Share this page
Tai mata. Amma kam ba don Ummul d’in ba da daga Leenah Har Vicky sun kwana ofishin ‘yansanda. Mommy ta bada umarni ma babba cikin ma’aikatan gidan cewa a raka Vicky waje da kayanta ta koreta. Ita kuma Leenah ko me kamanta securities suka kuma bari ta shigo gidan a bakin aikinsu. Harda Anisa akaima Leenah rakiya waje. Sai kallon mamakin cin amanar da Anisa Tai mata take ma Anisar. Anisa ta dubeta bayan Sun rage saura su biyu “Let me call you a cab for you..” D’aga mata hannu Leenah tai alamun dakatarwa “Ki barshi bana buk’ata. You know what Neesa ban tab’a zaton zaki ci amanata irin haka ba. Ta ya zaki d’aura min laifin da banyi ba. You planned the whole thing. Sann kin d’aura min laifi kaman wata sakarai. You know what? I think you’re right. I’m stupid and that’s why I remain loyal to you.” Tana gama fad’in haka tasa kai ta shige kaman zata tashi sama ba tareda ta kuma bi takan Anisa ba. Juya ido Anisa Tai had’ida furzar da huci kafin ta koma cikin gida. Nan ta tadda Mommy ta had’a kaf ma’aikatan gidan tana kafa masu warning. Ta dafa kafad’an Ummul tace “She’s my Son’s wife. I expect each and everyone of you to treat her with absolute respect, Including you Anisa.” Tai maganar tana duban Anisa da shigowarta kenan kafin taci gaba “The same respect da zaku bama D’ana Haidar. Bana so makamancin abinda ya faru yau Ya kuma faruwa. Do I make myself clear.?” Gaba d’aya suka jinjina mata kai hadida amsawa cikeda risinawa ** Bayan Ummul ta koma sashenta tana zaune saman darduma Ida sallarta kenan Anisa ta shigo da murmushi saman fuskarta. Ummul bata nuna mata komai ba dan itama wann sassanyar murmushin wanda a baya Anisa ta d’aukesa shashanci da gidadanci a halin yanzu shakkar wann murmushin take shine dai saman fuskar Ummul. Ta zauna tana tambayarta an sha ruwa lafiya. Ummul ta amsa mata da sakin fuska. Nan Anisa ta soma bata hakurin abinda Leenah Tai tana mai kuma tabbatar mata Lallai Babu hannunta cikin abinda Leenah da Vicky suka k’ulla mata. Murmushi Ummul ta kuma yi “Babu komai Anisa kar ki damu. Suma ban k’ullacesu ba. Daga k’arshe Allah Ya bayyana gaskiya. Ba wayona bane ba kuma dabarata bace. Allah ne Ya dube ni da rahamarsa Ya wanke ni daga k’agen da aka so min. Na kuma gode masa da Ya wanke sunana daga k’agen sata. Ina kuma fata ya shiryi duk masu tunani irin nasu damu baki d’aya.” Anisa ta jinina kai “You are a good person Ummul. You have a clean heart that’s willing to forgive and forget. Yanda kika wanke kanki cikin hikima ya burgeni. I wish zan zama kaman ke.” Ummul ta murmusa “Duk wanda ya dogara ga Allah Allah ya isar masa. Kuma duk wanda yaji tsoron Allah Allah zai samar masa mafita. Ba yin kaina bane Allah yakan wanke bayinsa da akai masu k’age ba tareda sun aikata laifin ba. Kaman yanda Ya wanke Ummuna Aisha (RA) daga k’agen da azzalumai suka mata. Kaman yanda Ya wanke Annabi Yusuf (AS) daga k’agen da aka masa. Kaman yanda Ya wanke bayinsa muminai da dama daga k’agen da aka masu. Kaman haka yanke wanke bayinsa da basuda hakki. Na gode masa da ya wanke ni daga k’agen da aka min ba tareda hakki ba. Amma ni Ummulkhair banida wani wayo. Saidai Inaso mutane irinki da Leenah su fahimci English is just a language and not a means to measure