Ummul.. Dan Allah kar ka yanke hukunci Har sai ka saurareni… Duk abinda ke faruwa ko ince abinda Ya faru.. Babu wani mai laifi face ni.. Duka laifina ne…”
Daidai lokacin Haidar Ya shigo. Kafin Mommy ta k’ara furta wani kalma Haidar yai karaf yace “Abba duka laifi na ne.. Ni nayi AUREN WATA UKU da Ummulkhair.! Ni nayi Aure mai k’ayadadden wa’adi da ita. Auren da zai Wanzu na tsawon Watanni uku. Ni na tilasta mata ta Aureni dan ta Sami damar biyan kud’in jinyarka.! Na saka sadakin Ya zama kudin da za’a maka aiki dashi muddin ta amince da Aurena.. AUREN WATA UKU.. Dan na cimma burina na mallakan wani aiki k’ark’ashin kampanin mahaifina..” Muryarsa ya soma shaking “It is all my fault.! Duka laifina ne ni Aliyu.. Umma da Mommy duka basuda laifi.. Laifin nawa ne… Da nai irin wann wulak’antaccen Auren da Ummulkhair..”
Cikin tsananin shock Abba ke dubansa. Ya soma takowa yana dogara sandarsa Har ya k’araso gaban Haidar Wanda tuni ta sadda idanunsa k’asa.
Abba yaci gaba da girgiza Kai yana ma Haidar kallon k’iyayya “Kai.. Har ka isa.. Har ka isa ka saka rayuwar ‘Yata a matsayin farashi.?!” Hawaye suka soma gangaro ma Abba sanda yaci gaba “Waye kai..? Wa ya baka ikon wulak’anta rayuwar ‘Yata irin haka.! Ka amsa min waye ya baka dama.!”
Haidar ya rintse idanunsa rad’ad’in da yakeji a zuciyarsa na ninkuwa.
Abba yaci gaba da jinjina kai “Shiyasa ka d’aukoni ka kawo ni nan.? Dan ka goge zumubinka ne.? Ka amsa min.!”
Parlorn yai shiru sai hawayen dake gangaro ma Mama Tani, Mommy harma da Azeema.
Abba yaci gaba da jinjina Kai yana duban Haidar dake tsaye gabansa kansa kife. Yaci gaba da nuna Haidar da hannunsa mai rawa “ Ka sani, rayuwar ‘Yata baida farashi.! Gwamma ace na rasa nawa rayuwan.! Yata tana da daraja.. Tanada k’ima.. Kuma ta wuce ayi irin wann wulak’antaccen Auren da ita. Zan tabbatar maka da hakan.!” Yaci gaba da jinjina kai yana haki da kyar. Lokaci guda ya dubi Tani yace “Ki shige mu tafi bamuda wajen zama a wann gidan.!”
Jiki a sanyaye Mama Tani da Azeema suka nufi hanyar d’aki yayinda Mommy ke k’ok’arin shawo kan matsalar amma ko kallo basu ishi Abba ba daga ita Har Haidar d’in balle Ya tanka musu.
A haka suka fito zasu wuce Haidar yai saurin kiran Sadis a waya ya sanar dashi Ya d’aukesu komin dare ya tabbata sun isa kano cikin k’oshin lafiya da izinin Allah.
Bayan tafiyarsu a waje Mommy ta iske Haidar. Ta zauna gefensa su duka biyun ba mai cewa komai.
A hankali Haidar Ya furta “It’s so painful and tiring Mommy…”
Ta janyosa jikinta tana Shafa sumarsa kadan “This too shall pass”
Haidar yace “Yaushe ne duka wad’ann zasu wuce Mommy.? It’s one challenge after another.”
Mommy ta jinjina kai “Wann sunnar rayuwa ce Haidar. Haka rayuwa ta gada. You cannot expect life to be hundred percent perfect.. Dole yau idan anyi dariya wataran zaayi kuka… Yau gareka gobe ga waninka.. Tsanani yana tareda sauk’i.. Duka wad’ann zasu zo su wuce.. All you need to do is put your trust in Him.. Ka saka yardarka wajen Allah shi kad’ai. Da sannu zai yaye mana duka matsalolinmu Ya cika ahalinmu da alkhairi.”
