Haidar yai zai zabe ta matsayin mahaifiya a kowace rayuwa ya yaye mata wani burden da take kwana ta tashi dashi.
Daddy dake daga k’ofa Akan idonsa komai ta faru.. Murmushi out of nowhere ya subce masa ganin ahalinsa cikin yanayi mai ban sha’awa da bai tab’a gani ba. Kasa shiga d’akin yai sai ya juya ya fice yana jin zuciyarsa na masa wasai.. Koda ace baida k’warin gwiwan tunk’aran ahalin nasa a yanzu. Ganinsu haka cikin farin ciki Ya wadatar masa. Yana Jin wani annashuwa da sakinah da ya jima bai tsinci kansa ciki ba tsawon shekarun.
Koda ya isa company ma Alhaji Gimba ya fuskanci relief da farin ciki da abokin nasa ke ciki.
Alhaji Gimba ya murmusa yana duban Daddy alamun da magana a bakinsa.
Kafin yakai ga furtawa Daddy ya katsesa “A fad’a maka Haidar ya farka..?” Yai maganar har lokacin dai murmushi ne saman fuskarsa.
Alhaji Gimba ya kuma murmusawa “Ka fad’a mun wann the moment labarin ya same ka. Har ka mance.?”
Daddy ya d’an shafi goshinsa “Aff haka fah..”
“Ya baka zauna can ba.! Ai da kayi zamanka.. I have everything under control here.”
“Kwaise tana can.” Ya fad’i jikinsa a dan sanyaye wann karon. Dan har kawo wann lokacin Mommy bata daina sha masa k’amshin da ta tsira ba. Kallo guda zaka masa ka gane duk baya wani hayyacinsa.
Shiru Alhaji Gimba ya d’an yi kafin ya numfasa yace “Ka k’ara mata lokaci abokina.. Ita mace fah duk girmanta sunanta mace. Kuma su mata rauni ne dasu… Ba wuya an janye wayonsu da kalamai da kyautatawa.. Nan da nan sai kaga Sun sauk’a daga dokin fushi.. Amma fah idan aka kaisu mak’ura kalamai da lallama basa aiki nan take.. Toh fah wann karon kaine zakayi hakurin da ita.”
Daddy ya dan dubesa sai ya furzar da huci a hankali.. Ya kishingida cikin kujera yana mai lumshe idonsa.
**
A can asibiti kuwa Hisham ne yaje duba Haidar.
Yana zaune gaban gadonsa ya k’ura masa ido fuskarsa fal damuwa.
Haidar yai gajeren tsaki “Kasan dai bana so ayita kallo na.. It irritates me..”
Hisham ya Kai masa punch a damtsensa maras ciwo. Haidar ya dan saki k’ara yana fadin “You are such a jerk you know.!”
Hisham ya girgiza Kai “You are the real jerk here Haidar.! This isn’t a joke.. I mean, You almost killed yourself in that accident.. I know you so well.. Idan ranka ya baci tuk’i kake ba tareda kana sanin ina kake zuwa ba.!”
“Kana tunanin akwai b’acin ran da zaiza nai yunk’urin kashe kaina..? Hisham akwai wata cikin motar nan. And she happens to be my wife.!”
Saida Hisham ya dago ya kallesa jin ya ambaci Ummul da matarsa.
Haidar yaci gaba “You know me.. I wouldn’t put someone in harms way.. Koda ace ni mutum ne da ya yak’i ahalinsa tsawon rayuwarsa…” Yana jinjina Kai yake fad’in haka kafin yaci gaba “Abinda nake tunani shine… the accident was planned. Someone planned it.!”
Gaban Hisham ya yanke ya fad’i amma sai ya dake . Ya dan girgiza Kai kad’an yana karantar Haidar d’in “What do you mean.? Kana so kace kana zargin wani da shirya maka had’arin.? Kamar ya kenan Haidar.?”
Ya dan rage girman idona still yana duban Haidar d’in “Wait don’t tell me har yanzu zargin ahalinka kake da yunk’urin kasheka.. My goodness Haidar.. Wai har yaushe zaka watsar da wann tunanin ne..? Sai yaushe zaka watsar da makaman fad’anka Akan ahalinka. Until when Haidar.?!” Ya k’arashe cikeda nuna kulawa kaman dai ko Yaushe.
