safe koda Ummul ta shigo gaida Mommy sai Mommy ta dakatar da ita bayan Sun gaisa. Ta nuna ma Ummul d’in gefenta saman kujera “K’araso nan ki zauna daughter, magana nake so muyi.”
Ummul ta jinjina Kai had’ida amsawa kana tai yanda Mommy tace.
Anisa dake k’ok’arin saukowa downstairs nan ta sinkayo zancensu. Ba shiri ta lab’e jikin staircase tana sauraronsu.
Mommy taci gaba yayinda kan Ummul ke kife k’asa “Bana so na zamto irin iyayen nan masu kutsa Kai a al’amari gidan ‘ya’yansu. But when it comes to Haidar you and I are team. Haka ne.?”
Ummul ta jinjina Kai a hankali.
Mommy taci gaba “Kuma zamuci gaba da zama team wajen ceto rayuwarsa daga halak’a. Tinda ni mahaifiyarsa ce ke kuma matarsa. Mu duka d’in yanada matuk’ar mahimmanci a wajenmu. Haka ne.?”
Nan ma jinjina Kai ta kumayi a hankali.
Wann karon sai Mommy ta d’aura hannu saman nata “Ummulkhair.!”
Ummul ta d’ago a raunane tana duban Mommy.
Mommy taci gaba “Nasan kina hak’uri da Haidar. Amma dan Allah ki k’ara. I have this strong feeling, with you by his side, Haidar zai mending ways d’insa. Kuma mun fara ganin hakan cikin ikon Allah..” Ta dan numfasa “Bazan tambayeki mai ya hadaku ba dan wann ba hurumi na bane. Sann dik hukuncin da kika zartar har kawo zuwa lokacin da zaki sauk’o bazan tak’ura miki ba. And always remember kina tareda yarda da kuma k’aunata a gidan nan. Tashi kije, Allah shi muku albarka gaba d’aya.”
Ummul ta jinjina kai a sanyaye kafin ta mik’e ta fice jiki ba laka.
Anisa da ta gama nad’e komai murmusawa tai. Cikin zuciyarta take furta ‘You are so selfish Mommy. Kedai kawai d’anki. Toh bari dai mu gani idan hak’arki zai cimma ruwa.’
Da dare ta iske Ummul a sashenta. Anisa ta saki murmushi tana duban Ummul “Da alama jikin D’anuwana kuma mijinki da sauk’i sosai tinda gashi har kin rigashi dawowa.” Tai maganar tana murmushi sai kuma ta k’arada “Kodai kema koroki yai kamar dai yanda ya koroni.?” Ta k’arashe tana d’aga gira d’aya.
Tinda Anisa ta soma magana k’irjin Ummul ke bugu.
Anisa ta kuma murmusawa “Saidai kuma nasan mahaifiyarsa zatai iya k’ok’arinta ta kuma maida masa ke koda kuwa korarki yayi. Sabida ita d’in kanta kawai ta sani. She’s so selfish.”
Ummul ta dubi Anisa da idonta da tuni sun kad’a. Murmushin ne dai saman fuskar Anisa. Ta matso dab kusan Ummul ta dafa kafad’arta “Hajiya Kwaise Maitama bata tab’a son talaka ba sann bazata tab’a so ba, ita d’in mace ce da bata so wani talaka ya rabeta balle har ta aura ma D’anta. Ki yarda dani, she’s just toying with you Ummul. She’s using you. Ki yarda dani amfani dake kawai take dan ki toshe gibin da ta jima da bud’ewa cikin ahalinta da kanta.” Anisa tai maganar babu ko alamun d’ar tattareda ita.
Ta d’ago idanunta masu cikeda k’walla tana duban Anisa. Sai Anisa ta karkad’a yatsa a saman fuskar Ummul d’in “No, I’ll do the talk today because, ni keda abin cewa.” Taci gaba da murmushi tana duban Ummul “Mommy is a very dangerous woman who’s capable of doing anything to protect her interest. She brought you into her son’s life not because she loves you for him. But because, she wants you to do what she couldn’t do.” Taci gaba da jinjina kai alamun tabbatar da kalamanta “She wants you to do the job for her. To knock some sense into her son. She brought you into his life to cleanup her mess. Ki nutsu kiyi tunani Ummul a koda yaushe Mommy zancen Haidar take miki. Ya za’ai ki shawo mata kan Haidar. Shin ta tab’a tambayarki idan kina cutuwa a zaman da kike da D’anta.? Ko ta tab’a tambayarki menene naki damuwar.? Shin ta tab’a tambayarki ko kinada wata damuwa da ya danganci ahalinki.? Bata tab’a ba. Koda yaushe maganar d’aya ce ‘Haidar.’ Haka ne.?”
