Share this page
d’auki Baba Ali na fice dashi to spend time with him..” Ya d’anyi k’asa da murya yana fadin “I wanted so badly to be with my family.. Shiyasa na fice dashi zuwa toy store..” Ummul ta dubesa da mamaki jin ya b’oye ma iyayensa ce masa da tai ya fice bata son ganinsa bata buk’atarsa. Mai hakan yake nufi.? Shin hakan yana nufin tsananin son da Haidar ke mata ne yasa ya b’oye kalaman da ta furta masa matsayinsa na mijinta ga iyayensa kodai wani dalili ne na daban.? Muryarsa ta sinkayo yanda yaci gaba “Na tura mata text cewa ina tareda D’a na ne so that she shouldn’t worry.” Mommy tace “Ai sak’on da ka tura d’in bazai karya ba.” Daddy yace duk akan sak’o ake wann rikicin. Ina sak’on yake.? Mommy Ta dubi Ummul cikeda confidence ita a dole sune akan gaskiya ba Haidar ba tace ta nuna sak’on da ya tura mata na cewa yakai ma matarsa yaron. Nan ne fah gaban Ummul ya fad’i dan ita dai bama ta karanta sak’on da Haidar d’in ya tura mata ba. Kawai dai bayan ficewarsa da Baba Ali da taga ya tura mata sako kawai sai ta saka ma ranta ya tafi dashi ne kaman yanda tace ya koma yanda ya fito bata bukatarsa tinda taji yace his son needs him and he missed him. Bugu da k’ari da taga Ya d’auki tsawon lokaci bai dawo da Baba Alin ba kawai sai ta saka ma ranta haka d’in ne. Jiki ba kwari ta mik’a ma mommy wayar sanda ta kai daidai kan sak’on. Daddy kaw yace da Mommy “Read it loudly.” Jiki a sanyaye Mommy ke duban sak’on. Daddy yace “Ke muke sauraro Kwaise. Nan kotu muke. Ki karanto a warware matsalar yarana. Murya a sanyaye Mommy tace “Na’am Engr.” Sosai Daddy ya tsareta da ido had’ida jinjina mata kai alamun ta karanta sak’on. A hankali Mommy ta soma karanta sak’on kowa naji _”I will spend time with my son.. Na kosa watannin da Mommy ta d’ibar mana su cika. Na kosa mu kasance tare mu ukun.. Kaman dai ahali. I love you so much Khairy. And I can’t wait to be with you again.!”_ Tinda Mommy ta soma karanta sakon jikin kowa yai sanyi Babu kaman Ummulkhair. Ga kunya da Ya gama lullub’e ta kaman k’asa ya tsage ta nitse ciki. Abinda Hajja dai ta fad’i Ya tabbata hasashen Ummul Ya raya mata wann tunani gameda mijinta. Hajja ta kula da yanayin da Ummul d’in ta tsinci kanta ciki gaban sirakanta sai kawai ta mik’e ta amshi Baba Ali hannun Mommy ta k’arasa ta kamo Ummul tace suje ta bama yaron abincin sa. Ai kaman jira take sum sum tabi Hajja kanta sanne a k’asa suka nufi k’ofa. Haidar Ya saci kallonta daidai sanda suka iso kusan k’ofa zasu fice. Ya kashe mata ido guda yana matse murmushinsa. Harda furtawa a hankali “Mission accomplished.” Labb’ansa ne kawai suka motsa. Ta kuma sadda idonta cikin saurin tana ayyanawa cikin ranta wato Haidar da nufi yai abinda yai. Tabbas hak’arsa ta cimma ruwa tinda gashi an isa gaban Daddy. Gashi ya sata jin kunya da alama shi ko ajikinsa. Dan a iso gaban Daddyn ma yai abinda yai. Sauri sauri ta fice biyeda Hajja tana jin wani sabon kunya na kuma lullubeta. Haidar ya mik’e shima cikeda risinawa Ya kuma bama iyayen nasa hakuri kan kuskuren da yai tareda alkawrin irin hakan bazai kuma faruwa ba in sha Allah. Ya k’arasa ya tattari toys d’in da ya shigo dasu Ya fice yabi bayansa su Ummul da kayan wasan. Daddy