Share this page
Kansa na kife yana d’igar da hawaye. Haidar ya daura hannayensa biyu saman hannayen Daddy dake bisa laps d’in Daddyn. Shiru ne ya ziyarci wajen baka iya jin alamun komai face motsin zuciya. Daddy ya rik’e hannayen Haidar tsam cikin nasa “I’m sorry son.. I’m sorry.. Please forgive your Dad…” Hawaye suka gangaro ma Haidar dake duk’e gaban Daddy hannayensu cikin na juna. Mommy da ta nufo k’ofan dan ta sanar da mijin nata gayyatar D’ansu da matarsa dinner matsayin maraba da dawowa gida ma Haidar d’in koda bazai nuna kulawarsa kaman yanda ta tsammata ba, nan ta riski wann babban al’ajabi. Rana mai d’inbin tarihi.. K’afafun Mommy suka kusan gaza d’aukarta.. Hawaye suka shiga zarya a k’uncinta.. Sai Mommy ta fad’i k’asa tana mai sujada na godiya ga Ubangijinta. Tama rasa mafarki ne take kokuwa dai a farke take. Haidar dinta da mahaifinsa take gani cikin yanayi da bata tab’a tsammanin zata gansu ciki ba. Allah buwayi gagara misali. Mommy ta kuma yarda cewa lallai duk Wanda ya dogara ga Allah toh fah Allah ya isar masa. Itakam babu abinda zata ce saidai taci gaba da gode ma mahaliccinta Wanda ya yaye duhun dake cikin gidanta da ahalinta ya yalwatasu da haskensa. Ta saki turban boka da suka d’auko daga fari ta rik’e turba na gaskiya sai gashi komai yana gudana cikin sauk’i. Lallai wann wani rahama ne daga Ubangijinta. Lallai wann izna ce ga tababbu masu bin hanyar b’ata. Wanda ya gane Allah shi yake yi ba boka ko Malam ba shi keda babban rabo duniya da lahira. Bata san sanda ta koma da baya ba ta nufi d’akinta ta maida k’ofa ta rufe ta fad’a saman gado tana kuka sosai. Kukan farin ciki wann karon. Kukan da ya goge Wanda ta jima tanayi a baya Kama daga zuciya har k’wayan ido. Alkhairin Allah yaci gaba da haska gidanta da ahalinta. Haidar yaci gaba da girgiza Kai yana rik’eda hannayen Daddy gam cikin nasa “Daddy ka daina bani hak’uri. We are all human beings.. We make mistakes. What’s important is that we learn from those mistakes.” Yaci gaba da jinjina kai a hankali “Ni yafi cancanta na nemi yafiya a gareka Daddy. Idan inada hakki akanka hakkinka dake kaina yafi girma. Duk yanda naje nazo banida madadinka.. I should’ve been more understanding with you. Cikin zuciyarsa yake tuno sanda Ummul take fad’a masa ‘A rayuwa wasu lokutan Allah yakan saka mana jarabawarmu ya zamto people that are tied to us by blood.’ Sai Haidar ya mik’a hannu ya d’auko folder d’in project da ya shigo dashi. Ya daura saman hannun Daddy suna kallon cikin fuskan juna. Murmushi gauraye da siraran hawaye saman fuskar Haidar yake fad’in “Daddy I can walkway from this Business because it’s my choice.. But I can’t walkway from you. Do you know why.?” Sosai Daddy yake kallonsa yana hawaye. Haidar yaci gaba da jinjina Kai “Because you are my Father.. Allah chose you for me… We are tied to each other by blood because haka Yake so ya kasance.” Yaci gaba da jinjina Kai yana murmushi “Daddy jininka shi yake circulating cikin jikina daga farko.. A karo na biyu Kai ka bani jininka, you couldn’t walkaway from me either. Sabida ni d’in D’anka ne.” Daddy sai ya janyo kan Haidar ya rungume cikin jikinsa. Muryarsa na rawa yake fad’in “Allah ya maka albarka Aliyu.” ** A lambum dake bayan sashen Mommy aka shirya