Izuwa lokacin idanun Ummul sun soma zubda ruwa.
Anisa ta dafata kad’an “Kar ki bari Mommy tayi amfani dake dan cimma wata manufa nata. Ke macece mai k’ima. Kar ki bari wann matar ta watsar dake gaban D’anta.” Ta kuma dafa Ummul “Kiyi weighing maganganun da na fad’a miki sai ki tantance. Abu guda nakeda tabbaci akai shine ban tab’a miki k’arya ba.!” Tana ida fad’in haka tasa Kai zata fice. Har ta Kai k’ofa ta kuma juyowa “Save yourself while you still can. Run as fast as you can.. Ki ceci kanki daga wann auren da da baida tabbatacciyar makoma.” Tana ida fad’in haka tasa kai ta fice tana sakin murmushi.
A hankali Ummul ta silale k’asa kukan da taketa k’ok’arin dannewa na zuwa mata gadan gadan. Meyasa takejin zuciyarta ta gamsu da duk abubuwan da Anisa ta fad’a. Meyasa takeji kamar dai itace ta b’ace cikin k’ok’arin lalumo ma Haidar hanyarsa. Meyasa takeji kamar dai kowa amfani da damarsa yake akanta.? Ba auren soyayya tayi ba sann bata tsammaci wani abu mai kama da farin ciki cikin auren ba. Musamman idan ta tuna yanda akayi auren Wanda sadakin auren Ya kasance kudin jinyar mahaifinta. Koda ace Mommy ba har zuciya take nuna mata so ba, koda ace manufar Mommy shine ta shigo rayuwar Haidar dan tai guiding d’insa bata jin Mommy tanada wani laifin cikin hakan tinda tin farko ga yanda akai auren. Sann A d’an zaman da sukai da Haidar kai tsaye bazata ce ta kamu da soyayyarsa ba. Amma tana jin damuwarsa Har cikin ranta. Saidai dukda wad’ann tunani can k’asan zuciyarta tana jin sosai take so ta gano manufar Anisa dan ta tabbata idan Babu wani boyayyan al’amari Anisa bazata samu k’warin gwiwa irin haka ba. Ta d’au d’amarar gano bakin zaren komai cikin ikon Allah.
A ‘yan kwanakin Mommy ke zuwa wajen Haidar ta yini dashi sann ko zancen bata kumayi ma Ummul ba. Iyaka damuwa Haidar yakai k’ololuwa. He misses her so much. Baisan ta yanda zai sanar da Mommy ba. Ya kula ma kaman Mommy punishing d’insa take da rashin Ummul d’in.
Da Haidar yaga abin ba na k’are ba Har ana shirin sallamarsa batazo ba dole ya tambayi Mommy Ina take mai take gida.?
Mommy ta dubesa a dan tsare “Hutawa take gida, ka kyale nurse room dinka ya kula dakai. After all, aikinsa ne. An biyasa domin yayi hakan.”
“But Mommy he doesn’t do anything right.. And I don’t want him touching my things.” Ya k’arashe fuskarsa duk a dame.
“Oh kasan da haka kai mata mugun hali.?” Mommy tace a dake.
Sai Ya d’ago a d’an firgice “Mommy mugun hali kuma.? ita tace Miki na mata wani abin.?”
Yanda yai tambayar ya tabbatar ma Mommy D’anta Ya fara nitso a tekun soyayya bai sani ba. Ta kifa kai ta murmusa kafin ta kuma d’agowa a tsare ta dubesa “Nasan ka mata wani abin ne amma wann ji da kan naka bazai bari ka amince kayi ba.”
Ya lumshe idonsa kadan had’ida furzar da huci “Mommy I didn’t mean to hurt her feelings.. Believe me.”
