Share this page
tsakiyar su ta rungumesu su duka biyun akaita kashe musu pictures. Daga bisani aka soma yima amarya da ango. Masu hoto suna bada direction. Aka ce ta d’aura hannunta guda saman chest d’insa sai ta d’an d’ago tana dubansa. Duban irin na mai yake nufi.? Ita fah har kawo wann lokacin bai mata magana ba gashi duk yanda aka ce ya rik’e jikinta kafin ma ace yayi. Wann fah shine mutumin da a baya he’s allergic to cameras. Ummul bata Ankara ba saiji tai ya d’ago hannunta ya d’aura saman chest d’insa. Anisa taji wani k’atutun bak’in ciki ya tokare mata makoshi. Ga wani kallo da suke bin juna dashi. A hankali take calming kanta cikin zuciyarta ‘Patience Neesa.! Patience.!! Na yau ne kawai.. Daga rana mai kaman ta yau ta zama tarihi a rayuwar Haidar dinki.’ Ta kuma murmusawa ‘I can’t wait for things to get chaotic.’ ** A can waje kuwa zabga zabgan bak’aken jeep d’in sukai parking. Motar farko Hajiya Asshe ce ta fito sai Inna Dije daga d’aya b’angaren. D’ayar motar kuwa daga can seat din ‘yanuwan Ummul guda biyu ne Badi’a da Azeema yayinda Umma da Mama Tani ke daga tsakiya. Suka neri suka fito sahu sahu. Kallo guda zakai ma Umma ka fahimci tsananin tashin hankalin da take ciki. Tayi tsuru tsuru da ido ko motsi mai kyau bata iyawa. Badia da Azeema kuwa kasa rufe baki sukai ganin irin gidan da Ummul wai take aure ciki.. Ummul fah. Wacce kowa ke gudunta cikin ahalin su. Wann maras sa’an.. Wacce ake mata lak’abi da mai farar k’afa.. Wann wacce maza da yawa ke guje ma Aurenta.. Allah mai iko. Gashi daga sauk’an su wasu ma’aikata masu uniform suka taho suna masu sannu da zuwa cikin harshen turanci cikeda ladabi suna amsan jakkunansu. D’aya daga ciki tai directing nasu zuwa masauk’i. Sukaja suka tsaya wann ya dubi wancan wancan ya dubi wann. Asshe ta furzar da huci kad’an ganin duk sunja sun tsaya suna duban tsoro ma juna “Ku taho muje mana. Wai ko Baku gaji bane.?” Sai Inna Dije ta murmusa da shike ita ta tab’a zuwa lokacin auren Ummul. Tace “Kunga ba masu yankan kai bane ko Shan jini. Ku taho muje..” Sai Mama Tani wacce ta kasa gasgata wata duniya ma tukunna take ta janyo Inna Dije tana rad’a mata “Ke Dije.. Da gaske kike.? So kike kice min nan shine gidan da Ummul take ko kuma dai matar nan ta shanshantar damu ne gaba d’aya Kama Suwaiba. Dije nan fah fadan shugaban k’asa ne. K’ur’ani shine a talabijin nake gani.!” Ta k’arashe harda dangwala yatsa saman harshe. Inna Dije taci gaba da janyo Mama Tani tana fad’in “Kin dai gani da idonki.. Na tabbata bazaki so ki bar Ummul cikin wann daula ba. Duk bala’in da za’ayi bazamu fice daga gidan nan ba saida Ummul.” Cikin sigan rad’a suke ma juna magana. Duk maganar da sukeyi ita dai Umma bama tasan mai ke faruwa ba jefa k’afafunta kawai take tana tuna kalaman Asshe a gareta tana tuna a daidai wann rana sukai AUREN WATA UKU da tai ma Ummul da d’ansu zaizo k’arshe. Azeema da abin ya fara bata tsoro ta dan jada baya tana janyo ‘yaruwarta Badia. Tai k’asa da murya “Badia nifah wllhi naga gidan zama.. Wllhi bazan koma Kano ba ina nan tareda ‘Yaruwata.!” Badia ta dara kad’an tace “Toh kiyi yaya da Habibinki kuma idan ya dawo miki.?” Azeema ta galla mata harara “A’a Mak’iyi dai ba Habibi ba. Ai ni idan kinga na fice a