taga mijinta ke kira wato Daddy. Zuciyarta yai wani irin yankewa..Sai tai saurin matsawa da baya. Saima ta fice daga parlorn cikin sauri ba tareda ta tab’a wayar ba sabida zuciyarta da Ya tsananta bugu.
Koda Daddy bai samu wayar Mommy ba sai ya kira na Haidar dake tareda Sadis daga waje saman wani d’an dakali. Nan Daddy ya buk’aci ya hadasa da mahaifiyarsa idan suna tare. Haidar ya mik’e Ya nufi cikin gidan yanda Ya taddasu gaba d’aya kasan rumfar dake tsakar gidan. Mama Tani da Ummul na daga ciki tana taimaka ma Ummul d’in da wanka. Jaririn kaw na rik’e cikin hannun Hajja shima an masa nasa wankan Mommy tana fad’in a kwantarsa cikin mosquito net d’insa. Hisham tsaye daga gefen Hajja yana kallon jaririn da murmushi saman fuskarsa lokaci guda yake tambayar “Hajja wai an masa suna kuwa..? Ya kamata dai na samu takwara.”
Muryar Haidar suka sinkayo yana fad’in “Aliyu..!” Gaba d’aya suka juyo suna dubansa.
Haidar yaci gaba daga nan yanda yake tsaye “Sunansa Aliyu..!”
Gaba d’aya sai murna Ya kacame waje Ya dauka ana Allah Ya raya Aliyu. Another Aliyu in the Family.. Aliyu the 3rd. Hajja Fannah ta mik’a shi ma Mommy tana fad’in Allah Ya raya musu BABA ALI.
Haidar Yaci gaba da takowa Har gaban Hisham da takaici Ya nuna k’arara a fuskarsa. Yayinda hankulan mutanen dake wajen Ya tafi ga murnan sunan Aliyu da aka sake sakawa cikin ahalin Haidar kaw yai tsaye gaban Hisham da tuni yayi mutuwar tsaye wajen like a loser. Kyakkyawan murmushi saman fuskar Haidar hannayensa sakale cikin aljihun jeans d’insa. Ya dan rank’wafo da Kansa saitin kunnen Hisham “He’s named after his Dad.. He will grow up like a Lion.. Just like his Dad.!”
Hisham ya had’iyi abinda yai masa tsaye a mak’oshi yanaji kaman ya shak’o Haidar amma ba hali.
Haidar yaci gaba “ I had a great Victory.. Like a Lion… I beat you Hisham.!” Yaci gaba da murmushi yana jinjina kai “I won.. You are the loser..” Ya gyara tsayuwarsa Ya tsaya k’yam gaban Hisham Har lokacin da murmushi saman fuskarsa. Har ya juya zai soma tafiya sai kuma ya juyo yace “You should change your last name.. You must be eager to bear the name Aliyu Maitama.!” Ya k’arashe still da murmushi lokaci guda ya tsime had’ida sa kai ya bar wajen. Ai Hisham bai kuma k’ara Minti d’aya tsaye wajen ba ya fice a gaggauce zuciyarsa na masa d’aci.
Ummul ma a sama taji wai Haidar yayi ma jaririnta suna ya kumayi ma Kansa takwara. Takaici ya cikata.. Sabida tsaban gadara ko sanar da ita bai ba yama kansa takwara. Tana Jin sai shelan sunan suke a tsakani bata ko bi takansu ba.
Bayan Mommy da Haidar Sun keb’e nan yake sanar da ita Daddy nata nemanta a waya baya samunta.
Mommy tace “Af aiko inaga na baro wayar can yanda nai sallah..” Aiko batai shiru ba Daddy ya sake kiran layin Haidar.
“He’s calling again.” Haidar yace yana kokarin daga kiran. Ya sanar da Daddyn suna tare da Mommy sann Ya mik’a mata wayar yana mai bata privacy.
Bayan sun gaisa Daddy ke tambayarta ina ta shiga yaketa nemanta duk a dame yake maganar.
Murmushi Tai kafin tace yai hak’uri hira ce tai dad’i.
Daddy yace “Ya kamata ki taho masauki haka nan.. Is getting late already.”
Daidai lokacin Hajja Fannah ta taho da abincin da ta kawo ma Haidar sai ta aje gefen Mommy ganin ba Haidar wajen.
