da Inna Dije cikin tsananin d’aurewar kai “Wa.. Wani batu kenan..?!”
Dije ta murmusa cikeda cin nasara. Cikin zuciyarta take ayyana lokaci yayi lokacin d’aukan Fansan rasa tilon D’anta Fa’iz da tai a dalilin Ummulkhairy.
Umma ta kuma girgiza Kai “Dije wa.. Wani dalili ne wann.. Kuma.. Wani magana muka tab’a binnewa mu biyun Wanda ni ban sani ba.?”
Dije ta murmusa “Suwaiba kar ki fara mana dramarki a nan.. Dan kinsan tar nake kallonki.. Kin shashantar Dani Karon farko na rasa Fa’iz dalilin ‘yarki bazan kuma bari ki shashantar Dani ba..!”
Umma ta kuma girgiza Kai hawaye na Neman b’allo mata.. Zatai magana Asshe ta dakatar dasu “Wai meke faruwa ne..?”
“Abinda yake faruwa shine D’anku ka iya zama gawa na gaba kaman dai yanda Fa’iz d’ina ya mutu..!”
Asshe ta mik’e tana kuma zaro idanu dafe da k’irji “Na shiga uku gawa fah..! Haidar ne zai zama gawa na gaba..?!”
Dije ta dubeta sosai tace “K’warai kuwa.. Domin Ummulkhairy da kike gani ba mace bace..!”
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.! Shine abinda Asshe take nanatawa tana ganin duniyar na Neman juye mata “Ba mace ba..? Mecece toh..?! Na shiga Uku ni Asshe me na aura ma D’an ‘Yaruwata..?!”
Umma na kuka take girgiza Kai tana duban Inna Dije jin irin sharrin da ake ma ‘yarta akan idonta “Dije kiji tsoron Allah..!”
“Idan banji tsoron Allah ba tsoronki zanji ko tsoron mushurikin mahaifinki wanda ya maida Ummulkhairy yanda take a yanzu..!”
Izuwa lokacin kan Asshe ya gama k’ullewa.. Ta dubi Umma dake duk’e wajen tana hawaye tace “Ke Suwaiba..! Fad’a mun.. Meke faruwa..? Wacece ‘yarki..?”
Umma bata iya cewa komai ba sai kuka tana girgiza Kai..
Inna Dije ta kuma murmusawa “Ai bazata iya sanar dake komai ba domin kuwa batada amsar baki.. Amma ki tambayeni ni zan sanar dake komai.. zan sanar dake Wacece Suwaiba da badak’alan data k’ulla a doron k’asa..!”
Asshe ta d’ago tana duban Inna Dije cikin tsananin shock.
Lokaci guda Inna Dije taci gaba “Yarinyar da kuka aura ma D’anku ba mace bace.. Domin kuwa a lokacin da Suwaiba ta samu cikinta ba cikin ‘Ya mace tai fatan samu ba.. Mahaifin Suwaiba ya kasance gasunkumin malamin tsubbu ne Suwaiba ta tafi wajensa amsar taimako a lokacin tana d’auke da cikin Ummulkhairy kan cewa ya bata lak’anin haifo d’a namiji... Sabida Sun mance Allah shi kad’ai yake halitta mahaifinta bai isa ya sauya halitta ba.. Wann dalili yasa aka haifo Ummul a idon duniya mace ce mai kyau son kowa k’in Wanda ya rasa.. Amma a zahiri ne kawai. A magana ta auratayya namiji bazai tab’a amfana da Ummul ba domin kuwa ita d’in an tsafeta tun a ciki.. Hakan na nufin Ummulkhairy bazata tab’a aure ba.. Idan kuma tai toh fah duk mijin da ta aura zai mutu. Idan bai Mutu kafin ta kaisu ga aure ba kaman dai yanda Fa’iz d’ina ya mutu toh zai mutu idan wata alak’a ta auratayya ta gifta tsakaninsu.!”
