Share this page
jagora zuwa kujerar da aka tanada domin su, lallai bikin Mai Jama'a ake dole kaga taron jama'a gaskiya tayi farin ciki sabida ganin mutanen da ke wajen da yawa daga cikin su wasu sunyi shekaru basuga juna ba wasu mate dinta ne na school wasu kuma childhood friends dinta ne da suka dade basuga juna ba sauran jama'ar kuma kunsan dan wa sukazo ita har mamaki take yanda akayi mutane sukaji labari har suka hallara haka, gaskiya dai tayi farin cikin ganin yanda mutane suka taru saboda su musamman yanda yayyen ta maza suka nuna ma kowa yanda suke ji da ita duk da lura da uban gayyar yanda yake wani jajjanye ta daga cikin su. Sai fatan allah ya maida kowa gidan shi lafiya ameen. Bayan Bude taro da addu'ane kuma aka ba iyaye dama wajen tofa albarkhacin bakin su, kuma alhmadulillahi sunyi jan kunne sosai kuma sun fadakar unyi bayani sosai akan aure, hakkin miji akan mata, da kuma hakkin itama matar akan mijinta wanda baba Adamu ne yayi wannan jan kunnen sannan kuma yakara jan hankali akan mahimmancin hakuri da abokin zama daga nan akaci gaba da shagali, kai gaskiya dai taron dinner din ya kayatar anci ansha kuma anyi rabon abubuwa kala²a wajen bayan an rufe taro da addu'a ne kuma aka fara watsewa dan karfe 10 dai dai aka tashi, masu wayau dai basu yarda sun bar wajen ba saida sukayi sallan ishsha'i, Da yawa daga cikin abokanshi da bata san suba ya gabatar mata dasu wasun su sun mata kyauta a wajen yayin da wasu sukace sai sunzo gida, Sun daiyi sallama da wadanda zasu koma garuruwan su wadanda sukazo daga nesa, Sai dai tana kasa tana dabo domin tun zuwan su wajen take an kare da tawagar wasu mata wanda ko shakka babu gasan suna cikin gayyar mai Jama'a kuma ko yanzun haka da mutane ke watsewa su suna ciki, tun dazun taso ta tanka amma dai ta danne to yasin bata barin wajen nan ta bar mijinta cikin kuraye duk da tasan halin kayanta Amma kula da kaya yafi ban cigiya, Ba tawagar kowa bane face tawagar Hafsat ita din kuma tsohuwar budurwar AK ce tun zamanin yarinta nasan baku manta da ita ba mijin data aure mutuwa yayi tun bayan data gama takaba kuma take ta faman bikon AK din sai dai kun san mai hali, kafin ta ankara kuma kawai sai labarin d'aurin aure taji har yanzun kuma bawai ta dena son AK din bane a wautar ta wai ko a mata ta biyu ne sai ta shiga gidan Mai Jama'a inba batar basira ba shidin dabai aureta tun tuntuni ba wai yanzun ne zai aureta, " Lallai dani suke wasan to wallahi sai naci musu uwa kana inbi da ruwan kanwa maganin kwarnafin ciki, kuma shima Zai fadamin dalilin da yasa yayomin gayyar karuwai," Tunda suka fito take cika tana batsewa, tayi² ta danne kishin dake yunkuro mata amma abun yana neman ya faskara......... Matsowa kusa da ita yayi, "meya sameki?"ya tambaya ganin yanda take ta wani kunbure kunbure, " Ai dole kace meya sameni tunda kayomin gayya harda na karuwai wajen tarona," "Ke waye ya miki gayyar karuwan?" Tura baki tayi bata amsa mishi ba "To bari kiji ni ban gayyace suba kuma ita Hafsan da kike magana a kanta in baki manta ba tun baki da wayau nike tare da ita kin san da ina ra'ayin ta daba wannan maganar akeyi yanzun ba," "To da baka ra'ayin ta basai ka fada mata ta fita a sabgar kaba, Shine kuma dan maita duk inda kake haka zata dunga binka Kamar karya to wallahi nikam a kiyayeni idan da nayi shiru yanzun ba abunda zai gagareni," haka nan ta dunga warwarewa