k'arfi.
"Waiyo waiyo waiyo wallahi Allah ni babu ruwana shine"
Meenal ta furta a firgice,
Cike da zafin nama shi kuma ya koma inda ya taso yana wani babbasarwa bayan ya lek'a dan ganin ko wani yayo tanan inda suke a cikin masu gadin gidan sai dai kuma babu wanda yake tahowa,
"Na sumbace ki!"
Ya fad'a hankali kwance,
"A yaushe?" Ta tambaya,
"D'azun mana!"
"A ina?" Ta kara tambaya.
"A kumatun ki da goshin ki"
Ya bata amsa.
"Kai ๐ณ"
Ta furta tana zare ido,
Kafin ta janyo jikinta zuwa inda yake.
"Ke miye hakan?" Ya tambaya yana makalewa a jikin kofa,
"Ki koma mazaunin ki ni wasa nike miki"
"Wasa?๐คจ ok ni kuma da gaske nikeyi in fad'a maka muahhh"
ta sake mishi sumba mai k'ara a fatar bakin shi, karar sumbar kai tsaye ya wuce cikin kunne ya cake shi a kahon zuciya, dan haka luuu yayi baya uwa wanda yake shirin somewa,
Ganin hakan yasa ita kuma ta koma kujerar ta tana fashewa da dariyar yanda taga yayi, yunkurowa yayi da niyyar cafkota sai dai kuma kafin ta ankare ita kuma ta balle murfin kofan gefen ta ta fice daga motar tana nuna shi tana kuma ci gaba da dariya a lokaci daya,
"Dawo mana kinji tsoro ne?"
"Ah tsoro halal ne"
"Dan Allah kizo please ๐"
"Kai Heart kai bakajin kunya nane? wai"
"Kunya fa naji kina magana akai bayan kinsa na rasa kunyar tawa a yanzun nan, me yayi saura kuma?"
"Aure" ta bashi amsa tana rufe fuska, kafin ta juya taci gaba da tafiya duk kiran da yake mata da cewar da yakeyi ta jira shi hakan bai sa ta tsaya ba,
"Kai Abdul!
Kai Abdul!!
Mai Jama'a fa, wai baka jina ne bazaka tashi ba kazo ka kwanta kamar wani mai shafar aljannu sai wani faman kiran sunan Heart kakeyi a'ah ba heart ba zuciya, dallah can tashi, ni anya kuwa Yaron nan ba dagaske bane kuwa da ake cewa ko aljannah ce ta aure ka shi yasa kake k'in kula yan mata ba kuwa?,
To inba haka ba miye wani na kwanciya kana mafarki da kiran sunan Heart da rana tsaka? Tashi da Allah ni bana son lalaci kana namiji kana baccin hantsi"
Duk surutan da Hajiya keyi tsaf yake jin duk abunda take cewa sai dai kuma gaba d'aya bashi da karfin dazai yunkura ya tashi, dan hatta labban shi ma ji yayi sun mishi nauyi ta yanda ya kasa bud'esu balle ya tanka mata ko sau daya ne dan tasan ya tashi.
Kuyi hakuri da guda 1 bamu da wuta ne wallahi kuma na cinye cajin wayar tun safe shi yasa.
Babu editing fa๐คจ
*Ummiee Zaria*โ๐ผ
[8/22, 7:00 PM] Ummiee Zaria: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA!*๐ฑโ๏ธ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
*~{{MY FAMILY}}~ BOOK 2*
ยฉยฎ *UZ-2023.*
*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
* ~{Ummiee Zaria}~*โ๐ผ
___*Page 7*
Kuyi hak'uri jiya nayi mistake wajen rubuta number mai makon insa page 6 saina k'ara maimaita number 5,
***Kai Abdul shin wai kodai dannau d'in dake danne mutane in suna baccine ya danneka shi yasa ka kasa tashi ne ban sani ba?"
