Share this page
jiya aka kawo mana wani case d’aki d’aya aka raba da labule aka aje mata biyu labule ne kawai Ya rabasu. Ina addini cikin wann al’amarin. Ga yaran nan haifo su ake ba mai zuwa makarantan islama balle na boko.. Ta ya za’a ce kana mutum mai hankali da Allah Ya halicceka da k’wak’walwa bakada tsari a rayuwarka.? Haka zakiga yaran Sun girma wasu ma a mak’ota suke kwana dan babu d’akin kwanansu a gidan mahaifinsu. Yarinya budurwa ace ita zata nemo ma kanta abinci ubanta mahaifi na nan da rai amma baisan yaya d’iyarsa take cin abinci ba. Kuma zaki samu bai fasa aure ba bai fasa haifo wasu yaran ba.. An bar yara kara zube an jefa rayuwarsu cikin garari Tun suna k’anana. Ta ya za’a tsammaci Al’umma mai nagarta da irin wann tauye hakki da ake ma wad’ann yaran da tuni Sun zama victims of circumstances.” Hajja ta jinjina Kai “Haka ne Suhaga.. Da yawa an sha’afa da hakkin yara na iyayen kawai ake hangowa. Tabbas iyaye sunada girman hakki akan ‘ya’yansu wanda bayan biyayya ga Allah da manzonsa sune suka biyo baya. Amma sai muna mance kafin mu Gina irin wad’ann yaran sai mun fara sauke nauyi da hakki nasu dake rataye wuyanmu Wanda za’a tambayemu akai. Dole mutum yai k’ok’arin Gina yau dinsa da kyau dan gobensa Ya inganta. Allah ya iyar mana da tarbiyar yaranmu ya bamu ikon sauke nauyi na zama iyaye da ratayu wuyanmu gwargwadon iko.” Suka jinjina kai suna amsawa da Ameen. Ummul dake mak’ale daga k’ofa ta juya da baya a hankali ta nemi waje ta zauna tana tunanin nan zuwa wani lokaci kadan wann nauyin zai hau kanta. Cikin zuciyarta take addu’an Allah Ya iya mata Ya dafa mata Ya bata ikon sauke nauyin dake gab hawa kanta. ** Gaba d’aya hankulansu ya karkarta ya koma ga jinyar Hisham. Daga Hajja Har Ummul Sun aje zancen tafiyar Ummulkhair Kano. Zuciyar Hisham fari tas dan dama wann dalili yasa yai ma kansa abinda yai. Ya d’auki wann risk din dan ya karkatar da tunaninsu da hankulansu. Sunyi waya da Haidar ya sanar dashi cewa Sun tafi da mahaifiyarsa can wani k’auye ne garin magani Shiyasa bai samu komowa bakin aiki ba. Sam Hisham bai sanar da Haidar cewa shine baida lafiya ba. Haidar yai shiru yana saurarensa sai kuma yace “Amma.. Meyasa baza’a kawo ta nan Abuja Asibiti ba Hisham. Idan ta kama a fitar da ita meyasa bazaa fitar da ita ba..? I see no reason da zaisa ka dauki mahaifyarka ka kaita wani jeji da sunan neman magani.. Meye amfanin karatun ka ne wai.?” Hisham Ya k’ak’aro murmushi “Engr kenan. Kasan ku yan bokon nan kunyi imani da boko amma ita Hajja tafi son na gargajiyan kuma kasan ance magani dace.” Yana maganar yana tamke fuskarsa sabida zogi da yake ji. Haidar Ya jinjina kai ba tareda yace komai ba. Hisham ya k’arada “Nace.. Ya labarin Ummulkhair kuwa..? How have you been coping..?” Haidar ya dan lumshe ido had’ida furzar da huci kadan “Every minute passes by feels like a century…” Cikeda nuna kulawa Hisham yace “Haidar I’m sorry.. I’m so sorry brother bana tareda kai a irin wann lokaci mai matuk’ar wahala.” Haidar ya katsesa “You have your own problems to deal with Hisham.” Ya danyi fasali kafin yaci gaba “Abu d’aya da nakeda yak’ini is that I will find Khairy… I will definitely find her no matter the cost… I will never give up.!” Yanda yake maganar with so much courage and determination sosai ya