Share this page
naso mu koma mu sanar daku halinda ake ciki amma mahaifiyarta tak’i hakan. Ta d’auki duk laifin ta aza ma kanta..A cewarta wann hukuncinta ne take karb’a.. Sannan har rana mai kaman wann Mahaifin Ummulkhairi dake cikin jinya baisan Aurenta ya mutu ba.. An dai sanar dashi tayi Aure a haka yana jinyar amma baisan da wann labarin ba dan jinyar tashi abu ne da ya danganci zuciya. Likitoci suna bada shawarin ba komai za’a sanar dashi kai tsaye ba duba da irin yanayin jinyar. Sann baisan da cewa mu kanmu bamu san yanda Ummulkhairi take ba.” Haidar yaci gaba da girgiza kai yana duban Daddy “This is all my fault Daddy.. Duka laifina ne.. Daddy idan na rasa Khairy.. Bansan ya zanyi ba..” Ya k’arashe cikin tsananin nuna damuwa. Daddy bai kaiga furta kalma ba Azeema ta fito da murmushi saman fuskarta. Kai tsaye ta furta “Bazaka rasa ‘Yaruwata ba Sirkinmu Dangayu. Domin kudin kuna son junanku.. Naga haka a k’wayan idonku.. ‘Yaruwata..” Bata kai aya ba Khulsum ta fito da sauri dan dama tin baya dawowar su Umma daga Abuja suka d’auko Khulsum da Abba daga gidan Inna Dije. Tani ta kuma d’inke bakin Inna Dije da fad’in idan taji fit wani abu ya fita daga bakinta ya karad’e dangi gameda Auren Ummul toh ta tabbata itama nata Auren ya Mutu kenan sann itada D’anuwanta Malam Isubu har abada. Khulsum ta girgiza kai tana duban Azeema “Kiyi shiru Azeema..” Duk sai suka maida dubansu ga Khulsum da Azeema. Azeema tace “Khulsum ki k’yaleni na sanar dasu.. Baki gani ne Yayanmu naso ya maida matarsa.. Meyasa bazaki bari a sanar dasu ba..” Khulsum na huci tace “Sabida ‘Yaruwata tace bata so a sanar dashi.. Sabida ita d’in bazata tab’a komawa gareshi ba.” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata. Haidar da baisan tuni ya mik’e tsaye ba ya isa gaban Khulsum yana girgiza kai “Kinsan yanda Khairy take..? Tell me, where is she.. Where can I find her.?” Ta dubesa sai ta kauda fuskarta gefe tana share hawaye. Haidar ya kuma jefo mata tambaya “Please tell me, kinsan yanda take..? Ina take.. Dan Allah ki sanar dani..” Azeema tace “Bazata sanar dakai ba. Dan nima bata sanar Dani ba.. Kaf gidan nan babu Wanda ta sanar dashi. Nima abinda yasa naji tana waya ne na lab’e na saurara nan naji da Addarmu Ummulkhairi take waya.” Mama Tani ta mik’e tana duban Khulsum “Ke Khulsumu meke faruwa..? Yanzu dik irin d’aga hankalin nan da kikaga munyi munata neman Ummulkhairi dama kinsan yanda take.. Shine kika kyalemu cikin duhu.. Muna nan muna tunanin Har yanzu fushi kike da ita Shiyasa baki tada hankali wajen neman ina take ba Ashe kina sane..” Kuka Khulsum take tana girgiza kai “ ‘Yaruwata bata sanar Dani yanda take ba.. Amma nayi waya da ita kuma ta sanar dani cewa tana nan lafiya kar na damu ta kuma tambayeni jikin Abba.. Sann tace na kula da Umma kuma na nemar mata yafiyar Umma.. Sann..” Sai ta dubi Haidar da yai mutuwar tsaye yana dubanta, taci gaba “Sann tace ko ka zo nemanta kar na sanar dakai cewa munyi waya.. Dan har abada bataso ta sake ganin ko mai kamanninka..” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka. Cikin wane irin yanayi Haidar ke furta “No please.. Don’t do this.. Please tell me.. Tell me idan ta sanar dake yanda take.. Ko kuma.. Ina layin da ta kiraki dashi..” Duk a daburce yake. Khulsum ta girgiza kai “Ta rufe lamban bai fito ba..” Ya lumshe idanunsa yana dafe kai “No.. There has to be something.. Just think please.. Or maybe we can try to retrieve all the calls from your line.. And see if we can track the number..” Ganin duk ya daburce yana neman ficewa hayyacinsa yasa Daddy d’an yin gyaran murya yace “Haidar, taho nan ka zauna.. Abi komai a sannu..” Ya dubi Khulsum yace “ ‘Yanmata jeki abinki ko.” Khulsum ta risina ta tana mai jinjina kanta kafin ta shige tana share ragowar hawayen da suka zubo mata. Azeema na take mata baya. Tani ma ta dawo mazauninta ta zauna. Daddy ya dubi Haidar yai gyaran murya “Haidar ina so ka natsu ka kuma natsa zuciyarka. Yanada kyau mubi komai cikin lumana dan tada hankali bazai tab’a kawo mana maslaha ba. Idan har Ummulkhair tana cikin k’oshin lafiya wann ma abun mu gode ma Allah ne. Kuskure ne an riga anyi shi dama kuma shi gyara sai a hankali.” Tani ta jinjina kai “Wann gaskiya ne.” Daddy ya kuma jinjina kai kafin yace “Amma yaya jikin Maigidan..? Yana asibiti ne Har yanzu kokuwa..? Mai likitoci suka ce gameda rashin lafiyar nasa.?” Tani ta dan gyara mayafinta “Toh jiki Alhamdulillah zamu ce. Sann asibiti kuma sai jikin ya d’anyi tsanani ake zuwa.. Yana nan a gida. Saidai maganar ne ba sosai ba.. Amma yakan fahimci wasu abubuwan.. Rahotannin asibitin nasa duk yana wajen d’iyarsa Khulsumu dan kusan tareda ita akai jinyar nasa gaba d’aya. Ba abinda zamuce ma yarinyar saidai Allah shi mata albarka.” Daddy ya jinjina Kai yana fatan lafiya ga Abban kana ya mik’e yace “Ko zamu iya ganin shi.?” Tani ta jinjina kai “Eh yana d’aki yana kwance. Mu k’arasa. Bismillanku..” Tai gaba Daddy da Haidar na biye da ita suka nufi wata ‘Yar k’aramar k’ofa da zai sadaka da d’akin Abba. Suka d’an tsaya daga waje kafin Tani ta shiga ta tadda Umma ciki nan take sanar da Umma su Haidar da mahaifinsa zasu shigo su gaida Abba dama tuni Tani d’in ta sanar da ita zuwansu. Umma ta gyara zamanta ta dan gyara Abba ma kafin ta rufe kanta da mayafi, Har rabin fuskarta saida ta rufe sabida surkunta. Tani Tai masu iso. Daddy ya soma d’an rage tsawonsa ya shige d’akin Haidar na biye dashi. Suka gaisa da Umma suka tambayi mai jiki kafin Tani ta d’an matso kusan Abba tana sanar dashi ga Surkin Ummul da mai gidanta zasu gaishe shi. Allah sarki Abba sai ya soma k’ok’arin mik’ewa jin an ambaci Maigidan Ummul d’insa da surkinta. Daddy yai saurin taimaka masa yana masa sannu da jiki dukda muryar Abban ba wani sosai yake fita ba. Bayan sun gaisa da Daddy sai ya fice amsa wayarsa dake ruri. Cikin muryarsa da bai fita sosai irinta majinyaci mai Jin jiki Abba yace “Ina Maigidan Ummulkhairina.?” Haidar ya k’araso cikeda risinawa yana gaida Abba zuciyarsa ya kuma cika da tausayin Khairy da ahalinta. Sai Abba ya soma k’ok’arin d’ago hannu yana mik’a ma Haidar alamun yana so suyi masabaha. Haidar yai saurin tallafo hannun Abban ya rik’e cikin nasa suka gaisa. Sai yaji Abba ya rik’e hannunsa gam yana fad’i da kyar “Kaine Aliyu mijin Ummulkhairi na..?” Sai Haidar ya jinjina kai a hankali “Eh.. Eh Abba ni ne..” Abba yaci gaba “Ina matuk’ar son ‘Yata Ummulkhairi, tanada zuciya mai kyau.. Ka rik’e mun.. Ita da amana kaji koh..” Dukda tausayin Abba had’ida wani abu mai kama da rauni da Haidar keji yana taso masa tin daga can k’asar zuciyarsa bai hanasa jinjina Kai cikin sauri, ya soma