Ya girgiza kai yana kallon labarin “Yanzu zaka yarda da batu na da nace da kai mu tafi asibitin. Rashin nuna damuwarka zai janyo hankalin press garemu. Idan son samu ne yarinyar tana warkewa ka kira koda kwaryakwaryar walima ce tsakanin business partners dinmu ka sanar da Auren D’anka.”
Daddy yaci gaba da girgiza kai yana fad’in bazai bari Haidar Ya tarwasta shi ba. A fusce ya fice Alhaji Gimba na take masa baya.
**
A can asibiti kuwa Haidar ne ya k’araso da yan sanda har guda biyu. Hisham na ganinsa da yansanda ya mik’e yana girgiza kai “No.. This is not happening.! Haidar mai kake shirin aikatawa.?”
Duk k’ok’arin Hisham na ganin Ya dakatar da Haidar bai nasara ba har saida Haidar d’in Ya kutsa kai cikin recovery room da aka aje Ummul.
Hisham yai wani irin burki zuciyarsa na bugawa sakamakon hango mutum da yai kwance saman gado. Dukda na’urar oxygen dake saman hancinta bai hana zuciyarsa bugawa sau uku a jere ba. Ji yai Ya kasa jurewa Har saida k’afafunsa suka kaisa gaban gadon. A daidai lokacin da Anisa harma da Mommy suke duban Haidar cikin tsananin mamaki Wanda shigowarsa dakin kenan ga yansanda biye dashi.
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*33*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Da tsananin mamaki Mommy ke duban Haidar. Ta kuma girgiza kai cikin rashin fahimta “Haidar meke faruwa. Why are the police here..? Who are they here for.?”
Haidar da Har lokacin dubanta yake. Wane irin duba da za’a iya fassara sa kai tsaye da duban k’iyayya Ya k’araso daidai gabanta. Ya d’auki dak’ik’ai a haka kafin Ya rank’wafo da kansa saitin kunnen Mommy “Isn’t it obvious? They are here for you Mommy. Sunzo ne su tafi dake.”
Mommy ta dago cikin tsananin mamaki tana dubansa. Ta girgiza kai cikin rashin yarda tana kuma duban ‘yansandan. Sai ta kuma duban Haidar cikin k’ok’arin tantance shin mafarki take ko kuwa da gaske ne hakan ke faruwa. Haidar ne ya kawo yansanda su tafi da ita. D’anta da ta haifa. Tilon D’anta da take duk wani fad’i tashi sabida shi a rayuwarta yau ya kawo yansanda suyi arresting dinta. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Bata tab’a tsammanin za’a kawo wann gab’ar ba. Duk k’iyayya da Haidar ke masu daga ita Har mahaifinsa bata tab’a tsammanin k’iyayyar zai tasiri irin haka ba.
“Aliyu.!” Ta ambaci sunansa cikin sanyin jiki “Ni ce ka kawo ma ‘yansanda su tafi dani.?” Ta k’arashe maganar nata tana nuni zuwa gareta da ‘yar yatsarta cikin tsananin shock.
Haidar da Ya kafe ta da ido lokaci guda yake jinjina kai “Remember this is a hospital Mommy. You can’t make a scene here. Ki fita ki tafi tareda ‘yansanda a tsanake.”
