Share this page
na taya maka,Gaskiya dai ku canza hali dan Wannan ba halin musulmin kwarai bane atoh ina ma amfanin kwaɗayi!, Allah ma shedane Wannan kwaɗayin naku ba'a wajena kukayo gado ba can dangin iyayen ku mata kukayo gadon shi ku anayin gadon abun arziki ku kuna na tsiya" Bai tsaya jin karshen zancen taba ya cika hannun shi da gyaɗar sannan ya mike dan yasan kaɗan daga cikin aikin hajiya ne yanzun ta nemi tara mishi jama'a kamar ba itace ta bashi gyaɗar kan radin kanta dan ganin damanta ba. "Au to dan na fadi gaskiya shine kaima ka mike wato ga jarabab biyar tsohuwa ko wani mara mutunci a cikin ku dana fara mishi magana saiya tashi ya bani waje, To wallahi nikam da bakina ko uban ninku basu isa su hanani magana ba, Dan ma Allah ya taimakeni nayi tsaye akan ku da addu'a da da nefa yanda na soya gyadar nan haka zatayi batar dabo ko sama ko kasa ban kara ganin ta kun biyo dare kun min fashin ta sai dai tashin zance, To shikenan kuma sai ace bazanyi magana akan gaskiya taba! Da zarar nayi laku²fa cutata zakuyi su kuma iyayan ku da shegen son y'a'ya ko kunyi ba dai² ba basa iya saku a daki su ladafta sai suyi ta sanyi² kamar ma tsoron ku suke, Kuma idan ka fitan ka kiramin shima daya gagaren duk kuzo ku koma gaban iyayen ku, ban iya wahala biyu nayi na iyayen ku yanzun kuma gaku to bazaku karasa tsofar dani ba Haka kawai kuna bigewa da zuwa hutu kuna zuwa kuna taramin taron mutane a gida kun maida min gida kamar gidan baitil mali to gidan nan dai na mijina ne bana iyayen kuba," Haka taci gaba da sababi itafa idan jidalin ta ya motsa ko dogon numfashi bata shaka saita gama tayi ta numfarfashi, Kuma fa duk wannan fadan da take Sadeeq din da take dashi tuni ya dade da barin mata falon. Shiko *MAI JAMA'A* koda ya fito majalisar baiyi mamakin rashin ganin *HAFSA* da *NUSAIBA* ba dan yasan daman bazasu bari ya same su a wajen ba sai dai yaji bakin cikin yanda kullum suke zubar mishi da kima to wallahi basu kaɗai ba harda ma sauran yan wahalan duk saiya shata musu layi tunda basa tashi yin jakancin faɗar su sai a kofar gidan nan tunda duk doɗaɗɗiyar kwalwa garesu, sun ma maidashi wani ɗan iska tunda duk wanda yaga suna faɗar idan ya tambaya cewa za'ayi akan shi suke faɗar. Sallama yayi Sannan ya koma kan kujerar da take dimun da iman a matsayin tashi ya zauna, Karfa kuyi zaton majalisar irin ta yan zaman sa idon unguwane! Inah tashi majalisar ta ban²ta da tasu domin da yawan mutane ma *FADA* suke ce mata kamar yanda yake rubuce a jikin shagunan da suke laye a kofar gidan na Hajiya Innah wato *FADAR~MAI~JAMA'A* Hatta da shagunan idan kwatance zakayi sai ka Kira *FADAR* Kafin a gane, Manyan Shaguna ne da suka kunsa Shagon ɗinki na Mata da mazan ƴan gayu, Shagon aski na maza masu ji da kansu, Shagon saloon na ƴan matan da sukejin cewa sun isa , Shagon kayan masarufi,Babban Restaurant, Shagon karshe shine na kallon kwallo domin shi yafi sauran girma dan haka wajen kamar karamar kasuwa haka yake cika da mutane a koda yaushe, Sai kuma gefen da aka ware na buga table tennis dasu snooker , Gaskiya dai yanda aka tsara wajen dole ya burge mai kallo dan haka wajen bashi rabo da matasan yan gayu mata da