Duniyar Asshe ya shiga juyawa.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Meke shirin faruwa dasu.. Shin ta yaya zata sanar dasu suma auren warware asiri kawai na watanni uku sukai da Ummulkhairy Wanda sai ya mu’amulamceta wann sihirin da aka masa ya karye.. Ta ina zata soma sanar da ‘Yaruwarta abinda ke faruwa.. Lallai tana tsaka mai wuya..!
Muryar Umma ne ya katse mata tunanin yanda take fad’i cikin kuka “Haba Dije..! Dije kiji tsoron Allah.. Ki tuna akwai mutuwa.. Dije har zaki iya tsara wann babban k’arya kan D’iyar D’anuwanki.. Dije baki tsoron hakki.. Baki tuna yau idan babu mahaifin Ummul ita amanace a gareki..?!”
“Rufe mun baki annamimiya..! Ke Har akwai maci amana irinki ne Suwaiba.. Kin mance Ya aurenki ya kasance ne na tuna miki Suwaiba..?”
Umma ta kuma kifa kanta a k’asa kuka na kuma zuwa mata. Lokaci guda Dije taci gaba “Talla kike kawowa cikin gari a lokacin Tani da mahaifiyarmu wato sirkarta kenan basu jituwa mahaifiyarmu tana so Yayana Isubu ya k’ara aure kafin ta bar duniya sabida yara mata da Tani ke haifa masa. Mahaifiyarmu tana son samun jika namiji daga wajen D’anuwana Isubu.. Ke Suwaiba kika yaudari Tani kikace a garinku mahaifinki malamin zaure ne kuma yana bada lak’anin mallaka, Tani ta biyeki kika kaita Har rugarku da sunan tana neman lak’anin mallaka. Shakuwa ya shiga tsakaninku kika d’auki Tani tamkar Yaya. Tani ta daukeki tamkar k’aramar k’anwa ta baki dukannin yardarta. Kika zamto mata ingiza mai kantun ruwa.. Kika zaga Tani kikaci amanarta. Maganin bakin jini keda Ubanki kukaita tura ma Tani Wanda zaisa mijin Tani ya tsaneta ya soki. Haka ne..?”
Idanun Umma suka kuma firfitowa waje tana jin sirrikanta kaf Dije na fito dasu. Dan wann b’angare da Dije take fad’i bata da haufi gaskiya ne. Cikin rawar murya irinta mai kuka take furta “Amma nayi nadama kuma mahaifina ya daina wann aikin kafin ya bar duniya Dije. Ke shaida ce mahaifina bai Mutu yana wann mummunan sab’o ba. Dije Allah Algafur ne kuma mai rahama.”
“Ke yimin shiru! yau ne kika san Allah Suwaiba.? Ashe kinsan da haka kika rufe ido kika doge sai kinga auren Ummul kaman lokacin baya da kika doge wajen ganin kin haifo d’a namiji.? Kaman yanda burinki na farko bai ta bata ba Suwaiba haka burinki na biyu ina nufin ganin ‘yarki Ummul a d’akin aure kaman ko wace ‘ya mace bazai tabbata ba.!”
Dije na huci taci gaba “Kusanci da yarda da Tani ta baki da shi kikai amfani kika aure mata Miji. Mahaifiyarmu babu irin soyayyar da bata Miki ba Dik a tinaninta zaki haifo mata jika namiji.. Wanda hakan yasa kukaje kukaita tsibbace tsibbacenku keda mahaifinki dan ki haifo d’a namiji..Idan kin mance na sake tuna miki da cikin Ummul mahaifiyarmu ta bar duniya bataga abinda kika haifa ba Wanda ta k’wallafa ran D’a namiji zaki haifo.. Bayan mutuwar Inna wato mahaifiyarmu mahaifinki ya Mutu shima. Daga nan ne Tani ta fara cuzguna Miki… Kika koma mata tamkar baiwa.. Duk abubuwan da kikai a baya basu isheki ba Suwaiba har saida kika saka mutanen da basuda hakki ciki.. Idan ni na rasa Fa’iz Watak’ila sabida tsanar da na Miki a baya.. Su wad’ann mutanen mai suka Miki kika jangala masu Ummul...? Suwaiba dole ki haukace da son ganin ‘yarki tayi aure kota halin k’ak’a tsoron kar tsafin da mahaifinki ya jefi ‘yarki dashi a lokacin da kike d’auke da cikinta ya tabbata.!”