Mommy ta dubi Hajja Fannah sai tace “Nidai idan ka min izini zan kwana nan gidan Fannah.”
Cak Hajja Fannah ta dakata da abinda take sanda ta jiyo abinda Mommy tace. Bata ida mamaki ba saida ma taji Mommy ta saka wayar a speaker. Tana jin sanda Daddy ke fad’i daga d’aya b’angaren “Shikenan ni kuma sai ki barni gauro a nan.”
Mommy ta murmusa kad’an “Toh ka k’ara mana kawai Engr… Kaga idan bani nan inada mataimakiya..”
“Aw haka ma kika ce.. Shikenan zan k’ara amma sai idan kece kika samo min matar.”
Mommy ta dan ware ido “Ina ka taba ji an nemo ma miji mata.?”
Daddy ya murmusa daga d’aya b’angaren “Za’a fara akanki.. Na baki wuk’a da nama Kwaise ta.”
Hajja Fannah da gaba d’aya ta gaza sukuni daga nan yanda take duk’e. K’afafunta Har rawa suke.. tana k’ok’arin mik’ewa taji Mommy ta kamo hannunta gam ta hanata barin wajen.
Mommy ta d’ago ta dubeta bayan sun gama waya da Daddy.
“Fannah nasan nayi kasalandan ma rayuwarki.. Amma bakida gidan da Ya wuce gidan Aliyu Maitama. A baya nayi zaton cewa zamana ni kad’ai a gidan Aliyu Maitama shi zai kawo min dawamammiyar farin ciki Shiyasa nayi duk yanda zanyi naga na rabaku.. Ashe abun ba haka bane.. Sai gashi bayan tafiyarki na rayu ni kad’ai amma Babu farin cikin da naci buri.. Ba abinda yafi komai kawo farin ciki a rayuwar nan kamar ka tsarkake zuciyarka.. Ka zauna da kowa tsakani da Allah.. Shi kuma Allah sai Ya saka maka nutsuwa farin ciki,harma da kwanciyar hankali a zuciyarka..!” Ta kuma kamo hannayen Hajja Fannah “Kaman yanda na zamto silan raba Aurenki da mijina a baya ina so ki bani dama na zamto silar maida Aurenku a yanzu.!”
Hajja ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Mommy yayinda Mommy taci gaba da jinjina Kai murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta “Na san bazaki ce a’a ba dan mijina d’aya ne tamkar da dubu. Ki yarda Dani.. Ina son mijina.. Ina matuk’ar k’aunarsa… This is the hardest decision of my life.. Amma bazan ja da hukuncin Ubangiji ba. Ina rok’on Allah Ya had’e kawunan ‘yayanmu Ya bamu ikon kyautata ma juna tareda yima mijinmu biyayya.” Sai suka rungume juna kukan Hajja Fannah na k’aruwa.
Asshe dake kallonsu daga nesa murmushi Tai tana mai goge hawayen da Ya gangaro mata.. A cikin zuciyarta take cewa ina ma ita da nata Abokan zaman zu zamto haka.
Bayan da Haidar Ya dawo wajen Mommy sai Tai masa tayin abincin da Hajja ta kawo masa. Tab’e baki yai kad’an had’ida girgiza kai “I’m good Mommy.” Ya kuma duban Mommy da kyau “Mommy nace are you sure this place will accomodate you all..?” Yai maganar yana daga ido yana duban gidan cikin wane irin yanayi.
Mommy ta jinjina kai “Eh mana. K’warai kuwa.. Kaga dukanmu mata ne haka nan zamuyi squatting.”
Da mamaki Haidar ke duban Mommy “Mommy keda kanki kike using word din squat.?!”
Mommy ta kuma murmusawa tana duban gidan “Mamaki kake Hajiya Kwaise Maitama zata kwana cikin gidan da bai kai darajan d’akunan ma’aikatan ta ba..?” Ta kamo hannayen Haidar cikin nata “Haidar my Son. Shi dan adam bai gane cewa shi ba koman komai bane until life humbles us.. Mu d’auki rayuwa da sauki dan mu d’in daga turb’aya muke kuma cikinta zamu koma.”
