Share this page
tai ta shige k’uryar daki wani sabon kuka na taso mata. Haka ta yini a daki bata aikin komai sai kuka. Asshe ke Lek’ata lokaci zuwa lokaci. Ko abinci Mommy ta kasa ci ranan. Can dare taji shigowar motar mijinta. Nan ta Mike da sauri tana lek’en window. Hangosa tai tareda Amaryar sa tana biye dashi kanta a k’asa. A haka suka shigo har parlorn gidan. Koda Daddy ya shigo ya tadda Mommy juya masa baya tai. Ya k’araso jikinsa duk a mace “Kwaise. My love..” Sai ya kasa ci gaba da magana yayinda kukan Mommy ya karu. A hankali ya isa ya rungumeta ta baya. Su duka biyun hawaye na gangaro masu. Cikin kwantar da hankali yake furta “Wann shine k’addarar mu Kwaise. Allah ya k’addari Fannah zata shigo cikin rayuwarmu. Yarinyar abun tausayi ce bata da kowa sai mahaifinta da ya rasu sakamakon aikin da yake k’ark’ashina. Mommy na hawaye take girgiza Kai “Ba hurumi na bane na tuhumeka dan ka k’ara aure Aliyu. Addini ya halatta maka auren mata d’ai d’ai har hudu idan kanada hali. Kawai alfarmar da zan rok’a daga gareka shine Kai Adalci tsakaninmu.” Ya murmusa yana dubanta. Ya saka hannunsa ya share hawayen da suka gangaro mata “I love you Kwaise.. So much..! Ban tab’a son wata mace sama dake a rayuwata ba. Ki tayani addu’a Allah ya bani ikon yin Adalci tsakaninku because.. I’m not sure idan son da nake Miki zai barni na kamanta adalci.. Kwaise ba kece cikin tashin hankali ba. Ni ne cikin tashin hankali.. Because son da nake miki baida match da ko wace mace. When it comes to you wayona baida yawa Kwaise.” Mommy ta tsaresa da ido kafin ta k’ak’aro murmushi ta riko hannayensa “You can do this in sha Allah mijina. I’m here for you.. Tashi na shiryaka amarya tana jira.” Kaman rak’umi da akala haka Daddy ya Mike Mommy ta shiryawa tsaf harda su fesa turare kaman ba ita ce ta yini kuka a daki ba. Koda suka fito suka tadda amarya ma Mommy bata nuna komai ba. Asshe taita mamakin canzawan ‘Yaruwar tata. A haka rayuwa ke tafiya masu Mommy bata nuna komai ga Daddy ya saki jiki ganin hankalin Kwaise ya kwanta. Ya maida hankali kan bunk’asa k’aramin kampaninsa a nan birnin Maiduguri da Kewaye. Watan Fannah biyu a gidan ta fara nuna alamun masu juna biyu. Kwaise da kanta ta dauketa ta kaita asibiti akai mata gwaji aka tabbata tana d’aukeda karamin ciki na tsawon watanni biyu. Sosai Mommy ta nuna marnanta har kaman tafi Fannah murna. Lokacin Daddy na cuku cukun Kai Kasuwancinsa tsakanin Abuja da wasu jihohi Mommy da kanta tai masa Albishir na cikin da amaryarsa ke dashi sanda sukai waya tinda shi a wann lokacin ya rage zaman Maiduguri. Farin ciki wajen Aliyu Maitama baya misaltuwa. A wann lokacin yai ma matan nasa kyauta ta sabuwar mota dal ‘yar yayi a wancan lokacin. Ya kuma d’ebesu gaba daya suka tafi Umra suka gode ma Allah da kyautar da yai masu dan a lokacin aurensa da Kwaise kusan shekaru biyar kenan babu rabo saida Fannah ta shigo sai gashi ta samu daga shigowarta. Bayan dawowar su daga Umra Daddy ya tafiya ta kasuwanci da zai d’aukesa kusan wata guda. Asshe ta dubi Mommy wacce keta faman sakin murmushi tana gustiran Apple. Ta d’an girgiza Kai tace “Kenan kin yarda ta rigaki Haifa masa Magaji Aunty Kwaise.? Ni fah kirkikin da kike ma matar nan tai yawa. Ke kaman bakijin kishi irin