Share this page
is in love with his wife… Kodai ku masoya ne dama tintinin.?” Ta k’arashe tana tsaresa da ido. “Think whatever you want to think.!” Ya k’arashe yana matsowa kusanta kaman zai shak’ota tana k’ok’arin matsawa baya. Anisa taci gaba da Zare ido “Malam idan baka k’yaleni ba zan maka ihun b’arawo.!” Yaci gaba da jinjina Kai “Go ahead and shout! Let see waye yakeda abun fad’i ma ‘yansanda.” Sai kuma tai shiru tana ci gaba da Zare ido. Hisham yaci gaba “If you dare think of hurting Ummul.. Believe me I’ll deal with you myself.!” Cikeda tsoro had’ida mamaki Anisa ke dubansa. Sai kuma ta girgiza Kai tace “And… who are you to Ummul.? Dan ban yarda kana son kareta ne kawai dan kana abokin Haidar ba.” Kallon shashasha yaci gaba da yima Anisa dan da tasan lokacin da ya bugi bayan motarta Ya hanata bin bayan Haidar ba don Ya kare Haidar yai ba sai dan ya hanata gano Matar Haidar da Ahalin Haidar d’in basu san da ita ba wato Dareen da wann doluwar bata tsaya tana bata bakinta ba. “Idan kika sake yunk’urin cutar da ita .. Sann ne zaki san ko ni waye.” Anisa ta murmusa tana dubansa “Ta Ya zan cutar da ita balle Har ka bata kariya bayan an riga an d’auketa.” Hisham Ya dubeta ya kuma girgiza kai da mamaki “Kina so kice mun Ummul bata asibitin nan.?! Is she kidnapped or something.? Waye ya saceta.?” Anisa ta kuma murmusawa “One question at a time. Wanda ya fimu kusanci da ita daga ni har kai shi ya saceta.. Ina nufin mijinta..!” Ta k’arashe da murmushi saman fuskarta. Zuciyarta na tabbatar mata abokin Haidar son Ummul yake ba tareda sanin Haidar d’in ba. Amma ita idan har haka Ya tabbata ribanta ne dan zasu had’a team mai k’arfi wajen ruguza tsakanin Ummul da Haidar. “Ina Haidar Ya kaita.?” Ya tambaya yana duban Anisa. Anisa ta murmusa “Why not ask him.. After all, abokin ka ne… Kasan me.? Although Haidar never introduce his friends to his family na rasa gane ya akai nasan fuskarka matsayin abokinsa… Koda yake wann Dan uwan nawa bamuyi zaton ma nada abokai ba.. Maybe kaima d’in dan wajen aikinku d’aya ne Shiyasa.. Im sure na tab’a ganinka ka kawo masa wasu takardu da Ya danganci aikin company gida.” “Shut up.” Hisham ya katseta jin tana sunbatun da babu Wanda Ya tambayeta. Yaci gaba da dubanta “Kina jina.. Yes ina son Ummul. With every fibre of my being. Hasalima ni na fara sonta kafin ta zama matar Haidar.. You and I are going to help each other out. Ina so ki tabbatar min cewa my secret is safe with you kaman yanda naki ya zama safe dani. That is idan kina so mu raba su biyun.. Ki mallaki Haidar na mallaki Ummul.. Zan iya tabbatar Miki with my help.. Haidar will be yours forever..” Anisa ta zaro ido waje “Da gaske kake.. Let’s team up then.. Zanyi komai.. In fact kokari kullum nake dan burina Ya cika.” “Your wish has been granted..” Ya fad’i yana jinina kai. Take sukai exchanging phone number cikin k’ok’arin yanda zasu fara zartar da plan dinsu na k’ok’arin raba Haidar da Ummul. Tsaye Hisham yai a dakinsa na sirri Wanda hotunan Daddy Mommy harma da Haidar sune kawai a cikin d’akin an mammannasu jikin wall. Had’ida dangin magazines masu d’auke da labarun Maitama Builders. Da duk wani article da ya k’unshi scandals wanda sukai popping a labarun kasuwanci wad’anda