haifar ma Hisham fad’uwan gaba. Ya had’iyi miyau da kyar kafin ya k’ak’aro murmushi yace “I trust you Abokina. The word giving up has never been in your vocabulary.. Keep searching until you find her.” Haidar baice dashi komai ba sai duban Anisa dake tunkaro yanda yake da yai. Taci Uwar ado kaman mai zuwa gidan biki. Sai yace da Hisham “We talk later..” Daga haka sukai sallama ya katse kiran. Anisa ta k’araso tana ci gaba da k’wark’warsa hannunta rik’eda k’aramin paranti. Fuska d’aukeda murmushi Tai masa sallama. Ya amsa babu yabo babu fallasa. Ta aje masa tray din tana fad’in “Sannu da hanya. Mommy tace yanzu sauk’ar daga Kano.. Ya hanya..? Ya ka baro su Ammi.?” A tak’aice ya amsa mata sai gani tai ya mik’e yana amsa waya Wanda ga dukkan alamu aiki Ya Shafa. Baiko bi takan ta ba ya fice yana amsa kiran. Anisa tabi bayansa da kallo kaman zata rusa ihu. Ko kallo fah bata ishesa ba.. Tazo tana tarbansa amma ko kallanta bai ba balle yaci abinda ta kawo masa. K’atutun bak’in ciki Ya tokare mata mak’oshi sanda ta waiga ta kalli k’atoton hotonsu shida Ummul Wanda akai masu a ranar bikin tariyarsu an kafa a parlorn kaman ka kirasu su zo. Nan taji k’walla ya ciko idonta ta mik’e ta isa jikin hoton. Cikin zuciyarta take fad’in ‘Meye ta fini dashi Haidar.? Meyasa bazaka mance da ita ba.? Meyasa bazaka hak’ura da ita ka so ni ba. Wllhi zan maka komai matuk’a kaso ni.. Ni Kai kawai nake so.. Dan Allah ka fahimce ni.’ Ta k’arashe zancen zucin nata tana Shafa hoton daidai fuskar Haidar. Mommy dake daga jikin staircase tanata kallonta tana karantarta daga nan yanda take tsaye. A hanakali Mommy ta soma takowa cikin parlorn. Anisa ta waigo da sauri tana duban Mommy. Murmushin da yafi kama da yak’e ta sakar ma Mommy. Mommy ma ta maida mata Martanin murmushin. “Sannu da sauk’owa Mommy.” Anisa tace tana risinawa. Da murmushi saman fuskar Mommy ta amsa “Sannu Daughter.” Sai takai dubanta ga parantin dake aje saman side table “A’ah! Ina Aliyun.. Har ya fice ne wai.?” Anisa ta jinjina Kai Jiki a sanyaye “Ya fice ko ruwa bai sha ba Mommy..” Ta marairaice fuska “Mommy I’m worried about him.. Bakiga yanda ya fice ba duk bashi a hayyacinsa. Ina fata a samu Ummul very soon..” Ta k’arashe tana kai dubanta go hoton Haidar da Ummul fuskarta fal damuwa. Mommy taci gaba da takowa tana jinjina Kai a hankali. Ta isa jikin pic din itama. Idonta naga hoton take fadin “Wherever she is. I hope she’s safe.” Anisa ta jinjina Kai. Cikin zuciyarta tace ‘Tana d’aukeda jaririn ciki. Jikanki da bazan tab’a bari ki sani ba. A fili kuwa sai ta kuma marairaice fuska tana duban Mommy cikeda kulawa “But.. Mommy mai zai faru idan bata dawo cikin rayuwar Haidar ba. Haka nan.. Zai k’arashi rayuwarsa a gantale Mommy..? It’s been three months now.” Tai maganar kaman zatai kuka. Mommy ta tsareta da ido sai ta d’an girgiza Kai kadan had’ida furzar da huci “I don’t know Anisa.. Bayan yarinyar can da tai masa asiri bana jin Haidar Ya taba son wata mace except Ummulkhair..” Ta danyi fasali “Ban sani ba.. Kodai zai so wata a gaba kodai ni ce zan sake aura masa wata.” Anisa tai sauri ta dubi Mommy “Mommy kina nufin zaki sake aura ma Haidar wata matar idan Ummul bata dawo ba..?” Mommy ta dubeta sai tace “Why not.! Idan har a baya lokacin da bai daukan magana na da mahimmanci