maza. Kuma duka shagonan mallakin *ABDUL-KHAREEMU* ne jikan Hajiya Innah. Wato *Mai Jama'a* Ita kuma fadar tana daura da shagunan ne. Babbar falo ne sai dai ba ginin bulo aka mata ba anyi amfani da Aluminum da glass mai karfi ne wajen ginata sannan aka zagaye ta da burglary dan bata kariya ga yara masu kiriniya ta yanda ko sun jefa dutse bazai cimma glass din ba balle ya fasata, Hajiya dai tace fadace ta magulmata domin dai indai ba sun zuge glass din bane to kai na waje komin kwa²rka baka sanin wake ciki amma su duk Abunda ake a wajen a kan idon su yake faruwa. Sannan an kawata cikin ta da duk wani abun bukata da za'a iya samun shi a falo na alfarma tun daga kan Kujerun zama, Kayan kallo fridge don sanya² abubuwan sha kai hatta da labulayen da aka zagaye falon dashi abun kallo ne gaskiya dai an gyara wajen dai² da zamani, Duk da falon ya kasance majalisa ta maza domin duk wani abu na matasa idan ya tashi anan sukeyi tun daga kallon kwallo zaman meeting dama duk wani Abu mai mahim manci daka iya tasowa, Sai dai ita wannan Majalisar ba maza kadai take dauka ba harda zafafan yan matan dake ji da kansu, Wasu yan makaranta ne anyi karatu tare, wasu kuma yan wahalan fataucin soyayya ne da suke fakewa da kawo dinki ko saloon ko zuwa cin abinci dan suzo su gwada sa'ar su ko tarkon su zai kama kurciya, wasu kuma yan matan sauran yan majalisar ne wasu ko zuwa kawai sukeyi asha hira su wuce, To haka dai wajen yake kullum baya rabo da mutane ko uban gayyar na gari ko bashi akwai masu kula da Fadar shi sukuma masu shaguna suna harkar kasuwancin su. Haka dai suka kare zaman wannan rana ba tareda wani daga cikin su ya tada maganar abunda ya faru tsakanin *hafsa* da *Nusaiba* ba. *Wannan kenan* ******* Cikin garin zaria *Unguwar Malamai* note(nasa sunan unguwan ne kawai bawai dan akwaita ba). Unguwace ta manya kuma fitattun malaman da akeji dasu a cikin garin na Zaria, Gidan *malam Almustapha* wanda mafi yawan mutane sukafi Sanin shi da *Malam Almu* yana daya daga cikin manyan malaman da suke rayuwa a cikin unguwar tsayin shekaru, Babban gidane wanda suka gada tun fil'azal dan haka gidan ya kasance babban gidan daya kasu kashi² kowa da sashen shi. *MALAM ALMUSTAPHA*(Baba Malam) shine babba dan haka ya kasance shine matsayin uba a wannan gida tunma kafin gushewar iyayen su, Yana da mata biyu da yara mata 8 da maza 12 duk da kasancewar shi babban malami allah bai jarab ceshi da yawan aure² ba domin duka matan shi biyu auren zumunci ne uwar gidan shi mai suna *Ameena* yaran gidan ke kiranta da (innan mu) ita din yar uwar shice ta jini da mahaifinta dana malam iyayen su daya, Sai matar shi ta biyu mai Suna *Hadiza* (dije) itama dai yar uwace ta fannin uwar su mahaifiya. Malam yana da kanni 4 maza 2 mata 2 maibi mashi namiji shine *ADAMU*(Baba Adamu) Shima babban Malami ne a cikin gidan yake zaune da matar shi daya da yaran shi 3 maza 2 mace 1 sunan matar shi *MURJANATU* (Aunty Murja) Bashi da yara da yawa saboda baiyi aure da wuri ba , Mai bin shi ita kuma mace ne *AISHA*(Momin Abuja) ita kuma a Abuja take aure dan haka ita da iyalanta can suke zaune, Sai *Mukhtar* (BabaAuta) Shi kuma professor ne yana karantarwa