Ganin cewa babu mai bata amsa a d'akin kuma shima da take magana dashi d'in bai nuna alamun cewa yana jinta bane hakan yasa ta koma da baya ta shiga cikin bathroom din dake d'akin, wani k'aramin roba ta ciko da ruwa sannan ta fito,
Ta gefen kanshi ta koma tayi tsaye tana k'are mishi kallo, can kuma sai tasa hannun ta ta zare pillow d'in da kanshi ke kai ta zauna a wajen sai ta maida kanshi akan cinyoyin ta,
Ruwan data d'ibo ta d'auko daga kan side drawer din data ajiye shi sai da ta karanto addu'o'i ta tofa a ruwan kafin ta dunga d'iban ruwan da hannun ta na dama tana shafa mishi bakin ta kuma yana karanto ayatul kursiyyu tana tofa mishi duka a lokaci d'aya,
Shigar ta da kuma fitowar ta cikin bayin duka akan kunnuwan shi hakan ya faru sai dai kuma har zuwa lokacin yak'i bud'e idon shine a nashi zaton in taga bai tashi ba zata fice ne ta bashi waje, kenan idan ta fita shima sai ya lallab'a ya fice a Sashen salin alin ba tareda tasashi a gaba da tambayoyin data fara jera mishi tun yanzun ba,
Sai gashi mai makon yaji ta fice daga d'akin ah ah sai ma saukan sassanyan ruwan da yake da tabbacin a cikin bayin ta dibo shi yaji a kan fatar fuskar shi wanda dole hakan yasa ya dunga sauke a jiyar zuciya dan sosai sanyin ruwan ya ratsa shi, a hankali sai ya dunga jin gabobin shi suna mikewa sab'anin d'azun daya rasa karfin jikin shi gaba d'aya,
dan haka sai ma kawai ya wani k'ara gyara kwanciyar nashi da kyau akan cinyar na Hajiya,yayinda ita kuma hakan ya bata damar bud'e mab'allan gaban rigar shi taci gaba da shafa mishi ruwan harta cikin jikin shi wato daga kan kafad'un shi kirji zuwa cikin shi,
"Abdul"
Hajiya ta kira sunan shi dan ta gani ko dannau d'in ya sake shi yanzun .
"Na'am Hajiya ta "
"Ya kakeji yanzun ?"
"Lafiya lau nike ji babu abunda yake damuna ni dama ai"
Ture kanshi tayi daga kan cinyarta tana sababin cewa.
"Aikin banza babu abunda ke damun ka dama shine kazo kamin Shane Shane a gado uwa wata mai jego sabuwar haihuwa, nifa nayi zaton ko dannau ne ya danne ka shi yasa harna tsaya ina wahalda kaina"
Ta fadi hakan a yayinda ta yunkura da niyyar tashi a inda take zaunen,
Ganin hakan ne shi kuma yasa ya k'ara murginowa ya maida kan nashi akan cinyar nata,
"Ina zakije kuma bayan kin tasheni ina cikin bacci na mai dad'i da mafarkin da nike fatan ina ma ace a gaske ne hakan ya faru kawai kika wani shigo kika katse min komai"
"Ai ni nasan dama bazai wuce mafarkin ba dama tundaga waje fa nike jin kana ta faman kwala kiran Heart ๐ Heart"
"Da gaske Hajiya kinjini ina kiran sunan ta?"
"To in banji kaba zan shigo ne?
nifa tsoro ma naji dan a iya sani na dai nasan mu biyu kacal muka kwana a cikin Sashen nan nawa dagani sai takwara shine kawai daga fitowana na fara jin ana kiramin sunan Heart a cikin gida ai dole in leko inga ko lafiya,
Wai bama wannan ba wacece kakeyin mafarki da itane?
