nawa Ummul d’in take ne..?”
Umma ta dago a zabure jin yace nawa Ummul d’in take. Tai karaf tace “Ta fah haura talatin Abban Ummul.”
Taci gaba “Yo wani ilimi zata nema ya wuce ilimin zama a gidan miji da naketa k’ok’arin bata.. Allah na tuba abu kaman jifa ko sa hannu.”
Abba ya kuma katseta “Kinga Suwaiba na rabaki da wann gurb’ataccen tunani.. Ki je kina jefa kanki cikin damuwan abinda Allah bai d’aura Miki ba.. Ko an fad’a Miki bansan kina amso ma Ummulkhairy Neman Taimako bane.. Nasan komai kawai ina kauda ido ne ina Miki uzuri.. Amma ki sani kar kawar da idanun da nake bana magana yasa kije ki auka ga sab’awa mahaliccinki kiyi shirka.. Ki natsu ki san mai Kike ciki.. Allah yana sane da duk abubuwan da suke faruwa.. Addu’an da zaki mata Har sai yafi na Wanda zaki saka wani ya mata domin kaw ke mahaifiyarta ce.. Idan har da gaske so kike tai auren kaman yanda kikaci buri. Sai ki rage bacci ki tashi cikin dare ki Kai kokenki ma Ubangijin duka. Ki zubda hawaye a yanda zuban hawayen zai amfani domin kaw wajen Allah ne hawayenki keda amfani ba mutanen da zasuyi murna da ganin hawayen naki ba. Haba Suwaiba kiyita korototo kina kin shiga uku..? Da irin wann korototo da ambaton uku da kike ma kanki toh fa babu abinda zaki gani sai ukun..”
Ta kuma kamo bakin zani tana share hawaye “Haba Abban Ummul dan Allah ka fad’a alkhairi..”
“Kece zakiyi ma kanki karatun ta natsu ki dinga fad’in alkhairi gameda ‘yarki ko dan rayuwarta ta inganta. Domin kuwa su ‘ya’ya amana ce Allah Ya bamu kuma za’a tsaida mu a tambayemu akansu ranan gobe.” Ya k’arashe yana mai janyo kwanon tuwon sa.
**
A can d’aki kuwa Khulsum ce ta duk’a gaba ga Ummulkhairy, tayi zaman rak’umi tana fuskantar ‘yaruwar tata da tin shigowarsu gidan take aikin abu guda wato kuka.
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU.!*
*03*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Cikin gunjin kuka Ummul taci gaba “Mai kuma zaki fad’a mun Khulsum.. Ba dai kinyi abinda kike so ba kin tari matan nan da fad’a har Zubair ya iso ya taddamu a haka.. Toh me kuma yai saura tinda gashi ko wayata bai d’agawa.. Khulsum, Nifa burin mahaifiyata kawai nake son cikawa..!” Ta k’arashe wani kukan na taso mata.
Khulsum ta girgiza Kai “Adda Ummul dan Allah ki saurareni.. Wllhi mutumin nan bai cancanceki ba.. Ba son gaskiya yake Miki ba.. Da ace son gaskiya yake Miki da ya baki dama ya saurara daga b’angarenki, amma baiyi haka ba ya hau kan dokin fushi..”
“Har akwai Wanda ya cancanceni ne Khulsum..?” Tai maganar tana nuni da kanta cikin rawar murya irinta mai kuka.
Khulsum ta girgiza Kai “Dan Allah kar ki bi maganganun Umma da mutane.. Kar ki kaskantar da kanki Adda Ummul.. Wllhi kin wuce gaban duk mazan dake fasa aurenki.. Kimarki da ajinki ya wuce nasu. Shima wann zubair din bai cancanceki ba shiyasa ya kasa ganin kimarki kaman dai sauran.”
Ummul tai murmushi mai ciwo “Watak’ila banida wani kima da gaske Kulsum.. Watak’ila abubuwan da mutane ke fad’i kaina gaskiya ne.”
“K’warai kuwa Ummul mace mai shekarunki batada wani kima matuk’a ba d’akin mijinta take ba..!” Muryar Ummansu ya katsesu wacce tai tsaye tana sauraron tattaunawar yaran nata.
