Share this page
makomar aurensa. Tasu’u wllhi sai ka sakar min ‘ya.!” Ta k’arashe tana dangwala masa paper. Bai rubuta ba hakan yasa samarin nan sukaci gaba da dukansa. Tasi’u da yaji bugu kaman zai Mutu sai yace su dakata su daina dukansa zai rubuta ma ‘yar Mama Tani Badia takardan saki da sharad’in samarin zasu mik’asa ga hukuma bazasu kashesa ba. Ya gwammaci su kira ‘yansanda su mik’a shi ga ‘yansanda da dai su masa dukan kisa wajen. Samarin sukace yaci darajan Mama Tani Ya rubuta takardan sakin su kuma zasu basa kariya bazasu bari a illatasa da bugu ba har ‘yansanda su iso. Haka kuwa akai Tasi Ya rubuta takardan sakin Badia Wanda Ya zame masa kariya daga dukan da yake kwasa. Mama Tani ta amshi takardan sakin tai hamdala kana tai godiya ma samarin tasa kai ta shige tana fad’in ta gode Allah da Ya kawo k’arshen auren ‘yarta Badia da miji irin Tasi’u. ** Kwanci tashi babu wuya wajen mai duka. A ranar da Ummul ta cika kwanaki arba’in da haihuwa Abba yace Ya cika alkawarinsa yau zata tafi ga mijinta. A zaton Ummul Haidar zai zo amma sai taga baizo ba. Aunty Asshe ce kawai tazo sann Abba bai bari wani daga gida Ya mata rakiya zuwa Abuja ba. A Cewar Abban tinda ba sabon aure bane kome ne ba sai an Tara mutane an mata rakiya ba. Daga ita sai Aunty Asshe da jaririnta suka nufi Abuja. Ummul taci kuka har ta gode Allah. Tarba mai kyau suka samu daga wajen iyayen Haidar baga Mommy ba baga Hajja ba an rasa waye yafi d’okin zuwan Ummul da jaririnta. Tuni an gyare musu masauk’i a b’angaren Mommy amma sai Hajja ta rok’i alfarmar Ummul ta zauna a nata b’angaren ta k’arashi bik’inta dan dama Mommy tace bazata tare gidan Haidar ba sai ta cika watanni uku da haihuwa. Koda Hajja ta buk’aci Ummul da ta zauna a b’angarenta Mommy cewa Tai hakan yayi dama ‘yarta ce. A b’angaren Haidar kaw da mugun mamaki yake duban Aunty Asshe yana jin wani sabon turanci wai Khairy bazata tare gidansa yanzu ba. Ya girgiza Kai kad’an still yana duban Aunty Asshe “Aunty, wai kina nufin akwai wani watanni biyu nan gaba da zan sake jira.?” Aunty Asshe tace “K’warai kuwa. Zancen kake so muyi Haidar. Mommy tace ‘yarta bazata tare da d’anyen jego ba sai ta cika watanni uku da haihuwa.” Girgiza kai yake disbelievingly “Unbelievable.!” Ya furta a hankali yana jinjina kai kafin ya gyara zamansa kad’an ya bud’e murya yace “Aunty ni kuma sai na zauna Har tsawon watannin nan ba mata.? Tsakani da Allah an min adalci kenan.? Seriously this is unfair fah.!” Yai maganar duk a gajiye. Ya dan fito daga cikin kujerar yana dubanta “Aunty you need to talk to Mommy. Knowing Mommy tinda tace sai Khairy sai ta cika watannin nan bazata bari ta tare d’in ba. Please Aunty do something.. Ki rarrashi sister dinki ta amince ta bani matata mu tafi. Aunty wllhi hakuri na gab yake da k’arewa.!” Ya k’arashe kaman wani maraya. Aunty Asshe dai tausayinsa taji kai har kunya saida Haidar yasa taji. Tinda Ya iya budan baki yace mata hakurinsa ya kusa k’arewa tasan an kusa wajen. cikin zuciyarta cewa take ‘Gata ake maka Haidar dan Mommy so take a gyara maka matarka sosai kafin akai maka ita. Ta yanda bama zakai tunanin ta haihu ba.’ A fili kuwa cewa Tai “Kai hakurin shekara sanda bata nan balle yanzu da watanni biyu ne jal bai cika wata biyu ba tinda Anci kwanaki arba’in already.” Girgiza kai yake yana furta “Aunty wancan lokacin daban. Nasan babu auren a wancan lokacin amma yanzu da aure. Thank goodness wann karon ba Mommy ce ta biya sadakin nan ba balle ta hanani Matata... Mommy Sam ta daina tausayi na Aunty. Kawai gwara na nemar ma kaina mafita.” “Ban gane ka nemar ma kanka mafita ba mai kake nufi Haidar.?” Aunty Asshe ta tambaya tana duban Haidar dake k’ok’arin mik’ewa. “Mommy taita ajiye ‘yarta amma Aure zanyi Aunty. Ki shirya zaki had’a mun lefe ko Mommy bata sani ba.” Ummul dake mak’ale jikin k’ofa tana sauraron su zuciyarta yai wani irin tsinkewa taga wani irin duhu ya gifta k’wayan idonta. Wani hajijiya Ya kusan aikata k’asa. Bata san sanda ta k’unshe bakinta ba cikin kokarinta na hana kukan dake zuwa mata. Muryar Aunty Asshe ta sinkayo tana ceda Haidar. “Dakata dakata.. Wane irin aure kuma Haidar.? Mai yai zafi.?” “Khairy da Mommy bakinsu d’aya Aunty.. Idan kuma kema zakiyi joining team din nasu ne fine. I’m used to fighting my battles alone.” Ummul bata ida k’arashe sauraron hirar Haidar da Aunty Asshe ba ta janye jiki da kyar ta fad’a kan gado tana rera kuka mai dalili. Shikenan itakam da gaske Haidar baya sonta. Badia tayi gaskiya da tace tana nan tana wauwauta zataji an shafa fatihan Aurensa a Abuja. Ashe dama aurensa yake nema Shiyasa Ya wofantar da ita bai kuma bi takanta ba. Kuka ya kuma b’alle mata. A haka Mommy ta shigo ta isketa. Da mamaki Mommy ke dubanta. Ta girgiza kai kad’an “Ahah.! Ummulkhair, kuka kuma.. meke faruwa.?” Tai saurin gyara zamanta tana k’ok’arin Had’iye kukan nata. Mommy ta zauna gefenta tana karantar ta sai tace “Lafiya kike kuka Ummulkhair.?” Shiru bata iya amsa Mommy ba tanata k’ok’arin danne kukanta. Ganin haka yasa Mommy yin shiru tana nazarinta. Sai ta tuna Haidar bai jima da ficewa daga gidan ba cikin yanayi na rashin walwala da fushi. Sann koda ta tambayesa abinda ke damunsa bai sanar da ita komai ba. Koda Mommy ta tambayesa bazai kwana nan gida ba sai ce ma Mommy yai no kawai zai tafi can gidansa Ya kwana da safe zai shigo. Ta tsare Ummul d’in sosai da ido kafin tace “Kunyi Sallama da Haidar d’in ne.?” Ambato sunansa da Mommy tai yasa ta kasa danne kukan kawai sai ta fashe da sabon kuka. Ganin haka yasa Mommy tsareta da ido tace “Fad’a min Haidar Ya Miki wani abun ne.?” Tai saurin girgiza kai “A’a Mommy.. Kawai.. Kawai ina kewan gida ne.” Mommy ta d’anyi still dan tasan bata fad’a bane kawai amma kukanta nada alak’a da Haidar. sai Mommy ta soma lallashinta ta k’arashe da fad’in “Gobe in sha Allahu YâGumsu zata taho daga Maiduguri.. Zata tayaki da kula da Baba Ali… Barin duba Hajjan taku.” Ta k’arashe tana mik’ewa. Da kai kawai Ummul ke iya amsa mata dan ita bama tace ta fahimci maganganun Mommy ba tsananin tashin hankalin da ta tsinci kanta ciki. Mommy ta fito tana sababin Haidar zaizo gidan Ya sameta dan ita bata yarda baima Ummul komai ba. Ta kula a yan kwanakin ‘yan halin nasa ne suka motsa. Tai k’wafa tana fad’in “Ai shi dama mai haki baya fasawa.” Aunty Asshe ta dubeta “Wai lafiya Aunty Kwaise keda waye haka.?” Mommy ta kuma yin k’wafa “Banda Haidar… Na rasa mai Ke yawo akansa cikin kwanakin nan.. Jibi dai yau Ummulkhair tazo gidan nan ya d’age