Share this page
d’an dubesa. Sai Hisham ya murmursa “Ban sanar da ita ina tafe soon ba. I want it to be a surprise.” Gajeren murmushi Haidar yai “Idan bazatan zai sanayata farin ciki.” Hisham ya jinjina kai “I hope so.. Nayi kewar Hajjata.. She’s my everything Haidar.. Ina mata son da bayada iyaka.. Na girma matsayin maraya amma bansan maraici ba sabida ita.. She’s my two in one.. Zatayi komai domin farin cikina..” Haidar ya jinjina kansa a hankali yana jin rayuwar abokin nasa total opposite da nasa rayuwar. Amma sabida k’arfin hali irin nasa sai ya kauda tunanin yana mai ci gaba da abinda yake. Saidai da alama tunanin yak’i barinsa, Ya kasa yakicewa daga zuciyarsa. Sosai Hisham da mahaifiyarsa suka birgesa. Inama shine yakeda kusanci irin haka da nasa mahaifiyar. Ba abunda ya nema ya rasa a rayuwarsa ta duniya face soyayyar iyayensa guda biyu. Da ace dukiya shine farin cikin rayuwar duniya tabbas da ahalinsu ya cika da farin ciki. Saidai kash sab’anin haka ne cikin ahalinsu. Da ace za’a karb’e duk abinda suka mallaka na duniya a azurtasu da farin ciki kwanciyar hankali da soyayyar junarsu tabbas da sai yafi masa duk wann k’yale k’yale na duniya da suketa bautuwa akai. Ya d’an limshe idanunsa yana mai canza direction d’in tuk’insa. Can k’asan zuciyarsa yana jin akwai gibi babba cikin rayuwarsa. Har ya iso k’ofar gidan mahaifinsa yana tunanin shiga ya duba Mommy wacce sukai kwanaki basuyi koda magana ta waya ba kaman dai ba d’ah da mahaifiya ba. Ringing d’in da wayarsa tai ya dakatar dashi. Dareen ce mai kiransa hakan yasa ya fasa shiga gidan ya juya Kan motar. ** A can Kano kuwa Tuni an tura Abba babban asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano. Ana kan basa kula na gaggawa had’ida da masa gwaje gwaje da yake bukata. Mama tai saurin funcuke takardan da likita ke mik’a masu tin kafin Umma ta mik’a hannu. Sai ka ranste tasan mai aka rubuta cikin takardan ne. Ta shiga juya takardan tana dubawa “Babu damuwa Likita za’a sayo maganin Allah sa babu tsada..” Dr dai bai tsaya sauraronsu ba yasa kai ya shige. Mama ta kuma yatsina baki tana juya takardan “ Toh ma Wai Ina yaga kud’ad’en da zaa masa jinya ne wai.. Wllhi Suwaiba keda d’iyarki dai anyi annoba.. Ummul ta haddasa masa wann ciwo..” Jiki a matuk’ar sanyaye Umma tace “Kar kice haka Yaya..” Ta watsa mata harara had’ida jan tsuka kafin tai saurin tare wata nurse da tazo shigewa “Yauwa ‘yar nan dan Allah nace ba ko zaki iya duba mun mai aka rubuta takardan nan..” Nurse d’in ta amshi takardan tana dubawa “Sunayen magani ne da allurai..” Mama tace “Tooh inji dai basuda kud’i..?” Nurse d’in ta d’an kuma duban Mama “ Magunguna ne da allurai masu kud’i dan allura guda a nan yakai dubu goma.. Kije pharmacy zasu Miki bayani..” Bata kuma tsyawa sauraron Mama ba tasa Kai ta wuce. Mama ta waro idanu “Tirk’ashi toh idan jinyar Malam da tsada haka ai akwai matsala dan irin wann babban jinya kankataraf sai