take fad’in “Ammi.. Mommy bazata sake stanata ba ma sai taji cewa had’arin da ya samu Haidar inada hannu ciki..!”
Cak hawayen Asshe suka k’afe “Na shiga uku.! Anisa mai kika zama..? Kin lalata komai kin b’ata komai keda nace kar ki aiwatar da komai ba tareda umarni na ba.!”
Anisa na kuka take fad’in “Har yaushe zan jiraki Ammi.? Har tsawon wani lokaci zaki d’iba kafin ki fitar da Ummul daga rayuwar Haidar.. Duk abinda na aiwatar sabida son Haidar nayi. Ammi I couldn’t wait for you to act.. I had to do it my way.. And I ended up screwing everything up as always.!”
Ta share hawayenta tana huci “But there’s no going back Ammi.. Abinda ya faru ya Riga ya faru. Idan kikai wani abu foolish ko kika tona asirina wajen Mommy. Ba ni kad’ai Mommy zata yak’a ba Ammi.. ‘Yaruwarki will wage a war against you zata tsaneki ne.. ‘Yaruwar da ta rik’eki har kawo Aurenki.. ‘Yaruwar da ta d’aukeki Aminiya abokiyar shawari. The best solution shine ki bar min komai a hannu na.. Ki tsaya a kano ki kashe wutan da Hilal ya kunna.!” Tana ida fad’in haka ta kashe kiran.
Wani irin kuka Asshe ta fashe dashi duniyarta tai mata d’aurin goro. Ta d’aura hannu biyu akai tana fad’in ‘ya’yanta biyu zasuyi ajalinta. Cikin duka abubuwan data aiwatar Bata tab’a tsammanin zai backfiring da yaranta tsamo tsamo ciki ba.
Mik’ewa Tai tana tunanin kuka bai ganta ba. Take ta danna kiran Dije.
Dije tana ganin kiran Asshe tai wata murmushi da gefen fuska. Cikin zuciyarta take ayyana kin kira akan gab’a.
Saida ta Lek’a ko ina ta tabbata babu mai ganinta kafin ta d’aga kiran. Babu b’ata lokaci Asshe ta sanar da ita dalilin kiran.
Inna Dije ta sanar da ita tana gari ta tsammaci ganinta washe gari kafin ta juya Dutse tinda dama a washe garin take shirin komawa. Da wann sukai sallama. Washe gari kuwa kaman yanda suka tsara. Bayan Inna Dije tayima su Umma Sallama cikin mutunci ta nufi gidan Asshe..
Asshe ta dubeta ta kuma gyara zama “Ni da ke munsan sirrikan juna.. Haka ne.?”
Dije ta murmusa “K’walliya munsan abinda muka sani dai.”
Asshe ta furzar da huci “And we have common enemy here.”
“A’a a’a yimin da yaren da nafi wayo.. Mai kike nufi.?” Ta k’arashe tana fiddo idonta waje.
“Ina nufin munada mak’iyiya guda d’aya.. Ita ce Suwaiba.!”
Inna Dije ta murmusa “Anzo wajen.. Ai ni a halin yanzu kallon ‘yaruwa Suwaiba take min ba mak’iyiya ba.”
Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Ban fahimceki ba.. Kina so kice mun keda Suwaiba Kun sasanta..? Kin yafe mata duk abubuwan da tai maki a baya.. Ciki harda mutuwan tilon D’anki.?”
Inna Dije ta murmusa tana kurban soft drink d’in da aka tarbeta dashi “Waye yace miki Dije tana yafiya..?”
Ta kuma gyara zama “Ni da kike gani bana mantuwa kuma bana yafiya. D’aukan fansa farilla ne. Na bama Suwaiba abinda take son gani ne a yanzu dan ta haka ne kawai zan cimma burina kanta.!”
Asshe ta jinjina kai “Toh idan kuwa haka ne bakida Wanda kike dashi da zai taimaka Miki ki kai Suwaiba k’asa kaman ni. Nikeda makullin auren Ummul a hannuna.! Nikeda makullin tashin hankalin da zai tarwatsa Suwaiba ya kaita k’asa.. Ni keda makullin AUREN WATA UKU.!” Ta k’arashe idonta tar cikin na Inna Dije.
Murmushi Inna Dije take tana dubanta “Maiyasa kika kirani.?”