Ya amince da zab’ina Maiyasa yanzu bazan sake zab’ar masa mata ba. Matsalar kawai ban san wace zan zab’o masa mai hankali kaman Ummulkhair ba..” Anisa ta sha jinin jikinta kanta a k’asa. Mommy ta kafeta Da ido sai ta gyara zama tace “But.. I have someone in mind already.. Saidai ban sani ba ko zata amince dukda itama inada iko akanta..” Anisa ta d’ago a zabure tana duban Mommy. Murya har na rawa take furta “Mommy.. I don’t think akwai macen da zata guje ma auren Haidar duk had’uwar ta da isarta.. He’s every girl’s dream.” Mommy taci gaba da dubanta murmushi saman fuskarta tace “You think so.?” Anisa ta jinjina Kai “Hundred percent sure.!” Mommy ta kuma jinjina Kai “Anisa what if.. Kece wann yarinyar da nai sha’awa ma D’ana Haidar..” K’iris ya rage Anisa bata yanki jiki ta zube k’asa ba dan a bazata taji maganar Mommyn. Tama kasa yarda da abinda kunnenta yaji mata. Ta girgiza Kai cikin rashin yarda tana duban Mommy “Mommy… Ni..? Kike so Haidar ya Aura.?!” Mommy ta jinjina mata Kai “Why not.!” Mommy tace cikeda kulawa. Ta k’arada “You are his cousin sann ko da ace Ummul ta dawo gidan Haidar nasan baza’a samu matsala daga wajenki ko wajenta ba.. I’m sure ku biyun zaku fahimci juna… But I’d have to ask you this question. Do you love Haidar..?” Anisa wacce ta koma tamkar statue baki sake take duban Mommy. Ta kasa gaskgata abinda ke faruwa. Mommy ta kuma jefa mats tambayar sai Anisa ta fashe da kuka. Mommy ta kamo hannunta tana girgiza Kai “A’a Anisa meye kuma abun kuka. Kinga idan baki sonshi bazan tak’ura ki ba zan nema masa wata can daban..” Mommy bata Kai aya ba Anisa ta shiga jinjina Kai tana murmushi “Mommy kukan farin ciki ne.. I never thought a day like this would come… I mean… Not this soon… Mommy I.. I can’t believe it… My dream is finally coming true.” Da tsananin mamaki Mommy ke dubanta sai ta girgiza Kai kadan tace “Do.. You love Haidar.?” “I’ve always loved him Mommy.. I love him since childhood…” Mommy tace “Aw..! wai so kike kice tuntuni kina son Haidar..?” Taci gaba da jinjina Kai yayinda farin cikinta ke ninkuwa. Tin ina yarinya nake son shi Mommy.. Kawai kun kasa fahimta ne.. But he’s the love of my life..” Mommy taci gaba da jinjina Kai tana dubanta “Does your Mom know..? Asshe tasan kin jima kina son Haidar..?” Sai a nan ne Anisa ta d’an ja jinin jikinta.. Sai ta girgiza Kai alamun a’a “Kawai.. Ni kad’ai na rik’e abuna cikin zuciya.. Ko Hilal bai sani ba.” Mommy ta jinjina Kai kaman mai nazari sai kuma ta sakar ma Anisa murmushi “Yazo gidan sauk’i had’aku aure bazai wahala ba.” Anisa ta d’an dubeta. Fuska dauke da alamun tsoro “Amma.. Mommy what if Haidar rejects the idea.. What if yak’i aminta da Auren.?” Murmushi Mommy ta kuma sakar mata “Kar ki damu. Yarona Haidar mai biyayya ne.. Ko a baya baya sab’a umarni na balle yanzu.. Kawai muyi fatan naki iyayen su amince musamman ma Amminki tinda har yanzu bamu koma kaman da ba.” Anisa ta waro ido tace “Haba Mommy dani da Ammi fah ke d’in duka uwa ce a wajenmu.. And a halin yanzu Ammi dalilin da zaisa zumuncinku ya sak’e k’ulluwa take nema kinga kuwa zatafi kowa farin ciki da wann had’in.. Abba kuma kinsan baida matsala tinda ba kudinsa zaa karb’a ba.” Mommy taci gaba da duban Anisa mamaki bai saketa ba. Lokaci guda take jinjina Kai “Shikenan.. Zan