kuma murmusawa kafin yaci gaba “Too bad idan bakiyi sauri ba zaki iya rasa kallon show d’in.. The fall of Maitama’s.. The biggest scandal of their lives is just about to erupt.!” Ya k’arashe yana shekewa da dariya.
Anisa ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Mai kake nufi.?”
Ya kuma murmusawa “You wouldn’t want to miss the show.!” Yana ida fad’in haka ya datse wayarsa yana dariya.
**
A can filin taro kuwa Haidar matsawa gefe kad’an yai sakamakon kiran Amininsa Hisham da ya shigo masa.
Cikin nuna tsananin damuwa tamkar gaske Hisham ke fad’in “Banida wani zab’i ne Haidar dole na bar duk abinda nake na tafi gida na duba jikin Hajja.. Jikin nata ya d’anyi nauyi ne Haidar. Dan Allah Kai hakuri. Nasan ya kamata ace ina tareda kai a rana mai matuk’ar mahimmanci irin haka a wajenka.”
Haidar ya girgiza Kai “Amma ka saurari kanka.? Maiyasa zaka bani hak’uri.. What’s more important than lafiyar Hajja.. Iyaye first kafin kowa Hisham.”
Mamaki ya kusa kashe Hisham jin yau wai Haidar ke d’aukan al’amarin iyaye da mahimmanci. Lallai ya yarda rayuwar Haidar ta fara d’aukan saiti bazai tab’a bari wann ahalin su dunk’ule waje d’aya ba. Sai ya dan jinjina Kai yace “Haka ne Haidar.. A gaishe mun da amarya ace mata ina nan zuwa gaisuwa da cin girki in sha Allah. Allah sa ta iya abincin gargajiya kasan nan nafi wayo ni, dan mijinta dai bature ne..!
Gajeren tsaki Haidar ya d’anyi “Kai komai sai ka saka wasa ciki. Ka gaisar mun da Hajja sosai. Idan tana iya amsa waya ka had’amu mu gaisa.. In sha Allah zan samu time nazo na dubata.”
Katse kiran yai bayan Sun gama kafin ya nufo wajen motar yanda Ummul take. Amarya da ango na k’arisowa media suka masu chaa suna nema ji ta bakinsu. Saidai securities basu wani basu chance ba balle su samu daman magana dasu.. Sann tuni Mommy ta hana wani d’an jarida shiga wajen taron Wanda hakan ba k’aramin tada hankalin Asshe yai ba. Shirinsu na barazanar rugujewa.
Hannunta rik’e cikin nasa suke tafe. Haidar kaw tin sauk’owarsu a mota yake karantarta.
Tafiya take tana ganin kaman duniyar na juya mata, ji take kaman dai wani babban al’amari ke shirin faruwa da ita. Gani take kaman duk illahirin jama’an dake wajen ita suke kallo. Jiri ya d’an d’ebe Haidar yai saurin tarota ta fad’o jikinsa. Cikeda kulawa ya rik’eta sosai “Are you.. ok..?”
Sai ta d’an jinjina masa Kai.
Har lokacin rik’e yake da ita. Cikin rashin gamsuwa ya dan girgiza kai “But.. You almost fell..”
Ganin yanda ya rik’eta ga idon mutane akansu duk sai taji kunya ya cikata. Tai saurin girgiza Kai tana yin k’asa da kanta shi kaw na dad’a rank’wafo da Kansa dan ya saurari abinda take cewa.
“Kar ka damu k’alau nake.. Inaga takalmin ne kawai da ban.. Ban saba tafiya da irinsa ba.” Ta fad’i duk a dan daburce cikin k’ok’arinta na ganin ya k’yaleta.
Maimakon ya sakarta saima sake rik’eta da yai, ya kuma girgiza Kai yana kallonta sosai “You look pale.. You sure you’re fine.?”
Jinjina masa kai kurum tai ba tareda ta iya amsa sa ba.
Sai Ya k’arada “Have you had lunch.?.”
Shiru batace dashi komai ba saima yan waige waige da ta soma kanta a k’asa dan gani take kaf mutanen dake wajen su kawai suke kallo. Muryarsa ta kuma sinkayowa “Wait.. Have you been skipping your meals..?”
