Share this page
k’unci da takaicin zama D’anka..! Ka yarda dani wann D’an da ka sheganta da bakinka tun yana ciki baizo duniya ba shi zaiyi ajalinka da duk wani farin cikin da kake tunanin ka samu a wann duniyar.!” Ya maida dubansa kan hoton Mommy Wanda shima anyi crossing da red pen. You’re the one who instigated all this chaos.. Kece kika tada duk wani k’ura.. Daga k’arshe kin kawo Ummul d’ina ciki.. Saidai d’iyar ‘yaruwarki Anisa ta mutu amma ba Ummul dina ba.. Sai na raba wann D’an naki da Ummul d’ita duk wuya duk rintsi.. Ummulkhair is mine.. Wllhi na ranste sai na d’auketa daga wajenka Haidar.!!” Ya k’arashe yana huci yana duban hoton Haidar dake daga tsakiyan na iyayensa Wanda shima anyi crossing anja layi da jan alk’alami. ** Su biyu ne cikin d’akin yana kwance daga saman gadon yayinda Ummul ke tsaye gefe tana fito da shirts daga cikin suitcase d’in da suka shigo dashi itada Anisa. Mommy ce ta d’aureta nan wajen tace Lallai ta nema ma Haidar rigar da zai canza dan tasan halinsa tinda Ya farfado bazai taba yarda ya zauna da kayan asibiti ba. Sai fito da t-shirts din take amma da alama Wanda take fito da Kayan dan ya gani yai selecting baida niyyan yin hakan. Dan ko kallo bata ishesa ba balle kayan da take cirowa. Ta lumshe idonta a hankali tana tunani cikin zuciyarta ‘Mai zanyi yanzu ni Ummul. Bai kallon b’angaren da nake.’ D’ago idon da zatai sukai ido hudu. Sai ta daburce gaba d’aya.. Ta suri t-shirt d’aya ta d’ago sama tana nuna masa “Wann yayi.?” Yanda tai maganar fuskarta d’aukeda murmushin da yafi kama da yak’e sosai zai baka dariya. Kai da gani kasan maganar zuwa mata kawai yai ba tareda ta shirya yinsa ba. Bai bata amsa ba Har lokacin dubanta yake da rikitattun idanunsa. Ganin bai daina kallonta ba bai kuma ce komai ba Ya sanyata aje rigar ta kuma d’auko wani ba tareda ta kalla mai ta d’auko ba ta shiga nuna masa “How about this one..? Duba kaga.” Wann karon sosai ya dad’a tsarewa yana duban abinda take nuna masa Wanda da alama ita kanta bata San mai take nuna masa ba. Ta kasa daina murmushin yak’en da take sai juya abin dake hannunta take idanunta naga Haidar Wanda yai k’ok’arin mik’ewa alamun zai nufo yanda take. Bugun Zuciyar Ummul Ya k’aru ta yunk’ura zata nufosa tana fad’in “A’a ka dakata.. Zan taimaka maka.” Bata rufe baki ba abinda ke cikin hannunta tana nuna ma haidar wanda a tunaninta riga ce ta fad’o k’asa.. Dubawan da zatai nan taga shorts ne ashe take ta faman nuna masa. Bama tasan da gajeren wandon cikin jakar ba. Anisa ce ta saka a sace dan kawai ta had’a Ummul d’in da Haidar fad’a tinda tasan Haidar mutum ne da baya so ana kutsa masa kai cikin rayuwa without an invitation. Ummul ta runtse idonta sanda ta d’auko gajeren wandon cikin hannunta.. Tai saurin b’oyesa a bayanta tana tuhumar kanta ‘Daga ina wann yazo. Mai kika aikata Ummul.?’ Bata Ankara ba sai jin hannayen Haidar tai ya kewayeta. Bakinsa kusan kunnenta yake furta “Who gave you the right to touch my things.?” Ta kasa cewa komai sai zuciyarta dake ci gaba da bugu. Jin tayi shiru bata ce komai ba yasa Haidar ci gaba sanda yake Zare shorts d’in daka cikin hannunta har lokacin tana rungume cikin jikinsa “I hate it when others invade my private space.!” k’arashe yana zare wandon cikin hannunta. Daidai lokacin Anisa ta turo k’ofa ta shigo Mommy na biye da ita. A tunanin Mommy Anisa ta nemi izinin shiga an bata Shiyasa ta kutsa kai. Anisa tai saurin cin birki had’ida cewa “Kuyi hakuri na shigo kaina tsaye. I’m sorry.!” Mommy tai saurin janyota suka nufi k’ofa tana fad’in “Ke ai bansan Randa zaki bar wann shashancin naki ba.” Haidar ya dan matsa baya kad’an yana dafe garu had’ida ciza labbansa kad’an sabida raunin da suke jikinsa Har lokacin. A hankali ya furta “It’s fine Mommy.. You can come in.” Ya k’arshe maganar sanda yake kishingid’a saman gadonsa ta majinyata. Ummul ta rintse idanunta tana jin kaman k’asa ya tsage ta shige. Ko d’agowa ta dubi Mommy ta kasa. Yayinda Anisa ke ta faman aika mata harara cikeda k’iyayya k’asa k’asa. Mommy ta karance yanayin da Ummul ke ciki sai ta bata aike wajen nurses d’in dake reception dan tana son magana da Haidar alone. Ta dubi Anisa ma ta aiketa can waje wajen driver d’inta. D’akin ya rage saura ita da Haidar. Mommy ta tsaresa sosai da ido. Duba irinta ta tuhuma. Ya d’an dubi mahaifiyar tashi sai ya d’an sadda idonsa kad’an ba tareda yace komai ba. Sosai Mommy taji dad’in hakan da Haidar yai alamun dai gradually yana sauyawa tinda tasan girmamawa ce yasa shi sadda idanunsa. Ta janyo kujera ta zauna kusan gadonsa gefen kansa. “Haidar.!” Ya d’ago ya dubeta jin ta kirasa in a serious tune. Mommy taci gaba “Kar kaga laifin Ummul dan an had’o kaya an kawo maka.. Ni ce na sakata yin hakan.” Ya d’anyi shiru sai kuma yace “But Mommy ba sai anje cikin kayana ana bincike ba.. You could’ve sent your driver ya saya ko a boutique.. Since I won’t be staying here for too long..” Mommy ta murmusa jin yanda yake ta kwanakwana yana maganar. Wai Haidar ne bai fad’a mata magana kai tsaye ba yaketa faman kwana.. Hakan na nuna mata Ya fara gudun b’acin ranta. Ta d’aura hannunta guda saman nasa tana murmushi “I know Haidar.. Zan iya yin hakan amma na zab’i matarka taje ta bincika cikin kayanka ta d’auko maka kaya.. Kasan dalili.? Sabida ita d’in matarka ce.. Bata da wani shamak’i da duk wani sirri naka.” Sai ya dan lumshe ido kad’an ba tareda yace komai ba. Mommy ta kuma gyara zamanta “Aliyu, my son.” Haidar Ya d’ago Ya dubeta. Mommy taci gaba “Kaman yanda Ubangiji Ya bamu daman kasancewar D’a da mahaifiya a karo na biyu.. Ina so ka nuna godiyarka ta hanyar kasancewa miji ga Ummulkhair.. Bani so na kuma tilasta maka wani abu musamman abinda ya danganci yanke hukunci ga rayuwarka.. Amma na maka alk’awari wann shine zai zamo abu na k’arshe da Ya danganci yanke hukunci cikin rayuwarka Wanda zan buk’ata daga gareka, in sha Allah.. Please do this for me Haidar.. For the last time.. Ka bama kanka dama da Ummulkhair.. Just this once.. Na maka alk’awari.. Daga k’arshe idan bai working ba I won’t force it..” Ta dan murmusa tana dafa hannunsa “Inada yak’inin ma Khair in sha Allah.” Ta k’arashe tana duban D’an nata. Haidar ya dan dubeta cikin yanayin da bazaka iya fasalta abinda ke cikin zuciyarsa kai tsaye ba. Mommy ta kuma murmusawa kafin ta mik’e “Ni zan wuce gida na duba Aunt d’inka Asshe da gajiyan hanya.” Haidar baice komai ba sai jinjina mata kai da yai. Yai mata fatan kasancewa lafiya. Da haka Mommy ta fice zuciyarta fari