A tare suka d’ago suna duban Umma dake aika masu mugun kallo tana huci.
Khulsum ta lumshe idanunta had’ida furzar da huci “Umma wai dan Allah meyasa Baki saka farin cikin yaranki a farko.. Mutanen nan fah tuni sunzo Sun amshe kayansu, wllhi ko Zubair baizo ya tadda Adda Ummul na rabon fad’a ba bazasu bari ya aureta ba tinda sunyi furuci kuma sun amshe lefensu.. Haba sai kace ana Neman Kai da ita.. Dik anbi an tsangwameta a gida da waje duk bata huta ba.. Umma auren nan fah ba’a ce yana cikin cika cikan musulunci ba.!”
Umma ta danna mata dak’uwa “Kinci ubanki Khulsum.. Idan baya cikin cika cikan musulunci ai sunna ce mai k’arfi… Ke baki San ko gawan mace mai aure yafi daraja ba.. Cikan mutuncin mace shine a ganta a d’akinta..” Ta d’an numfasa kafin taci gaba “Kina jina idan baki daina korarwa ‘yaruwarki mazajen aure da wann bak’in Zuciyar naki ba wllhi kinji na rantse zan saka k’afar wando d’aya dake.. Maimakon ki duk’afa Neman naki mijin auren kin tsaya kina lalata na ‘yaruwarki koh.. Toh ahir d’inki Khulsumu aure dai da izinin Allah ina numfashi sai Ummul ta tafi d’akin mijinta ko mai zai faru kuwa.!” Ta k’arashe sai tsuma take.
Khulsum ta d’ago tana duban mahaifiyar tasu da mugun mamaki. Lokaci guda ta girgiza Kai kad’an tace “Umma dan Allah a dinga Neman zabin Allah dai.. Kuma a dinga k’ok’arin furta alkhairi.. Auren nan duk yanda aka so bazafa ayi shi ba sai lokacin da Allah yace kuma yaso.”
“Aw Nima rashin kunyar zaki min.. Toh bismillah.. Nace bismillah Khulsumu..” Tai k’wafa tana mai k’arawada “Rikakkiya kawai.. Bazan dai Miki baki ba dan bana fata ki Kai shekarun Ummul a gabana baki tafi d’akin mijinki ba.”
Ita dai Khulsum bata ma ce komai ba dan tsanar mazan ma tai balle wani aure tin bayan abinda ke faruwa da ‘yaruwarta.
**
ABUJA
Akasarin gidajen da kake iya hanga tapka tapkan benaye ne masu tsananin kyau da tsari. Yanda aka tsara su aka kuma inganta gininsu zakace a k’asar turai kake. Tapkeken gida ne da ya amsa Sunansa, ga korayen shuke shuke da ciyayi masu d’aukan idanu da ban sha’awa. Komai na gidan fari ne k’al tamkar fadar White House.
A hankali yake Jin hasken ranan hantsi yana haske masa fuska sakamon baccin da ya d’aukesa a balcony d’insa saman wasu kujeru na shakatawa tin bayan da ya gabatar da sallar asuba. Sautin motoci da tsuntsaye jifa jifa suka soma gauraye masa kunnuwansa da bai cika shiri da hayaniya ba. Nan take kuwa suka katse masa baccin nasa.
Tafukan hannayensa yasa ya shafe fuskarsa dasu kana ya mik’e zaune yana duba agogon dake fuskar wayarsa. A kasalce ya jefo k’afafunsa k’asa ya mik’e tsaye yana kuma stretching gabb’ansa.
Kai tsaye bathroom ya shige bayan ya tura k’ofar glass da ta raba balcony d’insa da d’akin nasa.
Cikin mintuna k’alilan ya shirya tsaf ya fito cikin black business suit d’insa. Kallo guda zaka masa ka tsarkake Ubangijin da ya tsara halittarsa.