Dakatar dashi tai “Ba ba’asi na nema ba.” Sai ta kuma dubansa wann karon a d’an sanyaye “Haidar, ni na haifeka nasan halinka tun k’uruciya. Nasan abubuwan da kai going through a rayuwa. Tin kana yaro baka bari a gane lagonka dukda tarin k’alubale da ka fuskanta. Jarumtarka baya bari a gane raunin ka. Amma ka sani even the strong people need help sometimes.”
Sai ya dubi Mommy a d’an sanyaye wann karon.
Mommy taci gaba da jinjina kai “I know your psychological wounds are much deeper.. But I believe they’ll heel in time with Ummulkhair by your side.” Haidar ya kuma duban Mommy without saying a word.
Mommy taci gaba “Ba gazawa bane to Own up to your mistakes and apologies when necessary. Even if it hurts..” Ta murmusa tana dubansa “Kana so matarka ta dawo wajenka.?”
Sai ya dubi Mommy har lokacin baice komai ba. Saima kaikaitar da fuskarsa da yai.
“Shikenan zan sa driver ya kawota. But I have my conditions.”
Yai saurin duban Mommy “Mommy conditions kuma.? You.. just call her my wife fah.”
Dariya Ya kusa kufce ma Mommy tai k’ok’arin gimtsewa “Toh so kake na kawo maka ita ka wulak’anta ta. Ai dai naga ni na biya sadakin ba Kai ba.”
Ta kuma gyara zamanta “Conditions dina sune Bazaka sakata fushi ba. And you must kill that prideful behaviour of yours. Kayi alkawari.?”
Ya marairaice fuska “Mommy do I have to promise.?”
“Aw! Toh kaga ni saida safe.. Room nurse d’inka na jira.” Ta mik’e tana k’ok’arin d’aukar jaka.
Saurin kamo hannunta yai “Ok, fine. I promise.” Ya fad’i kaman Wanda aka masa dole.
Mommy ta k’unshe dariyarta dan sosai draman Haidar d’in Ya bata dariya. Ga abu kana so amma ka kasa fitowa kai tsaye ka furta. Wani abun sai Aliyunta. Ta tuna da fari da kyar Ya amince Ummul ta zauna wajensa sai gashi yanzu da kanshi yake nemanta. ‘Sannu a hankali ma zaka kawo kanka wajen Ummul d’ita Haidar.’ Mommy tace a zuciyarta.
Ba Mommy ce ta maida ma Haidar matarsa ba sai ana gobe sallamarsa. Dan so take ta wana Haidar kad’an yanda idan ta mayarsa da Ummul zai shiga taitayinsa. Sa’arsa d’aya ma dan jinya yake.
*
Yana nan kishingid’e saman gado yana duban yanda taketa fito da kayayyakin daga hospital wardrobe d’in tana shiryawa cikin suitcase. Fuskarta babu yabo babu fallasa. Dan tinda ta dawo bata yarda sun koma kaman da ba musamman idan ta tuna maganganun Anisa. Ta k’udiri niyyan gano koma menene ke b’oye da izinin Allah tinda tasan a shashanci irin na Anisa haka kawai bazata shirya zance irin haka ba face tanada k’wakk’waran hujja.
Ta dan saci kallonsa tana linke Kayan. Nan taga ya kafe ta da ido. Tai saurin janye idonta.
Mik’ewa yai Ya soma takowa a hankali. Ta bayanta ya tsaya had’ida rungumota, Ya rik’e hannunta da kayan cikin nasa. Ummul ta lumshe idonta a hankali jin hannunta saman nasa. A hankali yake k’ok’arin linke kayan ba tareda ya saki hannunta ba. Har lokacin idanun Ummul a lumshe suke tana jin kwalla na k’ok’arin ciko idonta. A hankali Ya d’aura hab’arsa saman wuyarta had’ida lumshe idanunsa. Wasu abubuwa yake mata Wanda k’afafuwansu ke barazanar gaza d’aukarsu. Rigar dake cikin hannunsu Ya silale Ya fad’i k’asa… Ta soma k’ok’arin cire jikinta daga nasa amma saiji tai ya rik’eta tsam. Murya can k’asa yake furta “I wanted to hate you.. I tried to hate you.. But I couldn’t..!” Ya d’anyi fasali yana mai ci gaba da sinsina wuyarta. K’amshinta da yai missing. Har lokacin idanun Haidar a lumshe suke. Yayinda hawayen da Ummul ke k’ok’arin makalewa suka shiga zarya.