tana yab'a maganganu gaba daya kishi yabi ya rufemata ido, kai jama'a gaskiya kishi jidaline shi dai daga karshe ido ya zubamata dan ba amfanin yin kace nace da ita a yanzun saida ta gaji dan kainta tayi shiru, ruwa yasa aka miko mashi shi kuma ya budemata ya kafamata ruwan a baki wai tasha, Kuma da tasha taji saukin tukukin da zuciyarta ke mata, "Nagode" Tace dashi bayan ya cire gorar a bakinta, Aunty hassana ce ta karaso inda suke ta cire hannunta a cikin nashi tana mishi tsiyar kodai su wucene shi zai wuce da amaryar shi da kanshi? AK fa ba kunyace ta wadace shiba Dan haka da sauri ya amsa mata "Eh aunty kuje kawai tunda dama ai da yawa sunje sunga daki kinga gobe sai suzo suma amaryar sallama kafin su wuce" " Kai 😳" ta fada tana zaro ido fincike hannunta dake cikin nashi tayi da gudu ta koma bayanta ta b'uya daga bayan Aunty Hassanan ta leko kanta tana fadin "wallahi ban yarda ba," Dariya jama'ar dake wajen sukayi shiko yasin ko a jikin shi sai ma kara matsowa da yayi yana neman kamota "Dan Allah kizo idan na sallami bak'i sai mu wuce tare" wata katuwar harara ta watsa mishi tana mak'e kafada alamar bata yarda ba, " Fine " shima ya fada yana dage kafadun shi wani shegen kallon kasar ido ya bita dashi alamar zaki shigo hannu yarinya, Ita kuma ta mishi gwalo tana murmushi, hannun shi manuniya ya nuna zuwa kirjin shi alamun "ni koh?" Had'e hannu tayi alamun ban hakuri 🙏. Motar da Musty ya d'auko su a ciki ita ta mai dasu sabanin d'azun da suka taho su hudu a cikin motar yanzun kam sun kara yawa, ita da Aunty hassana da Maimoon a baya sai Maryam da Sultana ne a gaban motar bata san ko miye sultanar take nunama Maryam din a waya ba kuma Faisal ne kejan motar, A haka suka jera tare da sauran motocin suna tafe suna hira har zuwa gidan Hajiya wanda yake matsayin gidan auren Meenal din a yanzun... Koda suka isa sun samu da yawa daga cikin motocin da suka kawo mutane sun wuce sai tsiraru wadanda suka tsaya tarbar amarya, Bayan sun faka a harabar gidan Hajiya ce da kanta ta fito ta tarbe su da sabuwar butan ta wanda ta ciko shi da ruwa ta fito dan haka saida ta umarce Meenal din da tayi alwallah da ruwan cikin butan, bayan ta idar Hajiyar ce ta k'ara rike hannunta sai da ta zaga da ita kaf sashen gidan iyayen ta su Baba Usman suka sa ma auren albarka kafin suka nufi sashen Meenal din, Sai da Hajiyar tayi mata umarni da ta shiga da kafar dama bayan sun gabatar da addu'o'in a kofar shiga sashen, haka suka rakata da addu'ar zaman lafiya, kwanciyar hankali, da kuma zuria masu albarkha, sun kumayi addu'ar yanda suka kawota cikin aminci ubangiji yasa mutuwa ce kadai zata fiddata daga gidan aure ta, Basu zauna a falon ba kai tsaye sama suka haura da ita zuwa dakinta suka mata masauki akan gadonta, Itadai fuskarta tana lullube dan haka bata samu damar karema gidan kallo ba, a bakunan mutane takejin yanda suke zuzuta kyawu da tsaruwar da gidan yayi, kun san dai yanda akeyi in ankai amarya dan haka itama mutane sukaci gaba da shigowa kallon ta duk da kasancewar fuskarta na rufe wasu sukan mata sallama akan sai sun dawo suna, wasu kuma sukance sai sun shigo gobe, a haka dai yawancin mutanen suka watse, Dan baba Malam yace bamai kwana ita dai taso ace sun kwana amma ba yanda zatayi tunda babane ya yanke hukunci itada tace bazata tare yanzun ba karshen magana dai to gashi har sun kawota sun barta na bakin