furtawa cikeda k’warin gwiwa “In sha Allah Abba.. Zan rik’eta… Zan rik’e Khairy amana.. Na maka alk’awari.!” Abba ya murmusa had’ida jinjina kai sai kuma yace “Ina Ummulkhairi.. Maiyasa bata biyoka ba..? Na jima ban ganta ba. Ina kewar.. ‘Yata sosai.” A nan ne kuma jikkunansu gaba d’aya yayi sanyi. Babu ya Haidar Wanda ya gama d’aukar ma majinyacin mutumin alk’awarin kular masa da ‘yarsa wacce baisan ina take ba. Sai Tani Tai karaf tace “Ai.. ai laulayi take… K’aramin juna gareta shiyasa bata samu zuwa ba.” Ita kanta Tani da tai maganar saida taji banbarak’wai. Yayinda Umma tai saurin dubanta da idanunta masu cikeda rauni. Shi kaw Haidar sai ya sadda kansa kad’an. A haka dai Har suka fito zasu tafi. Baffanin Ummul guda biyu da suka amshi kud’ad’e hannun Asshe suka bada Auren Ummul d’in nan suka jeru suna jiran fitowar su Haidar ganin hamshak’iyar motar da ke k’ofar gidan nasu. Sai jinjina lamarin suke suna fad’in albarkacin bakinsu gameda mijin Ummulkhairi da mahaifinsa Wanda Tani ta hana su gana dasu a cewarsu. Ai ko suna ganin fitowar su Haidar suka k’arasa kaman zasu kwanta suna mik’o ma Daddy hannu alamun musabaha. Daddy da Haidar suka tsaya suna gaisawa da mutanen cikeda girmamawa. Nan sukai introducing kawunansu matsayin K’annen Mahaifin Ummulkhairi kuma Wanda suka bada Auren ita Ummulkhairin. Nan suka sake sabon gaisuwa na musamman suka kuma cikasu da goma na arziki daga Daddy har Haidar din babu wanda aka bari baya. Kowa kokari yake yayi alkhairi daga aljihunsa. Alkhairin da ya bar su Baffah Ado cikin tsananin al’ajabi. An masu kyautan ban girma sai kawai suka fara wasa Ummulkhairi cikin gidan suna cewa ta kawo alkhairi. Wacce a baya suka kyamaceta da k’addararta Har cewa suke tana bata sunan zuri’a da muguwar bak’ar k’addararta yau sai gasu nan suna rigen kiranta jininsu. Rabon da su shiga sashen su Ummul su duba D’anuwansu tinda Abba da Khulsum suka dawo daga Jigawa can gidan Inna Dije. Yau sai gasu nan tsamo tsamo suna kiran Abba Yayansu. Tani kaw ta masu d’add’aya tana fad’in maza aci arziki. Ummulkhair da suke ambato da Ummulsharri a baya yau sai gashi suna k’aryata harsunansu dan cewa suke ta amsa sunanta Uwar alkhairi. ** Bayan Haidar ya kai Daddy masauk’i nan suke tattaunawa da Daddyn gameda ciwon Abba. Daddy yace “Inaga ko zakaje Asibitin ku tattauna da Likitocinsa na nan. Sai a duba hospital report din nashi kaji shawarwarinsu.. Idan yaso ko can Abuja ko dan ta kama a fitar dashi abroad ne sai su sanar dakai.” Haidar ya jinjina Kai “Ina da wann plan din Daddy.. Hospital din da na kwanta lokacin da na samu had’arin mota is a prestigious hospital, sunada likitoci k’wararru daga k’asashe da dama sunada advanced technology.. In fact is a foreign hospital.. Because a yanda naga jikinsa ba Lallai Likitoci su bamu shawarin a fita dashi kai tsaye matuk’a akwai solution a nan.. Duba da process din da za’a bi. Dan Ga dukkan alamu yana jin jiki sosai. Amma zan tuntub’i Likitocin nasa kaman yanda kace.” Daddy ya jinjina kai “Good.. Yayi kyau.. Toh ai inaga ni zan bi jirgin yamma na koma. Zan turo Sadis (Daya daga cikin trustees d’in Daddy ne a wajen aiki) sai ya tayaka ku kula da al’amran.” Haidar ya dan murmusa yana risinawa “A’a Daddy da ka barshi. Zan kula da komai by myself.. Financially da dik wani abinda ya kamata.” Murmusawa