“I can’t get you out of my mind Khairy… Please stay.. right here..And don’t let go.!”
Hawaye shar suka soma ambaliya a fuskarta. Ta shiga cikin rud’ani matuk’a. Ta rasa da waye zata yarda cikin ukun. Mommy ce, ko Anisa ce ko kuwa Haidar ne.
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*45*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Zame jikinta tai daga nasa tana mai goge fuskarta. Lokaci guda ta k’arasa saman sofa ta zaune tana mai ci gaba da goge hawayen da ya wanke mata fuska.
Ya d’anyi still a wajen yana dubanta kaman bazaice komai ba sai kuma ya zira hannayensa cikin aljihun wandonsa. Ya soma takowa a hankali zuwa yanda take. Har lokacin babu walwala a fuskar Ummul.
Haidar ya zauna daga gefenta ba tareda ya dubeta ba. Dak’ik’ai suka gifta. Ya soma tuno kalaman Mommy da tace he should own up to his mistakes. Ya dan lumshe idonsa kadan. Har Ta cire ran bazai ce komai ba ta sinkayo muryarsa “Are you.. Still mad..?”
Ta dan dube shi. Sai taji yace “Do you want me to apologise.?”
Nan ma batace komai ba sai d’an dubansa da tai.
Haidar ya dan furzar da huci wann karon yana janye idanunsa daga barin dubata “Oh no Khairy. You are not going to give me that silent treatment.”
Nan ma bata ce komai ba.
Sai ya mik’e a dan fusace “Ok fine.. Dama kawai baki dawo ba idan bazaki ce komai ba.!”
Mik’ewa tai itama cikin fushi “Da gaske, haka kace…?” Sai ta nufi k’ofa da zummar ficewa. Haidar yai saurin dawo da ita.
Ta d’an kalleshi “Ni ka sakar mun hannu.”
“Idan ank’i fah.?!” Ya fad’i yana tsareta da ido sosai. Sai ya dan sassauta rik’on da yai mata “Wai duk mema genesis na fushin nan ne .? Kan project d’in nan ne right.?”
Ta dan kallesa da wutsiyar ido. Kaman Wanda ya fama mata wani mik’i tace “Waye yake fad’a da mahaifinsa.? Waye yake d’aukan fansa kan mahaifinsa.!”
“Oh no please.. Not again.” Ya fad’i yana kame Kansa kad’an. Sai kuma ya dubeta a fusace “Maybe he pushed me into becoming this monster.. Don’t you think.!”
Sai ta girgiza Kai tana dubansa “A’a saidai idan hakan d’in ka zab’a. K’walla suka ciko idonta tana dubansa. Ta rik’o hannayensa cikin nata “Shin zakaci gaba da rayuwa a bayanka ne.? Meyasa zaka bar kanka rufe cikin kurkuku.. Wann k’uncin da kake ji cikin zuciyarka ba komai bane illa kasa karb’an k’addararka da kayi. A wasu lokuta Allah yakan saka mana jarabawar mu su zamto mutanen da suke da alak’a ta jini damu. Mutane mafi kusanci damu. Bamu ke zab’an ahalinmu ba, kuma hakan Rahamarsa ce.” Ta d’an numfasa kafin taci gaba. Allah ya jarabci salihan bayinsa Annabawansa da ahalinsu. Kaman Annabi Ibrahim (AS) Allah ya jarabce shi da Babansa. Kaman Annabi Yusuf (AS) Allah ya jarabce shi da ‘yanuwansa. Kaman Annabi Yaqub (AS) Allah ya jarabce shi da ‘ya’yansa. Kaman Annabi Nooh(AS) Allah ya jarabce shi da D’ansa. Kaman Annabinmu fiyayyen halitta(SAW) Allah ya jarabcesa da Uncles d’insa. Duka wad’annan Annabawa masu daraja sun fuskanci jarabawa daga cikin ahali. Ashe lallai muma zaa jarabcemu daga cikin namu ahalin. Wad’ann k’alubale da jarabawa suke k’arfafa imaninmu..Sann Allah shike shiryar da Wanda yaso..” Daga haka bata kuma cewa komai ba taci gaba da tattare kayyakin da take.