“Kiranki nai mu taru mu had’a k’arfi da k’arfe mukai Suwaiba k’asa. Dan bazan tab’a bari nawa ahalin Ya tarwatse sabida ita da zuri’arta ba. Bazan bari Alakan D’ana da mahaifinsa Ya samu nakasu ba. Bazan bari Na rasa mijina ba. Bazan bari na rasa D’ahna ba. Bazan tab’a bari D’ana ya auro jinin Suwaiba ba. Bazan tab’a bari na had’a zuri’a da Suwaiba ba.!” Ta k’arashe tana huci.
Inna Dije ta murmusa “Idan kina so na taimakeki fayyace min komai.”
Taryan taryan Asshe ta karanto mata yanda Tai da mijinta harma da D’anta Hilal da kudin da ya tura ma ‘yaruwarsa Anisa dan ya rufa mata asiri da cewa da maifin Hilal yai Ya maido masa kud’ad’ensa Har kawo auren da Hilal d’in yace yana son yin Wanda ba kowa yake so ba face ‘yar Suwaiba.
Inna Dije ta sauk’e ajiyan zuciya “Idan Har kina so kiyi ma Suwaiba da ahalinta iyaka da zuri’arki zab’i d’aya kike dashi a nan.”
Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Wane zab’i kenan.?”
“Ki fitar da Tani kishiyar Suwaiba daga kurkuku.!”
Asshe ta d’ago da mamaki tana duban Inna Dije “Tani kuma.? Meyasa zan fitar da ita.. Maiyasa zan fitar da matar da Suwaiba ke fad’i tashi wajen ganin ta fitar da ita.? Maiyasa zan taimaki Suwaiba.?!”
Murmushi Inna Dije tai tana mai fitowa kad’an daga cikin kujeran “Banida tabbaci kan tuban Tani. Da gaske ne ta canza kokuwa wasa da hankalin Suwaiba take kaman yanda nai. Tani a halin yanzu Babu abinda take buri kaman ta shak’i iskan ‘yanci.. Ina mai tabbatar Miki idan har Tani tasan cewa kece Kika fiddata Babu abinda zaki umurceta ta gaza miki shi. Zaki mallaki Tani a tafin hannunki.!” Ta k’arashe shu’umin murmushi irinta gogaggun mata saman fuskarta.
Asshe tai shiru kaman mai nazari. Tabbas fitar da Tani zai mata amfani ta wata fuskar bayan mallakar Tani da zatai. Zata jifi tsuntsu biyu d dutse d’aya. Zataja layi ma D’anta Hilal da hakan.. Tinda ta tabbata ba zaiso mahaifinsa yasan cewa ya tura ma ‘yaruwarsa Anisa kud’ad’en makarantar sa ba. Idan Hilal yai alk’awari baya tab’a sab’awa musamman tsakaninsa da ‘yaruwarsa. Yana k’aunar ‘yaruwarsa da zai iya zaban ya shiga matsala sabida nata asirin ya rufu. Idan ta fitar da Tani hakan na nufin ta samu igiyan d’aure Hilal.
Ta murmusa tana duban Inna Dije wacce itama can k’asan zuciyarta da nata manufan akan fidda Tani da take so Asshe tai.
“K’warai na fahimceki kuma na amince. Idan Har fitar da Tani daga kurkuku na nufin rugujewar Suwaiba na amince zan fitar da ita.”
Inna Dije ta jinjina kai “Suwaiba bazata san kece kika fidda Tani ba. Zan ci gaba da shashantar da ita.. Abin zai kasance kaman dai ni ce nai ma Tani hanyar fita daga kurkuku. Hakan zaisa Suwaiba ta kuma yarda da sakin jiki Dani. A sauk’ak’e zamu kaita k’asa.”
Asshe ta murmusa tana jinjina kai.. Nan take suka shirya komai da yanda zasu gudanar da komai.
**
Bayan kwanaki uku da faruwan wann al’amari Tani ta shak’i iskan ‘yanci. Duk a tunanin Umma Inna Dije ce Tai hanya aka fidda Tani ba tareda tasan cewa Asshe ce ta biya Bakauye kud’ad’ensa harda tara.
Tani taita kuka tana godiya ma Suwaiba da Dije da alk’awarin zama da kowa lafiya.