Girgiza Kai kurum Umma take tana hawaye ganin Dije ta d’aureta ko ta ina.. Babu bayanin da zatai ta wanke kanta. Dije taci gaba “Ke fah akan cikan burinki Suwaiba babu Wanda bazaki ci Amanansa ba. Koda kuwa wann mutumin ya Miki halarci kaman yanda Tani ta Miki..!”
Asshe ta shiga jinina Kai bakinta yana furta “Tabbas haka ne..! Sai yanzu nake fahimtar komai.. Tani taso nusar Dani gaskiya na rufe idanuna.. Ashe ita ce mai gaskiya.. Tabbas na Miki rana Suwaiba.. Babu abinda ban Miki amma kika zab’i ki b’oye mun wann bala’i dake k’unshe jikin ‘Yarki.. Da niyyan taimako na nema ma D’an ‘yar uwata auren ‘yarki.. Ashe ke akwai k’ulli cikin zuciyarki.. Kin cika butulu Suwaiba.!” Muryar Asshe ya soma rawa hawaye na gangaro mata “Ki sanar Dani mai zan fad’a ma ‘Yaruwata da ta aminta Dani Akan Tilon D’anta ta mallaka min wuk’a da nama.! Ki sanar Dani Suwaiba..!” Ta k’arashe kuka na kuma b’allo mata.
Umma na girgiza Kai tana hawaye take fad’in “Ki yarda dani Hajiya Asshe.. Wllhi cikin maganganun Dije akwai Wanda sam ba gaskiya bane.. D’anta had’arin mota shine ajalinsa amma ba auren Ummul d’ina da Ya tasamma bane.!”
“Wani gaskiya kike dashi da har zan yarda dashi..?” Asshe ta katseta cikin d’aga murya.
Lokaci guda taci gaba “Wann auren babu yanda zaije..! Bazan saka rayuwar D’an ‘Yaruwata Akan layi ba.. Za’a Warware wann aure tun kafin ‘yarki ta bar gidan nan.. Zan kira ‘Yaruwata na sanar da ita komai.. Ita zatai umarni ma D’anta ya datse auren Amaryar da aka aura masa wacce ko saninta bai ba..!” Tana ida fad’in haka ta mik’e zata nufi sama..
Umma ta bita a guje ta duk’a gabanta ta kamo k’afafunta tana kuka sosai take fad’in “Ki rufa mun asiri dan girman Allah Hajja Asshe.. Dan Allah kar ki bari a warware wann aure.. Dan Allah kar ki bari a maida sadaki.. Wllhi Ummul mace ce kaman ko wace ‘ya mace.”
Asshe ta fuzge k’afarta “So kike na kashe D’ah na Akan cikan makahon burinki Suwaiba..! Aure dole a warware..!” Tana ida fad’in haka ta kuma fuzge k’afar ta ta nufi sama a fujajan kaman zata kifa.
Hannu biyu Umma ta saka aka tana kuka maras sauti tsoron kar Ummul taji muryarta tasan abinda ke wakana. A fili take furta ta shiga uku ta Mutu ta lalace.
Daga yanda Dije ke tsaye tana dubanta murmushi ta saki. Cikin zuciyarta take furta “Da kyau Dije.. Fansan ran Tilon D’anki kike d’auka.. Aima baki shiga uku ba tukuna Suwaiba.. Dan yanzu ne aka fara buga wasan.. Ba ke kad’ai bace kika iya buga wasa.. Saima kin ci karo da duk tanadin da na miki..