Anisa ta hangesu daga saman bene tana murmushin cin nasaran kauda iyayen Ummul daga cikin picture d’in. Tinda taga Mommy bata nuna mata b’acin ranta gareta ba ya kuma tabbatar mata Mommy ta aminta da ta d’ari bisa d’ari. Yanzu ta tabbata zatai maganar Aurensu da Haidar dan dama tayi hakan ne dan ta samu ta kauda su a wuce wajen.
*
Koda su Abba suka isa Kano bai gane gidansu ba. Dan tuni an sauya fasalin gidan an d’aga gini na zamani gaba d’aya gidan hasken lantarki irin manyan fitilun solar d’in nan sun haske gaba d’aya layin. Ya dubi Tani da mamaki ganin ta nufi wann gidan da Ya sauya fasalin unguwar gaba d’aya yace “Nan kuma ina kika kawo ni.?”
Azeema ta d’an dubesa tace “Abba gidanmu ne fah.. Baka gane ba.”
Rai bace ya dubi Tani yace “Mai nake gani Tani.? Me hakan yake nufi.?”
Jiki a sanyaye Tani tace “Malam mu shiga mana tukuna.. Dare yayi sosai..”
Abba ya girgiza Kai cikin b’acin rai “Bazan shiga ba.. Bazan shiga wann gidan da aka ginasa da kudin da aka sayi Ummu ta ba.. Ki shiga ciki ki kirawo mun Suwaiba da duk wani ahalina dake cikin gidan. Ni Malam Isbusu na gama kwana a wann gidan.!”
Tani ta furzar da huci kad’an yayinda Sadis Ya k’araso yana rok’on Abba da yai hak’uri Ya shiga gidan. Dan motan Sadis d’in ma da fari bai yarda ya shiga ba saida Sadis Ya sanar dashi ba kobon ahalin Haidar jikin motarsa kafin Ya amince Sadis Ya kawosu Kano. Da kyar, har saida Sadis da Azeema suka kirawo ma Abba Dattijan unguwan da yake jin nauyinsa suka saka baki kafin Ya amince Ya shige cikin gidan. Ya kuma sanar da illahirin ahalinsa cewa basu ba Haidar da danginsa. Ko mai kamannin Haidar baiso Ya sake gani yazo yanda yake. Hakan yasa dole Haidar janye jiki da gidan musamman duba da irin yanayin rashin lafiyar da Abban ke fama dashi. Masu lalura irin wann dole lallab’asu ake had’ida guje ma duk abinda zai b’ata ransu.
Haidar ji yake tamkar Ya zama hopeless.. He’s tired and exhausted.. Ji yake Duk wani k’warin gwiwar sa da k’ok’arinsa sun gama k’arewa musamman yanzu da ya tabbata Abba baya b’angarensa. Ya tabbata koda Khairy ta bayyana zai matuk’ar wahala abubuwa su zo masa da sauk’i.
Furzar da huci ya kumayi a karo na Babu adadi yana duban hotonsu da aka musu ranar aure dake aje gefen bedside lamp d’insa an saka cikin k’aramin frame.
Ya d’auki hoton had’ida k’ura ma hoton ido. Cikin wane irin siga yake furta “where are you Khairy..? Do you hate me this much.? Haven’t I suffered enough.” Ya girgiza Kai kad’an “Ya isa haka Khairy. I’m exhausted..! Please, enough with the punishment. I can’t bear the pain anymore. I can’t Khairy..!” Ya k’arashe yana shafa fuskarta saman hoton. Ya d’an d’auki lokaci yana duban hoton kafin Ya mik’e kaman Wanda aka zaburesa. Shiryawa yai Ya fito Ya nufi sashen mahaifinsa.
Mommy da Daddy duk suna zaune parlor. Daddy na kallon news channel yayinda Mommy ke k’ok’arin mik’ewa tana fad’in zata shiga ta kwanta nan sukaji sallaman Haidar. Suka dubi juna da mamaki kafin Daddy ya bud’e murya yace “Haidar.? Is everything all right.?”
Haidar yace “Lafiya Daddy.. I’m sorry na shigo dare yayi.”
Daddy ya girgiza Kai “No.. No problem.. K’araso shigo mana.”
Haidar yaci gaba da takowa Mommy na hankalce dashi.
Ya zauna daga kusan k’afan Daddy. Ya gaida iyayen nasa. Bayan sun amsa Mommy ta k’arada “Inji dai lafiya.?”