Mommy ta kuma girgiza kai tana jin hawaye na k’ok’arin ciko idonta. Ta tuna shekarun baya lokacin da ta haifi Haidar. Bata raine shi ba haka bata tab’a shayar dashi drop na nononta ba. Ko zai kwana yana kuka a matsayin jariri bata tab’a attempting lallashin shi ba irin yanda uwa keyi ma jaririn ta. Bata tab’a rungume Haidar yaji d’umin mahaifiyarsa ba. Ta tuna Asshe tasha nusar da ita cewa hakan zai iya yin tasiri tsakanin dangantakarta da D’anta domin kuwa a wann lokacin ake samun bond na uwa da D’ah. Wann shak’uwa soyayya da tausayi dake tsakanin D’ah da uwa a wann lokacin ake building d’insa. Ba birgewa bane sabida gayu da zamani kice bazaki shayar da D’anki da kika haifa ba wai gudun kar jikinki ya lalace. Kar ki losing figure dinki koh. Toh ki sani wann ba wayewa bane ba kuma birgewa bane. Ba birgewa bane kice ke bazakiyi d’awainiyar komai ma D’anki da kanki ba sai Nannies. At least ki samu lokaci na musamman tsakaninki da D’anki koda bazaki masa wasu hidindimu na d’abi’a ba. Ke uwa ce mai k’ok’arin k’ulla alak’a mai kyau tsakaninki da D’anki. Mommy ta dago tana duban cikin idon Haidar Wanda sanda yake jinjiri bata bar shi ya kalli cikin nata idon ba. Bata hango tausayinta ba bata hango soyayyarta ba balle jin k’anta sai akasin haka. Saiga hawaye suna gangarowa daga idon Mommy.
“Haidar ni mahaifiyarka ce. Ni ce na d’auki cikinka tsawon watanni tara.” Bai bari takai aya ba ya dakatar da ita “Ki aje duk wani bayananki Mommy. Wann labarin da kike bayarwa akwai ayan tambaya akansa a halin yanzu. Kuma kinsan me? Whatsoever you’re hiding sai na binciko sa this is just the start.” Ya dubi ‘yansandan “You can take her with you officers.”
‘Yarsandar macen ta soma k’ok’arin matsowa da sauri Anisa ta shiga tsakiya tana hawaye take girgiza kai “Don’t touch her.! Don’t you dare come near her. Do you really know who you are arresting.?! This woman here is Hajiya Kwaise Maitama. You just can’t arrest her. Kudin zaku iya rasa aikinku gaba d’aya.!”
Haidar ne Ya matso kusan Anisa yana sakin huci Anisa ma na hawaye take dubansa cikeda firgicin yanayin da taga Haidar din ciki.
“Who the hell do you think you are to interfere.? Get out of the way now. Or else..!” Bai kai aya ba Mommy ta katsesa “She’s my niece, and she has every right to interfere.! Unlike you she’s not ungrateful.. Wane irin D’ah ne zai kawo wa mahaifyarsa yansanda..?!”
Jinina Kai yake yana duban Mommy “Since you went ahead and brought it up.. Are you really my real mother.? Da gaske kece mahaifiyata kodai sato ni kikai.? Tell me now Kwaise Maitama. Who are my real parents.? Where are they.? Did you kill them and kidnapped me.? Answer me now.!” Ya k’arashe idonsa na kuma kadawa.
Mommy ta kasa furta komai sai hawaye dake neman ciko idonta jin danta data dauki cikinsa tsawon watanni tara ta haifosa duniya na kokonto idan ita ta haifesa.
Haidar yaci gaba da jinjina Kai jin bata basa amsa ba “Of course you don’t have the answer. But I promise you, koda baki amsa yanzu ba zaki amsa a ofishin ‘yansanda.” Idonsa na kanta yaci gaba “Officers take this woman with you right now.!”
Yarsandan ta kuma matsowa Mommy taci gaba da girgiza Kai “No Haidar. Baka cikin hayyacinka..” Ta dubi yarsandar dake kokarin kamo hannunta ta aika mata wani kallo “You are doing this to lose your job. Do you have any idea who I am.?!”
Yarsandar ta d’anyi gyaran murya “I’m sorry Ma’am but we have the warrant for your arrest.” Ta k’arashe tana k’ok’arin warware mata takardan hannunta.
Mommy zata kuma magana Haidar ya katseta “Ki adana duka bayananki har a isa ofishin ‘yansanda. Zaki sanar dasu yanda akai kika Saka guba a turaren da kikai niyyan Kasheni dashi ta hanyar gayyato wata mace cikin rayuwana da sunan aure.!”
