikin d’ingishi yana danne gefen cikinsa yanda yai stabbing Kansa jini na fita. Waje ya fito had’ida jefar da wuk’ar cikin hanyar ruwa har lokacin matasan basu daina ta’addanci da tada hankalin Al’umma a wann layin ba. (Allah ka shirya mana Al’umma.) A gigice ya turo k’ofar gidan yana bin garu yana rik’e gefen cikinsa yana tamke ido alamun zogi. Lokaci guda yake rangad’a ma Hajja k’ira da k’yar. Daga Hajja har Ummul a birkice suka fito jin irin yanayin da Hisham d’in ke ambato Hajjan sann sunji hayaniya ya kacame unguwar Wanda hakan yasa Hajja zama tareda Ummul a d’aki dan kar ta razana. Jini suka gani na bin gefen cikin Hisham da tuni ya galabaita yana fad’in “Hajja.. They stabbed me.. Help me..!” Dukansu jikkunansu rawa ya d’auka. Hajja ta shiga salallami cikin tsananin kid’ima “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.! Mai zan gani.? Hisham..!” Sai ta fashe da kuka ta nufesa a kidime tana fad’in “Sun caka ma d’ana wuk’a sun saresa.. Inna’ilaihi wa inna’ilaihi raji’un..!” Ummul ma duk ta kid’ime sai aka rasa mai bama wani baki cikin ita da Hajja ga Hisham dake kwance shame shame yana nishi. “Hajja su waye suka caka masa wuk’a.? Mai ya faru dashi..?” Sai kuma ta nufi k’ofa a guje tana fad’in zata nemo agaji. Duk jikinta rawa yake. Shugaban committee na unguwar ne da wasu maza kusan biyu suka biyo bayan Ummul suka shigo gidan. Duk a rikice. Suna shigowa suka nufi yanda Hisham yake kwance shame shame ga Hajja gefensa sai hawaye take tana k’arfafa masa gwiwa da fad’in zai sami lafiya in sha Allah. Shi kuwa sai nishi yake mai nuni da yana jin jiki “Hajj..Hajja ki yafe mun.. Ki yafe mun Hajjah.. Mutuwa zanyi..!” Ta kuma matsan k’walla hannunsa rik’e cikin nata gam take fad’in “Ka daina fad’in haka D’ana. Zaka samu lafiya..” muryarta Ya sarkafe sai rawa da jikinta yake.. Daidai lokacin yan committee suka ciccibi Hisham da zummar kaisa asibiti. Hajja da Ummul suka take masu baya cikeda tashin hankali. SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!* *52* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* A gaggauce aka wuce da Hisham Emergency yanda aka soma kokarin ceto rayuwarsa. Idan kaga Hajja sai ta baka tausayi. Batada kowa sai tilon D’anta Wanda bata fata ta rasa shi. Ummul ma karfin hali kawai take dan sosai daga Hajja har Hisham sosai suka bata tausayi. Mutane ne masu mutunci, karamci da sanin darajan D’an adam. Bata fata wani abun tashin hankali Ya samesu. Suna tareda ita a lokutan k’uncinta da tashin hankalinta dan haka Ya zama dole ta aje nata damuwar da tashin hankalin ta ji da nasu damuwar. Fatanta Allah ya tashi kafad’un Hisham ya bashi lafiya sann ya sassauta ma Hajjah. Jiki a sanyaye Ummul ta k’araso yanda Hajja ke zaune bayan an shige da Hisham surgery. Hajja ta d’ago ta dubeta sai ta k’ak’aro murmushi na karfin hali tace “Ya kamata ki koma gida haka nan ki huta kema ba k’oshin lafiya ne dake ba. Stress ba naki bane.. Ya kamata ki samu hutu.” Ummul ta kamo hannayen Hajja tana girgiza kai “Bazanje ko ina ba Hajjah.. Ina nan tareda Ke in sha Allah.. Har sai munsan halinda Yayana Hisham ke ciki.” Hajja ta k’ak’aro murmushi tana duban Ummul d’in. Sai ta goge hawayen da Ya gangaro mata “Shi d’aya Ya rage mun.. Yazo cikin rayuwata a lokacin da nai zaton Babu wani k’ofa na haske da zai kuma budewa cikin rayuwata.” Sai ta d’an murmusa “I named him Hisham. Meaning generous. Sabida Ina so ya girma da zuciya mai yalwa. Zuciya mai son bayarwa da taimakawa cikin duk halinda ta Sami iko..” Ummul ta jinjina kai cikin kokarin k’arfafa ma Hajja gwiwa “Shid’in ya dace