Share this page
bayan Inna Dije ta sanar da ita sab’anin halinda ta baro Ummul ciki. Cewa da gaske Suwaiba ta saida ta ne ma wasu irin mutane marassa imani balle mutunci. Ba yanda bataiba ganin k’ok’arin ta dawo da Ummul amma mutanen sunce kudi suka sa sukai sayi Ummul. Ko Kotu za aje bazasu iya kashe auren Ummul ba tinda tak’ama suke da kudi . Yacce kasan zamanin cinikin bayi haka aka saida ‘yaruwarta a wulak’ance. Knocking d’in ne Ya d’auki hankalinsu. Inna Dije ta mik’e tana tambayan wanene. Ga mamakinta Hilal ta kuma gani. Ya sakar mata murmushi yana gaisheta had’ida tambayarta mai jiki. Ta amsa tana tambayarsa lafiya. Ko wani mantuwa ne Asshen Tai. Hilal Ya girgiza kai alamun a’a. Sai ya k’ara da “Em.. Da Allah dama nace.. Emm yarinyar nan da na gani d’azu..” Dan shi dik had’uwar da suke da Khulsum kusan sau uku bazaice ga sunanta ba. Inna Dije ta katsesa “Wace kenan..?” Hilal yace “Emm.. K’anwar Matar Haidar.” Dan ya tabbata ta haka kawai za’a ganeta. Jin haka yasa Khulsum lek’owa tana dubansa dan taso d’ago muryar. Ai kuwa shi d’in ne dai. Ta galla masa harara cikeda takaici musamman da Inna Dije ta sanar da ita yanda sukai da danginsa akan ‘yaruwarta Ummul. Hangota da Hilal yai sai ta sakar mata murmushi Ya d’ago mata hannu alamun gaisuwa. Inna Dije da Tai k’ebebe bakin k’ofa tace “Toooh mai kake nema wajenta.?” Hilal Ya rasa abun fad’i. Sai ya soma ‘yan kame kame “Em.. Dama akwai wani sak’o ne da zan bata.. Idan hakan na matsala.” Ta dubeshi a dak’ile, sai Ta juyo ta dubi Khulsum, ta kuma duban Hilal “Minti goma. Minti goma na baka. Kuma kar kuyi nisa Ku tsaya bayan lambun d’akin nan yanda zanke hango ku ta window ehe..” Ta dubi Khulsum tace “Zo kije ina kallonku ta window.” Har lokacin hararsa kurum Khulsum take. Kaf danginsu ta tsanesu. Suka jera suna tafiya har suka isa zuwa wajen wani dogon kujera na shak’atawa. Hilal Ya nuna mata kujeran “Bismillah..” “Kaga Malam ba zuwa nan nai dan na saurareka ba. Zuwa nai na baka sak’o ka fad’a ma azzaluman danginka. Ni UmmuKhulsum ‘yaruwarta sai na raba wann auren k’etar da sukai ma d’ansu da ita. Ka fahimta.!” Hilal ta girgiza kai kad’an dan sai yanzu yake jin sunan nata “Ki rik’e sak’on ki dan bazan isar ba. Kinsan dalili.?” Ya tsareta da ido yanda take huci kafin yaci gaba “Ni ba maras kunya bane. Kuma Ina daraja iyayena.” Ganin irin duban da Khulsum ke masa ya sanya shi saurin d’aga hannayensa biyu alamun surrender “Look, I’m not implying anything here. Kar ki dauka da wani manufa. Quite the contrary.” Ya jinjina kai kafin yaci gaba “But honestly, abinda kikaima mahaifiyarki d’azu ba daidai bane. Ko meye mahaifiya tayi ta cancanci a saurareta…. Ko dan girman hakkin da take dashi akan D’anta. Nasan kin sani amma tunasarwa yanada kyau.” “Malam kai baka san komai ba. Kar ka bada shaida kan abinda Bakada masaniya.” Ta fad’a hawaye na gangaro mata dan ita kanta tana jin ciwon abun cikin ranta. Hilal Ya jinjina kai “Matsayin iyaye musamman mahaifiya Ya wuce a k’ullacesu. Barin baki wani labari gajere. Ya d’an kuma takowa ya zauna saman kujerar. Lokaci guda yaci gaba “A lokutan baya inada kusanci sosai da Abba na. Baya iya bacci ba tareda ya ganni ba.. Ko baya gidan mahaifiyata idan yazo Ya tadda ban dawo