Sai tai k’arfin halin girgiza masa kai. Ganin dai idan bata amsa sa ba bazai daina jefo mata tanbayoyi baz Da kyar ta iya furtawa a hankali “Lafiya nake… Naci abinci… Kawai kar ka damu.. Ina so na zauna.”
Bai kuma cewa komai ba sai d’an jinjina Kansa da yai ba wai dan ya gamsu ba. Ya sakalo hannunta suka k’arasa wajen da aka tanadar domin su.
Bayan an sanar da zuwan amarya da ango, manyan bak’i da sauransu.. Nan aka soma gudanar da shagalin biki.. Asshe ta fito da niyyan gabatarwa kwatsam taji microphone baya aiki. Ta kalli microphone da mamaki tana kuma jijjigasa domin kuwa da kamar wuya abu irin haka Ya faru wajen taron da ya amsa sunansa ya kuma samu halartar manyan bak’i na musamman. Bata ida juya speaker ba taji sautin tafi ta bayanta. Juyawan da zatai da tsanani mamaki sai gani Tai k’atoton screen d’in dake bayanta wata budurwa ta bayyana.
Yayinda hankalin kowa yayi wajen. Dareen taci gaba da tafi cikin screen tana takawa. Lokaci guda take fad’in “Surprise.! Surprise.!! Ga Wanda basu sanni ba sunana Dareen.. Kuma Mata ga Haidar Maitama wacce mahaifiyarsa ta k’uduri niyyan raba Aurenmu.”
Wann ya kalli wann wancan Ya kalli wann.
Dareen taci gaba “Wann taron bikin da ake, an ginasa ne bisa cin amana, yaudara da kuma zallan k’arya.. An ginasa ne dan tarwatsa wani Auren. An ginasa ne dan a kashe nawa Auren da Haidar.. Haka ne Hajiya Kwaise Maitama.?”
Mamaki Ya hana Mommy motsi sai kallon screen din da take, yayinda Dareen taci gaba “Saidai abinda baki sani ba Hajiya Kwaise wann Auren da kikayi ma Haidar dan ki raba namu Auren bazai dore ba bazai je ko ina ba domin kuwa an gina auren ne bisa zalunci.. Dan kawai a raba masoya guda biyu. Ina nufin ni da masoyi na Haidar..” Taci gaba da murmushi “And now more than ever Aurenmu da Haidar bazai tab’a mutuwa ba Kinsan dalili Mommy.?”
Zukata sukaci gaba da bugawa. Mamaki da al’ajabi yaci gaba da bayyana tsakanin fuskoki. Yayinda video d’in Dareen yaci gaba “I am pregnant.! I am three months pregnant.. I am carrying your grandchild Hajiya Kwaise.. Your son’s child. Ina d’aukeda juna biyun Haidar har na tsawon Watanni uku.!”
Ba Haidar da yai mutuwar zaune yana duban Screen din ba, ba Ummul wacce ta koma tamkar mutum mutumi tana kallon abinda ke faruwa tamkar ba zahiri ba baga Mommy da ta koma tamkar hoto a wajen.. Baga su Tani da suka maida kawunansu k’anun alhaki ba sakamakon ganin abinda ke wanzuwa kan idonsu. Kai duk wani mahaluk’i dake wajen Daskarewa yai yana kallon ikon Allah..
Dareen taci gaba da murmushi cikin video d’in “Haidar my love.. I am carrying your child.. Our child.. The fruit of our love.. You are going to be a father my love.. Zamu zama iyaye.. Ba haka naso na sanar dakai ba sai dan naga an shiga tsakaninmu da yawa.. Na sani this is going to affect your family business somehow.. But believe me, I didn’t mean to jeopardize your business.. Please forgive me my love.” D’iff screen din ya d’auke.
A daidai lokacin Anisa ta k’araso ta tadda wann babban shiri da Hisham yai. Cak Anisa ta tsaya tana sakin murmushi tareda jinjina ma shed’anancin Hisham.
Asshe ta mik’e a firgice ta nufi yanda MC da sauran masu kula da event suke tana fad’in “What’s this.. What’s the meaning of this.. Who’s in charge of the event.. Wai meke faruwa ne.. Ya akai haka ta kasance..?”
Kowa yace bai san Ya akai aka sabotaging event din ba. Baga securities ba baga MC’s da sauransu ba.