AK, Hafees ne ya shigo dakin da sallama karasowa kusa da ita yayi "matar Ina wayata?" Da hannu ta mishi nuni da Sultana ba tareda tayi magana ba, shima baija maganar da tsayi ba ya juya inda Sultana din take mikewa tayi tace "muje waje wayar tana cikin jakata a mota," Oh ni y'asu wai ita zasu maida karamar yarinya da zata fita shine tama Maryam signal itama ta rufa mata baya kujifa Dan sun raina ta wai a tunanin su wayau sukama Meenal irin bari su gudu sai dai inji shiru din nan ni wallahi dariya ma suka bani, bayan sun fice ne Maimoon ta rufe kofar gyalenta ta cire sannan ta matso kusa da Meenal din, "kawata" ta fada tana mai mikar da ita tsaye daga zaunen da Meenal din take, lafayar dake jikinta ta warware ninkeshi tayi ta sashi cikin wardrobe, "tashi kiyi wanka na hada miki ruwa a ciki,"ta fada yayinda taci gaba da kakkabe² tana kara kimtsa dakin ta kara feffesa room freshener dan sun kunna turaren wuta dama tun kafin su Meenal su shigo, Mikewa tayi tana mita "Nidai gaskiya gaba daya yau kun takuramin kun mai dani Kamar wata agwagwa, haba bini² kadan kuce inyi wanka, dazun nan fa nayi wanka!" Barin abunda takeyi tayi ta juyo tana kallon Meenal din, "To wallahi sai kinyi shi kinjima na rantse kin maci uwar rainin wayau wato mun miki mai wuyar ai Bari kimin iskanci......." " Eh din to me yasa baku barni a gida ba" rike baki tayi tana kallonta da mamaki, Kayan baccin da Moon ta ciro ta ajiyemata akan gadon ta mika hannu na kwasa, Juyawa fayi cikin bayin tana tafe tana murguda mata mazaunai, "Yar rainin wayau in zakiyi murgud'e² ki sai ki jira har shi ya shigo dan nidai in kin min kinyi ne a banza" wanka sosai tayi da ruwa mai dumi dan wallahi gajiya takeji sosai a jikinta dan baccine taf cike da idonta, bata fito ba saida ga dauro alwallah, Koda ta fito ta samu Moon ta canza zanin gadon ta sanya wani kayan data fito dasu a hannunta Moon ta amsa sai da ta feshesu da turare sannan ta ninke ta adana, Gaban mirrow ita kuma Meenal din ta karasa ta mutstsuka mai sannan tadan bi fuskarta da hoda yar kadan dan ta kashe maskin man, "Baza kiyi kwalliya ba?" Ta tambaya " ke dan allah rabani da wani kwalliya da daren nan gado fa zan hau bacci nikeji" bataja da tsayi ba ta mika hannu wajen turarukan da suke laye akan mirror din taci gaba da fesa ma Meenal bayan ta tabbatar komai ya kammala gyalenta ta yafa, "Sister bari mu wuce dare yayi yau a unguwar malamai zamu kwana" shiru tayi ba amsa tana binta da ido, dariya tayi "Bari in kara miki tuni wallahi kazar mu! kazar mu!! Kazar mu!!! Kinji sau uku na maimata koh to wallahi ki adana mana ita da kyau, Dan ba yafiya tsakanin mu da wannan kazar tunda allah yasa muna da rabon ganin ranar biyan bashi to a biya a huta, Yauwa kuma kiji tsoron allah banda rowa, kin daiji wa'azin da malamai sukayi akan hakkin miji akan mata Dan haka yasa kikaga na canza zanin gado dan wancan yan ganin amarya sun dakuna shi, Ubangiji Allah kasa nan da wata Tara mu dawo taron suna Ameen ya rabbi " ta k'arasa addu'ar tana shafawa a fuska, "Asha amarci lafiya kidai tausaya ki daga mishi kafa kin san dai saurayine ba sabawa da buga wasan yayi ba sai kin bishi ahankali," "Kutmelesi amma wallahi gaba d'aya kin gama dani dan wulakanci nine ma zan d'aga mishi kafa? Gaskiya allah saiya sakamin wannan katon sharrin da kikamin, ke wuce ma ki tafi nagode allah ya huce gajiya, kuma sai Allah