Ya d’an murmusa kad’an “Lafiya Mommy.. Dama wata ‘yar magana na shigo muyi.”
Mommy ta tsaresa da ido “Kuma maganar baza’a iya yinsa da safe ba sai cikin daren nan.?”
Daddy yace “Haba Kwaise ki kyalesa muji binda yake tafe dashi mana.” Ya dubi Haidar “Ina saurarenka meke faruwa.?”
“Daddy dama akan Kasuwancinmu dake can SouthAfrica ne.. Ina so wann karan na tafi SouthAfrica a maimakon Kai and take care of our Business there.. If that’s ok with you.”
Daddy yana dubansa yake jinjina Kai “Of course that’s totally fine with me. In fact abu ne da nake matuk’ar so kuma yake cikin tsarina.. But duba da yanayin da kake ciki yasa ban kawo maka wann bukatar nawa ba…”
Da farko Mommy ta nuna k’in amincewarta a cewarta bata so D’anta yai nesa da ita musamman yanzu da rayuwa ta koma masu tamkar sabuwa. Da kyar Daddy da Haidar sukai convincing dinta da fad’in ba zuwa can zai Ya zauna gaba d’aya ba. Kaman yanda Daddy yake tafiya lokaci zuwa lokaci haka shima zai yi.. Kuma hakan zai d’an basa dama yai taking break regarding abubuwan dake faruwa.
Da kyar Mommy ta amince ita kuwa Anisa hankalinta ne Ya tashi ganin mutumin da tayi komai dominsa zai kufce mata Ya tafi wata uwa duniyar. Saida Mommy ta lallabeta da fad’in ba jimawa Haidar zai a SouthAfrica ba sann da zaran Ya dawo maganar bikinsu za’ayi. Kar ku mance Har kawo wann lokacin Anisa da Mommy ne kawai ke zancensu ko Haidar d’in baisan da labarin ba balle akaiga sako iyaye maza cikin maganar.
Idan Anisa ta tuna tana tare da yarda da amincewar Mommy kawai sai taji Har ta mallaki Haidar an gama hakan yasa ta kuma kwantar da hankalinta dan tasan dik daren dad’ewa dole Haidar ya dawo ya aureta kasancewarta zab’in mahaifiyarsa. Dukda zatai kewar fuskar da take matuk’ar so amma idan ta tuna Mommy tace da zaran ya dawo sai maganar aurensu ne tinda by then ya mance da batun Ummul sai Anisa ta tsinci kanta cikin annashuwa.
Aka bar Anisa da k’irga kwanaki tin bayan tafiyan Haidar. Daga lissafin kwanaki har ta shiga satittika ta soma k’irga watanni. Hisham na sanar da ita update gameda Ummul da cikinta. Tin bayan da ya warke ya komo Abuja bakin aikinsa sann shi yaima Haidar rakiya har zuwa Airport sanda Haidar d’in zai tafi SouthAfrica.
Hisham ya sanar da Anisa da zaran Ummul ta haife cikin zai salwantar da abinda ta haifa ya rufe Shafin Haidar cikin rayuwarta.
A lokacin da Haidar ya cika watanni uku a SouthAfrica a lokacin yake sanar da Mommy shirinsa na dawowa gida. A wann lokacin kuma Aurensu da Ummul ya cika watanni tara da mutuwa. Haka zalika Ummul ta shiga watan Haihuwarta.
Tinda Mommy ta shelanta labarin dawowar Haidar Anisa ta gaza zaune ta gaza tsaye Angonta zai dawo. Tuni ta fidda Ankon bikinta tsakanin kawayenta. Ko sanar ma Mommy batai ba dan ma kar Mommyn ta dakatar da ita. Dan a halin yanzu kam ta gama shiri ta kuma lashi takobin zama matar Haidar Maitama. Duk wann bidirin da take iyayen nata kansu basu da labari. A cewarta saidai suga IV musamman Amminta wacce har kawo lokacin basu koma normal da mahaifiyar Haidar ba. Bazata bari sab’anin dake tsakaninsu ya mata sanadin farin cikinta ba. Gwara kawai idan an gama komai Ammi taga IV.
*
Illahirin ma’aikatan gidan suna kitchen suna aikin abincin sauk’an Haidar. Mommy na tsakani tana directing nasu yanda take so komai Ya kasance perfect. Yayinda Anisa ke zaune gaban make-up artist da ta kirawo Har gida ana tsara mata make-up d’in tarban Angonta Haidar. Ga wata Uwar bridal gown da taci yanda kasan wata amarya. Ranta fari sol kaman yanda rigar tata take. At last mafarkinta zai zama gaskiya.