Dan wallahi nifa lamarin ka ya fara bani tsoro, kasan fa ance dama ita aljanah idan ta auri namiji mafarkin ta kawai zai dungayi a hakan sai kaji wai ta hayayyafa a rayuwar dashi yake ganin yana mu'amala da ita a mafarkin, niko in aljanah ta aureka har kuka tara yara a cikin baccin da ba komai zaka gane ba aita cuceni Wallahi.
haka kawai ina zaman zamana a haifomin tattab'a kunne da aljannuh"
Dariya ma ta bashi dan haka yako fara dariya sosai yana daga kwancen,
"Oh mahaukaciya ka d'aukeni ina fad'a maka gaskiyar zance kana dariya?,
Wallahi indai kasan kana mafarkin saduwa da mace harta haifo yara to gara tun wuri ka fad'amin gaskiya in tashi tsaye in yak'eta da karfin ikon Allah,"
"To ke Hajiya wai waye ma yace miki ni aljannah ta aure nine?"
"Ai ba wani ne zai fad'amin ba nice kawai nike ta hasashen hakan,
Fisabilillahi inba shafar aljannu ba d'an nan shekaru sunja amma ace har yanzun baka da wata tsayayyar budurwar da za'a nuna ace wacce ne budurwar da kake nema,
Naga suma masu biyoka gidan duk kamar anyi ruwa an d'auke duk sunsha fama kansu lafiya sun dena zuwa yanzun,
Ga Yusufu dai harda yara 3 Mustapha ma angwancewa zaiyi kwanan nan shi Sadeeq kuma duk da dai ba'asa ranar auren ba amma dai gara shi ko babu komai ai munsan yana da tsayayya,
To kaifa?
Iye nace kaifa?
Shiru ko maganar matan ma baka zama ayi dakai ba dole inyi tunanin ko da gaske aljanar ce da kaiba,
Ko ce maka akayi inajin dadin yanda kake zaune hakan ne bayan ba kudin auren ka rasa ba, ko kwanan baya da uwar ka ta matsa da maganar kayi min k'aryar cewa baka da lafiya na dai gyale Kane kawai dan bana son kaga kamar ina matsa maka, dan ban sani ba ko jira kakeyi sai na mutu ne kafin kayi auren?"
"Ki dena wannan maganar Hajiya insha Allah ko zaki mutu ba yanzun ba sai kin goya yarana kamar yanda nima kika goyani"
"To in haka ne ka fito da matar kayi auren mana, ko da gaske kana da aljanar ne?"
"Aljannah kuma dai Hajiya, ni babu wata aljana a tare dani ki yarda dani lokacin auren ne kawai baizo ba a shekarun da suka gaba ta da kuma nima da ban shirya ma auren ba"
Tashi yayi daga kwancen da yake ya zauna yana fuskantar ta kafin yaci gaba da cewa,
"Zanyi aure kwanan nan Hajiya ta,
ko badan kaina ba kodan in dena ganin damuwa akan kyakyawar fuskar nan naki"
Ya k'arasa fada da murmushi a yayin da ya mik'a hannun shi ya shafo fuskar nata,
Hannun ta guda ta d'aura akan nashi hannun dake fuskarta tana shafawa da murmushin itama tace,
"Ah ah Abdul so nike kayi aure dan ra'ayin kanka dan kana son matan bawai dan ni ina son kayi aure ba, domin so nike inganka cikin farin ciki da matar da nasan zaku kula da junan ku ko bayan bana raye, kaga kuwa hakan bazai samu ba sai ya kasance dukan ku kuna son juna, shi yasa kaga tun tuni ban tilasta ka akan kayi auren ba duk da nasan idan na kawo maka matar zaka amsa, sai dai nafi son naka zab'in wato macen da zuciyar ka tayi maka na'am da ita, ni kuma zan baka goyon baya na d'ari bisa dari har sai ka mallaketa ko wacece ita kuwa!"
"Ko wacece Hajiya kin tabbata zaki tsayamin har sai na mallaketa?"
Ya tambayeta yana mai tsare ta da ido.