ya tsare Mommy da ido. A matsayinsa na D’a namiji idan ya fahimci abinda ke faruwa dai Matarsa ne Tai fin k’arfi ma D’an nasa ta aje masa mata da D’a tak’i bari su tare gidansa Tun bayan da suka d’auro auren Haidar d’in da iyalinsa a karo a biyu. Ya jinjina Kai yana duban Mommy wacce ta d’an sha jinin jikinta. Jiki a sanyaye tace “Engr wai lafiya kake ta kallona haka.?” Daddy yace “Dole na kalleki Kwaise kin shigo da k’ara kotu ashe kece dai mai laifin.” Mommy ta marairaice fuska tace “Ni ce kuma mai laifi Engr..?” Daddy yace “Eh mana.. Laifinki mana. Ni na rasa zaman me iyalin yaron nan suke a nan..? Meye manufarki na aje masa iyali a nan...?” Mommy tace “Engr naga haihuwa fah tayi..” “Toh dan ta haihu sai ki hana ma yaro iyalinsa.? Harda wani watanni da kika d’ibar musu.. A wani aya ko hadisi kikaji hakan.?” Mommy ta girgiza kai kad’an “A’a Engr ba ko d’aya.. Amma ai..” “Babu wani amma a nan Kwaise. Ki kyale yaro ya tafi da iyalinsa haka nan.” “Engr naga wai watanni ukun da na d’ibar musu saura sati biyu ne kawai su cika.” Cewar Mommy a sanyaye. Daddy yace “Su cikite sati biyun a gidansu. Kar iyalin yaron nan su kuma kwana gidan nan. Ki barsu haka su tare yau d’in nan. Kinga dai abinda ya faru hannunka mai sanda D’anki yai Miki. He wants his family next to him. Ya kuma baki matsayin ki as mahaifiyarsa da Ya biyo ta hanya mafi sauk’i da zaki fahimcesa.” Mommy ta jinjina kai “Yanzu yau d’in su tafi Engr.?” Daddy ya kuma gyara zamansa cikin kujera “Toh mai zasu miki a nan d’in Kwaise.?” Mommy tace “Wai dama gani nai idan suka cika watanni ukun sai mu kira namu shagalin taron sunan da bamu samu munyi ba.” “Tafiyarsu bazai hana muku taron sunanku ba Kwaise.” Daddy ya bata amsa yana mai daukan remote control na tv cikin hannunsa. Mommy tace a sanyaye “Shikenan Engr.. Idan haka kace.. Barinje na sanar dasu su shirya.” Ta dan kara duban Daddy da Ya maida hankalinsa kacaukam ga TV tace “Na kawo maka shayin ne.?” Daddy ya girgiza Kai yace “No barshi zuwa dare.” Sai ya k’arada “Kimin kiran yaran nan Haidar da Ummulkhair.” Mommy ta amsada “Toh Engr.” Kafin ta fice. Nasiha mai ratsa zuciya Daddy ya musu gameda zamantakewa kafin ya saka musu albarka Ya sallame su. A ranar dai Mommy ta hakura ta sakar ma Haidar matarsa harma da D’ansa. Kafin dare ta tura wasu daga cikin ma’aikatan gidan suka tafi can gidan Haidar d’in suka gyare ko ina tsaf. A d’aki Hajja ta zaunar da Ummul Tai mata nasiha da Ya danganci aure da zaman aure. Ta k’ara nusar da ita mahimmanci communication tsakanin ma’aurata dan da yawan aurarrki Sun lalace ne sakamakon rashin daidaiton fahimta Wanda lack of communication Ya haifar. Ta k’ara nusar da ita gameda dabarun kula da miji da jawo hankalinsa sann tace duk abinda Ya shige mata duhu a gidan Aurenta she should call her kai tsaye. Koda Ummul ta shigo yima Mommy Sallama kanta a k’asa. Dan yau d’in wani mugun nauyin Mommy din ne ya k’aru a idonta. Mommy tashi mata albarka had’ida jero masu add’uo’i na kariya. Ta rungume Baba Ali cikin hannunta tana jin kaman su bar mata yaron kaman kar su tafi dashi. Sosai yaron Ya shiga ransu kaf gidan jimami da begen tafiyan Baba Ali suke. Haka ba don Mommy taso ba