na mata da ake fad’a.” Murmusawa Mommy tai “Asshe kenan. Sarai nasan abinda nake kuma lokaci yayi da zan executing plan dina. Trust me.” Asshe ta girgiza Kai “Toh amma Aunty Kwaise mai zakiyi yanzu.?” “Wann cikin da Aliyu Maitama ke rawar k’afa akansa da Kansa zai sheganta sa tin a ciki kafin a haifosa. Zai ma Fannah korar wulak’anci. Wann cikin kuma Engr Aliyu Maitama bazai taba accepting dinsa ba.” Asshe ta girgiza Kai “Amma ta ya zakiyi hakan.?” Mommy ta kuma gyara zama “Uban Fannah labourer ne a kampanin Maitama. Bincikena ya tabbatar min akwai wani lebura matashi kuma abokin aikin mahaifinta dake mutuwan sonta. Hasalima saurayinta ne kafin iftila’ain da ya samu mahaifinta ya samesa. Zuwa Kai ma mahaifinta abinci da take site a can Saurayin nata ya ganta ya fara sonta. Da uban ya Mutu mijina bai san da labarin tanada wani saurayi da suke soyayya ba Wanda shima yake aiki k’ark’ashin sa. danginta sukai wuf suka nuna masa batada kowa saidai ya aureta sabida tinanin zasu sami kudi. Ance sadaki suka yanka masa kaman dai mai biyan diya. Saida masa ita sukai. Fannah batada say ga danginta Wanda bayan rasa mahaifinta da tai ba rike ta zasuyi ba dole suka tilasta mata auren mijina dukda tanada Wanda take so. Dashi zanyi amfani na fitar da Fannah daga gidana dan ance har gobe yana mutuwan sonta.” Asshe ta sauk’e ajiyan zuciya “Toh ya abin zai kasance.?” Mommy ta kuma murmusawa “Abin shine kece zaki taimaka min har komai ya kankama K’anwata.” Asshe ta girgiza Kai cikin rashin fahimta “Kaman ya kenan Anty Kwaise.? Ki sanar Dani wane irin taimako zanyi dan nafi kowa burin matar nan ta fice daga gidan nan.” Mommy ta jinjina Kai suka tsara yanda zasu aiwatar da komai cewa Asshe ta tafi ta samu wann Saurayin suyi ciniki dashi da Mommy yazo gidan a ranan da Engr Aliyu Maitama zai dawo gari ya kamasa a d’akin matarsa zai hau kan dik abinda ya gani ya zauna tinda su biyun tsaffin masoya ne.” Ta k’arashe tana sakin murmushi. Da taimakon Asshe Mommy ta tsara komai har shigowa gidan da Auwalu tsohon Saurayin Fannah yai ba tareda kowa ya gansa ba. Fannah da fitowarta kenan daga band’aki tayi wanka cikin murnan mijinta na hanya zai dawo ya dubasu itada abin cikinta mai watanni uku a lokacin. Nan ta tadda Auwalu tsohon saurayinta kwance saman gadon ta daga shi sai singlet da gajeren wando. Jikinta ya d’auki kyarma ta soma salati tana karanto Innalillahi. Kafin tai wani aune Auwalu yai tsalle ya capkota had’ida toshe bakinta da k’arfin gaske. Fannah tana kuka tana k’ok’arin kururuwa amma inaa ya toshe bakinta. Daddy ya dawo cikeda d’oki da murnan ganin matarsa mai juna biyu. Ko sashensa bai nufa ba ya fara nufan b’angaren ta d’aukeda tarin tsaraba irin Wanda mata masu juna biyu ke so. Nan ya tadda Kayan tashin hankali maras misaltuwa k’ato rungume da matarsa dake d’aure da towel ya toshe mata baki da hannunsa guda. Ga wani mummunar murmushi saman fuskarsa. Daddy na huci yake duban mutumin Wanda ya saki Fannah bayan shigowan Daddyn. Ya duka jiki na kyarma yanda yake fad’in Engr ya masa sutura dole Yai ma Fannah bada amincewarta ba fyade yai mata. Daddy ya shak’osa tamkar zai aikasa lahira ya kasa furta komai sai huci da kyarma da jikinsa keyi sabida b’acin rai. Da kyar Mommy ta janye