samu Asshe da maganar..” Cikeda zak’ewa Anisa tace “Toh Mommy shi kuma fah..? Ina nufin Haidar..” Ta k’arashe cikeda sakarci. Mommy ta jinjina Kai “Haidar bazai zama matsala ba dan haka kar ki samu damuwa kinji.” Anisa ta daka tsallan murna ta nufi hanyan kitchen a guje tana rangada ma ma’aikatan kitchen k’ira tana fad’in duk su fice zatai ma mijinta abincin dare. Mommy ta bita da kallo har ta shige kafin ta jinjina kai kadan tace “Sannu a hankali.” Daren ranan Anisa bata sama bata k’asa. Sai kai komo take da sunan tana shirya ma Haidar dinner. Mommy ta shigo kitchen din tana dubanta fuska d’aukeda murmushi “Iyye lallai.! Ashe d’iyar tawa gwana ce wajen girki.” Mommy tace tana bude dishes din da Anisa Ke shiryawa. Anisa ta wani murmusa tana sadda kai alamun kunya. Mommy ta kuma murmusawa “Yau kuma Mommyn taki kike jin kunya..? Kinga ni ba wata surkunta tsakaninmu ki saki jikinki Dani fiyeda yanda muke a baya.” Anisa ta kuma murmusawa “Shikenan Mommy.. I’ll be open with you.. Ina so ki kaunaceni kaman yanda kika k’aunaci Ummul koma fiyeda ita.” Mommy ta jinjina Kai “Ko ba Haidar ni mamarki ce Anisa. You shouldn’t be hiding things from me haka ne..?” Anisa tai saurin jinjina Kai cikeda jin dadi. Mommy tace “Good. And if you want anything.. Don’t hesitate to let me know kinji koh.” Nan ma da sauri Anisa ta jinjina kai kafin Ta k’arada “Mommy ni kin gama min komai a rayuwar nan… Ina jin babu wani abu da zan nema kuma da Ya wuce Auren Haidar. Duk duniya ke kadai kika fahimci mai nake ciki. For so long Ina dakon soyayyarsa Babu Wanda Ya fahimta. Sai Allah Ya share mun hawaye yasa kika fahimta.. Thank you Mommy.” Mommy ta dafa kafad’arta “Anything for my Daughter..” Anisa na wangale hak’wara tasa kai zata shige cikeda jin dadi. Mommy ta tsareta da ido sai ta dan riko hannunta alamun dakatarwa “Ina kuma zakije Daughter..?” “Zanje na sake kwalliya ne kafin Haidar ya shigo.” Mommy ta girgiza mata Kai alamun a’a “Bana so kina rawar k’afarnan a gabansa sai ya rainaki. Ki dinga jan ajinki matsayinki na mace. And kar Ki mance Haidar baisan da zancen ba tukuna.” Anisa tai raurau da idanu had’ida tab’e fuska kadan. Ta dubi Mommy kaman zatai kuka “Amma Mommy zaki sanar dashi.?” Hannunta Mommy ta kamo “Taho nan kiji.” Suka zauna saman kujera. Mommy ta dubeta tace “Anisa nasan kinsan al’amarin aure ba abin wasa bane. Balle Haidar dake fuskantar k’alubalen rashin Ummul. Matuk’a muka tunk’aresa da irin wann batu a daidai wann gab’ar za’a iya samun matsala ne. Kinsan sa yanzu sai ya kwance mana ya koma Haidar d’insa na da. Sann Daddy ma bazai yuwu muzo masa da batu irin wann a daidai wann lokaci ba. Kowa zaiga rashin dacewar hakan musamman da yake Mahaifin Ummul na nan asibiti a Abuja. Ya kamata mu bar komai har sai an sallamesa sun koma can gida Kano ta yanda ba wani tashin hankali da zai bullo mana. A tsanake zamu tunk’ari lamarin. Kedai kawai ki kwantar da hankalinki kiyi duk abubuwan da na umarceki tinda kinada yarda da amincewata ki k’addara tamkar kin Auri Haidar an gama.” Anisa ta danyi jim sai kuma ta jinjina Kai tace “Gaskiya ne Mommy. And its a once in a lifetime in sha Allah. Kuma so nake Aurenmu Ya karad’e ko ina dan babban biki nake so Mommy.” Mommy ta jinjina Kai tana duban Anisa murmushi saman fuskarta. ** A haka Anisa