makaranta ba sai ya jira na dawo kafin ya tafi. Gidan stepmom d’ina da gidanmu isn’t that far. So takai ta kawo ko sallan asuba Ya fito sai ya biyo har gidanmu Ya tadani mun tafi tare. Toh wann tashi na da asuba da Abba yake sai yasa gaba d’aya naji bana son kusancina dashi a ganina tak’ura min yake yana yanke min bacci na.” Ya d’an murmusa yana girgiza kai “Back in the day, Haidar cousin d’ina yakan zo gidanmu yai kwanaki . Abin sosai yake birge Haidar yanda yake ganina tareda Abba na. What he’s been denied his whole life.” Ya girgiza kai “I know I shouldn’t be telling you all this amma ta kama ne shiyasa nake sanar dake.” Hilal yaci gaba “Bama son fita sallan asuba but Haidar yana mun sha’awan wann opportunity d’in na kasancewa da Abba na. Ko naji Abba yazo tada mu tafiya masallaci bana tashi sai na barsa yai knocking har ya hak’ura ya tafi. Amma sai Haidar Ya tadani dole yace mubi Abba masallaci ba tareda munyi alwala ba tinda shine bama sonyi wai mu gudun kar baccinmu Ya tafi. A haka za’ayi sallah damu idonmu a rufe muna bacci, idan mun dawo gida sai muci gaba da baccinmu.” Ya d’an dubeta ganin ta zuba masa ido “Hey ba wai fah bama yin sallah bane idan mun dawo gida. Quite alright zamuci gaba da baccinmu ne bayan mun dawo masallacin. idan mun tashi da safe sai muyi alwala muyi sallah mai alwala. Wai mu munyi dabara baccinmu bai gudu ba.. Crazy right.” Ya fad’i murmushi saman fuskarsa yana jinina kai. “That was then nake fad’a Miki. Lokacin k’uruciya.. Idan ban mance ba Babban Yayana Haidar kanshi bai rufa ashirin ba balle ni.” Ya fad’I haka tamkar wacce ta tsile shi. Hilal ya murmusa yana jinjna kai “I Guess a halin yanzu k’anan k’annena yaran third wife d’in Abba sun k’wace Fada na wajen Abba. Na daina ganinsa often musamman a gidanmu. And ya daina zuwa tadani sallan asuba. Ya zama everyday idan zan tashi sallan asuba sai na tuna Abba da yanda yake zuwa ya tadani koda baya gidanmu.” Ya d’ago ya dubeta “Moral of the story kar kayi wasa da damar da ka samu. Sometimes we don’t know the value of what we have in hand until we lose it. So please ki saurari mahaifiyarki tin kinada daman hakan.” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Lokaci guda ta mik’e yana fad’in “Barin tafi before you attack me da irin wann kallon da kike mun.” Khulsum ko janye k’afarta ta kasa jikinta yayi mugun sanyi da maganganun Hilal. Har ya soma tafiya ya juyo ya dubeta nan yanda ya barta tsaye “Kar fah wataran kiyi Haidar yaji labarin nan a bakin ki since he’s married to your sister now. My cousin will definitely kill me idan yaji na bada labarin k’uruciyarsa ma k’anwar matarsa. sallan da muka dingayi babu alwala.” Ya k’arashe yana murmushi. Har ya soma tafiya ya kuma juyowa “And.. kar ki damu zaki jima baki ganni ba daga yau. Cos I’ll be flying back to school in a couple of days. I hope zakiyi tunani kan abinda na fad’a Miki.. Goodbye.” Ya k’arashe yana d’ago mata hannunsa mai rik’eda mabud’in mota. Jiki a sanyaye Khulsum ta silale ta zauna saman kujeran tana dubansa yana tafiya har ya b’ace ma ganinta. Ba wai bata so ta aminta da kalamansa bane. Saidai har k’asan Zuciyarta bata in zata iya komawa ga Umma. Akan idon Inna Dije komai ya auku. Ta murmusa kad’an. Cikin zuciyarta