kafafunsa yayi tafiyarsa. Allah kad’ai yasan wani bak’in cikin Ya tura mata Ya fita yai tafiyarsa. Kuka sosai na shiga na tadda tanayi..” Murmushi Aunty Asshe Tai ba tareda tace komai ba. Mommy ta dubeta baki sake “Aw dariya ma abin ya baki?” Aunty Asshe ta kuma murmusawa “Toh idan ba memanmu kukeda fitina ba Aunty Kwaise Kun dakemu kuma kukan ma so kuke ku hanamu.” Mommy tace “Ban fahimceki ba. Haidar d’in yace an masa wani abin.?” “Eh mana mun d’auko matar mu Kun k’wace a nan.. Ni yanzu duk laifina ma yake gani yace da na d’auko masa matasa da straight can gidansa na wuce da ita da ba’a masa fin k’arfi ba a nan.” Mommy tace “Aw wai duk wann fushi da kumburi da yake akan ba’a kai masa ita bace.? Ai kaw saidai ya fashe dan kumburi, ba ta yanda za’ayi akai masa yarinya da d’anyen jego. Kema dai Asshe so kawai kike ki biye ma rigimar Haidar amma ina aka tab’a haka. Yoh idan acan gida Maiduguri ne ai sai ta kwashe watanni ma bai sakata ko a ido ba.” Aunty Asshe ta murmusa “An rage al’adun nan fah yanzu Aunty Kwaise a duba al’amarin yarona kar azo ana cewa bamu kyauta ba. Iyaka hakuri fah munyi kar kuma a k’ure mana hakuri. Dan takaiga mun fara maganar k’arin aure.” Galala Mmmy ke duban Aunty Asshe “Haidar d’in ne ke maganar karin aure.?” “K’warai kuwa.” Aunty Asshe tace tana karanto ma Mommy yanda sukai da Haidar d’in. Girgiza Mommy tai had’ida tab’e baki “Rigima ce kawai irinta Haidar.. Kuje can kuyita auren naku ‘Yata tana nan sai na tabbata Martabanta Ya inganta.” Daga haka Mommy bata kuma bi takan Aunty Asshe da rigimar Haidar ba. ** A b’angaren Ummul kuwa sosai ta damu da zancen Auren Haidar gashi ta kasa sanar da kowa damuwarta. Ga Haidar kaman ya k’ara janye jiki da gidan. Ko ya shigo gaisuwa kawai ke kawosa saiko duba D’ansa sam baya bi takan Ummul har kawo wann lokacin. Iyaka damuwa da tashin hankali Ummul ta shigesa. Da kyar ta iya sanar da Hajja halinda take cik. Hajja ta lallasheta da fad’in ta cire damuwar Auren da Haidar yace zaiyi a ranta. Ta maida hankalinta ga karan kanta. Ta natsu ta kwantar da hankalinta. Dan ita tama fi so lokacin da Haidar zai ganta ya kasa ganeta. Ga gyara mai aminci da take samu daga Hajja harma da YâGumsu wacce da alama ba don kula da Baba Ali kawai Mommy ta kawota gidan ba harda kula da Uwar Baba Alin. YâGumsu sunada dangantaka da Daddy dan mazaunin Kaka take ga Haidar. Gyara na kankaro mutunci da dawo da martabar d’iya mace bayan haihuwa YâGumsu ke mata. Gyara tin daga ciki Har kawo fatarta daga waje. Kan kace mai Ummul tayi kyau ta k’ara haiba. Ga wani haske da shek’i na musamman da take ba’a maganan wani musulmi k’amshi da tuni yabi jikinta Har zuwa suman kanta. Ita da kanta jinta take ta canza kama daga matantakanta har zuwa gangar jikinta. Wasu lokutan sai ta d’auki wayarta tana duban layin Haidar kaman zatai dialing sai kuma ta tuno kashedin Hajja na cewa ta maida hankalinta ga karan kanta ta mance da zancen Auren Haidar. Cikin zuciyarta take furta ‘Toh ma ni ina ruwana.. Ba sai yaje Yata auren nasa ba. Dama ni sabida Abba da Mommy na amince da aurensa.’ Ta Kai dubanta ga YāGumsu da shigowarta kenan rik’eda Baba Ali yaron ya girma yayi wayau ga kyau da ya k’ara kaman D’an turawa bazaka ce d’an wata biyu bane. Ga shiga rai wajen duk Wanda ya d’ora ido kansa. A haka suka doshi watanni uku suna samun kula da tarairaya daga ita har jaririnta. Tayi k’ok’arin kauda tinanin Haidar cikin zuciyarta kaman yanda Hajja ta shawarceta. Ita zama ta iya cewa ta mance da Haidar d’in balle wani zancen aurensa. Sosai ta natsu ta kwantar da hankalinta. Idan tana tareda Baba Ali ba k’aramin d’ebe mata kewa yaron yake ba. Ya shiga ranta yanda baka tsammani. A sama ranan ta stinci hirar YâGumsu da Mommy. Yâ Gumsun na shirya Baba Ali bayan ta masa wanka take jajen uban Babagana kaman yanda take kiran Baba Alin. Mommy tace “Ai zaman Lagos ya auresa yanzu yana can kudu bai Faye zaman nan d’in ba.” Abinda Ummul ta sinkaya kenan taji kanta na juyawa. Wai zaman Lagos ya auresa.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.! Toh kodai Haidar aure yai ya aje matar a Lagos ba tareda saninta ba. Toh kodai ya b’oye ma Mommy zancen Auren nasa ne kaman yanda yace da Aunty Asshe zata had’a masa lefe ko babu sanin Mommy.. Idan ba haka ba maiyasa zai tare garin Lagos.? Sam bama ta kawo tunanin aiki ko wani abu zai iya kaisa Lagos ba. Haka ta yini d’aki tana faman sak’e sak’e. Duk yanda taso ta yakice tunanin ta kasa. Haka ta shige band’aki taci kukanta ita kad’ai tana mai tausayin kanta. ** Kwance take da hantsi d’akin Mommy. Idanunta a lumshe irin na mai bacci.. Baba Ali na cikin cradle d’insa dake nan d’akin Mommy shima baccin yake. Haidar da shigowarsa gidan kenan Kai tsaye d’akin Mommy ya nufo yana nemanta. Cak yai tsaye yana dubanta zuciyarsa na wane irin fuzga.. Ta masa kyau har ta gaji ga wani k’yalli na musamman da fuskarta keyi. Shi zai iya cewa rabon sa da ita ya mance.. A hankali yake takowa cikin d’akin kaman mai tsoron kada ya tadasu daga baccinsu. Yai tsaye akanta yana dubanta sihirtaccen murmushi saman fuskarsa. Ya furta “sleeping beauty” a hankali kafin ya zauna nan gefenta yana kuma k’are mata kallo tin daga fuskarta har zuwa d’an yatsarta. Ga wani musulmin k’amshi mai sauk’ar da nitsuwa da yai ma k’ofofin hancinsa Sallama tinda ya zauna kusanta. Bai san sanda ya rank’wafo sosai yana shak’an k’amshin nata. Idanunsa a lumshe yake shak’an dadd’an k’amshinta Wanda ya sauk’ar masa da natsuwar da ya mance yaushe rabonsa da yaji irin haka. Kaman a mafarki Ummul ke Jin hucin numfashin mutum saman wuyarta. Tai saurin bud’e idanunta masu cikeda bacci. Nan kaw sukai ido hud’u da Haidar fuskarsu dab na juna har tsinin hancinsu na had’ewa. Zuciyarta yai wani irin yankewa. Dan ita dai rabon ta da Haidar zata iya cewa ta mance.. Ta d’anyi yunk’urin mik’ewa a firgice amma sai Haidar yai saurin rik’o ta ya hanata mik’ewa. Ya tsareta sosai da rikitattun idanunsa. A hankali ya furta “I’ve missed you Khairy.. I’ve missed everything about you..!” Yai maganar yana mai kuma shigar da Kansa wuyanta “Your smell..! Your skin..! Your lips..!” Ya k’arashe yana gangaro da bakinsa zuwa labb’anta. Sosai ta rintse ido tana Jin hawaye na ciko idonta sanda ta tuna daga Lagos ya dawo can wajen matarsa. Sai taji kuka ma zuwa mata da gaske. Tai ta maza ta taresa daga jikinta kukanta na k’aruwa “Ni dai ka k’yaleni.. Ka koma can wajen matar taka.. Nida D’ana bamu buk’atarka.” Cak Haidar ya dakata yana dubanta cikin rashin fahimtar