ta mik’a sa ma Yâ Gumsu tana fad’in kullum a kawo mata maigidanta yini. Ummul harda d’an hawayenta sanda suka fito daga b’angaren Mommy dan gaba d’aya yau d’in sosai jikinta yai sanyi jin yanda kowa ke mata nasihohi masu tsayawa a rai. Suna ficewa Haidar Ya shigo wajen Mommyn dan mata nasa sallaman. Ta d’an d’aure fuska ba tareda ta dubesa ba. Ya k’araso ya duka wajen k’afafunta. Hannayenta ya kamo cikin nasa yace “Har yanzu fushi kike Dani Mommy.? Haba Mommy na.. I said I’m sorry fah.!” Ta dubesa a dak’ile “Kaga Haidar ka tashi ka wuce. You can’t keep them waiting.” Ya dan marairaice fuska “Amma Mommy haka zan tafi without your blessings.” Kunnensa ta kama kad’an taja tace “Dan albarka.! Tashi kaje Allah Ya muku albarka. Allah ya kare ku da dukkan sharri..” Haidar ya amsa da “Ameen Mommy na. I love you.” “Maza tashi kaje haka nan..” Tace tana mai gyara zamanta. Ya murmusa yana jin k’aunar mahaifiyar nasa na dad’a ratsa zuciyarsa. Har ya kai k’ofa ya sinkayo muryarta tana furtawa a hankali “I love you more.. May you always be protected.” Murmushi ya saki kafin ya fice yana furta Ameen Mommy na a hankali. ** Koda suka iso gidan sai jikin Ummul Ya kuma macewa. Ta soma tuno abubuwan da suka faru watanni shabiyu baya. Yaa Gumsu tace da ita ta shiga da k’afar dama sanda sukai stepping a main door din gidan. Haka nan Ummul ke taka cikin gidan tana jin wani bak’on al’amari na faruwa da ita. Gidan yana nan a sanin da Tai masa sai wasu yan sauye sauye da baza’a rasa ba. Tinda ta shigo d’akin zuciyarta ke tsinkewa. Taci gaba da tuno abubuwan da suka faru a wann d’akin bugun zuciyarta na k’aruwa. Takai dubanta ga gadon dake d’akin sai tai saurin rintse idonta. Sai tana jin kaman lokacin ne komai ke faruwa. Alamun tab’a k’ofa da taji Ya sata saurin waigowa. Haidar ta gani tsaye daga k’ofa Ya hard’e hannaye yana dubanta. Tai k’ok’arin janye idonta daga gareshi sanda Ya soma takowa zuwa gareta. Ganin sai Ya tuna mata abubuwan da Ya faru tsakaninsu a wann d’akin. Sabon haushinsa da takaicin abinda Ya mata Ya taso mata. Ta janye jiki cikin sauri tana mai k’ok’arin ficewa daga d’akin amma sai Haidar yai saurin rikota. Ta d’an dubesa ba walwala “Ni ka kyaleni.” Ya d’ago gajiyayyun idanunsa yana dubanta “Khairy wai ban baki tausayi ba..” Hararsa ta d’anyi “Aw kaine ma abin tausayi ko ni da kasa naji kunya gaban Daddy.?” Ya murmusa kad’an yana dan ciza lip d’insa na k’asa kad’an “Aw wai ke dama baki karanta sak’on ba kika tada hankali Harda kai k’arata gaban Daddy.?” Kaman zatai kuka tace “Ai kai ka shirya hakan dama. Duka laifinka ne.” Ya kuma murmusawa “How am I at fault here.? Ni sak’on da na tura daban sak’on da kika sanar dasu Mommy daban. I don’t remember telling you nayi wani aure ko inada wata mata ba.. Ban san ina kika samo wann idea d’in ba.” Hararsa ta kumayi “Da kunne na naji kana fad’a ma Aunty Asshe ai. Har cewa kake zata hada maka lefe ko mommy bata sani ba.” Ya dan fito da idanunsa waje “Aw.! wai dama kina lab’e kina jin duk hirarmu da Aunty Asshe.?” Ya dan tsareta da ido “Wait.! Were you eavesdropping?” Ta kuma dubansa kaman zatai kuka wann karon “Ni wann kawai naji fah.. Kuma ban damu ba dan zaman Lagos Ya aureka. Ban