love you my sweet.. sweet..!” Bata k’arasa ba Haidar yai karaf yace “Your sweet mons…” Bata bari yakai aya ba tai karaf tace “My sweetlove..” Ta k’arashe tana mai manna masa kiss a lips d’insa. Daga haka ta zame ta fice cikin sauri tana murmushi ma Haidar da tuni Ya daskare yana shafa lips d’insa.
**
Tarewarsu da sati biyu ake bikin sunan Baba Ali a nan Abuja. Su Mommy suka hada nasu taron nan gidan Daddy. Ummul tayi waya da yanuwanta duk zasu samu halarta harda Babbar Yayarsu Aunty Salima wacce tuni ta baro yaranta gida wajen Mama Tani dan yaran ne kawai zasu samu halarta banda iyayen.
Sadis ne Ya tafi ya d’aukosu ana gobe taron sunan. Azeema na gaba yayinda Khulsum, Badia da Aunty Salima ke baya. Aunty Salima tana hankalce da Sadis da Azeema tin tasowarsu Har kawo isowarsu. Ko ba’ace ba zata iya cewa ta fahimci meke wakana tsakanin su biyun.
Sanda suka iso Salima ta tsare Azeema da ido bayan sunyi Sallama da Sadis Sun nufi cikin gidan.
Salima ta girgiza kai kad’an tana duban Sadis dake kuma waigowa yana satan duban Azeema. Itama Azeema sai murmushi take tana waigawa.
Salima ta tsareta da ido tace “Ke Azeema.. Wai meke faruwa ne a nan..?”
Azeema tace “Me fah Aunty..?”
Salima Tai mata nuni da Sadis da tuni Ya nufi mota tace “Shi nake nufi.”
Murmushi Azeema ta saki tana wani juya ido “Laa wai Sadis.. Ba komai fah Aunty Salima.. Kawai mutunci muke.”
Salima ta jinjina kai tana fad’in “Eh lallai fah mutunci.. Toh idan Tai tsami munji mun gani.” Ta k’arashe tana take ma Khulsum baya.
Badia kaw dake nan daga waje tin bayan isowarsu tana nan zaune gefen flowers dake jikin k’aton shataletalen dake tsakiyar gidan. Wayar Ummul take amsawa yanda take sanar da Ummul d’in Sun iso amma Sun sauk’a gidan Daddy. Ummul kaman zatai kuka take fad’in meyasa basu taho sun sauk’a gidanta ba.
Badia tace “Ayya ‘yaruwa kiyi hakuri wllhi tin kafin mu taso Mommy ke ta waya tana fad’in tuni an shirya mana masauk’i.. Kinsan bazamu iya ce ma Mommy a’a ba.”
Daga d’aya b’angaren Ummul kaman zatai kuka tace “Toh shikenan.. Gobe muma in sha Allah da wuri zamu shigo.. Idan mun zo Zan rok’i Mommy nasan zata amince mu taho tare.”
Badia tace “Toh shikenan Allah Ya kaimu goben. Kinga bara na shige ciki sauk’armu kenan.” Sukai sallama da ‘yaruwar tata a daidai sanda wata k’atuwar b’akar jeep ta shigo gidan.
Badia ta soma tafiya kenan taji wata murya na babban mutum mai cikeda kamala na mata Sallama.
Ta waigo cikeda girmamawa tana amsawa. Dan idan dai bai kai Abbanta a shekare ba zaiyi kusansa dukda hutu da jin dad’i na b’oye tsufa.
Bayan ta gaida mutumin sai Ya k’arada “Allah sa dai ‘yar gidan ce ke.?”
Ta d’an girgiza kai kad’an “A’a ni ba ‘yar gidan bace. Amma ciki zan shiga yanzu.”
Ya murmusa yana jinjina kai “Toh da Allah idan kin shiga kimin iso wajen Maigidan. Dan nayita neman layinsa bana samu.”
Ta d’anyi jim sai tace “Toh.. Wanene zance.?”
Mutumin yace “Kice Alhaji Gimba ne.”
Ta jinjina kai tana mai amsawa kafin ta shige.
Alhaji Gimba yabi bayanta da kallo murmushi saman fuskarsa yana jin wani abu na fuzgarsa.
Koda Daddy ya fito ya tadda Alhaji Gimba tambayar da Ya soma yi ma Daddy shine wacece wann yarinyar da Tai masa iso.?