Haidar ya jinjina Kai a hankali “Haka ne Mommy..” sai karada “But Mommy.. Kinaga Khairy da Baby zasu iya kwana a nan..? I mean anyi yawa a gidan.. The place is too crowded.. Plus I don’t like the vibe here..”
Mommy ta saki baki tana dubansa. Sai ta dunguri keyarsa wann karon “Rufe min baki ban son iyayi. Kai a dole kayi D’a ko.. Aiko dukanmu nan daka gani haka dai zamu kwana a nan har Allah ya wayi gari da izininsa. Naga ta yanda zakai kinibibin idan ka bud’e ido ka ganka Abuja Baba Ali na wajen uwarsa a Kano.”
Ya dan furzar da huci kad’an “Mommy ni fah.. Gaskiya bazan iya komawa Abuja ba tareda an maida Aurenmu da Khairy ba..”
Shiru Mommy tai tana dubansa. Sai ta girgiza kai kad’an “Haidar ni a nawa shawarin. Da ka bar maganar maida Auren nan ba yanzu ba.. Ummul bata jima da haihuwa ba… Ga abubuwan da suka faru.. Ga iyayenta can gida da zataje ta fuskanta.. Give her some time to recover.. Sai ai komai cikin lumana.”
Duban Mommy ya d’anyi fuskarsa duk a dame “But Mommy..”
Ta katsesa “No buts Haidar.. This is the right thing to do.. Yanzu ma ni abinda nake so da kai ka kira can station din da Anisa ke tsare ka bada umarnin a saketa.. Kawo wann lokacin nasan ta gane kurenta.”
Ya d’anyi jim yana duban Mommy. Sai Ya shafe fuskarsa da tafukan hannayensa “Mommy kiyi hakuri.. ba wai bana so a saki Anisa bane.. It breaks my heart seeing Aunty Asshe like this.. Mommy akwai Wanda nake so na kama ne.. Kuma through Anisa kawai zan kama shi.. But I promise you da zaran bincike Ya kammala Anisa will be free.”
Ta jinjina kai a hankali tana dubansa. Sallama yai ma Mommy kafin ya tashi ya fice ya nufi nasa masauk’in.
**
Washe gari kaman yanda suka tsara sassafe Sadis ya kwashesu suka d’auki hanyar Kano.
Tuni Daddy ma Ya tasa kan ‘ya’yansa Haidar da Hisham suka bi jirgi zuwa Abuja. A Cewar Daddy akwai gabatarwa na musamman da zaiyi a Company gameda ‘ya’yan nasa musamman Hisham Wanda daukacin ma’aikatan Kampanin suka sansa da ordinary employee a baya. A halin yanzu zai koma ne matsayin D’a ga mai jagorancin Kampanin.
Ba yanda Haidar ya so sabida Daddy dole yabi umarnin mahaifin nasa ya tafi tareda su.
*
Umma na zaune tsakar gida taji Sallama Ya kacame ko ina. Ta mik’e cikeda farin ciki tana ganin masu shigowa. Mama Tani dasu Azeema ne suka soma shigowa.. Su Azeema dasu Khulsum suka haye jikin Umma suna fad’in sunyi kewarta.
Umma ta dubesu jiki a mace ganin bataga Ummul tareda su ba. Cikin rawar murya take tambayarsu “Ina Ummulkhair..? ina ‘yaruwarku.?!”
Bata rufe baki ba ta hango Ummul na shigowa cikin matuk’ar sanyin jiki, kanta kife ga jariri sabon haihuwa nad’e cikin hannunta. Mommy da Aunty Asshe na biye da ita.
Umma ta mik’e cikin matuk’ar sanyin jiki tana duban Ummul dake shigowa. Tuni Umma ta soma tafiya ta nufi Ummul. Tana k’arasowa gareta taja ta tsaya kukan da taketa k’ok’arin dannewa yana kuma fizgarta “ ‘Yata.. ‘Yata Ummulkhair..!” Sai Umma tai bursting cikin kuka yayinda Ummulkhair ma kuka ya kufce mata.
Asshe ce ta amshe jaririn daga hannun Ummul wacce tuni ta zube k’asa gaban Umma tana kuka sosai.
Sai Umma ma ta duk’a ta rungumeta ‘ya da uwan suka b’ige da kuka mai ban tausayi..