Haidar ya tsaresa sosai da ido “Someone tampered with my brakes.!”
Hisham ya dan girgiza Kai “But.. who could have done that.? I mean all your life you thought ahalinka sune mak’iyanka.. Dukda cewa kanada b’oyayyun mak’iya masu son ganin bayan ahalinka da family business dinku.. Ina nufin masu kai maka suka a company da media.. But basu tab’a yunk’urin kasheka ba.. “
Katsesa Haidar yai da fad’in “What if I have a new enemy..? What if someone’s holding a grudge against me..? What if someone wants to take their revenge on me.!?”
Cikin sakanni Zuciyar Hisham ke bugawa dan gani yake Haidar Ya gama ganosa ne.
Daidai lokacin akai knocking a k’ofa.. Mommy ce ta shigo fuskarta d’aukeda murmushi.
Hisham ya mik’e cikin k’ok’arin bama Mommy da Haidar waje. Ya gaida Mommy had’ida mata sannu da jikin Haidar kafin ya maida dubansa ga Haidar. Sallama Yai masa tareda fatan samun lafiya had’ida k’arawa da zasuyi magana.
Mommy tabi bayansa da kallo fuskarta d’aukeda murmushi. Shi d’aya ne abokin da zata iya cewa ta sani na Haidar.. Dukda ba wani saninsa tai sosai ba tasan wajen aikinsu d’aya kuma he’s very fond of her son.. Tasan duk Wanda zai hak’uri da halayyan Haidar Ya zauna dashi irin haka sai Wanda yake masa soyayya na gaskiya tsakani da Allah. Tana ji Har cikin ranta he’s a good influence for her son.
Farin cikin Mommy gaba d’aya ya gaza b’uya. Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tamkar k’wai hannun jariri haka take ririta Haidar. Gaba d’aya jinsa yake Awkward dan shi tun tasowarsa zai iya cewa babu wata alak’a mai kamanceceniya da wann tsakaninsa da mahaifiyarsa.
Ya d’an soma yunk’urin mik’ewa Mommy ta k’araso da sauri tana k’ok’arin taimaka masa take tambayarsa mai yake so.
A hankali yake furta “Is ok Mommy.. I can manage..”
Mommy ta gyara masa pillow ya kishingid’a sosai. Tana dubansa tana sakin murmushi…
Gani tai sai kalle kalle yake kaman yana neman wani abin ko yana so ya tambayeta wani abu.
Ta matso ta dafa hannunsa kad’an “Akwai abinda kake so ne Son.. Should I call the Dr for you..? Kana jin wani ciwo ne..?”
Ya d’an girgiza kai kad’an “Where is she..? Why isn’t she here..?!” Magana yai a hankali amma bai san Ya fito fili ba.
Mommy ta girgiza Kai kad’an tace “Wace kenan..?”
Ya dan dubi Mommy kaman bazai ce komai ba sai Ya tsinci bakinsa kai tsaye da furta “Khairy..!”
Farin cikin Mommy ya k’aru. Sai tace “Oh.. Ai Sun tafi tareda Anisa ta kaita gida. Nace ko zata d’ebo maka wasu kayyakin da zaka buk’ata. Amma nasan Watak’ila ma suna hanyar dawowa.”
Baice komai ba sai Ya d’an kuma yunk’urin mik’ewa alamun yana son sauk’owa daga saman gadon.
Mommy tai saurin tallafosa tana tambayarsa mai yake so.
Ya d’an dafa gadon yana fad’in “I need to use the bathroom..”
Mommy ta soma k’ok’arin dafa masa tana fad’in bari ta taimaka masa.
Ya girgiza Kai cikeda kokari mai nuni da jarumta “You don’t have to worry Mommy.. I can manage..”
Ta girgiza kai a’a Haidar Bakada wani k’arfi fah.. Duba ka gani..”
Daidai lokacin su Ummul da Anisa sukai sallama.
Mommy tai hamdala tana fad’in “Gwara da Allah Ya kawo ku. Maza k’araso Ummul ki taimaka ma mijinki..”
Haidar yai saurin katseta “I said I can manage, Mommy..”
Girgiza Kai Mommy tai “So kake ka fad’i ka kuma jin wani ciwon…?” Ta k’arasa ta kamo hannun Ummul da tai sororo ga zuciyarta da bai daina tsinkewa ba. Ta dank’a mata hannun Haidar cikin nata “Assist your husband.”