Daddy ya d’anyi jim sai Ya dan girgiza Kai kad’an yace “Bansan wacece ciki ba amma dai ina tsamman d’aya daga cikin ‘yanuwan Matar Haidar ne..” Sai Daddy ya dan girgiza kai “Amma meke faruwa..? Allah yasa dai lafiya.?”
Alhaji Gimba yai saurin girgiza kai “Lafiya sai alkhairi.. Kawai dai.. Naga iri gidanka ne abokina.”
Da mamaki Daddy ke dubansa. Sai Ya girgiza kai kad’an yace “A’a Gimba.. You can’t be serious. Bazaka mana haka ba.”
Alhaji Gimba yace “Wllhi I’m serious Abokina.. Ai kasan ban tab’a zuwa maka da magana makamancin wann ba. Ba irin k’ok’arin da bakayi ba ganin na sake aure Tun bayan da na rasa iyalina amma banyi ba. Yau nazo maka da irin batun da kake son ji kana nema ka k’aryatani.”
Daddy ya girgiza Kai “Ni ba k’aryataka zanyi ba amma matar d ka d’auko d’in ne ban tsammaci haka ba. Bayan kasancewarta k’aramar yarinya ka fad’a mun ta Ya zamuje muna zubda gwiwoyin mu a yanda Haidar keyi. Ta ina zamu fara jera kafad’a muna surkunta a yanda Haidar keyi.?”
Alhaji Gimba Ya murmusa yace “Abokina kenan. Naga dai ba haramci cikin abinda nake son aikatawa sai alkhairi in sha Allah. Sann Tafiyar Haidar daban namu daban.. Kaman yanda kaje ka nemo ma Haidar haka zaka tafi a nemo min matuk’a na samu yarda da amincewar yarinyar.
Daddy ya girgiza Kai yana fad’in “Gaskiya Gimba ni baza’ayi wann kayan kunyan dani ba. Kaje can ka nemi aurenka ba hannuna.”
Alhaji Gimba Ya dan dara yana kuma fad’in lallai sai Daddy ya shige masa gaba a neman auren da yake.
Washe gari ta kama ranar taron sunan Baba Ali da Kakaninsa na Abuja suka shirya. Sann ranar mutanen SouthAfrica wato Hisham da Anisa ke dawowa gida Nigeria.
Hisham Ya kaikaito Ya dubeta sanda jirginsu Tai landing a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Airport. Shu’umin murmushin nan nasa ne saman fuskarsa “Mai ciki. Tashi ki daina baccin haka mun iso.”
Wani Uwar harara Anisa ta watsa masa tana jin kaman wani haraswan zata kuma dan tayi amai cikin jirgin yafi sau uku.
Huci take tana fad’in “Na tsaneka Hisham..! Allah ya isa fyaden da ka dinga mun.!”
Hisham yaci gaba da murmushi yana shafa hab’arsa “Daga baya kenan… Na Miki na k’arfi sau d’aya amma duka sauran da yarda da amincewarki akayi..!” Cikeda gargadi yaci gaba “Kuma bari kiji na fad’a Miki wllhi kikayi gigin cire cikin nan ko kika bari wani abu ya samu cikin nan..!” Sai ya girgiza Kai yana dubanta “I don’t know what I might do to you Anisa.!”
Murmushin takaici Anisa take tana dubansa “I can’t believe I’m three months pregnant with your child Hisham. A monster like you bai cancanci zama mahaifi ba.!”
Murmushi Hisham ya kumayi yana dubanta kafin ya sakalo hannunta cikin nasa “You won’t do anything foolish Anisa..! You will face them and act cool..!” Ya k’arashe yana mai finciko hannunta suka nufi arrivals.
Can ya hangi Mota mai d’aukeda plate number na Company d’insu. Ya rik’o hannunta yana fad’in our ride is here.
Babu wata wata suka shige bayan motar Hisham na kuma jero ma Anisa warnings. Tana fad’in yayi kad’an ya sakata yin abinda batai niyya ba. Haka akaita shera gudu dasu sai masifa suke tsakaninsu sam bama su kula da waye driver din nasu ba dan p cap ne akansa.
