Share this page
domin dai aikin gida ya daɗe da kammala komai na bukatar ku an zuba,ga bikin kannen Sarki da yake ta gaba towa nasan kina da labarin bikin kuma so samu ace ku iso da wuri koba komai kinga Sarki dai shine Babban ya'ya yana da kyau ke a matsayin ki na matar shi ki iso da wuri dan ayi komai dake" shiru tayi tana jiran jin amsa daga bakin Teemah ɗin domin tasan ko maganar nata ya samu karbuwa ko a"ah "hello kina jina kuwa" ta tambaya jin shirun yayi yawa,sai dai ga mamakin su sai ɗin ɗin ɗin sukaji alamar daga can gefen Teemah ɗin ce ta yanke kiran,cike da mamakin hakan Uwar gida ta daga ido ta kalli Sarki dake zaune ranshi In yayi dubu ya ɓaci kokari yake ta yanda zai danne fushin dake tasowa daga cikin zuciyar shi,wato abinda take mishi a duk sanda yake mata wani maganar da bai gamsheta ba shine yau ma ta yanke ma Uwar shi Mahaifiyar shi waya. Kara dialled ɗin number ɗin nata Uwar gida tayi sai dai wannan karon ko arzikin ɗaukar wayar bata samu ba.ba tareda ta iya cewa komai ba ta tattara wayar ta tayi cikin ɗaki ta barshi nan zaune bayan ta kira ɗaya daga cikin kannen shi akan ta kawo ma Sarki ruwa mai sanyi,bai tsaya jiran komai ba shima ya tattara ya fice a gidan rai ɓace gaba ɗaya kanshi kullewa yayi a wannan lokacin baya son ya ɗauki mataki akan Teemah cikin gaggawa domin duk abubuwan da takeyi darajar mahaifin ta yasa yake kauda ido dan su zauna lafiya,amma wannan karan zai bata mamaki. a wannan lokacin bai jira komai ba ya ɗauki hanyar komawa KD tun da yabar gidan kuma yake ta faman kiran layu kanta tun yana kira wayar na ringing har daga karshe ya dena samun ta dan ta kashe wayoyin,bai yarda ya kara kwana a KD ba a ranar ya dira Lagos sai dai kuma abin haushi bai isketa a gidan ba mai gadin shi ke shaida mishi cewar kusan satin ta biyu kenan bata gidan amma dai yaran tun kafin ta tafi ƙanwarta Aziza tazo ta kwashe su zuwa barikin su,ba tareda ya huta ba ya kama hanya zuwa gidan Brigadier inda can ɗin ma bai samu Uwar matar tashi ba dan tabi mijinta zuwa US yaran ne kawai a gida sai nashi yaran, a wajen kannen Teemah ɗin ne yake jin cewa wai ta tafi Makodi yin wani aikine na wata ɗaya saura 2 weeks yanzun ya rage mata kafin ta dawo,wannan abu ya kara tunzura shi duk da ba wannan ne karo na farko da take tsallakewa ta tafi wata kasa ko wani state da sunan aiki ba tareda sanin shiba,kayan yaran yasa ta haɗa mishi ya iza keyar su bayan ya tattaro kayan su dake can gidan da duk wani abun bukata nasu dan ankai matsayin da bayajin zai iya cigaba da sakar mata ragamar tarbiyar yaran shi ita bata damu dasu ba can kuma inda ta kaisu shima babu mai sawa bare hanawa, Washe gari ya iso garin na Zaria shida yaran shi dake ta murnar za'a kaisu wajen kakan nin su dan tun tasowar su basu san kowa ba dan Uwar su dai bataje ba balle taje dasu su kuma yan uwan Sarki baƙin halin Teemah yasa suka dena zuwa inda yake sai dai shike bin su, Koda Uwar gida ta ganshi da yaran bata iya cewa komai dan dama tasa ran hakan na iya faruwa ta daɗe tana sa ran ko zai dawo hankalin shi in giyar soyayya ta sake shi to gashi dai bayan shekaru yau yayi abin kwarai,ɗaki guda aka ware ma yaran anan sashen ta bayan ya ajiye musu komai da zasu buƙata ya koma bakin aikin shi. Koda ya koma bakin aiki bai ƙara kiran Teemah ba dan yasan dole inta dawo zata