Bata tsaya sauraron komai ba ta janye Anisa da tai mutuwan tsaye nan wajen tana kallon yanda Mommy ta saka hannun Ummul cikin na Haidar.. Bata ankara ba sai ji tai Mommy tana janyota tana fad’in ta shige su basu waje.
D’akin ya rage saura Ummul da Haidar. Ya kuwa tsareta da ido fuskan nan a murtuk’e kaman ba shine ya gama jajenta ba.
Ta had’iyi abinda ya tsaya mata da k’yar dan tinda yai regaining consciousness bayan gaisuwa da tai masa basuyi wani magana ta fatan baki ba.
Takai idonta kan hannunta yanda Mommy ta had’e da na Haidar waje guda. A hankali ta soma k’ok’arin zame hannun amma sai taji ya matse hannun ya hanata abinda take k’ok’arin yi. Ta d’ago ta dubesa ita d’in yake duba har lokacin babu wani walwala saman fuskarsa.
Hannunta taji ya janyo ya zagaye bayansa dashi ya d’aura saman waist d’insa.. Ta kuma dubansa cikin fad’uwan gaba. Har lokacin bai janye ido daga barin dubanta ba.. Bata kuma ankarewa ba saiji tai ya d’aura hannunsa guda saman kafad’arta yayinda hannunta guda ke saman waist d’insa irin dai yanda ake taimaka ma maras lafiya idan zai tafiya..
Maimakon ta soma takawa sai shine dai yai yunk’urin tafiyar Kai kace itace maras lafiyan.
Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Don’t look at me like you’ve seen a ghost… They say monsters don’t die early.!”
Yai maganar kaman ba shi ba saida ta dan dago ta dubeshi tana mamakin kar dai yaji kiransa monster da ta dingayi sanda yake kwance unconscious. Sai ta tsinci kanta da Jin kunya ta sadda kanta k’asa.
A haka suka ci gaba da takawa Zuciyarta bai daina yankewa ba. Addu’a kawai take cikin zuciyarta Allah ya bata k’warin gwiwa..
Aiko suna shigewa bathroom din ta soma k’ok’arin janye jiki daga nasa..
Cikin in ina take furta “Zan.. Zan jiraka a k’ofa..” Juyawan da zatai ta kunna musu shower akansu.. Haidar ya janyota jikinsa gaba d’aya “What if I fall..?” Ya fad’i yana mai manne goshinsu waje guda su duka biyun idonsu a lumshe. Sosai Ummul ta rintse idonta tana Jin yanda karan hancin Haidar ke gogan nata ga ruwa dake zubo musu.
“Amma.. Amma.. Naji kaman kace ma Mommy zaka iya..” Ta fad’i da kyar cikin k’ok’arin ganin ya k’yaleta ta fice. Amma sai taji ya kuma had’e fuskokinsu waje guda.
Murya na rawa ga ruwa dake jik’asu tace “Mai.. Kake aikatawa..?”
“I’m rebuilding my life..!” Ya furta a hankali saitin kunnenta kafin yaci gaba “Isn’t this what you want..?”
Tai saurin ware idonta tana dubansa zuciyarta naci gaba da bugawa.
Haidar yaci gaba “Isn’t this what you promised Mommy… That you’d help her son…rebuild his life… Are you scared now..?” Yai maganar yana mai kuma rungumeta cikin jikinsa. Cikin sigan rad’a yaci gaba “Are you sure you are ready to invade my sick world..? Don’t you think you are taking too much of a risk..? Are you not scared of a monster..?”
“But you are not a monster…!” Ta furta cikin rawar murya.
“What makes you believe… That… I’m sweet…?” Yai maganar d’umin numfashinsu na gaurayuwa da juna. Kaman zai sumbaceta. Har lokacin idanun Ummul suna lumshe. Ga heartbeat dinta dake k’aruwa.
Ta kasa furta komai sai k’ok’arin cire jikinta daga nasa da tai dan ta gama amincewa yanzu kam duk wasu maganganun da tai sanda yake kwance yaji komai.