Daga k’ofan d’akin sukaji ana knocking. Anisa sai tsuka take dan a zatonta d’aya ne daga cikin ma’aikatan gidan. A hasale tace “Wai wayene wajen.?! Na fad’a muku I don’t want anything before dinner.. Bazan saka komai a bakina ba sai Mijina yayi landing.!”
Aka ci gaba da turo k’ofan ana tafe hannu. Cak Anisa ta ja tai turus. Ba shiri ta ture hannun mai make-up zuciyarta naci gaba da bugawa. Ta mik’e a firgice had’ida juyowa tana duban wacce ta shigo. K’iris Ya rage Anisa bata kife k’asa ba. Jikinta ya d’auki kyarma ta shiga nunata da dan yatsa “You.!!!”
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*53*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
“Surprise.! Surprise.!!” Ta furta tana duban Anisa daga sama zuwa k’asa murmushi saman fuskarta.
Anisa ta dubi makeup artist d’in tace ta basu waje. Lokaci guda ta tako zuwa gabanta tana huci take fad’in “Mai kike a nan Leenah..? What exactly do you want from me.?!”
Leenah taci gaba da murmusawa tana duban Anisa “Haba Amarya.. Ai ba’a san amare da fushi ba. Kar ki b’ata kwalliyarki..” Ta karada “Kashh kinga Har kin fara jurwaye tun ango bai gani ba.!” Ta kamo bakin rigarta ta soma k’ok’arin gyara ma Anisa kwalliyar tana fad’in “Ki adana guminki Anisa dan ba’a fara wasan ba balle ki jik’e da gumi.”
Anisa ta kai hannu fusace ta bige hannun Leenah tana huci “I don’t have time for your stupid games Leenah.! Just tell me once and for all Mai ya kawoki gidan nan a daidai wann lokacin.?!”
Leenah ta kuma murmusawa tana duban Anisa sai ta isa ta zaune saman sofa ta d’aura k’afa d’aya bisa d’aya “Kar ki damu I’m not here to blackmail you.. Nazo tayaki murna ne. Girlfriend… Ko ince .. Mrs Haidar Maitama.! Oh! Na mance. Soon to be..” Ta k’arashe tana fad’ad’a murmushinta.
Anisa ta had’iyi abinda ya toshe mata mak’ogoro “Kinga Leenah ki tashi ki fice. Ba Wanda ya gayyaceki.”
“This is where you are wrong Neesah.!” Leenah tace tana dubanta. Sai ta kuma murmuswa “Amma Hajiya Kwaise tasan duk abubuwan da kika aikata..? Ina nufin kin sanar da ita kece kikai sanadin rufeta a cell..? Kaman yanda bana haufin kece kikai sanadin had’arin motar da D’anta ya kusa rasa ransa ciki.!”
Anisa bata bari Leenah takai aya ba ta k’araso ta shiga janyeta tana fad’in ta tashi ta fice ko ta kirawo mata securities.
Leenah ta finciki hannunta tana huci itama take duban Anisa wann karon “Kin zata zan barki kici banza ne.? Yanzu ba sai anjima ba zan wargaza duk wani shirinki Anisa. Dan sai na sanar da Hajiya Kwaise wacece ta zuba ma Ummul poison ta kuma d’aura mata blame d’in.” Tana ida fad’in haka tasa Kai zata fice Anisa tai saurin fincikota ta maidota baya. Ta marairaice fuska kaman zata fashe da kuka take fad’in “Oh no.. Sorry Leenah.. Please don’t expose me.. Tell me how much money do you want.?” Tana ida fad’in haka sai ta kece da dariya tana kuma duban Leenah wacce itama da mamaki take dubanta. Anisa ta dubi Leenah daga sama zuwa k’asa tace “Haka kike so nayi right.? Toh kinyi k’arya Leenah. Bazaki tab’a ganin haka daga wajena ba. Kina tsammanin Mommy zata yarda dake ne.? Idan bata yarda dake ba a baya meyasa zata yarda dake yanzu Leenah.? Kar ki mance kinada tabon sharrin sata da kikai ma Ummul a idon Mommy. And hello.! Last time I checked, Mommy ta miki iyaka da gidan nan. You might be charged with trespassing sweetheart.”