ya cinye d’an abinda zai bari ma yaran nasa bayan babu shi..” Ta juyo sosai tana duban Umma “Wann duk laifinki ne Suwaiba.. Ke da ‘yarki ku kuka kashe Malam a tsaye dan haka sai Kuje ku nemo kud’ad’en da zaa masa Jinya.” Cikin rawar murya Umma ke furta “Haba Yaya ki dubi yanda muke fah.. Asibiti fah muke.. Sann meyasa zaki d’aura alhakin ciwon mijinmu kaina nida ‘Yata.. Kinsan bazamu tab’a so haka ya same shi ba..” “Ke dalla rufe mun baki munafukar banza da wofi idan ba takaicin Ummul da hayagaganki ba me ya janyowa mijinmu ciwon zuciya.. Kinji na rantse Miki da Allah kije ki nemo kud’ad’en masa jinya.. Ina zaki samu bai dameni ba kawai abinda na sani shine alhakin ciwonsa na wuyanku keda Ummul.!” Jin hayaniya yasa wasu nurses k’arasowa suna masu fad’an asibiti suke ba dandali ko kasuwa ba idan hayaniya zasuyi zasu koresu. Mama tai saurin nuna Umma “Kun ganta nan ita zaku kora itace silan ciwon mijina gashi zata k’ara masa. Tinda mijina ya aureta tsiya ke bibiyarsa, Kayan kantinsa ya daina bunk’asa ta kuma haifo masa annoba wacce kowa ke gudu.” Nurse guda tace “Malama wann ba matsalar mu bace zan kira security yai waje dake idan bazaki mana shiru ba.” D’ayar tace “Visiting hours ya shige mutum d’aya ne zata iya zama, ki gode ma Allah mijinku ya samu d’aki mai d’aukan mutum guda godiya ga sabuwar gwabnatinmu dake k’ok’arin inganta hark’an kiwon lafiya da yanzu dole ku nemo namiji da zai zauna.. Yanzu mace d’aya cikinku zata tafi..” Ai bata Kai aya ba Mama ta nuna Umma “Itace zata tafi dan bamu San idan ya farka ya ganta mai zai faru ba tinda ita da d’iyarta ne silan ciwon.. Na tabbata zuciyarsa bugawa zai idan ya ganta.” Umma ta girgiza Kai tana duban Mama “Kiji tsoron Allah Yaya.” “Da tsoronki zanji Suwaiba.!” Ta girgiza Kai kurum tasa Kai ta fice tamkar kazar da k’wai ya fashe ma a ciki. A haka Umma ta dawo gida cikin jimami. Aiko tin daga bakin k’ofa take sinkayo sautin yaran Mama Salima Badia da kuma Azeema Sun saka Ummul gaba sai kwashe mata albarka suke suna fad’in ta kashe auren Azeema bai isheta ba zata kashe masu mahaifi toh wllhi idan mahaifinsu ya Mutu ta dalilin bak’in cikinta sai Sun d’auki fansa akanta. Duk fad’a irin na Khulsumu da k’ok’arin karb’ar ma ‘yaruwar tata ‘yanci yau sai ta gaza tab’uka komai sakamakon tuno halin da mahaifinsu ke ciki Wanda yake tsakanin rayuwa da mutuwa. Umma ta k’araso da sauri ta rungume Ummul. Umma kuka Ummulkhairy kuka. Kaman an jefo Mama haka ta shigo gidan tagajan magajan. Ashe koda Umma ta fice ta biyo bayanta. Nan ta tadda yaranta na d’iban albarka wa Ummul da mahaifiyarta. Mama ta cab’i zancen daga sama “Shisa nace bazan bari Suwaiba ta kwana wajen mijinmu ba. Kuma sun gama rab’ansa har Allah ya tashi kafad’unsa daga ita har ‘yar tata. Zuriyan annoba.” Azeema tace “Kinyi daidai Mama dan wllhi ko ni nan ko kan gawan mahaifina bazan bari Ummul taje ba.!” “Ya naji ana zancen gawa.. Abban ya cika ne..?” Badia