“Zan… zan jiraka a k’ofa ta fad’i tana mai tamke tufafin dake jikinta cikin tsananin rawar murya. Kaman zata kifa haka ta fice tana had’e hanya. Haidar yabi bayanta da kallo murmushin da ba lallai ka fahimta ba saman fuskarsa.
Ummul kaw tana ficewa ta jingine jikin k’ofa tana maida numfashi.
A b’angaren su Mommy kuwa Asshe ta iso gari dan haka Kai tsaye ta taho asibitin yanda ta tadda ‘Yaruwar tata.
Suna zaune saman wani kujera a wani hanya da zai sadaka da hanyar dakin Haidar d’in.
Asshe taci gaba “Aunty Kwaise yarinyar nan annoba ce.. Tsautsayi ke bibiyarta.. Ya kamata ayi gaggawan datse aurenta da Haidar… Allah na tuba bamusan dalilin da yasa boka yace mu aura masa mace irinta ba..”
Anisa da karyo kwananta kenan zata nufi d’akin Haidar ta sinkayi tattaunawar iyayen nata. Ta zaro ido waje tana dafe k’irji “Boka.!” Ta furta a hankali. Lokaci guda ta gyara tsayuwarta ta lab’e sosai.
Mommy ta girgiza Kai tana duban Asshe “A’a Asshe na yada batun boka tuntuni kuma na k’aryatasa kaman yanda Ayoyin Alk’ur’ani mai tsarki ya k’aryatasa a wajaje da dama. Asshe ba shakka munyi kuskure a yanda muka faro Auren Haidar da Ummul.. Amma na gode ma Allah da ya nufeni da tuba ya kuma bud’e min ido na na gane gaskiya dalilin shigowar Ummul cikin rayuwarmu. Sann inada yak’inin Auren Haidar da Ummul Alkhairi ne Asshe. Domin shigowar Ummul cikin ahalinmu shi ya fargar damu gaba d’aya.. Ita d’in ta zamto tamkar wani igiya mai k’arfi da ta had’e ahalinmu waje guda ta d’aure Asshe. She’s an Element of Union.. Na shafe skaru sama da talatin ina fad’i tashi da ganin na had’e kan ahalina sai gashi cikin watanni biyu na zaman Ummul tareda mu Allah ya jefa wann had’uwan ahalin da soyayyar d’ana da mijina da nake buri. Kuma in sha Allah Ummul ko Haidar cikin su babu Wanda zai San ga Manufar aurensu daga farko. An Gina auren ne bisa sharad’in boka domin a raba Haidar da wancan Hatsabibiyar da tai masa sihiri Wanda a halin yanzu ma bana tunanin suna tare.”
Anisa ta zaro ido waje tana Jin sirrin Auren Ummul da Haidar Wanda ba yanda batai ba Mahaifiyarta ta sanar da ita. Dama wann shine dalilin da yasa Kwaise Maitama ta auro ma D’anta D’iyar talakawa da taita mamaki daga farko.? Dama wann shine dalilin da yasa Mommy hak’uri da Ummul da nuna mata unconditional love.? Tirk’ashi Lallai yau akeyinta.
Mommy taci gaba “Asshe kimin alk’awari babu Wanda zai San wancan manufar tamu na farko domin na riga na bisne wancan manufar na lullubesa da tuba na gaskiya. Ummul da Haidar zasu rayu a k’ark’ashin inuwar aure tsawon rayuwarsu cikin yarda Ubangiji aure mai cikeda d’imbin albarka ba AUREN WATA UKU mai k’ayyadadden lokaci Wanda Boka mak’aryaci yaima Ummulkhair alk’awarin mutuwa ciki ba.!”
Anisa sai ta sake baki tana fito da ido waje.! Mutuwa..? Shiru tai tana sauraron yanda Mommy ke zayyano sharud’an boka gameda auren cikeda nadama. Anisa ta kasa rufe baki dan mamaki. Kenan An auro Ummul ne dan ta zamto makarin asirin da akai ma Haidar. Sai yanzu ta gane manufar turaren da Mommy ta bata ta bama Ummul. Sai wann lokacin take fahimtar komai.. So Mommy isn’t as innocent as she thought.. So duk wann soyayyar da Mommy take ma Ummul na k’arya ne tana mata so ne out of guilt tinda ta kawo ta cikin rayuwar D’anta ne dan ta kasheta ta kuma ceci nata D’an. Muryar Mommy ya kuma dawo da Anisa daga duniyar tunanin da ta tafi.