cin abincin daren. Hasken wutan lantarki ya karad’e ko ina tamkar ba dare ba. An shirya teburin gwanin ban sha’awa ga barbecue stand daga gefe. Suna cikin shirya plates saman teburin itada Anisa Anisa tai excusing kanta sakamakon kira da ya shigo wayarta. Nan Ummul ta hangosa na tahowa. Sassanyar murmushi saman fuskarsa. Ta shagala sosai da kallonsa kaman yanda shima ya shagala da kallonta dan sosai tai masa kyau. Yana k’arasowa sai ya tsaya daga bayanta ya dan rungumota had’ida rank’wafo da kansa kusan kunnenta “You look.. Gorgeous.!” Ya fad’i cikin sigan rad’a. Ummul ta soma k’ok’arin turesa daga jikinta tana ‘yan waige waige “Mai kake aikatawa ne wai.. Idan wani ya ganmu fah.?” Bai saketa ba ya kuma rad’a mata “So what.! Can’t I hug my wife.?” Ta waiga ta dubi Anisa dake can gefe tana amsa waya. Ta kuma duban ma’aikatan kitchen guda biyu dake gefe gaban BBQ stand. Kaman zatai kuka tace “Dan Allah ka bari akwai mutane wajen nan fah nan..” Juyawa yai ya dubi kitchen staff d’in. Sai ya dan murmusa “Is that problem.? fine. Zo muje.” Bai jira amsarta ba ya shiga janyo hannunta. Suka nufi yanda ma’aikatan ke gashin naman. Haidar yace musu suna iya tafiya zasu kula da barbecue d’in. Ma’aikatan suka amsa masa cikeda risinawa suna duban yanda Haidar ya janyo Ummul dake fad’in ita fah bata iya amfani da irin wann abin gashin ba. Yace kar ta damu tare zasuyi. Sosai suka birgesu kaman kar su daina kallonsu. Abu ne da zasu iya cewa basu tab’a ganin ya faru gidan ba. Basu tab’a ganin Haidar cikin farin ciki irin wann ba. Su dai kam Sun shaida zuwan Ummulkhair gidan Alkhairi ne. Anisa ta juyo baki sake tana duban ikon Allah Haidar da Ummul gaban barbecue stand sai zuba soyayya suke. Gwiwoyinta taji sun sake kamar wata maras laka. A haka Mommy ma ta k’araso wajen ta taddasu. Farin ciki maras misaltuwa ya kuma gauraye zuciyarta. Zuwan Mommy wajen yasa Ummul janye jiki ta kyale Haidar shi kad’ai. Haidar na fad’in ta mik’a masa bbq cutting board sai sann ya kula ta silale ta bar shi shi kad’ai.. Ba kowa wajen ma sai shi kad’ai. K’ila Sun shige yin wani abin cikin gidan. Ya dan tab’e bakinsa kad’an. Amma sai yaga wani hannu na mik’o masa abinda yake nema. Haidar yabi hannun da kallo. Ga mamakinsa Daddy ya gani. Kyakkyawan murmushi saman fuskar mahaifin nasa. Haidar yasa hannu ya amshi board d’in had’ida godiya ma Daddy. Jinjina Kai Daddy yai. Sai Haidar yaga Daddy na nad’e hannun long sleeve shirt din dake jikinsa alamun zai tayasa. Sai Haidar ya girgiza Kai “No Daddy you don’t have to.. Ya kamata kaje ka zauna.. I.. I’ll serve you some.” Ya fad’i awkwardly dan abu ne da bai saba faruwa ba koma bai tab’a faruwa ba tsakaninsu. Murmushi ne saman fuskar Daddy ya dafa kafad’an Haidar din “No Son, let’s do it.. Together.” Haidar yai murmushi yana tuna lokacin yarantarsa wann shine mafarkinsa. To make memories with both his parents… To strengthen their bond. Ya samu kusanci sosai da mahaifinsa. To have some quality time together.. To build something together. To play sports, video games, go horse riding da dai sauransu. Sai ya murmusa yana duban mahaifin nasa sosai. Kaman mafarkinsa ne yake zama gaskiya. Yana k’ok’arin yanka naman saman board din Daddy ya dafa hannunsa wana hakan Ya dakatar