gidan nan saidai idan fadan shugaban k’asa zan tafi..” Badia ta kuma darawa daidai sanda suka isa guest section din. Asshe ta dubesu tace su saki jiki su huta ga abinci dama tuni an jere musu idan da akwai abinda suke buk’ata ga ma’aikata zasuji dasu. Zata shiga cikin gida ta sanar da isowarsu. Inna Dije ne kawai ta amsa mata yayinda Mama Tani ta rakata da harara duk cikin acting ne da suke dan su shashantar da Umma. Badia da Azeema kam basu tsaya sauraronta ba suka tashi suka soma zaga gida suna kallon aljannar duniya a cewarsu. Bayan ficewar Asshe jikin Umma yaci gaba da rawa. Ba tareda ta dubesu ba take fad’in “Yau ne.. Yau ne tai alk’awari.. Wa’adin auren zai cika.. Yau d’ansu zai sakar mun Ummul d’ita.. Zan d’auki Ummul d’ita mu tafi.. Shine kawai abinda ya kawoni..!” Mama Tani da Inna Dije suka dubi juna.. Tani tuni shiga bud’e buden kayayyakin abincin da aka jere musu Wanda da yawa ma bama ta tab’a ganin irinsu ba. Da ta ga dai bata gane wasu abun ba sai ta d’auki Wanda takeda tabbacin naman kaza ne ta soma gwagwiya dama Tani da kaza. Tana ci tana Zare ido kaman za’a k’wace. Ta dafa Umma “Shiyasa na rakoki ‘Yaruwata. Kinga wann mata mai zubin akwati (Wai Asshe) kina ganinta kinga makira.. Wani abin take shirya Miki.. Ni da tuni kin sanar Dani ga yanda auren Ummul ta kasance ai da tuni anyita da wajewa an gama komai.. Haba Tani fah nake.!” Ta k’arashe tana kurban wani abu da bata tabbata kunu ne ko madara mai ‘yan’yan itatu ciki ba. Ta lumshe ido tana fad’in “Dole ace masu kudin nan kunci rabonku na Aljannah ehe.!” Inna Dije ta harareta sai ta dafa Umma tace “Suwaiba mu duka muna nan tare da ke bazan bari aci zarafin ‘yard’anuwana ba. Kafin su wulak’anta Ummul zamu d’auketa mu tafi dan kinsan masu kudin nan su wulak’anta D’anadam ba komai bane wajensu. Tinda auren ma a wulak’ance suka nema dan haka a wulak’ance zasu nemi rabuwa bacin haka meye dalilinsu na gayyato mu a wann rana da sukai alk’awarin kashe Auren. Kinga Suwaiba tashi ki shiga band’aki kiyo alwala.. Muje na nuna miki yanda ake amfani da irin bandakinsu kinsan ni na tab’a zuwa.” Ta k’arashe tana mai kamo Umma suka nufi band’aki. Ta nuna mata yanda zatayi kafin ta dawo ga Tani. Ta kafe ta da ido “Ke kuma Tani ba sallah ba salati kin fara ciye ciyen abubuwan da cikinki bai saba da irinsu ba.. Idan cikinki ya tsure kika kasa zuwa wajen shagalin bikin tozarta Suwaiba da ‘yarta saidai na kulleki a d’akin nan dan nidai billahillazi bazaki b’ata min shiri ba ehe..” Mama Tani ta saki gyatsa mai k’arfin gaske tace “Yo ka iya ibada ciki bai d’auka ba. Ibadanki ma maje ina Dije.. Yo naga k’eta ce da fansa ya kawo ki nan..” Inna Dije ta galla mata harara yayinda Mama Tani ta shek’e da dariya. ** Jikin Mommy ya d’anyi sanyi. Ta kuma duban Asshe “Asshe kika ce harda Mahaifiyar Ummul akazo..? Asshe ina Jin nauyi.. Ina matuk’ar Jin nauyin bayin Allahn nan.. Mu ya kamata mu fara zuwa musu ba su ba.. Kuma a yanda na shirya da anyi bikin tariyar zamu d’unguma mu tafi gaba d’aya mu gaida iyayen Ummul da danginta musamman iyayenta.. Mu kuma musu godiya sann a k’ulla alak’a da zumunci mai kyau.. Munada shirin zuwa gaba d’ayamu.. Ni, Haidar harma da Engr da Kansa. Sun cancanci haka Asshe.. Dama kawai na buk’aci