"To wacece ma zataga jikana son kowa kin wanda ya rasa tubarkhallah tace wai bata so, kana da asali da na saba mai kyau, kana kuma da rufin asirin da zaka iya rike mata hud'u ma idan kaso hakan balle kuma mace daya,kaf a cikin halayen ka babu na banza dan haka ina da tabbacin babu macen da zatace bata son ka"
Wai dan Allah dama ashe haka mutum yakeji aduk sanda za'a zauna ana kwarzanta shi?
Eh Alhamdulillah yasan shi din Allah bai rage shi da komai ba, haka kuma bai tab'a neman wani abun buk'ata a rayuwa ya rasa ba, mutane da dama kuma sun dad'e suna kwarzanta shi,
Amma yabawar yau da yaji daga bakin hajiya ya k'ara sawa yaji cewa lallai zai iya samun cikar burin shi,
"Wai Malam bazaka fad'amin ko wacece yarinyar dan in taya ka kamfe ba?"
"Hajiya saurin me kikeyi ne?"
"Har sai ka tambayeni bayan yanzun na gama shaida maka cewa auren ka nike son gani kafin in mutu"
"Nifa har yanzun ma ban fad'a mata cewa ina sonta ba!"
"Baka fad'a mata ba to uban me kake jira, so kake sai wani can ya maka shigar sauri ko me?"
"Hajiya yarinya cefa wallahi har yanzun ba wani hankali take dashi sosai ba, yanzun idan naje nace mata ina sonta kai tsaye ai rainani kawai zata k'arayi dama can kuma ba wani tsorona takejiba,"
Galala Hajiya tayi da idanuwa da baki tana binshi da kallo,
Can kuma sai ta fara tafa hannuwa da alama abun yakai mata ko ina,
"Amma kai dai kam Allah yayi shashasha a wajen nan ko sakarai zan kira Kane ma oho,
Oh wai ita wacce kake son ma har yanzun baka riga ka gabatar mata da kanka a matsayin masoyi ba tukun na amma kake nan kwance kana faman mafarke mafarke na banza da hofi, to kwanta a gida kaci gaba da bacci baki bud'e kaga duk sanda ka farka sai kaji ana sanarwar d'aurin auren ta,
Kuji min wani zancen banza fa, kasan karamar ce kuma ka fara son ta, in kana tsoron raini ai da tun farko sai kayi kokarin tankwara zuciyar ka ka hana kanka sonta, to wai ma dama duk shekarun nan jira kakeyi idan ka tashi aure ka d'auko min gansamemiyar mace mai irin k'irar ka?
Ako dai da nayi turr dakai dan bazaka mori mata ba, kasan ni shekara nawa ne tsakanina da mijina kakan ka? To a kallah shekarun kusan goma sha Biyar ne ko fiye ma da hakan a tsakanin mu, tunda baka son ta raina ka ai sai kayi ta zama kana kallo wani can zaizo wanda shi yarintar nata ma shine zaiga ya burgeshi har yaji kwadayin auren ta"
Tana gama fad'in hakan ta mik'e da niyyar barin dakin,
"Hajiya ya kuma zaki wuce bamu gama shawara ba?"
"Wacce shawarar kuma ta rage ban baka ba? Tunda k'arama ce ai sai kaje kayi ta raino koh!"