da Haidar. Suka dubi juna sai Daddy yace “Be careful Engr, this is not a construction side.” Su duka sai suka d’an dara kad’an. Daddy yace “You know Son, if I were to turn back time.. Da munyi aiki tare hand in hand.. Like professional Engrs.” Jikin Haidar Ya d’anyi sanyi Ya fahimci abinda sukeyi a yanzu d’in Ya K’wadaitar ma mahaifinsa inama lokacin da sukeda damar kasancewa tare a company sunyi ayyuka tare tare babu tsangwama babu hantara. Gashi yanzu Ya sanar da mahaifinsa Ya aje aikin company meaning ba lallai su sami irin wann damar ba. Muryar Daddy ya kuma sinkaya “Bana so na tak’uraka. Da na rok’eka wani alfarma.” Haidar yai saurin girgiza kai “No Daddy.. Ka wuce wann.” Daddy ya murmusa “Haidar, I can understand you, if you… don’t want to manage the project due to.. your personal priorities.. But please kar ka aje aikinka.. Kar ka bar Kampanin… Let this be the last abu da zan buk’ata ka mun.” Haidar yai saurin girgiza kai “No Daddy, I’m your son.. Hakkina ne matsayinka na mahaifina nayi maka biyayya cikin abinda bai sab’a ma mahaliccina ba. Kuma wann bazai zama abu na k’arshe da zan maka ba. Umarni kawai zaka bani a koda yaushe.. Kuma na maka alk’awari bazan aje aikina ba in sha Allah. Bazan bar company ba. Together we will take the company to greater heights.!” Ya k’arashe da murmushi saman fuskarsa. Sai Daddy ya kamo k’afafunsa Ya rungume “Thank you son. Allah ya maka albarka.” A haka Mommy ta k’araso wajen ta iskesu. Farin cikinta ya ninku. Itakam a halin yanzu tana jin babu sauran abinda zata nema da ya shige taita gode ma Ubangijinta da ya cika rahamarsa ga ahalinta. Bayan cin abincin suna zaune itada Haidar a parlor. Haidar ya kuma murmusawa ya dubeta “You know Mommy, After all these years it's today that I feel like… I'm part of the family.” Mommy ta rik’e hannayensa cikin nata. Kyakkyawan murmushi saman fuskarta “We gonna have some family bondings to makeup for all the time we've lost… Kuma.. Zamu fara da shagalin bikinka. Aurenka da Ummul ta cancanci biki na gaske irin na ‘yan gata.” Ya dan girgiza Kai yana murmushi “Mommy na kasa yarda bisa yarjejeniyar Wata uku na amince da auren Khairy.. Dan kawai Daddy ya bani wann project d’in.” “Shiii.” Mommy ta dakatar dashi “Babu wann maganar Haidar.. An rufe shi har abada. D’ago baya irin haka baida wani amfani. Bazaka sanar da Ummul wani abu mai suna auren yarjejeniya ko AUREN WATA UKU ba.” Sai ya d’an dubeta can k’asar zuciyarsa yana jin zuciyarsa ta katsa samun natsuwa har sai ya sanar da ita.. Sabida a halin yanzu Aure yake so ya gina da ita bisa zallan gaskiya. Ya d’an dubi Mommy “Mommy I want to build my marriage with her base on trust and transparency. Bana so daga baya tazo ta fahimci cewa na aureta ne bisa yajejeniya zuwa wani k’ayyadajjen lokaci. I want her to hear it from me first kafin taji daga wani waje.” Mommy ta jinjina Kai “Na fahimceka Haidar.. Amma kafin nan ka d’an dakata har a gama wann bikin tariyarku can gidanku da na saka nan da kwanaki biyu kacal. Idan yaso sai ka sanar da Ummul yanda al’amarin ya kasance..” Sai ya d’anyi jim kafin kuma ya jinjina Kai a hankali “Shikenan Mommy. Idan hakan kike so.” Ta murmusa cikeda jin dad’i. Burin ko wasu iyaye shine su samu ‘ya’ya masu biyayya a