Asshe tana haurawa zama tai gijif saman gado tana jin wani irin tashin hankali na ziyartarta. Yanzu ta ina zata fara b’ullo ma wann al’amari..? Mai zata soma sanar da ‘yar uwarta bayan d’inbin kud’ad’en da ta asma daga wajenta..? Ta sanar da ‘yaruwarta d’iyan mutane masu mutunci mai irin matsalar da boka yace a aura ma Haidar ta samu dukda kasancewansu talakawa amma sunada dattako. Sabida Hajiya Kwaise bata amince D’anta ya kasance da d’iyar matsiyata marassa dattako k’ark’ashin kalmar aure ba koda kuwa na tsawon watanni uku ne kacal. Shin ta yaya zata soma gabatar da wann ahali masu dabaibaye da matsala Wanda tashin hankali yai ma rayuwarsu marfi, dangin tsiya dangin matsafa. Ba’a nan ta tsaya ba Ita kanta yarinyar an tsafeta tin a ciki.. Sann ita d’in barazana ce ga rayuwar Haidar. Ta rintse idanunta tana jin tashin hankalinta na kuma ninkuwa.. Meyasa Tai komai a gaggauce..? Meyasa bata saurari Tani ba..? Meyasa Tai zaton kishi ne kawai da Hassada yasa Tani gaza zaune wajen ganin auren bai tabbata ba..? Ta Ware idanunta sanda zuciyarta ke ambato mata . ‘Mutuwar Kwasko kenan Haidar zaiyi da wann yarinyar da kika aura masa. Shin AUREN WATA UKU zaki ambaci auren ko Auren ajali.? Tabd’ijam! Wann shi ake kira cuta ta d’au cuta.!’
Ta kuma mik’ewa tsaye zufa na kuma tsartsafo mata. Zuciyarta ta shiga amsa mata d’imbin tambayoyin da sukai karan tsaye cimma Zuciyar nata ‘Me kike tunani a auren da aka faro bisa umarnin boka..? Me kike tunani a auren da ba’a nemi zab’in Allah cikinsa ba..? Me kike tunani cikin auren da ba’a d’aukesa umarni daga Allah ba..? Me kike tunani cikin auren da ba’a ginasa bisa ginshik’in auren ba..? Ma’ana ba’ayi sa domin cika sunnar ma’aiki (SAW) ba. Dole abubuwa su biyo baya.. Dole bazaku ga da kyau ba. Kaman yanda kika rufe ido kikai ma ‘yar mutane auren Mutuwa da D’anku haka nan wann matar da kika d’auketa shashasha tai auren mutuwa ma d’anku da nata ‘yar. Tirk’ashi. Lallai yau akeyinta.
Asshe taja wani irin gauron numfashi tana mai kuma mik’ewa tsaye daga zaune. Lokaci guda take furtawa a fili “Me zan aikata ni Asshe.. Me zan sanar da ‘Yaruwata..? Zata fahimci k’arya naita shera mata kenan ina amsar mak’udan kud’ad’e hannunta..? Shin waye zai fanshe kud’ad’en da na amsa hannun Kwaise da sunan AUREN WATA UKU ma d’anta. Shin ma ta ina zan iya mayar mata da kud’ad’en da ta bani na yak’in nemo ma Haidar matar wata uku..? Dan nayi imani nawa mijin ba biya zaiyi ba dan shi mutum ne da mata bata cin kud’insa sai wacce yake yayinta. Nida ‘Yaruwata kuma k’ar tasan k’ar ne akan kud’i. Zamu iya samun matsala ta tarwatsewar ahali akan kud’ad’en da ta tafka asara ba tareda ta samu biyan buk’ata ba. Uwa uba taji auren mutuwa na shirya ma tilon D’anta Wanda ita kanta ta saka nata Auren cikin had’ari domin ta ceto sa daga mugun asirin da aka jefesa dashi. Mijina will come to know everything. Duk abubuwan da na aikata harda zuwa wajen boka da AUREN WATA UKU da na k’ulla Wanda Ya k’unshi kisan kai. Zai rabu dani rabuwa ta har abada. Even my children will leave me. Kowa zai gujeni na zama banida tsuntsu banida tarko. Kishiyoyina su samu abun yawo Dani. Lallai ina tsaka mai wuya ni Asshe. Suwaiba ni ta cuta a duka wann al’amari. Gashi garin k’ok’arin gyara ahalin ‘Yaruwata ni zan tarwatsa nawa ahalin da farin cikina. Toh amma rayuwar Haidar ake magana a nan.” Ta shiga girgiza kai tana mai furtawa a hankali “A’a.. A’a bazan bari hakan ta kasance ba.. Haidar’s life is at stake here.. Bazan bari a kai masa ajalinsa ba.. I need to do something immediately.. I need to come up with something… I just.. Can’t sit back and do nothing.. Amma me zanyi..?”