suka danganci Kampanin Maitama da ahalinsa. kaf shi yake fitar da scandals d’in. Yai tsaye gaban hotunansu yana kallo lokaci guda yake furta “Why Ummul.? Why her..? Menene dalilinku na kawo Ummul cikin wann messed family din naku.!” Yakai dubansa kan hoton Mommy, lokaci guda yaci gaba “Kwaise Maitama ya kikaji zaman kurkuku.? you are the one who instigated everything.! You should suffer the consequences.. All the hardships nida mahaifyata had to experienced. Kece kika jawo.!” Yaci gaba da jinjina Kai “It is your fault that I had to search for people who would accept me all my life..?!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa. Yaci gaba da jinjina kai “You are now in Jail… Ke d’in yanzu kina tsare a kurkuku.. Abin takaicin kuma D’anki ne Ya kaiki. Did you know that… I was born in a prison..? Did you know that I grow up thinking ni ba kowa bane but a son of a criminal..?! Yai maganar cikin tsananin sakin huci kafin yaci gaba “This is the perfect time for me to ruin your life completely kaman yanda kika lalata nawa. Yanzu ne lokacin da ta kamata na fitar da labari akanki. Kinyi yunkurin kashe matar D’anki. Ya kika ji labarin Kwaise.? Abun zai matuk’ar k’ayatarwa musamman a shafukan labarun kasuwanci. Dan na tabbata Aliyu Maitama ba korar wulakanci kawai zai Miki ba muddin kika bata masa suna irin haka a duniyar kasuwanci. Zai tabbata dake da D’anki da kika koreni sabida shi naku rayuwar ya daidaice fiyeda yanda nawa rayuwar da na mahaifiyata ya daidaice. Saidai kashh.! Ummul ta shiga cikin wann ahalin naku. She shouldn’t get involved..! She shouldn’t.!” Yaci gaba da jinjina Kai yana sakin huci “Kaman yanda nai alk’awarin tarwatsaku haka nai alk’awarin fitar da Ummul daga wann ahalin naku. Sai na rabaka da Ummul Haidar domin kuwa ita d’in tawa ce.!” Ya k’arashe yana duban hoton Haidar da idanunsa da suka gama rinewa zuwa ja. ** Ba shi ya dawo gidan ba sai yamma lis. Tana nan kwance k’asa zazzabi Ya gama lullub’e ta. A hankali Haidar Ya tura k’ofan d’akin hannunsa rik’eda manyan ledodi. Hangota da yai kwance saman rug ya sanyashi saurin sakin ledojin Ya k’arasa gareta. Ya kai hannu ya tab’a goshinta ganin sai rawan d’ari take. Nan yaji jikin nata zafi k’au. A hankali ya furta “Oh no she’s burning up. What do I do..?!” Ya furta yana dubanta gashi ya mance magungunanta a pharmacy din da ya saya. Wani tunani ne yazo masa yai saurin d’agota daga k’asa Ya daurata saman gado ya shiga janyo bargo yana rufa mata ganin sosai take rawan sanyi.. Ya soma rurrufe windows trying to keep her warm. dan dik shi a tunaninsa haka ne zai sauk’ar mata da zazzabin ta daina jin sanyi. Amma sai yaji kaman zafin jikin ya karu ga rawan sanyin da take ya karu. Yai tsaye yana kallonta yana tunanin abunyi.. Ko room heater zai fita Ya nemo Yai warming dakin dashi..? Ya nufo waje sauri sauri yana tunanin nemo room heater. Cak kuma yaja Ya tsaya kaman Wanda aka dakatar dashi. “Dr Faruk.” Ya furta a hankali kafin ya soma jinjina kai “Yes I need to call him..” Ya k’arashe yana mai Ciro wayarsa daga aljihun jeans d’insa. Nan ya soma dialing layin Dr. Dr yana dauka Haidar Ya soma sanar dashi cewa jikin Ummul yayi zafi sann Ya mance bai taho da maganin ba. Meye first aid da ya kamata