taci gaba da mafarkinta na kasancewa matar Haidar cikin kwanciyar hankali sanin cewa tana tareda yarda da amincewar Mommy. Ba abinda yake gabanta a halin yanzu tamkar taga wann mafarki nata Ya zama gaskiya. Dole ta dad’a daure belt dinta da kyau dan ta tabbata Ummul bata dawo ba. Burinta bai wuce taga wann ragwababben uban Ummul d’in Ya bar garin ba. A can b’angaren su Ummul ma Hisham yanata samin lafiya saidai da yaga hankulansu zai karkata zuwa wani abin daban sai ya b’ullo da wani abin wanda zai dauke hankulansu. A haka aka kwashe kwanaki satuttuka Har aka soma k’irga watanni. Kowa da abinda yake burin cimmawa. Ummul na nan tana rainon cikinta. Hisham bai fasa kudirinsa da shirinsa ba. Haidar bai fasa neman Ummul ba. Mommy ta maida hankali kan Anisa yayinda Anisa taci gaba da mafarkin cikan burinta. Abba yanata samun lafiya. Daddy nata zarya tsakanin SouthAfrica da Nigeria kasuwancinsa na dad’a bunk’asa a k’asashen k’etare. Cikin Ummul nata girma cikin k’oshin lafiya. Saidai tinda cikin Ya fito ta kuma rok’on Hajja da cewa dan Allah ta barta tai rainon cikin gabanta ko dan guje ma abinda zaije yazo cikin ahalinta. A b’angaren Haidar kuwa dukda ayyuka da suka sha gabansa bai fasa k’udirinsa na nemanta ba. Dan tinda tafiye tafiyen Abba ya k’aru Sai ayyukan cikin gida Nigeria suka dawo wuyan Haidar gaba d’aya. Kusan shi yake kula da ragamar Kampanin. * Watan Abba uku a Abuja aka sallamesa daga asibiti. Tuni Haidar Ya kira Sadis ya sanar dashi tinda dama duk wani hidindimun asibitin Sadis d’in keyi. Kai tsaye gidan Daddy suka taho. Abba har tafiya yake da sanda, idan ka gansa bazaka gane sa ba ya samu lafiya da kula cikin ikon Allah. Sai son barka. Mama Tani da Abba ne a bayan motan yayinda Azeema ke zaune mazaunin mai zaman banza Sadis na tuk’awa. Koda suka iso gidan Mommy da kanta ta tarbesu. Tuni tasa an shirya musu sashen bak’i sai haba take dasu Anisa kaw sai cika take tana batsewa dikda cikin zuciyarta fal annashuwa ne an sallami nakasashen uban Ummul zasu fice daga rayuwarsu gaba d’aya su huta. Suka raka juna da mugun kallo itada Azeema dan dukansu basu mance karonsu da juna ba. Anisa taja dogon tsaki ta juya Azeema ma Tai shigewarta tana kad’a kai. Tinda suka iso gidan jikin Abba ba a sake bane. Ya kuma duban Mama Tani yace “Tani wai shin bazai yuwu mu tafi gida a yau d’in nan bane sai mun kwana gidan sirakanmu. Ni fah sabida naga Ummulkhairi na amince na taho.. Amma ina ganin rashin dacewar hakan. Abin zai yawa ai.” Dukda k’irjin Mama Tani dake bugawa sai tai k’arfin halin cewa “Haba Malam.. Daga sallamanka asibiti sai ka hau hanya.. Ai dai ka jira ka d’anji k’arfin jikin.” Shiru yai kaman mai nazari sai Ya girgiza kai “A’a Tani.. A Ina kika taba jin Uba yaje gidan sirakansa Ya saki jiki.. Wann ai bai tsari ba… Iyakacin karamci da duk wani taimako mutanen nan Sun mana. Kuma na shaida Ummulkhair tayi sa’an miji da iyayen miji masu dattaku da sanin darajan d’an Adam. Kinga bazan so ni kuma suga namu rashin dattakun ba.” Tani ta d’an murmusa “Haba Malam. Kamawa fah take. Ba don jinya da Allah ya jarabceka dashi ba da hakan bazai kasance ba. Fatanmu Allah ya k’ara maka lafiya su kuma ya biyasu Ida mafificin alkhairi.” Sai Ya dubeta kaman Wanda Ya tuna wani abu “Na shafe watanni banga Suwaiba ba..” Wai