Hisham “I’m sorry Haidar.. It wasn’t my intention to break your photo..” Sai yai aya har lokacin Haidar bai tankasa ba.
Hisham ya zira hannayensa cikin aljihun jeans d’insa “Koda yake dan na breaking hotonku bazai zama matsala ba.. After all, kayi breaking auren naku da kanka.”
Haidar ya had’iyi abinda ya tok’are masa mak’oshi. Ya mik’e tsaye ba tareda ya dubi Hisham ba. Yayinda Hisham yaci gaba da sakin muguwar murmushinsa silently dan ya tabbata ya tarwatsa Zuciyar Haidar da kalamansa kaman yanda ya tarwatsa hoton aurensu. Ga mamakin sa murmushi yaga Haidar ya sakar masa. Ya tako zuwa gaban Hisham d’in k’adan. Saida dak’ik’a ya gauta Haidar na duban Hisham na sakin murmushi kafin yace “You can do your worse Hisham. Amma bazaka tab’a iya raba tsakanina da Khairy ba.. Kasan dalili..?” Sai ya nuna masa fuskar wayarsa dan D’ansa ne Akan fuskar wayar.
“Wann kawai ya isheka amsa. Kuma ka yarda dani.. Zan kawo k’arshen karyarka da fuska biyunka.. Sai nayi unmasking dinka.!” Yai maganar yana jinjina Kansa alamun tabbatar da kalamansa kafin yasa kai ya shige.
Hisham ya bisa da kallo yana shafa hab’arsa muguwar murmushinsa saman fuskarsa.
Washe gari da safe Haidar da ya fito cikin shirin fita Office kaman yanda Daddy ya buk’aci yaran nasa da su shirya da wuri sabida gabatarwa na musamman da zai musu a company nan ya iske iyayensa saman dining table. Ya k’araso ya gaishesu Mommy tace ya zauna suyi breakfast.. Ba musu Haidar ya zauna.. Zai soma serving Kansa Daddy yace ya jira D’anuwansa ya shigo. It would be rude a fara breakfast ba tareda an jirasa ba musamman da yake bak’o ne shi a gidan.
Da mamaki Haidar ya dubi Daddy sai ya aje serving spoon din cikin sanyin jiki. Mommy ta dubi D’anta cikeda tausayawa tasan an fara kaisa mak’ura da al’amarin sabon D’an mahaifinsa. Hannunta ta d’aura saman nasa cikin k’ok’arin calming d’insa. Sai ya murmusa yana girgiza mata Kai alamun ba komai she shouldn’t worry.
Time Haidar ya duba saman agogonsa dake daure hannunsa na hagu. Ya dan furzar da huci kad’an.. Yana tapping yatsunsa a hankali saman table d’in.. Ba jimawa gogan ya shigo cikin shirinsa tsaf irin shirin da bai tab’a irinsa a baya ba idan zai tafi office. Da ka gansa kaga D’an manya. Ga wata expensive suit da ya saka da wata tsadaddiyar cover shoe bak’a sai shining take. Ga k’amshin turaren TomFord dake tashi jikinsa. Irin dai turaren Haidar yau shi ya saka. Haidar ya kauda fuska gefe yana sakin murmushin takaici. Ba shakka wann banzan competing yake dashi a halin yanzu.
Daddy ya mik’e da murmushi yana tarban D’ansa sanda Hisham d’in ya duka yana gaida Daddy cikeda ladabi. Daddy ya kamosa ya mik’arsa tsaye yana tambayarsa how was his night. Hisham ya amsa yana wani sadda Kai k’asa yawa mutumin arziki. Haidar ya kuma yin murmushin takaici yana kauda fuska. Hisham ya k’araso ya duk’a yana gaida Mommy.. Ta amsa masa da sakin fuska tana fad’in bismillah ya zauna suyi breakfast.
Hisham ya zauna a kujera mai kallon na Haidar murmushi saman fuskarsa yake fad’in “Good morning bro… I hope I didn’t keep you waiting.?”
Mik’ewa Haidar yai yana fad’in “I’ll.. Go ahead..”
Mommy ta dakatar dashi “Haidar ka tsaya kaci abinci mana.. You can’t go to work with an empty stomach.”
Haidar ya dan girgiza Kai “Kar ki damu Mommy zanci a Office.”