KASU shima anan cikin gidan yake zaune da matar shi 1 *Hauwa'u* Jidda (Momi Hauwa) da yaran shi 8 maza 5 mata 3. Sai *Fatima*(Momi Zahra) itace autar su ita kuma tana Auren wani babban dan kasuwa ne a Kano, Ahalin malam duk da kasancewar su manyan malamai basu zauna haka ba suna Noma kuma suna hadawa da kasuwanci dan haka suke da rufi asiri sosai. Sai dai kuma Allah yayi malam Almu cikin mutane masu wata irin baud ɗaɗɗiyar hali sannan Allah ya mishi wata irin kwarjinin da mutane ke shakkar shi yana da kwarjinin da ba kowa yake iya hada ido dashi ba, Kai hatta da matan shi na aure suna bala'in tsoron saɓa mashi daga su har yaran su, Ya kasance shi mutum ne mai magana guda 1 inyace eh to eh din zai tsaya akai ko tama saura daɗi ko kartayi su suka jiyo, Malam mafaɗaci ne kwarai domin da zarar ya shigo gida duk wani mai guntun kiriniya dole ya natsu dan tun kafin ya iso gyarar muryar shi ke isarma na cikin gidan isharar gani nan tafe, Sannan bai yarda ya shigo gida ya iske matan shi zaune da yaran su a tsakar gida da sunan suna hira ba, yanzun zai Kama sababi cewa "sun tasa yara a gaba suna koya musu gulma da tsugudidi" Dan haka ko zaune suke da zarar sunji motsin shi kowacce zata shige daki kota Kama wani aikin, Hakan kuma bashi zaisa su tsiraba dan saiya duba ko ina duk inda ba'a share da kyauba ko kuma ya dawo ya cimma ba'a kammala abinci ba to aiko ya dunga surfa faɗa kenan, shi dai haka nan Allah ya yishi ya iya fada harda marar dalili dan wallahi ko kajin gidan suka dameshi da kyar kyara ko cara sanyawa yake a tattare su a yanke, Sai dai kuma duk wannan halin faɗar nashi Allah yama malam son jama'a yana kuma da farin jini wajen al'umah kodan yanda yake kyautata musu, yana kuma da kyauta sosai dan haka gidan shi ko yaushe basa rabo da baki gashi dason zumunci yana son yan uwan shi sosai alkhairin shi bai tsallake kowa ba harda jama'ar unguwa, Malam yana da wata akida wacce kusan kowa yasan shi da ita , ta kin ilimin boko sosai yake nuna kyamar shi ga duk wanda ya karkata ma ilimin boko da akida irinta nasara duk da cewa ilimin bokon ta yawaita sosai, Dan haka ya zamana tun daga kanshi har zuwa kannen shi basuyi karatun ba,sai dai ya yarda ya kashe ko nawa ne ya tura su zuwa kasashen musulunci domin nemo ilimin islama, ba'a samu sassauci ba har sai da Malam Adamu yayi tsayin daka wajen nunama malam cewa shima fa ilimin bokon yana da ranar shi domin shi *Malam Adamu* ba mazauni bane mutum ne mai yawace² gari² kasa² yake zuwa yawon neman ilimi fitan da yakeyi ne yasa ya fahimci a wannan rayuwa ba ilimin islama kadai mutum yake bukata ba ya dace a nema harda na zamani dan haka ya fantsama neman ilimin, Sanda yayi wani dawowa ne ya samu malam da maganar dakyar dai ya shawo kanshi ya yarda cewa ya yarjema yaran shi maza da kanin shi *Muktar* su fara zuwa shima iya secondary kadai da kyar ya yarda matan suma aka sanya su da sharaɗin primary kawai zasuyi kuma hakan ce ta kasance, badan malam yasoba yanaji yana gani *Adamu* ya kai yaran makaranta. A haka har wasu daga cikin su suka kammala aka aurar da matan mazan kuma shida kanshi ya rarrabasu zuwa kasheshen musulunci domin karo ilimin