Mommy ta saki baki wann Karon cikin rashin fahimta “Turare kuma.? Mai.. Ni.. wane irin turare.?!” Ta k’arashe tambayar cikin rashin fahimta yarsandar na k’ok’arin janyota ta daka mata tsawa da fad’in “I am Kwaise Maitama. You just can’t arrest me.! Idan gayyata ta ofishin ku kuke zan iya tafiya a nawa motar amma baku Kai kuyi arresting dina a k’asar nan ba. Even your superiors sunyi kad’an.!” Ta k’arashe tana sakin huci ta fito asalin a Kwaisenta.
“And do you think you are above the law.? Just because you are rich and powerful.?!” Haidar ya katseta.
D’aya Dansanda namijin ya tare gaban Haidar yana dannarsa “Calm down Engr. If that’s what she wants let’s do it her way then.”
Ya dubi Mommy cikin risinawa yace “We are sorry Hajiya. We understand that you are an important figure in the society. Zaki iya zuwa ofishin mu a motar ki tareda rakiyar abokiyar aikinmu guda d’aya. I hope that’s ok with you.” Ya k’arashe cikeda risinawa.
Takaici ya cika Haidar ganin yanda ikin tsaro ya lalace wai idan kanada matsayi da mukami cikin Al’umma treatment dinka daban ne. Idan kuwa haka ne zai tabbata kudi da influence da Hajiya Kwaise keda shi baiyi tasiri a shari’an da zasuyi da ita ba because he waged a war on her. Sai yanda k’arfinsa ya k’are.
Haka suka fice salim alim dan Mommy dai bata so taja idon mutane da hankali kanta. Anisa na biye dasu tana hawaye tana ci gaba da rok’on Haidar.
Duk dramar nan da suka gama Hisham na tsaye gaban gadon ta har dai suka fice gaba d’aya d’akin ya rage saura su biyu Hisham da Ummul dake kwance saman gado ido a lumshe.
Hannu yasa ya share hawayen da suka zubo masa. A hankali ya soma furta “You know, when I first met you.. I told myself… Hisham, this is the time.. You’ve finally found her… Your soulmate.. The love of your life.. After all the rejections.. All the heartbreaks..” Muryarsa ya tike sanda ya kuma share hawayen da suka Zubo masa “Daga k’arshe ka hadu da ita. But it turned out to be the worse of all..!” Ya kuma murmusawa yana girgiza Kai “Do you know what’s the funniest thing.. And yet the saddest.. I never got the chance to tell you how I feel about you.. It was all a dream.. Kuma zai tabbata a matsayin mafarki Wanda bazan tab’a farkawa ba.”
Ya hade hannayensa biyu alamun rok’o wasu hawayen na gangaro masa “You are now married to Haidar.. My best friend. He’s like a brother to me you know. Kuma zan iya sadaukar da komai nawa for him if I had to.. Koda kuwa rayuwana ne.. so Please ki daina zuwa mun a mafarki na.. Please..!” Ya k’arashe wasu hawaye masu ciwo na kuma gangaro masa.
A hankali ya soma janyo k’afafunsa da k’yar cikin k’ok’arinsa na ficewa daga d’akin. Aiko yana ficewa yai bursting cikin wane irin kuka yana mai k’unshe bakinsa. Kai da gani kasan direct daga zuciya kukan ke fita.
**
Motan Mommy da su Daddy suka gani ya fice daga hospital ga na ‘yansanda biye dasu ya sanyasu cikin tsananin shock da mamaki. Uwa uba da sukaga motar Haidar biye dana su Mommyn.
Daddy ya dubi Alhaji dake gefensa “What.. What’s the meaning of this..? Motar Kwaise nake gani tareda ‘yansanda.!” Ya share gumin da yaji na tsartsafowa daga goshinsa “Kwaise da D’anta bazasu tab’a barina ba sai sunga bayana Gimba.!”
Alhaji Gimba ya girgiza kai “Kar kayi magana haka Engr. Bamu san abinda ke faruwa ba. Let’s follow them and find out.” Ya k’arashe maganar yana mai sanar da driver da yabi bayan motocin su Mommy.