Ficewa tayi a d'akin tana kana nan surutai,
Yayin da shi kuma ya koma da baya ya kwanta kanshi na kallon saman d'akin,
"To yanzun fisabilillahi ita Hajiya so take in tari yarinyar tun yanzun, to me zance mata idan na tare ta? , oh ya Allah ka bani kwarin gwuiwar da zan tunkareta dan Wallahi yanzun kam ni kaina nasan ina da bukatar ta a rayuwata dan an kai matakin da nike buk'atar kusanci da macen aure na"
Ganin zaman d'akin bazai bashi mafitar da yake nema ba, sai kawai ya mik'e ya fice a cikin d'akin koda ya fito tsaye yayi yana kallon kofar d'akin ta da murmushi akan fuskar shi,
Kafin ya gangara ya sauka daga matakalan zuwa k'asa Hajiya ce kadai a falon tana zaune tana cin abinci akan dinning wanda yake da tabbacin cewa yanzun take yin nata karin safen kenan, yanda yaga tana watso mishi harara yasan idan ya zauna tofa ba lallai su kwashe ta a dadin raiba sai kawai yasa kai ya fice daga Sashen nata dama gidan baki d'aya yana fitowa ya kira, Unaiza daya daga cikin yan matan dake aiki a restaurant din dake nan wajen ya fad'a mata abunda yake buk'ata ta kawo mishi yana gama karin kuma wani abokin shi yazo da mota ya d'auke shi suka bar unguwar gaba d'aya.
Baccine ya kwashe Meenal a cikin d'aki ba ita ta farka ba har sai wuraren 1 saura na rana, dan haka tana tashi sai kawai ta fad'a bayi sai da tayi tsarki kafin ta d'auro alwallah,
nasan wasu zasuyi tunanin cewa mai yasa bata k'ara yin sabon wanka ba?
To ita dai jikar Hajjaju a ka'idar ta sau biyu takeyin wanka a rana idan tayi na safe tofa sai kuma na kwanciyar bacci, inba dai irin taje makaranta ta dawo a wahale bane shine inta dawo zatayi wani sabon wanka amma inba haka ba ita bata takura ma kanta da cewa dole dole sai tayi wanka sau uku a rana๐คจ,
Bayan ta fito wasu takardu ta fara harhad'awa ta cusa su a cikin jakarta kafin ta fiddo wata atamfa da akayi ma d'inkin doguwar riga pitted gown kalar navy blue da gyalen da zai shiga da atamfar ta ajiye su a gefe kayan jikin ta ta cire ta maida wannan rigar jikin ta, agogon dakin ta kallah jin ana ta kiraye kirayen Sallah dan haka sai kawai ta shimfid'a dadduma ta zura hijjabi ta tada Sallah,
Bayan ta idar hoda yar kad'an kawai ta shafa a fuskarta dan ya rufe maskin man data dan murza ko kwalli bata goga a cikin idon taba sai mascara da tayi amfani dash tad'an taje gashin idon ta suka tsaya da kyau,
Girarta tsararre ne dan haka bata buk'atar bata lokacin wajen gyarar ta, jan baki kuma dama ita baya cikin tsarin rayuwar ta iya karta Vaseline to yau ma shi ta murza a bakin nata,
Ba wani iya d'aurin d'an kwali tayi ba domin kowa yasan daman yawancin kayan ta dogayen rigunan abaya ne sai English wear, dan haka ko yanzun bata tsaya b'ata ma kanta lokaci ba d'aurin nan na gargajiya wato ture kaga arziki tayi,
Bata tsaya duba mirror dan ganin tayi ko da gyara ba kawai ta feffesawa jikin ta turare ta kwashi jaka da gyalenta da takalmin duk a hannu tayi waje tana jin yanda wayar ta ke vibration amma bata damu da cewa sai ta duba ba,
Sai dai kuma koda ta fito daga dakin tsaye tayi dan sai yanzun kuma taji tanajin shakkar sauka kasan kar yazo ace wancan mutumin na nan a falon,
dan haka sai ta juya bayan ta kad'an ta bude kofar dakin hajiya bakinta dauke da sallama ta lek'a,
Babu kowa akan gadon dan gadon da Hajiyar ma ta tashi tuni ta gyare abunta tsaf kamar ba itace kwance akai d'azun ba,
Ganin babu hajiyar a dakin ne yasata komawa da baya sad'af sad'af haka ta dunga tafiya gudun kar ajiyo takun ta daga saman bene take lekowa kasa dan taga waye da waye a cikin falon, harta gama kalle kallen ta bata ga kowa ba dan haka sai taji kwarin gwuiwar saukowar cikin sand'a, kenan dai baya cikin Sashen,
To amma kuma ai bata da tabbacin cewa baya a harabar gidan dan ta sanshi yawanci a nan yake zama yana amsa wayoyin shi na fama da baya gajiya,
Itafa Allah ya sani kawai bata shirya yin ido biyu dashi a yanzun bane shi yasa take ta wannan kame kamen inba haka ba ina ruwan ta dashi ai da tuni tasan inda dare yayi mata,
Tana tura baki da kunkuni ta nufi window din falon shima ta yaye labulen wajen tana lek'a wajen duk da cewa ba komai take iya gani ba amma dai bataga alamar shi a wajen,
A yau dai kam tayi da na sani akan rashin mallakar number din ko mutum d'aya daga cikin masu gadin gidan,
Yanzun dan Allah da tana da number din wani a cikin su ba kira zatayi ba kawai ta tambaya taji ko AK na gidan koya fice, amma gashi yanzun sai wani kame kame takeyi,
"Mtwsss"
Taja tsaki mai tsayi.