Koda ya sauk’o k’asa yana iya sinkayo muryar mahaifiyarsa tsakanin ma’aikatan gidan ta yanda take shiga bata nan take fita ba. Ya d’an furzar da huci had’ida girgiza Kai. Wann morning routine d’in mahaifiyarsa ce. Idan da sabo duk mai rayuwa cikin gidan ya saba da wann. D’an girgiza kansa yai ba tareda ya nufi cikin gidan ba. Lokaci guda yasa Kai ya fice cikin sauri ya nufi yanda motarsa ke ajiye. Nan da nan yaja motar ya fice daga gidan a gaggauce dan Sam baiso yai arba da mahaifiyar tasa a safiyar.
Bai zarce ko ina ba sai wani makeken building maiji da tsawo da kuma girma had’ida tsari. Daga saman ginin anyi rubutu da k’araffa masu ruwan zinari *MAITAMA BUILDERS*. Rubutun anyisu ne da Manyan bak’ak’e.
Cikin sassarfa yake taku a katafaren ginin mai k’unshe da ma’aikata sahu sahu. Waya manne b’angaren kunnensa na hagu. Dik yanda ya shige kaw sai ya d’ibi gaisuwa Dikda ba amsawa yake ba.
Lift ya shige ya diresa a third floor. Wani hamshak’in office mai tsananin girma da tsari ya nufa, still waya yake.
Nan da nan wata mata cikin shiga cooperate ta biyo bayansa.
Cikin muryarsa mai cikeda k’warjini Yaci gaba da furta “You find a way to fix this Hisham…Honestly, I’m highly disappointed. I did not expect my team members to be so unprofessional like this… Iyakacin abinda na sani shine we must cover the deal by all means possible.” Yana Ida fad’in haka ya katse kiran ba tareda ya jira amsar Hisham ba.
Matar da tin isowarsa yai mata alama da hannu da ta biyosa sakatariyar mahaifinsa ne Wanda kuma ya kasance mammallakin wann shahararren Construction Company d’in wato Maitama Builders.
Ta d’an risina tana gaidashi “Good morning Sir.”
“Morning Jane.” Ya fad’i sanda yake kaikaitowa har lokacin idaninsa na kan fuskar wayarsa. Lokaci guda ya k’arada “Is my Dad here..?”
Ta d’an girgiza Kai alamun a’a “He….hasn’t arrived yet. Sir.”
Shiru yai kaman mai nazari. Securities masu tsaron gate d’in gidansu sun tabbatar masa Dad d’insa ya fita tun sassafe toh ina ya tafi idan ba Office ya taho ba. Yasan mahaifinsa mutum ne mai matuk’ar girmama aikinsa.
Jinjina mata Kai yai “Alright, let me know the minute he arrives.” Ya Fad’i yana mai nufan k’ofa.
Jinjina masa Kai tai had’ida amsawa kafin ta take masa baya suka rufo ofishin Wanda ya kasance ofishin mahaifinsa.
Engr Aliyu Aliyu Maitama kenan. D’ah d’aya tilo ga Engr Aliyu Maitama. Shid’in sunan mahaifinsa yaci sann same profession suke da shi da mahaifinsa. Su duka biyun Construction Engineers ne. Mahaifiyarsa ita ta tilasta masa yin karatu irin na mahaifinsa ba wai dan yanada buri ko mafarkin hakan ba. A cewarta ta ginasa Akan karatu da aiki irin na mahaifinsa ne domin kaw shine zai gaji mahaifin nasa. Wann dalili yasa harta da suna saida ta maida masa da sunan mahaifin nasa.
Second floor ya dawo ya nufin wani hanyar. Babban ofishi ne da ya k’unshi tables da dama, saman ko wanne table akwai na’urar computer bisa. Daga gefen ko’far glass d’in da zai sadaka da lobby an rubuta daga sama kad’an *Marketing Development Department*
Wani madaidaicin d’akin taro ya nufa. Daga tsakiya akwai doguwar table kewaye da kujeru a k’alla goma.
Tin daga nesa employee guda ya hangesa. A guje ya shigo Office d’in yana sanar dasu “Guys guys…” kowa ya kakaito yana dubansa. Saurayin yaci gaba “Sir Haidar is here and he seems to be in a very bad mood. Let’s all behave ourselves.” Ya karashe yana daga masu gira lokacin da yake daidaita zamansa cikin kujeransa.
Take kowa ya shiga taitayinsa.