ya soma bata. Dr Faruk ya murmusa daga d’aya b’angaren. Soyayyar Haidar ga matarsa na kashesa “A cool shower will help.. And she should wear lighter and more breathable clothing.” Haidar ya jinjina kai yana nanatawa “A….. cool shower.. Ok, cool shower..” Dr ya kuma amsawa yana mai fatan samun sauk’i ga matar Haidar d’in. Haidar yai masa godiya kafin yai hanging up. Dawowa d’akin yai Ya ganta nan yanda ya barta saman gado tana rawar sanyi. Yai saurin k’arasawa Ya yaye bargon da ya rufa mata. Ya soma k’ok’arin rage mata tufafin jikinta amma sai ta takure jikinta waje guda tana fad’in Ya kyaleta dukda rawan sanyi da take. Cikeda takaici Haidar yai jifa da hulan da ya zame daga saman kanta “Fine then, take the shower like this.” Ya k’arashe yana mai dagota daga saman gadon Yayinda Ummul ke k’ok’arin tattaro sauran strength da ya rage mata tana janyewa daga jikinsa tana fad’in ina zai kaita ya kyaleta. Bai tsaya amsata ba Ya nufi bathroom da ita cikin hannunsa. Taci gaba da k’ok’arin turasa Haidar na rik’eda da ita yana fadin “Stay here and take a shower. You are burning up.” Ya k’arashe cikin k’ok’arin tsaida ita kan k’afafunta amma sai ta soma k’ok’arin zubewa a k’asa sakamakon rashin karfi. Bai bari takai kasa ba yai saurin k’arasowa ya rungumeta cikin jikinsa a daidai lokacin hannunsa ya tab’a switch na shower din ai kaw nan ruwan ya soma zubowa kawunansu su duka biyun. Sauk’an ruwan da taji saman jikinta a bazata ya sa ta sakin ajiyan zuciya Wanda yasa Haidar yai mata cover da arms d’insa kaman mai tsoron kar ruwan Ya cutar da ita. Ya shigar da ita sosai cikin k’irjinsa ruwan naci gaba da zubowa kansu. Yana jin yanda ruwan ke ratsa dumin jikinta zuwa nasa jikin. A hankali Haidar ke lumshe idanunsa yana jin harbawan da zukutansu keyi kaman a tare. Sun d’auke minutes a haka kafin yaji temperature dinta na sauka a hankali. A haka Ya fito da ita daga bathroom din su duka biyu jikkunansu a jik’e. Cikin kayan da ya shigo dasu Ya Ciro towel sabo Ya rufa mata. Ya d’auki hand towel din yana tsane sumarsa. Lokaci guda yake furta “Change those clothes before you catch cold.” Yana ida fad’in haka yasa zai fice yayinda Ummul ta mak’ale sosai cikin towel din da ya rufa mata. Tabbas zazzabin da takeji ya dan sauka. Sanda taga haikan zai kuma ficewa ya kulleta a wann dakin tai saurin bud’e murya tace “Dan Allah ka dakata.” Haidar Ya tsaya Cak sanda yaji muryarta. Ganin Ya tsaya yasa Ummul ci gaba “Meyasa ka kawoni nan ka kulleni..? Dan.. Dan Allah.. Ka fitar Dani daga kurkukun nan.” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya. Juyowa yai yana dubanta sai ya dawo da baya. Yai tsaye kanta hannayensa hard’e yayinda Ummul ta soma k’ok’arin jada baya. Sai taji ya soma fad’in “Who are you.? Meyasa kika yarda da auren mutumin da baki taba sani ba. Is that even possible.?” Shiru tai ba tareda ta iya amsa masa tambayarsa ba sai bugun zuciyarta dake karuwa. “Did Mommy buy you with money.? Nawa ta biya ta sayeki dan kawai kizo cikin rayuwana.?!” Ya k’arashe cikin d’aga murya. Ta soma girgiza kai tana hawaye. Abinda baison gani a rayuwarsa. Yai gajeren tsaki yana kauda fuska gefe jin bata amsa shi ba sai hawayen dake gangaro mata. “Fine.. Since you don’t want to talk. Enjoy