Daddy ya d’anyi yana jin dad’in yanda D’an nasa ya zama responsible. Sai yace “Even so, Sadis zaizo ya tayaka da wani abin. Jirgin yamma nake son bi.” Ya k’ara maimaita ma Haidar d’in. Sai Haidar yai saurin jinjina kai “I’ll call the airport right away” Ya fad’i yana mai ficewa. Daddy ya jinjina masa kai. Haidar bai bar garin ba saida ya tabbata an shirya duk wani abinda ya kamata gameda tafiyan Abba zuwa prestigious hospital din da za’ai treating d’insa. Umma tace fir saidai Mama Tani ta tafi tareda Abba ita zata zauna da yaran. Haidar ya musu goma na arziki dukda cewa da Umma take ya daina d’awainiyar nan musamman idan ta tuna abinda ke faruwa na rashin Ummul. A cikin zuciyar Haidar kaw cewa yake baiyi rabin abinda Khairy ta musu shida ahalinsa ba. Cikin zuciyarsa yana kewarta sosai.. A koda Yaushe k’aunarta k’aruwa masa yake. Kafin ya bar garin da yamma yana zaune saman tabarma a haraban gidan dan tuni ya zama D’an gida. Azeema sai zuba masa surutu take ta d’auko wani tsohon album d’in Abba tana nuna masa hotunan Ummulkhairi harda Wanda take sanye da uniform na makaranta. Ya jima yana kallon hoton. Sihirtaccen murmushi saman fuskarsa. Azeema taci gaba da basa labarin k’uruciyarsu Har ta gangaro kan samarukan Ummul da ake saka musu rana a fasa. Har kan Zubairu da su Alhaji Kamilu da yanda kowa ya zata Zubairu zata aura sabida yanda Zubair d’in yaso Ummul. A nan ne fah sukaga Haidar ya had’e rai tamau. Badia sai mintsilin Azeema take tana fad’in Tai shiru haka nan amma inaa Azeema sai zuba take yawa kurna. Mama Tani ta kawo masa abinci tana fad’in su Azeema su kyalesa haka nan yaci abinci. Azeema ta dubeta ta dubi tuwon. Tuwon gero ne da miyar yauk’i. “Haba Mama ya zaki bashi irin wann abincin. Na tabbata bai ma tab’a gani ba.” Haidar kam ma iya cewa baima abindake faruwa ba. Dan tinda Azeema tai mentioning Zubair tsohon saurayin Ummul ya rasa sukuni.. Sai ya dan dubi Azeema ya girgiza Kai kad’an yace “Amma ina Zubair yanzu.. Yayi Aure.?” Azeema ta saka ma bakinta sakata tana Zare ido. Badia ta rankwafo had’ida rankwashin Azeemar kad’an ta rad’a mata “Kin gani koh. Ke baki san kishi irin na maza bane kinzo kina labarin tsaffin samarukan Ummul. Yanzu gashi kinsa mutumin na miki wasu tambayoyi. Haba Azeema mutumin nan fah ji yake kaman Ummul ta kufce masa kenan tinda sun rabu.. Idan baki basa k’warin gwiwa ba bazaki basa dalilin rura wutan tashin hankalinsa ba.” Azeema tai murmushin da yafi Kama da yak’e ta dubi Haidar tace “Wann ai tsohon labari nake sanar dakai Yayanmu. Zubairu ya jima da auren ‘Yaruwarsa wacce ake so a had’asu tuntuni..” Ta shiga tura foodflaks din abincin da aka kawo masa tana fad’in “Kaci abincinka Sirkinmu. Tuwon nan idan yai sanyi babu dad’i.” Badia ta harareta tana girgiza Kai ta janyo Azeema suka bar wajen tana rad’a mata “Kedai wacce tai jegonki bata farse wann bakin naki ba.” Azeema ta kuma kame bakin ta tana fad’in “Wllhi na sani… Duk yanda akai Inna Dije ce.” Suka dara a tare Badia tana fad’in Allah ya shiryi Azeema. * Kafin ya tafi saida ya k’ara tuntuban Khulsum ko ta sake samun kira daga Ummul. Khulsum tace bata sake kiranta ba. Su kansu saida Haidar ya basu tausayi. K’arshe haka ya hak’ura ya bar garin ba don yaso ba. ** Idanunsa na duban window yake ci gaba da fad’in “It’s been three months Hisham. Wata uku