Batakai aya ba wayarta ta soma ruri Hajiya Kwaise ke kira.
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU.!*
*21*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Jikin Asshe Ya kuma yin lak’was dan gani take kaman Kwaise ta riga ta san komai. Cewa Ajalin D’anta zata kai mata matsayin makarin asirinsa.. Har wayar ta kusa tsinkewa kafin Asshe ta iya tattara daidai gwargwadon natsuwan da yazo mata a wann lokacin. Murya a raunane ta d’aga kiran “Aunty Kwaise..”
Daga d’aya b’angaren Mommy ta kaste ta “Asshe duk yanda za’ai Amaryar wata uku ta iso Abuja a gobe.. Asshe a yanda na hango tsananin k’iyayya a idon Haidar Ya kuma haifar min da tsoron rasa D’ana. I can’t afford to lose him Asshe. Haidar shi kad’ai ne D’ah na zanyi komai zan sadaukar da komai nawa dan na kub’utar dashi da ahalina daga sharrin shed’aniyar can. Asshe bana so a sami wani mishkila. Ki kula da matar wata uku da kyau tamkar k’wai a hannun yaro tinda kinsan amfanin ta wajenmu. Rayuwar d’ana tamkar yana had’e ne da nata rayuwar. Har sai lokacin da zata karya wann asiri da aka jefesa dashi. We need to make sure ta iso a gobe cikin k’udurar Ubangiji.”
“Amma.. Amma.. Aunty Kwaise..”
“Asshe Babu wani Amma.. I cant afford to lose my son completely… Just do as I say.. The house is set. Everything is ready. Isowarta kawai ake jira na rik’e Haidar a gida kaman yanda yake bisa yarjejeniyar mu dashi. Engr ma cikin satin nan zai tafiya, Business trip. Akan Auren Haidar na hana kaina bin mijina tafiyar da zai d’aukesa makonni kinga kuwa na shirya ma wann aure. Na shirya karya asirin da akai ma Haidar.” Mommy ta k’ark’are wayar nata tana kuma jaddada ma Asshe lallai lallai kar a samu wani matsala.
Asshe Tai sakare tana duban wayar. Zama Tai gijif cikin gado zuciyarta naci gaba da tsinkewa. Shikenan.. Ta faru ta k’are wai anyiwa mai dami d’aya sata yanzu mi zatayi..? Ba tada ikon canza komai a halin yanzu. A dole ta nad’e Ummulkhairy ta kaita ma Yayarta Kwaise. Yanzu ita meye abinyi. Anisa ce ta fad’o zuciyarta. A fili ta furta “Anisa.. Anisa zata taimaka min na aiwatar da komai ba tareda Haidar Ya cutu ba sann ba tareda ‘Yaruwata ta fahimci komai ba. Lallai zaman Anisa a can shine kawai rufin asirina. Toh amma idan Anisa taje ta tafka wani shashancin fah.? Kuma kenan zaki sanar da Anisa komai.?” Ta soma girgiza kai a hankali “A’a Anisa doesn’t need to know about everything. Kawai umarni zan dinga bata daga nan.” A hankali ta shiga jinjina kai kafin ta nufo k’asa.