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*58*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Kan Ummul bisa cinyar Umma hawaye naci gaba da gangaro mata yayinda Umma ke ci gaba da Shafa kanta a hankali itama d’in hawaye ke gangaro mata.
“Nayi kewarki… Nayi kewarki sosai Ummata.. Dan Allah Ki yafe mun..!”
Umma taci gaba da Shafa kanta a hankali murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta “Baki na goma kenan kike neman gafara na Ummul.. Ni mahaifyarki ce kuma na yafeki tun kafin ki nemi yafiyata.. Babu abinda yake tsakanin ‘ya da uwa face yafiya da afuwa.!”
Sai Ummul ta sake bursting cikin kuka mai tsuma zuciya. Daidai nan Mama Tani ta shigo da Baba Ali dake yan k’anan kuka tana sanar da Umma tafiyar su Hajiya Kwaise da Hajiya Asshe.. Umma ta amshi jaririn tana lallashinsa lokaci guda take ce da Ummul maza ta mik’e ta kintsa kanta ta kula da yaron kafin Abbanta ya shigo.
Ummul ta d’ago ta dubi Umma tana goge ragowar hawayen dake fuskarta. Murya a sanyaye tace “Umma da gaske Abba ya samu lafiya Har ya fara fita kasuwa.?” Tai maganar tsantsan farin ciki na nunawa a fuskarta.
Umma ta murmusa “K’warai kuwa. Abbanki ya samu lafiya.. Nan bada jimawa ba zai shigo da yardar Allah.”
Sai Ummul ta mik’e jiki a sanyaye tana tunanin yanda had’uwarsu da mahaifin nata zai kasance.
Wanka sukai ita da jaririnta dan tuni Mama Tani ta d’aura ruwa bisa murhu tin isowarsu. Yaron Ya samu bacci da yaji ruwan d’umi. Umma ta saka yaron gaba tana kallonsa sassanyar murmushi saman fuskarta. Yau ga D’an Ummul dinta nan tana gani za kuma ta sab’asa a baya ta goya da izinin Allah. A haka Mama Tani ta shigo ta taddata. Su duka biyun suka tasa yaron gaba suna kallo. Mama Tani Tai saurin bud’e net d’insa tana k’ok’arin rufa masa Umma tace “Yaya naga dare baiyi ba da an kyalesa da gidan sauron nan tuk’uri ne dashi.”
Mama Tani ta rufe gidan sauron ruf tana fad’in “Um um Suwaiba gwara dai mu killacesa jikan Manyan mutane ne wann.. Ina mai baki labari gobe zakiga Hajiya Kwaise sassafe gidan nan matuk’a tana garin nan.. Muddin taga alamun cizon sauro jikinsa na tabbata bazata bari ya kuma kwana gidan nan ba.” Ta gyara zama tana kame hab’a “Umm Suwaiba am.! mu muka sha kallo yanda ake taltala yaron nan da kyar Ubansa Ya amince a taho dashi nan.” Ta k’arashe tana gyara zaman net d’in sosai.
Umma ta murmusa tana girgiza kai kad’an. Sai suka dubi juna itada Mama Tani sanda suka hangi ‘ya’yansu ras zaune daga parlorn Umman.
Mama Tani ta girgiza kai tace “Wato Al’amarin Allah sai a bar masa kayansa Suwaiba. Duk Wanda yace zai shishigi ko k’atsalandan a hurumin Ubangiji toh fah Tabbas sai Allah Ya nuna masa iyakarsa. Yanzu dai ki duba kiga yaran nan yanda muka ci musu burin zaman gidan miji gasu nan ras a gabanmu yanzu. Ba wai basu je gidan mijin ba sunje amma sai Allah Ya dawo mana dasu gabanmu dan mu hankalta mu kuma dauki darasi. sabida a lokacin da mukaci musu burin zama gidajen mazajensu bamu nemi zab’in Allah ba sann mun zata iyawan mu shi zaisa su samu mazajen aure kuma su natsu a gidajen Aurensu. Ashe ba iyawan mu bane ba kuma wayonmu bane.”
Umma ta jinjina Kai “Wann gaskiya ne Yaya. Allah yasa hakan ya zamto izna a garemu da masu hali irin Wanda mukayi a baya.”