babu Khairy.. And Dareen is nowhere to be found. I feel lost, tiny and insignificant in this world..” Hisham ya sauk’e ajiyan zuciya “I believe everything happened for a reason.” Ya dan furzar da huci had’ida girgiza Kai “I have never met your wife Haidar.. Amma abinda na kula shine kana k’aunarta sosai, because ban tab’a ganinka cikin yanayi na soyayya irin haka ba..” Ya dan numfasa “Kuma koda ka kasance mutum da bai cika bud’e al’amransa ba jikina yana bani ba k’aramin abu bane ya shiga tsakaninku.” Sai Haidar ya dubesa amma baice komai ba. Hisham ya jinjina Kai kad’an “Whatever is the case Haidar, know that I’m here for you.. And you can always count on my support.” Ya jinjina Kai alamun tabbatarwa. “Idan zakaje kaci gaba da Neman matarka ni zance naci gaba da nemar maka Dareen. Ko ba don ka hukunta Dareen ba sai dan D’anka dake cikinta. Ko ya kayi Haidar, that child she’s carrying is still yours.. Kuma baida laifin komai.. Bazaka hukunta shi da laifin mahaifyarsa ba.” Haidar ya tsaresa sosai da ido wann karon sai ya girgiza Kai yace “Are you even sure that child is mine.?” Shiru Hisham bai amsa shi ba saima tunani da ya soma cikin zuciyarsa ‘Bastard! Zaka sheganta wann D’an kaman yanda Ubanka ya shegantani a ciki.! Kai din baka rage ma Ubanka komai ba Haidar.’ Hisham ya sinkayo muryar Haidar sanda yaci gaba “Wha if babu wani ciki. What if k’arya take, tinda iyakacin tarayyata da ita k’arya ne kawai.!” Hisham ya dan furzar da huci yana mai d’aga gira sama “Bazan k’i maka ba. Kuma bazanga laifinka ba.. Because you’ve been fooled and betrayed. Amma Kai tunani Haidar.. Kayi rayuwa na Aure da Dareen koda ace rayuwar ta k’arya ce. You were once husband and wife.. You cannot deny that. So ba abin mamaki bane idan tana d’auke da gudan jininka.. I mean, if you neglect that child zai tashi ne da tsanar koma waye mahaifinsa.. Meyasa ‘ya’ya zasu biya kuskuren da iyayensu suka aikata..? Hakan ba adalci bane.” Yanda yake maganar tamkar yana digging ma Haidar past d’insa ne. Hisham yaci gaba “You can’t let that child pay the price Haidar.. You know exactly how it feels mutum ya girma babu soyayyan iyayensa. You can’t make that child a victim. You can’t let that happen to your own child.!” Ya k’arashe cikin tsananin k’warewa tareda tono ma Haidar bayansa. Yanda ya girma da tunanin iyayensa basa sonsa duk sabida wani kuskure da mahaifyarsa ta aikata. Ya rintse idanunsa yana jin kamar dai duniyar ta dad’a juye masa. Sann gaskiya ne abinda Hisham ke fad’i. Because shi Kansa Haidar d’in was once a victim. Bazai bari tarihi ya maimaita Kansa cikin ahalinsa ba. Hisham ya tsaresa da ido cikin zuciyarsa cewa yake ‘Kai da ahalinka bakuda daman yin wani farin ciki a wann rayuwar. A lissafi Ummul ta cika watanni uku tin bayan da k’addararren Aurenku ya k’are.. Hakan na nufin ta fice daga iddarka.. Ni kuma yanzu zan tafi na gina nawa soyayyar cikin zuciyarta…All my sacrifices are finally going to pay off’ A fili k’arasawa yai ya dafa Haidar kad’an fuska fal damuwa. Cikeda kulawa yake furta “Haidar bazan Barka ka koma irin rayuwar k’uncin da ka fuskanta a baya ba. Ka tafi ka nemo matarka yanda ta shiga ta fita.. Ni kuma zan tafi na nemo maka Dareen yanda ta shiga ta fita ko dan wann innocent soul d’in dake cikinta.” Ya k’arashe damuwa sosai saman fuskarsa. Haidar