Anisa ta saki murmushi sanda ta hangi Azeema. Ta shiga shafa b’arin fuskarta yanda shatin yatsun Azeema suka bayyana sakamakon marin da ta mata. A zuciyarta tace ‘Baki mari banza ba. Zan nuna miki barikin gaske.. Anisa nake, I always get what I want.’ Ta kuma murmusawa. Lallai dole tayi amfani da wann damar. Sai ta k’araso tana kuka tana rik’e Mommy tana fad’in “Mommy ni ce wacce ta kamata tai coordinating komai a wajen nan kaman yanda kika amince mun, amma wancan munafukar ta kulleni a gida sai yanzu na samu na k’araso.. Ma’aikatan dake cen gida sune shaiduna.. Mommy I’m sure bakinta d’aya da duk Wanda sukai sabotaging event din nan.. Ita ta taimaka musu ta rufeni a d’aki dan su samu saukin executing plan dinsu. Mommy ki yarda dani da shirinsu suka taho wajen nan.” Tai maganar tana nuni da Azeema.
Duk jijjiga Mommy da Anisa take Mommy bata iya cewa komai ta koma tamkar hoto, ko motsi k’akk’wara bata kuma yi ba tin bayan da Dareen ta bayyana cikin wann faifayin. Sai kawai AnisaTa tafi aguje zata shak’o Azeema tana fad’in she’s working with the people that sabotage the event. Ta shiga kiran securities tana fad’in su kama Azeema ita zata fad’i wad’anda take ma aiki wad’anda suka sakata ta kulleta a d’aki sabida kar ta samu damar halarta wajen event din.
Haba nan fah Azeema ta shiga kururwa tana fad’in ita wllhi bata san komai ba bata san kowa, sann bata aiki ma kowa. Mama Tani ganin securities sunyo kan ‘yarta ta nufesu cikin k’ok’arin k’watan ‘yarta tana fad’in su rufa mata asiri kar su kulle mata ‘ya ta d’and’ani zaman gidan yari bazata so wani nata ya kuma d’and’ana ba. Gaba d’aya taro ya yamutse ya hargitse ya rikice.
Kasa komai Haidar yai har lokacin idonsa na kan screen d’in dikda ya d’auke. Har lokacin Dareen yake hangowa cikin screen d’in. Wacce rabonsa da ita tin ranar da suka samu had’arin mota shida Ummul, exactly two months back kenan.. Kalmarta na cewa tana d’aukeda Juna biyu shine yaci gaba da duka dodon kunnensa.
Wajen taro ya yamutse ya watse. Masu tsegumi nayi masu nad’an rahoto nayi domin kuwa abun nema ne ya samu.
Asshe ce ta janyo Mommy wacce har lokacin bata komo daidai ba duniyarta na nema juya mata sama ya koma k’asa. A daidai lokacin Umma da Inna Dije suka take masu baya.
Can wani k’aramin lambu na shak’atawa dake daga cikin gidan ta baya kad’an Asshe ta k’arasa da ‘yaruwarta tana k’ok’arin zaunar da ita Umma ta k’araso ta rik’o hannun Asshe tana kuka “Ina zakuje.. Ina zaku gudu kuje ba tareda kun sanar dani makomar Auren D’anku da ‘Yata ba.?!”
Sai Mommy ta d’ago tana duban Umma dukansu biyu hawaye ne saman fuskokin su.
Daga can nesa Anisa ke hango su kawai sai ta saki murmushi ta koma da baya.
A can wajen taro kuwa Mik’ewa Ummul tai ba tareda tasan ina take jefa k’afafunta ba. Caraf Anisa tasha gabanta. Ta dan girgiza Kai kad’an tana duban Ummul d’in “This is life of the rich.. Surrounded by scandals.!” Ta d’ago gajiyayyun idanunta tana duban Anisa. Sai Anisa daketa k’ok’arin k’wak’ulo hawaye ta isa ta rungume Ummul. Ta fashe da kuka tana fad’in “I’m here for you Ummul.. I’m here for you. Ciwon ‘ya mace na d’iya mace ne.”