damu da kai ba kaman yanda baka damu dani ba. Kuma ni sabida Mommy da Abba kawai na amince da aurenka.!” Sosai taso basa dariya sai Ya dan murmursa yana yana shigar da ita jikinsa “Wow someone’s jealous..! Tell me, do you love me this much.?” Ya k’arashe teasingly bai daina matseta cikin jikinsa ba. Tab’e baki Tai kad’an tana kauda fuska. Ya kamo hannunta yana fad’in “Taho nan kiji.” Ta d’an cije tak’i tabi bayansa. Ya kaikaito yana dubanta cikin marairaice fuska “Please don’t give me this attitude Khairy.. Not tonight please.. Wllhi na yarda you are not an easy woman. I’ve been trying tirelessly to win you back for the past 12 months.. Dan Allah kiyi hakuri yau kam ki saurareni kinji Khairy na. Wllhi na tuba.!” Yanda ya marairaice yana maganar dole ya baka dariya. Ta kuma tsuke fuska kaman bazata bisan ba sai ta tuno jawaban da Hajja Tai mata kawai sai ta tsinci kanta tana mai take masa baya. Suka k’arasa yai musu masauk’i saman chaise-longue. Tsareta da ido yai yana dubanta. Ta d’an dubesa sai ta kauda fuska “Nifa ban son yawan kallo..” “If only you know how much I missed you Khairy..” Ya fad’i bai janye idanun nasa daga barin dubanta ba. Batace dashi komai ba sai kauda fuska da ta kumayi. Haidar ya kamo hannayenta cikin nasa “I don’t know where to start.. Na rasa da wanne zan fara..” Ta dan dubesa a dak’ile “Fara da labarin matarka ta Lagos.” Ya dan murmusa “Khairy are we going to talk about this again.? Wai ni dakata.. How many times do I have to explain myself.?” Ta tabe baki kad’an “Idan ba mata kake dashi a Lagos ba Meyasa zaman can ya aureka..?” Ya dan furzar da huci kad’an sai Ya Ciro wayarsa ya nuna mata fuskar wayar. Hoton road construction ne ya bayyana a fuskar wayar. Ummul ta dubi wayar cikin sanyin jiki. Haidar yaci gaba “Aiki ke kani Lagos. Akwai road project da Kampaninmu keyi a Lagos.. And I’m in charge. So idan kinji na tafi Lagos site nake. Happy.?” Ya k’arashe yana dubanta. Ya dan murmusa “Ai bansan Har haka aka damu dani ake kishi na ba..?” Cikin inina take furta “Ni.. Ni ba kishi nake ba.” Tana maganar tana avoiding k’wayar idonsa irin Wanda kunya ya lullub’e. Murmushi Haidar keyi kafin ya kamo hannayenta cikin nasa. Ya d’anyi gyaran murya kad’an “First, zan fara da baki hakuri Khairy.. Na sani ban kyauta ba in many ways. For the past few months na baki sarari ba wai dan na dena sonki ba. Sai dan Ki samu breathing space.. I thought I was suffocating you Khairy..!” Ya dan kamo hannayenta cikin nasa “Na baki space ne ba don na daina sonki ba sai don kiyi healing.. Because time is the only remedy I believe… But believe me it hurts.. It hurts more than you can ever imagine… Ki yarda dani.. A daddafe nayi watannin nan.. But then I had no choice but to punish myself.. For you..” Ta d’ago ta dubesa da idanunta da suka cika da rauni wann karon. Haidar ya dan numfasa “Now that we are finally together zan cike miki wann gurbin Khairy... I promise to make it up to you.” Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “Thank you for choosing me .. Thank you for being my wife again.. I promise you won’t regret choosing me.. I might not be a perfect husband.. but I’ll try my best to be the best.. Best Partner for you.. And best Dad for your kids.. Our kids.!” Ya kuma matse yatsunta cikin nasa “And this time around Aure mukai na Har abada ba AUREN WATA UKU ba.. Ba Aure sabida wani manufa ba.. Ba Aure dan Daddy ya mallaka min wani project ba. I love you so much Khairy.. And from now henceforth I want you to know that you are my FOREVER.. Mrs Haidar Maitama.” Hawayen da take mak’alewa suka digo saman hannun Haidar. Fuskarta Ya kamo yana dubanta “Forgive me Khairy..! Forgive your Sweetmonster.” Murmushi take tana dubansa hawaye na gangaro mata “Na yafe maka.! Na yafe maka mijina.. Na yafe maka tin sanda Aunty Kwaise ta sanar Dani gaskiyar al’amarin.. Na yafe maka because I always believed you are a good person.. Na yafe maka because I love you.!” Ta k’arashe cikin yin k’asa da muryarta. Kallonta yake kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yana duban yanda lips dinta ke furta kalaman so a gareshi. Bai san sanda Ya janyota jikinsa ya rungume ba. Idanunsa a lumshe yake furta “I love you more.. I love you more.!” Ya k’arashe yana kuma shigar da ita jikinsa. Jin zancen na neman canza salo Ya sata k’ok’arin janye jikinta tana fad’in zataje ta duba Baba Ali. Haidar bai saketa ba yaci gaba da rikitata da kalolin k’aunarsa yana fadin “But his Dad needs you more.. Besides Yaa Gumsu is there to take care of him.” Kaman zata sakar masa kuka take fad’in dan Allah yai hak’uri Ya kyaleta taje ta duba su ta barsu shiru tuntuni. Shima kaman zai kukan yake fad’in idan ta tafi wajen Baba Ali shi waye zai kula dashi. Ta kuma marairaice fuska “Toh ai shi Baby ne.. Kai fah babba ne.” Yaci gaba da shafa sumarta yana duban fuskarta “But I’m your big baby.” Ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta. Haidar ya janye hannayen suna duban juna cikeda so da kauna. “Tell me, am I not your big baby.?” Ta yunk’ura zata kuma shigar da fuskarta cikin jikinsa ya tallafo fuskarta yana tsareta da idanunsa. Ta kuma marairaice fuska zatai magana taji ya kuma had’e bakinsu waje guda. Da kyar Ummul ta samu ta kwaci kanta daga hannun Haidar. Ya d’ago idanunsa da tuni Sun k’ank’ance yana dubanta. Da kyar ya iya d’ago yatsun hannunsa guda uku yana mata alama “3 minutes.. Minti uku kacal na baki.!” Ya furta daga nan yanda yake kishingid’e yana maida numfashi. Lumshe idanunta Tai bayan ta fito daga d’akin tana mai sauk’e ajiyan zuciya. Haidar k’arshe ne Ya kware wajen mantar da ita duk wani b’acin rai da fushi da Ya jefata ciki a baya. A hankali ta furta “I love you.. I love you so much my bigbaby.” Ta tadda Baba Ali baccinsa yake Yaa Gumsu na bisa darduma da alama sallah ta ida. Bata ko bari Ummul ta zauna ba ta fatattake ta da ta koma wajen mijinta ta karada idan Baba Ali na nemanta zata kirata a waya. Cikeda kunya Ummul ta fice ta koma nata d’akin. Kasancewar bata tadda Haidar a d’akin ba ya bata daman fad’awa bathroom tayo wanka. Tsaye Tai gaban wardrobe tana nema tufafi mai sauki da zata sauya. Tana nan a haka taji hannun mutum ya zagayeta Ya rungumeta ta baya had’ida manna mata kiss a dokin wuyarta dake da dashi da dumin ruwan da Tai wanka. Tai wani irin jan numfashi a dan firgice. Ya kaikaito da ita suna duban