da sunansa Hajja. Tabbas yanada zuciya mai kyau mai kwad’ayin taimako ba tareda ta nemi wani abu in return ba. Ni shaida ce akan irin taimakon sa a gareni.. Shid’in D’a ne da ko wace uwa zatai Alfaharin samun irinsa. You are blessed to have him as a child Hajja.. A lokutan da wasu ‘ya’yan sukan zama jarabawa ga iyayensu wasu ‘ya’yan abun alfahari ne da sanyin idaniya ga iyayensu. Ked’in Lallai kinada sa’a Hajja.. Babu abinda yafi buk’ata daga gareki a halin yanzu face addu’o’in ki gareshi.” Ta k’arashe murmushi da siririn hawaye saman fuskarta. Hajja ma murmushi take tana hawaye tana jin dadin kyawawan shaidan da akai ma tilon D’anta musamman idan ta tuna mahaifinsa ya ciresa daga cikin ahalinsa Tun baizo duniya ba. Sai jikinta ya d’anyi sanyi. Ta soma jinjina Kai a hankali tana fad’in “A koda Yaushe fata na shine na kasance mahaifiya da zai alfahari da ita. Mahaifiya da zata sauk’e nauyi da hakkinsa da ya ratayu wuyanta..” Sai Muryarta ya soma rawa “Ina tsoro Ummul.. Ban sani ba.. Ko na gaza a wani fannin domin shid’in Ya girma baisan mahaifinsa ba..” Tausayinta ke ninkuwa cikin Zuciyar Ummul. Tai saurin girgiza kai “Ke mahaifiya ce da ko wani D’a zai alfahari Ya kirasa da mahaifiya Hajja.” Sai ta murmusa “Meyasa ma Ya Hisham bazai zama mai kirki ba bayan ya kasance D’anki.?” Murmushi Hajja Tai dan ta kula so take ta dan kwantar mata da hankali. Ummul ta matso jikin Hajjan tana kuma fatan sauk’i ma Hisham. Tana kwance jikin Hajja takai hannu a hankali tana Shafa nata cikin. Batasan labarin Hajja ba. Sann bata san abinda ya faru da mahaifin Hisham ba. Amma Hajja ta zama tamkar inspiration d’inta. Ita d’in ta raini D’a kaman Hisham. D’an da kowa zai alfaharin samun kaman shi. Sai taji k’warin gwiwa na shigarta akan cikinta. For the first time da taji tana so ta haifo abinda ke cikinta koda bazata tab’a sanar da mahaifinsa ba. Koda bata k’aunar mahaifinsa.. Zatai komai ma D’anta da izinin Allah. Zata zama masa uwa ta zama masa uba kaman yanda Hajja ta jajirce akan D’anta. Anyi aiki ma Hisham kuma aiki yayi kyau cikin ikon Allah. Hajja ta shigo ta tadda shi tareda ‘yan committee suna jajanta masa abinda ya faru da tambayarsa yanda abin ya kasance. Hisham dake kwance da d’inkakken ciki nan yake labarta ma yan committee cewa yaje taimakon wani yaro ne suka soka masa wuk’a. Hajja ta lumshe idonta tausayi da k’aunan D’an nata na ninkuwa cikin zuciyarta. Allah sarki, shidai kamar ko Yaushe cikin taimakon Al’umma yake. Ashe silan tsautsayin da Ya auka masa taimako yaje kaman yanda tai tsammani. Ta k’araso suna gaisawa da shugaban committee yanda yake sanar dasu ana kan k’ok’arin kama yaran dan a hukuntasu sabida rashin hukuntasu da ake yasa suke abinda suka so cikin Al’umma. Hajja ta girgiza kai tana amsawa. Ta k’arada “Allah dai ya shirya mana zuri’a amma al’amarin dad’a ta’azzara yake.” Shugaba ya girgiza Kai yace “Sai ka rasa ina matsalar take. Shin iyayen ne ko kuwa dai halin yau da muka tsinci kanmu ciki ne. Wai nan abinda suka fito sunayi na tada hankalin Al’umma sunansa shara. Ko mai suka gani sai Sun lahanta.. Yara k’anana samari da basu wuce ace suna makaranta ba.” Hajja ta jinjina kai “D’an yau ne ka haifesa baka haifi halinsa ba.” Ya jinjina Kai “Tabbas akwai jarabawa a wasu lokutan kuma sakaci na iyaye. Mutum karma ka haifo yaran da bazaka iya kula dasu ba yaran da bazaka iya basu tarbiya. Tarbiya Ya k’unshi kula da d’aukan nauyi tareda sauk’e wasu hakkoki da suka ratayu wuyan iyaye. Sai kaga mutum matansa hud’u d’akuna hud’u gareshi wani ma gidan haya ne. Kai shekaran

Chapter 48 of 64