sol. Cikin buwayar Ubangiji D’anta Ya soma dawowa kan turba. Bayan tafiyar Mommy daga bisani Ummul ta shigo. Aiko tana shigowa saiga Anisa ta take mata baya. Tai Sallama ma Haidar kafin ta juyo ta dubi Ummul “Ummul kema ya kamata mu tafi koh.. You know they don’t accept visitors here.” Kaman wanda aka zaburesa haka ya juyo yana duban Anisa jin tana fad’in Ummul ta tashi su tafi. Anisa tai murmushin da yafi kama da yak’e ganin irin duban da Haidar ke aika mata “Hos..Hospital rules.!” Ta fad’i cikin sauri da k’ok’arin kare statement d’inta. Har lokacin wani irin duba Haidar ke aika mata “She’s not a visitor.. You can leave.” Ya fad’i a tak’aice. Cikin sanyin gwiwa Anisa ke jinjina kai “Haka ne na mance..She’s your wife.. I.. am the visitor here.” Tai maganar cikin k’ok’arin danne k’uncin dake taso mata ga murmushi mai ciwo saman fuskarta. Ummul dai ta dubi Anisa ta dubi Haidar. Anisa taima Ummul saida safe had’ida fatan samun sauk’i ma Haidar.. Tasa kai zata fice Haidar Ya dakatar da ita “Do yourself a favour and quit coming around. As you mentioned, visitors ain’t welcome.!” Da mamaki Anisa ke dubansa jiki a matuk’ar sanyaye yayinda Ummul ma ke binsa da kallon mamaki. Anisa ta k’ak’aro murmushi mai ciwo tana jinjina Kai “As you wish..Dear Cousin.” Ta k’arada “Get well soon.” Ta k’arashe tana Kai dubanta ga Ummul wacce sosai damuwa ya nuna saman fuskarta. Anisa na ficewa tai bursting cikin kuka. Gudu gudu ta fice daga asibitin. Ummul ta maidoda dubanta ga Haidar Wanda ke k’ok’arin zame rigar dake jikinsa sai faman tamke fuska yake sabida zafin rauni da basu gama sake shi ba. Sam bama ta kula da abinda yake ba dan sosai korar da yai ma Anisa yai mata zafi. Kaman zatai kuka. Cikin sanyinta ta soma fad’in “Haba mana.. Mai ka aikata ne ..? Meyasa zaka Kori Anisa. Laifi ne dan an nuna damuwa akanka.?” Kallan Yanda tai da fuskarta kaman mai shirin kuka Haidar yake. ‘How dare she interferes! Who does she think she is?’ Cikin zuciyarsa yake zancen saidai Ya kasa furta komai. Bai ce da ita komai ba sai k’ok’arin sauk’owa daga gadon da ya soma. Sai sann Ummul ta kula babu riga jikinsa. Ai sai ta d’an daburce ta soma k’ok’arin kare idonta da tafin hannunta tana sadda Kai k’asa ga Haidar dake nufota. Ta soma matsawa baya tana fad’in “Wai mai kake aikatawa ne. Da.. Da cewa Kai na baka waje zaka canza..” Bai amsata ba bai daina nufota ba har suka isa jikin gini. Hannu yasa ta bayanta Wanda ya sanyata saurin d’agowa a matuk’ar tsorace tana dubansa zuciyarta bai daina bugawa da sauri ba. Sun d’an d’auki lokaci a haka kafin Haidar ya mik’a hannunsa sosai ya d’auki riga cikin suitcase d’insa dake daga gefen Ummul saman drawer. Ganin ya d’auki rigar ya soma takawa a hankali ya sanyata lumshe ido had’ida sauk’e ajiyan zuciya a hankali. Shi kaw Haidar na hankalce da ita yana kallonta ta wutsiyar ido. Murmushi ya saki da gefen bakinsa kafin ya dan saki k’ara yana rik’e gefen ribs d’insa Wanda yasa Ummul saurin Ware idonta. Bata san sanda ta nufosa da sauri ta mik’a hannayenta ta tallafosa tana masa sannu had’ida tambayarsa ko ciwo yake ji. Haidar bai daina ciza labb’ansa yana tamke ido had’ida sakin k’anan k’ara alamun yana jin pain har saida suka isa saman gadon. Ummul ta kuma dubansa a