garesu. Lallai mai rai kar ya cire tsammani daga rahamar Ubangijinsa. Who would’ve thought za’a zo lokacin da Haidar zai d’auki umarnin mahaifyarsa ba tareda jayayya ko nuna k’in amincewa ba.? Ya ke ‘Yaruwa da Allah ya Miki jarabawa da D’an da kika haifa, kar ki tab’a yanke k’auna daga rahamar Ubangijinki domin kuwa shid’in rahamarsa mai yalwa ne. Kar ki karaya, kici gaba da mik’a lamuranki ga Ubangiji. Duk Wanda Allah ya zama majib’icin al’amarinsa shi keda babban rabo. Haidar ya mik’e da zummar mata sallama ta dakatar dashi. “Yauwa nace ba sai abu na gaba..” Haidar ya jinjina kai yana sauraron Mommy. “Kanaji.. Ummul zata dawo nan sashena da zama har sai anyi bikin an kai maka ita.” Wann karon zaro ido yai kaman wani abin tausayi ya langab’e kai “Haba mana Mommy does it have to be this way.. I just came out of hospital fah..I’m still a patient.” “Mommy ko kin daina tausayina ne.” Ya kuma fad’i a marairaice. Dariya yaso bata amma ta gimtse tace “Ba tausayinka na daina ba. So nake kai d’aukin d’iyata idan an kai maka ita.. Waima dakata shin kai ka biya sadakin nan ne.?” Haidar ya sauk’e ajiyan zuciya kaman wani maraya “Shikenan Mommy.. Saida safe.. Amma please a k’yaleta ta kawo min coffee.” “Naji… Just coffee..” Tai maganar tana jaddada masa. Ta k’arada “Jeka Allah bamu alkhairi.” Haka ya fice duk jikinsa ba kuzari. Shi fah maganar gaskiya wann gadara da Mommy take masa da mata akan sadaki ya fara isansa. Shidai kawai gwara ya biya Mommy sadakinta ya huta. Bayan ficewar Haidar shiryawa tai ta nufi sashen Daddy. A parlor ta iske shi. Daddy ya dubeta da mamaki. For days yana k’ok’arin shawo kanta daga fushin da take dashi sai gashi yau ta kawo kanta har yanda yake. Murmushi yai cikin zuciyarsa yake ayyana lallai sai a bar uwa da D’anta. D’anta shine rauninta. Ta k’araso kanta a k’asa. Kaman mai shirin zama sai kuma ta silale gabansa. Ta kifa kanta tana hawaye. Cikin rawar murya irinta mai kuka take fad’in “Engr ka yafe min.. Ka yafe mun duk abubuwan da nai maka.. Na shekarun baya da na kwanakin nan..” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Daddy ya duk’a shima suna fuskantar juna. Sai ya rungumota zuwa jikinsa. Kamar wacce take jira kukanta sai ya k’aru. Shima ya saka d’an yatsarsa ya goge kwallan da ya mak’ale masa cikin ido. “Is Ok Kwaise. Ya isa haka.. Dukanmu ‘yan adam ne masu kuskure. Mafiya alkhairi sune masu tuba. Bayan tsawon shekarun nan idan akwai Wanda yafi cancanta ya nemi yafiya ni ne. I supposed to be the head of this family.. Amma duk sai na bar Miki nauyin.. Kece kika jajirce Akan wann ahalin Kwaise.. You never give up despite the challenges.. Kin tsaya Akan k’afarki ganin cewa ahalinki bai watse ba. Kinyi abinda ni na kasayi Kwaise.. Thank you for not giving up on us..” Murmushi ne gauraye da hawaye saman fuskarsa. Sai suka rungume juna wani kukan na kuma zuwa ma Mommy. ** A b’angaren Haidar kuwa koda ya koma sashensa zama yai shi kad’ai a balcony d’insa yana tunanin rayuwarsa. Da yanda shigowarta cikin rayuwarsa Ya canza komai lokaci guda cikin ikon Allah. Yana jin wani shauk’i can k’asar zuciyarsa Wanda bai tab’a jin hakan ga wata mace ba. He wants to build something special with her.. base on trust and transparency wanda hakan ke nufi dole