wasu daga cikin danginta suzo ne dan itama taji dad’i kar taga ba danginta ko d’aya wajen shagalin. Dan farin cikin Ummulkhair.” Duk jikin Mommy a sanyaye take maganar. Asshe ta furzar da huci kad’an tana mamakin dan dai Mommy batasan waye Suwaiba ba. Da bazata d’aga hankalinta kan wann shashasahar matar ba. Ta dan girgiza Kai “Aunty Kwaise ke ya kamata ki musu godiya ko su ya kamata su Miki godiya.? Yau kece zaki duk’a kiyi godiya ma talaka Aunty Kwaise.? Aunty Kwaise Anya kece kuwa ba’a canza ki ba.?” Asshe ta k’arashe tana bin‘Yaruwar tata da kallon mamaki. Sai Mommy ta dubeta ta shiga jinjina Kai “K’warai kuwa ni ce Asshe. Saidai ba Kwaisen da kika sani a baya bane.. Wancan Kwaise da kika sani capitalist, maison mulki, izza da d’agawa ta tafi kuma bazata sake dawowa ba. Wann Kwaise ce da ta fahimci duniya da rayuwa. Kwaise ce mai Neman dacewa da tsira duniya da lahira.” Asshe ta furzar da huci kad’an sai kuma tace “Aunty Kwaise nidai.. Da an kashe auren nan kawai mu basu d’iyarsu kaman yanda muka tsaro daga farko kawai a huta.. Aunty Kwaise wa’adin ya cika.. Kawai mu basu ‘yarsu kawai and save Haidar..” Ta k’arashe cikin rawar murya. Mommy sai ta d’an girgiza Kai kad’an cikin rashin fahimta “Save Haidar kuma Asshe. Kaman ya save Haidar.. If there’s someone to save here is Ummul. Balle ma boka makaryaci ne kinga dai yanda Al’amra suka kasance bayan mun bar hanyar b’ata mun kama hanyar gaskiya. Kinga bana ma so ana d’ago wann maganar kije ko da akwai abinda suke buk’ata sann kizo kimin iso na gaishesu.” Asshe ta kuma fruzar da huci “Wai Suwaibar zakije gaisarwa Aunty Kwaise.? Matar nan fah ko a ‘yar aikatau d’inki bata isa tazo ba.” Izuwa lokacin Zuciyar Mommy ya soma tunzura. A fusace ta dubeta wann karon “Matar da ta haifo Ummulkhairi idan ta kama na duk’a gabanta na mata godiya ne zanyi haka Asshe. Domin kuwa tinda Ummulkhair ta shigo rayuwarmu banda alkhairi babu abinda muke gani. Ke shaida ce a gabanki komai ya faru Asshe.. For years ina kuka kan ahalina.. Ahalin da na ruguza da hannu na.. Akan idonki Haidar da baisan hawa ba baisan sauk’a ba ya d’auki burden din da ba nasa ba tsawon rayuwa. Shin ba Akan haka bane muka tassamma kauce hanya.? Yau sai gashi cikin ikon Allah Haidar ya zauna da iyayensa lafiya. Ahalin da na jima ina mafarki ya dunkule waje d’aya. Ummul ta shigo ta farfado da duk wasu kyawawan d’abi’u da muka mance dasu ta cika gidan da nargartanta da alkhairanta.. Kinga kuwa ko duk’awa nai na mata godiya ban fad’i ba. Mahaifiyar Ummul ko wace iri ce Asshe tanada k’ima da mutunci a idona. Danginta ko yaya suke mun zama d’aya irrespective of our social differences. I expect you to do the same with them. Kin fahimta.!” Ta k’arashe cikeda umarni like a big sister. Zuciyar Asshe yaci gaba da tafasa. Ta kula Aunty Kwaise tsaf zata iya zab’en dangin Ummul ta mance ita ce danginta ta asali. Gaba d’aya itakam kaman an canza mata ‘Yaruwa. “Magana nake Miki Asshe..!” Mommy ta kuma tsawatar mata. Sai Asshe ta jinjina Kai da kyar tana k’ok’arin k’wak’ulo hawaye. Cikin muryar kuka take fad’in “Aunty Kwaise yanda kike magana kin fara bani tsoro.. Aunty Kwaise karfa k’warin gwiwar da kike dashi Akan yarinyar nan yasa ki mance komai.. Aunty Kwaise ni