Daddy yace “Koma ka zauna Haidar..”
Ba don yaso ba ya komo wajen zamansa.
Hisham ya murmusa yana duban Haidar sanda yake cakalan chips da fork “You shouldn’t be skipping your breakfast Brother.. Because, they say breakfast is the most important meal of the day… Haka ne Daddy.?”
Daddy ya jinjina Kai da murmushi saman fuskarsa “K’warai haka ne. Gwara ka dinga fad’a ma wann D’auwan naka dan bai son abinci tuntuni.”
Hisham ya murmusa yace “K’warai ni zan bada shaidan hakan.. Dan baida abokin da ya fini..”
Banda murza fork and knife din dake hannunsa ba abinda Haidar keyi sabida takaicin da ya turnikesa. Bai tunanin zai iya hakurin zama waje d’aya da mayaudari irin Hisham. Washe gari ma Daddy yasa yaran nasa su shirya cikin manyan kaya wann karon. Cikin su biyun babu Wanda yasan nufin Daddy. Bai kuma sanar dasu ina suka nufa ba.. A haka dai suka d’auki hanyar Airport cikin shiga ta manyan kaya.
Basu zarce ko ina ba sai birnin Maidguri yanda sukai rakiya wa mahaifin nasu ya amso aurensa da tsohuwar matarsa a karo na biyu. Saidai amarya bata biyosu Abuja ba ta buk’aci ango ya bari sai daga baya ta tare dan abubuwan komai ya faru ne cikin sauri. Ga dangi da bata gama zagawa ba. Taso Hisham Ya zauna nan Maiduguri tareda ita amma sai Daddy ya nuna yana buk’atan Hisham d’in can Abuja kusansa.
Farin ciki wajen Hisham baya misaltuwa. Shidai Haidar bai um bai um um.. Sam baijin haushin matar amma yasan D’anta bak’in k’umurcin maciji ne. Snn koda suka dawo gida ya jaddada wa mahaifiyarsa tana tareda goyon bayansa duk abinda zai faru. Mommy ce ta kwantar masa hankali da fad’in babu abinda zai faru da izinin Allah sai alkhairi domin Auren da mahaifinsa yai ma zabinta ne.
Bayan ficewar Haidar daga wajen Mommy Daddy ya shigo. Duban Mommy yai da murmushi saman fuskarsa. Zatai magana yai saurin daura d’an yatsarsa saman lips dinta. Yai gyaran murya kad’an sanda ya rik’o hannayenta cikin nasa “You don’t have to say a word Kwaise. Yau d’in ni zanyi maganar.”
Murmushi ne saman fuskokinsu suna duban juna hannayensu cikin na juna. Daddy ya dan sassauta murya kafin yace “Do you know that.. you are the pillar of this family..”
Murmushi Mommy tai had’ida girgiza Kai kad’an “Kai Engr.. Kar fah ka mance ni fah matar Engr ce so nasan matsayi da amfanin pillar a gini.. I might be the scaffolding that keeps the pillar upright.. But you are the pillar my Engr.”
Daddy yai murmushi mai bayyana hakwara kad’an kafin yace “Lallai na yarda ke matar magini ce. Amma a wann ahalin you are both the scaffolding and the pillar Kwaise..
Behind every successful man is a woman. Do you think I'd be Aliyu Maitama that I am today if it weren't for you..?” Yaci gaba da murmushi yana dubanta “Hak’ik’a Allah Ya gama min duk wani gata da Ya bani mace ‘yar aljannah irinki. Thank you for everything Kwaise.. Allah ya miki albarka..”
Ta sadda idonta kad’an tana mai amsawa da Ameen mijina.
**
Washe gari sassafe a station ya musu. Idan kaga Anisa sai ta baka tausayi. Ta fice a hayyacinta ta shiga makarantar ta natsu. Ga mahaifinta yace ba ruwansa ya cire hannunsa akanta sann idan Asshe ma ta taka k’afa taje yanda Anisa take a bakin Aurenta. Asshe tanaji tana gani an mata farrak’u da ‘yarta kaman yanda tai ma Umma da ‘yarta Ummulkhair a baya. Tabbas sharri d’an aike ne. Duk yanda ka tura shi zai dawo gareka.