Mommy ta kuma kamo hannayen Asshe “Asshe Alhamdulillah ahalina Ya fara daidaita cikin ikon Allah. Bazan kuma yin wani abu da zai tarwatsa min wann farin ciki da na jima ina fatan samu ba. Haidar da Ummul harma da Engr bazasu San ga manufar auren ba… Asshe idan suka sani ahalina zai kuma tarwatsewa Watak’ila yai rushewar da baiyi ba a baya… Kimin alk’awari kaman yanda muka shirya komai daga farko tare zamu bisne wann magana kuma bazamu sake d’agota ba har abada.” Ta k’arashe tana duban Asshe.
Asshe Tai shiru tana duban ‘yaruwar tata dan dik yanda Anisa ke sanar da ita irin makancewar da Mommy wajen nuna ma Ummul so bata kuma gaskatawa ba sai yanzu “Amma… Aunty Kwaise..”
“Babu amma Asshe. Inada yak’inin kafin a sallami Haidar daga asibitin nan shida Ummul zasu k’ulla alak’a mai kyau tsakaninsu.. Zasu k’aunaci juna a hankali. Domin da zaran an sallamesa ni Kwaise zan shirya gagarumin bikin na gaske. Za’ayi komai cikin mutunci da karramawa kaman yanda yake a al’ada. Za’a sallami Haidar ne tareda bikin tafiyarsa da matars in sha Allah. Ni da kaina zan tafi wajen dangin Ummul muyi masu gaisuwa a k’ulla alak’a da zumunci mai tsafta..” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta.
A hankali Anisa ta soma jada baya.. Shigowan da batai ba kenan ta soma tafiya jiri na neman kada ita.
Tana fita ta soma neman layin Hisham. Bugu biyu a na uku Ya d’aga.
“Tell me your location.” Abinda kawai Anisa tace kenan…
Hisham na sanar da ita location d’insa tasa kai zata fice sai kuma taja birki ta tsaya kaman wacce ta tuna wani abu. Ji tai ta k’agu ta tunk’ari Haidar da Ummul ta sanar dasu irin Auren yaudara da Mommy ta k’ulla tsakaninsu.
A b’angaren su Ummul kuwa tana nan lamo jingine jikin k’ofan bathroom taji motsin tab’a k’ofan alamun zai fito. Tai k’ok’arin saita kanta tana mai taimaka masa da bud’e k’ofan.
Suka dubi juna sai ta kauda fuskarta kad’an. Gaba d’aya saima ta rasa mai zatai musamman da taga yanda yake dubanta daga nan yanda yake tsaye dafe da garu.
Baice da ita komai ba sai soma takowa da yai. Ta yunk’ura da zummar magana saiji Tai ya kuma kamo k’ugunta had’ida tallafo kafad’an ta guda. Sukai tsaye nan haka suna duban juna.
A haka Anisa ta turo k’ofa taci karo dasu rungume da juna suna duban juna ga jikkunansu duk a jik’e. Takaici yakai Anisa k’ololuwa. Banda sakin huci bata komai. Wai Haidar Maitama ne dai take gani rungume da wann kucakar harma kaman ya makance a shauk’in kallonta baisan an tab’a k’ofa ba balle Ya kula da Wanda Ya shigo. A zuciye Anisa ta janyo k’ofar ta fice, kukan da ta rasa na takaici ne ko na kishin Abun k’aunarta Haidar ne na kufce mata. Haka ta fice tana kuka shar shar take driving. Da alama duk wani effort dinta a banza yake tafiya dan duk k’ok’arin taga Haidar da Ummul basu samu kusanci ba kaman k’ara rura wutan abun take.
Koda ta isa location d’in Hisham bata daina kuka ba.
Hisham Ya tsareta sosai da ido had’ida bata lokaci dan ta fitar da k’uncin dake ranta. Ganin dai kukan Anisa bazai k’are ba dan tinda tazo yanda yake kul take ta kasa cewa komai.
Hisham yai tsaki kad’an “Ke enough please. Ya isa haka mana.! Wai meye kikazo kika saka ni gaba kina kuka.? Ok dama kin nemi sanin yanda nake ne kawai dan ki cika mun kunnuwa da sautin kukan ki. Ai da baki b’ata mana lokaci ba daga ni har Ke tinda idan kinyi a waya ma zanji.”