addini, Duk da Ana ganin cewa malam yayi sauƙi a lokacin amma koda ya tashi aurar da Autar su da kuma yaranshi mata da suka kai aure a lokacin bata canza zani ba, kamar yanda kowa yasan cewa baya bada auren yaran shi mata ga kowa sai yayan manyan malamai ko Kuma wani babban mutum ko yan kasuwa shi dai har yanzun bai yarda ya hada zuria da ahalin boko zallah ba, dan har yanzun baya shan inuwa guda da ƴan boko. Sannan kuma duka yaran shi dana yan'uwan shi dake zagaye dashi shine yake zaɓa musu mazajen aure kedai sai dai ace miki (ki shirya kina da baƙo) ko ya miki ko bai miki ba wannan ke kika jiyo domin dai wannan zuwan da baƙon yayi bazai kara dawowa ba sa ranar aurene zai biyo baya, maganar fahimtan juna bayan auren kwayishi a gidan ku. Sai dai adalci daya da yake musu shi baya tallan yaran shi ma kowa haka kuma baya fidda ma yarinya mijin aure sai ya jira ta samu manema akallah 3 sannan shi da kanshi zai bincika wayafi nagarta a cikin su wanda ya ciri tuta shi zaiba sauran suyi hakuri, Haka kuma shi baya bada auren mace kamar sadaqa a'ah duk wani Abu na neman aure sai yasa kayi shi kuma in an kawo wanda bai mashi ba zaisa a canza, sai dai bai yarda da zaryar zuwa zance ba, haka kuma baya amsan karamin sadaki domin yana kafa hujja da cewa y'a'yan yan boko ma da sukayi karatun zaman duniya basa aurar da yaransu da arha ballantana shi da zai aura maka mahad daciyar Alqur'ani mai tsarki. Sannan kuma shi a tsarin shi baya aurar da yaranshi ma talaka domin dai yace "bazai saida akuya ta dawo tanaci mishi danga ba" dan haka saiya duba mai rufin asirin da yasan zai iya rike mishi ɗiya da kyau kafin ya bada auren ta. Sai dai yana rangwame wa yaran shi maza shi namiji yana da damar auro yarinya komai talaucin babanta idan ma ya Kama shi malam din da kanshi yakan dauki nauyin komai da iyayenta zasu mata na kayan daki amma fa banda *y'ar boko*! Hakan kuma ba iya kan ƴa'ƴan shi ya tsaya ba harta da ƴa'ƴan yan uwa ko makota in uba bashi da hali shi yake tsayawa a matsayin waliyyi haka kuma shi zaiyi ma yarinyar kayan ɗaki, Shi dai Allah ya sani har gobe baya shiri da duk wani dan boko. Sai dai duk wannan taka tsan² din da yake wajen ganin ya katange iyalanshi daga shiga sabgar boko Abunda bai sani ba tuni kannan shi biyu sunyi zurfi ƙwarai a cikin shi, domin sun gane cewa tafiyar tafi armashi idan ka haɗa ilimin duka biyu domin sun faɗaɗa karatun su sama da iya sacandiren dashi Malam ya sharɗanta musu , Dan haka shima Mukhtar ya dage sosai ya maida hankali wajen karatun shi duka biyun, kuma acan wajen yawon neman ilimin nashi ne ya haɗu da *Hauwa'u*Jidda ita din ta kasance yar babban gidace wadanda suka jiku da ilimin boko da islama soyayya mai tsafta suke gudanarwa a tsakanin su ba tareda Sanin malam ba, burin mukhtar bai wuce ya dawo gida ya gabatar ma Malam da jidda ba danya nema mishi aurenta. Bai taba zaton neman auren Jidda zai zamo matsala tsakanin shi da malam ba domin tun tasowar shi yasan cewa malam yana son shi yana son duk abunda yake so domin shi Mukhtar kallon uba yakema yayan shi yana matukar girma mashi, Sai dai ya manta da ra'ayin riƙau irin na Malam akan yan boko, ga kuma laifi na 2 dashi