Daddy. Ta isa ta yafa ma Fannah mayafi ta rufe mata jiki wacce towel ne kawai d’aure jikinta. Ta dawo ga Daddy tana fad’in “Engr kar ka biyesa kar Kai kisa. You are not like him. Ni dama tinda yake zuwa gidan nan ban yarda dashi ba.” Daddy ya dubeta da mamaki “Dama ya Saba zuwa.?!” Mommy ta jinjina Kai kaman gaske “Ai idan Baka nan yakan zo. Da abubuwa na kwadayi irin na masu ciki yakan ce Kai ka aiko shi zuwa wajen Fannah. Sabida abinda take so yake sayowa.” Asshe da fitowarta kenan sabida hayaniyar da taji ta dubi mutumin da Daddy dake duke yana kyarma tace “A’ah.. Wann mutumin ai mak’ocin su k’awata Baana ce. Kuma ta…” Sai tai shiru ta kasa ci gaba da magana. Mommy tace “Kuma me Asshe.. Meye Baana ta sanar dake..?” “Ta sanar dani shi d’in Saurayin Fannah ne Wanda mutuwan mahaifinta ya hana aurensu… Hasalima mahaifin Fannah kafin ya rasu ya masa alkawarin bashi ita..!” Daddy ya dago jiki a sanyaye yana duban Fannah wacce kuka yaci k’arfin ta “Haka ne.? Wann D’an iskan saurayinki ne.?!” Ya tambaya yana dubanta. Jin bata amsa shi ba ya sa ya kuma daka mata tsawa “Ki amsa min..! Haka ne..!” Auwalu ne ya bama Daddy amsa da fad’in “Duk Wanda zaka tambaya Rankayadade haka ne. Fannah toshuwar budurwata tace da nake matuk’ar so. Kuma mahaifinta ya min alk’awarin bani ita.. Amma ‘yanuwanta Sun karya wann alk’awarin sabida kwadayin abin hannunka. Saidai ni da Fannah bamu rabu ba.. Washe garin ranar da ta tare gidanka ma ba aiki na tafi ba gidanka na taho.. Kuma duk randa nazo mukan mu’amalanci juna da yarda da amincewarta. Amma yau din ba da son ranta na aikata mata ba fyade nai mata sabida ta sanar Dani akwai ciki jikinta Wanda batasan nawa bane ko naka..!” Bai Kai aya ba yaji saukar naushi a bakinsa. Duka Daddy yake Kai masa ta ko ina yana hawaye tamkar zai aikasa lahira A haka mai gadi ya shigo a guje yana sanar da Daddy window din section dinsa a fashe dik yanda akai b’arawo ya shigo gidan. Dan shi dawowarsa kenan daga masallaci ya tadda haka. Daddy ya ci gaba da huci “Ga b’arawon a nan. Ya Saba shigowa Shayibu ba tareda kayi la’akari ba. Yau da dubunsa zai cika sai ya fasa window. Ya damk’a sa ma shayibu yana fad’in bari yaje ya duba section d’insa. Ai kaw nan Daddy ya tadda an fasa safe d’insa na cikin gidan an kwashe kud’ad’en ciki. Koda aka mik’a Auwalu ma ‘yansanda bai yi musun shi ya kwashe kud’ad’en ba. Ya ce da taimakon Fannah ya kwashe kud’ad’en dan su gudu su bar gari. Daddy bai saurara daga b’angaren Fannah ba. Musamman da ya tabbatar da gaske Auwalu tsohon saurayinta ne kowa yayi wann shaidar. Sosai take kuka duk’e gabansa tana girgiza Kai tama kasa cewa komai. Mai ma zata ce bayan an kulleta ta ko ina. Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “Ki sani wann shegen da yake cikinki ba nawa bane. Kuma har Abada kar ki taba danganta ni dashi. Kije can keda wancan Daniskan ku rainesa a gidan Yari.” Yana ida fad’in haka ya mik’e yana hawaye sosai. Bai wata wata ba ya tura su duka biyun gidan Yari. ‘Yanuwan Fannah suka barranta da ita cewa basu ba ita. Ta tona ma kanta asiri ta cuci kanta. A prison Fannah ta raini abinda ke cikinta har ta haifesa. Bayan faruwan haka da wasu watanni Mommy ta fara nuna alamu na masu ciki. Batai gaggawan sanar da mijinta ba