Share this page
zama mahaifiya a garesu zan zama. Idan ban samu daman gyara kura kuran da nai a baya kan nawa ‘ya’yan Ummulkhairi da UmmuKhulsum ba zan kwatanta gyara akan Azeema da Badia cikin yardar Ubangiji Dije. Ki kirani da duk sunan da kikaga dama amma in sha Allahu ni Suwaiba bazan sake maimaita kura kuren da nai a baya ba.” Inna Dije ta murmusa ta matso kusan Umma sosai “Idan dai Tani da iyalanta ne gaki gasu. Sai ki fita ki nemo ki dafa ki basu. Idan ma aikatau zakiyi ki nemo masu wann ke ta shafa. Amma kinga wann abincin Ya haramceku daga ke Har su.” Ta k’arashe tana sunkuman kwalin taliya. Kaman daga sama taga Azeema da Badia kanta ko wacce tana sakin huci. Shigowarsu gidan kenan. Azeema ta nuna mata kwalin taliyar “Ajiye.” Ta fad’i cikeda gargadi. Inna Dije ta dubeta da mamaki “Ke Azeema ni zaki ma rashin kunya.” “Zaki ajiye ne ko zaki jira na tayaki ajewa.” Cewar Badia tana shan d’amara. Inna Dije ta saki baki da mamaki “Ke Badi’a.. Ni zaku ma d’iban albarka ina kanwar Ubanku.?” “Allah yasa k’anwar uban kikace ba uban ba. Rashin kunya kuma ai mai sauk’i ne wann. Billahillazi akan abincin nan sai mu tara Miki na jaki a nan mu bama idon mak’ota abinci dan kinsan dai wann ba bak’on abu bane a wann k’ofar.” Azeema tace tana kuma shan d’amara. Har lokacin mamaki take baki bud’e “Ni Dije zaku daka ke Azeema.! Eh Lallai! Ai idan bakuyi ba baku cika jinin Tani ba. Ba laifinku bane Kunsha a nono.” “Wllhi Inna Dije zakici bugu a banza dan kin fad’a da bakinki nida kunya dama munyi hannun riga. Ke d’in banza tinda na tafi na tari fad’a da budurwar Habibu mai tak’ama da uniform da bakin bindiga banga uban da bazan taresa ba. Ke mu fah fad’a ma rancenta muke ko ya kikace Badia.?” Badia ta dubi Inna Dije da bakinta ya gaza rufuwa sabida mamaki “Inna billahillazi idan baki kira yaran nan sun maido da abincin da suka fitar ba wllhi Kinji na ranste Miki kaf takaicin duniya da Tasi’u Ya juye mun zan juyesu akanki. Dan wllhi yanzu a haka hannayena k’aik’ayi suke.!” Inna Dije ta jinjina kai “Eh na yarda dole ku kasa zaman gidan aure dan babu Wanda zai zauna da shed’anu Irinku. Me za’a tsammata daga wajen yaran da uwarsu ke tsare a gidan gyaran hali.” “Saki nawa aka Miki.? Yaji sau nawa kikayi da wayonmu kafin ki zauna gidan auren.?da wayonmu muna rakaki kome. Naga gado mukai wajenki” Badia tace tana fincikan kwalin taliya dake hannun Inna Dije. Inna Dije ta jinjina kai tana duban Umma da ta zuba ma sarautar Allah ido. K’wafa tai tasa kai zata wuce Badia da Azeema suka shiga janyota suka nufo waje suna fad’in saita maido kayan abincin da ta sace ta saka a keke napep. Haka Azeema da Badia suka tirsasa ma Inna Dije ta dawo masu da kayan abinci. Suka k’araso da kayan suka jirge gaban Umma. Har lokacin ko waccensu da d’amara a kunkuminta. Azeema taci gaba da nuna ma Umma kayan abincin “Kema kiji da kyau bamu k’wata abincin nan sabida Ke ba sai don yunwar cikinmu. Kici gaba da girkawa kina bamu.” Umma bata ce komai ba har suka gama maganganun da zasuyi. Dan tun bayan abubuwan dake faruwa kaman abun nasu k’aruwa yai. Cikin Zuciyarta tabi su da addu’ar shiriya. Ta d’au alwashin zatai hak’uri dasu kuma bazata fasa masu nasiha ba har lokacin da abubuwa zasu