fah amana ce wajenki.. Iyayenmu Sun bar Miki amanata.. Banida wacce ta fiki kaf fad’in duniya.. Aunty Kwaise dan Allah kar ki tab’a mance hakan.. Idan kika rabu dani bansan ya zanyi ba… Duk abinda nakeyi kawai dan na damu dake ne.” Jikin Mommy ya d’anyi sanyi. Sai taji dan dafa Asshe “Haka ne Asshe. Idan ba mutuwa ba babu abinda zai rabamu ‘Yaruwata. Likewise banida wacce ta fiki. A lokacin kuka da lokacin dariya duk muna tare. Ta dalilinki Ummulkhairi ta shigo rayuwarmu Asshe.” Bata k’arasa sauraronta ba zuciyarta ya shiga tafarfasa. Dole dai sai ta ambaci wann mayyar yarinyar. Gaskiya ta fara yarda da batun su Dije yarinyar mayyace dan gashi ta lashe Zuciyar ‘yaruwarta. Sauri sauri Asshe ta nufi kiran Dije da Tani. Suka keb’e tana sanar dasu tsarin yanda zasu tarwatsa wann biki. Asshe ta rik’e kunne tana duban Tani da Inna Dije alamun kashedi “Kunaji biki ne na manyan mutane. Biki ne da zai samu halartan manema labarai. Dole ‘Yan jarida zasu sanin ‘yar gidan wane hamshak’i tilon D’an Aliyu Maitama yake Aure. Inaso da zaran manema labarai sun soma jefo muku tambayoyi ku fara amo duk abinda muka shirya.” Tani ta chab’i zancen da fad’in “Zan fed’e musu daga buzu Har fata. Zasuji wacece Ummul da kuma yanda auren Ya kasance. Wayyo wayaga Tani cikin talabijin tana bayani.” Asshe ta furzar da huci had’ida yin gajeren tsaki. Ta dubi Inna Dije alamun tana jiran nata ba’asin. Dije ta murmusa “Ita ce tayi sanadin mutuwan tilon D’a na Faizu sabida bala’in farar k’afarta. Maza bila adadi sun mutu ta dalilinta.” Asshe taci gaba da jinjina kai tana sakin murmushin cin nasara. ** Su Badia tuni Sun nufi cikin gidan suna fad’in a kaisu wajen Ummul. Da kyar Anisa ta kyale su suka shige wajen Ummul d’in a Cewar Anisa ana gyara mata kwalliyarta dan tuni ta canza zuwa wani shigan. Sai kallonsu take tana yatsina fuska tana toshe hanci wai dik warin talauci suke. Azeema tana hankalce da ita jira take su fito daga wajen ‘yaruwarsu Ummul suji da ita. Suna shigewa katafaren bedroom d’in suka tafi a guje suka rungume Ummul. Ummul wacce ta gansu a bazata sai ta mik’e cikin tsananin shock tama rasa mafarki take ko gaskiya. ‘Yanuwanta take gani. Sai ta rungumesu ta k’ank’ame tana mai fashewa da kuka. Saida tai mai isarta suna bata baki suna fad’in kar ta bata kwalliyarta. Ummul ta kuma dubansu dan ta kasa yarda “Azeema, Badia.. Wai dan Allah kune.?” Azeema ta murmusa tace “K’warai kuwa mune ‘Yaruwa. Kawo hannunki ma ki kuma tabbatarwa. Ta had’e hannuwansu su duka uku waje guda. Ummul ta murmusa tana share guntun hawayen da ya digo mata da tissue “Ina Abba na.. Ya jikinshi..? Ina Khulsum da Anty Salima.? Meyasa basu biyoku ba..? Ina Mama da Umma.?” Azeema da Badia suka dubi juna sai Badia ta kamo hannun Ummul tace “Abba jikinsa da sauk’i sosai Ummul.. Yana tashi yana zama saidai maganar ne da sauki. Sann har fita dashi waje yasha iska anayi. Abubuwa ne dai har yanzu ba kasafai yake ganewa ba. Likitoci sunce sai a hankali..Kinsan ciwo idan ya had’u da shekaru.” Ummul ta jinjina Kai a hankali tana addu’an samun lafiya ga mahaifinta. Azeema taci gaba “Anty Salima tana tana gidanta yaranta ba lafiya kyanda suke gaba d’ayansu. Amma tace muce Miki tana tayaki murna kuma taso zuwa Allah bai