bai iya ce masa komai ba sai shafe fuskarsa da yai da tafukan hannayensa. A haka Hisham ya tattari files d’in da ya shigo dasu ya fice fuskarsa d’aukeda mugun murmushin da ba kowa ke iya fahimta ba. Cikin zuciyarsa yaci gaba da ayyana Ummul tasa ce a halin yanzu. Da wann farin cikin Hisham ya taho garin Bauchi zuciyarsa fari k’al da nufin ya tafi Neman Dareen a zahiri kuma wajen Ummul yazo da niyyan k’ulla soyayyarsa. Babu Wanda yasan da zuwan nasa. Hajja batai mamaki ba dan dama ya saba mata irin wann zuwan na bazata. Saidai ta kula wann karon da wani irin farin ciki yazo maras misaltuwa. Suna cikin gaisawa da Hajja yake tanbayarta “Hajja nace ina Ummul kuwa..?” Bata kaiga basa amsa ba suka hango Ummul da fitowarta kenan daga babban parlorn da Hajja ke sana’arta na d’inki, nan suka hangota tana tafiya da kyar tana dafe garu tana kame kanta dake matuk’ar juya mata.. Kafin suyi wani aune jiri ya kusan kaita k’asa. Hajja ta nufeta hankali tashe ta tallafota tana ambaton sunanta dan tuni idanunta sun soma juyawa. SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!* *51* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* Bud’e ido tai sai gani tai fanka na wainawa saman kanta, ta yunk’ura zata tashi sai taga igiyar drip daure hannunta. Nan ne ta fahimci saman gadon asibiti take. Ta waiga kad’an sai taga wani mutumi da ko shakka Babu Likita ne tsaye daga gefe hannunsa rik’eda file kansa kife kaman yana rubutu. Hankalinsa naga abinda yake ta sinkayo muryarsa yana mata sannu. Ya k’arada “Malama Ummulkhair right.?” Ta jinjina kai kad’an. “Kina Jin wani pain..? Akwai yanda ke Miki ciwo.?” Ya k’arashe yana mai janyo kujera had’ida zama gefen gadon. Ta d’an girgiza Kai sai ta dafa kanta kad’an “Kaina na d’an juya min sann yana ciwo.” Sai ta dan tab’a gefen cikinta kad’an tace “Ciki na na ciwo kad’an ta gefe.” Ya jinjina kai “It’s normal to experience such pains in early stage lokaci zuwa lokaci.” Bata gano abinda yake nufi ba amma tana Jin heartbeat dinta na k’aruwa da sauri. Kaman yasan tana jiran Karin bayani ya soma jero mata wasu tambayoyin. “Amma… Yaushe rabonki da kiga al’adarki.?” Yai tambayar fuskarsa na nuna alaman tsananin kulawa. Sai ta kalleshi da mamaki. Ganin irin duban da ta masa yasa shi d’an sakin murmushi “Kinga kar ki ba ma tambayar wani manufa na kula kaman.. Baki fahimci meke damunki bane bayan kin d’ebe watanni cikin yanayin..” Kanta ya kuma k’ullewa.. Ta d’an girgiza kai “Dr.. Meke faruwa dani..? Dan Allah Ka mun bayani..” Ta fad’i duk a d’an tsorace Jinjina kansa yai yana kuma tabbatar da hunch d’insa. Sai Ya dan girgiza Kai kad’an yace “Kar ki damu ba wani abin tashin hankali bane.. Amma ki amsa min tambayata first. When last kikaga menstrual period d’inki.?” Sai ta soma tunani.. Ita zata iya cewa damuwa da tashin hankalin da ta tsinci kanta ciki yasa ta ma mance wani abu wai shi menstrual period. Ta girgiza kai tace “Ni.. ni … Ni ban sani ba..” Ta basa amsa tana d’an kauda fuskarta. Dr ya rage girman idanunsa had’ida girgiza kai kad’an cikeda mamaki “Is it possibile.?” Ta d’an dubesa fuska d’aukeda alamun k’osawa wann karan dan Likitan Ya fara hawa kanta da tambayoyinsa marassa kan gado. Sai Ya dan tab’e baki kad’an yace “Ina mijinki.?” Tambayar ya kuma tunzurata, ya fama mata gyambon dake cuziyarta, ta kuma jin