Hisham dai Ya gama k’ulle Anisa cikin case din ko ta ina. Sam bai bar wani k’ofa da zargi zai hau kansa ba.
K’arshe Daddy da Haidar suka buk’aci belin Anisa Daddy ya bada umarni da a rufe case din gaba d’aya .. Saidai ana tsaka da processing release papers d’in Anisa sukaji sauti daga bayansu na fad’in “Bada garaje ba. Babu yanda wann macuciyar zataje har sai ta biya kisan yar mu da tai.!”
A tare Daddy da Haidar harma Hisham suka waigo suna duban mutanen da suka shigo station d’in.
Daddy ya girgiza kai yana dubansu cikin rashin fahimta “Su waye ku.?”
Mutumin yace “Mune iyayen Dareen da ‘yarku ta kashe.!”
Sabon tashin hankali da ba’a saka masa rana.
Ga dai iyayen Dareen Sun bayyana Sun kuma d’au alwashin sai an karb’ar ma ‘yarsu hakkin kasheta da akai wanda hakan ke nufin ba ranar fitar Anisa daga gidan kasu babu kuma ranar rufe case. Sann ba ranar yanke hukuncin shari’a har sai angano gawan Dareen.
Anisa ta amsa laifin ta na cewa ita ta bige Dareen da mota sabida soyayyar da take ma Haidar dan ga shaida an samu a gidan Aliyu Maitama motar da Anisa tai amfani dashi ta bige Dareen.
A halin yanzu case ake na kisan Dareen Wanda duk wani evidence yake pointing zuwa ga Anisa. Itace prime suspect. Ita keda babban dalilin kashe Dareen sabida son da take ma Haidar kaman yanda ta tassama kashe Ummulkhair.
Allah sarki Anisa dole ta baka tausayi dan ba wanda zai fiddata daga cikin wann masifa da take ciki sai Allah. Ta saduda ta koma ga Ubangiji. Shi kawai take ambata da ya kawo mata d’auki.
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*59*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Safiyar ranar Alhamis Haidar ya fito cikin shirin fita Office. Can wajen motoci ya hangi Hisham na zab’en motar da zai d’ale. Saida ya hangi fitowar Haidar kafin yai murmushi ya isa jikin farar SUV da Haidar ke hawa time to time ya dafa motar yana duban Haidar murmushin nan nasa saman fuskarsa “How about this ride.. Baka tunanin zai dace Dani..? Dear brother..!”
Haidar baice dashi komai ba ya nufi motarsa. Har ya isa jikin motar ya d’ago yana duban Hisham da murmushi saman fuskarsa “Bazaka tab’a zama kaman Haidar Maitama ba, no matter how hard you try.. Kasan dalili..?” Ya tsare Hisham sosai da ido “You are nothing like me.!” Yana ida fad’in haka ya saki murmushi kad’an kafin ya juya zai shige motarsa. Sai kuma ya juyo kaman Wanda ya tuna wani abu. Ya dubi Hisham yace “Make sure you don’t lose track of time.. You don’t want your Boss to arrive first before you.!” Ya k’arashe yana nuni da agogon dake daure hannunsa. Lokaci guda yasa kai ya shige mota yaja motar ya fice daga gidan.
Takaici ya cika Hisham. Ya bigi tayar motar da k’afarsa guda tsanar Haidar na kuma ruruwa cikin zuciyarsa musamman idan ya tuna yana sama dashi wajen aiki. Da takaicin Haidar ya nufi Company. Yana tafe hanya Daddy ya kirasa ya sanar dashi ya zama in charge bazai Sami shigowa company ba ranar. Haba nan fah kan Hisham ya kuma fashewa yana jinsa sama da Haidar.. Alla alla yake ya isa Company ya nuna ma Haidar kasawarsa tinda gashi Daddy shi ya k’ira ya bar masa ragamar komai a hannunsa. Yau sai ya wulak’anta Haidar ya k’ask’antar dashi a company. Allah yasa ya Riga Haidar isa ya wulak’anta sa.
Haidar kaw bai isa Company ba Daddy ya kirasa yace ya juyo zuwa gida. Ba musu ya dawo ya tadda mahaifin nasa.