Girgiza Kai Daddy yake sanda yaga sun nufi hanyar headquarter na yansanda “What.! No way Gimba.. I can’t be seen there.. Bazai yuwu a haskoni a ofishin ‘Yansanda ba it will be a disaster for our business. Kai kasan hakan.!” Yaci gaba da girgiza Kai yana fad’in karshen zamansa da Kwaise harma da D’anta yazo.
Wani Kayan tashin hankalin shine suna isowa kusan kofan ofishin suka hangi masu nad’an rahotanni kowa na jefo masu tambayoyi cikin son sanin mai ahalin ke ciki.
Daddy ya shafe fuskarsa da duka hannaye biyu yana girgiza Kai. Sai wani irin huci da yake furzarwa. Ya dubi Alhaji Gimba “Saida nace maka zuwa police station ba shawari mai kyau bane. Kaga abinda nake sanar dakai. Our company is handling one of the top government infrastructure project at the moment. We can’t afford to lose credibility a idon gwabnati.!”
Alhaji Gimba ya furzar da huci kad’an dan shima abun na neman fin k’arfinsa. Ya dubi Daddy yace “I’ll take care of the media. Zan tabbata basu publishing wani labari ba. Wancan labarin Auren Haidar da suka daura, I’ll make sure they take it off.. Ka shiga ka samu ahalinka.. Bamu San meke faruwa ba. Su d’in suna buk’atar ka.”
Da kyar da sud’in goshi Alhaji Gimba ya shawo kan Daddy ya amince ya nufi ofishin yayinda aka barshi nata kokarin ji da Media.
Daddy yana shiga akai directing dinsa zuwa ofishin daukan bayanai yanda akai detaining Mommy ana koro mata laifukan da ake tuhumarta dashi ga Haidar tsaye a gefe ya kafeta da ido Kai kace shike interrogating din nata.
“D’ansandan yaci gaba “Maiyasa kikai yunk’urin kashe yarinyar.? Shin kinsan turaren da kika bata turare ne mai d’aukeda guba.”
Zuciyar Mommy yaci gaba da tsinkewa. Shikenan boka ya sakata a uku. Ashe guba ya bata matsayin turaren da zai janyo Haidar zuwaga Ummul. Meyasa ta kasa yarda cewa boka mak’aryaci ne.? Dama da ake cewa boka makaryaci ne bata yarda ba amma yau ta yarda. Wato ya bata turare mai guba ciki idan Ummul ta shak’a ta Mutu shikenan sai ita kuma tai zaton asirin dake jikin D’anta ne ya karye kaman yanda Bokan yace. Zatai zaton tsafin Boka ne yai aiki. Ashe ba haka bane annamimin guba ya saka cikin turaren Wanda zai ajalin Ummul shikenan ita kuma ta hau kan aikinsa ne yai tasiri. Kai Kaicon rayuwa cikin b’ata. Gashi nan Boka mushuriki mak’aryaci ya sakata a uku, ya kulleta cikin bala’in da bata san yanda zata wanke kanta a idon mijinta da D’anta ba.
Muryar Daddy suka sinkayo “Kisa Kwaise.?!”
Mommy tai saurin juyowa tana duban Daddy hawaye na kokarin ciko idonta take girgiza masa Kai alamun a’a.
Daddy ya dubi ‘Yansandan “Would you please, excuse us.?”
‘yansandan suka mik’e cikeda risinawa suna fad’in “Sure Sir, of course.!”
Haidar dake tsaye gefe jinjina Kai yake yana duban Daddy bayan ‘Yansandan Sun fice “Matarka tayi attempting kashe ni ta hanyar wann yarinyar da ta auro ta kawo cikin gidan da sunan matata.. Shiyasa ta dage sai nazo gidan na zauna tareda yarinyar. Tayi poisoning d’inta cikin turare sabida motive dinta kawai shine taga bayana. Wann matar ba ita ta haifeni ba.. Kuma yau zata fad’i a yanda ta sato ni.!”
Daddy ya Kai k’ololuwa cikin b’acin rai a hasale ya maida dubansa ga Haidar “Ka daina maganar shiririta a nan.! Kwaise is your real biological mother. She gave birth to you. She’s your mother.!”