one’s intelligence or education. Snn duk wani wayewar da yai karo da koyarwar addininmu da d’abi’u da kyawawan al’adunmu ba sunansa wayewa ba.” Tai maganar murmushi saman fuskarta. Baki sake Anisa ke kallonta “So you can speak English.?” Ummul ta murmusa “Ba sosai ba abinki da Wanda taje makaranta na gwabnati.” A hankali Anisa ke jinjina kai “Na yarda da duk abubuwan da kika ce. A yau kin kuma tabbatar min da haka. “ Ta kamo hannayen Ummul “Mommy tayi zaton ni zan koya miki abubuwa musamman zamantakewan rayuwar civilized world. But it turned out ni ce wacce ke koyo wajenki. Yau na raina duk wani exposure na Ummul.” Ummul ta girgiza kai “A kullum ko wani shafi na rayuwar mu darasi yakan bude mana dan mu koya. Kullum cikin koyo muke a duniyar nan. Kaman yanda muke had’uwa da mutane iri daban daban.” Ta d’an murmusa “Nima ina koyo daga gareki Anisa.” Shiru Anisa Tai sai kuma ta saki murmushi da yafi kama da yak’e. Tin daga wann rana Ummul ta samu sanyin abubuwan da Anisa ke mata. Sai ta koma kaman tana shakkan Ummul d’in koda bata nuna a fili ba. A kwanakin da alama Anisa ta maida makaman yak’inta. ** Kano… Batai k’asa a gwiwa ba dukda fargabn abinda ka iya zuwa yazo ta nufi gidan Hajiya Asshe. Juyin duniya Umma tayi amma masu gadi sun hanata shiga sabida dokan da Asshen ta basu tin kwanakin baya. Asshe na kitchen tana had’a ma maigidanta abinci kasancewar ranar yake dawowa daga tafiya kuma gidanta yake. Mai gadi yai Sallama ya sanar da zuwan Umma wacce babu yanda basuyi ba amma tak’i barin bakin gate din tace sai ta gana da Hajiyar. Zuciyar Asshe ya tsinke yanzu idan matar nan ta tada mata hargitsi a k’ofan gida har mijinta ya iso ya tadda wann al’amari mai zata ce masa. Oh! Ita kam dai ta d’ebo ruwan dafa kanta. Wann wasu irin ahali ta kwaso masu ne wai ita Asshe. Bata gama da fitinan Dije ba ga Suwaiba da tai tunanin ta ajeta yanda ya kamaceta yanzu ta dawo. Toh uban mai ta dawo zata mata.? Fuuu ta nufo gate tana huci dan wllhi bazata bari d’aya daga cikin watsatsun matan nan su mata sanadin aurenta da take lallab’awa ba. Tana fitowa ta shiga janyo Umma tana fad’in yau hukuma ce zasu mata iyaka da ita muddin bata bar mata k’ofan gida ba. Umma bata tafi ba bata fasa rok’on Asshe tana fad’in ta dubi girman Allah ta saurareta. Hilal daga sashensa yake jiyo haniya yak’i k’arewa daga gate. Babu shiri ya bar abinda yake ya nufo gate d’in. SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!* *29* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* Asshe taci gaba da janyo Umma tana fad’in kodai ta bar mata k’ofar gida ta mik’a mata ma ‘yansandan dan ta gaji da fitinan fitinannun mata Irinsu. Wanda tin had’uwar ta dasu Masifan yau daban na gobe daban. Umma taci gaba da girgiza kai “Idan kina ma Allah ki tsaya ki saurareni Hajiya Asshe.” “Na saurareki na saurari mi inyi.? ‘Yarki ce nace Miki akwai wa’adin da na d’ibar Wanda zan dawo da ita gareki. Amma a halin yanzu ni Asshe banida wani sauran alak’a dake da sauran zuri’arku. Na gode ma Allah da yasa auren Ummul ba mai d’orewa bane. Mi za’ayi da zuri’arku dangin masifa dangin mayu dangin matsafa.. Zo ki wuce.. Idan kika kara minti d’aya k’ofar gidan nan ki kwana ofishin ‘yansandan” Ta k’arashe tana hankad’a