"Allah kuwa fitana zanyi ai ba tsoron shi nike ji ba inma kunya ne ai shine zai biye kanshi tunda ya aikata abun kunya ya shigomin daki ba tareda izini ba"
Da kwarin gwuiwar data aro ma kanta ta fito,
"Ke wai dama tun safe kina cikin gidan nan bakije makarantan ba?"
Ta jiyo muryar hajiya daga gefen ta,
Waigawa tayi sai taga hajiyar zaune akan dadduma daura da kofar falon ta baje wasu takardu kona minene oho,
"Ban tafi ba Hajiya na samu kira da safen cewa an canza lokacin da zamuyi lecture din ne sai da ranar nan shi yasa zan tafi yanzun, na lek'a dakin ki ban ganki ba dama ince miki zan fita dan nasan bazan dawo da wuri ba sai can yamma"
"To Allah ya tsare kidai kula da kanki in kin fitan kuma dai nasha fad'a miki banda kula samari atoh,"
Wucewa tayi bayan ta amsa ma hajiyar da cewa "to insha Allah hajiya sai na dawo"
Bata fita a gidan ba sai da ta tsaya ta k'arbi number din Isah daya daga cikin masu gadin gidan tayi saving a wayarta.
*UMMIEE ZARIA*โ๐ผ
[8/22, 10:33 PM] Ummiee Zaria: ๐ฑโ๏ธ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA!*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆโ๏ธ๐ฑ
*~{{MY FAMILY}}~BOOK 2*
ยฉยฎ *UZ-2023.*
*RUBUTAWA*
*~{Ummiee Zaria}~*โ๐ผ
..... *Page 8*
Acan makaranta Meenal ta iske su Meelat bayan tayi submitting abunda take buk'ata ne kuma suka rankaya zuwa kasuwar sabon gari can Babban shagon Ya Mashkur dan su duba ankon da zasu fitar,
Tafe suke suna k'ara tattauna wa akan batun ankon,
Meenal na fad'in atamfar a fidda mai haske wacce zata d'auki kalar fatar kowa in yaso less din kuma sai a fitar da peach color saboda shima yana ma bak'ar fata kyau, ita kuma Amarya dama shigar farare zatayi har a gama biki dan farar kala dama shine zabin Meelat din,
Tattaunawa suke tayi dai in Maryam tace kaza za'ayi meenal kuma tace ah ah kaza dai za'ayi a haka har suka isa kofar shagon nashi, can gefe suka faka,
"Bebs wai kun lura da motar nan dake bayan mu kuwa?"
Maryam ne ke tambayar su, bayan sun faka.
"Wace motar?"