your stay here. Dan bakida ranan fita a nan.!” Ya k’arashe yana mai jifa da hand towel din da ya gama tsane sumarsa dashi zuwa gefenta Wanda saida ya dan firgitata. Da taga haik’an da gaske zai kuma ficewa ya sanyata saurin fad’in “Nayi ne sabida Iyayena.!” Tai maganar cikin rawar murya irinta mai kuka. Haidar Ya kaikaito yana dubanta. Ya tako zuwa gabanta “Kin amince da auren mutumin da baki tab’a sani ba sabida iyayenki .? Are you that desperate.?!” Ta girgiza masa kai tana hawaye “Kud’in aure na.. Shi…. Shine kudin jinyar Abba na… Sann mahaifiyata…” Ta kasa ci gaba da magana sakamakon rawa da muryarta keyi. Haidar ya kafeta sosai da ido. Ya dan d’ibi dak’ik’ai a haka kafin yace “So I was right. Mommy sayenki tayi da kudi.. Nawa ta sayeki dashi.?!” Ya k’arashe maganar zuciyarsa na masa zafi. Ta rintse idanunta sosai hawaye na zubo mata. Ba yanda ta iya dole ta fad’a ma Haidar mak’asudin aurensa koda zai kawo karshen zamansu. Ita dai burinta taje ta fidda Mommy daga kurkukun da ake k’ok’arin kaita. Zatai komai dan ta kub’utar da Mommy matar da tun shigowarta gidan bata nuna mata komai ba face zallan k’auna. Muryar Haidar ta kuma ji cikin tsananin huci yana fad’in “You sold yourself to her.. You don’t deserve to go free.!” Yana maganar yana jinjina Kansa. Lokaci guda yasa kai ya fice rai bace. Kallo d’aya zaka masa ka fahimci abun ya masa zafi sosai. Ummul ta kuma runtse idonta wasu hawayen na gangaro mata. Can dare ta kuma jin shigowarsa dan har tayi zaton bazai kuma dawowa ba. Wann karon bai ko kalli yanda take tak’ure ba ya aje mata wasu ledodi. D’aya na abinci d’aya na magani. Baice da ita komai ba ya nufi k’ofa. Yana k’ok’arin fita ta rarrafo garesa tana rok’onsa “Dan Allah ka fitar Dani daga gidan nan.. Wllhi tsoro nakeji.. Dan Allah kar ka barni a nan..!” Ta k’arashe tana had’e hannu alamun rok’o. Wani kallo ya watsa mata kafin yasa kai ya fice yana mai rufe d’akin. Ummul tai lamo a wajen tana mai lumshe idonta Wanda kuka ya zame masu jiki. Ga dare ga jeji. Bata jin komai sai kukan tsuntsaye. Addu’a kawai take tana kai kukanta ga Rabbil Izza da Ya jibinci lamuranta. ** Washe gari Haidar bashi yazo gidan ba sai wajajen azahar. Ta Ida sallah kenan taji tsayuwar motarsa. Ga yunwa da ya azalzaleta. Tin bayan abincin da ya kawo mata bata kuma saka komai cikinta ba. Tai saurin mik’ewa ta Lek’a window dan tabbatar ma idonta ko shi d’in ne. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa sakamakon tuno abinda ya faru jiya. Tai saurin komawa da baya tana jin bugun zuciyarta na k’aruwa. Sanda Haidar ya turo k’ofan kanta a k’asa. Ya dan d’auki lokaci tsaye daga k’ofan yana dubanta. Janye idonsa yai daga barin dubanta yana k’ok’arin shigowa d’akin dan shima a b’angarensa yana shigowa Ya soma tuna kasancewar da sukai tare k’asan shower a jiya. Yai gajeren tsaki yana mai shigowa dakin. “Have you taken your meds.?” Ya fad’i kaman baya so. Daga nan yanda yake tsaye. Jin bata amsashi ba yasa shi yin gajeren tsaki ya isa ya janyo ledan maganin yana d’aga ko wani maganan Wanda a rubuta dose jikin ko wanne. Nan yaga dai tasha duka. Cikin ko inkula Ya aje mata ledan abinci kafin ya tako zuwa gabanta “Ke.!” Ya fad’i yana dubanta. “Sunana Ummulkhairi.” Ta basa amsa