Farar shadda mai dankaran kyau da tsada Daddy ya basa yace ya sauya shiga zasu wani wajen. Ba musu Haidar ya amsa yai yanda Daddy yace duk a tunanin Haidar Maiduguri zasu sake komawa tinda bai jima ba sukaje suka amso auren Daddyn.
Wann karon ma airport suka nufa saidai ga mamakin Haidar maimakon Maiduguri wann karon Garin Kano suka nufa. Suna isa Sadis ya isa ya d’aukosu. Shidai Haidar sai aika ma Sadis kallon tuhuma yake yayinda Sadis ke ta faman k’unshe dariyarsa dan shima Sadis d’in cikin shiga ta manyan kaya yake.
Haidar bai ida Shan mamaki ba saida yaga Sadis ya dire su k’ofan gidan su Ummulkhair. Ga tsirarun mutane da basu shige a k’irga ba zaune k’ofar gidan. Can ya hangi mahaifinta yayi shiga ta manyan kaya shima. Kan Haidar ya kuma d’aurewar.. Toh kodai bikin radin sunan little Haidar ake bacin haka bai tunanin Abba zai barsa ya tako k’ofar gidansa balle har ya basa wajen zama.
Haidar ya saci kallon Daddy da mamaki sai yaga Abba ya mik’e ya nufosu ya tarbi Daddy suna masabaha. A hankali Haidar ya janyo Sadis ya rage murya sosai yace “Now you tell me.. What is going on.?”
Sadis ya murmusa “Baza’a ji a bakina ba Ango.”
Haidar ya girgiza kai “Ango.?”
Sadis yace “Kashh.! Ka jini da sub’utan baki.. Kaga gashi can Daddy na mana alama da hannu.. Mu k’arasa.”
Jiki ba wani k’wari Haidar ya soma takowa da jagorancin Sadis dan gani yake kaman Abba zai fatattake sa kaman dai yanda ya saba.
Ga mamakin Haidar baki har kunne Abba ke nuna masa wajen zama “Bismillah Aliyu.. Taho ka zauna.. Ga Imam din ya k’araso.”
Haidar ya zauna bugun zuciyarsa na k’aruwa. Bai k’arasa Shan mamaki saida yaji da kunnuwansa Daddy na nemar masa da a sabunta aurensa da Ummulkhair.
Abba yai na’am da batun a take Daddy ya fiddo sadaki ya bayar aka samu cika cikan aure. Sadaki siga da kuma shaidu nan take a sabunta Auren Haidar da Ummulkhair cikin abinda yai saura na wancan Auren.
Tuni Sadis ya mik’e yana rabon goro da alawa.
Tsananin shock ya hana Haidar furta koda kalma har saida Abba ya mik’a masa hannu sukai masabaha ya kuma tayasa murna sann ya jaddada masa amanar ‘yarsa Ummulkhair a karo na biyu.
Daddy ya tabbatar masa in sha Allah zasu rik’e amana dan Ummulkhair ‘ya ce wajensa kaman Haidar.
*
Koda Abba ya shigo gida sai yasa aka masa kiran Ummulkhair. Kanta a k’asa ta k’araso ga Abba. Kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yai gyaran murya kad’an “Ummulkhair.”
“Na’am Abba.” Ta furta a hankali.
Abba yaci gaba “A yau na maida aurenki da mijinki Aliyu kaman yanda na Sami yarda da amincewar ki.. Ki sani ke ‘Yata ce banida burin da ya shige na ganki cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Burin ko wani mahaifi shine rayuwar yaransa ya inganta. In sha Allah zaki kasance cikin aminci kaman yanda kika kasance mai biyayya a garemu. Na jarabta mijinki ta hanyoyi da dama a lokacin da baki nan kuma Tabbas Aliyu yaci jarabawa dan na gamsu da hankalinsa tarbiyarsa dattakunsa da kuma irin k’aunar da yake Miki. Hak’ik’a bani tunanin akwai wani Wanda ya cancanci zama mijinki sama da Mahaifin D’anki. Allah ya muku albarka ya albarkaci zuri’arku ya kuma zaunar daku lafiya.”
A hankali ta amsa da Ameen Abba.