A b’angaren Hilal koda mahaifinsa Ya tutsesa da maganar kudi Asshe tai karaf tace taimako yai ya fidda sirkar Haidar da aka lak’a ma sharri daga gidan kasu. Taci gaba da matsan hawaye tana fad’in “Alhaji ni bansan wane irin Zuciyar taimako Hilal keda shi ba. Kaf kud’ad’en yayi amfani dasu wajen d’aukar ma surkar Haidar Lawyer da biyan tara. Ina laifin Ya sanar damu ko iyayen Haidar ko shi Haidar d’in halinda ake ciki.. Ni yanzu na yanke shawarin zan d’aga koda k’adarata..”
Katseta yai da fad’in “Ba sai kin saida komai naki ba.. Dama so nake nasan mai yai da kud’ad’en.”
Ya dubi Hilal “Taimako abu mai kyau ne koda ace wasu ka taimaka ba Dangin matan Haidar ba. Amma ka sani komai yanada tsari da hanyar da ya kamata abi a aiwatar duk kyaunsa.. Kud’ad’en nan da kai taimako dasu ka kai munzanin da zaka iya nemansu. Ka d’aukesu matsayin bashi na baka. Zaka tafi kasuwa kai aiki tuk’uru ka nemesu da guminka sann ka biyani kud’ad’ena.” Yana ida fad’in haka Ya mik’e ya fice yana sab’a babbar riga.
Hilal ya sauk’e ajiyan zuciya yana mai lumshe ido. Ya bud’esu ya dubi Amminsa cikin mamakin yanda ta tsara zance ma mahaifinsa.
Kafin yai wani magana ta dakatar dashi “K’warai na fitar da Tani tinda nasan burinka kenan ka fitar da ita ka burge Suwaiba. Sann abu na gaba nasan cewa kud’ad’en da ya baka na makaranta ka turasu ma Anisa. Kuma nasan ko mai zai maka bazaka tab’a cewa ma Anisa ka bayar ba. Abinda nake so kai a nan shine ba kai ba ‘yar Suwaiba.! Ka nemi ‘yar gidan ko waye ka aura amma ba ‘yar Suwaiba ba.!”
Hilal ya girgiza Kai yana duban mahaifyarsa “Kinyi haka ne dan ki d’aureni Ammi..? Sabida haka kika zab’i taimaka masu.?”
“Burinka kenan ai ka fitar da Tani koh..? Toh na cika maka wann burin.. Saura nima ka cika min nawa burin ka fita daga hark’an Suwaiba da zuri’arta. Idan kuma ba haka ba yanda nasa kudi na fidda Tani sai na sa kud’i na kulle Suwaiba.! Idan auren kake so da gaske ka nemi ‘yar gidan ko waye ni zan tsaya maka koda mahaifinka bai tsaya maka ba. Amma banda ‘yar Suwaiba ehe.!”
Ya girgiza Kansa “Kiyi hak’uri Ammi.. You don’t have to go this far.. Kimarki ya wuce haka a wajena.. Maganar aure kuma ki kwantar da hankalin ki na jinginesa , har sai na nemi na kaina kaman yanda Abba yace. Da yardar Allah.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice.
K’arshe dai Asshe ciwon k’arya ta kwanta gudun kar taje duba Haidar.
**
Abuja..
Yau kwanan Haidar ak’alla biyar kenan a coma an doshi sati guda. Babu alamun farkawarsa. Duk wani masoyinsa Ya duk’ufa addu’a gareshi da rok’ar masa sauk’i wajen Ubangijin komai. Babu kaman Mommy da Ummul.. Mommy yini take asibiti yayinda Ummul ke kwana wajensa.
Yau suna zaune saman doguwar sofa dake fuskantar gadon da Haidar ke kwance bisa, na’urar nasara Sun masa k’awanya. Su duka biyun Sun saka shi gaba sun tsura masa ido.