nemeshi da kanta akan batun yaran ta,hakan ce kuwa ya kasance dan tun kafin ta kammala abinda ya kaita ta samu labarin abinda ya faru awajen ƙanwarta Aziza a daddafe ta samu ta kammala ta duro garin na Lagos bayan ta tabbatar da abinda taji a waya tayi ta kiran number ɗin shi bai ɗauka ba dan haka ba kunya ta daga waya ta kira Uwar gida,lallai Fatima ta cika mara ta ido domin tsawon shekaru da take auren Sarki dai² da rana ɗaya bata taɓa ɗaukar wayar ta tayi kiran Uwar gida da sunan gaisuwa ko kuma wani abu na mutuntawa ba,sai gashi yau dan an kwaso mata yara ta iya kiran waya kota manta tarin kiran da ita tayi mata ne oho. Maida komai ba komai ba tayi a matsayin ta na babba ta ɗauki wayar ba tareda wani gaisuwa ko nuna mutunta war cewa da uwar mijinta take magana ba kai tsaye taje ga dalilin da yasa tayi kiran wayar "na kirane dama inji in yarana suna wajen ki" Too dama baki san da batun ɗauko sun da yayi bane ko bai faɗa miki inda zai kai su bane dama? Itama Uwar gida ta tambayeta,amsa ta bata da cewa "inya faɗamin ai bazan ɗaga waya da sunan kira in tambaya ba,tabbaci kawai nike nema in suna nan ɗin ne inzo in kwashe su dan bazan iya barin yara na suyi rayuwa nesa dani ba",amsa mata Uwar gida tayi da cewa "ai ba laifi kina iya zuwa ki kwashe su duk sanda kika so hakan tunda kece mai iko dasu dama ba uban suba" tana gama faɗin hakan ta yanke wayar tana mai jinjina rashin kunyan Fatima lokaci yayi daya kamata ta nunama yarinyar nan cewa bafa son ɗanta bane batayi data bar mata shi tsayin shekarun nan tana ta kwallo dashi kamar tamola,bata faɗa ma kowa yanda sukayi da Fatima ba sai Amina Uwar gidan Malam ita kuma tace mata su zuba ido su gani ɗin ko zata zo ɗin kamar yanda tace, Aiko ga mamakin su sai gata a Zaria a cikin satin da ake bikin gidan inda ta samu rakiyar kawayen ta mutum biyu wannan zuwa nata ya haifar da mummunan saɓani tsakanin ta da Sarki dan fa sunzo sun tata rashin mutunci iya iyawar su ita da kawayen ta Allah ne kawai ya kiyaye dan tabbas Sarki taso ace iyayen shi sun barshi ya tsinke koda igiya 1 ne daga cikin igiyoyinta dake wuyar shi sai dai sam Malam ya shiga maganar ya hana sai dai Uwar gida tayi rantsuwa ko bayan ranta bata yarda yaran su koma hannun Uwar suba,dan yanda ta nuna musu rashin tarbiyar ta haka zata tarbiyar tar da yaran ma,har zuwa wannan lokacin kuma Brigadier bai san halin da ake ciki ba domin Malam sam ya hana Sarki ya faɗa mishi a cewar shi koba komai dole Fatima taci albarkhacin mahaifin ta. Haka ta tattara ta koma lagos cike da ɓacin ran rashin sanin matsayin da auren ta yake kai,suko kawayen ta ba haka suka so ba domin dama su sun mata rakiyane ta yanda zasu zigeta tayi abinda dole a raba auren ta da Sarki dan ba karamin bakin cikin dacen miji da tayi kamar Sarki sukeyi ba,domin kaf cikin su babu wacce ta ke abinda take so kamar ta. Bayan komawar ta duk yanda taso ta hasaso cewar abinda ta aikata bai dace ba shegun kawayen ta sunki bata dama gashi kuma Sarki gaba ɗaya ya tattara ta ya watsar kota kira baya ɗauka daga ƙarshe dai saida ta dunga kamun kafa daga wajen abokan shi kafin ta samu ya sauko ya fara kulata dan Allah ya sani cewa tana mutuwar son mijinta ba ƙaramin cutuwa takeyi da shariyar da yake nuna mata ba,ta ina ma zata fara rayuwar da babu Sarkin ta a cikin shi, tayi ta lallaɓa shi