Abba ya jinjina Kai kafin yaci gaba “Gameda maganar tarwarki gidan mijinki mahaifiyarki ta buk’aci da an dan bada lokaci ki Sami k’arfin jikinki jariri Aliyu ma ya dan yi kwari. Tuni nayi magana da mahaifin mijin naki ya kuma samu mijinki da batun kuma an samu daidaiton fahimta. Ina fata hakan kema ya miki.”
Ta kuma sadda kanta kad’an “Duk yanda kukayi daidai ne Abba.”
Ya kuma murmusawa cikeda Jin dadin biyayyarta a garesa shi mata albarka ya kuma kafin ya sallameta.
Cikin gida ya kacame da guda da murna. Ga murnar radin suna ga murnar sabon Aure. Murna ta ko ina sai son barka.
Saidai Sam Amarya Ummulkhair bata bari Angonta ya sakata a idonsa ba har ya Kama hanyar Abuja a washe gari. Koda shima din bai nemi ya ganta ba.
**
Isowarsu Abuja Kai tsaye company ya nufa dan yasan can zai Sami Hisham.
Hisham sai cika yake yana batsewa. Haidar yanaji yana bada umarnin kar a bar kowa ya shigo ya damesa yanda kasan shine shugaban kampanin. Haidar bai tsaya sauraron kowa ba ya tura k’ofar ya shige. Idon Hisham naga computer din dake gabansa ba tareda ya dubi Wanda ya shigo na ya soma fad’a yana fad’in waye ya shigo masa office ba izinin sa. D’agowar da zai suka had’a ido da Haidar.
Murmushi Haidar ya sakar masa sai yace “Tuba nake Mr CEO, na shigo ba tareda izini ba.”
Murmushi Hisham d’in ma yai kafin ya nuna ma Haidar wajen zama “Welcome brother. Bismillah have a seat.”
Haidar ya girgiza Kai kad’an “Ba zama nazo yi ba. But thanks anyway..Nazo ne na baka wann.!” Yai maganar yana saka hannu a aljihun sa. Sai ya Ciro goro da alawa na Aure. Tinda Hisham yaga haka zuciyarsa ke tsinkewa.
Haidar ya aje masa goron da alawan saman table d’insa.
Hisham Ya girgiza Kai kad’an cikin rashin fahimta “What are.. we celebrating, Brother.?”
Har lokacin murmushi ne saman fuskar Haidar “Ka tayani murna. Jiya an maida aurena da matata UMULKHAIR.! Don’t you think is enough reason for us to celebrate.?”
Kaman sauk’an aradu haka Hisham yaji batun. Ya saki baki da hanci cikin tsananin shock yana duban Haidar.
Sai kuma Haidar ya janye alawan. Sosai Ya matso da fuskarsa kusan na Hisham. Ya rank’wafo suna duban juna cikin ido. Murya a dake yake furta “Goro shi ya kamaceka dan na tabbata kana jin d’aci a ranka fiyeda dacin goron nan. !” Ya sakar masa murmushi yana jefa candy din a bakinsa ya kashe ma Hisham ido guda sann yaci gaba “Enjoy the bitterness of those kola nuts.” Daga haka sa kai yai ya fice.
Har lokacin Hisham bai dawo daidai ba. Ya kasa yarda da abinda yaji. Wai dama tafiyar da Haidar da Daddy sukai ba tafiya bace ta kasuwanci. Tafiya ce ta Auren Haidar d’in. Lallai ma Daddy yama raina masa hankali.. Shi yana nan yana k’ababa yana murnan Daddy ya fara sakar masa ragamar company Ashe munafuntarsa yai.. Ashe ya tafi ne dan ya karb’ar ma d’ansa Auren Ummul d’insa da yai komai dan ya tabbata ya rabasu da Haidar d’in. Yaci gaba da huci yana jinjina kai. A zuciyarsa yake furta ‘You don’t want to play fair Haidar.! Idan haka kake so.. I can play dirty as well.. Yanzu wasan zai fara kawai ka jira ka gani.’ Ya k’arashe zancen zucin nasa yana sakin huci idanunsa na kuma kad’awa. Sauri sauri ya fito daga Office d’in ya nufi elevator. Wata staff tai saurin dakatar dashi sanda zai shige elevator din “Em excuse me sir. That’s Mr Haidar’s private elevator.”