Wanda tsawon shekarun da suka diba tare suna jiran wann batu mai dad’in ji tin kafin shigowar Fannah cikin rayuwarsu. Yau gashi ta samu juna. Tasan Engr zai farin ciki fiyeda lokacin da Fannah ta samu. Tai shiru tana tinanin da Fannah tana nan k’ila da an fara k’irga ma abinda ta haifa watanni. Suna hira itada Asshe wani rana, nan Mommy ke zayyano ribar da taci bayan ta k’ulla ma Fannah Makirci gashi ta fice cikin rayuwarta cikin ruwan sanyi. Tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu. Sam bata San Daddy ya shigo ba take b’arin zance. Daddy ya dubeta da mamaki “Kwaise.. Sharri kikai ma Fannah.?!” Sai Mommy ta mik’e tana girgiza Kai “A’a Engr dan Allah ka saurareni.” “Mai zan saurara bayan abinda naji da kunnuwa na.. Ki bud’e baki ki sanar Dani.. Sharri kikai ma mata..? Kece kika shirya komai..?!” Cikin kuka Mommy ke jinjina Kai “Wllhi Allah shine shaida na Engr sharri kawai nace yai mata.. Wllhi ban ban bashi umarnin wani abu bayan haka ba..” Gijif ya zauna cikin kujera yana jin duniyar na juya masa yayinda Mommy ta rarrafo zuwa gabansa tana Neman afuwa. Mik’ewa yai ya fice ba tareda ya dubeta ba. Kai tsaye prison yaje amma koda yaje ta gama sentences d’inta an kuma sallameta bayan ta haihu sann babu Wanda yasan yanda ta tafi. Shima Auwalu babu Wanda yasan yanda yake bayan Sallamansa daga prison da akai. Haka Daddy ya zauna yana kuka sharshar da hawaye tareda nadaman hukuncin da ya zatar ba tareda yayi bincike ko ya saurara daga Fannah ba. Gaba d’aya Mommy ta rasa gane kansa tin daga wann lokacin. Baya mata magana baya kulata baya shiga sabgarta. Kasuwancinsa ta soma girgiza bayan hab’akar da tai sabida halin k’unci da damuwa da ya tsinci kansa ciki. Daddy ya koma tamkar baya rayuwa cikin wann duniyar. Ya daina fita ya daina magana ya daina mu’amala da kowa da komai. A haka Mommy ke rainon cikinta cikin damuwa da k’unci hopping idan ta haihu zuwan D’an cikin rayuwarsu zai canza komai. Har zuwa lokacin da ta haihu Daddy bai dawo normal ba. Yana nan jiya iyau ba um ba um um. Bayan Mommy ta haihu ta shigo da jaririn cikin hannunta tana hawaye take nuna masa “See burinka ya cika Engr ka samu Magaji and I named him after you. Aliyu Aliyu Maitama.. Zai girma ya zama Engr kaman Kai. Zai girma ya zama d’an da zakai alfahari dashi.” Tin bayan abinda ya faru bai kuma duban cikin idonta ba sai wann lokacin. Mommy tana hawaye take dubansa cikeda Jin dadin yau yau ya kalleta. Amma sai taga ko kallon jaririn dake rik’e cikin hannunta baiba balle ya karb’e sa. Sai ma mik’ewa da yai a ranan ya koma aikinsa gadan gadan. Baya shiga sabganta balle na D’anta sai hidiman bunk’asa Kasuwancinsa da yake. K’unci da damuwa suka taru sukai ma Mommy yawa tinda taga wann lokacin Mommy ta shiga damuwa kullum cikin kuka da tashin hankali take bata kula jaririnta Wanda tinda taga mahaifinsa bai amshesa ba. A nata zaton zai zamto makamin da zatai amfani dashi ta kuma janyo hankalin mijinta gareta. Asshe ita ke rainon Haidar. Hasalima ita take kiransa Haidar bayan mahaifiyarsa ta sanya masa suna Aliyu har Haidar ya bisa. Asshe ita ke kula da Haidar tamkar itace ta haifesa. Madararsa d’awainiyarsa komai itace. Mommy kullum cikin kuka da damuwan wofantar dasu da ita da D’anta da Daddy yai