kid’ime bayan ta taimaka masa ya d’an kishingid’a “Kana jin ciwo ne.? Kana so na kiraka maka Likita.? Kaga barin kirawo su.” Ta k’arashe tana k’ok’arin dirowa daga saman gadon amma sai taji Haidar ya rik’o hannunta. Cak ta dakata da abinda take ta juyo a sanyaye tana dubansa. Ya d’an sha mur ganin tana duban fuskarsa kafin ya sakar mata hannun “Why would you call them.? Bayan gaki nan a nan.!” Ya k’arashe maganar yana d’aura mata rigar saman hannunta. Ta dubesa ta dubi rigar da ya saka cikin hannunta da mamaki. Sai ta d’an girgiza Kai kad’an alamun bata gane mai yake nufi ba. Mai zatai da rigarsa. Sai shima ya d’aga mata gira had’ida yi mata alama da ido da ta saka masa rigar. Sai Ummul ta soma girgiza Kai “A’a bazan iya ba.. Ka saka rigarka da kanka.” Bata Kai aya ba ya bata amsa da “But I can’t move my arms.. It hurts.. And since you are my caretaker, Ke yafi kamata kiyi. Haka ne.!” Ya k’arashe yana tsareta sosai da ido. Sukai shiru su duka biyun suna duban juna kafin Haidar ya k’ara da “I thought kin d’auki alk’awari ma Mommy.. Cewa zaki iya shiga cikin rayuwata..? Here.. Do it.!” Ya k’arashe cikin sigan rad’a yana mai kuma dank’a mata rigar cikin hannunta. Ummul tai rau rau da idanu tana dubansa kaman zata sakar masa kuka tace “Amma..Toh.. Amma ya akai ka cire wancan.?” Har lokacin muryarsa k’asa k’asa “It’s just a patient wear.! Hakan na nufin zan iya cirewa cikin sauk’i..” Ya k’arashe yana tsareta da ido. D’an rausayar da ido kad’an tai tana mai satan kallonsa. Har lokacin idon Haidar na kanta alamun yana jiran ba’asinta. Sai Ya kashe mata ido guda alamun yana jira. Ta d’an gyara zamanta tana duban gefe da gefe. Ta kai idonta kan hospital gown da ake sanyawa wa marassa lafiya Wanda Ya cire. Tace “Amma.. amma Na zata saka rigar asibitin ma dokace.” Kafin tai shiru ya bata amsa da fad’in “You should understand by now that I don’t follow rules.!” Ya k’arashe yana mai tsareta da ido. Wanda hakan Ya kuma sanyata maida idonta k’asa. D’akin Ya d’anyi shiru banda lugude Babu abinda k’irjinta keyi. Ta Ya zata soma sanya masa riga.? Haidar ya soma k’ok’arin saka rigarsa yana hankalce da ita sai faman juya yatsun hannunta take. Sarai yasan tunani take. A hankali yake zira hannunsa still yana kallonta. Out of nowhere ta sinkayo muryarsa “Kenan k’arya kike da kika ce kin dau ma Mommy alk’awarin shiga rayuwata.?” Shiru batace komai ba sai sadda kanta k’asa da tai kaman wata maras gaskiya. Dak’ik’ai suka gifta babu mai cewa komai cikinsu. “Zamanki a nan baida amfani.. You shud also leave please.” Ya fad’i yana k’ok’arin saka rigar da kansa. Ta soma girgiza kai tana dubansa cikin d’an daburcewa. K’ara ya saki kad’an alamun ya fama ciwonsa. Ba shiri Ummul ta k’araso da sauri ta rik’e hannunsa da rigar tana masa sannu had’ida tambayarsa ko ciwo ke masa. Duk ta daburce a hankali take zira masa rigar Har saida ta fitar masa da hannunsa. Idonsa kyam a kanta Har ta gama zira masa rigar ta gyara masa pillow ya kishingid’a. Zata mik’e Ya rik’o hannunta. Ta kaikaito suna duban juna. “You should.. also change.. You can’t sleep with…those cloths.!” Yai maganan yana nuni zuwaga kayan jikinta da idonsa. Ta k’ak’aro murmushi “Kar ka damu.. Zan iya.” Bai kuma cewa komai ba sai tab’e bakinsa