nufa ba. Mun taho da Mama da Inna Dije.. Da..” Sai Badia ta dan dubeta dan Umma ita ta rokesu cewa ko sunga Ummul cikin gidan kar su sanar da ita zuwanta tukuna. Basu kawo wani abu ba dan Umman ta kwana biyu cikin wane irin yanayi. Ummul sai bata tambayesu Umma ba dan tinda sukace Mama ta taho sai tayi tunanin Umma ke tare da Abbanta. “Khulsum fah.? Meyasa batazo ba..? Har yanzu tana fushi dani koh.?” Ta tambaya jikinta a sanyaye. Murmushin da yafi kama da yak’e sukai. Badia tace “A’a ko kad’an bata fushi dake Ummul…” Ta d’anyi fasali sai kuma tace “Ummul ki yafe mana duk abubuwan da muka Miki a baya..” Azeema ma ta saka baki suna rok’on Ummul yafiya. Dadi gauraye da farin ciki Ya mamaye Ummul. Ta kamo hannayensu tana fad’in komai Ya wuce Allah Ya yafesu gaba d’aya. Nan ta soma tambayarsu labarin gida. Badia ta d’an numfasa tace “Abubuwa da dama Sun faru a lokacin da baki nan.. Kedai sai mun samu lokaci kawai.. Yau ranar ki ce bani so wann hawayen yaita b’ata Miki kwalliyarki na ‘yan gayu.” Cewar Badia tana k’ok’arin gyara mata fuskar. Azeema tace “Wai Ummul kece kika zama haka.? Kin ganki kuwa.? Saikace wata shahararriyar ‘yar gayu irin Wanda muke gani wayoyin mutane ana turawa..” Ta mik’e tana zaga d’akin Wanda Ya amsa sunansa wajen kyau da girma “Dank’ari mak’ari wani aikin sai amale. Rayuwa kenan Ummul kiga yanda Allah Ya sauya miki rayuwa lokaci guda.. Tabbas kinyi hak’uri kuma kinga ribar hak’uri.. Sai na tuna Zubairu dasu Hajiya Dudu irin tijaran da suka zuba lokacin da suka amshe lefenki dashi Zubairun. Ai wllhi yanzu kam saidai Zubairu yazo a direbanki.” Ta k’arashe suna darawa daga ita Har Badi’a. Ummul ta murmusa had’ida girgiza kai “A’a Azeema ni duk wad’ann kayan kyalekyalen basu dameni ba matuk’a akwai kwanciyar hankali da zaman lafiya..” “Chab ai kudi sune kwanciyar hankali wllhi.. Yo ina cikin wann daular k’aryar bak’in ciki Ya tunk’areni ai.” Azeema tace tana mai hayewa saman gadon. Anisa ce ta banko k’ofa ta shigo tana fad’in maza su fice za’a k’arisa shirya Ummul. Azeema ta kuma harararta Tai k’wafa. Ummul ta kamo hannayen ‘yanuwanta tana sanar dasu kar su koma masauk’i su jirata nan parlor tana fitowa. Koda suka fito parlor Azeema dai bata zauna ba sai zagawa take tana bama idonta abinci a cewarta. A haka Anisa ta k’araso daidai sanda Azeema take tab’a wani k’aton flower vase. Anisa ta rausayar da ido tana fad’i a fili “Dealing with Ummul is already giving me a headache. Now I had to deal with these local champions.?” Ta rausayar da ido tana furzar da huci. “Excuse me.!” Ta darara ma Azeema tsawa. Azeema ta juyo da mamaki tana dubanta. Anisa taci gaba da nunata a wulak’ance “That flower vase worth your entire family.. Tell me, idan kika fasa zaki iya biya ne.?” Badia ta d’anyi k’asa da murya taceda Azeema tazo ta zauna su jira fitowar Ummul. Ta dubi Anisa tace “Kiyi hak’uri bazata fasa ba. Hararsu take daga sama zuwa k’asa kafin taja dogon tsaki ta shige tana toshe hanci. Azeema ta yunk’ura zata bi bayanta Badia Tai saurin rik’ota. “Ki k’yaleni na shayar da wann mai k’irar zabon mamaki Badia.” Badia ta girgiza kai “A’a Azeema yau ranar farin cikin Ummul ne bazaki b’ata mata da wani abu ba. Musamman fad’a da dangin mijinta.. Ki kyaleta