akan ya siya mata gida ko a KD ne ta dawo yaƙiya saboda yasan yanda ta tsani zaman bariki ne yasa shi ce mata sai dai ta dawo suci gaba da zama a bariki,to kun dai san halin yar gaban goshin dan haka taki yarda ta dawo har yanzun sai dai takan ɗanzo ta mishi weekend in taga dama wani lokacin kuma yakan ɗauko mata yaran in tazo kd su tayata zama. Tun wannan lokacin Uwar gida ta kuduri aniyar cewa dole Sarki ya ƙara aure tasan cewa shi bamai shiga harkar mata bane dan haka wannan aikin ita da kanta zata yishi ba kuma zata yarda ta ɗauko wata bare ba a cikin yan uwan ta kona mahaifin shi zata duba tasan in ta zaɓa mishi bazai mata musu ba,tofa a cikin tantancewar nata ne ƙuri'a ya faɗa kan *Ameenatu* bayan ta yanke hukunci kai tsaye ta samu mijin ta da maganar domin tasan cewa inta tsaya sanya sai dai a kawo musu goron sa ranar auren Meenal ɗin dan kowa dai yasan cewa auren wuri suke ma yaran su mata,koda taje mishi da batun shima baiƙi ba domin dama yasa idone yaga ta yanda za'aci gaba dagudanar da auratayya mata na kudu miji na arewa, Dan da karfin gwuiwar shi yaje ma Malam da Maganar dan wannan shine Aure na farko da yake fatan su kulla na zumunci atsakanin su dan kaf yaran su babu wanda suka taɓayi ma auren zumunci daga mazan su har matan. Koda yaje bai rufema Malam komai na dangane da irin zaman da Sarki yakeyi da matar shi ba duk da cewa yasan Malam ɗin na sane,In baku manta ba Malam shi yayi jagorancin neman auren Sarki a wancan lokacin. a sanda Malam Sulaiman yaje ma Malam da Maganar kuma ita Amina ko shekara 14 bata kaiba,kafin zuwan shi kuma dama akwai mutane biyu da sukayi magana suna so aba yaran su sai dai su ɗin ba yan uwa bane,dan haka Malam bai amsa da cewa ya bayar ko zai bayar ba yadai ce mishi suje suyi ta addu'a Allah yayi zabin alkhairi in matar shice zuwa sanda zata gama makarata sai ayi amma dai subar Maganar tukun na. Bayan ya tafi Malam ya daɗe yana nazari dan shi dai gaskiya bawai auren dangine baya soba,a'ah tsoron abinda ka iya biyowa baya in auren baiyi daɗi ba yakeji dan shi baya son abinda zai taɓa zumuncin shi da yan uwan shi dan haka bai tattauna maganar da kowa ba, Sai gashi bayan kwanaki Uwar gida da kanta ta wanke kafa taje da sunan samun Malam akan maganar sai dai tayi rashin sa'a koda ta isa ya riga ya fita,dan haka ta zarce wajen Uwar gidan shi a can take faɗa mata abinda ta yanke nason a haɗa auren Sarki da Meenat dan ita dai tana son Aminatu sosai, sun daɗe suna tattaunawa kafin ta koma gida,yayin da ta tafi tabar matar Malam da dogon nazari ta yama za'a haɗa karamar yarinya kamar Meenat da Sarki wanda a haife ya haifeta,duk bama wannan ba fisabilillahi ai rashin imani nema ace an aurar da ita a gidan mai kishiya balle kuma kishiya irin Fatima wacce tafi karfin mijinta, kai inah gaskiya wannan son kaine,bata taɓa sa baki akan auren ko wacce yarinya a gidan ba amma kam gaskiya bazata bari ama Uwar Malam irin wannan auren ba, Gaba ɗaya wunin ranar kasa sukuni tayi Allah² takeyi Malam ya dawo taji ta bakin shi taji me ya yanke akan maganar. Koda ya dawo kuwa batayi kasa a gwuiwa ba duk da cewa ba ranar girkin ta bane,kai tsaye ta faɗa mishi zuwan da uwar gida tayi da kuma dalilin zuwan nata harma da abinda suka tattauna Malam yana saura ranta ba tareda yace mata komai ba,ganin bai ba zancen nata mahimmanci