da ya d’anyi. Tana kallonsa daga nan yanda take zaune ya tada sallan isha har ya sallame. Can wani ma’aikacin asibitin Ya nemi izinin shigowa Ummul tai masa iso. Nan ya shigo yana turo wani keke irin Wanda ake d’aura abincin majinyaci. Iyakacin k’ayaddajen abincin da majinyacin zaici aka shigo dashi harda dose din maganin da zai sha na wann lokacin. Mutumin zai soma b’alle magani Haidar ya dakatar dashi “Just leave it from here. Kana iya tafiya.” Ya jinjina masa kai kafin ya dubi Ummul Ya bata wani k’aramin card Wanda zata karbi abincinta dashi a cafeteria. Ita dai Ummul sai juya card d’in take tana mamakin asibiti kaman a turai. Dole ma ace ba’a buk’atan d’an tayin jinya tinda duk wani kula za’a baka. Ga na’ura dake indicating musu abubuwa da dama Wanda daga yanda suke zasu fahimci hakan. Haidar yai gyaran murya kad’an Wanda hakan Ya dawo da hankalinta gareshi. Yai mata alama da ido da ta k’araso ta zauna. Ba musu ta k’araso saidai idonta a k’asa dan ita dai tinda ta sanya masa riga ta kuma kasa had’a ido dashi. “Can I take my drugs…now.?” Yai maganar yana mai kai dubansa ga agogon bango dake manne d’akin. Alamun yana nuna mata lokacin shan maganin zai shige. Sai ta dubi magungunan ta girgiza kai “Ban.. Ban san ya zanyi ba.” Ya tsareta da ido sai yace “Come close.. I’ll show you.” Da dan dubesa sai ta d’an matso kusansa kad’an. Shi kaw har lokacin ya tsareta sosai da ido “Closer.!” Ya furta a hankali. Ta kuma dubansa sai ta d’an kuma matsowa.. Saida ya tabbata ta matso kusansa sosai kafin yace ta d’auko parantin maganin ya nuna mata. Ita dai jinsa kawai take amma da ganinta zaka fahimci a tsorace take. Ta d’auki glass cup da bottle water da mutumin ya shigo dashi ta soma tsiyayawa hannunta sai rawa yake alamun nervousness. A haka take yunk’urin kai ruwan da maganin bakinsa Har lokacin hannunta bai daina rawa ba. Shi kaw Haidar sosai ya tsareta da ido. Charaf yai grabbing hannunta. Wanda hakan Ya sanyata d’ago ido tana dubansa a d’an tsorace. Shid’inma ita yake kallo “Just.. relax..!” Ya fad’i yana mai kai hannun nata saitin bakinsa har lokacin idonsa akanta. A haka dai ta ko k’arta ta basa maganin. Akazo maganar abinci zata tashi nan ma yace bazai iya moving arms dinsa ba she should feed him. Haka dole ba yanda ta iya ita ta basa abinci. Ko wani motsi nata kan idon Haidar. Ranar dai ta zamto tamkar personal nurse d’insa. Dan duk wani abu da suke na kula da majinyaci baya bari suyi ita takeyi saidai Wanda yafi k’arfinta ko layin ma’aikatan lafiya ne kawai. Dik yanda taso ta zille ma Haidar Ya kasa barinta. Can dare tana kishingid’e saman sofa shi kaw sai kallonta yake daga nan saman gadonsa ta majinyata. Nan yaga ta tak’ure waje guda ta k’udindune cikin hijab dinta. A hankali Ya mik’e daga saman gadonsa da kyar. Ya tako zuwa yanda take. Zama yai gefenta yana k’are ma fuskarta kallo. Kallo irin Wanda bai tab’a tsayawa yai mata ba. Hannu yasa yana zare Hijab d’in hakan yai daidai da juyin da zatai. Take yaji wani abu ya tsargar masa kaman electric shock. Nan yake binta da kallo head to toe. Ya jima sosai yana k’are mata kallo kafin ya karkatar da ita kad’an Ya kwanta nan gefenta kasancewar kujerar mai fad’i ne sosai. Ya matso da ita cikin jikinsa Ya janyo abin