ya sanar da ita wasu abubuwan daga past d’insa musamman abinda ya danganci personal rayuwarsa. Aurensa da Dareen Wanda ko family d’insa basu sani ba har ya faru ya k’are da kuma yanda nasu auren da ita Ummul d’in Ya kasance. Yarjejeniya sukai da mahaifiyarsa zata shigo rayuwarsa a matsayin matar wata uku dan kawai Ya mallaki project d’in da yai niyyan tarwatsa mahaifinsa dashi. Ya lumshe idanunsa a hankali yana furzar da huci. Shigowa Ummul Tai rik’eda kofin coffee da ya buk’ata a hannunta. Ta mik’a masa cikeda risinawa. Ya amsa yana mata godiya. Sai ya nuna mata gefensa “Come sit here... let’s talk.” Haka kurum taji gabanta ya fad’i sai ta d’an girgiza kai kad’an “Magana kuma.?” Haidar ya jinjina Kai bayan ya sipping coffee din “Kar ki damu yau magana zamuyi ba akan kowa ko komai ba... Magana ce akanmu.. Let’s talk.. about us.” Ya k’arashe yana kashe mata ido d’aya gajeren murmushi saman fuskarsa. Bugun zuciyarta Ya dan karu musamman da taga yanda yake binta da kallo. sai ta k’arasa a d’an sanyaye ta zauna a yanda Ya nuna matan. Dak’ik’ai suka d’an shige kafin Haidar Ya aje coffee din dake hannunsa bisa teburin gefensa. Ya gyara zamansa Ya karkato sosai yana facing dinta gwiwarsu na gogar juna. Sai ta d’an sadda idonta kad’an ganin irin yanda ya tsareta. Hannayensa ya d’aura saman nata dake bisa laps dinta. Ummul ta dubi hannayensa da Ya d’aura bisa nata dake bisa cinyarta. Sai ta d’ago ta dubesa a d’an sanyaye. “Khairy..!” Ya ambace sunanta kaman yanda Yake kiranta. “You came into my life to make it better.. You’ve changed all areas in my life..” Ta dube shi sai ta dan murmusa “Bani nayi ba duka yin Allah ne..” Ya jnjina kansa “Kece sanadi...” Yaci gaba da jinjina Kai hannayenta cikin nasa “I.. know there’s still a lot.. to do.. But you showed me the way Khairy..” You made me want to be a better son… You made me wanna wake up and reflect. You made me wann be.. a better business man, take my brand far.. And above all, you made me believe,.That I can be a better person. Thank you.. For coming into my life.” Ya k’arashe labarin na neman sauya direction. Jiki a sanyaye ta soma k’ok’arin zame hannunta sabida zuciyarta dake bugawa cikin sauri. “Dare yayi.. Ya kamata ka kwanta ka huta… Kaifa patient ne.” Ya kamo waits dinta ya zaunarta saman laps d’insa. Cikin sigan rad’a yake fad’in “Wa yace miki ni patient ne har yanzu.? Bari ma na nuna miki na warke.” Ta zaro ido tana k’ok’arin turasa “Kaga.. Ni tafiya ma zan..” Bata kai aya ba ya rufe bakinta da nasa. SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!* *46* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* Da kyar ta samu ya k’yaleta yai mata rakiya har k’ofan parlorn Mommy. Suna isowa ta zame jikinta daga nasa. Sai ya mik’a mata k’aramar paper bag d’in dake hannunsa. Ta d’an girgiza Kai “Ta mecece.?” “Don’t open it yet sai kin shiga.” Ya fad’i yana kashe mata ido d’aya . Bai kuma tsayawa sauraronta ba ya soma tafiya yana waving dinta kaman kar ya tafi ya barta. Ta girgiza Kai kurum tana binsa da kallo a haka har ya shige. Anisa tana nan ta kasa ta tsare tana jiran dawowarta dan kusan komai Akan idonta ya faru. Sam Ummul batasan da mutum a parlorn ba sai muryar Anisa da ta sinkayo. Batada lokacin sauraron