Shiru Leenah bata ce mata komai ba. Anisa tai murmushin cin nasara “Ko mai zaki sanar da Mommy Leenah kin riga kin makara domin a halin yanzu Mommy ta aminta Dani d’ari bisa d’ari.!” Taci gaba da zagaye Leenah tana fad’in “You can go ahead and tell Mommy everything Leenah. It’s my word against yours. Kije ki ce mata Ni Anisa ni na canza turaren da ta bani na bama Ummul na kuma zuba guba ciki.! Ni Anisa ni nayi sanadin jefata a cell har ta shafe kwanaki.! Ni Anisa ni nayi sanadin had’arin motan da Haidar ya kusa rasa ransa ciki dan kawai naga bayan Ummul.! Ni Anisa ni nayi sanadin mutuwan Auren Ummul da Haidar sann zan tabbatar Ummul da abinda ke cikinta basu dawo cikin rayuwar Haidar ba.!”
A daidai nan sukaji an bud’e k’ofar d’akin. A tare suka waigo suna ganin waye ya bud’e, ba kowa bane face Mommy cikin wane irin yanayi da basu tab’a ganinta ciki ba.
Jikin Anisa ya d’auki rawa sai ta fashe da kuka ta nufi Mommy tana nuna mata Leenah take fad’in “Mommy kisa securities securities Ki koreta. Kin mata iyaka da gidan nan tin lokacin da ta k’ulla ma Ummul sharrin sata.. Kuma wlhi ni yanzu ba kawata bace babu abinda ya hadani da ita.”
Anisa bata Kai aya ba taji sauk’an Mari maiji da lafiya a k’uncinta. Ta d’ago a firgice tana duban Mommy wacce fuskarta ya gama rinewa haka ma idanunta.
Anisa ta dafe k’uncinta bata daina kallon Mommy da mamaki ba. Murya na rawa take fad’in “Mo..Mommy..” Nan ma bata Kai aya ba Mommy ta kuma d’auketa da wani marin. Tana kuma tasowa ta sake Kai mata wani Marin..Sai Anisa ta duk’a a k’asa tana kuka tana dafe duka b’angaren fuskanta. Ta soma jada baya cikeda tsoron Mommy.
Leenah tasa k’afa ta take k’afar Anisa dake daga zaune tana jan jiki Wanda hakan ya hanata motsawa.
Leenah na k’are mata ma Anisa dake duk’e kasa dafe da fuskanta tana bin Mommy harma da Leenah da kallon tsoro. Baki na rawa Anisa tace “Waht’s… going on here…?”
Leenah ta katse ta “Hm Anisa kenan. Kin zata ke kad’ai ce kika iya buga wasan.?”
Sai ta murmusa kafin ta saka hannu ta Ciro kwalban turaren da Mommy ta bama Anisa dan ta bama Ummul Wanda bata ma Ummul d’in ba suka canza da mai guba.
Baki sake Anisa ke dubanta tana duban kwalban turaren. Ya akai ya isa hannun Leenah.? Sai ta tuna lokacin da Ammi ta dauketa suka tafi Kano ta bar turaren nan d’aki cikin wardrobe bata tafi dashi ba. K’ila Leenah ta shigo ta bincika ta samu kenan. Muryar Anisa na rawa ta d’ago hannaye ta had’e waje guda tana duban Mommy “Mommy Kar ki yarda da duk abinda Munafukar nan zata sanar dake.. Wllhi Mommy sharri take mun ni bansan komai ba. Bakin ciki take mun taga zan auri Haidar.”
“Idan kika sake magana sai na d’aukeki da wani Marin.! Maras mutunci kawai. Ai da Haidar ya aureki Anisa gwara ya k’arashi rayuwarsa a haka.!” Mommy ta katseta tana ci gaba da huci. Lokaci guda Mommy ta k’araso gabanta “Banida lokacin sauraran sauran makircinki bayan Wanda naji da kunnuwana. Abu d’aya zan tambayeki yanzu Anisa, ki fad’a mun ina Ummul take.?!”
Anisa na hawaye take ci gaba da girgiza kai “Mommy dan Allah ki min rai.!”
“Zaki fad’a mun yanda Ummul take ne ko sai nasa anyi k’asa k’asa dake.!”