Ummul bata motsa ba sann batace komai ba sann babu wani abu mai alamun kuka ko hawaye cikin idonta. Idanun ne kawai a bud’e amma ita kanta bata san wace duniya take ciki ba. Anisa ta dubeta tace “Ummul mu bar maganan scandal din da matar Haidar tayi.. Na fad’a Miki, rana irin wann nake tsoron zuwanta.. Su d’in Sun jima suna b’oye abubuwa.. Taho muje.. Muje.. Ki gani da idonki ki kuma ji da kunnuwanki.. B’oye b’oye ya k’are.” Ta k’arashe tana janyo hannun Ummul wacce har lokacin bata um bata um um. Tafiya kurum take Anisa na janyota. Anisa ta kauda fuska gefe tana wata muguwar murmushi Wanda idan ba ita Anisar ba ko wanda suke shirya abubuwa tare ba lallai wani ya fahimta ba. Daga can gefe da yanda su Umma, Mommy, Asshe da kuma Inna Dije suke suka ja suka tsaya.
Umma taci gaba da girgiza Kai tana fad’in “Ba haka mukayi dake ba Asshe.. K’warai nasan yau ne wa’adin Auren zai cika Shiyasa da kuka shirya biki jiki na ya bani bikin mutuwar Auren kuka shirya..! Wacece wancan matar kuma meyasa kukayi ma D’anku AUREN WATA UKU da d’iyata? shin kunyi masa Auren domin mahaifinsa ya basa wani kwangila wajen aiki ne. Ko kuma dai Kun masa AUREN WATA UKU da d’iyata dan ku raba Aurensa da wancan matar tasa ce.?”
Mommy taci gaba da girgiza Kai tana hawaye.
Yayinda Inna Dije ta k’yalla ido ta hango su Ummul sai ta dubi Umma ta fara fad’in “Kar kiyi wani dramarki na k’arya a nan Suwaiba. Kowa ya kwana da sanin zakiyi fin haka idan Akan Auren da kika kudiri niyyan yima Ummul ne..!” Taci gaba da huci “Kina so ki ce mun ba da hannuwanki kika saida musu Ummul ba.? Kina so kice kin mance tsananin son da kike Ummul tai aure ko ta halin k’ak’a zaki iya jefata cikin ko wani irin Masifa da sunan Aure.! Suwaiba harta ‘yarki Ummul tasan zaki iya mata ko wani irin Aure matuk’a zatayi Aure ta bar gabanki..! Ta shiga nuna Asshe tana fad’in “Wann matar ta sanar Dani komai Suwaiba.. Ta sanar Dani yanda kika wulak’anta d’iyar D’anuwana kika saida musu ita dan a karya asirin da wancan shed’aniyar matar D’an nasu ta masa.! Ta sanar Dani yanda kika basu Auren Ummul domin ta zamto makarin asiri.! Ta sanar Dani cewa Boka shine ya basu lak’anin cewa su nemo ma D’ansu mace mai irin matsalar Ummulkhairi wacce maza ke guje ma Aurenta. Irin wann budurwar ita ce irin macen da za’a karya asirin da akai ma D’ansu da ita.. Ta sanar Dani yanda idonki ya rufe kikayi ma Ummul AUREN WATA UKU.. Auren mutuwa..!”
Baki na rawa Umma ke girgiza Kai “Auren mutuwa kuma Dije.?”
Inna Dije ta d’aga mata hannu alamun dakatarwa “Har haka kika tsani Ummul Suwaiba..! D’anuwana yana kwance yana jinya kika d’auki Ummulkhairi kika saidata dan ta zamto makarin asiri kamar yanda Boka ya fad’a ajalin Auren na tareda ajalin Ummul cikin watanni uku. Kaman yanda Auren D’ansu da wancan shed’aniyar zai Mutu haka Ummul zata Mutu tare da wancan Auren.!”
Sai Umma ta d’ago cikin tsananin daburcewa Jin Dije tana zayyano kalaman da batasan dasu ba dan a nata iya sanin Auren kwangila sukayi ma Ummul da D’ansu wanda Auren zai faru ne kawai na tsawon watanni uku dan mahaifinsa ya basa kwangila. Umma taci gaba da girgiza Kai bakinta ya kasa furta koda kalma.