Saida akai nisa sukaga driver ya canza hanya ya d’auki wani hanyar.. Hisham ya fara fad’in “Lafiya..? Wane hanyar kake bi.. Hey who are you.. Why can’t you turn back..!” Hisham ya k’arshe yana k’ok’arin fizgoshi saidai tuni driver d’in ya murda AC din motar take wani abu kaman hayak’i ya gauraye cikin motar. Suka soma tari gaba d’aya idan ka d’auke driver d’in da hancinsa ke rufe da nose mask..
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*62*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Suna zaune gaba d’aya parlorn Hajja a sama, hira suke na yaushe rabo cikeda nishad’i. Ga gidan tuni Ya soma cika sakamakon taron da zaayi da yamma. Dan har wasu dangi daga Maiduguri Sun samu hallara. Koda Haidar Ya Lek’a yaji hayaniyar mutane sai bai haye saman ba yai zamansa a parlorn k’asa. Wayarsa ya Ciro Ya tura mata sak’o.
Ana tsaka da hira sak’on Haidar ya shigo ma Ummul.
_I’m hungry_
Ta karance sak’on sai ta soma waige waige. Ta tura masa reply
_Where are you_
Ya mayar mata da amsa
_Downstairs.. Waiting for you_
Mik’ewa Ummul Tai da zummar barin wajen Salima tace ina zata suna tsaka da hira. Ummul ta d’an juya ido tana mata alama da k’asa.
Badia tai gyaran murya tace “Haba Aunty Salima sai kin mata tonon silili ne. Wajen Oga Haidar zata.”
Salima ta jinjina kai “Haka kuma. Toh a dawo lafiya..”
Murmushi kawai Ummul tai tasa kai ta fice. Tana ficewa kuwa Salima ta dawo kan Azeema tana fad’in sai ta fad’a meke tsakaninsu da Sadis d’in can. Nan Badia ta saka baki tana fad’in itama ta kula tsaf da su biyun. Azeema kaw sai cewa take ita ba komai tsakaninsu fah sai mutunci.
Ita dai Khulsum kallonsu kawai take jikinta duk a sanyaye ba tareda tasan dalili ba. Bata san meyasa ba amma haka kurum taji tunaninsa Ya zo mata. Tinda ya koma makaranta bata sake ji daga garesa ba. K’ila ma Ya mance da ita. Saurin kwaban zuciyarta tai da fad’in ‘Toh ke ina ruwanki dashi.. Meyasa zakiyi tunaninsa Har haka.. Ya mance da ke kema ki mance dashi.’ Saurin mik’ewa Tai ta bar wajen cikin k’ok’arin kawar da tunanin.
A parlor Ummul ta iske Haidar. Sanye yake da jampa ruwan k’asa harda hula. Ya turo hular saman fuskarsa had’ida kishingid’a cikin kujeran. Tai tsaye tana dubansa murmushi saman fuskarta. A hankali take takowa Har ta iso kusansa. K’amshin ta ne yai masa Sallama. A hankali yasa hannu Ya janye hular. Ya bud’e lumsassun idanunsa yana dubanta. Tayi kyau cikin leshi golden brown color. Dinkin sosai yai mata kyau Ya zauna jikinta kaman wacce bata jima da haihuwa ba.
Ya bud’e mata hannayensa daga nan yanda yake kishingide “Come here.”
Ta d’an fito da ido tana dubansa. Sai ta soma ‘yan waige waige.
Haidar yace “What..! Taho mana.”
Ta d’an langab’e kai kad’an “Wasa kake.. Ka mance ina muke ne.”
Gyara zamansa yai kad’an had’ida furta “Fine.. Kin sama min mai zanci.?” Yai maganar yana mai janyo hannunta.
Ta d’an girgiza kai “Gidan gaba d’aya cike yake.. Barin kira kitchen naji mai suke dashi.”
Tabe baki yai kad’an “Banson abincin Chefs din gidan nan.. Sun Faye cika yaji…”
Ta d’an marairaice fuska “Toh ya kake so ayi Rankaidade.? Mu fah bak’i ne a nan. Kai hakuri kaci haka.. Idan munje gida sai na girka maka abinda kake so.” Cikin sigan lallashi take maganar.
Sosai suka birge Hajja har taji dama bata sauko parlorn ba dan kar ta katse musu soyayyarsu.
Ummul ta d’an matsa baya kad’an daga kusan Haidar tana ma Hajja sannu da sauk’owa. Haidar ma gaisar da Hajja yai kafin daga bisani Hajja ke musu tayin Burabusko miyan taushe da ta dafa ma Daddy. Ta k’arashe tana fad’in Ummul ta taho ta kawo ma Haidar.