daga nan yanda kanta ke kife. Bai ambaci sunan nata a fili ba dukda zuciyarsa ya maimaita the moment she closed her lips. Takarda ya mik’a mata “Sign these papers.” Ya fad’i cikeda umarni. Ta dubeshi ta dubi takardun da yake mik’a mata. Sai ta girgiza kai kad’an “Na menene..?” “You want be free. Then sign these..!” Ya kuma fad’i yana mik’a mata. A hankali tasa hannu ta karbi takardun tana dubawa. Dukda ba wai ta fahimci bayanan da suke kan takardun sosai bane. Ta gane takardu ne daga Kotu Wanda idan ta saka hannu tamkar tayi k’arar Mommy ne kai tsaye. Bata San meyasa Haidar ke fad’a da mahaifyarsa irin haka ba. Mahaifiyarsa fah yake yunk’urin kaiwa prison. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Anya yasan k’ima da darajan mahaifiya.? Waye yake fad’a da iyayensa sai tab’ebb’e. Ta d’ago a d’an tsorace tana dubansa “Bazan iya ba.. Bazan iya kai Mommy gidan Yari ba.!” Ya duk’o da fuskarsa kusan nata “Why.? Are you even related to her.?!” Yanda yake maganar tamkar fuskokinsu zasu hade waje guda. Ummul na iya jin huci da tururin numfashinsa saman fuskarta mai cikeda tsoro. Ya damk’o hannunta da iyaka k’arfinsa yana fad’in she should sign the papers. Batajin tana da k’arfin da zatayi kokawa dashi amma abu guda da ta sani shine har abada bazata kai Mommy prison ba. Wani dabara Ya fad’o mata kawai sai ta fashe da kuka tana k’ok’arin rik’e b’angaren da akai mata aiki alamun na mata ciwo. Haidar yai saurin sakinta yana kallon yanda take kuka tana kama wajen. A d’an daburce Ya soma fad’in “I.. I didn’t mean to hurt you… This is your fault you know. Da ace kinyi abinda nace it wouldn’t have to be this way. Wait let me see..” Ya soma k’ok’arin janye rigarta ai sai ta zaro ido da gaske ganin zai dage mata riga. Ta soma turasa cikin tsananin k’idimewa tana fad’in “Ai Ya.. Ya ya daina.. k’alau nake yanzu ka gani..!” Ta mik’e tsaye kan k’afafunta kaman wacce aka razaneta cikin k’ok’arin nuna masa lafiya take ba ciwon dake damunta. Ya tsareta sosai da ido. Wato kukan da take acting ne kawai ba ciwon da take ji. Da taga da gaske zai d’age rigarta ta daina acting d’in. Women are so good in acting kaman dai mahaifiyarsa. Sai shima ya mik’e tsaye yana binta da kallo daga sama Har k’asa. Ya kula har lokacin kaman rawa jikinta yake. Ai kuwa idan Har haka ne Ya gano lagonta. Zaisa tai signing papers din cikin sauk’i. Ya soma takowa gareta tana k’ok’arin jada baya. “Kodai ki saka hannu a takardun nan a dad’in rai… Ko kuma…” Yana maganar yana k’ok’arin balle botiran rigarsa. Bai kuma fasa nufota ba. Ta soma girgiza kai hawayen gaske na zubo mata “A’a dan Allah..!” Cikin rawar murya take maganar har saida Haidar Ya cimmata. Zuciyarta bai daina tsinkewa ba ganin ya mata rumfa “Zaki saka ne ko na sakaki kisa da k’arfi..!” Ya fad’i fuskarsa dab nata. Dukda zuciyarta dake tsananin bugu bata fasa girgiza masa kai tana fad’in “K’ima da darajan mahaifiya Ya wuce ai fad’a da ita balle a kaita kurkuku duk girman laifinta.!” Bakinta dake fitar da kalaman yaketa kalla zuciyarsa na kuma masa zafi da kiran Mommy mahaifiya da take dan shi a idonsa Mommy bata canci a kirata mahaifiya ba. Jinjina kai yake yana huci “You think I’m playing here right.?!” Batai aune ba taji ya rufe bakinsa da