Huci Hisham yake yana dubanta “Ke kinsan ni waye.? Kinsan da waye kike magana.?!” Yanda yake mata maganar cikin tsananin tsawatarwa ya janyo hankulan sauran mutanen.
Hisham yaci gaba da huci yana furta “I am Hisham Maitama.! I own this company.. I can fire you right this instant if I want.!”
Sai ta soma basa hakuri tana neman hanyar tsira. Yaci gaba da duban mutanen wajen kaman wani zararre “Sunana Hisham Aliyu Maitama. The Eldest Son of Engr Aliyu Maitama. Did you all get it.! Ni ne Hisham Maitama. Hisham Maitama.. Everything here is mine. I own this company.! Dukkanku ku saka wann a cikin kawunanku.!” Yana ida fad’in haka yasa Kai ya shige cikin k’unan rai.
Shi d’ayansa yana driving yana buga steering wheel yana furta “Damn you.! Damn you Haidar.! Damn you..!”
Waje ya nema yai parking yana maida huci. Sai k’ullawa da sak’awa yake yana neman ta yanda zai b’ullo ma al’amarin. Dan Alk’awari Ya dauka bazai taba saduda ba. A fili Ya futa “ANISA.!” Anisa dai ita kad’ai ce card d’in da zai sake amfani da ita. Kai tsaye motarsa ya shige ya nufi jail din da Anisa ke tsare.
Sosai Anisa taji mamakin wai Hisham Ya kawo mata visit.
Hisham Ya tsareta da ido yanda ta rame tai duhu duk ta fice hayyacinta kaman wann Anisa ‘yar gayu da Ya sani ba.
Ta dan rausayar da ido had’ida furzar da huci. Wanda saida tai wann d’abi’ar nata ma Hisham Ya tabbata ita d’in ce.
“Mai ya kawoka wajena.?” Ta tambaya tana dubansa.
Hisham Ya murmusa “Alkhairi.!”
Ta dan girgiza Kai kad’an “Kai har akwai wani alkhairi tattareda kai Hisham. Bayan duk abubuwan da ka mun. I’m in this situation because of you.”
Hisham ya dakatar da ita “No Neesa. You are in this situation because of your stupidity. Kinga duk ba wann ba.. Idan Har kika amince da batun da nazo Miki dashi ki yarda dani you’ll be set free..”
Tai murmushin takaici “Now I understand everything. Kai din ka jima da sanin Haidar d’an mahaifinka ne. Kaidin fansa kawai kake nema kan Haidar da Aunt dina Shiyasa kai amfani dani. Shiyasa ka b’oye min komai naka baka sanar Dani cikinka ba kaman yanda ni na sanar dakai nawa. Ashe amfani Dani kawai kake dan ka cimma burinka.” Taci gaba da jinjina Kai tana dubansa “Kayi amfani dani a karo na farko bazan bari ka sake amfani dani ba Hisham.. Dareen was right kaman yanda kai amfani da ita ka jefar da ita gashi nan Nima na faruwa akaina.. Ban tab’a ganin azzalumin mutum macuci irinka ba Hisham.. Kuma nayi alk’awari ma Haidar sai yanda k’arfina Ya k’are wajen bankado gaskiya da bayyana true color dinka. Bazaka sake samun dama akaina ba Hisham.!”
Murmushi yai kad’an had’ida gyara zamansa “Neesa kenan. Kina magana kaman baki san wane irin serious crime ake tuhumar Ki dashi ba.. Tuhumarki ake da kisan kai Anisa. Bana jin akwai Wanda zai iya wankeki daga wann babban tuhuma da ake Miki koda kuwa Haidar ne.” Ya kuma gyara zama “You are alone in this Anisa. Ahalin ki Sun juya Miki baya.. Ina nufin mahaifinki da mahaifiyarki.. Sann Haidar da kika dogara dashi ki yarda dani yana yin komai ne to win Ummulkhair back.” Ya kuma karkacewa yana gyara zamansa “For your information Neesa.. An maida Auren Ummulkhairi da Haidar kinga kuwa Haidar baida sauran dalili da zaisa Ya taimaka Miki Ya cireki daga cikin wann tuggu.”
Anisa ta saki baki da mamaki tana dubansa “An maida Auren Ummul da Haidar.?”