Ai kaw yana shigowa mutanen dake zaune saman table d’in alamun isowarsa suke jira nan suka soma kwasan gaisuwa.
Bai amsa ba saima nufan kujeran dake daga tsakiya da yai. Laptop d’in da ya shigo dashi ya bud’e ba tareda ya tanka kowa ba ya shiga danne danne.
Wannan ya kalli wancan wann ya kalli wann. Ganin shugaban nasu ya had’asu ya kuma samu isowa sann baice komai ba.
Shiru mintoci suka shud’e kafin ya kaikaito masu da fuskar computer d’in kowa ya na gani.
“This is our new marketing development plan… I suppose..”
Kowa ya jinjina Kai alamun haka ne.
Haidar ya gyada Kansa kafin yaci gaba “Wanda mukai discussing kuma muka b’ata lokaci sosai muna aiki akai in our last meeting.. Haka ne..?” Nan ma gyada kawunansu sukai alamun eh haka ne.
“But unfortunately, we can’t go on with this new strategy.. And do you know why..?” Ya k’arashe cikin tsananin tsarewa yana dubansu d’aya bayan d’aya. Babu Wanda ya iya basa amsa.
Lokaci guda ya jinjina Kai kafin yaci gaba “Sabida bansan ya akai other company suka samu irin wann strategy d’in har suka rigamu applying cikin kasuwancinsu..”
Nan kuma suka soma maganganu k’asa k’asa kowa yana duban d’anuwansa yana mamakin ya hakan ta kasance.
Cikin bud’e murya ya katse k’anan cecekucensu “So tell me now.. who is selling our company..? And I’m pretty sure is someone from this department.. Kuma yanzu zaku sanar dani yanda akai abinda muka tattaunawa ya fita har wasu company suka samu.!”
Kowa yaci gaba da cewa baida masaniyan yanda akai hakan ta kasance.
Table d’in ya buga da k’arfin gaske. Cikin tsananin b’acin rai yake furta “Do you even realize the kind of loss we are going to suffer..? What do you want me to tell the board members..! Mai kuke so na sanar dasu..? Let me tell you this..!” Yai maganar yana nunasu da yatsa d’aya bayan d’aya “I don’t tolerate incompetency. And I don’t work with traitors. A cikinkun nan zaku nemo mai mana zagon k’asa. Before the day ends.!”
Baikai aya ba sukaji an banko k’ofar zauren taron. Gaba d’aya suka juyo suna duban Wanda ya shigo.
Engr Aliyu Maitama mammalakin Kampanin shine ya shigo cikin tsananin b’acin rai. Ko la’akari da mutanen dake zauren taron baiba ya k’arasa ya cakumo matashin nan cikin tsananin karaji sai sakin huci yake. Yana k’arasowa bai wata wata ba ya d’auke Aliyu da mari mai kyau.. Yana d’agowa ya kuma Kai masa wani Marin Wanda saida ya tsaga masa baki jini ya fita.
Rintse idanunsa yai yana k’ok’arin nitsa zuciyarsa.
Ganin haka yasa mutanen suka soma kokawan ficewa daga cikin zauren. Kowa ya kwana da sanin rashin jituwar dake tsakanin Engr Maitama da tilon D’ansa amma zasu iya cewa basu tab’a ganinsa cikin yanayi irin na yau ba.
Engr Maitama ya kuma shafe fuskrsa da tafukan hannayensa yana nuna ma Aliyu fuskar iPad d’in da ya shigo dashi “Ka amsa min.. Menene wann.. What is the meaning of this.?”
Aliyu bai iya furta komai ba sai sadda idanunsa k’asa da yai dan yasan haka zai faru tinda shi dai dama a idanun mahaifinsa kullum ba daidai yake ba.
Mahaifinsa yaci gaba “Na zata Kai d’in kasan abinda kakeyi by now.. Na zata bazaka bani kunya ba wann karon.. Na zata zaka proving mun cewa zan iya mallaka maka ragamar jagorancin Kampanin nan in three months time.. But I was wrong.. You are not capable of anything good..!”
Cikin kwantar da murya yake furta “Dad believe me, I have no idea how our new development plan get disclosed.. I believe someone is sabotaging our company..”