Haidar ya koma ya zauna had’ida zuba mata ido ba tareda ya kuma cewa komai ba. A hankali yasa tafukan hannayensa ya shafi fuskarsa.
**
Koda suka dawo gida maganganun Anisa suke yawo a kwanyarta, tayi k’ok’arin ta yakice tinanin amma ta kasa. A lissafi saura kwanaki uku kacal ta cika watanni uku da aure. Hakan na nufin alk’awarin da ta d’aukar ma mahaifiyarta yana gab da cika. Ya kamata ta waiwayi gida. Tana buk’atan sanin wani hali ahalinta ke ciki. Musamman majinyacin mahaifinta. Tinanin kalaman Anisa suka ci gaba da dukan kwanyarta. ‘Shin Mommy ta tab’a tambayarki wani abu gameda ahalinki.?’ Tai saurin rintse idonta ta mik’e da zummar ficewa taji muryar Haidar daga bathroom yana kiranta. Ta isa jikin closet din kafin ta d’anyi gyaran murya ta amsa. Haidar yaci gaba “Could you please pass me my towel.”
Ta shiga bin closet din da kallo tana duban yanda komai yake cikin tsari. Nan ta hangi towel d’in dan sama kad’an anyi folding an jerasu cikin open shelf cabinet. Ta ciro towel din mai dan girma tai knocking a k’ofan bathroom din “Ga.. Gashi nan na kawo maka.”
Muryarsa ta sinkayo “The door is open.. you can come in.”
Ta zaro ido waje jin abinda yace. Sai ta soma girgiza kai ita kad’ai “A’a.. A’a kawai ka karb’a.” Ta k’arashe tana mai tura hannunta dake rikeda towel d’in ta tsakanin k’ofar. Bata ankare ba saiji tai ya had’e da hannunta Ya janyota cikin bathroom d’in.
Ummul ta rintse idonta sosai sai ta fashe masa da kuka. ta shiga dukan k’irjinsa “Mai kake aikatawa ne.. Dan Allah ka… k’yaleni na fice. Please..!”
For the first time da taji sautin dariyarsa. Cak ta tsaya da abinda take still ta kasa bud’e idonta.
Haidar murmushi yake Har hak’waransa na bayyana “Okay.. Open your eyes now.. You are here already..!”
Ummul ta mak’e kafad’a tana kuma dukan k’irjinsa “A’a nidai bazan.. bazan bud’e ba.”
“Okaaaay.. Let’s see now..” “Trust me, I’m gonna make you open those eyes.” Har lokacin murmushi mai sauti mai bayyana hak’wara yake. Abinda Ya jima baiba na tsawon lokaci.
“Wai.. Mai kake k’ok’arin aikatawa.?”
Bai amsata ba yaci gaba da niyyansa.
A yayinda Ummul ke k’ok’arin zillewa bata ankara ba sai ji tai Haidar Ya janyota sun fad’a cikin jacuzzi tub d’in a tare.
Ummul ta ja numfashi tana mai fiddo kanta waje had’ida shafe ruwan da Ya jik’a mata fuska.
Ta kafesa da ido baki a ture kaman zata fashe da wani kukan.
Haidar ya kashe mata ido daya “See. I told you zansa ki bud’e idonki.”
Ta soma k’ok’arin mik’ewa yayi saurin kamo hannayenta “Ina kuma zakije bayan kin riga kin jik’e.”
Baki a ture tace “Ba kaine ka jik’ani ba... Kuma kasan Mommy ta gayyacemu cin abincin dare. Ya kamata naje sashenta da wuri dan na taimaka da wasu abubuwan..”
“Kar ki damu Mommy bazata ce komai ba..”
Ta d’an hararesa baki a ture “Kuma na riga na shirya.. kasa na jik’e gaba d’aya.”
Ya dan tab’e baki kad’an had’ida lifting shoulders d’insa “Shikenan sai ki sake wani wankan.” Ya matso saitin kunnenta yana mai rage murya “Let’s bath.. Together..”
Turasa tai da duka k’arfinta ta tashi . Murya na rawa ta shiga nuna masa forehead d’insa da hannunta “Kaga duba kaga.. akwai abu kusan idonka..” Yakai hannunsa goshinsa sai Ummul tai amfani da damar ta tashi a guje ta zille masa. Wann karon itake masa dariyar.