rufuwar Ya rufa musu. ** A can gida kuwa yanda Anisa taga rana haka taga dare. Sai kai komo take a d’aki ita kad’ai tana safa da marwa. Ta lallaba ta tafi d’akin da aka sauki Amminta. Ta tsaya tana kallon mahaifiyar nata dake sharan bacci tana tunanin hirarsu da Mommy da ta sinkaya a asibiti gamed auren Haidar da Ummul. Kodai ta tashi Ammi ne ta sanar da ita taji komai. Tasan komai a halin yanzu.? Toh Amma Hisham yace ta bar masa komai.. Ya mata alkawarin zai cire Ummul daga rayuwar Haidar ko ta halin k’ak’a.. Idan ta sanar da Ammi wani abu yanzu shirinsu da Hisham ka iya b’aci. Bazata bari hakan ta kasance ba. Sauri sauri ta koma nata d’akin. Ta kagu gari ya waye ta bullo da wata hanyar da zata samu taje ta duba Haidar da Ummul tinda Haidar dai ya mata iyaka da asibitin. ** Asubahin fari ta farka tana mamakin yanda bacci mai nauyi ya dauketa itada take yawan farkawa cikin dare. Nan tajita cikin jikin mutum kuma. Zuciyarta ta tsinke. Ita tsoro ma abin ya bata dan Sam bata kawo a zuciyarta majinyaci irin Haidar ka iya mak’alewa gefen kujera har yayi bacci irin haka ba. Ta yunk’ura a tsorace zata tashi sai ta sinkayo muryarsa yana sakin ‘yar k’ara had’ida rik’e gefen hak’ark’arinsa. Su duka biyu duban juna suke kasancewar akwai hasken dim-night cikin d’akin. Tai saurin mik’ewa tsaye daga kan kujerar tana kuma kallonsa. Ganin da gaske na cikin pain dan har lokacin bai daina tamke ido yana dafe hakarkarinsa ya sanyata saurin duk’awa gabansa tana tambayarsa “Da zafi ne.? Na bige maka ciwo ko.? Dan Allah kai hak’uri wllhi ban kula bane.!” Ta k’arashe maganar kaman mai shirin kuka. Sai Ya daina tamke idon da yake yana Ware idanunsa a hankali yana kallon yanda take magana kaman itace cikin pain d’in. Ta d’an saci kallonsa “Kai hakuri zan tabbata na taho da abin rufuwa yau in sha Allah.” Ya tsareta sosai da ido kafin ya girgiza kai kad’an had’ida lumshe idonsa “It’s fine..” Ya fad’i a tak’aice. Ya mik’e a hankali yana fadin “I.. Will use the bathroom.. It’s subh prayer time already..” Ta jinjina masa Kai a hankali “Kana buk’atan taimako na.?” “No I.. Can manage.” Ya fad’i yana dingisawa har ya nufi hanyar bathroom din. Yana shigewa ta zauna had’ida sauk’e deep breath. Hannunta na rawa ta janyo mayafin da ya rufesu dashi. Sai ta runtse idonta da sauri wai yau ita Ummul ke bacci mayafi guda da Haidar.. Kunya ne.? Damuwa ne? tsoro ne? Duk sai ta ma rasa mai ke mata yawo cikin zuciyarta. A b’angaren Haidar Shima haka nan ya lumshe idonsa a bathroom abubuwa fal zuciyarsa. Cikin zuciyarsa yake tuhumar kansa ‘What’s wrong with you Haidar.? Why are you so soft with her..?’ Take zuciyarsa ta shiga tuno kalaman mahaifiyarsa garesa ‘Ka ba ma kanka dama da Ummulkhair.. Kamin wann Haidar koda shine abu na k’arshe da zan buk’ata wajenka.’ A fili yake furta “Sabida Mommy. You are doing it for Mommy and because of Mommy.. Kaman yanda ta buk’ata.” Da safe kuwa su duka biyun yanayinsu ya dan sauya bayan baccin da sukayi tare musamman ma Ummul wacce ta kasa had’a ido dashi. Gaisuwa ma k’asa k’asa tai masa. Haidar nata karantarta. Sassafe take shirin tafiya gida dan ta samu ta kintsa kanta kafin ta dawo. Zata fice ta sinkayo muryarsa “Khairy.!” Cak ta tsaya tana sauraron sunan da ya kirata dashi. Haidar yaci gaba “Don’t take long.. And.. kar ki sake ki zo da wani abin rufuwa asibitin nan.” Sai ta dubesa da mamaki “Amma maiyasa.?” Ya tab’e baki kad’an “Hospital rules.!” Ta jinjina Kai a hankali tace “Shikenan bazan zo dashi ba” Haidar ya jinjina mata Kai sihirtaccen murmushi saman labb’ansa. (Kunji wani salon wayo wajen Haidar. Wai asibiti ta hana zuwa da abin rufuwa daga gida.) Ita dai Ummul Haka ta fice tana mamakin wann wane irin asibiti ne masu tarin dokoki da k’a’idodi. Bayan ficewar ta da kad’an Anisa tai knocking a k’ofa. Duk a tunaninsa Ummul ce ta dawo. Kai tsaye ya bada izinin shigowa. Ga mamakin sa Anisa ya gani rik’eda jakan kaya. Ya tsareta sosai da ido alamun yana jiran ba’asi tinda yasan ya mata iyaka da asibitin. Ta k’ak’aro murmushi tana masa gaisuwar da bata samu amsa ba. “What are you doing here? I thought I made it clear to you…” Saurin katsesa tai ta hanyar d’ago masa jakar Kayan “Kayan Ummul… Mommy ce ta Aiko ni na kawo..” Sai ta d’an saci kallonsa “And.., I…wanted to check how you’ve been holding up.. Laifi ne hakan..? After all, we are cousins.” Katseta yai “I just don’t want you here.. Don’t you get it” Kuka ta fashe dashi tana mai barin d’akin. Ta rasa mai tai ma Haidar yake mata irin wann kiyayya.. Toh kodai ya fahimci da saka hannunta ne a had’arin da ya samesa.? Dole ta nemi Hisham su san ta yanda zasu bullo ma al’amarin. ** Hisham ya dubeta sai kuma ya girgiza Kai yana murmushi “Kar ki bani dariya mana Neesa. Quite alright Haidar na zargin had’arin mota da ya samu shiryayyen abu ne.. Amma ina mai tabbatar Miki ba kece yake zargi ba.” Anisa ta dubesa ta d’an girgiza kai “Ta Ya ka tabbatar da haka.? Sann waye yake zargi.?” Hisham Ya murmusa “Wani hujja yakeda shi da zai zargeki.?” Shiru bata basa amsa ba. Hisham yaci gaba “A kalaman Haidar cewa yayi yana zargin wani ne dake boyayyen agenda akansa. Waye keda dalilin ganin bayansa.?” Shiru bata amsa ba. “Dareen.! Ita ce kawai takeda motive na hallak’a Haidar tinda ta rasa shi bazata bari wata ta same shi ba. Haka ne.?” A hankali Anisa ke jinjina kai. Hisham yaci gaba da murmusawa “Which is why dole na cimma Dareen kafin Haidar Ya cimmata..” Ya kaikaito sosai yana duban Anisa “Duk abinda nakeyi.. Everything is calculated. Ki bar mun komai kaman yanda na fad’a.. Aikinki kawai shine ki saka ido akan Haidar da kuma Ummul.” Ta rausayar da ido “But it is not as easy as it seems. Haidar is making it difficult.” Ya kurbi drink dake hannunsa had’ida d’age kafad’unsa kad’an ya tabe baki “You must do it. You don’t have a choice. Find a way to keep an eye on those two” Ta shiga jinjina kai a hankali tana furzar da huci. Basu ida maganar ba wayar Hisham tai ruri Haidar ke kiransa. Ya murmusa yana duban wayar “Speak of the devil… he shows.!” Ya furta a fili kafin ya d’aga kiran. Bayan Sun gaisa irinta abokai Haidar yace “I sent you an email.. Since you can’t come to visit.” Ya murmusa “Haba abokina ba haka bane.. Kasan asibitin naku ne na turawa. Komai d’an k’aida.. And work’s been too demanding lately.. Musamman da yake baka nan. On the other hand ga neman Dareen da nake. Kasan bazan tab’a barinta ba sai na nemota ta biya abinda ta aikata ma abokina. “Speaking of Dareen. Are

Chapter 39 of 64