Haidar ya dan shafa kansa kafin ya katse hanzarin da fad’in “But.. I don’t eat Burabusko..”
Hajja ta dan murmusa tace “Lallai kace zamu maida Kai Yerwa Haidar. Ya zaace Kanuri bai cin Burabusko.? Kuma naga favorite din Daddy kenan. Ya kamata ace ka iya ci.”
Daga k’ofa suka sinkayo murya na fad’in “My brother is more Shuwa arab… Abincin larabawa yake ci.”
Gaba d’aya suka waigo suna duban mai maganar ba kowa bane illa Hilal.. Ya kara girma da k’warjini kaman ba shi ba.
Ya k’araso cikin parlorn yana gaida Hajja da Ummul lokaci guda Ya k’araso ga Haidar suka gaisa Hilal na hugging d’insa kad’an na yaushe rabo.
Hajja ta shige ta basu waje abinta bayan tayi ma Hilal lale da zuwa.
Haidar ya dubi Hilal “Kai kuma daga ina kaman an jefo ka.?”
“Daga gida Kano.. Tare muke da Ammi.. I arrived in the country yesterday.”
Haidar ya jinjina Kai yana tambayarsa ya sch. Allah sa dai ya tab’uka abin arziki wann karon. Ya k’arada “Kasan ban tab’a ganin unserious human being irinka ba. Gaba d’aya baka d’auki rayuwarka da mahimmanci ba Hilal.”
Hilal ya Dara kad’an “Sanin da ka mun da ne D’anuwa. Well, I can finally say it with full chest.. I’m a graduate now. Kana magana da cikakken accountant ne a nan.”
Jinjina Kai Haidar yake yana dubansa “Idan gaskiya kake fad’i, I’ll hire you.”
Suka dan murmusa gaba d’aya. Hilal na fad’in Lallai shi D’angata ne gashi daga dawowa ya samu aiki.
Ummul da ta b’ace b’at kaman bata a wajen muryar Hajja ta sinkayo tana fad’in maza ta taho ta shige kitchen dinta dake bangarenta ta samar ma Haidar abinci. Dan ta kula kaman abincin matarsa yake son ci.
Hilal yai karaf ya dakatar da Ummul da fad’in “Addarmu ina Baby yake.? Ni fah shi nazo gani.. Naji ance takwara akai ma Yaya na Haidar. Meyasa ba’a min ba.
Haidar ya dalla masa harara “Waye zai maka takwara.? Ba dai ni Haidar ba.”
Hilal na murmushi yake Shafa Kai “I’m a changed person fah.. Zaka sha mamaki. Ni fah yanzu na zama responsabile Human being.. Na jima da daina sallah ba alwala..”
Haidar ya kuma aika masa wani duba dan baiso a d’ago yarintar su gaban Ummul.
Murmushi Ummul take tana fad’in bari ta kawo masa yaron. Saidai kafin tai shiru ta hangi su Khulsum dasu Badia suna sauk’owa downstairs ga Baba Ali cikin hannun Khulsum d’in. Sam Khulsum bama ta kula da mutumin dake zaune gefen kujeran Haidar ba.
Shi kaw Hilal mutuwar zaune yai yana dubanta. It’s been long.. So long rabonsu da su saka juna a ido.. Ta k’ara masa girma da kyau.. Saidai ya hangi wani abu mai Kama da salihanci saman cute grumpy face dinta.
Sam bata kula ba sai wasa take ma Baba Ali. Bataji sanda Ummul ke introducing Hilal masu Aunty Salima. Bata Ankara ba sai sinkayo muryarsa tai yana fad’in “May I please.. see him..”
Cak ta dakata da abinda take bugun zuciyarta na k’aruwa. Ta ina zata mance muryarsa. Ta d’ago a hankali tana dubansa. Shi d’in ne dai.. Saidai wann karon ya k’ara mata girma fiyeda sanin da tai masa a baya. Wann sumar tasa mai laushi da tsantsi irinta asalin k’abilar shuwa arab ya tara shi wann karon. Harda jiki ya k’ara saidai girman yasa ya k’ara duhu kad’an. Har Hilal ya amshi Baba Ali daga hannunta bata dawo daidai ba. Sam bama ta kula har su Azeema Sun wuce sashen Mommy ba. Gaba d’aya sai ta daburce.. Ga Hilal kusan k’ofa yake tsaye rik’eda Baba Ali yana fad’i ma Haidar yaron dashi yake kama ba da Haidar ba. Harda cewa za’a basa yaron he’s his Godfather.