bane yasa ta gyara zama ta zayyane ma shi duk abubuwan da suka faru dama waɗanda ke kan faruwa a gidan Sarki tsakanin shi da matar shi duk a kokarin ta nunama Malam irin cutar war da auren zai zama akan Meenat dan kowa yasan Sarki na son matar shi duk da tasan Malam yasan da yawa daga cikin abubuwan data lissafa mishi,sai dai duk yanda taso taji wani abu daga bakin Malam hakan ya faskara amsa ɗaya dai ya bata cewa taje tayi addu'a Allah yama Meenal ɗin zaɓi mafi alkhairi,haka ta koma sashen ta jiki ba kwari duk tausayin Meenat ɗin ya rufeta,lokaci² kuma haka Malam Sulaiman ke zuwa wajen yin ma Malam tuni akan maganar su, Kuma Uwar gida ta nemi ganin Sarki bayan yazo ta zaunar dashi akan aure take so ya ƙara,wannan magana ba ƙaramin tashin hankalin ya zama a wajen Sarki ba dan shi a ganin shi ina shi ina kara wani aure kuma fisabilillahi guda ɗaya ma kullum cikin sa mishi ciwon kai take balle kuma biyu,bai ƙara tabbatar da cewa lallai Uwar gida so take hawan jini ya kamashi ba sai da ta faɗa mishi wai yar gaban goshin Malam ta zaɓa mishi fisabilillahi kwata² nawa Meenat ko Meenal ne yaji suke kiranta take,wallahi ko rantsuwa bazaiyi ba yasan tsaf da yayi auren wuri zai ajiye wacce tafita girma,amma ya zaiyi yasan dai ko shaye² yakeyi bai isa ya kalli idon Uwar gida yace mata bai son zabin taɓa,dan haka bai iya mata musu ba haka nan ya amsa mata da toh cikin zuciyar shi kuwa ji yake kamar babbakewa takeyi dan shi dai rayuwar shi kaf bai taɓa hasaso kanshi a tsakanin mata biyu ba.ga kuma sharaɗin da uwar gida ta gindaya mishi na ya janyo yarinyar a jikin shi dan Malam ya tabbatar da gaske sukeyi. Wannan shine takaitaccen bayanin Sarki da abinda rayuwar shi ya kunsa,ina fatan kun rike cewa shine na uku a cikin manema auren Aminatu a yanzun da take matsayin kwaila nasan zuwa gaba sai sunkai 10 ko kuma waya sani ko itace zatayi gadon farin jinin kakarta Hajiya innah😂,mun gama da wannan fannin bari mu koma kan su Moon budurwar Sarki. ******** Bayan sun bar kofar gidan ya mashkur takaddama ce ta kaure a tsakanin su Meelat da Moon suna cewa a wuce gidan su Maryam su kuma Meenal da Aisha na cewa a wuce bayan layi wajen siyo awara mai kwai ɗin da Meenat ta basu labari jiya in suna dawowa sai su wuce gidan su Maryam ɗin,kafiyar da Meenat tayi akan zuwa bayan layin ne yasa dole suka hakura akan aje a siyo awarar dan haka suka yanke hanya,a cikin tafiyar nasu ne Aisha ke tambayar Meelat akan meya haɗa Sarki da Meenat da ɗazun Meelat ɗin tace Meenat batayin shi shiyasa ita ma batayin shi, "Kai kema Aisha wallahi kin iya tambayan gangan ke yanzun dan Meenat batayin wani har sai kin tambayi dalilin hakan bayan kinsan ta haka take kamar mai iskokai ita ai bata neman dalilin so ko ƙi akan wani abu, Kin san mutuniyar ki da ci,to bayan dawowar Sarki da aiki a KD duk weekend nan yake dawowa yayi shi kamar yanda kuka ganshi yanzun to idan yazo yana zaman karatun da akeyi na maza a masallacin Malam wani zubin kuma a cikin gida sukeyi to in sun gama karatun sai Malam yace ya shiga suci abinci a falon shi to kuma kun san mutuniyar kota koshi sai taje ta ciyo na Malam to zuwan da Sarki keyi yana rage mata bojet dan haka ta fara adawa dashi wai yana zuwa kwaɗayi a gidan su,shine fa kawai ba wani dalili mai ƙarfi ba sai kuma wani lokacin yakan tsareta akan ta