maganganun Anisa hakan yasa tuni tasa kai ta nufi upstairs ba tareda ta tsaya sauraron maganganun Anisa ba. Amma sai Anisa ta bud’e murya tace “Auren Haidar Maitama might seem to you like a golden opportunity na samun nasarori da Jin dad’in rayuwa.. Musamman duba da irin rayuwar da kika baro cikinta… But what if, this golden opportunity comes at a very high price.?” Ummul taci gaba da k’ok’arin dannar kanta. Dan a yanda ta tsara ba a wann lokacin zata fuskanci Anisa ba. Ta gama shirya lokacin da zata tunk’ari Anisa da kalamanta. Sai ta bud’e lumsassun idonta a hankali taci gaba da tafiya ba tareda ta juyo ta dubi Anisa ba. Anisa ta take mata baya tana ci gaba da fad’in “Abinda yasa kikaga na dage miki Ummul dan inada gaskiya ne. Bana so ki saki jiki cikin auren da zakiyi danasani a gaba. Kuma ciwon ‘ya mace ta ‘ya mace ce.. Ba komai cikin wann auren face k’ask’anci.” Ummul ta dubi Anisa da murmushi saman fuskarta. Sai kuma ta maida k’ofan d’aki ta rufe ba tarda tace komai ba. Dan Sam bazata bari ta b’ata shirinta ba. Anisa taci gaba da sakin huci dan ta tsani wann silent treatment din da Ummul ke bata dan bata mance karonsu da Ummul d’in ba. Tasan she’s sharp and smart dik yanda akai wann shirun da take tana murmushi wani abin take shiryawa tinda Tasha lalata mata shiri ba d’aya ba. Taci gaba da sakin huci ita kad’ai. Ummul tana shigewa d’aki ta lumshe idonta tana karanto addu’o’in samun sauk’i da sukuni cikin zuciyarta dan sosai take Jin maganganun Anisa har cikin k’ahon zuciyarta da b’argonta. Ta isa saman gado ta zauna gijif sai ta dubi ‘yar jakan da Haidar ya bata. Ta soma k’ok’arin bud’ewa. Nan taga wayar salula ce ta yayi mai d’ankaran kyau. Da alama komai an saka cikin wayar. Kaman daga chaji har zuwa simcard. Taita juya wayar kafin ta kunna. Sak’o ne ya fara mata Sallama _I've bought a new book.. and open a brand new page… together with you_ Taita karanta sak’on yayinda jikinta ya kuma mutuwa. A b’angare na kunnenta guda kalaman Anisa ke mata yawo a d’aya b’angaren sak’on Haidar cikin yanayin muryarsa na mata yawo. Ta rasa wanne d’aya zata saurara sai ta toshe duka kunnuwanta biyu kuka na zuwa mata. Ganin koke koke da tunanin bazasu fishheta ba kawai sai ta mik’e ta d’auro alwala ta soma Kai kukanta ga Mabuwayin Sarki da babu kaman shi. Tana bisa darduma tayi lamo tana duban wayar kira na shigowa Wanda tasan kiransa ne tinda lambarsa ne kawai kan wayar. Bata bi takan wayar ba haka akaita kira har dai ya hak’ura. K’arshe ya tura sakwanni Wanda suma batabi takansu ba. Duk Haidar sai ya damu ya fara tunanin ko bataji dad’in kyautar da yai mata bane. Kodai ya mata wani abin ne. Washe gari da safe Fashion designer tazo har gida da manyan bridal dress catalog dan amarya Ummul ta zaba yanayin rigar da za’a mata. Anisa ita ke tayata zabe. Ummul sai duban Anisa take tana mamakin wai wacce ke mata gargadi da kashedi da auren Haidar sai gashi itace mai zakewa wajen zaba mata Kayan da zata saka. Aka nuno wani farin gown mai dankaran kyau Anisa tace “Yauwa perfect. I think this one is ok.” Kaman daga sama suka sinkayi wann muryar nasa daga bayansu “This is too revealing.. My wife can’t wear this.” Ya fad’i cikeda gadara hannayensa sakale cikin aljihun jeans d’insa yasa kai