Mommy taci gaba “A lokuta da dama mukan mance wasu ni’imomin da Allah yai mana na d’an lokaci ne ba mai tabbata ba… Allah yakan mana kyauta da samun wasu mutane cikin rayuwarmu. Kaman ‘ya’ya, Iyaye, miji, mata da sauran makusanta. Wann kyautar ba mai tabbata ciki.. Ba Wanda yasan adadin kwanaki, watanni, a’a shekaru nawa zakuyi tare kafin Allah Ya amshe wann kyautar.. Shin kayi appreciating wann kyautar.? Shin ka sauk’e nauyin da aka d’aura maka na hakkoki..?” Ta juyo tana duban Ummul da idonta masu rauni “Ina rok’on Allah yasa da sauran rayuwar da zamuyi tareda Haidar a gaba.. Ina rok’on Allah Ya tashi kafad’unsa Ya raya mun shi cikin aminci Ya zamo majib’icin Al’amaransa..” Ta kamo hannayen Ummul cikin nata baya ta share hawayen da suka gangaro mata “Ina rok’on Allah Ya nuna mun zuri’ar Haidar kafin na bar wann duniyar Ummul.. He’s all I have.. I can’t lose him..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.
Ummul ma hawaye ne suka ciko idonta. Ta shiga jinjina kai cikin k’ok’arin k’arfafa ma Mommy gwiwa, hawaye na gangaro mata “Mommy Haidar zai tashi cikin yardar Ubangiji.. Zakuyi rayuwa irinta D’ah da mahaifiya mai cikeda albarka da aminci.!”
Ta d’ago tana duban Ummul wacce itama d’in Mommyn take duba hawaye fal idonta.
Ta kuma kamo hannayen Ummul cikin nata “Na fad’a zan k’ara fad’a, kin amsa sunanki Uwar alkhairi.. Kinzo da d’imbin alkhairi cikin ahalinmu.. Ummulkhair.!” Ta ambaci sunanta cikin wane irin siga mai nuni da yarda da aminci. Ummul ta d’ago ta dubi Mommy a sanyaye jin yanda ta ambaci sunanta. Mommy taci gaba “I entrust my son to you.. Please take care of him.. Be patient with him.. Don’t let go of his hand.. Help him find his way.. Nasan zaki iya.. Allah ya zama maku jagora Ya albarkaceku rayuwarku da zuri’a ta gari.”
Sai Ummul ta sadda idonta k’asa cikin jin nauyin Mommy.
Mommy ta murmusa kad’an tana dubanta kafin tace “Tashi ki shiga alwalanki.. Ni zanje na samu Daddynku naga sak’on sa yana jirana a reception.”
Ummul ta jinjina kai a hankali tana mai amsawa kafin ta mik’e ta nufi bathroom.
Koda Mommy ta mik’e sai ta nufi jikin gadon Haidar.. Ta dafa goshinsa tana dubansa. A hankali ta furta “My handsome Boy. Allah ya baka lafiya.” karanto masa addu’o’i samun sauk’i tai. Ta sumbaci goshin nasa cikeda so da k’auna kafin ta fice.
Tana ficewa hawaye suka gangaro daga lumsassun idon Haidar.
A hankali yatsarsa guda ke motsi.. Ya soma k’ok’arin bud’e idonsa da suka masa nauyi. A haka Har ya bud’esu tar yana kallon sama.. Komai ya soma dawo masa gameda had’arin da sukai.
Ya tuna sanda motar ta sauk’a saman shoulder.. Ya tuna tsallen da yai ya rufe Ummulkhair gudun kar wani abu ya sameta. A hankali ya kai hannunsa ya zame na’urar dake hancinsa lokaci guda ya furta “KHAIRY.!”
A daidai lokacin Ummul ta fito daga bathroom.
Haidar na jin an tab’a k’ofa ya kuma lumshe idonsa kif.
Ummul takai dubanta garesa. Batasan ko idonta bane amma sai taga kaman ya motsa daga kwancen.
Ta nufi jikin gadon nasa Tai zaune saman kujeran da take kusan yini akai tana dubansa dake nan jikin gadon. A ‘yan kwanakin da sukai asibitin..
Tagumi tai da hannayenta biyu had’ida tsura masa ido daga nan yanda yake kwance. Ta shiga tuno kalaman Mommy a gareta wanda tamkar amanar Haidar d’in ta damk’a hannunta. Sai ta tsinci kanta da shakku da kokonto musamman da ta tuna kafin had’arin ya faru ya furta mata cewa he’d set her free.. Zai sawak’a mata. A b’angaren guda ga Mommy tace don’t let go of his hand..! Mai zai faru idan k’addara bai bata daman sauk’e alk’awarin da ta d’aukar ma Mommy ba.? A wani b’angare na zuciyarta tana tunanin aurenta ya k’are a daidai wann gab’ar bayan ta d’aukar wa mahaifiyarta alk’awarin bazata waiwayi gida ba har sai ta cika watanni uku da aure. Wani k’alubale zata fuskanta bayan ta koma gida.? Shin ta Ya zata fuskanci Umma da sauran ahalin gidansu idan har aurenta Ya Mutu. Auren da ga yanda Ya kasance Tun farko.. Tabbas batasan yanda zata fuskanci Umma ba muddin aurenta Ya k’are kafin aje ko ina.. Ita duk ba wann ba. Ko kiran waya Umma ta haramta mata mai zai faru idan ta koma da sunan auren ta Mutu.? Ta lumshe idonta a hankali tana furtawa cikin zuciyarta ‘Allah duk yanda kayi daidai ne.! Ka shiga al’amari na ka zamto majib’icin lamrana.!’