tace tana dubansu. Mama tace “ Baidai cika ba amma yana hanya. Dan idan ba’a samu kud’ad’en da zaa masa jinya dasu ba nan da kwanaki k’alilan toh fah mahaifinku zai zama gawa silan wad’ann..!” Ta k’arashe tana nuni dasu Umma. Sai sann da abun ya ishe Khulsum ta mik’e idanunta na zubda hawaye take dubansu gaba d’aya “Tir da hali irin naku.. Tir da ahali irinku.. Abba na gadon asibiti kuke maganganun marassa kan gado irin haka.. Idan burinku ya Mutu ne domin ku tozarta ‘Yaruwata da mahaifiyata in sha Allahu babu d’aya daga cikin burinku da zai cika.. Allah zai tashi Abba zai basa lafiya sann rayuwar mahaifiyata harma da ta ‘Yaruwata zai inganta.” “Ke rufe mana baki k’aramar maras kunya.!” Mama tace tana huci. Badia da Azeema suka soma k’ok’arin kwance d’ankwali zasu yi d’amara. Badia na dukan k’irji take fad’in Mama ta k’yaleta ta gurji bakin Khulsum yayinda Umma ta mik’e da sauri ta tare yaranta guda biyu hawaye bai daina ambaliya a fuskarta take fad’in “Yaya dan Allah kuyi hak’uri.” Ta dubi su Salima kafin taci gaba “Ku tuna halinda mahaifinku ke ciki.. Yanzu ba lokaci ne na tada rikici ko nuna yatsa ba. Yanzu lokaci ne da ya kamata mu had’e matsayin ahali ko dan samun lafiyan mahaifinku.. Kunfi kowa sanin yanayin gidan nan yanda ‘yanubanci ya raba kan ahalin tin kan iyaye da kakkanni.. Idan bamu had’e kawunanmu ba kunfi kowa sanin babu mai yiwa mahaifinku kaf gidan nan. Dan Allah muyi hakuri duka mu nemawa Malam lafiya koda da abinda ya mallaka ne.” Mama tai saurin katseta “Ban gane koda da abinda ya mallaka ba.. Yo me ma ya mallaka da zaa masa jinya dashi.?” Umma ta jinjina kai “K’warai ya mallaki kanti. Ko Kayan ciki aka sayar da gaba d’aya kantin na tabbata zaa iya rage wani abin saura sai a nema wajen bayin Allah tinda ga yanayin ciwon nasa ciwo ne da za’a buk’aci kudade ga yanda komai ya koma a k’asar.” “Ke malama da Allah dakata.!” Mama ta katseta kafin taci gaba “Wllhi Suwaiba kinji na ranste Miki idan ina numfashi babu mai saida shagon nan.. Toh a bar ma yaran nawa mai..? Inyi.. Shikenan su koma basuda gadon mahaifinsu miji ya samu abun goranta masu ..? Toh ahir d’inki wllhi koda wasa kar na kuma jin wann batu daga bakinki.. Idan keda yaranki Baku buk’ata mu muna buk’ata dan bazai yuwu Ana shafe shekaru bila adadi ina dawainiyar Malam a barni fankinfayo ba.. Ke bari ma kiji na fad’a Miki.. Wann ciwo dai ba warkewa zai ba dan haka bazamu zubda dan abinda zai bari Akan jinyar da ba tashi zai ba. Shi fah irin wann jinyar kaf abinda ka mallaka sai ya k’are ba’a samu biyan buk’ata..” Ta d’an dakata kafin taci gaba “Toh ma ai Suwaiba keda yaranki bakuda gadonsa dan Kune kuka kashe sa.. Ku kuka jaza masa wann ciwo.. Ko a sharia duk Wanda ya kashe wani bai cin gadonsa.. Dan haka Kun fita da fitarku.! Ko ku nemo kud’ad’en da zaa masa jinya ko ya rub’e a gadon asibiti. Ta juyo ta dubi yaranta “Kusha kuruminku babu uban da ya isa ya tab’a maku gadonku ina raye ehe.!” Yaranta suka rangada shewa suna kuma ingizata. Daga Umma har Khulsum da Ummul Cak kukansu ya d’auke suka ma nemi kukan da suke suka rasa. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Wacce irin duniya muke rayuwa ciki.? Ace iyalanka daka rayu dasu ahalinka Wanda kafi kowa kusanci dasu ba damuwarsu ya zaayi ka samu lafiya ba. Ashe damuwarsu mai zaka Mutu ka bar masu ne..? Shin ina allan attajiran dake tara dukiya kota halin k’ak’a su Mutu su bar ma magadan da ko tausayinsu basa ji balle suyi masu addu’a.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Matarka da ‘ya’yanka.. Hasbunallah wa ni’imal wakil.. Muyi ma kanmu karatun ta natsu tun munada dama kafin dama ta kufce mana. Mu Gina ma kawunanmu ayyukan alkhairi. Mu d’ibi dukiyoyin mu muyi aikin alkhairi dasu tun munada dama. Mu Gina ma kawunanmu sadaka mai gudana har bayan rayuwarmu dan ba Lallai abinda ka bari su maka ba. Allah ka bamu ‘ya’ya masu albarka Wanda su kansu zasu zame mana sadaka mai gudana Ameen. Wann rana da jimami Umma da yaranta suka yini. Ummul ta dubi Umma su duka biyun idanunsu a kod’e “Umma yanzu ya zamuyi. Haka zamu bari Mama da yaranta suyi yanda suke so..?” Khulsum dake gefe ta k’ura ma waje guda idanu tace “Mai kuke tunanin a gidan da cikin Umma ma gaba suke da juna balle ‘yanuba..?” Umma ta kuma goge hawayenta dan ta d’ago ina maganar Khulsum ya dosa. Ummul ma tai saurin d’agowa ta dubi Khulsum sai kuma ta dubi Umman “Umma ko Inna Dije zamu kira mu sanar da ita halin da Abba ke ciki..?” Shiru Umma tai kaman mai nazari kafin ta girgiza Kai tace “Har yau babu Wanda yasan abinda ya haddasa gaba da k’iyayya tsakanin mahaifinki da tilon ‘yaruwarsa da suka fito ciki guda.. Mahaifinku ya b’oye mana bai sanar damu abinda ya rabasa da Dije ba.. Amma ya datse alak’a da ita kuma itama ta datse alaqa damu.” Khulsum tai saurin d’agowa ta dubi Ummul wacce keta k’ok’arin danne marayan kukan dake taso mata jikinta har rawa yake tamkar wacce ta tuna wani abu. Lokaci guda Khulsum ke ci gaba “Tin sanda Ya Fa’iz tilon d’an Inna Dije ya rasu Abba da Inna Dije basu kuma zama ‘yan uwa ba.” Take Ummul tai boasting cikin kuka mai tsanani ta mik’e ta nufi uwar d’aki. Umma ta dubi Khulsum “Maiyasa Khulsum.. Maiyasa zaki ambato mata Fa’iz… Meyasa zaki d’ago mata wann mik’i..” Sai kuma muryarta ya soma rawa. Cikin rawar murya take furta “Tinda Fa’iz ya koma ga mahaliccinsa ahalinmu bai kuma daidaito ba.. Tabbas da Fa’iz nada rai duk abubuwan da suke faruwa watak’ila da basu faru ba.. Tabbas da Fa’iz na nan a raye da yanzu Ummul d’ina ta jima a d’akinta.. Allah sarki Fa’iz ka tafi ka barmu da tarin k’alubale da iftila’i.. Tabbas rashinka babban gurbi ne a garemu.. Ka tafi da kurwar ahalinmu Fa’iz…!