Mommy da hawaye suka wanke mata fuska sai ta soma girgiza kai. Murya na tsananin rawa take furta “Wann duk haka ne kafin mu gyara niyyarmu.. Bayan da muka fahimci Allah shi keyi ba Boka ba. Wllhi tuni mun mance wancan shirin namu kuma Aure na tsakani da Allah nake fata da burin Haidar yayi da Ummul. Ita d’in Alkhairi ce ga ahalina.”
Anisa ta juyo ta dubi Ummul wacce har lokacin ko motsi batayi sai kallon Ummanta da Mommy da take ga wasu hawaye suna sauk’owa zuwa k’uncinta ba tareda ta iya koda k’ifta ido ba.
“Yau kin yarda dani Ummul.. Bayan tsawon lokacin da na d’iba ina k’ok’arin fahimtar dake soyayyar bogi da Mommy ta jima tana nuna miki.? Matar nan ‘Yaruwar Mahaifiyata ce nasansu farin sani na kuma san zasu tafi da nisa koda zasu kashe rai ne dan su samu biyan buk’atansu.. Na fad’a miki idan ranan tazo zaki yarda ni kad’ai ce na zauna dake bisa zallan gaskiya a cikin gidan.”
Bata kuma tsayawa sauraron Anisa ba. A hankali ta soma takawa zuwa yanda suke duk sai suka juyo suna dubanta. Kai tsaye gaban mahaifiyarta ta tafi ta tsaya.
Umma ta d’ago idonta mai zuban ruwa tana duban Ummul tana girgiza Kai.
Har lokacin idon Ummul Akan Umma “Wann shine dalilin ki Umma..? Wann shine dalilin da.. Yasa.. Kika hana na waiwayi gida sai bayan Watanni uku..? Haka ne Umma.?” Muryarta yaci gaba da rawa . Yayinda Umma taci gaba da girgiza kai tana hawaye tamkar wacce aka d’aure harshenta.
Duk sunyi shiru sai zuban hawaye. Mommy ma ta kasa tsaida nata hawayen.
Ummul taci gaba “Na kasance inada kurakurai na amma ba ni na zab’i k’addarata ba..” Muryarta yaci gaba da rawa “Umma nayi k’ok’arin na kasance ‘ya mai biyayya a gareki.. koda a wasu lokutan Babu Wanda zai fahimceki nakanyi k’ok’arin na fahimceki.. Sabida ke d’in mahaifiyata ce..” Taci gaba da jinjina Kai tana hawaye “Duka rayuwana k’ok’ari nake naga na faranta ma mutanen dake kewaye dani.. koda hakan na nufin na mance kaina.. Na kasance banida wani fata nawa..” Taci gaba da girgiza Kai “Auren karya sihiri..! Auren mutuwa..! Auren wata uku..!” Sai ta soma girgiza kai sosai “Ki gafarceni Umma.. Ki gafarceni..!”
Umma tai yunk’urin bin bayanta amma inaa ta wuce cikin gidan a guje tana kuka sosai.
Mommy tai saurin rik’o Umma tana fad’in ta kyaleta abi komai a sannu.
Ummul shiga cikin gidan kawai take ba tareda sanin ina take zuwa ba har saida ta isa wani bedroom.. Tana shigewa ta maida k’ofan ta rufe ta silale nan wajen tana mai fashewa da wani irin kuka. Sam bata kula da Haidar dake zaune shattered k’asa a d’akin ba. K’afafuwansa mik’e a k’asa ga babbar rigarsa a gefe.
Sosai take kuka tana girgiza Addu’a take cikin zuciyarta Allah yasa mafarki take. Allah yasa zata farka daga wann mummunar mafarkin.. Mahaifyarta.. Ashe har mahaifya zata iya jefa ‘yarda ta haifa cikin irin auren da ta jefata.. Shin har haka Umma take so ta bar cikin rayuwarta.? Umma ta mik’ata ayi tsafi da ita.!’ Sai ta rintse idonta sosai tana jin wani irin tashin hankalin da bata tab’a tsintar kanta ciki ba. A haka Haidar Ya rarrafo gareta. Duk a tunaninsa maganganun da Dareen tayi ne Ya jefa Ummul cikin wann yanayi baisan idan maganganun Dareen Ya jefata cikin rud’ani da firgici bai kama k’afan abinda taji mahaifiyarta ta aikata mata ba.