Anisa ta d’ago tana huci “We can’t let them be happy while we are stuck here just.. Freaking miserable you know..! Wllhi na tsani Ummul.. Na tsaneta.. Na tsani Mommy da taima Haidar AUREN WATA UKU.. Auren karya asiri da ita.. I hope she dies kaman yanda Boka yace.!”
Da mugun mamaki Hisham ke kallonta.. Ya girgiza Kai cikin rashin Fahimta “Mai kike nufi..?!”
SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!*
*42*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Anisa ta d’ago fuskarta da Ya jik’e sharkaf da hawaye “Ina nufin ko ban kashe Ummul ba Boka ya mata alk’awarin mutuwa.!” Ta k’arashe tana kecewa da wani irin dariya mai sauti.
Hisham Ya daka mata tsawa da fad’in “Cut the crap.! Wai meye yake faruwa ne.? Wani boka kike magana.?!”
Sosai Anisa ke dubansa kafin ta mik’e suna fuskantar juna “Your beloved Ummulkhair.. Hajiya Kwaise Maitama my Aunt ta kawota cikin rayuwar D’anta Haidar ne domin ta karya asirin dake jikinsa da ita.. Meaning, Auren Haidar da Ummul an ginasa ne bisa k’arya, yaudara da kuma cin amana… Aure ne mai k’ayyadadden wa’adi..! AUREN WATA UKU.! Sann daga k’arshe mutuwar Ummulkhairy shine cikan AUREN WATA UKU.!”
Hisham dake dubanta babu k’ifta ido Ya kuma girgiza kai “Ki min bayani dalla dalla.. Ban fahimci komai ba..!” Ya k’arashe kaman zai shak’o wuyarta ga wani irin huci da yake.
Sosai Anisa ta razana da yanayinsa sai ta mik’e tana girgiza Kai “I think it was a wrong move to come here.!”
Hisham ya daka mata tsawa da fad’in “Kina tunanin zan barki ki tafi ne ba tareda kin fayyace min komai ba.. Mai kike nufi da AUREN WATA UKU.?!”
Anisa ta kuma daidaita tsayuwarta tana duban Hisham cikin ido. Taryan taryan ta karanto masa sirrin Mommy da mahaifiyarta da taji Wanda ta jima tana zargin akwai wani b’oyayyen al’amari mai tattareda sark’ak’iya gameda auren.
Shiru Hisham yai yana kallonta bayan ta gama karanto masa kafin taci gaba “Amma idan har Haidar yayi wani aure ba tareda sanin ahalinsa ba.. Auren da Mommy ta kawo Ummul cikin rayuwarsa dan ta warware shi toh wacece matar da Haidar Maitama da ya aura a sirrance.? Meyasa babu Wanda ya Santa.?”
“Except me.!” Cewar Hisham daga nan yanda yake zaune.
Anisa ta waigo da mamaki tana dubansa “You.? Ta yaya..?”
“Because I’m his only friend.. Na san wani b’angare na rayuwarsa da ahalinsa basu sani ba. Dareen..!”
Anisa ta dubesa da mamaki tana girgiza Kai “Dareen.? Wacece Dareen.?”
“Ita ce matar da ta aure Haidar da asiri kuma inada tabbacin ita ce Hajiya Kwaise Maitama taima Haidar Auren karya asiri da Ummul d’ita dan ta rabasu..!” Yaci gaba da huci “Why Ummul..? Meyasa ita..?” Cikin zuciyarsa yake furta ‘No.. Banyi asiri ma Haidar dan macen da nake so ta zamto makarin asirin ba. Wai meke faruwa ne.? Could this be my Karma.? Na yi asiri ma Haidar dan ya kasance da wata mace sai gashi the only mace da nake so ta zamto makarin wann asirin.. But asirin Ya riga Ya karye.. Amma what if Ummul ta mutu sakamakon Auren Haidar kaman yanda Boka yace.?’ Sai Ya soma girgiza kai a fili yana furta “No I can’t lose her.. I need to protect her from this marriage at all cost.!’
Anisa ta girgiza had’ida katse masa tunanin nasa “Wai mai kake fad’a ne..? Wacece wann Dareen d’in.. Where is she..?”