Nan Asshe ta tadda Inna Dije ta titsiye Umma sai ta fito mata da Ummulkhairy ta tafi da ita. Umma sai kuka take tana rok’on Mama Dije ta rufa mata asiri kar ta tona mata Auren Ummul ya mutu tun a daren aurenta kafin tafiyarta. Cikin gunjin kuka Umma taci gaba “Dije ki dubi girman Allah ki rufa mun asiri.. Wanda kika tona min ma Ya isheni wllhi.. Yanzu idan auren Ummul Ya Mutu Tun a daren yau da wani idanun zan kalli mutanen unguwarmu da dangi baki d’aya… Dije idan kina ma Allah kar ki d’auki Ummul.. Kar ki tafi da Ummul..”
Kaman daga sama muryar Asshe ya katse su “Babu yanda za’a tafi da Ummul domin kuwa a halin yanzu mutum d’aya keda iko da Ummul shine mijinta..!”
Gaba d’aya suka juyo suna dubanta, daga Umman Har Mama Dije.
Asshe taci gaba da sauk’owa daga bene cikeda k’asaita. Ta k’araso gaban Inna Dije dake tsaye gaban Umma wacce ke duk’e kaman mabaraciya tana Koke Koke.
Dije ta zuba ma Asshe idanu. Su duka biyun suna duban juna. kowacce tana sak’awa cikin zuciyarta.
Murmusawa Dije Tai tana kuma duban Asshe da kyau “Da gaske..? Bayan duk abubuwan da kika ji… Kin amince a kaima D’anki ajalinsa..? Oh! D’an ‘yaruwarki..? Haka ne..?!”
Asshe ta murmusa tana ma Dije irin duban da biri yake ma Ayaba “Ko mai zai faru a halin yanzu.. Ummul tana k’ark’ashin ikon mu ne.. Sadaki D’anmu Ya biya Wanda Ya tabbatar da wanzuwan igiyoyi Har guda uku da suka mallaka masa cikakken dama da iko akan Ummul. Duk wani abinda zai biyo baya, hukunci zai zamana yana wajenmu.!”
Sosai Mama Dije ta tsareta da idanu tana ji akwai wata a k’asa. Dan ta tabbata wann aure ba auren Allah da Annabi bane.. Duk yanda akai akwai wata shiryayya. Idan auren tsakani da Allah ne bayan duk abinda ta sanar ma Asshe a gaban Suwaiba wacce take mahaifiya ga Ummul ba yanda za’ai Asshe ta amince akaima D’ansu mace irin Ummul.
Umma harda sujudusshukur tayi dan farin ciki. Ta shiga d’aga hannaye sama tana mik’a ma Allah godiya “Alhamdulillah..! Alhamdulillah Allah abin godiya.. Allah gatan bawansa.. Kai amma dai annamimi baiji dadi ba.. Zakaran da Allah ya nufa da cara ko fah ana Muzuru ko ana shaho sai yayi.. Kuma wllhi idan rana ta fito tafin hannunki bata isa ta rufesa ba Dije..! Tani ma ta buga Dani ta barni balle ke..!” Ta k’arashe tana mik’ewa tsaye harda rangad’a gud’a.
“Bada garaje ba Suwaiba..!” Muryar Asshe ya dakatar da ita.
Umma ta waro idanu waje dafe da k’irji tana duban Asshe. Sai kuma ta soma girgiza Kai “A’a dan Allah.. Ki rufa mun asiri Hajja Asshe.. Ki dubi girman Allah kar ki bari mak’iya suyi dariya.. Wllhi duk abinda kikaji daga bakin Dije ba komai bane face sharrin mak’iya..”
Asshe ta dafa Umma tana murmushi “Kin yarda cewa aure rai ne dashi..?!”
