son Meenal yakeyi, amma kuga ita ko a jikin ta kamar ma bata gane halin da yake ciki ba,ko kuma ta gane tana basarwa ne kawai oho mata"
Meelat ce ta gyara zaman ta kafin ta amsa ma Maryam din da cewa,
"Tabbas hakan take kamar yanda kika hasaso dan ni (Love sunan da suke kiran juna ita da Musty)...
Shi ya fad'a min hakan da kanshi kwana biyu bamu samu zama ni dakeba shi yasa ban miki bayani ba dan shima AK d'in tsabar zurfin ciki wallahi da kyar ya iya fad'ama Yusuf gaskiyar abinda yakeji akan Meenal d'in sannan kuma har yanzun bai iya fitowa fili ya fad'a mata cewa yana sonta ba sai faman kame kame yake ita kuma nasan bazata tab'a kawo zancen wani soyayya a tsakanin suba dan bashi bane a gaban ta,
Love ya rok'i arzikina akan mu d'an janyo musu hankalin ita Meenal din dan shi Mai Jama'a har yanzun tsoron tunkaranta da batun yake, shi yasa kikaga d'azun na tabbar mishi da cewa wasu ne suka biyo mu dan ina son in k'ara tabbar wa, kuma gashi kema kin tabbatar, kedai shaida ce cewa mutumin nan bashi da wani mugun halin da mace zatak'i shi saboda su, kuma koba komai shi d'in d'an uwanta ne kuma wallahi da ace ba son nata yakeyi da gaske ba bazai yarda har su Abokan shi Susan da batun ba dan bai tab'a nuna shaukin shi akan ko wacce mace ba shi yasa suma suke girmama tarin kaunar da suka tabbatar yana mata kuma na mishi alkawarin cewa muma zamuyi bakin kokarin mu wajen ganin mun saita ta a hanya ta yanda cikin sauk'i zata gane son da AK yake mata kafin wani yazo ya mishi shigar sauri"
"Aiko in haka ya tabbata ba k'aramin farin ciki zanyi ba, sai dai kuma ba anan gizo ke sakar ba dan ita dai kin kwana da salin halin ta, wallahi nasan koya fad'a mata cewa yana son ta d'in bai zama lallai ta d'auki abun da mahimmanci ba kina jin tana cewa wai ita ba yanzun zata k'ara aure ba karatu zataci gaba dayi, ban san uban miye zataci da karatun ba, kuma ni tsoro nikeji kar Baba Malam yazo ya maimaita mata wani auren irin wancan a karo na biyu dan kin san dai yanzun batun auren su Fauxieyerh akeyi Suda suka kammala Secondary to wallahi yana iya cewa zai had'a harda ita,inta tsaya wasa sai dai taji shelar d'aurin auren ta amma ita ko ka tsaya ka mata bayani ba lallai bane ta maka kyakyawan fahimta ba,
Sai dai kuma abunda muke hasashe zai tabbata cikin sauk'i ne idan ya zamana shi din yayi gaggawar gabatar da kanshi saboda kinga a yanzun dai babu wani jajirtaccen da zan nuna ince shi take so kinga idan ya fada mata gaskiyar shi koba komai duk wanda zai kawo nashi kokon barar soyayyar to bayan shi zai biyo, dan kinga Ya Salman wallahi ina kula da takun shi muna zaune zakiji yazo yace son Meenal yakeyi, ke nifa hatta da Ya Sa'eed dan dai nasan yanayin kusancin dake tsakanin shi da Meenal tun zamanin yarinta ne amma da nace sonta yakeyi a yanzun saboda yanda naga yana shishshige mata, ke tsaya wai kin san ma cewa Dan Gidan Master ya dawo Kasar nan kuwa?๐ค".
"Wani d'an gidan master din badai Bash ba?" Meelat ta tambaya
"Shi dai Bash tsohon saurayin Meenal din dai da kika sani, wallahi mun had'u ni dashi ranar alhamis d'in nan daya wuce a kofar doka na tsaya a asibitin Dr Meerah ina fitowa shi kuma yana Saukowa daga benen dake saman nan kin gane wannan plaza d'in nasu dai?"
"Kwarai na gane cigaba da bayanin ki sai me ya faru?"