Ta bud’e lumsassun idonta ta zuba su tsaf akan Haidar dake kwance.
Sosai k’irjinta ke bugu sanda Takai hannunta dake tsananin rawa mai d’aukeda damshin ruwan alwala tana shafa goshinsa zuwa sumarsa a hankali. Abunda tasan ko bindiga za’a saka mata idan idonsa biyu ne bazata tab’a iya yin hakan ba.
Tamkar electric shock haka Haidar yaji sauk’ar hannun nata saman goshinsa. Har lokacin bai nuna alamun farkawa ba.
A hankali taji tana samun natsuwa, bugun zuciyarta na daidaita bata daina abinda take ba.
Ta tsinci kanta tana mai sakin Murmushi a yayinda take dubansa. Har lokacin bata daina shafa goshinsa zuwa sumarsa ba “Kasan mai..!” Ta furta a hankali had’ida gyara zamanta. Ta d’aura hannunta saman yatsunsa a hankali “Kanada sa’a. Kai d’an gata ne.. Ina nufin kanada mahaifya da take matuk’ar k’aunarka..!” Ta k’arashe maganar cikin sanyin jiki tunowa da nata mahaifiyar da tai da kuma irin rabuwar da sukai bayan tayi aure. Ta jinjina kai a hankali tana share hawayen da suka gangaro mata. Sai ta d’an tsura masa ido kad’an “Kanaga zan iya sauk’e nauyin alk’awarin da na d’aukar ma Mommy.?”
Sai ta d’an girgiza kai “Na tabbata da idonka biyu zaka ce.. Ke! Get out of my face.! You don’t want to have a monster for a husband.!” Tai maganar cikin tsarewa ita a dole tana kwaikwayonsa.
Sai kuma ta bama kanta dariya. Ta murmusa kad’an tana mai tsura masa ido tsananin tausayinsa kwance cikin k’irjinta. Tai raurau da ido Kaman mai shirin kuka tace “Watak’ila You are a bit of a Monster, but you are also sweet.. So sweet…. Sweet Monster.!” Taci gaba da sakin sassanyar murmushi tana dubansa “Na gode da ka ceci rayuwata.! Na gode da rayuwata ta kasance mai mahimmanci a wajenka. Allah ya baka lafiya.!” Ta k’arashe tana k’ok’arin mik’ewa. K’ok’arin zame hannunta daga nashi take amma mai .? Sai ji tai gam Haidar ya tamke hannunta cikin nasa.
K’irjinta yai wani irin bugawa. Ta zaro ido waje tana jin bugun zuciyarta na k’aruwa. Ta kasa juyowa ta dubesa sai rawa da jikinta yake.
SameenAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*41*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Duk sai ta daburce ta rasa mai zatai. Ta kasa furta komai sai duban juna da suke su duka biyun… A haka aka turo k’ofan d’akin.. Ba kowa bace face Mommy. Ganinsu a haka yasa Mommy saurin k’arasowa murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta. Farin cikinta ya gaza b’uya.
“Haidar. My son.! Alhamdulillah.. Haidar ka tashi..!” Sai kuka ya b’alle ma Mommy. Ta d’aga hannayenta sama tana fad’in “Alhamdulillah.! Allah na gode maka da ka tashi D’ah na. Allah na gode maka..!” Hawaye na gangaro mata tafukan hannayenta tallafe da fuskan Haidar din duka b’angare biyu taci gaba “I can’t believe you are finally here with us again son.. You know, I don’t mind losing everything.. But.. Amma bazan iya rasaka ba Aliyu… Bazan iya jure rashin ka ba..!” Ta daga hannayenta guda biyu sama “Allah na gode maka daka tayar min da D’ahna… Allah na gode maka for giving me such a blessed opportunity to be with my son again..!” Ta k’arashe tana mai rungumo kansa daga nan yanda yake a kwance. Dole duk Wanda ke duban Haidar da mahaifiyarsa su basa tausayi.