Ya maida dubansa ga Mommy “Tell me Kwaise, meke faruwa a nan.. Meye wann yaron yake fad’a..?!”
Mommy taci gaba sa girgiza Kai tana hawaye “Engr bansan komai ba. Wllhi bansan turaren da na baiwa yarinyar matsayin kyauta akwai guba ciki ba. Why would I poisoned her.. What could be my motive.? You need to believe me. Ina son yarinyar nan like my own. Kowa a gidan shaida ne. Ita kanta Ummul shaida ce.!”
Daddy yaci gaba da girgiza Kai yana dubanta “You brought that girl into our family Kwaise. Bansan dalilin ki na dagewa sai kin aura ma D’anki wann yarinyar ba.”
“Her motive’s quite clear. To use her and get rid of me without being detected. Maybe she realises that I’m no longer useful to her. That I stoped being her weapon. She couldn’t use me to get what she wants. So she decided to get rid of me…” Yaci gaba da jinina kai “When I was a child she used to call me…A useless child. Yes useless.! D’ah maras amfani. Haka kike kirana Mommy… Banida amfani cikin rayuwarki.. Yanzu da kika tabbata banida wani amfanin da zan miki.. I couldn’t be what you wanted me to be.. I couldn’t make you proud.! I couldn’t be just like him. Haka ne.?!” Ya k’arashe yana nuni da Daddy hannunsa har rawa yake jijiyoyin jikinsa na kuma mik’ewa.
Daddy ya katsesa “Enough.! I’ve had enough of you and your Son Kwaise. I won’t allow your problems to affect my business in any way.!”
Haidar na huci yake dubansa “Is this about your business again Daddy..?” Yaci gaba da huci yana duban mahaifin nasa “This is about me and my life Dad..!”
“Of course I do not give a damn about you and your chaotic life.!” Daddy ya katsesa da fad’in haka cikin tsananin huci.
Haidar na girgiza Kai cikin rashin yarda yake duban mahaifin nasa. Ya saki murmushi mai ciwo “Those words ain’t new to my ears. But I want you to keep this in mind. You can use all the power and influence you have. Amma ina mai tabbatar maka, your wife won’t get acquitted until she answers all my questions.! Until she pays for all the crimes she’s committed.!”
Bai Kai aya ba Daddy ya daura masa Mari maiji da lafiya su duka suna huci yayinda Mommy tai saurin mik’ewa ta shige tsakaninsu tana kuka sosai.
Haidar na jinjina Kai yake duban iyayen nasa “All I ever wanted is a quite and happy life. Away from all this chaos. Yana maganar Mommy tana dubansa hawaye na gangaro mata. Ta rasa tausayin waye take ji cikinsu gaba daya.
Haidar yaci gaba “Amma Idan wann shine Abu na k’arshe da zanyi a rayuwata zanyi. Na ranste sai na isa k’arshen komai. Mark my words.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice daga room d’in.
Mommy ta dubi Daddy “Engr we need to stop him. Da gaske yaron nan ba cikin hayyacinsa yake ba.”
“Ki min shiru Kwaise. This is all your fault you know. I’ve warned you.. Na Miki gargadi amma bakiji ba. I knew nothing good would come out of this marriage da kika dage sai kinyi ma d’anki. Ga abinda nake Miki gargadi akai amma bakiji ba.”
Mommy ta girgiza Kai “Ka yarda dani Engr wllhi ban saka guba ma yarinyar ba.”
“Just shut up Kwaise.! Meke tsakaninki da wann yarinyar is absolutely none of my business..” Ya kuma matsowa yana nunata da yatsa yana sakin huci “Na gargadeki cewa idan har wann watsattsen auren da kikai ma wann D’an naki ya shafi Kasuwanci na ki kuka da naki auren.!”
“Har yanzu barazana kake mun da Aurena.” Mommy ta katsesa. Taci gaba da jinjina Kai tana hawaye “Shin meye matsalar.? Auren da nai ma Haidar ne matsalar kokuwa dai har yanzu akan Fannah ne da abinda ke cikinta.!”