"Ke Qawata kinga yanda ya dawo kamar wani bak'on balarabe kuwa kinsan dai ko dacan dama shid'in masha Allah balle kuma yanzun an k'ara girma kud'i da hutu sun kara bin jiki,
Ina fad'a miki nidai ina ta sauri dan gida nike son isa da wuri sai naji ana kiran sunana daga baya,
Koda na waiga na rantse miki da allah daga farko ban gane shiba, sai da yace min,
(Baki ganeni bane 3ple M)
kin san Allah koda ya kira sunan da yake kiran mu dashi a wancan lokacin k'ara jefani yayi a cikin rud'ani har sai da shi da kanshi yace min,
(Suna na El Bashir Al Hassan Master).
Allah naji kunya amma na maze dan ya riga ya gane cewa ban gane shiba, mun gaisa dai a tsai-tsaye kafin muyi sallama kuma ya tabbatar min da cewa zaimin har gida mu gaisa, kuma na tabbata cewa zaizo din tunda in baki manta ba Ada can ma bai tab'a cewa zai ma abu kuma ya kasa cikawa ba"
"Turkashi lailai to akwai matsala inhar muka sake Bash ya bayyana kanshi a wajen Meenal ba tareda AK ya bayyana kanshi ba, duk da dai bani da tabbacin cewa har yanzun tana son shi amma dai abun bazaiyi dad'i ba sam idan ya dawo, kin san dai yasan gidan Hajiya kuma zuwa can d'in bazai mishi wahala ba"
"To wai me yasa bazata so shi AK dinba bayan kuma naga alamar akwai fahimtar juna a tsakanin su?" Sultana ta tambaya.
"Hummm kishi ne ke damun ta ba tareda ta sani ba, saboda shi dai mai makon ace idon shi akan mata, sai ya zamana su matan ne idon su yake kanshi ita kuma haushin hakan takeji, yanzun kina tambayar ta zatace miki ai yafiye kyaune shi yasa matan ke binshi ita kuma bazata iya auren mijin da yake da kyau ba bayan itama kullum cikin bibiyar ta mazan keyi cewa suna sonta, amma ah ah ita bata ganin nata kyan kullum nashi kadai ne ya tsole mata ido dan haka shi kad'ai take hangowa,
Kin san tsohon mijinta a tsayin shekarun zaman da tayi gidan shi a matsayin matar shi ban tab'ajin ta yaba kyan shi ko sau d'aya ba duk da shima yana da kalan nashi kyan,
sau tarima bata son muna sako shi koda hira mukeyi, amma da zarar ana hirar farin jini sunan mai jama'an shine na farko da zakuji ta ambata, dan allah ku fad'amin hakan da takeyi shi din ba soyayya bane? Amma ita shegen taurin kai gareta"
"Ku tsaya kuji ni ina da shawara indai har zaku bani goyon baya to tabbas kwalliya zata biya kud'in sabulu komai zaizo cikin sauk'i"
" Shawarar me kike dashi Sultana?"
Suka tambaya a tare suna maida hankalin su a kanta, taso wa tayi daga inda take zaune ta koma tsakiyar su ta zauna,
Kasa kasa sosai tace,
"Kishi ko wanne namiji yana kishin abunda yake so kamar dai yanda shi din ya nuna, haka kuma itama duk da tana nuna batajin komai a kanshi amma dole ai kishin ta akan shi zai tona asirin zuciyar ta dan haka daga gobe wasan zai soma ni zanji da ita ta gefen shi, ku kuma sai kuji da ita ta nashi gefen sai dai kuma in har abunda nike fata ya tafi akan yanda muka tsara to dole zai zama nid'in zan kasance a inda take, ina nufin mai makon in zauna a family house dole zan zauna ne a gidan Hajiya inda shi da ita suke rayuwa ina fatan kun fahimci abinda nike nufi?"
Mun gane mu kuma menene abunda zamuyi?,
Dariya tayi kafin tace,
"Hirar samarin da suke bibiyarta zaku dunga yi da gayya kuna ruruta abun aduk san yake kusa ina nufin kamar yanda kukayi d'azun dafatan dai kun fahimci me nike nufi?"