Umma da iyaka k’arfinta Wanda saida ta kaita k’asa. Daidai nan Hilal Ya fito ya taddasu. Ya isa da sauri yana ma Umma sannu had’ida tambayar bataji ciwo ba. Umma ta d’ago tana girgiza masa kai alamun a’a. Da tsananin mamaki yake duban mahaifiyarsa “Ammi what’s the meaning of this.? Kan wani dalili zaki aikata abu makamancin haka..? Mai yayi zafi..? Wai meke faruwa ne ma.?”Ya k’arashe damuwa saman fuskarsa. Asshe na huci take furta “Babu ruwanka Hilal. Ba abinda ya had’aka da Matar nan zo ka shige gida.” Hilal ya girgiza kai “Ammi matar nan sirkar Haidar ce.. ‘Yarta Haidar ke aure.. We are practically family now.” Bai kai aya ba Asshe ta k’araso a guje ta toshe bakinsa “Allah tsari gatari da saran shuka. Allah mana tsari da had’a iri da wann zuri’a.. Shige gida kar na sake jin bakinka.” Ta k’arshe tana nuna masa k’ofa. Girgiza kai Hilal Ya kumayi “Ammi I’m sorry. Bazan iya barin Umma a nan ba har sai na san abinda ke faruwa.” Baki sake Asshe ke dubansa “Umma.?” Ta nanata a fili. “Umma ka kirata.? Toh sunanta Suwaiba. Kanwar uwarka ko na ubansa da zaka kirata da Umma.?. Ka sake kiran mahaukaciyar nan Umma sai naci maka. Zo ka shige kafin Abbanka Ya k’araso.” Ta k’arashe tana janyo Hilal yana tirjewa haka Har ta shigar dashi cikin gidan ta janyo k’ofa tana fad’in masu gadi kar su bari Suwaiba ta zo koda kusan gate din ne. Mamaki Ya cika Hilal. Shi Ya kasa gane wann irin al’amari ne wann da kuma abindake tsakanin mahaifiyarsa da da Umma. After some hrs da faruwan hakan. Tsaye yai bayan mahaifiyar tasa sanda take lek’e daga window ko zata hango Umma. Cikin zuciyarta tana addu’an Allah yasa mayyar ta tafi dan bata fata mijinta ya dawo ya tadda Suwaiba kofan gidan balle asirinta ya tonu. Ya girgiza kai kad’an yana kuma takowa kusan mahaifiyarsa. Aiko a firgice ta juyo tamkar maras gaskiya. Ta dafe k’irjinta tana fad’in “Haba Hilal, halin Anisa na lab’e ka koya kaima. K’iris zuciyata bata buga ba.” Ta k’arashe har lokacin hannunta dafe da k’irji. Sai kuma ta canza maganan da fad’in “Lek’e nake naga ko Abban naka Ya iso.. Gashi dai da alama har yanzu bai iso ba.. Lallai da alama zai dare.” Ta kuma duban Hilal tana tsimewa “Waima mai ya shigo da Kai nan ne. Mai kake nema.?” “Dama na shigo ne na fad’a Miki zan d’an kwanta kafin la’asar tinda naga har yanzu Abban bai iso ba.” Ta jinjina Kai tana dubansa “Idan ya iso zan tada Kai.” Ta fad’i tana nufan k’ofa yayinda Hilal ya take mata baya. * Fitowan Hilal sallar la’asar bayan an Ida sallah a masallaci a hanyar sa ta dawowa gida ya hangi Umma tana sallah jikin wani gini dake manne da karantar gidansu. Kasancewar akwai interlocks wajen. Mamaki ya cika Hilal. Ikon Allah yanzu dama ashe matar nan bata tafi ba. Lallai ba k’aramin Abu ya zaunar da ita ba. Ya k’araso gefenta daga can ya tsuguna kan k’afafunsa har ta Ida addu’arta. Hilal ya tayata shafawa. “Umma.” Ya ambaci sunanta daga nan yanda yake tsugune kaman dai yanda yaji Khulsum na kiranta. Umma ta d’ago ta dubesa sai ta sakar masa murmushi “Hilal d’an albarka.” Ta fad’i tana dubansa dan bazata tab’a mance alkhairan yaron ba koda kuwa ita mahaifiyarsa suna buga dabi. Kaman yanda nata yaran basuyi halinta ba haka zalika Hilal baiyi halin mahaifiyarsa ba a cewarta. Hilal