ance kishi dole saida Mama Tani taji zuciyarta ya d’an sosu. Sai Tai kokarin kauda tunanin tace “Malam a yau kawai sau uku kai waya da Suwaiba.. Kai hakuri zaka ganta ne da zaran mun koma gida. Kasan Suwaiba da kunya da surkunta bazata iya zuwa nan ta duba ka ba Shiyasa bata zo ba amma ai nakan had’aku a waya tin bayan da likitoci suka ce zaka iya amsa wayan talho haka ne.” Abba ya jinjina Kai a hankali sai kuma yace “Ummulkhairi fah.? Kince bata iya fita ko k’ofa sabida junan da take d’auke dashi. Likita yace mai tattare da had’ari ne. “ Ya d’anyi fasali “Amma ai zan iya ganinta yanzu.. Zan iya zuwa Har yanda take ko Tani.” Ya fad’i yana k’ok’arin mik’ewa da sandarsa. Mama Tani ta rasa ta ina zata b’ullo masa. Mai zata sanar dashi gameda Ummul da Aurenta.? Ganin yana k’ok’arin mik’ewa yasa Tani saurin kamo hannunsa “A’a Malam ka dakata ka dan huta kaci abinci.. Ai.. Ai nan gidan sirakan Ummulkhairi ne.. Ba.. Ba nan bane Gidanta Shiyasa baka ganta ba.” Ta fad’i cikin k’ok’arin had’o kalaman tanayi tana kauda fuska gefe. Abba ya tsareta sosai da ido dan yasan matar tasa sosai. Ya sani idan tana had’o zance. “Tani.” Ya kirawo sunanta cikeda kulawa. Ta d’ago ido a sanyaye ta dubesa “Na’am Malam.” “Ina Ummulkhairi..?” Ya jefo mata tambayar. Tani ta d’an sosa keyarta “Tana gidanta Malam. Dan Allah ka kwantar da hankalinka. Kaji mai likitan nan yace sam shiga tashin hankali ko damuwa ba naka bane… Kaga lokacin sallan la’asar ta gabato barin taimaka maka ka d’auro alwala.” Ta fad’i tana mik’ewa. Bayan ta masa rakiya ban d’aki ta nuna masa yanda zaiyi nan ta dawo d’akin tana waya da abokiyar zamanta Suwaiba. Ko shakka Babu matsalan suke tattaunawa. Sam Tani bataji fitowar Abba daga Band’aki ba sai muryarsa ta saurara yana fad’in “Tani… Mai nake ji kina cewa? Za’a sami Ummul da izinin Allah..? Tani meke faruwa..? Ina Ummulkhairi…?” Ya k’arashe tambayar jikinsa na rawa daga nan yanda yake tsaye. Har sandarsa rawa take. Murmushin da yafi kama da yak’e Mama Tani tai. Ta k’araso tana fad’in “Wai Har ka fito bakai kirana ba.” Abba ya girgiza Kai ba alamun wasa “Baki amsa min tambayata ba Tani. Da waye kike magana a waya? Sann meyasa kikace za’a samu Ummulkhair.?” “Da Suwaiba nake magana Malam. Kuma tambayata take ko kun gana da Ummul tinda tasan kana matuk’ar son ganin Ummulkhairin.. Shine take ce min an sameta a waya nace za’a sameta in sha Allah.” Ta k’arashe cikin k’ok’arinta na gamsar dashi. Abba yai shiru kaman mai nazari dan Sam baijin zuciyarsa ta natsu da maganganun Tani d’in. Bayan yayi sallah Tani ta taimaka masa suka fito parlor yaci abinci Ya sha magani. Nan Mama Tani ta soma waige waigen neman Azeema. Ta mik’e tana fad’i ma Abba bari ta nemo Azeema cikin gidan. Dan Sam zuciyarta bai kwanta ba da rashin ganin Azeemar tinda tasan sam ita da Anisa d’iyar k’anwar Hajiya Kwaise had’uwarsu baya dad’i. Ficewar Mama Tani da kad’an aka soma k’wank’wasa k’ofar. Abba ya mik’e kad’an daga kishingid’en da yake. Ya bud’e idanunsa yana duban k’ofan yake fad’in “Bismillah.” Wata budurwa ce ta turo k’ofan da Sallama saman bakinta. Abba ya gyara zamansa yayinda murmushin Anisa Ya k’aru tana tambayar Abban ko zata iya shigowa. Abba ya jinjina Kai yana bata izinin shigowa had’ida amsa gaisuwarta. Anisa ta risina yawa mutumiyar arziki