Haidar ya shigar da ita cikin jikinsa tana kuka shid’inma k’ok’ari ne kawai. Sosai Ya matseta cikin jikinsa yana fad’in “Let it all out.. Na cancani duk hukuncin da kika mun amma kafin ki hukuntani.. Zan so ki saurareni.. Hear me out first please..!”
Tana nan cikin jikinsa su duka biyun suna zaune k’asa. Saida tayi mai isarta kafin ta soma furtawa a fili “Labarin duka k’arya ne.. Babu wani gaskiya cikinsa...”
Haidar Ya kuma matseta cikin jikinsa “Akwai abu d’aya da yake gaskiya cikin labarin.. Shine soyayyarmu.. The love that I have for you Khairy.. I.. I love you.. I love you with everything I am..”
Jin kalaman take har k’wak’walwarta. Ta cire jikinta daga nasa tana dubansa. Sai ta girgiza kai “Shin kana sane da cewa AUREN WATA UKU suka mana.?”
Haidar da baisan da batun warware sihiri ba. Saidai yanada masaniyar AUREN WATA UKU na yarjejeniyar project da sukai da Mommy. Sai Ya soma k’ok’arin kauda fuskarsa kaman yana avoiding kallon idon Ummul d’in.
Mamaki Ya cika Ummul. Ta dan girgiza kai kad’an “Kasan da labarin AUREN WATA UKU.?”
Sai Ya lumshe idonsa a hankali Ya shiga jinjina kansa alamun haka ne.
Kawai Ummul sai ta soma girgiza kai tana ja baya gareshi.. Tsoro ne firgici ne ta ma rasa mai takeji..
Haidar ya soma girgiza kai cikin kid’emewa yana k’ok’arin nufota “But you need to listen to me first Khairy..”
Dakatar dashi Tai ta hanyar d’ago masa hannu. Muryarta na tsananin rawa “Kar ka masto yanda nake.. Kar ka k’araso yanda nake.. Gaskiya ne.. Cikin labarin gaba d’aya ni kad’ai aka shashantar..!”
Haidar bai fasa nufota ba yake fad’in “Khairy please listen to me.. Please hear me out first.. Allah shine shaida na.. Nayi niyyar sanar dake komai yau d’in nan.. Ciki harda Aurena da Dareen da kuma yanda namu Auren Ya kasance.. Dan Allah ki saurareni.. Na sani ni mai laifi ne.. But ki saurareni first.”
Jikinta Har rawa yake bata daina k’ok’arin dakatar dashi da hannunta ba “Kar ka k’araso yanda nake.. Bakada sauran abinda zaka sanar dani dan naji komai.. Auren.. Ya cika watanni uku a yau d’in nan… Ya cika wa’adinsa.. Ba abinda yai saura.. Lokaci yayi da zamu fice daga rayuwar juna.” Ta k’arashe tana k’ok’arin mik’ewa ta isa k’ofa.
Haidar ya tafi da sauri yai ma k’ofar lock. Yaja Ya tsaya.
Huci take tana dubansa shima d’in huci yake yana dubanta.
“Ka bud’e min k’ofa na fice ni ba matarka bace dan wa’adin Auren Ya cika.. Ko baka gani bane.!”
“Ank’i a bud’e d’in baza’a bud’e ba.. Nace ki saurareni first kafin ki yanke duk wani hukunci.. And one more thing.! Kar ki sake cewa ke ba matata bace.!”
Taci gaba da huci zuciyarta na mata rad’ad’i tasa hannu zata bud’e k’ofan Haidar Ya cire d’an makullin Ya jefa bayan gado.
Ummul ta d’ago tana dubansa cikin wane irin yanayi da bai tab’a ganinta ciki ba “Ka bud’e mun k’ofa na fice..!”
“Baza’a bud’e ba.! Ank’i a bud’e d’in.. Na ce ki saurareni muyi magana.”
Rintse idonta Tai ta toshe kunnuwarta sai ta fashe da kuka sosai “Bana so.. Bana so na saurari komai daga gareka..! Kawai ka bud’e mun k’ofa ni na fice.. Na tsaneka..! Na tsani ganin wann fuskar taka balle sauraron muryarka.!”