Cak Daddy ya tsaya ya dago yana dubanta yana jinina kai “You are right Kwaise. You are absolutely right. You should be grateful ban miki korar kare ba bayan abinda kika mun.!”
Mommy taci gaba da hawaye tana duban mijinta nata yanda yaci gaba “Bayan abinda kika min nayi hakuri na zauna dake da abinda kika haifa tsawon shekarun nan.!”
“Nasan albarkacin Haidar naci kake zaune Dani kawo wann lokacin.!”
“Will stop with your guilt tripping Kwaise.! Idan kinsan da haka kar ki bari na tuna Miki abinda kika aikata mun a baya.!”
Mommy na hawaye taci gaba “Meyasa baka barmu munyi tafiyarmu ba nida Haidar idan har zaka rik’esa ka kasa accepting dinsa tsawon shekarun nan.?!” Taci gaba da hawaye “Na sani nayi kurakurai da dama a baya. Kuma babban kuskuren da na kasa yafe ma kaina shine k’iyayyar da na nuna ma Haidar a lokacin da na haifosa ka k’i accepting dinsa.”
Daddy Yaci gaba da jinina kai yana huci yayinda Mommy taci gaba da hawaye.
“How do you expect me to accept your child bayan kinsa na sheganta D’an wata.? Ta ya kike zaton zan rayu da naki D’an na bude ido na ganshi yana girma bayan akwai wani D’an nawa can Wanda na sheganta sa da bakina. A kullum na bude ido naga D’anki Kwaise ba komai yake tuna mun ba face mummunan kuskuren da na tapka. Kuskuren da na zartar da hukunci akansa ba tareda bincike ba.!” Ya jinjina kai kafin yaci gaba “Dik randa naga Haidar sai na tuna akwai D’anuwansa can wanda naki accepting d’inshi tun yana ciki. Ta ya kike zaton naki D’an zai girma da soyayya na.? Ki gode ma Allah da na bama D’anki sunana.”
Cikin kuka Mommy tace “Haidar D’anka ne dole ya amsa sunan ka.”
“Amma kin haramta ma wani D’an nawa Ya amsa sunana Kwaise.!” Ya katseta da fad’in haka jikinsa Har rawa yake.
Hawaye yaci gaba da gangaro ma Daddy “Na tuna miki zaluncin da kika mun ne.?! Kwaise kin kawo wani k’ato yayi fyade wa Matana a cikin gidana.. Da aurena akanta da cikina a jikinta Wanda kika sa na Sheganta shi tin yana ciki baizo duniya ba. Kinsa na rabu da matata a WATA UKU na farkon aurenmu. Kinsa na tura Fannah gidan Yari ta raini cikinta a can ta kuma haifesa a can. A gidan Yari ta haifi D’ah na da na sheganta sabida son zuciya irin naki Kwaise.!”
Mommy tai bursting cikin kuka tana girgiza kai take fad’in “Wllhi Allah shine shaida na ban basa umarnin ya aikata ma Fannah wani abu ba. Sharri kawai nace Ya mata. Allah shine shaida na babu fyad’e a plan d’in.”
“Just shut up already.! Kar ki sake ambatan sunan Fannah da wann bakin naki.!” Daddy ya katseta.
Haidar Ya banko k’ofar Ya shigo cikin wane irin yanayi yake duban iyayen nasa “Wacece Fannah..?!”
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*34*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Kallo daya Daddy yaima Haidar ya watsar. Kaman dai baiji tambayan da yai ba. sai kuma ya kalli Mommy “Kina iya sanar da D’anki zunubanki idan kinso. I’ll send our lawyer to handle your case. As you know, I have a reputation to protect bazan bari ke ko D’anki ku min sanadi ba .” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice.
Haidar yabi bayan mahaifinsa da kallo kafin ya maidoda dubansa ga mahaifiyarsa. Ya dauki lokaci kadan yana tsaye wajen yana dubanta kafin daga bisani ya soma janyo k’afafunsa ya zauna saman kujera mai fuskantar nata “Tell me Mommy. Wacece Fannah.?”