Ai kawai sai Khulsum tabi bayan Ummul ta nufi kitchen.
Ummul ta dubeta da mamaki yanda ta shigo duk a daburce “Ke kuma fah.? Mai kikeyi a nan.. Na zata kun tafi sashen Mommy gaba d’aya..”
Kasa amsata Khulsum tai sai ma dibi dibi da take. Ummul dai d’an tabe baki tai kadan Ta d’auko carrots zata pilling Khulsum tai karaf ta amshe tana fad’in zata fere mata.
Ummul ta tsareta da ido yanda take komai sauri sauri ba natsuwa. Ta aje chopping board din dake hannunta tana kuma tsare Khulsum da ido “Khulsum.” Ta k’ira sunanta cikeda kulawa.
Khulsum ta amsa tana dubanta.
“Fad’a mun.. Meke faruwa ne.?”
Khulsum ta d’an girgiza Kai “Ba.. Ba komai.. Mai kika gani Adda Ummul.?”
Ummul ta jinjina Kai “Idan zaki b’oye ma wani nidai kinsan bazaki b’oye min ba.. Ki fad’a min meke faruwa.?”
“Da gaske ba komai fah Adda Ummul..”
Daidai lokacin suka soma sinkayo kukan Baba Ali daga parlor.
Ummul ta zame apron din dake jikinta tana nuna Khulsum “Ni dake bamu gama ba.. K’arasa fere mun carrot d’in ki yankasu k’anana ina zuwa.”
Daga haka Ummul ta fice sauri sauri.
Ta tadda Hilal ya mika yaron ma Babansa yana fad’in ya kamata ya sanshi dan shine Godfather d’insa. Ba maganan k’iwa tsakaninsu.
Haidar ya amshe yaron yana fadin “Come to Paapa.” Ya shiga jijjiga yaron yana fad’in yai shiru Maama is here. Daidai sanda Ummul ta zauna gefen Haidar tana k’ok’arin amsar yaron.
Yanda gaba d’aya attention d’in iyayen ya koma kan yaron sosai hakan ya birge Hilal ya kuma basa sha’awa. Sai ya dan murmusa yana k’ok’arin barin parlorn. Hanyar da yaga ta nufa yabi. Nan ya hangeta tsaye cikin kitchen din tana dicing carrots. Ya jima yana dubanta sihirtaccen murmushi saman fuskarsa kafin Ya soma takowa cikin kitchen din a tsanake.
Sam bataji alamun mutum ba sai taji gyaran murya daga bayanta yana fadin “Hello.. Excuse me..”
Ta dan razana Wanda hakan ya sata saurin aje knife d’in da take yanka carrots din dashi had’ida rintse idanunta alamun ta razana.
Hilal ya dan leko yana duban fuskarta. Murya a hankali yace “Sorry..! I didn’t mean to scare you.”
Huci Khulsum keyi ba tareda ta dubesa ba. Lokaci guda tana dunk’ule knife din cikin hannunta. A fusace ta waigo tana fad’in ya kuwa bazataji tsoro ba mutum yana shiga waje ba Sallama kaman goyon yahudu. Tana maganar a fusace tana juya wuk’ar dake cikin hannunta.
Kallon yanda take juya wukar kawai Hilal yake ya d’ago hannayensa sama alamun surrender lokaci guda yake jada baya yana fadin “Easy.. Easy..!” Yanda yake ja da baya kaman zai auna a guje sai ya kuma tsorata Khulsum. Ta soma waigawa baya tana duba mai ya gani yake shirin guduwa. Hilal bai daina jada baya ba ai kawai sai itama ta nufo k’ofa a guje dan ta zata wuta ne ya gani a kitchen din ko wani abu mai Kama da haka.
Kafin tai aune Hilal ya tare k’ofan kitchen d’in wanda hakan ya hanata k’arasawa. Bai daina nunata ba bai daina daukan saiti na gudu ba bai daina furta easy ba.
Ta kuma waigawa cikeda tsoro wann karon “Wai meye ne.. Meye ka gani.?”
Ya nuna mata hannunta mai rik’eda knife “Pleae keep that away..” Yai maganan yana rik’eda k’ofar kitchen din gam. K’afarsa d’aya na waje d’aya na kitchen din.