Daidai lokacin suka sinkayo muryar Haidar da shigowarsa gidan kenan.
“What is going on here.?.. Mommy did you mention Whereabouts d’in Khairy..?”
Suka waigo gaba d’aya suna dubansa yayinda Haidar yaci gaba da shigowa d’akin.
Idanun Mommy naga Anisa dake duk’e tana kuka taci gaba da nunata da yar yatsa “Gata can Haidar.! Anisa ta jima tana k’ulla abubuwa a cikin gidan nan ba tareda mun Kai hankulanmu kanta ba. Anisa da muka dauka shashasha wacce bamu bama al’amarin ta mahimmanci… Anisa itace ta k’ulla ta kuma wargaza a gidan nan.!”
Cikin rashin fahimta Haidar ke girgiza Kai yana duban Mommy ya kuma dubi Anisa. Sai ya kara duban Mommy yace “Mommy.. Ban fahimceki ba..”
Mommy taci gaba da jinjina Kai “Yau zaka fahimci komai Haidar. Kaman yanda watanni k’alilan baya na soma fahimta.” Taci gaba da jinjina Kai “A lokacin da na soma zargin Anisa sai na tafi Kano na dawo da ita gidan nan dan na tabbatar da zargina akanta na kuma Kamata red handed. Na karanci Anisa na tsawon watanni yanda na fahimci ita d’in ta jima tana sonka.. Sann duk abubuwan da ta aikata da sunan soyayyar da take maka ne..!”
Da mamaki Haidar ke girgiza Kai “Ni kuma.. Anisa.. Anisa ke sona. Did you hear yourself Mommy..?!”
Mommy ta jinjina Kai “I couldn’t believe it either har saida na gano abubuwan da ta tapka in the name of tana sonka. Bayan na gano haka sai na nuna mata ina tareda ita d’ari bisa d’ari.. Na nuna mata tanada goyon bayana zan maka umarni da ka aureta.. Nayi wasa da tunaninta kaman yanda ta jima tanayi da namu. Nan na binciko yanda wann kawar tata take dan ban mance wani rana da suka k’ulla tuggu ma Ummul su biyun har naima kawar tata iyaka da gidan nan.” Mommy taci gaba da jinjina Kai “Anisa itace ta zuba ma Ummul poison a turare dan ta kasheta slow dead sann ta d’aura blame d’in akaina.! Anisa itace tai sanadin had’arin motan da ya auka muku kaida Ummul duk dan ta kashe Ummul ta cireta daga cikin rayuwarka.! Anisa ita ce tai sanadin mutuwan Aurenka da Ummul Wanda bana haufi bakinsu d’aya da wancan azzalumar da ta aureka ta hanyar sihiri.. Anisa tasan yanda Ummul take tsawon lokacin nan.! Sann..” Sai Mommy tai shiru tana ci gaba da huci “Sann tana saneda cewa.. Ummul is pregnant har ta shiga watan haihuwarta.. Duka Anisa na sane da wann tsawon lokacin nan.!”
Gumi ne ke gangaro masa tin daga tsakiyar sumarsa har zuwa goshinsa.. Ga jijijiyoyin jikinsa dake kuma mimmik’ewa.. Ya saki k’aramin briefcase din dake hannunsa. Yayinda yaga wani duhu ya gifta k’wayar idonsa..
Anisa ta soma jada baya tana hawaye take girgiza Kai ganin Haidar gaba d’aya ya rikice ya sauya mata. Cikin rawar murya tana jan jiki tak fad’in “ No Haidar please.. Haidar..! Haidar dan Allah ka yarda dani.. I did everything out of love… I didn’t mean to harm you or Mommy.. Wllhi nayi komai ne sabida ina sonka.. Kuma.. Kuma wllhi ban tab’a had’a baki da Dareen ba… Sann..” Bata Kai aya ba Haidar ya shak’ota da iyaka k’arfinsa yana wani irin huci “I will kill you..! I swear I’m going to kill you.!” Wane irin huci kurum yake yana shak’e wuyan Anisa har saida Mommy ta soma k’ok’arin janyesa.
Baza’a kira abinda ke tsartsafowa daga cikin idanunsa hawaye ba saidai ruwan tururin k’unan zuciya.
“Tell me..! Tell me. Where is my wife..?!” Yai maganar gumin dake tsartsafowa ta ko wani kofan sumar dake jikinsa naci gaba da gangarowa.