Mukhtar din ya aikata nayin karatun bokon mai zurfi batareda Sanin malam ba. Bayan da Mukhtar ya kammala karatun shi kasa dawowa yayi saida ya jira ya'yan shi Adam dan so yake suna komawa a fara maganar auren shi da Jidda dan haka tare suka dawo gida harma da sauran yaran. Sai dai Abunda basu saniba shima malam a gefen shi ya fara nemawa dukan su biyun aure domin zuwa lokacin ya fara damuwa da rashin auren *Malam Adamu* domin kullum idan ya mashi maganar aure sai yace mishi "ba yanzun ba" dan haka ya gaji tare zai haɗasu ya aurar dan malam Adamu zuwa lokacin ya wuce a kirashi tuzuru dan ma yana da rufin asiri shi yasa girma bai nuna sosai a jikin shiba. Shiko malam Adamu a inda yake yayi kafuwar da yake tsoron ya matsa daga wajen yabar dukiyar shine saboda rashin amana da tayi yawa a wajen al'umah da kaɗan² yake so ya kwaso arzikin daya Tara acan idan ya dawo gida gaba ɗaya sai yayi aure dan duk yarinyar da yace zai aura yanzun zai shiga hakkinta da yawa tunda yana dadewa bai waiwayi gida ba. Ɗiyar wani babban Malami malam ya fara nemawa Mukhtar ba tare da shi ya sani ba, shi malam a wajen shi bazata ya shirya yi musu da sun dawo sai aure sai kuma gashi bayan dawowar su kafin malam ya gabatar musu da nashi bazatan su sun bashi nasu. Domin shi mukhtar da kanshi yaje ma malam da zancen Hauwa'u a matsayin matar da yake son aura, Malam yana son Mukhtar sosai a cikin kannin shi wannan dalilin shiya hanashi kawo mishi maganar murjanatu anashi zuciyar ya kudura cewa idan aka gama maganar jidda daga baya zai bijiro ma mukhtar din da nashi zabin daya mishi koba komai ai Namiji mijin mata 4 ne dan haka ya taushi kanshi. Abubuwa basu rikice ba sai da yasa a mishi bincike akan ita Jidda ɗin yar wasu ahali ne? Ranshi ya baci sosai ayayin da waɗan da ya wakilta akan su mishi bincike suka kawo mishi rahoto iri daya. Duk da yarinyar ta fito daga babban gida sannan sun bincika bata da wani nakasu tana da ilimin addini mai zurfi sai dai fa ita da ahalinta dukan su alhazi bokone domin binciken su ya nuna musu a kasar waje tayi karatunta na gaba da secondary saboda ilimin da Allah ya bata yanzun haka dai ta dawo kasane a matsayin likitan mata da ƙana nan yara. Ran Malam ya baci sosai taya mukhtar zai aikata haka? Ya rasa yarinyar da zai nema sai yar boko ita nata bokon ma tafi karfin tayi shi a gaban iyayenta har sai ta ketare ƙasar waje! Koda yake ai uwa batayi gudu yarta ta rarrafa ba waye zaice bai san ubanta *ABDUL~KHAREEM* Ba? Mutumin da kowa yasan rikakken dan boko ne naƙin ƙarawa shida ahalin shi! Kai ina ai wannan zagi kawai *Mukhtar* yake so yaja mishi wajen mahassada dan haka wanna magana ma bamai yuwuwa bane kuma ba a gidan shiba!. A wannan rana malam yayi faɗa kamar ya ari baki baiyi kasa a gwuiwa ba ya nemi ganin *Adamu* yace mishi ya taho tareda *Mukhtar* bayan sun iso duk son da yake ma *Mukhtar* ajiye shi yayi gefe ya mishi kacha² har Adamun bai shaba a wanna rana, karshe kuma ya fada mishi ya rufe maganar wata Jidda a cikin ahalin shi anan yake fada musu dama ya fara nema musu aure tun kafin dawowar su. #Share please # #My first novel ina fatan zaku soshi🤍 #Ummiee~Zaria #25/4/2023 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_# My first novel *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._ *MOM TEEMAH* *AISHA HUMAIRA* *JIKAR HAJIYA* *CHIDA* ```Page 3 *Sosai hankalin *Mukhtar* ya tashi dan ba karamin so yakema *Hauwa'u Jidda* ba, tunani yake akan taya²ma zai tun kareta yanzun yace mata *ya fasa auren ta!