kawai karma ki kulata.” Azeema Tai k’wafa “Wllhi darajar Ummul taci da nayi wasan kura da ita dan dama hannuna k’aik’ayi yake kwana biyu. Ban saba da wann salihancin ba.” Badia tace “Naji dai bazakiyi ba..” Ta k’arada inata so na tambayi Ummul ina surkin namu mu gaisa.” Daga can Azeema ta hango Haidar na tahowa dukda bata sanshi ba amma kallo d’aya ta masa ta gane shine angon. Sai ta shiga tab’a Badia tana fad’i a hankali “Ke wllhi gashin can yana zuwa.. Shine ango. Shine surkinmu.. Na shiga uku Badia kiga irin mijin da Ummul ta samu bayan duk k’alubalen da ta fuskanta saikace tauraron fina finan Hindiyan nan. Ummul ta had’a komai Badia kawai ta nemi lahira. Gaskiya na yarda da karin maganar nan da ake cewa Wani JINKIRIN alkhairi ne. JINKIRIN Ummul ya zama Alkhairi Badia. Wllhi ta amsa sunanta Ummulkhairi.” Jin Azeema duk ta zauce yasa Badia take mata k’afa kad’an dan ya kusa k’arasowa yanda suke. A hankali take furta “Ke meye haka wai. Ni dan Allah ki natsu saikace wacce kikai gamo sai sunbatu kike. Ki mata fatan alkhairi kawai.. Kinga gashi nan ya iso da alama d’akin da Ummul take zai shige.” Kafin Badia ta rufe baki Azeema ta mik’e ta hau d’aga masa hannu “Sirkinmu.!” Haidar ya juyo da mamaki sai ya shiga ‘yan waige waige yana tunanin kodai ba dashi ake ba. Azeema ta kuma nunasa da yatsa “kaidai sirkinmu.” Ta k’araso yanda yake bata daina washe baki ba “Mu ‘yanuwan Ummul ne.. Ni k’anwarta ce.. Waccan kuma dake zaune Yayarta ce Babanmu d’aya ai da Ummul..” Badia dake zaune daga saman sofa takaici ne ko kunyar abinda Azeema take ta ma rasa wanne ne d’aya take. Sai sukaga Haidar Ya murmusa ya fasa shigewa d’akin Ya nufo yanda suke. Anisa da k’arasowarta wajen kenan mamaki kaman ya kasheta ganin da gaske Haidar Maitama kema kucakan nan sannu da zuwa kuma fah ransa a sake. Wai anya ba’a canza shi ba kuwa. Tana tsaka da tunaninta ta sinkayo muryar Azeema tana fad’in “Sunana Azeema. Ni ce ta hud’u wajen Abbanmu ai.. Daga Ummul sai ni ke biye mata..” Haidar Ya jinjina kai har lokacin da murmushi saman fuskarsa. Ya nuna Badia yace “And.. you are..?” Sai Badia da Azeema suka dubi juna. Azeema ta k’araso da sauri tana rad’a ma ‘yaruwarta “Adda Badia, kinsan dai mudai boko rakiya mukayi dan na tabbata Har yau ko shakeki za’ai da kyar ki iya rubuta sunanki. Su Ummul da Khulsum ne masu kwakwalwar ganewa. Turanci fah yake miki.. Tambayarki yake Ya kike.. Kice masa you are fine. Haka nakeji ake fad’a. Kar ki masa shiru zaki disga Ummul.” Badia tace “You fine.” Sai Ya d’an murmusa kawai yace “I’ll check on.. Khairy.. Sannunku da zuwa once again.” Azeema taci gaba da waving d’insa har ya shige. Badia ta fuzgota tana fad’in “Ke dan Allah wai meye haka ne.? ki kama kanki mana.” “Mutanen da muke gani a tv mun gansu a zahiri Har gaisar damu yake kice na kama kaina.. Ke Nifa yanzu ko unguwarmu na koma wllhi ba ma kowa zanke magana ba ehe… Kiji wani sunan yan gayu da yake kiran Ummul dashi.. Kai wllhi na Miki murna ‘yaruwa Kekam taki addu’ar ta amsu.” Badia ta girgiza kai “Allah Ya baki lafiya Azeema.” Azeema ta kyalkyale da dariya tana amsawa da Ameen. Anisa da takaici Ya cikata furzar da huci Tai tana barin wajen. Dik yanda zatai bazata bari sunan wad’annan Almajiran ya