Sosai kalamanta ke masa zafi.. Sosai zuciyarsa ke masa zafi.. Bai bari takai aya ba ya k’araso da sauri ya rufe bakinta da nasa.. Ta shiga turasa da duka k’arfinta amma kaman zugasa take. Duk iya k’ok’arinta na ganin ta hana Haidar abinda yake k’ok’arin aikatawa ta kasa. Haka Ya rik’e bridal gown dinta ya k’eta da k’arfin gaske.
Ba a haka yaso zuwa mata ba. Ba haka yaso su shimfid’a tarihin soyayyarsu ba. Sam ba nufinsa bane ya saka mata force amma bazai iya jurewa ba, bazai iya jure kalamanta a garesa ba.. Idan hakan shine masa saura dan ta sauraresa zai aikata.
Taci kuka har ta gode Allah. Sabon tsanar Haidar da illahirin ahalinsa Ya kuma ruruwa cikin zuciyarta.
Hannayenta ya rik’o cikin nasa yana shafa sumarta a hankali.. Idanunta a lumshe suke gashin idon duk Sun jik’e da hawaye still hawayen basu daina fitowa daga lumsassun idonta ba.
Yaci gaba da Shafa gaban goshinta zuwa farkon sumarta da gumi yasa suka dada kwanciya luf. A hankali ya lumshe idanunsa ya sumbaci goshin nata “I.. I’m sorry Khairy… I didn’t mean to.. force myself on you.. But you forced me to..” Shiru yai ganin har lokacin idanunta a lumshe hawaye basu daina ziraro mata ba.
“Please don’t hate me.. Don’t hate me Khairy.. I grew up thinking.. My life was a complete mess.. Ba wani abu da yake gaskiya cikinta.. Duka k’arya ce kawai.. But then you came.. And changed everything..” Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “Idan akwai abu d’aya da yake gaskiya cikin rayuwana.. It is you Khairy.. Kece..!” Sai Ya d’an murmusa yana k’ok’arin maida kwallan da suka ciko idonsa “You know, For the first time in my life.. I experience true happiness.. You filled the emptiness inside me Khairy.. With you, I feel complete..” Sai ya d’ago yana dubanta sosai siririn hawaye ya gangaro masa “Punish me all you want.. But don’t say na rabu dake Khairy..I.. I just.. can’t bear the thought of it..”
Sai sann ta d’ago masa hannu alamun dakatarwa. Dan yanda kasan garwashin wuta haka takejin kalamansa.
Ta bud’e lumsassun idanunta a galabaice. Ba tareda ta dubesa ba ta yunk’ura zata tashi sai taji zafi sosai daga k’asanta. Ta rintse idanunta tana jin wani kukan na zuwa mata.. Ba kukan physical wounds din dake jikinta take sai na rad’ad’in da zuciyarta ke mata.
Haidar yai k’ok’arin taimaka mata ganin tana so ta mik’e amma sai yaji muryarta cikin kuka “Kar ka tab’a ni.. Na rok’eka kar ka sake d’aura koda d’an yatsa a jikina.” Ta k’arashe cikin k’ok’arin mik’ewa.
Ya zuba mata ido yana dubanta zuciyarsa zallan k’aunarta da tausayinta ne. Yanaji yana gani yana son taimaka mata Babu hali. A haka ta lallab’a ta bud’e k’ofan da take tsammanin bathroom ne. Nan kuwa taga shid’in ne ta shige Haidar na binta da kallo har ta b’ace ma ganinsa. Ya lumshe idanunsa yana mai furzar da huci had’ida shafe fuskarsa da tafukan hannayensa. Ya maidoda dubansa kan bridal gown d’inta da Ya b’aci da stain. Ya kuma lumshe idanunsa yana jin wani abu kaman tsanar Kansa can k’asar zuciyarsa… A hankali ya furta “Oh no.! What have you done Haidar.!” Ya furzar da huci zuciyarsa na tuhumar sa ‘What if she hates you.’?.. Saurin girgiza Kansa yai bai so ma ya tuna. He needs to save their marriage at all cost.
A b’angaren Ummul ma tana shigewa bathroom din wani sabon kuka ta fashe dashi. Zata iya cewa ita dai batasan wani abu soyayya ba sai akanshi.. Koda ace an gina Aurensu ba akan soyayya ba ta tsinci kanta da aukawa ma soyayyarsa..
A fili ta furta “labarin ya k’are ne Tun kafin ya fara dan na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 45 Chapter of 64