Sai ta d’ago wukar dake cikin hannunta tana kallo. Gajeren tsaki tai had’ida sauk’e ajiyan zuciya kafin ta koma bakin aikinta.
Hilal ya murmusa kad’an kafin ya kuma takowa gareta. Wann karon Sallama yai. Kaman bazata amsa ba sai kuma ta amsa da kyar.
Hilal ya k’arada “You haven’t changed a bit.” Ya fad’i da murmushi saman fuskarsa. Bata ko dubesa ba balle ta kulasa. Saima ci gaba da tai da abinda take.
Ya dan langab’e Kai yana dubanta “Wai ko darajan gaisuwa bazan samu ba balle sannu da zuwa.?”
Ta dan dubesa a dak’ile sai ta tabe baki had’ida janye idonta “Wanda yai Sallama idan zai tafi shi ake ma sannu da zuwa.”
Hilal ya dan murmusa dan ya tuna sanda zai tafi bai mata sallama ba. Dikda lokacin itama tana Jigawa gidan Inna Dije amma ko a waya bai kira ya sanar da ita tafiyarsa makaranta ba. Sann tinda ya tafi bai sake nemanta ba. Alk’awari yai ma Kansa zai natsu yai abinda ya kaisa once and for all ya k’arasa karatunsa ko dan ya share hawayen Amminsa ya kuma tabbatar ma Abbansa bazai sake asaran kudi Akan karatunsa ba. Above all, zaiyi ne ma Kansa ta yanda idan yazo ma Abbansa da batun Aure zai tsaya ya sauraresa.
Gyaran murya ya d’anyi yace “Lallai ban kyauta ba amma kiyi hak’uri.” Ya d’anyi shiru kafin ya ambaci sunanta cikin wane irin siga da ya haifar mata da sanyin jiki.
“Khulsum.”
Ta d’ago ta d’an dubesa. Hilal yaci gaba “Tafiyar da nai ba Sallama yanada dalili wanda nasan idan muka samu time na miki bayani zaki fahimta.Ki yarda Dani nayi hakan ne for us.”
Sai ta d’an kuma dubansa. Yayinda Hilal yaci gaba da jinjina Kai “Believe me, Ban manceki ba daidai da dak’ik’a guda. A koda Yaushe kina nan a nan..!” Ya k’arashe yana nuni da b’angaren k’irjinsa yanda zuciyarsa take bugawa. Yayinda Khulsum taci gaba da dubansa jiki a sanyaye. Kyakkyawan murmushi saman fuskar Hilal yaci gaba “I never stopped loving you my cute cute miss grumpy.!”
Daidai lokacin sukaji alamun ana shigowa kitchen d’in.
Khulsum tai saurin juyawa tana ci gaba da yanka carrot din sanda Ummul ta shigo kitchen d’in.
Shi kaw Hilal saurin daukan glass cup yai yana fadin “I.. I will have a glass of water.!” Ya k’arashe da murmushi yana daukan ruwan gora dake wajen. Ya dubi Khulsum ya kashe mata ido yayinda Khulsum d’in ma ta bisa da wani kallo sihirtaccen murmushi saman fuskarta.
Ita dai Ummul dubansu kawai take. Ta dubi wann ta dubi wancan har Hilal ya fice sai waigowa yake yana duban Khulsum.
Bayan Hilal ya fice Ummul ta tsare Khulsum da ido wacce ke ta faman sakin murmushi a hankali.
Ummul tai gyaran murya tace “Toh ai ya fice sai ki daina wann murmushin da kike.”
Khulsum ta dan zaro ido “Na’am Adda Ummul..!”
Tsareta Ummul tai da ido sai ta murmusa tana aje Kayan miyan dake hannunta cikin roba a sink “Zama kimin bayani ne dalla dalla yarinya. Bari dai mu k’arasa da kitchen din nan.”
Dan darawa Khusum tai tana fad’in “Adda Ummul ba fah abinda kike tunani bane.”
Ummul tace “Toh ni mai kikaji nace.. Kin Kama kanki tin baaje ko ina ba yarinya..”
Khulsum ta sanne Kai tana dariya.