Mommy ta dago idonta masu zuban ruwa tana duban D’an nata kafin ta jinina Kai “She… She was your Dad’s wife.. Matar mahaifinka ce kafin su rabu.”
Haidar ya jinina Kai a hankali “So Daddy yanada wata matar a baya.?”
Mommy ta jinina Kai a hankali.
“What happened then, mai ya faru da ita..? Ina take yanzu.?”
Mommy ta girgiza Kai a hankali “I have no idea Son. Bansan yanda take ba a halin yanzu.. Kuma na nemeta shekara da shekaru ban sameta ba.”
“Meyasa kika nemeta.?” Ya kuma jefo ma Mommy tambaya.
Ta d’ago tana dubansa “Dan na nemi yafiyarta.”
Ya kuma jinjina Kai “So tell me Mommy. Mai kika aikata mata.?”
Mommy tasa hannayenta biyu ta share hawayen da suka zubo mata. A hankali take jinina Kai “Zan sanar dakai komai Haidar. Abinda ya faru a wancan lokacin… Watak’ila ka samu gurbi cikin zuciyarka ka yafe min D’ah na.” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya yayinda Haidar ya zuba mata ido.
Waiwaye…
Years back..!
Borno State, Maiduguri.
Hajiya Kwaise zaune saman kujera a madaidaicin parlorn ta Wanda ya tsaru iyaka tsaruwa a wancan lokacin. Kuka take sharshar da hawaye a lokacin da taji sautin wayar landline na gidan na kururuwa. Ta mik’e da kyar ta isa ta daga wayar. Daga d’aya b’angaren muryar Aliyu Maitama ta sinkayo “Kwaise an d’aura auren.. An daura auren.. An daura aurena da Fannah..” Yanda yake maganar zaka fahimci kaman Wanda aka saka shi dole haka yake maganar. Bata k’arasa sauraro ba ta saki wayar ya fad’i kasa tana mai kuma rushewa da kuka. A haka Asshe ta k’araso ta sameta. Asshe k’anwarta da tin bayan da Kwaise tai aure rik’on Asshe ta dawo hannunta dama ba wani girme mata sosai tai ba kuma su biyu iyayensu suka Haifa.
Mommy ta dago tana duban Asshe cikin rawar murya “Asshe Aliyu yayi aure.. Aliyu ya auri d’iyar leburan dake aiki k’arkashinsa Wanda block na gini ya fado ya fasa masa Kai ya rasa ransa dalilin haka. Asshe Aliyu na ya aure ‘yar wann mutumin..!” Ta kuma rushewa da kuka.
Asshe ta dubeta cikeda tausayawa “Aunty Kwaise mijinki loves you. Wllhi koda ace yayi aure bazai daina sonki ba. Ni fah ban taba ganin wacce mijinta ke mata irin Son da Uncle Engr ke Miki ba. He loves you dearly. Zai komai dan farin cikin ki Aunty Kwaise. Keda kanki kin fada Aurensa da wann yarinyar Fannah k’addara ce kawai batada kowa bayan mahaifinta da ya Mutu ta dalilin aiki k’ark’ashin ma’aikatan mijinki da yake. Wllhi na tabbata dan ya taimaketa ya aureta. Ba wai dan yana So ba ko dan ya daina sonki. Idan ba so da mijinki ke Miki ba. Mutum kaman Engr Aliyu matashi mai tashen kud’i ga k’uruciya ga dama na rayuwa da ya samu ai da tuni ya cika gidan nan da mata sai yanzu da k’addarar hakan tazo. Dan Allah kar ki saka wani Abu a ranki.”
Mommy ta dago tana share hawaye “Asshe bazaki taba ganewa ba. Namiji Akan mace sunansa namiji bazakiyi shaidarsa ba. Nidai bazan iya sharing Mijina da wata ba balle wann bagidajiyar ‘yar lebura.”
Asshe ta furzar da huci “Toh ya kike so ai yanzu.?”
Mommy bata iya bata amsa ba sai mik’ewa da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 64