nata. Hankalin Ummul yakai k’ololuwa wajen tashi. Al’amarin da ko a mafarki bata tab’a hasasho kanta ciki ba sai gashi na k’ok’arin faruwa da ita. Numfashinta ne Ya soma fita sama sama… Take taja wani irin numfashi ta zube masa a wajen. Ya duk’a yana jijjigata yana fad’in ta tashi ta daina wann wasan kwaikwayon. Shiru bata tashi ba har dai Haidar Ya soma tunanin ko sumar gaske ne tai. Ya tashi ya fice cikin k’ok’arin kawo ruwa ya yayyafa mata aiko yana ficewa Ummul ta mik’e a guje dikda rawa da jikinta keyi ta isa ta rufe k’ofan dan dama ya bar key d’in jiki. Da mamaki ya juyo yana duban k’ofan. Ta dai k’ara shashantar dashi a karo na biyu. Ya girgiza Kansa k’adan yana mamakin yanda Ya fad’a tarkon yarinyar Har sau biyu dikda matsalan saurin yarda da yake dashi gashi har sau biyu ya yarda da acting da Ummul tayi. Lallai da alama wann yarinyar zata basa matuk’ar wahala kafin ya samu ya cimma burinsa na tura Mommy prison. Sai kuma yaji gaba d’aya jikinsa ya sake kaman baida sauran kuazari. Ya isa saman kujera ya zauna gijif had’ida kishingid’a. Ya lumshe idanunsa bugun zuciyarsa na k’ok’arin daidaita. ** Police headquarters. Barr ya dubi Daddy da Mommy ya dan girgiza Kai “Zamu iya making abun Ya zama kaman illegal detention tinda Haidar ya b’oye matarsa babu Wanda yasan yanda take.” Daddy yace “So does that mean they would let her off the hook.?” Kafin Barr yakai ga bada amsa Mommy ta katsesu “No.. I don’t want money or power to speak for me.. Iyakacin abinda nake so shine D’a na ya dawo gareni.. I’ll plead guilty, if that’s what it takes… Zan amsa laifin gaban Alk’alai zan tafi prison for Haidar to forgive me.” Daddy ya dubi Barr yace ya dan basu waje. Bayan Barr ya fice ya tsare Mommy sosai da ido kafin ya soma girgiza kai cikin rashin yarda “You don’t know what you are talking about Kwaise. Do you really want to get convicted.? That ungrateful Son of yours doesn’t even care about you..!” Mommy na hawaye take jinjina kai “Yes.. Zanyi idan hakan zai kawo maslaha cikin rayuwar Haidar. Na rasa shi a farko.. I can’t lose him again.” Daddy yaci gaba da girgiza kai “You know you can’t appear in court da aurena akanki, bearing my name… Mai kike tunanin sunana zai zama a duniyar Kasuwanci.?!” Mommy na kallon Daddy take girgiza kai “Then end it Engr.!” Da tsananin mamaki Daddy ke kallonta. Duk juran zaman da tai a gidansa dukda rikon ko inkula da yake masu daga ita Har Dan nata bata tab’a zab’an rabuwa dashi ba daidai da rana guda sai gashi yau tana fad’in haka kai tsaye. “It has always been… an empty marriage that’s hanging by threads… Watak’ila sabida Haidar ka barni na zauna. Saidai a bangarena na zama lost between zama Mata ko Uwa.. Watak’ila na zab’i na zauna ne Thinking one day komai zai wuce ahalin Ya daidaita… Na Had’iye komai sabida D’ah na da mijina. I even named him after you… I turned myself into a monster a k’wayar idonsa ba tareda nayi la’akari ba. Na tilasta masa ya zamo abinda nake so thinking watarana zaka k’aunacesa zakai alfahari dashi kaman yanda ko wani uba yake… Ya kai matsayin da Har na mance cewa ni Uwa ce dik cikin k’ok’arin ganin burina na had’e kan ahalin Ya cika. But then I realise wann burin nawa bazai tab’a cika ba… Dik abinda naso ma