Meelat ta tambaya itama a yayinda ta juya baya tana leke dan taga motar dan dama itace a baya su kuma suna zaune a gaban motar ne Meenal na tuk'i Maryam kuma na zaune a kujerar mai zaman banza hankali kwance sukeci gaba da hirar su kamar ba'a cikin mota suke ba dan Meenal gyalen tama a gefen sitiyari ta ajiye shi kuma glass din gefen ta ma ta sauke shi kusan rabi,
"Wai wannan farar motar dake bayan mu kike magana akai?"
Ta tambaya bayan ta dawo da kallon ta kan Maryam din,
"Ita fa inata lura da motar tun d'azun take bin mu nayi tunanin ko kila anyi katari ne ko kila waje d'aya zamu nufa da mai motar sai yanzun na k'ara tabbatar da cewa mu dai yake bi"
"Dallah can kyale koma waye bashi da aikin yine,"
cewar meenal a yayinda ta dauko gyalen ta gyara zaman gyalenta a saman kanta ta bud'e kofar gefen ta tana shirin fita,
"Ke Meenal karki fita ga mai motar nan fa ya fito kuma wallahi nan suke nufowa su biyu"inji Meelat
"To sai me in nan yake zuwa ina ruwan mu dasu? Ina ce dukan ku dai kuna da mazajen aure to uwar me zaku musu? Kunga Malamai dallah ku fita muje ni bani da lokacin b'atawa kunsan abunda ke gabana gobe a makaranta,ina ga in mun gama danan ma can zan koma ko zan samu ganin Na'eem yasan yanda za'ayi in rubuta shegen test din nan mu kaishi office din shi mu ajiye, naji haushi sosai wallahi da kukace Sir Emma yayi shegen test d'inshin nan yau kuma duk wancan mugun ne yajamin rashin zuwa makaranta da wuri yau, ga Emmanuel din nan wallahi ni ko hanya bana son ina had'awa dashi yanzun nasan jira yake gobe zanje in dunga rok'on shi yana yarfani, Allah sai ya saka min wallahi"
Ta k'arasa fad'a yanayin fuskarta na canzawa zuwa fuskar damuwa,
"To wai ke meya hanaki fitowa da wuri to bayan kuma dama mun shirya fitowa tun safen?"
Meelat ta tambaya.
"Ba wancan Dan mai karfin bane yajamin!"
Ta bata amsa tana tab'e baki,
"Ban gane yaja miki ba, miye had'aku?"
Meelat ta kara tambaya.
Dariya Maryam keyi kafin tace "wa yaga qawata a gaban Mr Emma tana rokon shi"
"Ke ai wallahi bama zani ba balle ya samu damar fadamin maganar banza irin yanda ya saba yima wadanda ya raina"
"Kingani koh aina fad'a miki da bakiyi mata ba to tsaf zata murje idone tace bazataje ta roke shiba"
Cewar Meelat,
"Lah wai Maryam dan Allah kin min da gaske? Kai masoyiya allah ya jefa min ke a cikin aljannah"
Ta fada fuskarta na washe wa,
Knock knock karar glass din window din gefen mai zaman banza,
Dukan su suka maida hankali a wajen,
"Kungani koh wallahi masu motar can ne ai dama nace muku mu suke bi gashi kuma kun gani๐คท๐ปโโ๏ธ"
"Kisan yanda zaki damk'o mana wuyar koma waye zuwa cikin shagon nan mu tatse mishi yan canjin dake jikin shi, Allah dai yasa ba yaron oga bane aka aika ya biyo bayan mu, aiko da na mishi rashin daraja wallahi"
Inji Meenal,
"Kee a wani dalilin zakice in kula shi bayan yanzun kika gama tunamin cewa ina da nawa mijin auren a hannu, in haka ne ai kece yan zun for sale"
Zuge glass d'in gefen nata Maryam tayi zuwa k'asa, kafin tace komai wanda yayi knocking din ya riga ta da cewa,
"Assalamu Alaikum yan mata kuyi hakuri please Allah yasa dai ban katse
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 49 Chapter of 92