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka. Khulsumu ta k’araso ta rungume mahaifiyarta. Cikin rawar murya take furta “A’a Umma duk abinda ke faruwa tuntuni rubutacce ne.. Allah ya nufa hakan dole sai ya kasance.. Wann itace k’addaran ahalinmu.. Auren Adda Ummul kuma ko ya Faiz na raye ko baya raye bazai tab’a faruwa ba sai lokacin da Allah yaso. Umma kiyi k’ok’ari kiyi tawakkali da sannu Allah zai kawo mana mafita kinji Umma ta… In sha Allah Abba zai samu lafiya kuma farin ciki zai dawo cikin ahalinmu da izinin Allah.!” Umma ta rungume ‘yar tata kuka na kuma kufce mata. Tamkar wacce aka sinkara haka Umma ta janye jiki daga na khulsum. Ta shiga girgiza Kai tana duban Khulsum d’in “Yaya tayi gaskiya Khulsumu, Anya ba wani mugun k’addara bane yake bibiyan ‘yar uwarki..? Meyasa Fa’iz ya Mutu kafin yakai ga aurenta.? Meyasa tin bayan da Fa’iz ya bar duniya duk wani maneminta basa kaiga aure maganar ke watsewa.. Shin Anya ba alak’ar Ummulkhairy da Fa’iz bane yai Ajalin Fa’iz..? .. Anya ba wann dalilin bane ya raba tsakanin ‘yan uwa biyu..? Ina nufin mutuwar Fa’iz shine ya raba tsakanin Mahaifinku da ‘yaruwarsa.. Anya ba Ummul ce tayi sanadin Fa’iz ba.?!” SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU.!* *09* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* Saurin rik’e bakin Umma Khulsum tai tana girgiza Kai “Haba Umma wace irin magana ce wann.. Umma magana kike fah kaman bakiyi imani da k’addara ba..Umma na zaci ciwon Abba ya dawo dake hayyacinki daga wann rashin tawakkalin.. Haba Umma saikace ba musulma wacce ta yarda da k’addara ba..” A zafafe cikin zuban hawaye Umma ta katseta “Ki gaya mun cikin abunda nace wanne ne ba haka ba..?! Ki gaya mun Khulsum..!” Taci gaba da kuka mai sauti tana girgiza Kai “Bak’in K’addaran Ummul shine yai ajalin D’an ‘yaruwar mahaifinku Fa’iz..! Bak’in k’addaran Ummul shine ya raba tsakanin mahaifinku da ‘yaruwarsa.! Bakin k’addaran Ummul shine ya jefa mahaifinku halinda ya tsinci Kansa ciki..! Bak’in k’addaran Ummul shi yake sa ko wani namiji ya guje ta..! Bak’in k’addaran Ummul shi ya jefa ahalinmu cikin yanayin da muka tsinci kawunanmu ciki..!” Kaman daga sama sukaga Mama ta d’age labulen parlorn. Ta jinjina Kai tana duban Umma “Na gode ma Allah da yasa kika furta duka wad’ann da bakinki Suwaiba.. ‘yarki Ummul itace tai sanadin Fa’iz.. Yaron kirki aka lik’a masa annoba aka rabasa da rayuwarsa.. Toh wllhi kinji na ranste Miki da Allah bazan bari ‘yarki ta kuma kusantar mijina ba balle ta lashe nasa kurwan.. Kai kaf d’inku babu mai kusantar min miji..” Khulsum dake faman sakin huci goge hawayen dake kwance saman fuskrta tai ta k’araso gaban Mama “Wllhi wllhi banga Wanda ya isa ya hanamu ganin mahaifinmu a asibiti ba..” Badia ce ta k’araso ta tsaya gaban mahaifiyarta tana murmushi tana duban Khulsum dake ci gaba da sakin huci. Lokaci guda ta d’ago hannunta dake rik’e da wayar salulanta. Take tai playin recording d’in muryar Umma da tai sanda take fad’in Ummul ce tai sanadin mutuwan Fai’z harma da ciwon mahaifinsu. Tana gama playing suka kuma sakin murmushi itada Mama. Mama taci gaba “Ko Kotu aka tafi wann kad’ai ya ishemu shaida… Badia shige mu tafi wajen mahaifinku..” Daga haka sa Kai sukai zasu shige Khulsum ta yunk’ura zatabi bayansu Umma tai saurin dakatar da ita tana girgiza Kai hawaye na fita mata dan kukan nata ya daina fita da sauti. Khulsum ta dubi Umma. Ta rasa k’unci ne ko takaicin mahaifiyar nata ne k’unshe cikin Zuciyar “Haba Umma.. Haba Umma, kinga ga irin abinda nake fad’a Miki.. Yanzu makirar matar nan zatayi amfani da wann damar ta iya cutar da mahaifinmu.. Umma dan Allah wai sai Yaushe zaki daina maganganu marassa kan gado fisabilillahi.. Umma a gabanki matar nan da yaranta suke lissafin mai Abba zai Mutu ya bari. A bayyane take so suke mahaifinmu ya Mutu.. Umma mai zai faru idan sukai amfani da wann damar suka k’arasa mahaifinmu dake kwance gadon asibiti.. Umma kin cuce mu wllhi idan Mama da yaranta suka k’arasa Abba ba kowa ne Sila ba face ke.!” A guje Umma tabi bayan su Mama tana rok’onsu su rufa mata asiri kar sukai ma hukuma muryarta da Badia ta nad’a cikin wayarta. Takaici ya kuma Kama Khulsum dan tasan yanzu Mama da ‘yarta Badia Sun samu makamin shashantar da Umma dole su tilasta mata yin duk abinda suke so musamman da sukaji tana tsoron wai sukai recording d’in da Badia tai ma hukuma. Khulsum ta bud’e murya tana kiran mahaifiyar tasu. Lokaci guda take furta “Umma ki bi bayansu su Kai ki ma hukumar kinga ‘Yaruwata ma ta huta da muggan kalaman da kike jifanta dasu duk wayewar garin Allah.!” Tau!!! Taji sauk’an mari saman k’uncinta. Ta d’ago da mamaki tana duban Ummulkhairy data d’auketa da Marin. Lokaci guda take furta “Shin Kinsan girman mahaifiya Khulsum..! Shin Kinsan matsayin mahaifiya..? Shin Kinsan darajarta Akan ‘ya’yanta..?” Cikin huci Khulsum take duban Ummul lokaci guda take furta “Akan na fad’i gaskiya shine zaki mareni.. Mahaifiyarmu tana buk’atar mai tunasar da ita.. Mahaifiyarmu tana buk’atan mai nusar da ita..!” “Ya isheki Khulsum.!” Ummulkhairy ta dakatar da ita kafin taci gaba “A haka ne zaki nusar da ita kina d’aga mata murya kina fad’in ta cucemu mu ‘ya’yanta har Kina cewa taje hukuma su kamata.. Mahaifiyarki Khulsum.?!” Tai birki tana girgiza Kai tana duban Khulsum cikin rashin yarda “Mahaifiya ce zaki fad’a mata haka.. Ina karatunki na islamiya ya tafi..? Kin mance cewa ko nasiha za’a ma iyaye cikin kwantar da murya da lallama ake. Kin mance k’issan bawan Allah Junaid da ya keb’e kansa a wajen gari yana bautan Allah. Mahaifiyarsa tazo ta kirasa yana ibada bai amsa ba. Akai haka har sau uku a na uku tace Allah ya had’asa da sharrin ‘ya mace daga k’arshe wann bawan Allah saida ya had’u da sharrin mace. Karuwa taje tai . Bayan Allah ya wanke shi daga sharrin karuwa da ya fad’a . Daga baya mahaifiyarsa ta fad’i cewa wann bakin da tai masa shine ya kamasa.. Kinga darajan mahaifiya dukda ba sab’on Allah yake ba bautan Allah yake saida bakinta ya bisa saida yai tasiri akansa.. Wann itace Uwa