shiga guest list ba tin daga waje zata sa securities suyi watsi dasu. Ana shirin fita wajen event Anisa tai kicibis da Azeema a dan wani lobby. Sai kawai ta k’ara wayarta a kunne alamun tana amsa kira “I need to double-check the guest list because ba ko wasu shara bane za’a barsu su shiga. You know is a high class event.” Ta k’arashe tana aika ma Azeema harara. Zata wuce Azeema ta cakumo wuyarta ta dawo da ita baya “Toh ya ne.! nace ko kinada abin cewa ne.?” Ta k’arashe tana tunkud’a drink din dake hannun Anisar ai kaw ya zube ma Anisa a jiki ya b’ata mata expensive gown dinta. Mamaki ya hana Anisa rufe baki ganin bata ko tanka Azeema ba amma tai mata wann d’ibar albarka. Girgiza Kai Anisa take tana fad’in “No this is not happening.. Not my dress..!” Ta dubi Azeema dake nad’e hannu riga Kai kace zata d’aga wani abin ne tace “You ask for it.!” Tai maganar tana sakin huci tana k’ok’arin Kai ma Azeema Mari amma sai caraf Azeema ta rik’e nata hannun ta kuma d’auketa da maruka har biyu masu kyau. Anisa ta kuma zaro ido cikin mamaki. Saima Azeema ta soma bata tsoro ta fara tunanin jada baya zata gudu Azeema ta kuma jawota tana fad’in “Ashe k’aryar tashanci kike k’aramar maras kunya ba yanda zakije.” Anisa taji rik’on manyan yan dambe ta soma kokawan k’wace kanta tana fad’in “Let go.. let me go.. What are you doing you witch.. I said let me go.” Wani d’aki mai kaman store Azeema ta turata ta janyo k’ofar da k’arfin gaske Wanda taga har wani d’an haske ya kawo daga wajen rik’ewar mai d’aukeda alamun wajen danna yatsa, sann harda wasu lambobi jiki. Bata tab’a ganin irin k’ofar ba. Sai ta d’an matsa da baya ganin k’ofan na haske. Anisa ta fara girgiza Kai tana bugun k’ofan tana fad’in ta bud’eta. K’ara Anisa ta saki tana Kama Kai sanin cewa da tai k’ofan Smartdoor ne. A fili take fad’in a taimaketa tana buga k’ofan. Azeema kuwa shek’ewa da dariya tai jin Anisa tanata ihu daga cikin d’akin sann ta kasa fitowa. Sauri sauri Azeema ta bar wajen tana kyalkyale dariya ga wayar Anisar da ya fad’i nan wajen sanda take k’ok’arin turata d’akin. Tasa k’afa ta kuma cilla wayar a gefe tai wucewarta abinta. Sai nishad’i takeji tayi maganin zabuwar can. Anisa taci gaba da bugun k’ofa tana neman d’auki ga wayarta can a gefe Hisham sai kira yake no response. SameenaAleeyou📚*AUREN WATA UKU..!* *47* *©️Sameena Aleeyou…✍🏽* Da kyar Anisa ta samu d’aya daga cikin ma’aikatan gidan wacce k’ofan ke amfani da fingerprint dinta tazo ta budeta. Duk ta galabaita kwalliyar ma duk yaji jiki a fuskarta. Ba’a maganar daurin kai da tuni ta kwance. Haka ta fito a firgice tana neman wayarta. Can ta tsinceta gefen madubin console daga k’asa. Sauri sauri ta fice ma’aikatan na mata a dawo lafiya ko ta kansu bata kuma bi ba. Tana driving take dialing layin Hisham duk a d’imauce take. Hisham yana d’agawa Anisa ta soma jero masa tambayoyi a gigice “Hish.. Hisham.. Tell me I didn’t screw up like always.. Tell me I’m not late.. Tell me, we can still execute our plans…I.. I’m just few minutes away from the venue.!” Ga mamakinta muguwar murmushin nan taji Hisham yayi. Yaci gaba da fad’in “Do you think I’d let your stupidity ruin my plans.? I always have plan B for every situation Neesa.” Ya

Chapter 44 of 64