ya shige upstairs gaida Mommy ba tareda ya dubi ko yanda Ummul d’in take ba. Ta bisa da kallo duk jikinta a sanyaye. Toh ko dai fushi yake da ita sabida yayita kiranta a Daren jiya bata d’aga ba har sakwanni ya turo bata amsa shi ba. Gaba d’aya sai taji babu dadi. Anisa na hankalce da ita da Haidar d’in. Lokaci guda tana mamakin wai Haidar ke cewa kaya is too revealing dik girma da tasowa cikin gogaggun wayayyu da yai. Lallai ta yarda ya fara nisa cikin soyayyar wann Bagidajiyar. Idan batai sauri ta rabasa da wann Bagidajiyar ba haka zata maida mata Haidar d’inta Bagidaje irinta. Haka har aka gama zaben rigunan ita dai bama tace ga rigar da aka tsaida ba. Duk tunaninta na kan Haidar.. Bata san ta damu da fushinsa har haka ba. Abinda yafi bata mamaki shine ko ta kanta bai sake bi ba.. Bai nemeta bata ma sake saka shi a idonta cikin gidan ba. Ta d’auki wayar kaman zata kira layin sa amma sai ta kasa. Haka kaman wasa har ranan da ake saka ran ranan ne Mommy ta tsaida dan shagalin bikinsu bata saka Haidar idonta ba. Wani abinda ya k’ara bama Ummul mamaki shine Anisa batai k’asa a gwiwa wajen shirya komai ba. Ita Mommy tasa ta kaita saloon aka gyara mata gashi sann ta d’auko mai lalle da makeup artist har gida. Kaman wata maid of honor haka Anisa ta zak’e tana mata komai. Ummul bata daina karantarta ba. Cikin wata farar doguwar riga da dinkin ya zauna jikinta ta shirya. An mata dauri na zamani da irin fabric d’in rigar Wanda da gani zaka san an b’arar da kudi wajen sayensa da d’inkasa. Ba’a cika mata kwalliyar ba amma tayi kyau har ta gaji. Duk Wanda ya kalle ta sai yaso sake kallonta. Haka masu kwalliyan da shiryata sukaita santin kyaun da tayi. Ita dai Ummul gaba d’aya ranan ta kasa gane kanta gaba jinta take ba daidai ba. Something feels wrong. Sai kawai ta danganta hakan da fushin da Haidar keyi da ita. Koda akace ta fito su d’auki hoto da Haidar sai rashin nutsuwar da take ciki ya ninku. Zuciyarta yaci gaba da bugu. Yanda kasan bata tab’a sanin shi ba haka takeji. Da kyar ta iya fitowa k’irjinta sai bugu yake. Tin daga saman bene masu camera ke haskota har zuwa saukowarta parlorn basu daina d’aukarta hoto ta ko wani angle ba. Anisa ta dubeta ta saki murmushi “Relax Ummul, ki natsu a Miki hotuna masu kyau dan wad’ann hotunan a manyan mujallu zasu fito.. Mrs Haidar Maitama.” Ta kashe mata ido guda tana fad’in a d’auke su tare. Mommy ta k’araso tana dubanta kwalla kaman zai zubo mata ta k’arasa ta rungumeta “Kinyi kyau daughter.. May yours be among the best.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. Nan aka d’auke su hoto. K’wallan da Ummul take makalewa ya gangaro. Mommy tai saurin goge mata tana girgiza Kai “A’a Ummul, yau fah ba ranan kuka bane.. Bana so hawayen nan ya bata Miki kwalliya.” Ta waigo cikin k’ok’arin danne nata kukan tana tambayar wai ina Haidar d’in ne.? Anisa da takaicin acting Mommy ya isheta sai ta juya ido tana furzar da huci. Tana k’ok’arin barin wajen ta hango Haidar na shigowa cikin shiga ta farar shadda k’al babbar riga harda hula. Shigan da zata iya cewa bata tab’a ganinsa ciki ba. Sosai ya amshe sa dan ba Anisa kawai ba harta ita Ummul d’in saida ta shagala da kallonsa. Ya k’araso aka musu su uku da Mommy. Ta shige

Chapter 43 of 64