“Don’t worry, I’ll get you next time.” Ya k’arashe yana mai mata alama da yatsarsa.
Anisa da tin shigowarta sashen ta soma sinkayo kaman sautin mutane nan ta sad’ad’ kaman mai shirin satan wani abu. Ta lab’e yanda take sinkayo sautin. K’iris Ya rage Zuciyar Anisa bai buga ba. Kasa jurewa tai dole ta fice daga sashen.
Tana ficewa ta d’auki waya ta kirawo Hisham. Cikin tsananin huci take fad’in “No way Hisham. I can’t wait till that day.. I’m losing my patience here. Na tsani wann kucakar.. She’s driving me crazy.. Ji nake kaman naje na shak’eta.”
“You will not do anything foolish.”
Ta katsesa “Na gaji Hisham.. Bakaji yanda suke dariya cikin nishad’i ba. They were having a good time.” Ta saki kara tana fad’in “It’s so irritating.. Ka gane we can’t let those two be happy while we are stuck here.. just freaking miserable. We need to act fast.!”
Hisham dake ci gaba da sakin huci Ya katseta cikin tsawa “Just shut up Neesa.! Na gaya Miki bazaki aikata komai ba ba tareda umarnina ba. Na dan lokaci ne. Haidar bazai taba samun dama akan Ummul dita ba. So just trust me.!” Ya k’arashe idanunsa ba kuma kad’awa in rage.
A fusace ta katse kiran tana kuma ci gaba da zagaya d’akin zuciyarta naci gaba da tafarfasa. Sautin nishadin Haidar da Ummul Ya kasa barin kwanyarta da kunnuwarta. Ta saki k’ara kad’an tana durk’usawa wajen. A hankali take furta “I hate you.. I hate you Ummul.!”
*
Koda Ummul ta koma nata d’akin murmushi ne Ya kasa barin fuskarta. Ta Tina sanda sukai juyi cikin jacuzzi tub tare sai ta lumshe ido a hankali tana sauk’e sassanyar ajiyan zuciya. Wata doguwar riga silk kalan peach da ya zauna a jikinta sosai ta d’auko ta saka ta yane kanta da mayanin rigar. Ba makeup a fuskarta sai d’an man leb’e amma sosai tai kyau. Fatarta da bai cika haske ba sann bai cika duhu ba ya k’ara murjewa yayi kyau. Kwantattun sumarta irinta asalin k’abilar fulani da ta d’auko daga mahaifiyarta sun kwanta sunyi luf tin daga gaban goshinta Har zuwa gefen fuskarta. Kallo d’aya zaka mata kaso sake kallonta. Kalan rigar sosai ya tafi da Kalar jikinta. Abinda bata saba ba sai ta tsinci kanta da duban kanta a madubi. Kunya da dariyar kanta suka zo mata lokaci d’aya. Harga Allah zata iya cewa ta mance da wata damuwar gidan duniya da batun Anisa. Shi d’in kawai take hangowa a duniyar ta Wanda takeji tamkar su biyu ne ciki. Parlor ta sauko tana jiransa dan yace ta jirasa zasu shiga sashen Mommy tare.
A b’angaren Haidar kuwa bayan Ya d’auki file din ya jima yana juyawa yana tinanin maganganunta kai tsaye sashen mahaifinsa Ya nufa.
Daddy yana zaune study Haidar yai Sallama Ya shigo.
Daddy ya d’ago ya dubi Haidar da idanunsa dake rufe cikin farin gilashi na k’ara k’arfin gani ga wad’anda shekaru Ya d’an ja masu.
Tin daga yanda Daddy ya amsa masa Sallama jikin Haidar Ya d’anyi sanyi. Dan yanayin amsa masa da yai yasha bambam da irin yanda yake amsa masa a baya.
Sun d’auki lokaci suna duban juna kafin Daddy ya nuna masa kujera mai kallon table d’insa yace ya zauna.
Haidar ya k’arisa ya zauna.
Shiru Ya dan ratsa tsakani kafin Haidar yai k’arfin halin cewa “Daddy.. Barka da dare.”