Dariya suka fashe dashi suna tafa hannu a tare,
"Oh Sultana gaskiya nagode Allah daya kawo mana ke a daidai sanda muke buk'atar ki, dan haka kamar yanda aikin mu ya fara daga yau haka zamu cigaba da d'aurashi a gobe ma har zuwa ranar da hak'ar mu zata cimma ruwa"
Sun dad'e suna tufka da warwara akan yanda zasu tafiyar da Meenal dama shi kanshi gogan kafin suka tashi suma sukaje suka nemi wajen bacci.
*washe gari*
koda suka idar da Sallah komawa sukayi suka ci gaba da bacci,
Hajiya dai mai karin Sassafe ita kad'aice ta fito falon ta k'arya da nata kayan dad'in da Meenal ta ware mata tun jiyan,
To shima Dan mai karfi dai tun fitar da yayi masallaci bai dawo gidan ba, Hajiya kuma ganin su d'in basu da niyyar barin gidan sai kawai bayan ta shirya ta amshi key d'in Motar Meenal taba Mansoor shi ya kaita gidan gaisuwar ya dawo ma da Meenal d'in da key din,
Suko basu suka tashi daga baccin ba sai wajen karfe 10, koda suka fito kuma raba aikin sukayi, Meenal ce ta tsaya gyaran d'akunan baccin su wanda suka kwana ita da Hajiya da kuma wanda su Meelat suka kwana a ciki batayi yunkurin lek'a d'akin mai jama'an ba duk da bawai tasan baya gidan bane, Meelat ce tayi gyaran falo su kuma Maryam da Sultana suka shiga kitchen,
Nan da nan suka kammala aiyukan su kowaccen su taje tayi wanka kafin suka dawo falon suka fara shirin karin safe kafin subar gida,
Suna zaune suna karyawa,
Sadeeq ne ya fara shigowa falon da sallama kafin AK dake biyoshi a baya,
Amsawa sukayi, kafin Meelat dake kallon Sadeeq tana dariya tace,
"Anya kuwa ya Sadeeq in ka zarge wuyar Qawata da igiyoyin auren ka zaka dunga bari tana nisa dakai kuwa?
Dubi fa jiya ne kawai amma har ka biyo bayan ta yau, Allah sarki ni nawa mijin ko yana ina oho, yau ko wayar safen ma bamuyi ba bawan Allah"
Wuce wa ciki AK yayi tun bayan daya gama amsa gaisuwar su shiko Sadeeq gefen da Maryam ke zaune ya nema ya zauna, yana ma Meelat dariyar maganar ta,
"Baby ko dai bakiyi murnar ganina bane in koma inda na fito naga sai wani k'ara duk'ar da kai kikeyi?"
"Dama to kace min zakazo nan ne? Ina fa d'azun ma munyi waya kuma bakace min zakazo ba"
Ta fad'a tana tura baki da kauda kanta gefe,
Sai da ya mik'a hannu ya d'auko kofin shayin da take sha ya kurb'a kafin ya ajiye yana mai cewa,
"Kiyi hakuri nima banyi zaton zan samu damar isowa nan d'inba Mai Jama'a ne ya tattago ni ko bakiyi murnar ganina ba? "
" Nayi wallahi sosai ma,"
"To ki shirya mu wuce Zaria anjima!"
"Ah ah wallahi ai bamuyi haka da kaiba mukam sai gobe zamu koma gida kai dai Allah ya kiyaye hanya,"
"Haka zamuyi Baby?"
Ya tambaya yana marairaice mata,
Fitowa AK yayi shima ya nemi waje ya zauna, a gefen Sadeeq sai ya zamana suna kallon juna shida Meenal,
Ita ko Sultana dama tana ganin fitowar shi ta tashi tsam ta koma cikin d'akin da suka kwana Meelat ma ta rufa mata baya tana cemata bari tazo ta nuna mata wani abu,sai ya rage daga AK da Meenal sai Maryam da Sadeeq wadanda ke hirar su kamar ma sun manta da wanzuwar su AK a wajen, saida su Meelat suka share kusan minti goma sannan suka k'ara dawowa falon,
Suna fitowa tun basu zauna ba Sultana ta fara cewa,
"Sister Meenal wannan guy din naki wanda yace zaizo miki yawo jiya ya kira wayar ki na d'auka, nace mishi bakya kusa yadai tambayeni Address d'in gidan nan Meelat kuma ta mishi kwatance yace zaizo kafin mu wuce gidan rasuwar"
"Waye yace ki tab'amin waya to?"