* Kai ina gaskiya da sake. A takaice dai ankai ruwa rana sosai kuma rayuka sun baci saida *Mukhtar* yayi kamun kafa sosai wajen sauran iyayen su da suke raye da kuma manyan Malaman da yasan Malam yanajin nauyin su sannan da kyar suka shawo kan Malam. Sai dai kuma Malam yayi fushi sosai dan tunda yake da kannin shi bai taba kafa musu doka suka ƙetare ba, sai a wannan karan da *mukhtar* yake shirin ɗauko mashi yar boko ya kawo mishi cikin ahalin shi a matsayin suruka dan haka gaba ɗaya yaji ya baya ra'ayin ta, tun yanzun tana neman shiga tsakanin shi da kannan shi tana son raba haɗin kan dake tsakanin su *taya ma zai sota?* Ina har abada..... Dan haka ya kafama *mukhtar* dokan cewa bazai matsa ko ina da sunan zama ba dole anan cikin gidan zai zauna, To shima dai baijaba tunda har yasamu an shawo mishi kanshi ai komai zai biyo baya mai saukine dan haka cikin kankanin lokaci saboda tsoron kar zuwa gaba Malam ya kara botsarewa aka tada ginin da Amarya zata zauna anan cikin gidan kamar yanda malam ya buƙata, anyi ma gidan gyare² sosai ta yanda ya nuna lallai anma bikin shiri na musam man, kowa na ɗaukin wannan biki amma banda Malam domin komai na neman auren ma zame kanshi yayi ya wakilta *Malam Adamu* haka dai akaci gaba da shirin biki ba yabo ba fallasa domin kowa taka tsantsan yake karyama Malam laifi. Allah da ikon sa an daura aure lafiya amarya ta tare a dakin ta. Kowa yayi tunanin cewa bayan aure Malam zai sauko to ya sauko ɗin domin bai rage kanin nashi da komai ba, sai dai tsakanin shi da *jidda* ba wani abunda ya canza tsakanin ta da *Malam* gaisuwa ne kawai bayan shi baya shiga sabgarta bawai ƙiyayyarta yake nunawa ba amma dai gaskiya kowa yasan cewa baya wani yinta, Da farko yaso ya hanama iyalan shi shiga sashen ta saida *Mukhtar* ya nuna ɓacin ranshi sannan ya barsu suke mu'amalan tar juna, Itama tunda ta gane cewa ƴa'yan mijin nata baya yinta take taka tsan² bata shige mishi, Ko gefen matan shi bata zuwa indai yana gida sai dai su suje mata sannan rashin jituwarta da *Malam* baisa yaran gidan sun rainata ba, sai ma komawa shashen ta da wasu daga cikin su sukayi suka tare acan. Malam yasa ido ko zaiga wani sauyi na tarbiya daga wajen yaran sai dai baiga hakan ba dan dole ya kauda idon shi akan su. A haka rayuwa taci gaba da tafiya har zuwa sanda *Allah* yaba Jidda ciki haihuwar fari ta samu namiji aka sa mishi sunan mahaifin su Malam wato ~{{ UMAR FAROUQ }}~ haihuwarta na biyu shima Namiji ta kara samu aka sa mishi sunan Malam ~{{ MUSTAPHA }}~ na ukun shima Namiji Allah ya bata tayi zaton ko za'a mata kara a sanyawa yaron sunan Mahaifinta domin tana da cikin Allah yama Baban ta rasuwa, Tanaji tana gani haka yaro yaci sunan ~{{ ADAM }}~ taso ta nuna bacin ranta yan uwanta da mijinta suka bata hakuri, Koda ta kara samun wani cikin Allah

Chapter 2 of 92