Daddy ya amsa masa had’ida jinjina Kai.
Sai Haidar ya aje folder d’in saman table din Daddy.
Daddy ya girgiza Kai kad’an kaman Wanda yake avoiding k’wayan idon Haidar d’in “What’s this for.?”
Haidar yai clearing throat d’insa “Yarjejeniyar project d’in ne Daddy.. Tareda resignation latter.. Na janye ragamar kula da kwangilar.. Sann.. Na aje aikina na company.”
Daddy sai Ya d’ago yana dubansa sosai wann karon.
Haidar sai Ya mik’e kansa a kife “I.. I’m sorry idan ban kasance wann d’an da kake fata da buri na zama ba..”
Ya soma k’ok’arin ficewa daga study d’in mahaifinsa ya dakatar dashi.
“Aliyu.!” Daddy ya ambaci sunansa.
Ya d’ago Ya dubi Daddy.
Da ido Daddy yai masa nuni da kujeran “Koma ka zauna.”
Haidar ya komo ya zauna har lokacin Kansa a kife.
Cikin tsawa da fad’a kaman yanda ya saba masa a lokutan baya ya soma fad’in “Ni kake ce ma ka aje aikinka..?” How dare you.? Who do you think you are...! Kai har ka kai ka dubeni kace min ka aje aikinka.? Kai har ka isa.?!”
Da a lokutan baya ne da ya amsa ko ya maida ma mahaifinsa martani cikin daga murya. Amma ga mamakin Daddy sai yaji ya soma magana a natse “I’m sorry.. But I can’t do it Daddy.!” Ya fad’i k’walla suna ciko idanunsa. Cak mahaifinsa ya tsaya yana dubansa.
Haidar yaci gaba da girgiza Kai “I can’t destroy you.!”
Daddy ya koma ya zauna yana duban Haidar d’in sosai cikin tsanani shock.
“My plan was… To use this so called project and destroy you.. I wanted to show you the kind of monster you created in me.. But then I couldn’t.. I couldn’t destroy the hands that raised me koda ace mun kasance munada alak’a mai rauni cikeda tarin k’alubale.” Yaci gaba da girgiza kai. Sai murmusa kad’an wann karon “I just want to be free from this prison. I.. I don’t want to keep on living my life tied to all this rage and hatred.. I want live a normal life.. To start a family of my own..” Muryarsa yaci gaba da rawa “I.. I’m sorry Daddy.. I’m sorry idan ban kasance wann d’an dake fata da burin samu ba.. I’m sorry idan ban kasance wann D’an da zakayi alfahari dashi ba.. Believe me.. I truly.. am sorry..”
Baikai aya ba Daddy dake ta k’ok’arin danne hawayensa sai ya zame farin gilashinsa ya kauda fuskarsa kadan yana goge hawayen da suka mak’ale masa a ido.
Kaman daga sama Haidar ya sinkayo muryar mahaifinsa “Aliyu, my son..”
Da mamaki Haidar ke duban Mahaifinsa Jin ya ambacesa da D’ansa abinda bai taba ji daga mahaifin nasa ba.
“Shin ka tambayi kanka koda ka farka daga coma meyasa baka ganni wajenka ba.?”
Shiru Haidar baice komai ba.
Daddy yaci gaba da jinjina Kai har lokacin bai kalli b’angaren da Haidar d’in yake ba “Sabida bazan iya kallonka a ido ba.. Bazan iya ambatan kaina da mahaifinka because I.. I haven’t been a good father to you.. And I treated you badly..” Daddy ya kifa Kansa hawaye na gangaro masa “Fad’an da kaji ina maka a yanzu borin kunya ce kawai sabida ni d’in ban sauk’e wani nauyi da hakki na mahaifinka dake rataye wuyana ba. Hadisi ne guda cewa ko wannen mu mai kiwo ne kuma za’a tambayemu gameda wann amana na kiwo da aka dank’a mana. Bazan iya duban idanunka na nemi gafararka ba Haidar… Bazan iya ba..!” Saiga alamun kuka cikin muryar Daddy.
Haidar ya mik’e jikinsa a matuk’ar sanyaye ya tako har zuwa gaban kujeran da Daddy ke zaune bisa. Duk’awa yai gaban Daddy Wanda har lokacin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 42 Chapter of 64