ina kalamanta suka dosa. Ya dan girgiza Kai kad’an “Wait.. What do you mean… Na koma wajen matata.?” Cikin kuka taci gaba “Eh wajen matarka da ka baro can Lagos.. Ni dai kawai ka koma wajenta ka kyalemu.” Izuwa lokacin dariya maganganun nata suka so basa. Yai k’ok’arin gimtse dariyarsa “Kinga.. Saurareni Khairy.” Ta mak’e masa kafad’a cikeda shagwab’a “Ni dai kawai ka koma. We don’t need you here” Ya jinjina kansa “Tinda bazaki saurareni ba shikenan.. Kece dai baki buk’atana amma D’a na yana buk’atana.. I’m sure he missed his Dad.” Ya k’arashe yana nufan gadon Baba Ali. Annurin fuskarsa ya k’aru sanda ya Ciro yaron daga cikin gadonsa. Yana kissing d’insa yake fad’in “Hello Son, Wakey wakey.. Dad is here..” Yai maganar sai kissing yaron yake yana mai cillasa sama yana fadin ya tashi daga bacci su gaisa. Haka ya fice da yaron cikin hannunsa sai masa wasa. Aka bar Ummul da matse matsen k’walla. Ficewar Haidar da Baba Ali da kad’an taji sak’o ya shigo wayarta. Ta janyo wayar tana dubawa zuciyarta yai wani irin tsinkewa. Kuka ta fashe dashi sosai ta nufo downstairs a guje tana ambaton Mommy cikin kuka. SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!* *61* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* Mommy taci gaba da jijjigata tana tanbayarta lafiya meke faruwa. Ummul ta kasa furta komai sai kuka da take tana girgiza kai. A haka su Hajja da Yaa Gumsu suka shigo suka taddasu. Sud’in ma bakin Mommy suka bi suna tambayar meke faruwa. Mommy tace “Yanda kuka ganni a nan tambayar da nake mata kenan.” Ta kuma duban Ummulkhair “Ina Baba Ali wani abin ne Ya faru.?” Cikin kuka Ummul ke fad’in “Baya nan Mommy.” Suka saki baki gaba d’aya. Mommy ta girgiza kai kad’an “Ban gane baya nan ba.. Wane irin bayi nan.? Inji tare na barku a d’aki kuna bacci.?” Murya Har na sark’afewa take fadin “Mommy Haidar Ya tafi dashi.” Mommy tace “Haidar kuma..?” Ummul ta kuma jin kai cikin sauri bata daina matsan hawaye ba “Ya shigo ya d’auki Baba Ali ya tafi dashi.. Mommy dan Allah Ki kirashi.” Ta k’arashe cikin shesshek’ar kuka. Da mamaki suke duban juna gaba d’aya. Mommy ta girgiza kai tace “Haidar kuma Ya tafi da Baba Ali..? Toh ina zai kaisa.? Yaushe ma ya shigo gidan.?” Yaa Gumsu ta dubi Mommy tace “Ah ah.! wai ba jiya nakeji kina cewa yana birnin ikko ba.?” Mommy tace “Dama akan yau jirgin safe zai biyo yazo shi Abuja. Amma bai sanar Dani ya taso ba.. Sann yaushe ma ya shigo gidan..? Sam banji alamunsa ba.” Yaa Gumsu taceda Ummul K’ila dai mafarki take amma basuga shigowan Haidar gidan ba. Ummul na kuka take fad’in ba mafarki take ba a shiga d’akin a duba babu Baba Ali Haidar ya tafi dashi. Mamaki Ya cika su Mommy gaba d’aya. Yaa Gumsu da Hajja suka nufi sama duba Baba Ali amma wayam bashi a makwancinsa. Mommy ta shiga dialing layin Haidar amma baya shiga. Neman duniya anyi ma Haidar wayarsa baya shiga. Ran Mommy idan yayi dubu ya b’aci k’wafa kawai take tana fad’in Haidar zaizo Ya sameta. Akan wani dalili zai d’auki yaro jariri mai shan nono ya fice dashi Har tsawon sa’o’i. Abu kaman wasa ba Haidar ba Baba Ali sann wayoyin Haidar kaf a rufe suke basa shiga. Lamo Ummul tai saman cinyar Hajja hawaye naci gaba da gangaro mata ga k’irjinta da tuni Sun ciko sai ciwo suke sakamakon ba mai sha. Ita bama physical pain d’in bane Ke damunta psychological pain din Ke dawainiya da ita. Tana jin Hajja na fad’in Tai hakuri haka ta daina kunan nan tinda dai Haidar ba cutar da Baba Ali zai ba. Cikin zuban hawaye tace “Hajja wa ya sani yaci abinci ko bai ci ba.? Koma kuka yake.? Waye zai hada masa abincinsa.? Waye zai canza masa diaper.? Hajja ni nasan kawai wajenta yakai shi..” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka. Hajja ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Wajen ita wa.?” “Wajen matarsa.” Ta bata amsa kai tsaye cikin rawar murya. Muryar Mommy suka sinkaya tana fad’in “Wajen matarsa.? Wace matar kenan.? Haidar d’in keda wata matar.?” Ummul taji kukanta na k’aruwa sai ta mik’e zaune tana jinjina ma Mommy kai “Eh Mommy.. wajenta yakai Baba Ali.” Hajja ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Ummulkhair kinkuwa ji abinda kikace yaushe Haidar d’in yai aure bamu sani ba..” Cikin kuka Ummul ke fad’in “Hajja da gaske aure yai.. Gashi Ya turo mun sako cewa Ya d’auke dansa kuma nasan ma matarsa zai kaisa.” Hajja ta girgiza kai kad’an had’ida murmusawa “Banda abinki Ummulkhair a ina Haidar zai tafi yai aure duk bamu sani ba..? Kuma har ya d’auki Baba Ali ya kaishi ma matar .?” Mommy tai k’wafa tace “Toh wa ya sani masa ne yanzu. Zai aikata tinda yayi a baya ba da sanin namu ba..” Ta d’aga waya da zummar kiran Aunty Asshe ko zata Sami wani bayani gameda Haidar d’in tinda tasan d’an gidanta ne amma sai Aunty Asshen ta riga kira. Mommy tace da Hajja “kinga ma Asshen na kira” Ta daga wayar tana jin da mai Aunty Asshe ta kirata. Aiko tambaya Aunty Asshe ta soma ma Mommy meke faruwa ne Haidar Ya mata waya yana tambayarta yanda ake had’a baby formula da canza diaper. K’wafa kawai Mommy take kafin tace “Zan kira kika rigani.. Kinsan yaron nan zuwa yai Ya d’auki D’ansa Ya kuma kashe wayoyinsa.. Wato iyakacina yake son nuna min.!” Hakuri ta fara ba Mommy tana fad’in “Kinga yace ma I should keep it a secret. Kawai so yake ya kasance da D’ansa.” “Dan yana so ya kasance da D’ansa shine sai Ya d’auke sa yai tafiyarsa Ya kashe wayoyinsa.. Waye Ya tab’a hanasa kasancewa da Dan nasa.?” Mommy ta kuma fad’i cikin fad’a. Aunty Asshe tace “A’a Aunty Kwaise banda son kai mana. Watak’ila bai Sami breathing space bane a gidan shisa ya fice dashi.. Keda Ummul kun suffocating min yaro. Ni dai dan Allah dake da d’iyarki ku daga masa k’afa haka nan yasha iska.” Gajeren tsaki Mommy tai tace maza Asshe ta kira mata shi. Daga haka katse kiran Tai. Sai fad’a take har saida Ummul taji ba dad’i dan bata tab’a ganin fushin Mommy irin haka ba. Har Daddy ya dawo gida ba Haidar ba dalilinsa. Daddy ma fad’a yai tayi yana fad’in wane rashin hankali ne zaisa Haidar Ya d’auki yaro jariri mai shan mama Ya fice dashi. Daddy yasa akai masa kiran Ummul. Duk sai jikin Ummul ya kuma yin sanyi wai yau ita Daddy yake kira sashensa. Gaba d’aya iyayen suna had’u parlorn Daddy. Mommy da Hajja ga Daddy daga nasa kujeran. Ta risina daga can gefe tana goge ragowar hawayen dake gangaro mata tana janyo mayafinta zuwa fuskarta. Ta risina sosai ta gaida Daddy da kyar. Mommy kam har lokacin huci kawai take ba walwal saman fuskarta. Daddy yaci gaba “Ummulkhair nasan kin