Mama Tani ta amsa da Ameen Suwaiba.
A b’angaren Ummul kuwa sabon tashin hankali ta shiga dan tinda Abba ya dawo daga kasuwa yak’i ya dubi koda yanda take balle ya amsa gaisuwarta. Ko jaririnta bai kalla ba balle ya amshe sa.
Tai kwance lamo saman cinyar Umma hawaye naci gaba da gangaro mata “Umma Abba yak’i ya min magana. Yak’i amsa gaisuwata.. Yak’i ya dubi jaririna.. Umma Abba bazai tab’a yafe min ba..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.
Saurin toshe bakinta Umma tai “Kul Ummul. Kar ki sake magana irin haka..Kiyi ma Abbanki uzuri dan tinda ya farka daga jinyar nan nasa al’amarinsa sai a hankali. Musamman idan ya hau dokin fushi. Masana sun alak’anta hakan da magunguna masu k’arfi da yake sha ga kuma ya hadu da girma. Ki basa lokaci a hankali zai sauk’o ya huce kinji koh. Maza tashi ki daina kukan nan haka.. Kici abinci ki sha ruwan d’umi kafin Babban mutum ya tashi a nasa barcin.”
Ummul ta mik’e zaune tana goge hawayenta tana tunanin irin soyayya da shak’uwar dake taakaninta da mahaifinta yau an wayi gari itace Abba take gaishesa ya juya mata baya ba tareda ya dubi koda yanda take ba balle ya amsa gaisuwarta. Jiki a matuk’ar sanyaye ta nufi band’aki nan cikin d’akin Ummanta. Dan a gyaren gyaren da Haidar yasa akai ma gidan harda band’aki akai masu gaba d’aya kowa cikin d’aki aka kuma kawata ginin gidan kaman ba shi ba.
Zama tai ta saka abincin gaba ba tareda taci ba. A haka Umma ta shigo d’akin ta taddata zaune saman pillow kaman yanda ta shirya mata wajen zaman. Umma ta soma da lallashi amma Sam Ummul bata iya cin abincin ba har dai Umma ta dan soma mata fad’a maimakon taci abincin kawai sai ta b’ige da kuka. Ta kasa yarda wai ita Ummulkhair d’in Abbanta Abba ke fushi da ita irin haka. A haka Khulsum ta shigo rik’e da waya tana fad’in “Adda Ummul ga Ya Haidar a waya yace a baki.”
Ko sauraron Khulsum batai ba balle ta amshi wayar.
Khulsum ta dan furzar da huci tace dashi “Tak’i ta amshi wayer.”
Umma ta tsare sosai tace maza ta amshi wayar. Ba don taso ta amsa Umma da Khulsum suka fice suka barta rik’e da wayar ba tareda tace dashi komai ba. Mugun takaicinsa ne ya kuma taso mata. Ita gani take duk laifinsa ne Abba ke fushi da ita. Watak’ila da bai amince da Auren Wata Uku da yai da ita ba tun a fari da duk wad’ann abubuwan basu faru ba. Duka laifin na Haidar ne da ya amince zai AUREN WATA UKU da ita.
Maganan duniya Haidar ya mata tak’i ta amsa. Yayi magiyar yayi lallab’in duk bata amsa shi ba har saida suka sinkayo kukan Baba Ali alamun ya tashi a bacci. Dan ta k’ara basa haushi sai kawai ta barshi yanata suararon kukan D’ansa cikin wayar. Har lokacin ba abinda tace sai kukan yaron dake k’aruwa.
Zuciyar Haidar yaci gaba da masa zafi. Ya sani intentionally ta kyale yaron yana kuka dan yaji zafi.
A zuciye yace “Khairy wai ina karatunki ya tafi ne.? Ta ya kike punishing k’aramin yaro for his Dad’s mistake.?!”
Bata amsa shi ba har lokacin sai hawaye dake gangaro mata.
Haidar ya jinjina Kai yana Jin zuciyarsa na masa zafi sosai “Fine Ummulkhair.!” For the first time da taji ya ambaci sunanta kai tsaye ba kaman yanda Ya saba fad’a ba. Haidar yaci gaba “Do as you wish.! Mommy tana nan cikin garin Kano bata dawo Abuja ba.. Zata zo ta d’aukar min D’ana zai iya rayuwa da baby formula.. Bazan bari tarihin abinda ya faru Dani ya maimaita Kansa Akan D’ana ba..!” D’if ya kashe wayar ba tarda ya kuma cewa komai ba. Aiko yana kashe wayar kaman ance nan ta b’ige da kuka sosai jaririn nayi itama tanayi a haka Umma ta shigo ta taddasu.