Umma ta jinjina kai tana duban Asshe.
Asshe taci gaba “Bazai Mutu ba sai kwanakin Sa ya k’are.. Haka ne..?”
Nan ma a sanyaye Umma ta jinina Kai.
Asshe ta juya ta basu baya daga Umma har mama Dije lokaci guda tana taka parlorn nata a hankali take ci gaba da fad’in “Bari muce auren Ummul zai rayu ne na wani d’an lokaci..!”
Dummm! Haka k’irjin Umma ya buga. Jiri ne taji na neman aikata k’asa. Ta dafe garu tana furta “Ban ban.. Ban fahimceki ba Hajja Asshe.. Mai Kike nufi da cewa auren Ummul zai rayu ne na wani d’an lokaci..?”
Assshe ta juyo tana dubansu “Ina nufin zai rayu ne na tsawon watanni uku kacal.!”
Dije ta gyara tsayuwarta sosai tana duban Asshe makirin murmushi kwance saman fuskarta. Cikin zuciyarta take furtawa ‘Eh Lallai.. Da alama yanzu ne wasan zai d’au zafi.. Bari dai mu gani..!’
Muryar Umma ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi.
“Ban.. Ban gane tsawon watanni uku kacal ba.. Me kike nufi Hajiya Asshe..? Me kike nufi da auren Ummul zai rayu ne na tsawon watanni uku kacal..? Ki min magana dan Allah.. Ki sanar Dani mai kike nufi..?!”
“AUREN WATA UKU..! Ina nufin AUREN WATA UKU kawai mukayi ma D’anmu da ‘yarki.. Bayan wata uku.. ‘Yarki zata dawo gareki.. Sai ki shirya mata wajen zama bayan wata uku..!”
Duniyar Umma ya shiga juyawa sama na koma mata k’asa… Ta girgiza kai tana jin hankalinta na neman gushewa da gaske. Cikin rawar murya Umma ke furta “Amma.. Amma meyasa haka Hajiya Asshe.. Shin wani irin aure kukai ma D’anku da ‘Yata… Meyasa na wata uku kawai..?”
“D’an ‘Yar uwata yana aiki ne k’ark’ashin Kampanin Mahaifinsa. Mahaifinsa zai basa wani k’wangila ne na tsawon watanni uku kawai idan yayi aure.. Bayan wata uku zai gama wann kwangilar.. Daga nan kuma bamuda buk’atar ‘yarki dan kwangilar ta k’are.. Kin fahimta..?” Ta k’arashe tana duban Umma sosai.
Umma na girgiza kai cikeda rashin yarda take duban Asshe “Amm.. Amma.. Amma.. Bamu yi haka dake ba.. Wann zalunci ne.. ‘Yata ta jima, ta d’auki lokaci batayi aure ba.. meyasa kuka zab’i cutar mun da ‘ya.. Ummul.. Ta wahala a rayuwa, ta fuskanci k’alubale na gujewan manema.. Ta fuskanci k’alubale da dama.. Bata cancanci irin wann auren ba.. ‘Yata ta cancanci aure na gaske.. Aure mai d’orewa ba mai rabewa ba.. Shin Auren Kwangila kukaima D’anku da ‘yata..? Hajiya Asshe kin cuceni.!”
“Ban cuceki ba hasalima taimakon ki nayi.. Idan baki mance ba sadakin ‘yarki shine kud’in jinyar mijinki.!”
“Wani irin taimako ne wann..? Wane irin taimako ne haka.. Wann zalunci ne ba taimako ba..”