“Shut up.!” Mahaifinsa ya katsesa kafin yaci gaba “Dama ta ya za’ai ka sani.. Kana can kana shashashancinka other companies are doing great..” Yaci gaba da nunasa da d’an yatsa “Ban d’auraka a matsayin Head of Marketing development department ba saida na tabbata na turaka k’asar Amurka na musamman domin ka karanci course na musamman a fannin Business Management.. Don’t make me regret this Aliyu.!” Yatsansa har rawa take sanda yake pointing D’an nasa dashi.
Wani gauron numfashi Haidar yaja had’ida lumshe idanunsa cikin k’ok’arin nitsa zuciyarsa. Muryar mahaifinsa ya kuma sinkaya yana ci gaba “Our website is is.. is just a photo catalog and nothing more.. Tell me waye zai tsaya b’ata lokacinsa a nan.. A kasuwanci irin namu your website is often the first place potential costumers will go to find more information about your company and its services. Therefore, it should be well designed and offer them exactly what they are looking for.!”
Haidar ya kuma furzar da huci “Dad, you please listen to me first.. Na sani our company hits a bit of a marketing plateau. But that doesn’t mean we should simply give up..” Ya d’an sassauta muryarsa kafin yaci gaba “Daddy, I believe we can come up with a new marketing strategy that would help us to not just get our business back in the game but ahead of the game. Aikin da Kampanin mu zaiyi zai tabbatar da hakan.”
“Shut up.. Rufe mun baki..!”
Haidar ya Had’iye k’uncinsa yana furzar da huci mai d’umin gaske.
Cikin karaji yaci gaba da nunasa da d’an yatsa “How could you have failed in accomplishing a simplest of tasks.. How could you have let our business rivals get ahead of us.. Because of your foolishness now, our company is at risk of going bankrupt.. kana can kana shashancinka other companies are doing great.. A haka ne kake tunanin ni Aliyu Maitama zan d’auki project d’in da ci gaban Kampani ya ta’allak’a a Kai ka jagoranta cikin watanni uku.. Bari kaji na fad’a maka.. I did not build this company to hand it over to a pathetic loser like you..” Yai fasali kafin yaci Gaba da nunasa “You are a disgrace to me Aliyu.. Kai baka cancanci sunana ba.. Mahaifiyarka tayi kuskure da tayi zaton zaka zamto kaman ni.. Har abada Kai bazaka tab’a zama kaman ni ba.. Kasan dalili..?” Ya k’arashe yana mai kuma takowa sosai gaban Aliyun “Sabida Kai baka saka komai a gabanka ba face shashanci… Ina nan ina Fad’i tashi to make a proper man out of you kana can kana shashanci da abokan banza.. Kana so kace mun duk kudaden da sukaita fita under your department a banza suka fita babu result a k’asa..? Ya jinjina Kai yana sakin huci “Ina sakamakon aikin..? Nace ina sakamakon aikin..?! Chacha kake da Kampanina..? Answer me, are you gambling with my company.!” Ya k’arashe yana cakumosa da hannaye biyu yana jijjigasa da iya k’arfinsa.
Izuwa lokacin Zuciyar Aliyu ya gama tafarfasa. D’agowa yai sosai suna fuskantar juna shida mahaifin nasa. Lokaci guda ya murmusa kad’an kafin yace “Oh really Dad. Is that the only problem..?”
Cikin huci mahaifinsa ya katsesa “Ya isheka haka.. Kar ka soma. Kar ka kuskura.”
“It has always been like this Daddy.. Hatred..! Eh tsana.!” Haidar ya katsesa cikin tsananin huci. Lokaci guda yaci Gagaba “Why do you always look down on me Daddy.? Despite all the good things that I’ve done for this company.. The only thing you can see are my mistakes.. Haven’t I done everything you told me to.. Shin bana aikata duk abubuwan da kake umurta na ne. Wanne ne banayi ciki..? Tell me Daddy..!”
Idanunsa suka kuma rinewa zuwa ja, lokaci guda yaci gaba da girgiza Kai yana furta “Of course bazaka ce komai ba.! Because you don’t have the answer.. I’m sorry if I’m not as smart as you Dad.. I’m sorry if I’m not as skillful as you.. And I’m really sorry if I’m a disappointed..!”