take. Ta duk’ufa Neman Fannah dan ta nemi yafiyarta amma Fannah was no where to be found. Sanda Asshe tazo aure ji tai kaman ta tafi da Haidar sabida son yaron da take da tsoron barin sa tsakanin iyayen da babu shi a gabansu. Damuwar gabansu kawai suke. Burin Mommy shine Uban ya kalli d’an matsayin D’a da ko wani Uba ke alfahari dashi yayinda Daddy ya ta’allak’a ga bunk’asa Kasuwancinsa. Wann dalili yasa kasuwancin Aliyu Maitama ya fiye masa ahalinsa dan wann Kasuwanci shi yai keeping dinsa going a tunaninsa bayan abinda ya faru dashi. Shi ya zame masa tamkar therapy. A haka rayuwa take tafiya ma wad’ann bayin Allah. A haka Haidar ya taso ya tsinci Kansa tsakanin iyaye biyu Wanda baisan wani Abu mai suna soyayya tsakaninsa dasu ba. Koda ya soma girma Mommy kullum cikin tilasta masa yake yai abinda zai birge uban ko zai alfahari dashi yayinda Daddy bai tab’a ganin k’ok’arin Haidar ba har kawo girman sa. Wann kenan. (Kar mai karatu ya mance kacaukam labarin nan an Ginasa ne kan ‘ya’ya da Allah kan jarabcesu da iyayensu da kuma iyaye da Allah ke jarabtansu da ‘ya’yansu. Wasu mutanen ana sanyasu ne cikin rayuwar sashe matsayin jarabawa). * Ci gaban labari.. Haidar ya share hawayen da suka zubo masa “So that’s the reason why he hates me.!” Ya fad’i haka Kansa a kife. Mommy tai saurin girgiza Kai hawaye naci gaba da gangaro mata “No Haidar.. Your Dad doesn’t hate you.. He loves you.. In fact inada tabbacin bayan abinda na masa albarkacinka naci bai koreni ba.. That’s just.. his way of punishing me.!” “Well I don’t care.!” Ya fad’i haka yana mai buga teburin gabansa da k’arfin gaske. Ga wane irin huci da yake fiddawa. Yaci gaba da jinjina Kai yana ci gaba da fad’in “I wish you let me die as a child. I hate you. I hate you.!” Yai maganar a hankali har lokacin girgiza Kansa yake. Mommy na kuka sosai take girgiza masa Kai “I’m sorry my Son.. I’m sorry.. Ba garin Allah da zai waye banyi nadaman abubuwan da na aikata ba da yanda yai affecting rayuwarka.. Haidar ka yafe mun..!” Kauda fuska yai dan baya fatan ya kuma d’agowa ya dubi fuskar mahaifiyarsa. Ya saka tafukan hannayensa ya goge fuskarsa da ya koma jazir. Cikin wane irin tune yake furta “Serving jail sentences won’t be enough punishment for you Mommy. Amma dikda haka nan shine yanda ya kamaci criminal irinki. Now more than ever, I won’t rest until I see you locked up in jail.. Koda zaki k’arar da duka resources dinki sai na tabbata you rot in jail. I don’t want to see your face ever again.!” Ya k’arashe cikin tsananin huci hawayen zafin rai na fita daga idonsa. Lokaci guda ya mik’e ya nufi k’ofa kaman zai kifa Mommy na kuka na kiransa amma inaaa tuni ya finciki k’ofa ya fice cikin tsananin huci.. SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!