ya gaisheta kafin ya k’arada “Umma mai kikeyi a nan.? Mai ya zaunar dake nan.?” Ya dan numfasa kiyi hak’uri da tambayar da zan Miki “Shin akwai wani matsala ne tsakaninki da mahaifiyata.? Meke faruwa tsakanin ku biyun.?” Umma ta girgiza Kai kad’an “Babu komai Hilal. Amma Kai hakuri bazan bar k’ofar gidan nan ba har sai mahaifiyarka ta saurareni.” Hilal ya zuba ma sarautar Allah ido yana tuno yanda sukai da Amminsa. Ya d’an kuma girgiza Kai “Amma.. Kiyi hak’uri da tambayarta da zan Miki.. Wani abu ne kike nema wajen mahaifiyata.? Ki sanar dani dan Allah idan wani Abu ne da zan iya taimakawa.” Umma ta kuma murmusawa “A’a Hilal. K’arshen abinda zanyi shine na saka ka cikin matsalolinmu. Kai d’in kanada zuciya mai kyau. Ina rok’on Allah yasa D’anuwanka dake auren Ummul d’ina ya zama mai kyaun hali da d’abi’u irin naka..” Ta k’arashe cikin rawar murya irin na mai kuka hawaye na gangaro mata dan a koda yaushe cikin tunanin Ummul d’inta take da halinda zata iya kasancewa ciki. A gaggauce tai k’ok’arin goge fuskarta kafin ta kuma duban Hilal tace “Mahaifiyarka nake son magana da, sabida wajenta nazo. Domin dani da mahaifiyarka munada alak’a mai kyau.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. Mamaki ya kuma cika Hilal. Kansa ya kuma k’ullewa. Tabbas wad’ann mata wato Amminsa da Umma al’amarinsu abin dubawa ne sann yanada rikitarwa. A b’angare guda mahaifiyarsa tana ikirarin datse alak’a da Umma da ahalinta. A b’angaren Umma tana fad’in itada mahaifiyarsa sunada alak’a mai kyau. Shin na waye zai d’auka cikin su biyun.? Juyin duniya Hilal yayi Umma ta hakura ta koma gida amma fir fir tak’i ta kafe lallai lallai sai Asshe ta saurareta. Ganin yamma nayi yasa Hilal d’aukan mota ya fice daga gidan. Dan yasan watak’ila maganarta kawai Umma zata saurara ta amince ta bar k’ofar gidansu. A bakin ward din ya hangeta tana k’ok’arin shiga. Sauri sauri ya k’arasa ya cimmata. Kaman Wanda aka jefo shi haka Khulsum taga Hilal gabanta. Da mamaki take dubansa. “It’s a good thing that I found you here. You need to come with me.” Abinda kawai Hilal yace kenan. Khulsum ta girgiza Kai cikeda mamaki “Malam lafiya.?” Yai gajeren tsaki “Wai ke ko yaushe haka kike ne. Abun fad’a baya Miki kad’an ne.?” Ya kuma girgiza Kai “I need you to come with me right away. And please you alone. You don’t need to inform that aunt of yours… She might stop you.” Dan bai mance ba kwanakin can da suka shige ita ce ta hana Khulsum bin Umma Akan idonsa. Daga haka sa Kai yai ya soma tafiya yana fad’in tai sauri ba lokaci. Takaici ya cika Khulsum, mai wann D’an rainin hankalin ya d’auketa da zaice tazo ta bisa. Ina ma zata bisa.? Mai ya maidata.? Ganin ya soma tafiya ya nufi mota yasata bin bayansa da sauri tana fad’in “Kai Malam.. D’an dakata.? Kana tunanin kai waye.? Mai ka d’auke ni.. Mai ka maidani da zaka tako har yanda nake kace nazo na bika kuma kar na sanar da Innata.. Ce maka akai..” Bata Kai aya ba Hilal ya kaikaito yana dubanta cikeda takaicin kuskuren fahimtar da tai masa “Hey cut it out will you.!” Ya katseta da fad’in haka kafin yaci gaba “Seriously, is that what you think of me.?” Har lokacin da mamaki yake dubanta kafin yaci gaba “If that’s what I wanted I’d have gone straight to a hotel