juna. A dan shagwab’e tace “Ka bani tsoro.” Ya d’an Ware ido “Really I scared you..?” Yai maganar yana janyota jikinsa sosai. Lokaci guda yai kasa da murya “Tell me, ta Ya na baki tsoro..? By… hugging you.. Or.. by… kissing you.?” Yai maganar cikin kashe murya yana kuma shigar da ita jikinsa. Kaman zata sakar masa kuka tace “ All..!” Ya kuma shigar da ita jikinsa yana mai ci gaba da sumbatar wuyarta yake furtawa a hankali “I want you to scare me too.. with your sweet kisses.. Warmed hugs.. And your sincere smile..!” Ya k’arashe cikin kasheta da wani irin salo mai wuyan fasaltuwa. Cikin k’ok’arin janye jikinta take fad’in Ya kyaleta ta saka kaya. Ya tsare fuska yana dubanta “Do you need it.?” Cikeda kunya ta rufe bakinta da tafukan hannu tana zaro ido. Kashe mata ido yai kafin yace “Zo muje.?” Ta girgiza masa kai “To where..?” “To my bedroom obviously.. I have cloths for you there.” Zata kuma magana ya duk’a gabanta yana mai kwantar mata da gadon bayansa. Itakam dariya ma abin ya bata ganin Ya duka ya juya mata baya “Wai mai kake ne.. Meye haka.?” “What..? D’ale mana.” Yace yana nuna mata gadon bayansa. Murmushi mai bayyana hakwara take. Ta d’an girgiza kai kad’an tana nuni da kanta “Wai ni ce zan d’ale baya.?” Ya d’ago gira da ido yana dubanta “Oh mamaki kike.? Of course I’ll give my wife a piggyback to my bedroom.” Itakam dariya da kunya duk sai Ya rufeta musamman da ta d’ale bayan Haidar d’amas ya nufi bedroom d’insa da ita. Saida suka isa d’akin ta raina wayonta dan Haidar dai bai aje mata wani kayan sakawa ba kaman yanda yace. Kaman zata masa kuka take tambayarsa ina kayan nata suke. Ya dan tsuke fuska yana dubanta “It’s not.. necessary.. You don’t need it.. You’ll be fine like this..” Ya k’arashe yana kashe mata ido guda. Kaman zatai kuka take fad’in ita dai tak’i wann wayon. Haidar Ya janyota jikinsa yana lallashinta da fad’in yayi alk’awarin zasu sharing nasa kayan kafin wayewar gari. Nan kuma suka soma sinkayo kukan Baba Ali. Ummul ta dubesa tana girgiza kai “Ka gani koh.. Yanzu ya zanyi na fita a haka.. Daga corridor fah nake sinkayo kukan nasa.. Wayyo Allah na nasan zagawa take dashi dan yai shiru.. Ta ya zan soma fita a haka.?” Ya kamo hannayenta “Relax Khairy.. You stay here.. I’ll go check on them. Ok.” Ya karshe yana dubanta. A hankali ta jinjina masa kai. Ta koma tai zaune tana k’are ma d’akin kallo. A haka Haidar ya shigo da Baba Ali cikin hannunsa idanun yaron tar a bud’e da alama hira zaiyi. Sai cillasa Haidar yake shi kaw yaron sai k’ekata dariya yake. Haidar Ya diresa saman gado yana ci gaba da masa wasa. Ya kwanta ringingine ya dora yaron saman k’afafunsa yana cillasa da k’afafu. D’a da uban duk dariya suke mai cikeda nishadi. Ita kam Ummul sai suka zame mata tv dan sosai suka birgeta. Ganin Haidar ya shagala da wasa da D’ansa yasa ta fice nata d’akin ta sako tufafi mai sauk’i. Haidar ya dubeta sama da k’asa sanda ta turo k’ofan d’akin. Ya dan tsuke fuska yace “Mrs Aliyu, what’s the meaning of this..?” Ta dan girgiza Kai “Mai fah.?” Ya mata nuni da bakinsa zuwa kayan jikinta “I mean, do you really have to wear that..?” Ta dan rausayar da ido dan tasan rigimace kawai irinta Haidar. Sai Ya dan