ma ya saka min, Kai gaskiya kin kwareni wainice zanbi tsohon tuzuru a hankali to yasin kofar dakin ma zan rufe inba hakaba nasan tabbas gobe a asibiti za'aci gaba da zuwa ganin amarya muguwa dake kawai" Dariya ta fashe dashi bata kara kulata ba ta bude kofar ta fita Hijab Meenal ta zira ta take mata baya domin gidan yanzun tsit yake ba jama'a a side din amma tanajin hayaniya a farfajiya kilan angwayen ne suka dawo, Saida ta taka mata har zuwa bakin kofar falon kasa, ta bude kofar kenan najiyo muryar Mai Jama'a, Ai da gudun besfa wallahi bibbiyu ta dunga tsallake benen Allah dai ya tsare batasha kasa ba, Tana shiga daki ta maida kofar ta rufe tana numfarfashi, ta baya ta fada gado tana ma Kanta dariya, itadai bata san abunda ya sameta ba tunda aka yi auren nan gaba daya wani irin shakka da tsoron Mai Jama'a takeji, Yana daga cikin manyan dalilan da suka sa ta tsiri wasar buya dashi, wallahi ita kadai gasan kalar jidalin da take hangowa a cikin kwayar idonshi, Nima dai mai rubutun na tausaya mata shi din tun fil azal dama ya lafiyar kura bare kuma yanzun! "Lallai dole in zage damtse dan dazarar ya gane abunda nike ma tsoro na kade har ganye na" Tashi tayi ta koma cikin makewayi ta kurkuro baki sannan ta koma gefen da aka ware domin ganawa da ubangijin al'arshi, Bayan ta idar ta dade akan dadduman tana gabatar da addu'o'in samun zaman lafiya tsakaninta da mijinta sannan nltayima iyayen su addu'a dama sauran musulmai baki daya. Hijab dinta ta cire ta ninke shi sannan ta karasa ta kashe hasken wutar daya cika dakin gabar wanda yake a gefen gadon, saida tayi addu'ar bacci ta shafema jikinta sannan ta kashe sauran hasken data bari tabi lafiyar gado, A gefen mai Jama'a kuwa.... Bayan su Amina sun wuce sadeeq yama magana akan ya sallami duk wata mace da take wajen baya bukatar ganin su, sai da ha tabbatar da sun wuce din sannan ya fito daga mota cikin hall din suka koma da sauran abokainshi, Abunda ya dauremai kai a lokacin shine ganin wajen dund'um wato babu haske a cikin hall din duk da kasancewar ga haske ko ina a waje, "mutane sun gama watsewa ne? " ya tambaya sai dai bai samu amsa daga wajen kowa ba kutsa kanshi yayi cikin hall din dan haka nan hikejin kamar wani abu suke shiryawa, yana shiga yaji fashewar Abu a saman Kanshj a dai² sanda wasu kana nan abubuwa masu kyalkyali suka fara zuba a jikinshi wutar wajen ya dawo. Happy married to you! Happy married to you!! Happy married, happy married, happy married to youuu........... Haka suka hada baki dukan su wajen fada, Bude idonshi yayi baki sake yna kallon su, dan yayi zaton koda zan iske mutane to zasu kasance tsiraru ne a wajen Amma ga mamakin shi sai yaga wajen cike yake dam da mutane kuma mazane zallah ba jinsin mata, wasu daga cikima bai gansu wajen ba sai yanzun, Lallai gayun nan sun shammace shi wai dan fitan nan da sukayi shine har sun canza docoration d'in dake wajen sun kara gyara wajen ga kuma kayan kida a gefe ba wanda akayi amfani dasu dazun ba, gaskiya dai yayi farin ciki matuka domin abun yazomai unexpected Ashe sun san Abunda suka shirya shi yasa da yace musu ba wani event basuja zancen da tsayi ba, Ganin yayi tsaye cak ne yasa suka jawoshi zuwa cikin fili bayan sun umarci DJ daya basu sauti, gaskiya sunyi kokari domin wai wankan ango suka shirya ba tareda sani shiba sun kuma wanke shi da turaruka da tarin kudade, Duk wani turaren