or club, and not a hospital.” Ya dan girgiza Kai “Look, ni ba irin wad’ann mutanen bane. And I’m not kidnapping you.. Idan na zo nan kawai nazo ne sabida mahaifiyarki dake zaune k’ofar gidanmu through out the day. Idan Ammi na ta fito ta taddata wajen it would be a disaster. Idan akwai girman mahaifiyarki da kike gani kike ji a cikin Zuciyar ki koda kad’an ne zaki taho tare Dani dan na tabbata ke zata iya sauraronki.” Ya k’arashe yana bud’e motar. Jikin Khulsum yai sanyi ta dubesa da mamaki “Umma ce take k’ofar gidanku.?” Hilal ya zuba mata ido yana dubanta. Baice komai ba sai tada motar da yai “Zakije ne ko nai tafiyata.?” Ta hareresa sai kuma tai still a wajen kaman mai tunani. Shin ta sanar da Inna Dije ne.? Toh amma idan ta sanar da Innah Dije wani wutan zata kunna tinda tasan Ummanta da Inna Dije basa jituwa. Sann Inna Dije zata iya hanata zuwa. Tana tsaka da tunanin taji sautin horn ya cika mata kunne alamun Hilal na jiran decision dinta. Harara ta b’alla masa kafin ta bud’e marfin motar ta shige. Ya soma driving babu mai ce da kowa komai cikin su biyun har suka iso k’ofar gidansu Hilal. Can Khulsum ta hangi Umma rakub’e jikin gini tana lek’en gate din gidansu Hilal kaman wata mabaraciya. Sosai abin ya mata ciwo ganin mahaifiyarta a haka. Hilal na Ida parking ta fito ta nufi Umma. “Umma.!” Khulsum tace daga nan yanda take tsaye kusan Umma. Umma ta d’ago tana dubanta. Khulsum tai saurin k’arasowa ta duk’a gaban Umma “Umma Mai kike a nan. Dan Allah mai kike haka a nan.? Umma wann fah zubda mutunci ne. Dan Allah ki tashi ki bar k’ofar gidan nan. Duba fah kiga mutane masu shigewa suna kallonki.. Umma dan Allah ki tashi haka nan.” Hawaye Umma ta soma tana girgiza Kai “A’a Khulsum bani tafiya sai Hajiya Asshe ta sauraren.” Khulsum ta juya ta dubi Hilal dake can jikin motarsa yana tsaye. Shid’in ma su yake duba. Ko ba’a ce ba damuwan halinda Umma ke ciki ne saman fuskarsa dukda baya iya sauraron mai uwa da ‘yar ke cewa. Khulsum ta maidoda dubanta ga mahaifiyarta “Umma matar nan tareda ita ina nufin keda ita kuka k’ulla auren ‘Yaruwata. Bansan dalilinta na juya Miki baya ba. Bansan meye ku biyun kuka bisne ba. Bansan meye a tsakaninku ba. Amma ke mahaifiyata ce kuma bazan so ki walak’anta ba. Dan Allah Umma ko mai kike nema wajen matar nan kiyi hak’uri ki bar k’ofar gidan nan.” Umma ta kuma girgiza Kai tana hawaye “Khulsum idan na tafi mai zanje nace da Tani. Na mata alk’awarin zan nemo kud’ad’en belinta. A nan ne kawai nake da yak’inin zan samu kud’in fiddo Tani Khulsum.” Baki sake Khulsum ke dubanta. Da mamaki tace “Umma wai dama kan kud’ad’en belin Mama kike nan.?” Umma ta jinjina mata Kai alamun eh. Shiru Khulsum tai na d’an lokaci kafin ta dubi mahaifiyar tata tace “Umma kece zakiyi belin Mama. Wai Mama Tani dai da ta saida shagon Abba.?” Umma ta kuma jinjina mata Kai “Dukkanmu masu kuskure ne Khulsum. Tani ta salwantar da dukiyar Malam ni kuma na salwantar da rayuwar ‘yarsa. Cikin mu biyun idan akwai Wanda tafi girman laifi toh ni ce Khulsum. Ni yafi cancanta na tafi gidan kasu ba Tani ba. Idan har zan zuba ido ni ina shak’an iskan ‘yanci yayinda Tani ke gark’ame kurkuku bana tsammanin nayi ma kaina adalci. Sann bana jin ‘yancin iskan da nake shak’a a mak’oshi na. Tani ta tuba Khulsum. Dukanmu mun gane kurakurenmu. A halin yanzu bamuda wani buri da ya wuce mu koma ga mijinmu mu kula dashi mu masa jinya mu samu aljannarmu.” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka. Jikin Khulsum yai sanyi. Tasan mahaifiyarta tanada zuciya mai kyau Wanda da yawan mutane suna amfani da wann damar su shashashantar da ita. Kaman dai yanda takeda kokonto Akan tuban Mama Tani. Dan tasan kad’anda aikin Mama ne ta shashantar da mahaifiyarta ta samu ta fito daga prison. Muryar Umma ta kuma sinkayo sanda ta tallafo fuskar Khulsum d’in cikin zuban hawaye take fad’in “Nayi kewarku Khulsum daga ke har ‘yaruwarki. Ina zaman kad’aici a gidan.. Babu ke.. Babu Ummulkhair.. Babu mahaifinku.. Tani ma bata nan.” Tai shiru tana tinanin daga ita sai su Azeema Wanda suka maidata wofi cikin gidan barikinsu kawai suke bugawa. Su fita sanda suka so su dawo sanda suka so. Idan tai masu abincin da bai musu ba su mata tatas. Har wankin kaya Badia ke sakata. A cewarsu idan batai ba zata fice ta bar masu gidan uba tinda gidan na ubansu ne. Ganin tayi shiru ta tsunduma tunani yasa Khulsum kamo hannayenta “Umma.” Ta kirawo sunan Umman a hankali. Umma ta d’ago tana duban Khulsum. “Zaman kad’aici yasa kike so ki fiddo Mama Tani.?” Shiru Umma bata ce komai ba sai hawaye dake kuma gangaro mata. Khulsum ta janyo mahaifiyarta ta rungume sai dukansu biyun suka fashe da kuka. Cikin muryar kuka Khulsum ke fad’in “Umma kiyi hak’uri ki koma ki zauna. Nayi ma Abba alk’awari bazan sake barin kusansa ba bayan abinda ya faru.” Cikin rawar murya taci gaba da fad’in “Umma ba zama da Inna Dije na zab’a ba. A’a zama da Abba na na zab’a. Inna Dije bazata kuma barinki kije kusan mahaifina ba Umma. Zanfi kowa so naga ahalinmu ya kuma cika amma a halin yanzu Abu ne mai matuk’ar wuya Umma. Ki koma kici gaba da addua ma Abba har Allah ya bashi lafiya iyakacin soyayyar da zaki nuna masa kenan a halin yanzu. Da sannu Allah zai duba Zuciyar Wanda yai tuba na gaskiya ya yaye masa matsalarsa kinji Umma na.” Ta k’arashe cikin rawar murya. Umma ta shiga jinjina mata Kai a hankali har lokacin tana hawaye. Cikin zuciyarta kaw cewa take ita kanta bazata so ta bar Malam k’ark’ashin kulawar Dije kawai ba. Gwara ace Khulsum d’in na tare dasu. Zatai hak’uri kuma zataci gaba da addua kaman yanda ‘yar nata ta shawarceta. Hannunta Khulsum ta kamo suka nufo Motan Hilal. Hilal na ganin su ya isa ya bud’e back seat Khulsum suka shige tareda Umma hannayensu rik’e cikin na juna suna Jin d’umin juna da suka jima basu samu hakan ba. Ta mirror Hilal yake dubansu yanda suka shige jikin juna. Kan Khulsum na kwance gefen kafad’an mahaifiyarta yayinda Umma ta rik’e hannun Khulsum d’in k’am cikin nata tamkar kar wani Abu ya rabasu. Murmushi ne yaji out of nowhere na zuwa fuskarsa. Shi a duniyar sa duk yanda yaga shak’uwa da soyayya mai tsafta tsakanin iyaye da ‘ya’yansu ba kowa yake hasashowa ba face D’an Uwansa Haidar. A kullum addu’arsa kenan yaga irin wann bond d’in tsakanin Haidar da iyayensa. Har gida Hilal ya kawo Umma. Khulsum ta fito taima Umma rakiya zuwa cikin gida ta kuma tausarta had’ida kwantar mata da hankali amma fah dukda haka bata ji cikin zuciyarta zata iya baro Abba ta dawo