wani k’atutun bak’in ciki ya tokare mata mak’oshi. A kufule tace “Bani dashi.!” Sai ya kuma girgiza kai cikeda mamaki “Baki dashi kuma..? I.. thought mutumin can da ya kawoku keda mamarki mijinki ne..” “Na fad’a maka bani da miji.. Ni Ummulkhairi banida wani miji..!” Ta fad’a kaman zata fashe da kuka. Likitan ya dan jada baya kad’an yace “Ok.. Ok easy..” Sai ya soma bud’e file d’in dake hannunsa yana duban file d’in yake fad’in “Amma sakamakon gwaje gwajen da muka Miki Ya tabbatar kina d’auke da juna biyu har na tsawon watanni uku which is why kikaji Ina miki tambayoyin da nake miki.. Amma sai na fahimci wann shine karonki na farko shiyasa Har juna biyun Ya shafe tsawon wann lokacin a jikinki tareda kin fahimta. Although pregnancy is not typically visible at 3 months, especially in a first pregnancy.. Most women begin to show in the second trimester, around 16- 20weeks.. However,…” Aya yai ma kalamansa sanda ya d’ago yana dubanta dan idanunsa naga file din dake rik’e hannunsa yaketa wad’ann bayanan da sam babu mai saurarensa balle fahimtarsa ga dukkan alamu. Abu d’aya zata iya cewa taji cikin kalaman nasa shine juna biyu bayan wann kalman bata sake fahimtar komai ba… Dr ya dan girgiza kai yana dubanta “Hello.. Are you with me..?” Ya fad’i cikin k’ok’arin dawo da ita daga duniyar da ta b’ace ciki. Dubansa take tana girgiza kai tana jin kaman duniyar ke juya mata “Ju..juna.. biyu..!!” Ta fad’i labb’anta Har rawa suke. Ta kuma girgiza kai cikin rashin fahimta “Mai.. Mai hakan.. yake.. Nufi Dr.. Ni.. Ni Ummulkhair.. Juna biyu..?” Ta k’arashe tana nuni zuwa gareta hannunta na matuk’ar rawa haka ma muryarta. Dr ya jinjina Kai alamun tabbatarwa “Of course. You are 3months pregnant.” Sai ta soma girgiza kai “A’a.. A’a baku gwada daidai ba Likita… Dan Allah ka sake gwadawa.. ni banida komai..” Cikin tsananin damuwa mai gauraye da tashin hankali take maganar. Dr ya shiga nuna mata sakamakon yana fad’in “Gwaji na jini mukayi wanda ya tabbatar da hakan.. Ina shawartanki da ki rage stressing kanki sann ki rage shiga damuwa ko dan lafiyarki da lafiyar abinda ke cikinki… I’ll prescribe some medications for you.. Sai a kiyayesu..” Ya k’arashe yana k’ok’arin mik’ewa. Kuka ta fashe dashi tana girgiza kai “A’a Dr.. A’a..Dan Allah ka cire mun cikin.. Wllhi bana so.. Dan Allah ka ceceni..” Shima wann karon a kufule yake dubanta “Bakiyi kama da maras Kamun kai ba da nace ta wani hanyar daban kika samo.. Amma ko ta ina kika samu ki sani bama cire ciki a nan.. Excuse me..” Ya k’arashe yana k’ok’arin ficewa yayinda Kukan Ummulkhairi Ya karu Wanda hakan yasa Hajja dake daga bakin k’ofan d’akin shigowa ba shiri. Dr ya dubeta “Yauwa.. Akwai magunguna da zan rubuta mata dan Allah sai a kula ta sha su akan kari..” Hajja ta jinjina kai “Eh akwai yarona da Ya kawomu yana waje.. Zai sayo magungunan.” Bai kuma tsayawa sauraronta ba ya fice. Hajja Tai sauri ta k’arasa ga Ummul dake cazgan kukan kamar wacce aka aiko mata sak’on mutuwa. “Ummulkhair.. Jikin ne..?” Ta tambaya cikeda damuwa. Shiru Ummul bata bata amsa ba sai kuka da take tana girgiza kai. Hajja ta dubeta sai ta dubi takardan dake aje saman drawer dake gefen gadon. Nan taga pregnancy test ne kuma ya nuna positive. Ji Tai tamkar jinin jikinta Ya k’afe. Taji kaman an d’add’aure jijiyoyin jikinta..

Chapter 47 of 64