Cikin karaji mahaifin nasa ma ya katsesa “Yes that’s what you are.. A disappointment.. I gave you everything so you can be the best.. The best schools, the best trainings.. The best of everything.. I invested so much in you to make sure I groom you well.. Amma duk a banza.. You are nothing but a pathetic loser.”
Idanunsa na kallon k’asa yake furtawa a hankali “That’s enough Daddy. Enough please.!” Yai maganar yana murza tafin hannunsa cikin k’ok’arinsa na danne zuciyarsa dake zillo kaman zai fito daga cikin k’irjinsa sabida b’acin rai.
“I don’t want see your face in my company ever again..! Get out now.. You are fired.” Mahaifinsa ya fad’i yana nuna masa k’ofa.
Kansa na kife k’asa ya saki murmushi. Lokaci guda ya d’ago idanunsa ya sauk’e su tar cikin na mahaifin nasa “And do you actually think I’d give you this satisfaction..?”
Ya kuma murmusawa kafin ya girgiza Kai yace “No Daddy bazan jira ka koreni ba. Kasan me..? I’m sick and tired of trying to impress you all the time.. I’m done being your puppet… I quite.. You don’t need to fire me.. To hell with your damn company… Daddy.!”
Cikin huci mahaifinsa ya dago hannunsa dake rawa zai Kai masa Mari “How dare you talk to me like that..!” Rawan da hannunsa keyi yasa hannun ya gaza sauk’a saman fuskar Haidar. Sai haki yake da kyar irin na Wanda zuciyarsa yakai matuk’a wajen baci.
Haidar ya finciki ID d’insa na Kampanin dake mak’ale jikin suit d’insa yai jifa dashi a wajen kafin yasa kai ya fice a fusace.
A daidai k’ofa ya kusan cin karo da aminin mahaifinsa Alhaji Gimba. Kallo d’aya kurum Haidar yai masa kafin ya watsar yasa kai ya fice cikin sassarfa.
Alhaji Gimba ya k’arasa shigowa cikin ofishin yana duban abokinsa dake zaune saman kujera guda yana sakin hakin b’acin rai.
Cikin kwantar da murya ya soma fad’in “Abinda nake nusar dakai a koda Yaushe yana gab da faruwa Engr.”
Daddy ya d’ago idanunsa masu cikeda ba’cin rai yana dubansa dasu “Kaga Gimba dan Allah kar ka mun maganan yaron nan a nan.. Na riga na Sallama shi..”
Alhaji Gimba ya murmusa irinta manya “Abokina kenan. D’a d’aya tilo ai ya wuce gaban a sallamashi.. Ai Kai Sallama d’ah ba naka bane..”
“I don’t care if he’s my only son.. Baka ganin abinda ya gama min yanzu ne.. Ban haifi dan da zaiga bayana ba..!”
Alhaji Gimba ya kuma murmusawa had’ida girgiza kai kad’an “Yara ko dubu Allah ya baka bazaka ce ka Sallama guda ba dan hannunka baya rub’a ka yanke..”
“Saidai idan bai rub’e d’in ba..” Daddy ya basa amsa a fusace.
Alhaji Gimba ya tsaresa da idanu kafin yace “Wai kasan matsalar ka kuwa..?”
“Ai idan Akan Haidar ne ni da Kai bazamu tab’a samun daidaito ba..” Daddy ya basa amsa Kai tsaye.
Ya d’an girgiza Kai kad’an “You are putting in a computation with your Son, and neither of you want to lose.”
Daddy yai saurin dubansa “Mai kake nufi..?”
“Baka so Aliyu ya taso ya fika k’wazo Shiyasa har kullum kake gani a idanunka shi bai daidai ba.. You refuse to see his potentials. Da zaka basa dama yaron nan ba k’aramin asset bane ma Kampanin ka.. Ka bashi dama koda na k’arshe ne ka k’yalesa yai project d’in nan at least koda na k’arshe kenan kafin kace ka koresa.. Inaga dan yayi failing business plan ba yana nufin yayi failing project d’insa bane.. Ina nufin bridge project dake gabanmu..”