Khulsum.. Ba’a wasa da al’amarin iyaye..” Khulsum ta jinjina Kai tana hawaye “Na yarda Miki ‘Yaruwata.. Shin koda ace mahaifiyarka zata apka ma b’ata sai ka k’yaleta..? Ummul sanin kanki ne rayuwar Umma akwai gyara cikinta.. Sanin kanki ne Umma bata yarda da k’addara ba.. Shin bakiji yanda ta d’aura alhakin komai akanki ba har Mama da yaranta suka sami hujja.. Ummul rayuwar mahaifinmu na cikin had’ari a wann gab’ar dole na nusar da Umma kuskuren ta..” Cikin sanyi jiki Ummul ke duban Khulsum. Sai kuma ta girgiza Kai tace “Watak’ila gaskiya Umma ta fad’a.. Itace ta haifeni.. Tafi kowa sanina..” Khulsum ta k’araso ta dafa ‘yaruwarta “Ubangijinki da ya halicceki yafi kowa saninki ‘Yaruwata.. Dan Umma tana mahaifiyarki bai zama hujja akanta ta dinga kausasa harshenta Akan k’addararki ba.. Sabida Dani dake da Umma dama duk wani mahalik’i bamuda ikon canza k’addararki.. Allah shi yake k’addara rayuwar mu yanda yake so ya kasance.. Iayakacin namu shine addu’a Allah yai mana tsari da k’addara mai muni.. Ki daina kuka ‘Adda Ummul.. Da sannu Ubangijinmu zai daidaita mana al’amranmu ya kuma bawa mahaifinmu lafiya.. Kuma na Miki alk’awari zan bawa Umma hak’uri nai mata nasiha cikin lallama da kwantar da murya.” Sai suka rungume juna suna kuka mai ban tausayi da tsuma zuciya. Shiru shiru Umma bata dawo cikin gidan ba. Ummulkhairy tace subi bayan Umma su dubata. Koda suka fito ma wayam basuga Umma ba. Ummul da Khulsum sukai tsaye suka jimami. Khulsum tace “Kar dai Umma tabi su Mama ne..? Mai zai faru yanzu Adda..?” Ummul ta rasa abin fad’i. Sukai tsaye suna duban mutane masu giftawa. Daga can nesa suka hango mashin d’in mijin Azeema ya nufosu ga Azeema zaune d’amas saman babur d’in. Suka k’araso sukai parking. Ta dafe shi ta sauk’o sai karairaya take “Yauwa Habibi, da alama mun kusa mallakan mota dan na gaji da babur din nan. Kar ka damu na maka alk’awarin da an bani kaso na na gado zan biya maka duk bashin da ake binka..!” Ta k’arashe tana aikawa su Ummul wulak’antaccen kallo. Khulsum ta dubi Ummul mamaki kwance saman fuskrta. Wai mahaifin su ke kwance gadon asibiti Azeema ke wann maganar. Daga ita har mijin nata kaman sunga kashi haka suka dubi su Ummul. “Habibi bara na shiga na fito da kaya na mu tafi tinda mun hadu da Mama a hanyar asibiti.” Azeema tace bayan ta dira daga bayan Babur d’in. Haka ta k’araso ta shige ta gaban su Ummul tana watsa masu wulak’antaccen kallo. Khulsumu tai saurin Shan gabanta “Adda Azeema kinga Ummanmu tareda Mama ne.?” Azeema taja tai birki tana watsa ma Khulsum banzan kallo “Ajiyanta kika bani da zaki tambayeni ko na ganta..?” Ummul ta girgiza Kai cikin sanyin muryarta tace “A’a Azeema gani mukai ta biyo bayan Mama kuma munji kince kin hadu da mama a hanya Shiyasa muke tambayarki..” “Mahaukaciya ce ita ko k’aramar yarinya ce ita..! Tinda ku kanku kunsan cewa mahaifiyar taku b’elb’el ce sama Sama ce sai ku nemi igiya ku d’aureta a gida ko