kwaso takardun ta tazo yaga ni ko tanayin abinda ya dace a school abuna ƙarshe dai waɗannan karnukan daya kawo waɗanda suke hana mutane sukuni,ina fatan yanzun kin gamsu zaki barni in huta da tambayiyin kin nan" ta karasa faɗa tana haɗa hannayen ta biyu alamun roko,dariya duka sukayi banda mutuniyar data ɗaure fuska dan ita ko maganar shi bata so ayi a kusa da ita. Sunzo wucewa ta kofar wani gida suka hangi wata mata rike da yaro sai faman tsaga kuka yake duk yanda take lallashin shi yaron nan yaki yin shiru,sunzo dai² kofar gidan da niyyar su wuce su yaron ya kara fasa kuka kamar wanda ake yanka naman jikin shi,ina wuni suka gaisheta haka nan ta amsa su hankalin ta ya kasu biyu rabi a kansu rabi akan yaron da take lallashin "wai bazaka min shiru ba dame zanji da jarabar kukan ka koda aikin gidan zanji shi uban naka ai yana kallon kana kukan ya tsallake yabar gidan gashi na leko bashi ba dalilin shi,yau ko yaran dake wasa a unguwar ma babu balle In samu mai rikemin kai inje in karasa girkina,yan mata nace ko zaku ɗan rika min shi ya muku rakiya? Kunga wallahi aiki nike duk ya gama ruɗani nasan kafin ku dawo na gama aikina shima kukan wanda zai fita dashi yakeyi" Mika hannun ta Meenat tayi ta karɓe shi aiko kamar aikin asiri sai gashi yayi shiru ya lafe a jikin ta sai ajiyar zuciyar da yake faman saukewa na kukan da yasha, "Kun gani koh! Dama na faɗa bari in miko miki zanin goyon shi da feeder ɗin shi,ai wallahi nagode miki na samu in karasa aikina a tsanake" ta karasa fadar hakan a yayi data juya cikin gidan da saurin ta bata jima ba ta dawo da showel na goyo da wata yar madaidai ciyar jaka data zuba kayan bukata na kula da yaro tana ta musu godiya ta basu kayan sannan ta juya cikin gidan Tafiya sukaci gaba dayi ba tareda wata tace komai ba zuwa can Meelat ta kalli Meenat dake saɓe da yaron a kafaɗarta ba tareda ta goya shin ba tace "Beb wai ina zaki kai yaron nan da kika karɓo shi a hannun Uwar shi? "Ya akayi hala? Itama ta maida mata amsa da tambaya,"nasan baki fiye son ɗaukar yara ba sai naga kin karɓe shi,me kike shirin yi? Dariya Meenal ɗin tayi,"yarinya lallai zuwa yanzun kin sanni da kyau to tsaya kiji kinga can" ta fadi can ɗin tana mata nuni da hannun ta,kallon inda take nunawan dukan su sukayi, a tare suka haɗa baki wajen cewa police station suna masu zaro idon su cike da tsoro, "Kwarai Ganuwa Police Station aka rubuta,can zan kaishi wai hala bakuji abinda Uwar tace bane?" Bata jira amsar suba ta ɗaura da cewa " cewafa tayi mijin ta tsallakewa yayi ya fice ya barta da yaro yana mata kuka duk da tarin aikin dake gaban ta bai sa ya tausaya ya taya ta aikin dan ta gama da wuri taji da ɗanshi ba ko kuma ya ɗauki yaron ya fito dashi dan ta samu damar kasara aikin gaban ta cikin kwanciyar hankali,ku duba kuga yanda duk kukan yaron ya ruɗata tayi rarrashi shima ɗan Baban shi yaƙi shiru,saboda tsabar rashin tausayi irin na uban matar nan ta ɗauki ciki wata Tara koma fiye da haka duk tsayin watan nin nan ita kaɗai tayi ta fama da lafiya ko babu tazo tasha wahalar nakuda Allah ya ceceta tasha da kyar yanzun da lokacin dazai tallafa mata wajen kula da yaron yayi shine ya tsallake yabar gidan wato ita yar wahalar tayi ta fama koh? To ya gamo yawon nashi ya dawo yazo ya ɗauki yaron nashi a police station" ta faɗa tana yin gaba hankali