tana kuma yima Abba sannu da jiki had’ida fatan samun lafiya. Harda addu’o’i ta jero masa. Abba ya amsa cikeda jin dad’I musamman da yaga yanda yarinyar ke girmamasa sai ta tuna masa da Ummul d’insa. Anisa taci gaba da risinawa tana fad’in “Abba ni sunana Anisa, kuma k’anwa nake ma sirkin ka Aliyu.. Sann munyi zaman dad’i da Ummul dan har mun k’ulla k’awa ce da Ya zarce Ya koma tamkar ‘yanuwan juna..” Abba yace “Allah sarki.. Toh.. Ma sha Allah.. Ai ga dukkan alamu halayyanku ne yazo d’aya da Ummulkhair.. Dole kuyi abota.” Anisa taci gaba da murmusawa tana kuma sadda Kai. Sai ya dan gyara zamansa kad’an yace “Amma.. Nace ina ita Ummulkhairin.. Har yanzu ban ganta ba… Ina so naga d’iyata.. Ina so naga yanayin jikin nata.” Anisa ta waro ido tana dubansa. Sai ta d’an waiga baya kad’an tace “Ban gane baka ganta ba Abba.. Wai har yanzu basu sanar dakai ba.?” Abba ya dubeta da mamaki “Akwai wani abinda Ya kamata na sani ne gameda Ummulkhairina..?” Anisa ta soma girgiza kai “Abba ai Ummul ta jima bata nan.. Idan ban b’ata lissafi ba mun d’ebe a k’alla watanni shida bamusan yanda take ba..” Abba ya girgiza Kai cikin rashin fahimta yana dubanta “Ban fahimceki ba yarinya.. Kina nufin b’acewa Ummulkhairi tai baku san yanda take ba.?” Anisa sai ta fara hawaye murya na rawa take fad’in “Abba Auren Ummul da D’anuwana Aliyu Ya k’are… Ta tafi babu Wanda yasan ina ta tafi..” Daidai lokacin Mama Tani da Azeema suka shigo suka tadda Abba na dafe k’irjinsa ga Anisa duk’e wajen tana kuka. Mama Tani ta soma salallami ta isa ta tallafi Abba dake k’ok’arin kaiwa k’asa yayinda Azeema ta tafi a guje ta shak’o Anisa tana tambayar mai tai ma mahaifinta. Tani taci gaba da jijjiga Abba tana fad’in “Malam meke faruwa..? Lafiya na Barka.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Malam.!” Ita kuwa Azeema tuni ta shak’e Anisa tana fad’in sai ta sanar da ita mai tai ma mahaifinta.. Hayaniyar yaja hankulan mutanen gidan. Mommy ta shigo a fujajan tana tambayar meke faruwa.? Azeema taci gaba da mak’ura Anisa tana fad’in ko ta fad’a mai tai ma mahaifinta ko itama ta shak’eta sai ta daina numfashi. Jikin Anisa yaci gaba da karkarwa. Fad’i take “Mommy ki yarda dani wllhi babu abinda nayi.. Gaishesa na shigo yi Ya tambayeni Ummulkhair ni kuma na sanar dashi bata nan.. Mommy bansan Mahaifin Ummulkhairi baisan meke faruwa ba.. Wllhi iyakacin gaskiyata kenan.” Azeema ta kuma yowa kanta tana fad’in “K’arya kike bak’ar munafuka shak’esa kikayi..” Mommy ta daka musu tsawa da fad’in “Ya isheku dukanku..!” Ta dube Azeema tace “Maza kirawo Sadis a koma asibiti.” Sai suka sinkayo muryar Abba yana fad’in “A’a ba sai an koma asibiti ba.. Magana guda nake son ji!” Ya dubi Tani dake hawaye yace “Tani, ina Ummulkhairi..? Shin gaskiya ne Aurenta Ya k’are ta tafi babu Wanda yasan ina take.? Shin wann ne dalilin da yasa na kasa ganin Ummulkhair.? Shin wann ne abinda kuketa b’oye min keda Suwaiba.? Wann ne dalilin da yasa Suwaiba ta kasa zuwa ta dubani tsawon watannin nan.? Tani mai kuka aiwatar lokacin da nake kwance..? Wane irin Aure Suwaiba da ‘yanuwana sukaima Ummulkhair da zaisa ta guji gida bayan mutuwansa.?” Sai kukan Tani ya k’aru yayinda jikin Mommy yai sanyi. Tai k’arfin halin k’arasowa. Ta dubi Abba sai ta dubi Tani.. Tace “Abban

Chapter 49 of 64