kashe murya yace “But still.. you look spicy..!” Ya k’arashe yana kashe mata ido. Ya dan bud’e mata hannu yace ta k’araso. Cikin tsanaki take takawa har ta isa garesa. Yai mata masauk’i zuwa b’angarensa guda yayinda Baba Ali Ke cikin d’aya b’angaren nasa. Ya had’esu gaba d’aya ya rungume. Ya dan lumshe idonsa kadan “Finally we are together.. The three of us.!” Ya fad’i yana sumbatar su biyun. Sosai ta shige cikin jikin mijinta ga D’anta daga d’aya b’angaren. Mai kuma zata nema a duniyar nan. A hankali take furta kalmar godiya ga Ubangijinta da ya cika rayuwarta da d’imbin albarka. Haidar ya dubeta yanda Tai lamo gefen kafad’arsa “Mrs Maitama.” Ta amsa murya a mak’oshi kafin ta dan d’ago ta dubesa. Haidar yaci gaba “Put him to sleep now.. Let’s have our own time..” Ya k’arashe yana mika mata Baba Ali. Ba musu ta amshesa ta soma kiciniyar basa abincinsa. Haidar ya rik’e rigar nata yana mai fad’in “Allow me.” Batai yunk’urin hanasa ba. Batai yunk’urin dakatar dashi ba har ya saka ma yaron abincinsa a baki da basmala. Haka Haidar yai zaune ya sakasu gaba yana kallon yanda take feeding jaririnsu gwanin bansha’awa. Sosai ya shagala da kallonsu suna k’ara birgesa Har Baba Ali ya samu bacci. Bayan ta shimfid’a Baba Ali Haidar ya umarceta da ta d’auro alwala tazo suyi sallah. Haka kuwa akai. Ya jasu sukai sallah raka’a biyu kaman yanda yazo a sunnah. Sukai addu’o’i da duk wani abinda Ya kamata suyi. Bayan nan ne fah ta yarda lallai Haidar na buk’atan nasa lokacin. Dukda tsananin son kasancewa dashi take a wann daren bai hanata tuno wahalan da ya bata a kasancewarsu ta farko. Haidar ya kula da hakan. Cikin lallama da dabara yake sanar da ita it will be different from the other time. Gently yake biyeda ita. Saida ya tabbata ta mallaka masa kanta, zuciyarta, ruhinta da gangan jikinta gaba d’aya. A haka yai leading nasu zuwa wata duniya da basu tuna kowa cikinta sai su biyun. Kaman yanda yace zai kasance na daban haka d’in ne ta kasance. Ta yarda yayi kewarta ya kuma nuna mata tsantsan k’aunarsa gareta. He made sure wann daren zai tabbata na musamman a tarihin rayuwarsu.. A kwanakin soyayya sukaita nuna ma junansu Babu kaman Haidar da gaba d’aya ya sake rikicewa akanta. Idan suna tare basu tuna komai basu tuna kowa sai su biyun wasu lokutan kukan D’ansu Baba Ali ke dawo dasu wann duniyar. Sunyi nisa cikin faranta ran junansu suka sinkayo sautin kukan sa. Ummul Tai yunk’urin zame jikinta daga nasa tana fad’in zataje ta duba Baba Ali. Rik’eta Haidar yai yana kuma shigar da ita jikinsa. A hankali yake rad’a “Do you know why he’s crying..?” Ta dan girgiza Kai “No.. He’s hungry.. probably..!” Haidar ya kuma matseta cikin jikinsa “Cewa yake he wants a sibling.” Cak suka daina sinkayo kukan yaron. Haidar yaci gaba da rikitata da salon k’aunarsa yana fadin “See I can read his mind.. You don’t need to go check on him.. Just stay and give him a sibling..” Da dabara Ummul ke zame jikinta Har ta samu ta zille masa. Saida ta kai k’ofa taji ya rik’o hannunta. Ya manneta jikin k’ofa had’ida d’ago hab’arta kad’an suna duban juna “I love you Khairy.. I love you so much.” A hankali bakinta itama ke furtawa “I love you too.. I

Chapter 59 of 64