**
Washe gari kaw su Mommy da Aunty Asshe suka zo duk a tunanin Ummul sunzo su tafi da Baba Ali ne kaman yanda Haidar yace. dan tayi zaton Haidar ya sanar da Mommy kaman yanda yace amma sai bataga hakan daga Mommy ba. Kayyaki ma taga ta kawo musu ita da jaririn da wasu abin buk’ata. Nan take sanar dasu washe gari zata bi jirgin safe ta tafi Abuja kafin ran suna. Umma sukaita mata godiya da san Barka.
Mommy ta dubi Ummul dake zaune daga mazauninta kanta a k’asa. Ta murmusa tace “Toh Daughter ni zan wuce gobe in sha Allah. Na samu urgent call daga Daddynku. Duk dai bazai wuce magana akan yaransa ba ga kuma case din Anisa da ba’a warware ba har yanzu. Naso na tsaya ayi suna kafin na koma.. But still idan na samu dama zanzo ayi suna Dani idan kuma ban samu Aunty Asshe zata wakilceni in sha Allah.”
Ta jinjina Kai a hankali ba tareda ta iya cewa komai ba.
Mommy ta kuma murmusawa tana duban jaririn dake baccinsa peacefully tace “Gameda batunku keda Haidar.. You have the final say here.. Kin cancanci hakan. Dan a baya an Miki dole. Idan aka sake Miki dole wann karon ba’a Miki adalci ba… He’s my son.. Ina son shi fiyeda komai a rayuwar nan.. Amma hakan ba yana nufin zan sake fifita shi sama da komai kaman yanda nayi a baya ba.” Mommy ta dan numfasa kafin taci gaba “ I couldn't manage to change him for years.. Amma cikin buwayan Ubangiji you came and changed him.. Ina nufin kece sanadi.” Mommy taci gaba da jinjina Kai tana duban Ummul “Ki sani, You are the most precious truth in his life.. But still zab’i naki ne Ummulkhair.. Bazan sake tilasta Miki kasancewa da D’ana ba kaman yanda nayi a baya.. Sabida ke d’in ma ‘ya ce a wajena.” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta. Ta k’arasa ta sumbaci Baba Ali dake bacci kafin ta kuma yima Ummul Sallama. Har Mommy takai k’ofa Ummul ta mik’e cikin sauri tana duban Mommy. Ta ambaci Mommy a hankali.
Mommy ta juyo tana dubanta. Sai Ummul ta isa da sauri bata san sanda ta fad’a jikin Mommy tana hawaye.
Mommy ta rungumeta sosai tana bata baki tareda mata fatan alkhairi. A haka dai suka sake wani sallaman.
Ummul ta kuma yarda kaunar dake tskaninta da Mommy daga Allah ne ba wai dan ta kasance mahaifiyar Haidar ba. Dan ita dai tin farkon haduwarsu tin kafin ta saka Haidar a idonta Allah ya jefa mata k’aunar matar.. Matar da tai defending dinta a gidan da babu kowa nata cikinsa gidan da mijin da taje domin sa ya gujeta. Koda ace Mommy da manufa ta nuna mata so a fari itakam bataji son da take ma Mommy ya ragu ba ko kadan.
**
Abuja…
Isowan Mommy gidan ta hangi sashen Haidar a bud’e ana fiddo da wasu kayayyaki. Mamaki ya cika Mommy. Ta dubi d’aya daga cikin ma’aikatan ta tambayesa lafiya meke faruwa meyasa suke fiddo da wasu kayayyakin.
Kafin ma’aikacin ya bata amsa ta hangi Hisham ya fito daga sashen sai stretching hannayensa yake yana Ware su alamun duniya tana masa dad’i.