Ummul ta share kwallan da suka zubo mata. Ta janye jikinta ta matsa gefe kad’an cikeda farin ciki musamman yanda taga farin ciki Ya mamaye Mommy.
Mommy ta dubi Anisa da shigowarta kenan tace maza ta kirawo Likita. Cikin sauri Anisa wacce itama farin cikinta had’ida mamaki Sun gaza b’uya ta shiga jinjina akai tana fad’in “Sure Mommy. Right away.!”
Koda Likita ya shigo tambayoyi ya soma masa yanda ya fara da tambayarsa meye sunansa.
Shiru Haidar baice komai ba sai kallon da yake binsu dashi d’aya bayan d’aya. Zuciyar Mommy yai wani irin yankewa ganin irin duban da Haidar ke masu tamkar Wanda bai tab’a saninsu a rayuwarsa ba. Duba irinta rashin sani.
Mommy ta soma girgiza Kai tana duban Haidar tana duban Likita “Dr.. Meke faruwa da D’anah..? Why can’t he say anything..?”
Dr yai k’ok’arin calming Mommy kafin ya dan soma ‘yan dube dube dangin su ido da k’irji ma Haidar dake nan kwance yana musu kallon rashin sani musamman Mommy.
Mommy ta dubi Haidar ta kuma dubi Dr “Likita sanar Dani meke damun D’ana.?”
Dr ya girgiza Kai kad’an had’ida furzar da huci kafin ya maida dubansa ga Mommy “I’m not sure if he’s having a temporary memory loss.. But there are some testes he has to undergo ta haka zamu iya fahimta matuk’a baiyi magana ba har na tsawon dak’ik’ai.”
Mommy ta lumshe idonta hawaye suka gangaro mata. Taci gaba da duban Haidar tana hawaye take girgiza Kai.. Ta rungume kan Haidar cikin k’irjinta hawaye naci gaba da gangaro mata. Mai zai faru idan Haidar ya mance ta.? Mai zai faru idan D’anta bai kuma tuno ko wacece ita ba. Just when she thought rayuwa ta basu daman kasancewa tare a karo na biyu kwatsam wann tashin hankalin ya Kunno Kai.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.!
Cikeda tsananin tausayi Ummul ke duban Mommy da Haidar hawaye na gangaro mata. Allah sarki Mommy ta jira farkawan D’anta ta sanar dashi how much she loves him sai gashi ya farka amma ba Lallai ya kuma sanin ko wacece ita ba.. Kai Lallai rayuwa abar tsoro ce.
Anisa ce ta kamo hannun Ummul itama guntun hawaye ne cikin idonta “Let’s go Ummul. Let’s wait outside.. Mommy needs some time with her Son alone.”
Ummul duban Anisa kawai take tana Jin zuciyarta na wani irin yankewa.. Tamkar rak’umi da akala haka tabi Anisa suka fice daga d’akin.
Kan Mommy na kife gefensa tana hawaye taji hannun Haidar saman nata.
“Mommy.!” Taji ya furta a hankali cikin murya irinta majinyata.
Ta d’ago tana dubansa yayinda Idanun Haidar ke kallon sama.
“Aliyu..!” Ta furta a hankali tana dubansa “Ka.. Kana iya magana..? Ka gane ni..? Ka.. Ka ambaci Mommyn ka.!”
Still idanunsa na duban sama yake fad’in “Even back then.. Lokutan da kike hukunta ni bisa laifin da ba nawa ba ban tab’a mance ki ba Mommy.. And do you know why.?!” Ya k’arashe yana mai karkato da fuskarsa suna fuskantar juna shida ita. K’walla ne tab cikin idonsa yayinda hawaye suka ci gaba da gangaro ma Mommy.
Haidar yaci gaba “Because you are my mother.! Ban tab’a tunanin rejecting d’inki matsayin mahaifiya ba. Haka ne.?”
Mommy taci gaba da hawaye yayinda Haidar yaci gaba da jinjina Kai siririn hawaye na gangaro masa “Koda ace wann D’an talikin yaron babu abinda yake mafarki da buri sama da soyayyar ki da kulawarki.. Not once have I ever looked down on you..!” Ya lumshe idonsa siririn hawaye ya gangaro masa.