"Kiyi hakuri nima dan naga tun jiya kuna ta waya dashi nasan saurayin kine shi yasa na d'auka, to miye tun yace zai zo dama batun jiya yaso zuwa ba"
"Dallah can ni bani wayata, shegen karambani kawai meya kaiki tab'amin waya yanzun yana zuwa zai dameni da surutu"
"Nifa ban fito da wayar ba tana can na saka miki a caji"
Tunda Sultana ta fara maganar wai wani guy ya kira Meenal a waya, daga AK har Sadeeq suka bar abincin da suke ci, shi Sadeeq Sultana yake kallo kamar a cikin fuskarta ne zai hango fuskar saurayin daya kira Meenal din shiko AK meenal din ya kafe da kallo,
"Waye shi kike shirin gayyato min shi gidan nan?"
"Eh gaskiya kam waye shi?" shima Sadeeq ya tambaya fuska a daure,
Maryam ce tayi saurin amsawa da cewa,
"Kai Baby ba wani bane fa Ya Salman ne yake ta k'ok'arin ganen ya maye gurbin Yayan shi,
Kaga muma muna ta tayashi yak'i amma ita Gimbiyar sai yanga take mana niko banga abunk'i a jikin shiba wallahi, in Babban yaya yaja baya shi k'arami basai ya shigo ciki ba sun mafi dacewa da Salman d'in wallahi"
"Maryam kin san dai bana son haka koh! Ni da yau she mukayi dake cewa sona Ya Salman yakeyi harda zaki min sharri"
"Oh bai fad'a miki ba wai dama? To nima ai ba fadamin yayi ba kawai alamun hakan na gani shi yasa ni kuma nike mishi kamun k'afa"
"Ke Baby Salman SS Ladan kike magana k'anin Sarki? Kowa?"
"Shifa Baby ashe ka gane shi, wallahi sonta yakeyi amma ita sai wani basar dashi takeyi bayan kuma auren ta dashi bai haramta ba ko a musulunce"
"To ke tunda tace ba haka ba ai sai ki kyaleta koh, tunda ta nuna bata ra'ayi soyayya aiba dole bane, koh koh haka kawai dan su sukafi kowa gata ta auri yayan yanzun kuma sai ta k'ara auren k'anin to allah ya kyauta amma ai ana barin halak kodan kunya'
"To Baby gani nayi gida bai koshi ba ai ba'aba dawa nama ba, tunda shi ya nuna ra'ayi ai gara ta bada kai kawai"
"Meenal kina son shine?"
Ya tambayi meenal din,
AK da bashine wanda yayi tambayar ba har yafi Sadeeq din k'aguwan son jin amsar da zata bayar,
"Allah ya kyauta min mai zanyi dashi"
Ta bashi amsa tana cigaba da cin abincin ta,
Wata k'atuwar ajiyar zuciya ce ta kwacewa AK
Ba tareda ya d'auke idon shi akanta ba yace,
"Ki kirashi ki dakatar dashi da zuwa min gida, kuma ko kin koma ban yarda inji ance yana zuwa wajen ki a gidan Hajiya ba kinji dai na fad'a miki"
Suna gama karyawa suka kimtsa wajen suka fice daga gidan,
Ita dai unin ranar rasa gane kan su Maryam tayi dan lokaci lokaci sai taga sun had'a kai suna k'us da Dariya a tsakanin su,
ga kuma Sultana data isheta da shegen tambaya akan wai lallai sai ta bata Labarin waye AK,
Wai ita dai wallahi yana burgeta, haka tasa ta a gaba sai uban kod'a shi take kamar shi kadai ne namijin daya rage a doron k'asa,
duk yanda ake cika ciki yau yan matan nan uku sun cika ta, gidan mutuwa suke shi yasa ta d'aga musu kafa ita kuma sultana taga alaman sai ta ci mata uwa k'ila idan ta nuna mata true colors dinta zata kiyaye ta a lokacin, Allah ma dai yasa gobe za'ayi addu'ar uku kowa ya kama gaban shi masu zama sai anyi bakwai kuma su bada himma ita dai gobe kam Zaria zata kwana koda motar Haya zatabi ta koma gida kuwa,
Yauma kamar jiya anayin Magrib suka koma gidan AK dan tunda yamma dama ya kira Maryam akan su dawo gida da wuri.