da suka san AK na so saida suka yayyafa mishi duk son shi da kamshi saida yaji yana hawa mai kai a yau, ( gaskiya dai anci amanar turare haka akayi ta feshe turarukan makudan kudade a iska, yo suba kudiba balle in kwaso mu raba damasu karatu) Gaskiya kamshi abun sone daure ko turaren durine ki siya ki dunga shafawa kawata, karki yarda ki dunga shiga mutane kina tsami please!!! Sunyi k'ok'ari kuma yaji dad'i ya kuma yaba musu basu bata lokaci sosai a wajen ba sukayi sallama da dayawa daga cikin su suka kuma raka wasu masauki, sannan Yusuf da Sadeeq suka daukoshi zuwa gida, bayan sun iso nan din ma dai bamu samu mutane ba domin dare ya farayi a lokacin, " Yane anan zaku kwana ne ko wucewa zakuyi?" Dariya musty yayi "kai malam me kake nufi? Muda muka rako ango ai kasan bama tafiya sai mun damka ka a hannun Amarya Dan haka muje ciki mutumina ya fada yana kallon Sadeeq," "Wa zaku raka dakin amarya kamar wani yaro?" "Sabon shiga zamu mik'a" cewar Yusuf Gyara zama hayi akan kujerar motan haci gaba da latsa wayarshi yana kallon hotunan Meenal da yasa Hafees ya dauko mishi ita dazun ba tareda sanin taba, Har sun fita sun fara tafiya yana ganin dai sun lura ban biyo bayan su bane shi yasa Sadeeq juyowa Amma ga mamakin shi koda ya dawo bayan motar ya bude ya fiddo ledoji daga ciki, su kuma sauran motar daya hango su hafees a ciki suka k'arasa, motar Maryam kenan Maryam dince ta tambaye su "Ina angon" nuni suka mata da motar da suka iso a ciki, fitowa tayi ta iso inda yike nocking din side din da yake zaune Maryam tayi bayan ya sauke glass din gefen gaishe shi tafarayi "Mai Jama'a Barka da dare ya akaji da taron jama'a? " "Alhmadulillahi "ya amsa dashi "ya naku gajiyan mun godefa ubangiji Allah yabar zumunci ya kuma saka muku da gidan aljannah," Murmushi tayi "zamu wuce ne dama nace sai na jira isowar ka dan allah Ya Abdul duk da nasan ko ban baka amanar kawata ba zaka riketa da amana, sai dai ince kayi hakurin zama da ita sannan ka kula mana da ita ubangiji Allah ya baku zaman lafiya yasa ace gara da akayi" "Ameen ya rabbi" ya amsa dashi yana mata godiya fitowa yayi suka jera har zuwa inda motarta sannan yama sauran godiya suma Musty yama magana akan ya sallami kawayen Amarya a yayin da Maimoon ke fitowa daga cikin gidan, in baku mantaba jin muryar shine yasa Aminatu komawa cikin gidan da gudun besfa. Bayan wucewar su Maryam ne Sadeeq cikin dariya Yake cewa "kai ai da munyi katuwar mantuwa fa a shiga dakin amarya ba tareda kazar amarci ba aiko dai da anji kunya wallahi," Yusuf na dariya yace "Aiko dai yau da amarya ta kullema ango kofa kuma wallahi tafiyar mu zamuyi mubar ango yayi kwanan keso", Shafa kai Mai Jama'a yayi bayan sun kai bakin kofar falon yana murmushi kasa² yake cewa " wai yaushe kukayi wannan cefanen?" Yayi tambayar yana mai tsaresu da idanuwanshi, musty ne yace "Dan Allah Mai Jama'a kadena tsareni da wadannan idanuwan naka to gudun mawar na Faisal ne dan nima na shafa'a shine ya aiki su Ahmad dazun suka siyo kafin mu taso daga wajen can," " nagode" yace yana mai rungume su gaba dayan su, sadeeq ne cikin shashsheka yake cewa "wallahi ji nike Kamar a mafarki wai yau Abokina yayi aure da burin zuciyar shi har gamu munyo rakiya zamu damka ango ga amaryar shi ya fada yana share hawaye, lallai rabon kwado baya hawa sama ko yahau saiya sauko. Congratulations once again friend ubangiji ya