Ya dan tab’e baki kad’an kafin Ya kuma gyara zamansa “Abu d’aya zai cireki daga wajen nan Anisa shine Ki amince zaki Aureni..!”
Kaman sauk’ar aradu haka taji batun. Ta d’ago da mugun mamaki tana dubansa “Ni Aneesa kake cewa na Aureka.?!”
Hisham ya murmusa “Ba don Ina sonki zan Aureki ba Anisa.. Sai don kawai ina so na taimaka Miki na cireki daga cikin wann k’ulli mai wuyan warwarewa da kike ciki.!”
Girgiza kai Anisa take tana dubansa cikin shock “You have no shame Hisham.. You are a demon.! Baka da zuciya cikin k’irjinka.. Tir da D’anAdam irinka..! Ta nan ka b’ullo..? Toh ka sani ni Anisa bazan tab’a auren mutum irinka ba.. Never.!”
Hisham ya mik’e yana gyara zaman suit d’insa “Think about my offer Neesa.. Wann shi kad’ai ne hanyar tsira da Ya rage Miki if you don’t want to rot in here.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice.
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*60*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
A parlour Hisham ya iske Daddy after dinner. Mommy na zaune gefensa suna tattauna yanda auren Haidar ya kasance. Da yanda Daddy da Abba suka shammacesu gaba d’aya da al’amarin auren.
Ya shigo da Sallama saman bakinsa. Suka amsa masa da sakin fuska Dddy yana masa iso da ya shigo ciki ya zauna. Can bakin carpet Hisham ya zauna had’ida risinawa kaman dai yanda yakeyi gaban Daddy a ko Yaushe.
Daddy ya dubesa cikeda kulawa dan ya kula da yanayin D’an nasa kaman dai babban Al’amari ke tafe dashi koda bai furta ba.
“Son, lafiya dai koh..? Inji komai lafiya..?”
Hisham ya jinjina Kansa kad’an “Lafiya Daddy.. Dama..” Sai ya d’anyi fasali ba tareda yaci gaba ba.
Mommy ta soma k’ok’arin mik’ewa tana fad’in “Bari dai na baku waje.”
Hisham yai saurin dakatar da ita da fad’in “No Mommy.. You should also stay.. Please...”
Mommy ta dan yi still sai tace “Shikenan ba damuwa.” Ta koma mazauninta.
Hisham ya dan gyara zamansa kad’an sanda Daddy yace “Muna sauraronka.”
“Daddy dama.. Ina so na nemi Auren Anisa ne idan babu damuwa. Idan hakan ya muku.. Ina nufin both you and Mommy.”
Da mamaki Daddy da Mommy suka dubi juna.
Mommy ta girgiza Kai kad’an “Wace Anisar.? Kana nufin Anisa my niece.?”
Hisham ya jinjina Kai kad’an “Eh Mommy.. Idan har babu wani damuwa.”
Daddy ya katsesa da fad’in “Ka kuwa san mai kake fad’a Hisham.. Auren Anisa fah kace. Anisa dake facing court case.?”
Hisham ya jinjina Kansa cikeda risinawa “Eh Daddy.. Kasancewar akwai court case akanta bazai hana Aurenmu ba. In fact wann shine dalilin da yasa na yanke hukuncin neman Aurenta. Dan na fitar da ita daga cikin situation d’in da ta tsinci kanta ciki Wanda ba komai bane face jarabawa daga Ubangiji.” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “Daddy Anisa tayi kuskure amma ta fahimci kuskuren ta kuma ta gyara.. Dukanmu munga yanda tai repenting bayan ta fahimci kuskurenta.. We shouldn’t abandon her.. Ina nufin dukanmu munyi kuskure a baya.. Kuma mun yafi juna. Bai kamata mu kyale Anisa ita kad’ai cikin wann ba. Daddy ni zan Auri Anisa matuk’a hakan yayi muku.”
Muryar Haidar suka sinkaya Wanda shigowarsa parlorn kenan yana fad’in “Did I hear that right.? Zaka nemi Auren Anisa.?” Yai tambayar cikin tsananin shock yana duban Hisham d’in.
Hisham ya murmusa had’ida jinjina Kai yana duban Haidar d’in “Eh Haidar.. You heard that right.. Ina so zan Auri cousin d’inka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 56 Chapter of 64