daidaita da taimakon Allah. ** Abuja… Anisa taci gaba da juya kwalaben turare da Mommy ta bata tace ta kaisu ma Ummul. Waya ta d’aga ta kira Amminta. Asshe na ganin wayar Anisa Tai saurin d’agawa “Ina sauraronki Anisa meke faruwa.? Shin Haidar yazo gidan.?” Anisa ta rausayar da ido “No Ammi he hasn’t shown up until now. And I don’t think zaizo gidan anytime soon.” Asshe ta jinina kai “Toh ina sauraronki, wani abun ne Ya faru.?” Anisa taci gaba da juya kwalban turaren “Ammi Kince duk abinda ake ciki na dinga sanar dake.” Asshe tace “Eh K’warai. Remember you are my eyes there.” Anisa taci gaba “Ammi Mommy ta bani wasu kwalaben turare guda biyu.. Kaman turaren black khumra amma banaji suna k’amshin khumra.. Tace na bama Ummulkhair.. Lallai Lallai na bata na kuma sanar da ita had’in khumra ne na musamman Mommyn Tai mata kyautar su.” Ai Asshe bata San sanda ta mik’e daga zaunen da take ba. Ta soma tuna lokacin zuwansu wajen boka sanda za’a masu aiki akan makarin asirin Haidar. Boka Ya basu wani turare mai launin bak’i ya kuma ce lallai lallai duk matar da za’a karya asirin jikin Haidar da ita sai ta zamto tana amfani da wann turaren domin kuwa turaren tamkar shine kuran k’arfe da zai janyosa zuwa gareta Har dai sihirin Ya lalace. Idan kuwa haka ne bazata bari Ummulkhairi Tai amfani da turaren ba tinda ita d’in barazana ce ga rayuwarsa. Baki na rawa Asshe tace “Turaren humra.? Kar ki bata su Anisa..!” Anisa tace “Meyasa Ammi.?” “Na fad’a Miki no asking questions Anisa. Just do as I say. Ki zubar ki zuba turaren Khumra cikin kwalban ki bata. But koda wasa kar ki bata wann turaren idan har kina son ki mallaki Haidar.” Anisa ta kuma juya ido “But Ammi what if Mommy ta ba ma Bagidajiyar nan turaren da zata mallaki Haidar ne since she wants her for her son. What if I use it instead.. Kinga sai ya soni bai sota ba..” K’iris Ya rage Asshe bata kurma kururuwa cikin waya ba jin nata ‘yar zata zama makarin asiri “Ke Anisa. Zan tsine miki albarka idan kikai amfani da turaren nan.. Wai ke wace irin shashasha ce. Nace duk abinda nace kiyi kawai kiyi zan miki bayanin komai daga baya.. Just dispose it and replace with natural Khumra. Kin fahimceni.?” Ta k’arashe cikeda gargadi. Anisa ta furzar da huci dan ta gaji da wann mysteries d’in “Ok fine Ammi. As you wish.” Ta k’arshe tana katse kiran. Taci gaba da juya turaren kafin ta nufi d’aki ta nemo wani kwalban ta juye turaren ciki ta wanke kwalban kafin tai yanda Amminta tace. Can k’asan kayanta ta b’oye turaren da Mommy ta bata Wanda zuciyarta ke raya mata turaren da zaisa Haidar yaso Ummul Mommy ta bayar a kai ma Ummul d’in tinda tana mata makahon so. Idan kuwa Har hunch dinta ya zama gaskiya ita ce wacce zatai amfani da wann turaren dan Haidar ya so ta. ** Gaba d’aya Ji take bata kyauta ba tin bayan abinda Ya faru tsakaninsu da Anisa. Musamman da taga yanda fuskar Anisar Ya b’aci. Ita a halin yanzu ba abokin fad’a take nema ba. Hasalima Tun farko batada abokin fad’a dukda kuwa masu nemanta da fad’an sunada yawa kama daga cikin gidansu har izuwa mutanen unguwa. Khulsum ce ta fad’o ranta wacce a ko yaushe idan an taresu da fad’a ita ke d’aukan fad’an. Tayi nata Tai na Ummul d’in. Ta murmusa a hankali. A fili ta furta “Nayi kewar ki fitananniyar ‘Yaruwarta.” Ta share hawayen da Ya gangaro mata. tunanin mahaifinta ne Ya fad’o mata sai ta tuna alk’awarin Inna Dije gareta a lokacin da suka kawota cewa kar ta saka damuwan mahaifinta a ranta domin kuwa zata kula dashi cikin yardar Ubangiji. Umma ta fad’o ranta. Sai ta lumshe ido a hankali tanajin kuka na zuwa mata. Kalaman Umma na k’arshe a gareta su take tunawa cewa kar ta nemeta kar ta nemi kowa cikin danginta Har na tsawon watanni uku koda kuwa a wayan salula ne. Meyasa Umma zata yanke mata hukunci mai tsauri irin wann. Shin ko haka take a al’adarsu idan anyi aure sai bayan watanni uku kai magana da ahalinka.? Bata jin hakan ne. Ta lumshe idonta wasu hawayen suka kuma gangaro mata. Tana a haka taji ana knocking a b’angaren ta. Ta mik’e Tai k’ok’arin kintsa kanta kafin ta nufi k’ofa. Ga mamakinta Anisa ta gani tsaye tana sakin huci. Ummul ta sakar mata sassanyar murmushi had’ida bata hanya “Bismillah shigo.” Anisa ta watsa mata harara kafin tasa kai ta shigo. Sai faman yatsina yank’wanannen fuskarta da bai Ida warkewa ba take. “Ba zama nazo yi ba. Ban kuma zo dan na rama abinda kika min ba dan naga kin sha jinin jikinki. Sak’o Mommy ta bayar a kawo miki.” Tai maganar tana mai aje turaren saman centre table. Ummul ta katseta “Ni ban miki komai ba Anisa. Ke shaida ce keda k’awarki ku kuka shirya abunku.” Ganin Anisar ta tsareta da ido Ya sanyata samun k’warin gwiwar ci gaba “Ni bana nemanki da fad’a. Kuma ki yarda dani har cikin zuciyata banji dad’in abinda Ya sameki ba.” “Oh please shut up! Spare me your false sympathy.” Taci gaba da takowa gaban Ummul. Tana huci take nuna fuskarta. Muryarta ya soma rawa alamun kuka “Just look at my face.. Look at what you did to me. Kalli yanda fuskata ta lalace.. This is what you want right.? Farin ciki kike ko..? Na sani tun farkon zuwanki gidan nan baki sona.. Amma ban tab’a tunanin zaki min abinda kika min ba. Leenah ita ce ta zuba miki cream din ba ni ba. Meyasa kika zab’i b’ata nawa fuskar… It was Leenah’s plan and not mine. Bansan ta shirya Miki haka ba amma ki zab’i cutar dani. Look duba kiga abinda kika min.” Ta k’arashe cikin kuka. Jikin Ummulkhairi yai sanyi. Ta soma girgiza kai “Anisa ki yarda Dani banji dad’in abinda ya samu fuskarki ba. Amma ki sani shi rayuwa abinda ka shuka fah shi ke dawo maka. Idan khairan khairan idan sharri sharri. Ya kamata ki d’auki darasi cikin abinda Ya faru.” “You are not in a position to dictate to me what I should do with my life. Idan kuma shawari ne ban nema ba. We are not even friends to begin with.” Ta k’arashe tana juya ido. Ummul ta kuma girgiza kai “Ni bance mu zama k’awaye ba. Amma ki sani bana neman abokin fad’a.” Anisa ta kafeta da ido sai kuma ta marairaice fuska ta k’arasa saman kujera ta zauna tana Shafa fuskarta. Ta d’ago tana duban Ummul da idonta masu zuban ruwa “You are right you know. Duk abinda ka shuka a duniyar nan shi yake dawo maka. At first I hate you Ummul.. Bazan b’oye Miki ba. Ina kishinki musamman ganin yanda daga zuwanki gidan nan hankalin Mommy da soyayyarta gaba d’aya ya koma kanki.” Ta mik’e Tai tsaye gaban Ummul da idonta masu zuban ruwa “I’m not a bad person Ummulkhair. I’m so sorry for everything I did to you.. I don’t want us to fight anymore.. Ko bamu zama kawaye ba I believe we can get along and live in peace..” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. Ta mik’a ma Ummul d’in hannu murmushi saman fuskarta “Mu mance komai mu zauna lafiya.” Sosai Ummul tasha mamaki da sabon sauyin Anisar. Amma sai ta murmusa ta mik’a mata hannu sukai musabaha. Anisa Tai saurin hugging d’inta tana fad’in fad’a tsakaninsu Ya k’are tayi alkawari. Ta dubi saman dining table yanda abinci suke nan a jere alamun tinda aka kawo ma Ummul d’in bata ko tab’a ba. Ta murmusa ta dubi Ummul “Don’t tell me you still haven’t eaten. Koda yake zaman kad’aici Babu dad’i. Come zo muje. Barin tayaki cin abincin.” Ta janyo hannun Ummul suka nufi dining table. Anisa tace da Ummul ta zauna ita zatai serving d’insu. Ta zuba abinci ta shirya table. Nan suka zauna suna facing juna itada Ummul d’in. Ganin Ummul ta matsar da table knife gefe yasa Anisa murmusawa tace “Ya kamata ki koyi cin abinci to our level. You must keep your table manners. And that includes the use of utensils. Kar ki mance ke sirkar gidan nan ce a yanzu. Hakan na nufin, your social status has changed. You should learn how to mingle with upper class people. Mijinki Haidar mutum ne da ya girma cikin wayayyu sann yake hulda da wayayyun mutane, so you must adopt our lifestyle.” Anisa ta k’arashe tana gyara zamanta ta d’aura napkin saman laps d’inta. Sai faman kwarkwasa take. Ta dubi Ummul tace tai irin zaman da Tai. Murmushi Ummul Tai had’ida yin yanda Anisa tai. Anisa tace “Good. Haka wayayyun mata ke zama bisa table especially in public. Yanzu ki d’auki fork and knife muga.” Ummul ta kuma murmusawa dan harga Allah dariya Anisa ke bata. Nan tai yanda Anisar tace. Anisa ta girgiza kai “No, fork should be in your left and knife in your right. Like this.” Ta k’arashe tana nuna mata. Murmushi Ummul ta kuma yi. Sai ta girgiza kai wann karon “ Amma addininmu harma da al’adarmu basu koyar damu cin abinci da hannun hagu ba. Shed’an shi yake cin abinci da hannun hagu.” Anisa ta kauda fuskarta gefe tana juya ido. She had no other option than to put up da wann Bagidajiyar. Sai ta juyo ta murmusa “Of course you are right. Kinyi gaskiya. Na gode da kika tunasar dani.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. A haka sukaci abinci Har Ummul Tai mata rakiya sanda zata tafi. Sai mamakin canzawar Anisar Ummul d’in take. Amma cikin ranta taji dad’i da suka shirya da Anisar dan harga Allah bata neman abokin fad’a. Anisa tana shigowa ta tadda Mommy zaune a parlor alamun tana jiran shigowarta. “Mai ya tsaidake can.? Shin kin bata turaren da na baki ki bata ko kin tsaya shashancinki ne.” Mommy ta tambaya tana duban Anisar . Murmushi Anisa tai “Na bata Mommy. Tace ta gode sosai. Taji dadin kyautar dan tin kafin na bar wajen ta shafa.” Annurin fuskar Mommy ya k’aru jin tayi amfani da turaren. Anisa taci gaba “Na tsaya na tayata cin abinci ne Mommy. Sai kuma na mata hira..” Ta k’araso ta zauna kafin taci gaba “Da alama kad’aici na damunta. Dan ko abinci bata wani iya ci. Kar kiga yanda taci abinci sosai da muke tare..” Ta kuma muskutawa “Em Mommy nace why not gobe Ummul ta shigo muci abinci gaba d’aya tare. Zata d’an rage