take ayyana lallai idan hasashenta ya tabbata D’an Asshe son Khulsum yake ko shakka babu ta samu makamin da ta yak’i Asshe dashi cikin sauk’i tinda a halin yanzu Khulsum a hannunta take. Tsaf tasan ta yanda zata b’ullo ma Asshe bariki. Ta kuma sakin murmushi tana jinina Kai a hankali. A fili take furta “Asshe bariki kin shigo hannu.!” ** Hisham ya dubi mahaifiyarsa Wanda Ya kula gaba d’aya ranar kaman tana avoiding d’insa ne musamman da ya d’ago mata zancen Ummul. Bai kuma mata maganar ba sai shirin fita da yai da yammaci. A parlor ya taddata tana zaune tana kallon tv. Ta dubesa da mamaki “Ina zaka.. Kaida ba wasu abokai gareka a garin nan ba.” Ya d’an sauk’e ajiyan zuciya kad’an “Emm.. Gidansu Ummul na nufa Hajja.. Inaso naji ya jikin mahaifinta..” Bata san sanda ta mik’e tsaye ba. Ta soma girgiza kai “A’a Hisham.. Koda wasa. Ba kai ba mutanen nan har abada kuma.. Ka cire Ummul a ranka.” Hisham Ya girgiza kai cikin rashin fahimta “Hajja ban fahimceki ba.. Wai meke faruwa da Ummul d’in ne..?” Ganin mahaifiyarsa bata amsa shi ba ya sanya shi sakin murmushi mai ciwo “Kinje nema min aurenta kaman yanda kikace.. Suma sunyi rejecting d’ina kaman dai sauran ko.. Haka ne Hajja.” Yaci gaba da jinjina kai idonsa na kuma rinewa zuciyarsa na kuma karaya “Hajja I love Ummul. I sincerely do.. I want to build a family with her.. Ahalinda a kullum kike min fata da burin ki gani.” Katsesa tai “Ya isa na ce ka cireta a ranka. Kuma ko hanyar da Ya danganci ahalinta kar ka kuma bi.” Girgiza kai yake cikin rashin yarda “Hajja ki gafarceni.. Not that I’m being to pushy about this.. Kece kika fara saka mun hope akanta.. Yanzu da zuciyana ya tabbatar mun Ya kamu da sonta why the sudden change of mind.? Hajja Wai meke faruwa ne dan Allah.?” Ya k’arashe cikin rawar murya. “Abinda yake faruwa Hisham shine Ummul ta haramta a gareka.! Ummul tayi Aure.! Ita d’in matar wani ne a yanzu..!” Duban mahaifiyarsa yake cikin tsananin shock.! SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU.!* *25* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* Ya girgiza Kai kad’an disbelievingly “Hajjah.. Ban.. Ban fahimceki ba. Aure.? Ummul tayi aure..?” Ya kuma girgiza Kai “Ina nufin, wane irin aure kuma.?” “Zauna.” Ta fad’i tana nuna masa kujeran dake gefensa. Jiki a matuk’ar sanyaye Hisham ya ja k’afafunsa ya isa ya zauna had’ida zuba ma mahaifiyarsa ido. “Hisham, ba wann karon bane ka fara Neman aure baka samu ba. Ka kai sadaki, har an saka rana a wasu lokutan amma daga k’arshe an hanaka. Toh ina so ka saka ma ranka wann bazai zama na k’arshe ba. Kuma shi aure da kake gani nufi ne na Allah. Matar mutum kuma bazata wuce shi ba. A kullum hud’ubar da nake maka kenan. Kar ka saka damuwan rejecting d’inka da akeyi cikin zuciyarka. Lokaci ne kawai baiyi ba amma idan lokaci yayi zakayi Aure. Abinda yasa na maka sha’awan Unmulkhair ba komai bane face aminta da nayi da hankalinta, tarbiyarta da kuma addininta. Kaman yanda yazo cikin hadisin Abu Hurayrah Wanda bukhari ya rawaito ‘Manzon Allah (SAW) yace ana auren mace sabida abubuwa guda hudu, sabida dukiyarta, sabida nasabarta, sabida kyaunta ko sabida Addininta. Sai Manzon Allah SAW yace Na horeku da ma’abociya addini hannunka zai samu riba.’ Wann yasa nai maka sha’awar Ummulkhair.” Ta kuma daidaita zamanta cikin kujeran kafin taci gaba “Bugu da k’ari kaida Ummul kunada k’addara mai kamanceceniya. Dukanku Kun fuskanci k’alubale na lalacewar neman aure kafin akaiga auren. Toh amma a ko yaushe shi mutum ya zama mai d’aukan k’addara da hak’uri da jarabawar Ubangiji a yanda tazo masa. Duk iyaye burinsu kenan. Farin cikinsu kenan suga ‘yarsu ta natsu a gidan aure. Haka zalika idan namiji ne suga yayi archiving a rayuwa sann ya zama mutum mai cikan kamala yayi aure. Shi aure abun so ne ba abun gudu bane ba abun k’i bane. Hasalima ya inganta a hadisin Anas dan Malik wanda Bukhari da Muslim sukai ittifak’i akai. Cikin hadisin Manzo SAW ya tabbatar Aure sunnarsa ce kuma wanda ya k’yamaci sunnarsa baya tare dashi. Toh kaga kuwa aure sunnah ce mai girma kuma koyi ne da Manzo SAW. Yayi umarni ma samari da suyi aure ga Wanda Allah ya bama ikon yi. Domin shi aure yana tsare gani da kuma kamewa. Ga Wanda baida hali kuma yayi azumi domin shi azumi garkuwa ne. Hadisin Abdullahi bn Umar wanda Bukhari da Muslim suka rawaito shi.” Ta d’an numfasa “Toh kaga duk wad’ann hadisan suna nuni da aure ba abun k’i bane aure ginshik’i ne na ko wani Al’umma. But you can’t force it. Kuma ka nemi zab’in Allah cikin duk abinda ka sa gaba. Kana so kana buri kana kuma fatan kayi. Cikin aure akwai tarin albarka kuma ibada ne. Allah ya halicci ‘yan Adam jinsu biyu domin su samu natsuwa da juna. Kaga wann natsuwar sai ta hanyar aure za’a samu. Kai hak’uri d’ana, Kai hakuri da jarabawarka. Kai hak’uri da Ummulkhair. Ka cireta a zuciyarka ka nemi wata daban. Allah yasa haka shi yafi zama maka alkhairi da mu baki d’aya.” Sauk’e ajiyan zuciya Hisham yai yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa. Sai ya kifa Kansa na d’an lokaci. Ya d’ago yana duban mahaifiyarsa broken “Hajjah.. Hajjah wanene Ummul ta aura.?” Tambayar da ya haifar mata da fad’uwan gaba. Ta girgiza Kai kad’an “Shin baka d’auki k’addara bane.? Are you having doubts kan abubuwan da na sanar dakai.?” Girgiza mata Kai yai a hankali ba tareda da ita cewa komai ba. Hajjah Fannah ta jinjina Kai “Sanin waye Ummul ta aura baida wani alfanu wajenka. She’s someone’s wife now. Ka cireta gaba d’aya a ranka kuma kar ka waiwayi baya.. Ka min wann alk’awarin D’ana.” D’agowa ya kumayi ya dubeta. Sai yai murmushi mai ciwo “Kamar yanda kika ce Hajjah.. Zanyi kaman yanda kikace..” Ya mik’e yana kuma shafa fuksarsa “Inaga zan koma bakin aiki ko zuwa… Gobe idan Allah ya kaimu. If that’s with you.” Ya k’arashe jiki a mace. Sosai tausayin shi ya cikata. A hankali ta jinina masa Kai “Hakan yayi D’ana.. Allah ya tsareta da tsarewarsa ya baka dukkan kariya. Ya saka maka albarka cikin duk abinda ka sa gabanka.” Ya k’ak’aro murmushi ya sakar mata kafin yasa kai ya shige. Sauk’e ajiyan zuciya tai tana jin ciwon da D’an nata ke ji har cikin zuciyarta. Shin har yaushe zata ci gaba da b’oye masa.? Shin sai yaushe zata sanar dashi gaskiyan lamari gameda mahaifinsa.? Shin rufe masa da tai tayi daidai..? Shin yaushe zata sanar dashi gameda Ahalinsa.? Shin Anya wann ba alama bace a gareta na cewa ya kamata ta fayyace ma D’anta komai. Musamman da yanzu d’an uwansa ya auri Ummul.? Anya ba baya bane