A zuciye Asshe ta katseta “Kar ki sake cewa na cuceki.. Ke kika cuci kanki.. Magana akan cuta.. Shin tsakanin ni da Ke waye ya cuci wani..? Ni da naima D’ana auren cikan buri da ‘yarki ko kuma keda kika cuceni kika sakani a tsaka mai wuya, nai jagoranci wajen aura ma d’an ‘Yaruwata wann ‘yar taki mai lullub’e da Illan asiri da farar k’afa.. shin ki fad’a mun… Tsakanin mu biyun waye ya cuci wani..? Rayuwan d’ana yana tsaka mai wuya a nan.. Idan Haidar Ya Mutu ‘yarki ce Sila.. Shin banyi adalci ba da nace zata zauna na tsawon watanni uku..?!”
Umma taci gaba da hawaye tana duk’e wajen.
Asshe taci gaba “Ki gode ma Allah.. ‘Yarki bazata fuskanci tozarci na mutuwan aure a daren aurenta ba.. Ki gode ma Allah bayan duk abubuwan da kikayi ‘yarki zata zauna k’ark’ashin Inuwan aure na tsawon watanni uku.. Ki gode ma Allah bazaki fuskanci dariya da gori harma da wulak’anci idan har auren ‘yarki Ya Mutu a daren yau ba.. Domin kuwa duk wani Sirrinki da naji sai na bankad’e.. Kuma Kinsan me..?” Ta k’arashe tana mai duk’awa gaban Umma dake duk’e tana hawaye “Zaki amar da duk wasu kud’ad’en da na kashe wajen nema ma D’an ‘Yaruwata auren ‘yarki. Kaf ko kobo bazan bari yai ciwon kai ba.. Kin shirya biya.?” Ta k’arashe tana tsare Umma sosai da ido.
Inna Dije ta k’arada “Daga nan kuma sai kiyi bankwana da Mijinki Suwaiba bayan kin rasa yaranki. Dan bayan abinda Ya faru ki sani zan d’auke D’anuwana na masa jinya bazan barshi tsakanin mata guda biyu da Babu Allah cikin zukatansu ba..!”
Umma ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana duban Dije da Asshe “Dan Allah.. Kar ku jefa rayuwata cikin garari.. Kuji tsoron Allah.. Kuji tausayin rai.. Ku tuna kuma iyaye ne.. Kuma burin ko wace uwa ta kai ‘yarta d’akin miji.”
“Kar kiyi mana maganan zama iyaye a nan.. Domin kaw baki tab’a zama uwa ga ‘ya’yanki ba Suwaiba.. Kuma yau zaki fara girban duk abinda kika shuka..!” Dije ta k’arashe tana sakin huci.
Asshe ta gyara tsayuwarta “A tsakanin watanni ukun ma inada sharud’a.. Dan Kinsan a daren nan zan iya kashe auren ‘yarki Suwaiba haka ne..?!” Ta k’arashe tana duban Umma kannare da idanu.
Umma ta share hawayenta tana kuma jinjina kai a hankali kaman marainiyar mage.
Asshe ta jinjina kai “Shradina shine bazakiyi magana da Ummul ba har na tsawon watanni Uku. Ina nufin iyakacin wa’adin zaman da zatai da D’anmu. Keda had’uwa da ita kuma sai kwangilar D’ana Ya k’are randa Ya cika aikinsa ya warware auren.. Ni kuma zan d’auko ‘yarki da kaina na kawo miki ita cikin mutunci. Kin amince..?”
Umma ta d’ago a raunane tana duban Asshe jin da gaske dai Auren wutin gadi Ummul tayi ba kaman yanda taci mata buri ba. Sann ga wasu dokoki da sharud’a Wanda aka gindaya na datse alak’arta da ‘yarta “Dan Allah kar kiyi haka.. Kiyi hakuri… Kar ki rabani da Ummul.. Wllhi Ina son ‘Yata..”
“Na zata kinfi so tayi aure tayi nesa dake… Ko ba haka bane..?” Asshe ta katse ta.
Umma ta kuma rintse idanunta tana hawaye.
Muryar Inna Dije ya katseta “Burinki Ya cika Suwaiba.. Mata mazan ‘yarki tayi aure.. Amma aure mai gibi.. Wanda bada jimawa ba angulu zata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 64