dauwamar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaman auren ku," ameen suka amsa dashi baki daya, Shiko Yusuf daurawa yayi da cewa "nasan mai Jama'a yana matukar kaunar Amina Amma tun aurenta na farko sai nayi zaton tunda ya rasata a lokacin shikenan zai kulle babin ta duk da gaskiya na bashi laifi sosai a lokacin domin shi yayi nauyin baki harta subuce mishi, Ashe tukun na dai Wasa farin girki ban kara tabbatar da kaunar da yake mata ba sai yanzun Alhmadulillahi gashi yau komai yazo karshe, shi dama mahakurci akace mawadaci yau Kam ba burin mai Jama'a ne kawai ya cikaba burin mune gaba daya ganin abokin mu cikin farin ciki dauwa mamme," Oh! Oh!! Wadannan abokai sunsa sassan jikina yayi sanyi, nasan masu karatu ma sun yaba! "Kai! Kai!! Kai!!! Dan allah ku cikani kun wani bi kun dukunkune ni Kamar sabon kwabo a hannun kuturu, bayan kun san amaryata na jiran shigowa ta" Dariya suka fashe dashi dukansu sannan suka karasa cikin falon matakala suka hau zuwa sama, falon dake saman sukayi ma kansu masauki sadeeq ne yace ma mai Jama'a Dan allah kirata mu samu mu wuce dare yayi. Ok yace yana mikewa "wallahi nasan tayi bacci yanzun Amma bari in d'auko muku ita" ya karasa fada yana mai shigewa cikin corridor din da dakunan bacci ke jere kofar dakin da yake a matsayin nata ya karasa handle din kofar ya murda da niyyar bude kofar baiyi mamakin jin kofar a kulle ba domin yasan dama za'ayi hakan, murmushi yayi "lallai ma yarinyar nan waima ni ta rufema kofa kai! " Juyawa yayi zuwa nashi dakin Bude kofar yayi da key sannan ya shiga da sallama a bakin shi kofar closet din dake dakin nashi ya bude ya shiga sannan ya danna wani madanni ga mamakina kofa naga tana budewa, shiga yayi sai gashi a cikin wani daki duhun daya rufe dakin ne yasa banyi saurin gane ko inane wajen ba, Da wayar hannun shi yayi amfani wajen haska dakin harya isa inda gadon dakin yake, gefen side drawer yaje ya kunna lamp sannan haske ya haska dakin duk da hasken bamai yawa bane bai hanashi hango kyakyawar fuskar masoyiyar nashi ba dake baccin ta hankali kwance. Gefen gadon ya karasa ya zauna sannan ya mika hannun shi ya sauke bargon data rufe jikinta dashi zuwa kasan cikin ta ya maida bargon sannan yayi amfani da hannun shi guda wajen gyara mata gashinta da suka fita a cikin hulan dake kanta daya zame duk da bawai hulan ya cire bane Amma gashin tadai kusan rabi yana waje, Cigaba da shafa fuskarta yayi a hankali har zuwa kan kananun lips dinta da suke nan fresh, dukawa yayi a saman kanta saida ya manna mata kiss a goshi sannan ya sauko da bakin shi kasa zuwa dai² bakinta yana daura bakin shi a nata ita kuma ta bude idanuwanta suka fada cikin nashi ya kuwa riketa gam da idanuwan shi yana cigaba da kissing dinta a yunwace, motsawa ta farayi alaman tana son tashi, dagowa yayi daga jikinta yana marai²ce fuskar shi, "Yanzun fisabilillah kissing din ma bazanyi shi hankali kwance ba, to tashi muje falo su musty da sadeeq suna jiran ki in mun dawo sai mu daura a inda muka tsaya dan yau No gyangyadi! No bacci! Yarinya zatayi kwanan bautan Aure..........." Gyara kwanciyar ta tayi "Allah ni bacci nikeji" ta fada tana Kara jan bargon rike bargon yayi, "wai ta ina ka shigo?" Ta tambaya tana tashi zaune, " ke to miye nufin ki? Ai wai Kenan nufin ki kin rufemin kofa ne in kwana a dakina ko me? Kedai a jiki gashi kin girma

Chapter 87 of 92