yake hunting d’inta..? Bayan ta datse duk wani alak’ar da take da tabbacin zaisa su waiwaya.. Meyasa kwatsam abubuwa ke neman sauyawa..? Shin Ummul zata iya kasancewa dalilin da zaisa su waiwayi baya.? Ta kuma girgiza kai cikin sauri. A fili take furta “Bana fatan hakan. Allah ya gani tsakani da Allah naso Ummul tamkar ‘yarda na haifa a cikina. Watak’ila iyaka lokacin da zamuyi kenan a tare. Tabbas ya zama dole na datse alak’a da Ummul da duk wani abinda zai had’a d’ana da Aliyu Maitama.” ** Abuja… Tsaf suka fito cikin shirin fita. Doguwar rigar abaya Anisa ta bata ta saka. Da shike kaf dogayen rigunan Anisa ta rage fad’insu hakan yasa ya kama Ummul sosai sai yafi kyau a jikin Ummul d’in saidai tsawo da ya d’an mata yawa sakamakon Anisar ta fita tsawo. Sai faman yatsina fuska Anisa take tana mata kallon wulak’anci. Mommy kaw suna fitowa ta mik’e ta isa ga Ummul wacce tuni ta sadda kanta k’asa. Murmushi saman fuskar Mommy take fad’in “Ki saki jikinki ‘Yata. Ki zabi duk abinda kike so. Ko menene.” Ta dubi Anisa “Ki tayata ta zab’i kaya masu kyau Wanda zasu k’ara fito da kyaunta. And make sure you take good care of her.” Anisa ta kauda Kai gefe tana rolling ido. Kuji Mommy fah wani wai ta kula da ita saikace watchdog d’inta or something.? “I’m talking to you Anisa kina kallon wani wajen. Kinsan bana san shashancin nan naki..” Mommy tace ba walwala. Anisa ta juyo fake smile saman fuskarta “Ok Mommy. Kaman yanda kikace .. I’ll take good care of your daughter in-law for you. I promise.” Mommy tace “She’s my daughter, not daughter in-law..” Anisa ta kuma kauda Kai tana fuzar da huci. Sai yanzu ta yarda da kalaman Haidar idan ya kira Mommy good actress. Tayi imani ba a banza take ma wann kucakar makahon so irin haka ba. Yarinyar da gaba d’aya duniyarsu ya banbanta. Su d’in gaba d’aya ma ba d’aya bane. Wai Hajiya Kwaise Maitama ke treating ‘Yar talaka haka. Wllhi idan za’a Mutu bazata tab’a yarda auren nan na Allah da Annabi akayi ba. Kuma ko menene ke rufe cikin auren she vowed to find out about it. Sai ta binciko to the core. Credit card Mommy ta mik’a ma Anisa bayan ta tambayeta zatai driving ko driver ya kaisu. Anisa tace no zata tuk’asu. Murmushi Anisa ta sakar ma Ummul harda bud’e mata front Seat gaban Mommy. Dan Mommy ta tabbata zata kula mata da sirkarta. Cikin zuciyarta kaw cewa take ‘I’ll play your little game Mommy har na gano bakin zaren komai.’ A haka suka d’auki hanya. Suna tafe Anisa ta d’aga waya ta k’ara a kunne “Hello Girlfriend kina ina..?” Ta murmusa “Toh ki bar duk abinda kike let’s go shopping.” Ta kuma darawa “Ok just wait there yanzu zaki ganni.” Tana Ida fad’in haka ta katse kiran. Tai parking ta dubi Ummul “Ke koma baya zan d’auki k’awata” Ummul ta dubeta sai ta murmusa. Kaman zata fita sai kuma ta fasa. Ta juyo ta dubi Anisa “Amma ba a gidan baya Mommy tace na zauna ba. Kiyi hak’uri bazan iya sab’a umarninta ba.” Ta k’arashe murmushi mai k’untata ma Anisa saman fuskarta. Hararta Anisa tai kafin taja motar. A haka suka k’arasa kusan wani k’aton gini mai gidaje iri guda a jere. Can wata budurwa ta fito cikin shigar Wando sai top bajajje wanda bai matseta ba sai d’ankwali d’aure kanta. Tana k’arasowa Anisa ta bud’e motar ta fito suka tafi a guje