d’aukeni kaman Abbanki.. Bazan bari wani abu na cutarwa ko rashin adalci Ya faru dake ba.. Kaman yanda nai alk’awari ma Abbanki.. Ki sanar Dani akwai wani matsala ne tsakaninki da Haidar.. Tinda nasan ba k’aramin abu bane zaisa Aliyu Ya d’auki jariri Ya fice dashi Har tsawon lokacin nan.” Ummul bata iya bama Daddy amsa ba sai hawayen dake ci gaba da gangaro mata. Mommy tai karaf tace “Wai har sako yake tura mata zai kai D’ansa ga sabuwar matarsa sabida shi ga shafaffe da mai.!” Daddy ya girgiza Kai cikin rashin fahimta “Sabuwar matarsa kuma.? Yaushe Haidar d’in yai aure.?” “Oho masa mana.! Iyakacina yake son nuna min tinda na hanasa matarsa bari yaje yai wani Auren Wanda ban isa da shi ba.!” Mommy tace cikin b’acin rai. Hajja tace “A’a fah Aunty Kwaise. Auren nan mai yuwa hasashen Ummul ne kawai amma Haidar bazai aikata abu makamancin wann ba.” Mommy tace ba maganar hasashe zai aikata dan ya nuna mata iyakarta. Daidai nan Haidar yai Sallama rungume da Baba Ali cikin abin goyo dake d’aure daga kafad’a zuwa k’irji. Hannayensa kuwa rik’e suke da manyan bags mai k’unshe da manyan teddies da dangin kayayyakin wasa na yara. Zuciyar Ummul yai wani irin tsinkewa. Yayinda iyayen nasa suka zuba masa ido gaba d’aya suna dubansa. Ga dai Baba Ali sai baccinsa yake peacefully rungume cikin k’irjin Babansa. Babu Wanda ya amsa masa gaisuwar nasa cikin iyayensa sai kaw Hajja. Mommy kam mik’ewa Tai ta isa garesa fuu fuska a matuk’ar tsare ta hau kwance belt din da ya rik’e yaron tana fad’in “Bani shi nan.!” A hankali Haidar ke furta “Mommy I’m sorry.!” Ya fad’i yana mai shan jinin jikinsa. Bata sami zarafin amsa sa ba ta koma mazauninta tana jijjiga yaron cikin hannunta. Daddy yai masa alama da hannu yace yazo Ya zauna. Ba musu Haidar Ya isa yanda Daddy ke nuna masa ya zauna a sanyaye. Daddy yai gyara murya yace “Aliyu.” “Na’am Daddy.” Haidar ya amsa a sanyaye. Dan yasan idan Daddy ya ambaci sunansa kai tsaye akwai bayani. Daddy yaci gaba “Have you realized what you’ve done.? Wani dalili zaisa ka dauki yaro jariri ka fice dashi ka rabashi da mahaifiyarsa Har na tsawon sa’o’i.?” Haidar yace “Daddy nayi kuskure Im sorry.. But I just wanted to spend time with my son.” Mommy tai karaf tace “Mu zaka fad’a ma kana son spending time da danka.? Ka cire yaro a nono na tsawon sa’o’i.. Kai ko tausayin uwa da D’an bazaka ji ba.! Harda turo sako kana wani cewa ka kaisa ma sabuwar matarka ko.? dan ka nuna min ni ban isa ba.!” Haidar ya dubi Mommy da mamaki “Mommy sabuwar mata kuma..? Ni Haidar.?” “Auho karya ma aka maka kenan..!” Daddy yace “Shi fah al’amari na aure ba abin wasa bane Haidar. Bai kamata ka maida wann word din abin wasa ba. Kai ya kamata kafi kowa sanin hakan.” Cikin d’aurewar kai Haidar yace “Daddy meyasa zanyi wasa da al’amarin AURE. Idan akwai Wanda zaifi daukan al’amari na Aure da mahimmanci that person should be me. Because I once joke with it kuma naga yanda Ya juya mun.” Mommy tace “Shi kuma sak’on da ka tura ma Ummulkhair na menene.?” Haidar Ya dan saci duban Ummul dake zaune daga gefe saman carpet d’in yace “Mommy ni ban tura ma Khairy wani sako mai kama da haka ba. Eh quite alright na shigo wajenta na tadda tana bacci.. I didn’t wanna wake her up sai na

Chapter 58 of 64