ku Sakata a turu maganin hauka…” Kafin takai aya taji saukan tagwayen maruka d’aya bin d’aya. Azeema ta malmalo wani ashar tana duban Khulsum dake sakin huci wacce itace tai Marin. Cikin huci Khulsum taci gaba “Baa haifi wacce zata ci mutuncin mahaifiyata na barta ba bari kiji na fad’a Miki..!” “Ni kika Mara Khulsumu.. Toh wllhi yau idan baki kwana cell ba wllhi ba sunana Azeema ba.. Dan uwarki Suwaiba sama sama daga kaina kin gama rashin kunya..!” Ta k’arashe tana ihu tana k’walla kiran Habibi.. Kan kace me mutane sunyi caa a wajen. Babu shiri Mijin Azeema ya ko k’araso yana fad’in wllhi baiga ballagazar da zata marar masa mata ya barta ba. Fad’i yake wllhi sai ya d’aure Khulsum.. Kan kace mai ya d’ale mashin d’insa ya bar wajen. Ummul sai kuka take tana rok’on Azeema tai hak’uri ta bari suji da ciwon mahaifinsu da kuma b’acewar mahaifiyarsu. Azeema kaw sai tsalle take tana jijjiga tana fad’in wllhi yau bataga uban da ya isa ya hanata d’aure Khulsum ba. Bakin Khulsum bai Mutu ba fad’i take wllhi Azeema ta kuma gigin zagar mata mahaifiya sai ta k’ara mata da wasu marukan. Kuma idan ta haifu kar ta fasa rufeta a gidan yari. Wasu daga cikin ‘yan gidan masu goyon bayan Azeema sai dad’a ingizita suke. Wasu kaw cewa suke Ummulkhairy da ‘yaruwarta kullum cikin jaza masu fitina suke. Idan kaji ana bala’i da rikici a gidan toh ba kowa bane face su biyun. Allah sarki Ummulkhairy idan ka ganta dole ta baka tausayi. Jim kad’an motar police ya k’araso tafiya da Khulsum. Mijin Azeema na gaba yana fad’in idan zai kashe k’arshen kud’insa sai ya k’watarwa matarsa hakkinta. Ummul kaw ganin za’a tafi da ‘yaruwarta da gaske ya sanyata saurin k’arasawa tana rok’on Habibu mijin Azeema da yai hak’uri ya taushi Zuciyar Azeema ko dan halinda mahaifinsu ke ciki a asibiti. Haka akai ayari anai masu rakiya yayinda wata ‘yarsanda ta tasa k’eyar Khulsum zuwa cikin motar su. Ummul ta kamo ‘yaruwarta tana kuka shar shar tana rok’onsu dan Allah su k’yale mata ‘yaruwarta. Sergeant d’in ta bige hannun Ummul tana tsawa wa Khulsum ta shige mota. Azeema da mijinta suka d’ale babur suka take masu baya. Durk’usawa Ummul tai a wajen wani irin marayan kuka ma taso mata. Hannayenta biyu ta d’aura akai jikinta kaw har wani irin rawa yake. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Wann wani irin jarabawa ne.. Wani irin iftila’in rayuwa suke gani.. Ba’a gama da wann ba a fad’a wann..! Ta rintse idanunta hawaye na kuma ambaliya a fuskarta. Da wanne zata fara mahaifinta dake kwance asibiti.? Mahaifiyarta da bata san ina ta tafi ba.? ko kuwa ‘yaruwarta da aka tafi da ita police station.? “Hasbunallah wa ni’imal wakil..! Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifli khairan minha..!” Ta furta cikin tsananin rawar murya. Ta mik’e tamkar zautacciya tana Neman ta hanyar da zata nufa. Batasan ina take tafiya ba k’afafunta kawai take jefawa. Bata tsinci kanta a ko ina

Chapter 6 of 64