suka rungume juna suna kiran juna Girlfriend. Da mamaki budurwar ta tsaya tana kallon wacce ke zaune gaban motar. Ta juyo ta dubi Anisa “Neesa wacece kuma wann..?” Anisa ta rausayar da ido “Kinsan a duniya ba abinda ke burge bakauye irin zaman gaban mota. Kedai shige muje Leenah we gonna shop the entire city..” Ta k’arashe tana d’aga mata card d’in mommy dake hannunta. Leenah ta shige backseat sai labari suke itada k’awarta Anisa. Tanata k’are ma Ummul kallo wacce batabi ta kansu ba. Can Leenah Ta bangaji Ummul ta mik’a hannunta jikin radio na motar ta k’ure kid’a. Har lokaci Ummul batabi ta kansu ba. K’arshe hannu tasa ta cikin mayafi ta toshe kumnuwarta dan ita dama ba mai sauraron irin wad’an wak’ok’in na turawa bane. Sanda suka isa ma gaba sukai suka barota baya. Har sun d’an yi nisa kafin Anisa ta rausayar da ido ta juyo ta dubeta. Nan ta hange Ummul na kokawan d’alewa escalator. Sai kuma ta dubi Leenah “I can’t believe this is happening to me. I can’t believe we are hanging out da bagidajiya irinta. Dubi abinda take neman wani ya mana video yace tare muke. Anjima mu ganmu ana tagging d’inmu. Nidai yau Mommy ta kashe ni. Wann da kyar idan ba daga kauye aka d’aukota ba dan ba dai cikin birnin Kano ba.” Ta k’arashe tana furzar da huci. Daidai sanda Ummul ta k’araso “Kuyi hakuri takalmin ne nakeji kaman zai kadani.” Leenah da Anisa suka dubi juna suka dara a tare. Kafin Anisa tace “Malama karkiji Mommy ta ce na kula dake. If you go missing babu wanda zai b’ata lokaci wajen nemanki dan da alama this is your first time in a place like this.” Leenah ta tab’e baki sai kuma ta nufi wani wajen cikin sauri tana ambaton sunayen designers. Anisa ta rausayar da ido tana duban Ummul da Leenah ta barsu nan tsaye tare “Baiwar Allah. We are here already. Select what you want.. Ko shima sai na tayaki.?” Ta k’arashe tana kuma rausayar da ido had’ida furzar huci. Tuni Anisa ta tafi wajen k’awarta Leenah. Suka kyale Ummul ita kad’ai. Saida suka jida kaya nik’i nik’i suka tadda Ummul tsaye da wasu dogayen riguna da basu wuce uku ba. Duban juna suka kuma yi kafin Anisa tasa hannu ta finciki Kayan dake hannun Ummul. Ta d’aga kayan sama ta Ware tana gani Leenah na tayata “What.! Are you kidding me..? Wann shine iyakacin abinda kika iya zab’a tuntuni.?” Ta girgiza Kai tana kuma duban Kayan. Leenah tace “Wai zallan jallabiya ta zab’a. Ina zata dasu.. Ba azumi ake ba balle nace ittik’afi zata shiga.” Anisa ta girgiza Kai tana duban Ummul take d’aga rigunan “Baiwar Allah. We are shopping with Hajiya Kwaise Maitama’s card, we can buy the whole mall if we want.. And hello! You are married to Haidar Maitama. So get used to spending a lot.” Leenah baki sake take duban Anisa Jin ta kira budurwar da suke tare matar Haidar. Saurin janyota tai suka matsa daga kusan Ummul. Leenah ta dubi Anisa “Wait, did I hear that right..? Wann d’in matar Haidar.. Haidar Maitama da na sani. Our long time crush..?” Anisa ta juya ido “You heard it right. Wai wann d’in matarsa ce. Amma bana tunanin auren mai d’orewa ne dan dai tin jiya da aka kawo masa ita gidan he didn’t show up. Mommy ce kawai mai son Auren Amm Wanda akai domin shi baisan anayi ba da alama.” Leenah ta jinina Kai “No wonder. Dan dai wann