“She’s nowhere to be found.. Haidar ya rabu da ita a ranan da zaiyi accident d’in.. Amma idan har muna son cimma burinmu na raba Haidar da Ummul.. Dole mu dawo Dareen cikin rayuwar Haidar.!” Ya k’arashe yana duban Anisa.
“You must be crazy..! Bayan ya rabu da rak’ai so kake ta dawo..? So kake idan Ummul bata Mutu ba ni na mutu.?!” Ta k’arashe tana firfito da ido waje.
Makirin murmushi saman fuskar Hisham yake fad’in “For once in your life, use that tiny brain of yours..!” Ya k’arashe yana mata lamu da yatsunsa alamun yana nuni da k’ank’ancin kwakwalwarta kaman yanda yace.
Anisa ta galla masa hara tana duban yanda yake Kallonta with that infuriating half smile on his face. A kufule tace “ Toh mai babbar kwanya make me understand.
Har lokacin murmushin ne saman fuskarsa. Ya dan kauda fuska ga barin dubanta “Abun shine zamu dawo da ita ne domin ta tarwatsa yarda da aminci da Ummul tayi ma ahalin Maitama.. Zamu dawo da ita ne domin mu bud’e idon Ummul ta fahimci dalilin kawota cikin ahalin da Hajiya Kwaise Maitama tayi. Zamu dawo da ita ne matsayin matar da Haidar yai zaman daduro da ita ba k’ark’ashin kalmar aure ba..Zamu dawo da ita ne domin mu b’ata image d’in Haidar da ahalinsa a idon Ummul.. Zamu dawo da ita ne domin mu nuna ma Ummul cewa gaba d’aya ahalin Maitama Sun yaudara ta ne. Su d’in macuta ne mayaudara kuma azzalumai Wanda zasuyi komai sabida cikar burinsu..!” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “Dareen ta sani a halin yanzu bazata sake mallakan Haidar ba.. Dan haka zatai komai domin ta tarwatsa masa farin cikin dake k’ok’arin shigowa cikin rayuwarsa Wanda ya rasa hakan tsawon rayuwarsa.. Kinga idan har Ummul ta fice daga rayuwarsa you can have Haidar all to yourself .. Isn’t that genius..?!” Ya k’arashe da murmushin saman fuskarsa.
Anisa sai ta soma murmushi tana jinjina Kai “Wow.. tunani mai kyau.. I must admit kwanyarka na ja… Toh amma yanzu.. A ina zaka samo Dareen or whatever.?”
Murmushi kawai Hisham yake yana duban Anisa tareda jaddada shashancinta. Dan Hisham dai bai sanar da ita cewa tareda Dareen suka k’ulla komai ma Haidar ba. Komai d’aurawa yai kan Dareen. Bazai ba ma Anisa reason ko wani k’ofa da zata samu abun threatening d’insa dashi ba. Bazai tab’a bud’e ma Anisa cikinsa tasan ko wanene shi da asalin manufarsa Akan Haidar da ahalinsa ba.
“Kar ki damu zan kula da wann.. Kedai kije kici gaba da monitoring komai acan.. Ki saka mana ido kan Haidar da Ummul kiga ina relationship d’insa ya nufa.. Sann ki saka mana ido Akan Kwaise Maitama.”
Anisa ta jinjina Kai “Kar ka damu da wann.. Zan kula da wann b’angaren.”
Ya jinjina Kai suna Sallama da Anisa.
Bayan Anisa ta fice shid’in ma gidansa ya nufa ya isa jikin hotunan Haidar da Ahalinsa Wanda yai crossing da red pen gaba d’aya. A fili yake furta “Ban jure duk wani wahala a banza ba..! Banyi duk wani fad’i tashi na ganin na zama cikakken architect a banza ba.. Nayi haka ne to easily invade your lives.. Nayi haka ne domin na fanshe duk wani k’uncin da kuka jefamu ciki nida mahaifiyata..!” Ya kuma gyara tsayuwarsa yana huci “I’m resourceful today because you rejected me Aliyu Maitama.!” Yai maganar yana duban hoton Daddy Wanda shima yayi crossing. Yaci gaba “I’m who I’m today sabida na girma cikin wahala,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 38 Chapter of 64