kwance kamar ba tashin hankali take shirin ballo musu ba, Moon ne tayi saurin shan gaban ta, "Meenat kawo shi dan Allah mu mayar ma Uwar shi karki kaishi wajen can please" Wallahi sai na kaishi in tsoro kukeji kubi tanan lungun ku fita ta can ku jirani idan na kaishi zan fito in same ku muje wajen mai awarar," Muje in rakaki" cewar Meelat, Ke Jamila ashe kema bakida hankali irin ta nidai wallahi ba ruwa na Aisha zo mu ƙara gaba mu jira su" lungun da Meenat ta nuna mata suka bi su kuma kai tsaye suka wuce police station ɗin, Mutum biyu suka samu cikin police ɗin sai da suka gaishe su cike ladabi sannan Meelat ta ɗaura da cewa," muna cikin tafiya ne zamu wuce ta layin Sule Ajasco munzo dai dai kofar wani gida shine muka haɗu da wata mata tace mu riƙe mata wannan yaron taba ma kawata shi wai zata ɗauko abu a gida tayi mantuwa,to dama koda muka ganta yaron yana ta kukane koda ta bamu shi kuma bai dena ba,shine ta bamu harda wannan ta faɗa tana mika musu jakar tarkacen su feeder ɗin yaron da zanin goyo,shiko yaron ganin su maza yasa yaketa washe baki yana mika musu hannu hakan yasa Meenat ta mikama su yaron sannan Meelat taci gaba da cewa, " Munyi tsoron kar azo sato shi tayi dan mun daɗe a tsaye wajen bamu ga ta dawo ba da muka bi lungun kuma sai mukaga ashe hanyace kawai ba gida ko ɗaya a wajen balle mu shiga mu tambaya mu kuma ba yan nan unguwar bane daga tudun jukun mukazo neman gidan wata yar makarantar mu kuma bamu gane kwatancen ba, shine mukace gara mu kawo shi nan tunda bamu san gidan mai unguwa ba, Su kuma police ɗin kamar Allah ya rufe musu baki basu wani tsanan ta bincike ba suna kallon su suka wuce a dai² kofar police station ɗin ne sukayi karo da Ibrahim kwaro yayin fitan su dukkan su basuyi tsammanin ganin shi a wajen ba dan haka sosai suka tsorota amma tsabar Jan wuyanci sai basu nuna ba sai ma gaishe shi da sukayi suka wuce dan sun san dai shike nan aikin su ya buɗe. 🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Wannan tar gaban goshin Malam ɗin fa sai kun mike da addu'a dan wallahi batajin magana. Domin jin yanda zata kaya sai ku Tara a page na gaba. Gaskiya mutane na bakwa comment anya bazan ajiye alkalamina ba kuwa?🤕 Share please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _*Ina mai bada hakuri sakamakon jina shiru da kuma yi* gashi nan dai aci da hakuri..... ```Page14 Tafiya suke suna waige alamun rashin gaskiya duk da yanda sukayi mursisi kuwa dan Allah ya sani jinin su a kumba yake Allah² suke suga sun ɓace a wajen kafin ɗaya daga cikin police ɗin nan ya fito neman su,dan haka suka canza hanya izuwa wata lungu daba a fiye binta ba har saida suka kule cikin lungun kafin Meenat ta juya cike da fargana tana kallon Meelat tace "kawata Allah ya cece mu! Waiyo Allah kinji yanda nike jin zuciya ta tana tsalle kuwa? na rantse da Allah banyi zaton zamu sha ba,ke wai uwar me ma ya kawo wannan sojan wajen nan ? Shike nan mun shiga uku dan nasan da zarar yasan abinda ya faru yana komawa gida zaiba Sarki labari. Dukewa tayi dafe da kirjin ta,kamar kuma wacce aka tsikara sai gashi ta zabura "kina ji koh shiru zamuyi karki sake ki faɗama su Moon abinda ya faru dan wallahi suna sani tofa magana ta ƙare ba lallai su iya shiru da bakin suba dan shegen tsoro garesu,shiru kawai zamuyi mu jira abinda zai biyo

Chapter 12 of 92