* *35* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* Bayan Daddy ya turo mata lawyer d’insa aka basu waje dan su gana. Lawyer ya dan dubeta sai ya jinjina Kai yace “I don’t want to say this, but a halin yanzu farkawar matar D’anki ne kawai zamu iya cewa zai kub’utar dake Hajiya. Sabida ba zargi ake ba keda kanki kika tabbata kin bata wann turaren.” Mommy ta girgiza kai “Kana so kace baza’a iya granting bail dina ba a halin yanzu.?” Yai shiru kaman mai nazari “I’m afraid yes. Laifin babban laifi ne.. Kuma akwai evidence a hannu. Zai matukar wahala. But still nothing money can’t buy in this country. Akwai hanyoyi da dama da za’a bi dan a rufe case din. Amma abun shine kince baki so ai amfani da kudi wajen siyan freedom d’inki.” Bai Kai aya ba tai saurin jinjina masa Kai “It will only complicate the situation even more. Ni a halin yanzu bana son duk wani abinda zai hadani fad’a da Haidar. Idan har nai amfani da kudi ko wani k’arfi nawa D’a na zai k’ara k’ina ne kan wanda yake. I want to make things right with my son..Ba wani hanya da za’a bi wanda rashawa bazai shiga ba.” Lawyer yai shiru sai kuma ya girgiza Kai “Saidai idan ita yarinyar ta farka tayi withdrawing charges. Let’s pray she wakes up soon.. Shine kawai mafita.” Mommy taja gauron numfashi had’ida jinjina Kai. Ta k’udiri niyyan bazatai wani abun da zai kuma b’ata ta a idon ahalinta ba. A haka dai sukai sallama da Lawyer aka kaita detention cell dinta. Ta d’ago ido tana duban cikin cell d’in. Sai ta tuna lokacin da tai ma Fannah sharri itama kurkuku aka kaita. Hawaye suka gangaro ma Mommy. Tabbas ta kuma yarda duk abinda ka shuka a rayuwa zai dawo maka harda riba. Sai gashi nata D’an ya turata kurkuku bayan ta tura Fannah da jaririn da baida laifin komai kurkuku. Dirshan Mommy ta duka wajen hawayen nadama na gangaro mata. Anisa ce ta k’araso k’ofan cell d’in hawaye tab idonta. Ta duka tana duban Mommy “Mommy..!” Anisa tace cikin murya irin ta mai kuka. Mai ta dago tana duban Anisa. Yayinda Anisa taci gaba da share hawaye tana fad’in “Mommh you will get out of this place soon. I’m sure of it.. Zaki fita in sha Allah. We all believe you are innocent.” Ta k’arashe tana mai kamo hannayen Mommy. Mommy ta murmusa tana duban Anisa “I hope so Anisa. Muyi addua Allah ya tashi Ummulkhair na tabbata bazata barni a nan ba, ita d’in tanada zuciya mai kyau.” Wani k’atutun bak’in ciki ya tokare ma Anisa mak’oshi Jin Mommy na yabon Ummulkhair dikda kaman itace sanadiyar kasancewarta cikin halin da ta tsinci kanta ciki. Anisa ta jinjina Kai sai kuma tace “But Mommy Meyasa abubuwa suke faruwa tinda Ummul ta shigo cikin ahalin nan. I don’t want to think about it amma I couldn’t help.. Tinda ta shigo cikin ahalin nan problems keep piling up.. Misfortune after misfortune.. It’s like she brings bad luck with her… Mommy I’m only concern about you..!” Ta k’arashe wasu hawayen na gangaro mata. Ganin Mommy tai shiru kaman nazari yasa Anisa ci gaba “Mommy what if.. What if she’s a curse or something.. hasn’t this crossed your mind..? Mommy Ammi ce kawai fah tasan asalin Ummul..” Mommy tai shiru tana nanata maganar Anisa cikin ranta. Kuma fah Boka ne yace ta auro ma d’anta mace irin Ummul. The same Boka da ya bata turare mai guba ciki. Maganganun Anisa akwai k’amshin gaskiya tinda Ummul dai dama duk namijin da yazo nemanta gudu yake hasalima Shiyasa Boka yace ta aura ma d’anta dan ta zamto makarin asirin da akai ma d’anta. Anya batai gangancin kawo irin wann macen cikin rayuwar D’anta ba.? Anisa ta kafe Mommy da ido makirin murmushi saman fuskarta. Plan dinta na tafiya yanda ya kamata. Sannu a hankali sai ta fitar da Ummul daga rayuwarsu. Ganin Mommy na k’ok’arin maidoda dubanta gareta ya sanyata ta