Anisa ta soma sosa wuya da kyar tana tarin azaba take fad’in “Zan fad’a maka.. Please let go..!”
“Tell me now..!” Ya kuma fad’i yana fidda huci kaman zaki.
“Ta.. Tana Bauchi…”
Mommy ta dubeta da mamaki “Bauchi.?”
Anisa taci gaba da jinjina Kai ga gumin azaban da ya wanke umburarren fuskarta da ya sha tafin Mommy ba adadi.
“Bauchi wajen wa.? Mai ya kaita Bauchi.?” Cewar Mommy.
Anisa taci gaba da jinjina Kai daga durk’ushe kaman Marianiyar Kenyawa “Wajen mahaifiyar Hi… Wajen mahaifiyar Hisham.”
“Hisham..!” Mommy ta maimaita cikin tsananin mamaki da rud’ani dan tama rasa tuna waye Hisham. Yayinda Haidar yai mutuwar tsaye yana nanata abinda Anisa tace cikin kwanyarsa.
“Waye Hisham kuma.?” Mommy ta tambaya.
Anisa ta yarfe gumi da hawayen da suka gauraye mata fuska “Hisham Abokin Haidar.. Bansan dalilinsa ba amma ya jima yana bibiyan Haidar da ahalinsa da sharri. Kuma.. Kuma bakinsa d’aya da Dareen tare suke k’ulla komai tin kafin na had’u da Hisham.. Hisham has been shadowing Haidar for quit some time.. Tin kafin Ummul ta shigo rayuwarka.”
Kalmar Shadow da Haidar yaji ta ambata sai Ya tuna masa wani rana Ya taba jin Dareen tana waya da wani mai suna Shadow koda Ya tambayeta sai tace Uncle dinta ne.
Muryar Anisa Ya kuma dakan dodon kunnensa “Sann koda Ummul ta shigo rayuwarka sai akalar yakinsa Ya koma ga k’udirin raba tsakaninku. A cewarsa shi ya fara ganin Ummul ya kuma fara sonta kafin Haidar….Ni kawai.. Kawai nayi tarayya da shine dan na cimma burina na mallakan Haidar kamar yanda yake so ya mallaki Ummul.. Kuma ya d’au alwashin raba Haidar da Ummul ko ta wani hali.”
Juyawan da Mommy zatai b’at suka nemi Haidar a wajen suka rasa.
Anisa ta soma k’ok’arin mik’ewa tana Neman gafaran Mommy. Mommy ta nunata da dan yatsa “Kika kuskura kika motsa daga yanda kike sai nasa an canza Miki kamanni da bugu. Munafuka azzaluma.!”
Leenah ta dubi Mommy tace “Amma ai ni zan iya tafiya..?”
Bata rufe baki ba sai ganin wasu mata guda biyu sanye da Kayan ‘yansanda Sun shigo d’akin ma’aikaciyar gidan na directing nasu.
Mommy ta nuna musu Anisa da Leenah tace “Arrest them.”
Anisa ta saka hannu biyu aka ta kurma ihu tana fad’in “Mommy ki min rai.. You can’t send me to jail.. I’m your niece.. You can’t do this to me Mommy.. Wayyo na shiga uku ni Anisa.”
Leenah ta katseta “Ba ke kika shiga uku ba Anisa ni kika jefa a uku.. Allah ya isa ban yafe Miki ba. Yau ga yanda bak’in shashancinki da son zuciyarki ya kaimu.. Wayyo ni Leenah guba kawai na kawo ba ni na zuba ba ma Ummul ba.!”
‘Yarsanda ta tasa k’eyar Leenah tana fad’in “Ki k’arasa bayaninki a station. Move.!” Ta k’arashe tana hankad’eta.
Haka aka tasa k’eyar Anisa da Leenah aka wuce dasu police station.
*
Tinda ya fice yake sharara gudu saman kwalta. Waya manne kunnensa na hagu. Sadis yake kira. Sadis na d’agawa Haidar yace “I need a plane ticket to Bauchi. Right this instant.!” Bai kuma tsayawa sauraren Sadis ba ya katse kiran yana ci gaba da tururi. Fuskar Hisham kurum yake hangowa. He trusted him. He believed in him. How could this be possible.? Hisham.! Hisham fah.. Mutumin da ba komai a tsakaninsu face zallan gaskiya, yarda da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 50 Chapter of 64