Mommy ta lumshe idonta hawaye suka gangaro mata. Tana tuna rayuwar k’unci da ta ba ma d’anta ba tareda tayi la’akari ba.
Haidar yaci gaba da jinjina Kai yana duban mahaifiyarsa “Dukda duka wad’ancan abubuwan da kika mun.. Dai dai da rana d’aya Mommy ban tab’a danasaninki matsayin mahaifiya ba.. Ban tab’a hanaki yanke wani hukunci na rayuwata ba.! You dictated my whole life.. Karatuna..! Aikina.! Daga k’arshe har aure na Mommy… Kece kika zabo matar kika kuma yi a lokacin da kike so koda auren ya kasance k’ark’ashin yarjejeniya.! Koda ban kasance wann D’an da kike so mahaifinsa yayi alfahari dashi ba. Ban tab’a taka wani dokanki ba sabida ina ganinki matsayin mahaifiya.!” Suka ci gaba da duban juna hawayen Mommy na k’aruwa.
Haidar ya maida dubansa ga duban sama “Amma daga lokacin da na dubeki da kallo na k’ask’anci.. Na Miki kallon tir da zama mahaifiyata. Na kulle ki a kurkuku Mommy.. Na fad’a Miki kalamai masu tsanani Wanda duk rayuwar da mukai lokutan baya ban tab’a fad’a Miki irinsu ba.!” Sai ya d’an girgiza Kai kad’an “Ummulkhair..!” Ya furta a hankali kafin yaci gaba “Thanks to her na fahimci ke d’in Mahaifiyata ce. Kuma ba’a tab’a iyaye irin haka a zauna lafiya.!” Ya Kuma duba Mommy kafin yaci gaba “Na fad’a Miki kalaman ne cikin b’acin rai bayan kin sanar Dani labarin yanda kika salwantar da ahalin mahaifina... D’anuwana ko ‘yaruwata dake ciki bai zo duniya ba da kuma matar mahaifina da batada hakkin komai..!” Yaci gaba “Na mance cewa dukanmu ‘yanadam ne.. And we all have our shortcomings. Na mance cewa we all make mistakes and We are far from being perfect…!” Yaci gaba da duban Mommy daga nan yanda Yake kwance “Watak’ila na shiga hurumin da ba nawa ba..! She was right Mommy… Khairy was right, I shouldn’t have looked down on you.! I shouldn’t have locked you up in jail..! I shouldn’t have said all those horrible words to you.” Ya d’an karkato sosai yana duban mahaifiyarsa. Hannunsa na matuk’ar rawa ya d’aura saman na Mommy. Mommy ta dago da idonta masu zuban ruwa tana duban Haidar da kuma yanda ya d’aura hannunsa saman nata.
“Please forgive me Mommy..!” Ya k’arashe muryarsa na shaking sosai. The sincerity in his voice was clear.
Sai Mommy ta rungumosa daga nan yanda yake kwance saman gadonsa. Cikin kuka take girgiza Kai tana fad’in “Baka mun komai ba Aliyu.! Tun tasowarka ni ce na cuzguna maka na bak’anta maka rayuwa sabida son zuciya....! Tabbas abinda mutum ya shuka shi yake girbewa. Na cutar da Fannah da abinda ke cikinta dan na samu dawamammen farin ciki a cikin gidana. Shi kuma alhaki kwikuyo ne. Sai na samu akasin haka tsawon shekarun nan. Ban samu wann farin cikin ba. Bakada laifi ta ko wace fuska Haidar kuma banji ciwon abinda ka mun ba sai ciwon abinda ni na jima ina maka. Na aza maka nauyin zunubaina bisa kafad’unka ba tareda hakki ba.” Ta numfasa hawaye na kuma gangaro mata “Aliyu D’anah ina matuk’ar k’aunar ka.. Ina rok’on Allah ya bud’e Zuciyar D’ah na ya mun kwatankwacin kaunar da nake masa.!” Ta k’arashe hawaye da murmushi saman fuskarta.
Ya rik’e hannun Mommy cikin nasa sosai “I would pick my mother to be my mother again in any and every life time..
Farin ciki ya gaza b’uya a fuskar Mommy cewa da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 64