ta zauna da Umma musamman idan ta tuna abinda matan Abban nata suka masa. Tana fitowa ga mamakinta ta tadda Hilal na nan na jiranta. Daga can yanda take tsaye ya zuba mata “Rankidad’e jirana ake gida muje mana.” Ta had’e fuska sosai “Toh ce maka nai ka jirani. Kai tafiyarka mana.” Tace tana canza hanya. Furzar da huci yai kad’an ga wayarsa da ta kasa shiru sakamakon kira da Mahaifiyarsa ke jero masa. Yasan bazai wuce Abbansa ne ya iso ba. Baisan mai zaice mata ba dan shi dai bai iya k’arya ba amma muddin ya sanar da ita Umma ya kawo gida ya taro match ne tsakaninsa da Ammi. Ya k’arasa da mota gaban Khulsum yai rolling glass “Zaki shiga ne ko sai na fito na shigar dake da k’arfi.? Be thankful, albarkacin Umma kikace idan na maidake.alk’awari na daukar mata zan maidaki yanda na d’aukoki.” Yace a mugun tsare. Khulsum ta dubesa dan yanzu gadararsa da k’arfin halinsa ya daina bata mamaki. Bata son dogon hira dashi dan kaf zuri’arsu haushi suke bata. Sann ga magarib ya k’arato hasalima batasan yanda za’ai ta koma ba tinda ba kud’in abun hawa wajenta. Ta kauda fuska gefe cikeda takaici zata bude backseat ya saka motar a lock. Fitowa yai daga mazauninsa yana fadin “You must be kidding. D’azunma albarkacin Umma kikaci na barki kika zauna baya.” Ya bud’e mata front seat “Shige muje.” Ta hararesa kafin ta shige. Tana shiga ya sakar mata murmushi had’Ida kashe mata ido kafin ya zaga ya shige. Takaici ya kuma cika Khulsum. Suna tafe babu mai cewa komai. Khulsum ta saci kallonsa. Yanzu wai godiya ya kamata ta masa ko hakurin kuskuren fahimtar da tai masa zata basa.? Kai ina ita dai bazata basa hakuri ba dan bataga laifin da tai masa ba. Ta saci kallonsa suka had’a ido. Sai ta wayance dan bata so ya fahimci tana dubansa. tai kaman bata kalli b’angaren da yake ba. Saida tai gyaran murya da kyar kafin tace “Idan kana jira na baka hak’uri ne kan abinda ya faru ni dai bazan baka ba. Abinda Kai kuma shima Kai ka saka kanka shima bazan maka godiya ba.” Ta k’arashe tana kauda fuska. Hilal ya murmusa “Guilty conscience.? Kar ki damu na yafe miki.” Yace idonsa naga kwalta. Bata amsa shi ba sai kuma tace “Toh mai za’a tsammata daga wanda yake sallah babu alwala.?” Ya kuma murmusawa “Allah yasa dai ba kece mai karb’an tuba ba balle ki k’i karb’an nawa tuban.” Ta kuma hararsa “Ka fad’a ma wann D’anuwan naka mai sallah babu alwala ‘Yaruwata musulma ce bazata zauna dashi ba. Ni Khulsum sai na datse wann auren.” Hilal ya jinjina Kai “Why not ask your sister to tell him. After all su biyun sunfi kusa a halin yanzu.” Ya d’an dubeta a kaikaice kafin ya k’ara “And remember they say, Wanda ya shiga tsakanin mata da miji shi zaiji kunya.” Ta hareresa musamman da taga murmushin dake bisa fuskarsa. Yana ida parking tasa hannu ta bude marfin motar a fizge ta fice. Ko kallon yanda yake bataiba balle tai masa sallama balle ya samu arzikin godiya. Bayanta yabi da kallo yana murmushi. Cikin zuciyarsa yake jin yanzu yanada k’wakk’waran dalilin da zaisa ya k’ara delaying lokacin komawarsa makaranta koda hutunsa ya k’are. Bazai tafi ba har sai ya tabbata baida wani pending matters. Saida ta b’ace ma ganinsa kafin yaja motarsa ya bar wajen. ** Cuba… Waya manne b’angaren kunnensa na dama.

Chapter 25 of 64