kuma canza fuska ta koma kalar tausayi. Ta kamo hannayen Mommy “Mommy I’ve brought food for you. Nasan bazaki ci abincin nan ba. Bai kamaceki ba. Mommy you don’t belong here. You are Hajiya Kwaise Maitama.” Ta k’arashe cikin k’ok’arin tunasar da Mommy wacece ita dan da alama kaman Mommyn ta mance. Murmushi Mommy tai tana duban Anisa “Thank you Anisa. Thank you for being here for me.” Anisa ta murmusa “Anything for you Mommy.” A haka dai sukai sallama da Mommy tareda alk’awarin kullum zata zo ta dubata har dai al’amra su daidaita. Anisa tana fitowa daga station taga wayar Leenah na shigo mata. Gabanta ya yanke ya fad’i. Leenah kuma a daidai wann lokacin.? Rage speed din motar tai kafin ta daga wayar tana mai rausayar da ido “Girlfriend what’s up.!” Ta fad’i zuciyarta na mata wasai dan wani dadi take ji Mommy ta soma fad’awa tarkonta. Leenah ta murmusa daga d’aya b’angaren “Da alama duniya tana Miki dadi kawata.” Anisa ta murmusa “Keda kika sani. Shawarin ki yayi kawata dan komai ya tafi just as we planned.” Leenah ta kuma murmusawa “Tinda nayi nawa part d’in kuma kwalliya ta biya kud’in sabulu. It’s your turn to return the favor Neesah.” Anisa ta girgiza kai cikin rashin fahimta murmushin fuskarta na gushewa “Wha.. What do you mean. What favor.?” “Oh c’mon Neesa. Everything has a price in this life.. You said it yourself..” Ta kuma murmusawa “Wait.. Na tuna miki ne.? Well bari na tuna miki statement dinki “Leenah idan kika taimakeni Nima zan taimakeki. Zan tabbata baki k’arashi rayuwarki washing white cloths with bleach.. Just to keep them white. Now it’s the time Neesa.” Anisa tai murmushi Wanda yafi Kama da yak’e “Idiot.! Ba yanzu nace zan Miki hanyar arziki ba. Until I become Mrs Haidar Maitama.” Dariya Leenah ta fashe dashi “Don’t try to be funny Neesa. I want those money now. Kuma yanzu dole zaki bani.” Cikeda mamaki Anisa tace “Wait.. Are you trying to betray me.?” Leenah ta girgiza Kai “No I’m just being honest here. What if I open my mouth..? Mai zai faru idan na sanar da Kwaise Maitama wacece dalilin tafiyar ta jail.? Meye kike tunanin zai faru.?” Anisa ta kuma girgiza kai cikin rashin yarda “Are you trying to blackmail me Leenah..?” “You can take it that way Neesa. But I want money in exchange for my silence.! 1million, Anisa.” Anisa da ta kasa rufe baki girgiza Kai ta kuma yi “Leenah are you crazy. Ni.. ni ce kike blackmailing..? Ni Anisa.? Your very own best girl.?” Dariya Leenah ta fashe dashi “Oh Neesa. Kinsan matsalarki. You are too dumb. Baki fahimtar komai.. Na baki nan da three days kiyi abinda nace ko na bud’e baki na. I know you wouldn’t like that.” Murya na shaking Anisa ke fad’in “No Leenah you can’t do that to me. Leenah 1M fah kike magana in three days.. A ina zan samu..? Kin sani sarai Abba na Alhajin mak’o ne kudi basu fita hannunsa saida bayani.. Ko mahaifiyata ma bata ci balle ni..” “I don’t care Neesa. After all, a gidan Aliyu Maitama kike zaune. Idan sata zakiyi ki bani kudi ban damu ba. Kuma ki sani wann phase one muke. Next kudin zai ninka na farko.!” Tana ida fad’in haka ta katse kiran. Dole Anisa ta nemi waje tai parking tana nanata maganganun Leenah. Yanzu ya zatai da Leenah.? Just when she thought abubuwa suna tafiya

Chapter 30 of 64