kewa kuma zata k’ara samun daman sakewa damu tinda har yau Haidar baizo ba..” Mommy ta murmusa “Da alama ku biyun Kun fara sabo sosai. Sai ki samu ma’aikatan kitchen ku shirya komai.” Anisa ta murmusa “Okay Mommy..” Ta mik’e tana murmushi. Har ta soma tafiya ta juyo “Em.. Mommy nace, can I invite my friend over..?” Sanin ba ko wani shirgi Hajiya Kwaise ke bari a kawo mata cikin gida ba Shiyasa ma ta tambaya. Mommy ta jinjina kai “Of course you can..” Tai maganar tana murmushi zuciyarta fari sol tinda Anisa ta sanar da ita Ummul tayi amfani da turaren da ta bata. burinta Ya kusa cika. Haidar d’inta zai dawo gareta. ** Saida Anisa tai shirin kwanciya kafin ta d’aga waya ta kira Leenah. Tana tsaye gaban mirror tana cleansing soyayyan fuskarta da auduga taci gaba “I told you Leenah. Yarinyar nan sai tayi nadaman soyan fuska da tai. Zamanta a gidan nan yazo k’arshe. Kedai kizo da wuri ki sha kallo. Kar ki damu na karba Miki katin gayyata daga wajen Hajiya Kwaise Maitama dan kinsan da k’a’ida ake shigar mata gida. Matsalar kawai I need someone who can help me to carry out my plan .” Leenah ta murmusa “Girl I’ve got your back. Just say the word kiga aiki da cikawa.” “Oh shut up Leenah! As if your tiny brain is capable of helping me out.. last time I checked stupidity dinki ne yasa fuskata ta soye.” Leenah ta murmusa “Haba Neesa trust me we re not going to repeat the same mistake.. You need me. After all, I’m the only one you can count on.” Shiru Anisa tai “Fine. But wait , if you screw up my plan Leenah. I swear I’m going to kill you myself.” Leenah ta murmusa “I’m on it girl. Kar ki damu zamu shirya komai ta yanda yarinyar zata bar gidan a gobe. I give you my word.” Jinjina kai Anisa take tana sakin murmushi lokaci guda tana duban fuskarta a mirror. A fili take furta “Tomorrow I am going to get rid of my problem. Goodbye to you. Ummul..!” Ta k’arashe tana mai fashewa da dariya had’ida duban kanta cikin mirror. ** Bayan ta Ida shirin baccinta alwalwa ta d’auro ta soma jero nafilfili tana kai kokenta ga Rabbil Izza. Kama daga kan sabon rayuwar da ta tsinci kanta ciki zuwa ahalinta da ta baro Har dai izuwa kan wann k’addararren aure da Ubangijinta Ya jarabceta dashi. Auren da batada tabbaci akan makomarsa auren da har kawo wann rana bata san kalan mijin ba bata kuma da tabbacin mijin Ya san da ita. Dan dik kyautatawa da d’imbin alherin mahaifiyarsa gareta bata tab’a jin a ranta ta samu sukuni cikin fargaban abinda ka iya zuwa yazo cikin auren. Addu’a ta dingayi Allah ya shiga al’amarinta. Idan har akwai alheri a cikin auren. Idan har zamanta alheri ne a gidan Allah Ya kawo mata komai cikin sauk’i. Haka zalika idan Babu wani alheri Allah Ya sauk’ak’a mata ya kawo hanyar da zata bar gidan cikin sauk’i. Ta jima sosai tana kai kokenta wajen Ubangijin da Babu abinda yafi k’arfin buwayarsa. A nan kan sallayarta bacci yai gaba da ita. ** Cuba.. Bacci yake yana jin Kansa na juya masa cikin baccin. Nan kuma ya soma mafarki da mahaifiyarsa. Mommy ya gani durk’ushe gabansa tana kuka hannunta rik’eda farin takarda. Tana fad’in mahaifinsa yayi canceling project d’insa. Saurin amsar takardan yai daga hannunta saidai yana ware takardan yaga sab’anin abinda Mommy tace. Domin kuwa takardan sakin mahaifiyarsa ya gani wai Daddy ya saki Mommy. Juyowa yai bayansa yana huci kaman zai shak’e Daddy yana fad’in maiyasa zai saki mahaifiyarsa. Daddy bai basa amsa ba saima nuni da yai masa da bayan wata mace tana tafe tana jan akwatinta. Jikin Haidar yai sanyi sanda Daddy ke fad’in ‘Mahaifiyarka ita ta saka nata Auren cikin had’ari dan wanzuwar AUREN WATA UKU. Ka tuhumi kanka Aliyu.!’ Daga haka ya farka daga baccin duk ya had’a zufa. Nan yaga yamma ne sosai a agogon Cuba. Around karfe shida na yamma. Ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa yana mamakin baccinsa a daidai wann lokaci. Ba bacci bane yafi basa mamaki kaman mafarkin da ya tsinta kansa da yi cikin barcin. Meyasa hankalinsa ya tashi sanda yaga Mommy na kuka a cikin barcinsa. Baya son ganin hawaye. Baya so yaga ana kuka amma ya sani hawayen Mommy bai tab’a damunsa ba. Meyasa ya tsinci kansa yana mai damuwa da hawayenta cikin barcinsa. Meyasa zuciyarsa tai zafi da yaga mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa.? Wann shine abinda yake fata yake buri tsawon rayuwarsa ahalin ta ruguje ta lalace. Meyasa hankalinsa zai tashi bayan abinda yake buri ne Ya faru cikin barcin nasa. Ya furzar da huci a hankali yana kuma shafan fuskarsa. Can k’asan zuciyarsa ji yai yana son kiran Mommy amma wani b’angare na zuciyarsa na kuma tunzurasa gameda al’amarin iyayen nasa. Why would he even care. Toh su rabu mana for all he cares. Yai gajeren tsaki kafin ya mik’e yana neman Dareen yanda ya hangeta cikin pool tana waving d’insa tana fad’in he should join her. ** Washe gari ta kama Alhamis hakan yasa Ummul ta tashi da azumi dan dama azumin litinin da alhamis basa wuceta hasalima Sun zame mata jiki. Anisa ce ta shigo Tai inviting b’angaren Mommy kaman yanda Mommyn ta buk’ata a Cewar Anisa. Ummul ta shirya tsaf kafin suka jera suka nufo b’angaren tareda Anisa. SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!* *28* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* A parlour suka tadda Mommy. Tana ganinsu ta fad’ad’a murmushinta. Ummul ta k’araso ta zauna daga can bakin carpet ta gaida Mommy. Bayan Sun gaisa Mommy ke ce da ita ta dinga shigowa b’angaren tana cin abinci tare dasu duk sanda take son hakan sabida zaman kad’aicin babu dad’i. Murmushi kurum Ummul tai dan harga Allah sosai take jin nauyin Mommy dukda k’ok’arin janta jiki da take. Nan take mata godiyan turaren da Anisa ta kai mata injita. Mommy ta murmusa tace Babu komai. Cikin zuciyarta kaw dad’i ne ya mamayeta. Daga k’arshe burinta yana gab da cika. Haidar ya gama gudunsa duk yanda zaije amma tanada yak’inin aikin Malaminsu zai tasiri akansa. Anisa ce ta janyo hannun Ummul tace ta taso su duba ma’aikatan a kitchen. Aiko kaman wacce take kan k’aya ta mik’e tabi bayan Anisa. A kitchen d’in ma saida ta janyo Anisa suka keb’e ta d’an mata nasiha kan wulak’anta d’an adam koda na k’ark’ashin ka ne. Musamman da taga yanda duk ta birkita ma’aikatan da tsiwa. Anisa ta kauda fuska tana rausayar da ido. Cikin zuciyarta fad’i take ki gama duk wani kilibibinki bayan abinda na shirya Miki kin zama tarihi a gidan nan. Zuwan Leenah yasa Anisa barin kitchen d’in dan security personnel sun kira daga can