Bayan Sun gama girkin ne kuma suka soma shirin shagalin. Tuni masu kwalliya Sun iso sunyi mata light make-up da ya matuk’ar mata kyau. Shima Haidar d’in saida ya k’ara shiryawa sabida pictures da zasuyi da jariri. Haka kowa ya dinga santinsu dan ba k’aramin kyau sukai ba. Daga bisani Ummul da jaririnta sukaita hotuna da ‘yanuwa da abokan arziki.
**
Wasa wasa har rana ta kusa k’arewa su Hisham basu iso ba. Har akaci taron shagalin suna aka watse basu Anisa ba dalilinsu.
Izuwa lokacin hankulansu ya soma tashi dan tuni anyi conforming jirginsu ta jima da landing.
Ana haka wayar Sadis ya shigo ma Daddy yanda yake sanar da Daddy sun kalla daga security footage na airport Hisham da Anisa Sun shiga wata mota mai d’auke da fake plate number na Kampaninsu. Akwai possibility din kidnapping dinsu akai daga Airport.
Daddy yaci gaba da karanto Innalillahi wa inna’ilaihi ilairaji’un.
Daidai lokacin da su Hajja da Mommy harma da Aunty Asshe suka shigo parlorn a kid’ime dan tare Sadis da Hilal suka tafi airport binciko abinda ke faruwa kuma tuni Hilal ya kira mahaifiyarsa yayi updating d’inta.
Aunty Asshe kuka kawai take tana fad’in anyi kidnapping su Anisa ne dan ance tun rana jirginsu ta sauk’a ga kuma shaida wani mota da ba’a tantance ba ya d’auke su.
Kwantar musu hankali Daddy keyi da fad’in in sha Allah ba komai dan idan ma kidnappers ne dole zasu kira su nemi ransom kuma ko nawa sukai demanding zai bayar dan ya ceto yaransa.
Girgiza Kai Haidar yake yana duban Daddy “Na tabbata this is one of his games Daddy.. There’s nothing like kidnapping here.. Hisham shi ya shirya wann wasan kwaikwayon. And he used Anisa as a bait.!”
A fusace Daddy ya daka masa tsawa da fad’in “Ka rufe mun baki Haidar.!” Cikin b’acin rai Daddy yaci gaba “Your brother is kidnapped.. Ba shi kad’ai ba harda iyalinsa wacce ta kasance Yaruwarka.! And you are here blabbing nonsense..!” Yaci gaba da girgiza Kai yana duban Haidar cikin rashin yarda “For once in your life Aliyu, call a truce with your brother.! If you can’t do anything to help. Then just shut your mouth and get hell out of my house.! Fitar mun a gida nace.!” Ya k’arashe yana nuna ma Haidar k’ofa cikin tsananin b’acin rai.
Idanun Haidar Sun kad’a sunyi ja yake duban Daddy. Meyasa Daddy bazai yarda dashi ba.! Meyasa idonsa ya rufe Akan d’aya D’ansa.?! Ya soma girgiza Kai yana jada baya lokaci guda ya fice daga parlorn kaman zai kifa.
Mommy tabi bayansa da kallo tana kiransa amma inaa bai tsaya ba. Hajja kaw tashin hankalinta ne ya ninku. Duk yanda taso ta hana zuciyarta yarda da abinda Haidar ke fad’i gameda D’an nata meyasa taji yau d’in kaman ta yarda da Haidar. Addu’a take a cikin zuciyarta Allah yasa Haidar kuskuren fahimta kawai yake ma D’anuwansa. Allah ya bayyana Hisham da Anisa cikin k’oshin lafiya ya warware komai ya kuma kawo k’arshen matsalolin Ahalinsu.
Haidar na fitowa sashen Mommy ya nufa kaman zai kifa. Ya shige su Salima a parlor Wanda tuni suma sunyi jigum jigum dan sunga ficewar su Mommy dasu Aunty Asshe hankali tashe.
A d’aki ya iske Ummul tana bama Baba Ali nono.
“Tashi mu tafi.!” Ya fad’i babu walwala.
Ta dan dubesa da mamaki. Dan tin shigowarsa bata gane yanayinsa ba.
“Ban.. Ban gane ba.. Na tashi mu tafi kuma.? Amma meyasa zamu tafi yanzu.?”
“Kar ki bata mun rai Khairy.! Ki tashi nace mu tafi.!” Ya kuma fad’i cikin tsananin b’acin rai.
Itakam sai taji k’walla na zuwa mata. Ga Baba Ali da tuni ya rigata fara kuka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 60 Chapter of 64