Da tsananin mamaki Daddy ke duban aminin nasa wann karon “Alhaji Gimba, ka kuwa ji abinda kace..? Shin ka mance cewa the company’s future defends on this very project.. Ta ya zan mallaka ma Aliyu ya jagoranta.. Do you want us all to go down..?”
Alhaji Gimba zai kuma magana Daddy ya mik’e yana gyara zaman business suit d’insa “This conversation is taking us to nowhere Alhaji Gimba.. Kamata yai yanzu ka tayani mu san mai zamu sanar da Board members sabida shashashncin d’anah.” Daga haka ficewa yai cikin sassarfa.
Alhaji Gimba ya girgiza Kai kurum kafin ya take masa baya.
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU*
*04*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Tafiya yake cikin mota sautin Marin da mahaifinsa ya shata masa bai daina k’uwa a dodon kunnuwansa ba. Shi ba wai zafin Marin bane ya tsaya masa a rai, Marin nasa da yai gaban employees d’in Kampanin kuma masu aiki under department d’in da yake running shine abinda yafi komai k’ona masa rai. Ya sani shi dai a idanun mahaifinsa baya yin komai daidai sabida haka wann ba sabon abu bane wajensa. Ba a wajen aiki ba a gida ba.. Amma meyasa zai wulak’antasa gaban ma’aikatansa irin haka..? Ya cije labb’an bakinsa kad’an zuciyarsa na kuma k’una. Mahaifinsa ya tsanesa baya k’aunarsa, kai duka iyayen sa guda biyu basa sonsa basa k’aunarsa. Shi zai iya cewa tun tasowarsa baida wani good memories da both mahaifansa wato mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa. Mahaifiyarsa tin tasowarsa cikin tilasta masa da tsaurara masa take wajen ganin yayi abinda zai burge mahaifinsa ya kumayi alfahari dashi. Saidai duk abinda yayi baya burge mahaifin nasa. Kullum cikin nuna masa baiyi daidai yake ba. Kullum cikin kusheshi yake da jifansa da kalamai masu muni. Tsakaninsa da iyayensa akwai wani Katanga da yai ma soyayya shamak’i dashi. Baisan soyayyan iyaye ba. Ya taso ne cikin tilastawa da k’ok’arin burge mutanen da bai tab’a birgewa ba a cewarsa. Yai gajeren tsaki yana mai kokarin kauda tinanin.
A farfajiyan gidan yai parking motarsa jikin wani tapkeken roundabout da furanni suka k’awata tsakiyarsa ga ruwa na kwaranya daga tsakiya. Cikin sassarfa ya nufi cikin gidan har lokacin zuciyarsa bai daina masa zafi ba.
Zaune ya taddata a parlornsa ta mik’e santala santalan fararen k’afafunta da suka sha ado da k’unshi . Sai faman karkad’a k’afafun nata take tana tururi ita kad’ai alamun dai isowarsa take jira.
Baiji mamakin ganinta a parlorn tinda yasan kullum cikin controlling rayuwarsa take.
Baice komai ba sabida ransa da yake a mugun b’ace.
Har yasa Kai zai shige ya sinkayo muryarta “Ai na zaci daga can bazaka dawo nan ba tinda ka zama sallamamme .”
Cak ya tsaya yana saita numfashinsa a hankali “Couldn’t you wait for me first to at least do something wrong kafin ki fara aibatani.” Ya k’arashe daidai sanda mahaifiyarsa ta k’araso gabansa ta tsaya suna fuskantar juna.
Ganin ciwo a fuskarsa ya sanya yanayinta canzawa. Alamun rauni ya bayyana saman fuskarta “Haidar.. Me ya sameka.. Ina ka samo rauni..?” Ta tambaya cikin nuna kulawa.
Murmushi mai ciwo ne saman fuskarsa. Lokaci guda ya girgiza Kai yace “Don’t act like you care Mom. Kin San hakan zai faru. Am I right.?”
Ta d’an tsare fuska “Wani irin magana ne nasan haka zai faru.. Had’arin mota Kai ko me.. Tinda dai nasan baka shiga sabgan mutane balle nace fad’a Kai da wani..”
“Babu ko d’aya Mommy..”
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 64