gate sun sanar Anisa tanada bak’uwa. Hakan yasa bata bi takan Ummul ba ta fice. Ummul na tsaye gefe ta hangi madara kan wuta yana gab da zuba. Cikin sauri ta isa ta d’auki abun motsawa tana juya dan hanasa zuba. Chef d’in da bata jima da barin wajen ba ta k’araso da sauri tana bama Ummul hak’uri da fad’in urgent call ta samu daga gida Shiyasa ta tafi amsa kiran. Ummul ta murmusa had’ida girgiza mata kai “Laa babu komai kar ki damu nima nayi kewan aikin ne. Ban Saba zama haka nan bana aiki ba. Duk sai ina jin ba dad’i.” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta. Dan ta lura cikin ma’aikatan wann wacce ta d’an manyanta mai kula da sauran ‘Yanmatan dake kitchen din ita kad’ai taji tana hausa sosai. Matar ta d’an murmusa “I’m the chief chef here. I’m the one supervising and monitoring the kitchen staff. Kar ki damu munada yawa a nan.. Zamuyi komai kan lokaci in sha Allah.” Ummul ta murmusa kad’an “Amma zan d’an iya tsayuwa a nan na tayaku da wani abun..?” Matar ta kuma murmusawa “I’m afraid you can’t. Idan Madam tazo taga mun baki aiki zai iya shafan namu aikin musamman ni.. Kar ki damu zamu kula da komai a nan.. Kije kawai.” Ba don Ummul taso ba ta jinjina kai ta nufi k’ofa matar sai sakar mata murmushi take. Tafiya take a katafaren gidan tana waige waige. Tabbas batada tabbaci idan bata b’ace hanya ba. Tana tafe tana tinanin ta ina zata bi nan ta hangi wani k’ofa tabi k’ofar. Wata ma’aikaciyar gidan mai sanye da uniform ta gani. Budurwar ta tambayi Ummul “Ma’am, are you looking for someone.. Do you need something..?” Ummul ta dubeta sai tace “Hanya nake nema dan Allah.” Budurwar ta murmusa “Oh that’s the way to the main house Ma’am.” Ta k’arashe tana nuna ma Ummul b’angaren dama. Ummul ta jinina kai a hankali kafin Tai mata godiya tabi hanyar da budurwar ta nuna mata. Tana tafe taga wani k’aton hoto manne a wani madaidaicin parlorn mai kaman waiting. Ta gane Mommy a hoton dukda k’uruciya da ya nuna a fuskar Mommyn. Gefe da Mommy wani mutumi ne mai Kamala da bata tantance ba amma tanada tabbacin shine mai gidan kenan. Tsakiya dasu wani yaro ne Wanda duka duka bazai gaza shekaru 10 ba. Kansa an tara masa suma irin mai laushin nan da cika. Ga kamannin iyayensa d’auke a fuskarsa. Yanda yaron ya b’ata rai cikin hoton ga fuskarsa da Ya buya cikin sumar kansa sosai abun yaso bata dariya musamman da taga kaman ita yake harara. Kai da gani kasan camera yasha harara kaman dai Wanda aka masa dole. Muryar su Anisa da ta soma jiyowa ne Ya janyo hankalinta. Ta nufi hanyar da take sinkayo muryoyin. Nan ta kuma cin karo da wani hoton a wani dogon corridor. Saidai wann hoton matashi ta gani tsaye gaban wani k’atoton zanen gine gine hannunsa rik’eda wani k’aramin abu kaman kara yana nuna ma mutanen dake zaune saman kujeru bayansa zanen dake gabanshi. Ko ba’ace ba zaka fahimci ma’aikata ne. Matashin yana sanye da suit saidai fuskarsa bai bayyana cikin hoton ba sakamakon Ya bada baya alamun yana bayani gameda hoton dake gaba gareshi. Bata san dalili ba amma kallo guda Tai ma mutumin dake cikin hoton zuciyarta ya yanke. Ta tsinci kanta da fad’uwan gaba dukda ba wai ganin fuskarsa tai ba. A haka tana nan tsaye su Anisa suka k’araso suka

Chapter 23 of 64