*Ummiee ce*โ๐ผ[9/7, 9:27 PM] Ummiee Zaria: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
*BOOK 2*
*PAGE 21*
Yau dai duk yanda Meenal taci burin su fita yawo hakan bai samu ba domin dai koda suka dawo gidan sun iske Mai Jama'a ya rigasu dawowa gida, ko bai fad'aba tasan da gayya yazo ya kafa ya tsare dan dai kawai karsu fitan tunda ya dawo daga sallan ishsha'i ko bakin gate bai k'ara lek'awa ba,
harma da wani ba Mansoor Umarnin cewa ya kulle gate d'in kawai shima ya wuce ciki wajen nashi iyalan saboda babu mai k'ara fita a gidan.
Da wuri ta mishi magana akan fitan da zasuyi, saboda kar yace yauma basu nemi izinin fitan ba amma sai wani cewa yayi ai dama abinci suke fita siya koh?,
Dan haka in dai dan abinci ne su shiga kitchen su girka duk abunda suke son ci ya riga ya tanadar musu da komai,
Duk yanda tasa shi a gaba da magiya k'iyawa yayi, sudai su Meelat tunda yace ba'a zuwa ko ina dama suka shafa ma kansu lafiya,
Hajiya najin Meenal d'in na ta faman magiya amma bata sa baki ba har saida shi d'in yabar wajen ya shige d'akin shi saboda yanda ta dameshi, sannan hajiya tace,
"Ina kuke batun zuwa yanzun da daren nan Meenal?"
"Hajiya wani shago muka gani a fitar da mukayi da dare jiya shine muke so muje dasu Meelat ko zamu samo abubuwan da zamuyi amfani dashi na biki"
"Shi shagon ba'a bud'e shi da rana ne?, lallai sai da darene zakuje siyayyar a garin da ba naku ba? Jiya mafa haka kuka fita kuma baku dawo da wuri ba, kunyi zaton ban sani bane tunda bakuji nace muku komai ba koh?
Ai Abdul ya kyauta min da yasa Mansoor ya kulle kofar sai inga ta inda zakubi ku fita!
In kuma ta katanga zaku ciccib'a ku fidda motar duk zan gani"
Simi simi suka shige kowacce ta kama abinda zai fishsheta Maryam da Meelat sune suka fad'a kitchen ita kuma sultana ciki ta shige ta tsalo wanka, dan ita hakan ma ya mata dai dai ta yanda abunda ta tsarayi zai tafi mata batare shamaki ba zata jefi tsuntsu biyune da dutse guda d'aya.
Wanka ta d'auka na d'aukar magana kamar wata mai shirin zuwa dinner riga da skirt na wani lafiyayyen bakin less d'in da aka mishi d'inkin daya zauna dai dai jikin ta ta sanya bayan ta fente fuskanta kuma saida ta b'ata lokaci wajen d'an d'asa d'auri kalar yan matan Abuja sannan ta rufe k'ofar wankan nata da turare mai d'ad'in shak'a kafin ta fito daga cikin d'akin da wayarta a hannu duk da kasancewar dare ne hakan bai hanata d'aukar kanta Selfie ba,tafa wanku tass wallahi
Kamshin turaren ta da kuma k'arar da takun takalmin ta ke badawa ne ya maido hankalin Hajiya da Meenal wad'anda ke zaune a falon suna d'an hira jefi jefi wajen ta,
cike da salon tafiyar ta mai d'aukar hankalin mai kallo ta k'araso inda suke kafin ta nemi waje a gefen Hajiya itama ta zauna,
"Hajiyar mu barka da war haka!" ta ambata a yayinda takai zaune.
Tun daga fitowar ta har zuwa sanda ta zauna da kallo kawai Hajiya ke binta, kasa shiru tayi har sai da ta mata tambaya cewa,
"Bak'o zakiyi ne hala naga daga dawowar ki kin wani shiga kin shawo wanka kamar wata mai shirin zuwa turakar miji ranar kwanan ta?"