nawa D’an na hana ma D’an wata ya samu.. Na rabaka da D’anka da matarka… Ta Ya zanyi zaton zan samu wann farin cikin da nake fad’i tashi akai tsawon rayuwata..? I am so selfish.” Kuka ya hanata ci gaba da magana yayinda jikin Daddy yai matuk’ar yin sanyi. Mommy ta share hawayen da suka zubo mata kafin taci gaba “Na gode da hakurin da kai Dani tsawon shekarun nan. For letting me stay koda sabida D’anmu. Na gode da ahalin da ka bamu koda bai zamto kaman ko wani ahali ba. Koda cike yake da tarin k’alubali.” Taci gaba da jinjina Kai “I give up Engr.. I’m tired.. Na gaji.. Iyakacin abinda nake so a yanzu shine D’ana Ya dawo gareni. The wealth, the name.. Duka na hakura dasu. Na zab’i D’ah na.. Na rasashi daga farko bazan kuma sake rasashi a karo na biyu ba.!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya hawaye na gangaro mata. Daddy ya kauda fuskarsa gefe yana k’ok’arin maida hawayen dake yunk’urin ciko idonsa. Bai kuma cewa komai ba sai mik’ewa da yai ta fice cikin sauri. Mommy ta kuma rintse idonta wasu hawayen na gangaro mata. A halin yanzu ta gama aminta bokan da suka je wajensa itada Asshe mashahurin makaryaci ne. Tinda gashi turaren da Ya bata ta bama Ummul yasa ta fad’a uku. Dama ita bata tab’a yarda da aikin boka ba ko can baya Asshe ce ta ingizata sukaje. Sann she was desperate ta dawo da D’anta gareta. Bazata gushe ba zataci gaba da rok’on Allah Ya yafe mata kaucewa da tayi dan Tabbas taga aya. Zuciyarta na cikin natsuwa da aminci matuk’a Haidar d’inta na tareda Ummul. Ta aminta da hankali da natsuwar Ummul. Tanada yak’inin D’anta bazai tab’e ba cikin ikon Allah matuk’a na tareda Ummul. Da wann tunani Zuciyar Mommy ya dan samu natsuwa. SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!* *37* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* Bayan shud’ewan awanni ta mik’e da kyar dan a tunaninta ya tafi musamman da taji sam babu d’uriyarsa. Window ta lek’a a hankali kaman mai tsoron kar a ganta. Ga mamakinta shi ta hango zaune k’asar wata bishiya Ya bada baya ma yanda take tsaye daga cikin d’akin. Tsuntsayi ta gani kaman dangin tattabarai Sun taru gabansa sai watsa masu abinci yake suna ci. Wasu Har kaman zasu d’ale saman hannunsa. Kai da gani zaka fahimci yana cikin annashuwa da jin dad’in abinda yake. Juyowa yai yana watsa ma sauran abincin nan ta hango kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Abinda bata tab’a gani ba. Zuciyarta yai wani irin yankewa tai sauri ta koma da baya had’ida jingina jikin gini. Ta d’auki lokaci a haka. Kafin ta kuma rintse idonta sakamakon tunowa da tai da yanayin da suka kasance ciki bada jimawa ba. Bata San dalili ba amma sai taji hawaye Sun ziraro mata. Ta jima nan a haka kafin ta bud’e lumsassun idonta da suka jike da hawaye. Ta kuma leka window amma sai taga bata gansa ba wann karon. Babu tsintsayen shima baya nan. Babu ko alamunsa. Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin tai k’ok’arin saita kanta. Bata San ya za’ai tai escaping kurkukun da Haidar ya boyeta ciki ba. Bata san hanya ba bata kuma san idan zata iya isaga Mommy ba. Saidai abinda take da tabbaci akai shine zata fice tinda tai saa makulin na tareda ita. Zata fice kodan taje ta ceci Mommy. Har abada

Chapter 32 of 64