Mommy ta zuba masa ido tana duban ikon Allah. Daidai nan Hisham ya k’araso yana mata sannu da zuwa. Bata iya amsa shi ba sabida mamaki da ya daure mata Kai. Can ta hangi Daddy na k’arasowa da murmushi saman fuskarsa. Ganin Daddy sai Hisham ya koma ga ma’aikatan yana ci gaba da nuna masu abubuwan da yake so da Wanda baya so a sashen.
Daddy na mata sannu da sauk’a bata iya amsa shi ba sai nuni da tai da sashen Haidar cikin tsananin shock “Engr. Meke faruwa..? Ya naga ana fidda wasu kayayyakin Haidar daga sashensa.?”
Sai Daddy ya murmusa “Banda abinki Kwaise Haidar kam ai yanzu bak’o ne a gidan nan.. Ko kin mance tin bayan bikin tariyarsa saidai yazo mana bak’unta..”
“But still.. Sashen sa ne.. Akwai sections da yawa a gidan nan.. Meyasa na Haidar..?” Cewar Mommy har lokacin a shock take.
Murmushi Daddy ya kumayi “Haba Kwaise is just a section.. Ba wani abu bane dan D’anuwansa ya zab’i ya zauna a nan. Hisham da Kansa ya zab’i wann section d’in.. Ni kuma ganin yanzu Haidar ba mazaunin gidan nan bane yasa nace zai iya amfani da wann b’angaren. After all, nan ne ya kamace shi ba b’angaren bak’i ba.”
“Amma Engr.. Haidar ya sani.? Kasan yanda yake. Kasan yanda baya so ayi invading space d’insa ba tareda saninsa ba..”
Muryar Haidar ta sinkayo daga bayanta yana fadin “Is ok Mommy..” Yai maganar kyakkyawar murmushi samar fuskarsa.
Ta waigo tana dubansa murmushin ne saman fuskarsa. Yana k’arasowa ya bud’e mata hannaye alamun hug. Sai ta fad’a’da murmushinta suka rungume juna yana fad’in “welcome Mommy.. Ya hanya.. Ya kika baro Little Haidar.?”
Daga Mommy har Daddy murmushi sukai Mommy tana fad’in ba ko kunya D’ansa kawai yake tambaya. Su duka ukun raha ne saman fuskokin su yayinda Mommy ta Ciro wayarta tana nuna musu hoton littile Haidar yanda Ya k’ara wayau. Daddy na fad’in dashi yake Kama ga hancinsa da sumarsa ya d’auka. Mommy na cewa hasken fatanta da manyan idanunta ya d’auka. Haidar ya saka iyayen nasa gaba yanda ko wanne yake fad’in jikan nasu dashi yake kama. Sai murmushi kurum Haidar yake. Hisham na tsaye daga gefe rik’eda hoton Haidar da Ummul Wanda aka musu ran bikin tariyar su ya fito dashi daga sashen Haidar d’in. zuciyarsa sai faman tafarfasa yake.
Basu Ankara ba sai karan fashewan abu sukaji. Hisham ya saki hoton ya fad’i k’asa ya fashe.
Suka juyo gaba d’aya suna duban Hisham Wanda tuni ya d’uka yana k’ok’arin tattare hoton yake fad’in Haidar yai hakuri bai sani bane. A garin k’ok’arinsa na tattare hoton glass ya yanka masa hannu. Daddy ya k’arasa da sauri ya rik’o hannun Hisham d’in yana duba yankan da yai. Hisham yana fad’in Daddy ya bari ba komai it’s nothing serious. Tuni Daddy ya rikosa ya nufi cikin gidan dashi yana fad’in “You are bleeding Son.. Are sure ba sai anje asibiti ba. Come We need to clean your wound.” Ya k’arashe suna nufan cikin gidan.
Mommy da Haidar suka bi bayansu da kallo kafin Mommy ta kamo fuskar Haidar “Son..”
Saurin girgiza mata Kai yai ya kamo hannayenta murmushi saman fuskarsa “I’m fine Mommy.. Don’t stress yourself..” Ya rik’o hannunta yana fadin “You just arrived.. Ki shiga ki huta..”
Saida ya tabbata ya mata rakiya har cikin gidan kafin ya dawo yana duban hotonsu shida Khairy Wanda Hisham ya fasa. Duk’awa yai ya d’auki fasasshen hoton yana kallo. Daga bayansa ya sinkayo muryar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 55 Chapter of 64