hanyar da Haidar yabi ma bata isa bi ba.” Sai ta kuma gyara tsayuwarta tana duban Anisa “But what about you girlfriend. I know you love your cousin so much. Does that mean.. You give up..” “Giving up is not in my vocabulary Leenah. You should know better. Kawai lokaci na d’ibar masu. I have to study my target well before I strike.! But trust me sweetheart hakan zai faru ne kafin ta samu kusanci da Haidar.” Ta k’arashe makirin murmushi saman fuskarta. Leenah ta murmusa “Then do it fast sweetheart. Kinga irin wadnn makiran babu wuya sun saye Zuciyar namiji.” Dubanta Anisa take fuska a yatsune. Tai nuni da Ummul wacce mata me kula da kantin keta faman nuna mata wasu kalolin designs din. Anisa ta murmusa ta kuma duban Leenah “Haidar Maitama ya fada soyayya da wann bagidajiyar. You know what Leenah. I hate to burst your balloon but what you’re imagining is never ever going to happen.” Ta k’arashe tana kuma rausayar da ido. Leenah ta murmusa “Lallai Neesa toh barikiji na fad’a miki. You’ll remember this moment idan baki tashi tsaye tun yanzu kin kawar da ita ba. Ina nufin tun kafin Haidar ya zame Miki k’alubale wajen kauda ita.” Shiru Anisa tai sai kuma tace “I don’t want things to reach the point where I have to stain my hands.” Leenah ta murmusa “Then hire someone to do the job for you.. I can’t wait to get my hands dirty..” Ta k’arshe tana kashe mata ido. Juyawa tai ta kalli wani cream yanda aka rubuta do not apply on face. It contains strong fragrances that might irritate your facial skin. Ta murmusa ta kuma duban Anisa “Hey Girlfriend. Daga nan ya kamata mu ziyarci beauty Spa.” Tai maganar tana d’auko cream d’in ta nuna ma Anisa. A tare suka dara kafin suka k’arasa wajen Ummul suka ci gaba da tayata shopping kaman babu abinda ke faruwa. Har cewa Anisa take ita tasan taste d’in Haidar so zata zab’a ma Ummul kaya to taste d’insa. Ita dai Ummul bata tankasu ba amma jikinta ya bata wani abun suke shiryawa. Daga nan Beauty Spa suka tsaya. Ummul ta dubi Anisa “Mai zamuyi a nan.” “Face treatment sweetheart.” Ta bata amsa tana unbelting kanta daga cikin kujeran. “Amma ba abinda ya samu fuskata ni..” Ummul ta bata amsa. Gajeren tsaki Anisa tai “Beauty treatment ake magana ba sai kinji rauni ba. Dan Allah bani son stinginess naku na talakawa. Mommy card ta bayar mu k’arar dashi akanmu idan munso.” Ummul ta murmusa had’ida girgiza Kai ganin Anisa ta fice zata rufeta a mota. Koda suka shiga Ummul na hankalce dasu. Anisa da Ummul ake ma gyaran fuskar yayinda Leenah ke tsakani tana jira ta cika aiki kaman yanda suka tsara itada k’awarta Anisa. Ana fara face massage cikin dabara Leenah ta dauko wann cream din ta zuba cikin bowl din da aka kwaba kayan gyaran fuska na Ummul. Tana gama zubawa ta fice dama idon Anisa a lumshe suke sakamakon abinda aka daura mata saman idon. Ummul ta murmusa a hankali dan taga sanda Leenah ta matse tube din ciki. Aiko nan Ummul ta soma kokawan mik’ewa a birkice jin ana juyata mata fuska alamun bata saba ba. Aiko nan bowls d’in suka fado k’asa saidai basu zube ba. Ummul tai saurin d’aukan na Anisa wacce idonta ke lumshe sai faman tsaki take Bagidajiyar nan na bada ita. Ummul ta mik’a ma mai mata gyaran fuskar robar gyaran fuskan

Chapter 21 of 64