K'aramin dariya Sultana tayi tana mai rufe idon ta da tafukan hannun ta alamun maganar na Hajiya ya bata kunya tace,
"Kai Hajiya sai masu mazane suke kwalliyar dare?
To su kuma matan da suke farautan wasu kuma fa? Nidai tarko nike d'anawa kuma ina fatan ganin ranar da tarkon nawa zai kama kurciya,
Nagode allah iyamu ne anan da kin sani a kunya Hajiyata ashe shike nan mu yan mata bamu da damar yin kwalliyar domin d'aukar hankalin abokin farautar namu kenan ko ya abun yake?"
Tab'e baki hajiya tayi kafin ta amsa mata da cewa,
"Zance na dai ya fito kenan tunda dai wani ne akayi kwalliyar domin shi!
To Allah yasa yana da rabo, amma ke ai in namiji zai soki ko bakiyi fente fente ba tsaf zaki kwaci zuciyar shi amma hakan ma ba laifin dama yan magana cewa sukayi ko kina da kyau ki k'ara da wanka,
ai gara kiyi kiyi kekam ki bada himma wallahi kiyi auren ki, karki biye ma halin yar uwarki gatanan ita da anyi magana sai tace wai ita ba yanzun zatayi aure ba, ko zaman me take nufin zata zauna tamin a cikin gida ni ban sani ba"
"Nidai Hajiya duk ba wannan ba,
Nidai dan Allah kimin kamun k'afa dan kece kawai nasan zakimin tsaye har in samu muradin raina"Sultana ta k'ara fad'a a marairaice tana kwabe fuska,
"To wani abun ne kuma yake faruwa hala?"
"Ah ah Hajiya bai farun ba tukun ina dai fatan faruwar hakan shi yasa nace gara kawai in sanar dake tun da wuri dan Wallahi ke k'adaice nasan zaki samar min da mafita cikin sauk'i"
"Ke nifa a rayuwa babu abunda ke b'atan rai irin mutum yayi ta kwane kwane bazaiyi magana dani kai tsaye ba,
To in baki fad'amin ba taya kike zaton zan gano"
K'asa sosai Sultana da duk'ar da kanta tana cigaba da murza yan yatsun ta data jerama zubuna guda uku, tace
"Hajiya dan Allah karkice bani da kunya, wallahi ba rashin kunya bane kawai nidai inajin tsoron kar wata tazo tamin shigar sauri ne idan nayi nauyin baki, kuma naga aiba laifi bane dan mace taga namiji tace tana son shi mai makon Inbar abun a cikin zuciyata ya zamar mini wani k'atoton cutar da zai iya Kaini gushewata bayan nasan idan na furta ana iya samar min da mafita"
Shiru tayi tana cigaba da mutsu mutsu dan gaba d'aya zuwa wannan lokacin tama kasa zaman da kyau kunyar k'aryar data aro ta d'aura ma kanta kuma ya hanata iya d'agowa ta kalli Hajiya duk da yanda takejin kallon da Hajiyar take mata,
Itama kuma Hajiyar k'in cewa komai tayi har sai da ita Sultanan ta gaji da mutsu mutsun ta aro ma kanta jarumta kafin taci gaba da cewa,
"Hajiya zaki taimaka min wajen samun abun da nike so?"
Bata jira hajiyar ta amsa ba taci gaba da cewa.
"Nidai ko bazan samu taimakon kowa ba zan fad'i abunda nike ji, Hajiya wallahi nidai ina son Ya Abdul Khareem Mai Jama'a dan Allah ki gabatar dani a wajen shi ko zan samu ya taimaka ya aureni! Wallahi ina son shi son da nike jin cewa bazan iya rayuwar aure dako wani mijiba inba shiba, dan Allah Hajiya kisa baki yanda zai saurareni su Meelat sun fad'amin duk yan matan dake nuna suna son shi basa sha ta dad'i amma ni kuma daga jiya zuwa yau son shi yamin kamun da bana jin zan iya jurewa ba tareda na bari ya gane ba shi yasa na fara tun karar ki dan ki tallafa min ko zan samu ya kulani"
Ta k'ara fad'a harda matso wasu k'ananun hawaye na munafunci,
Idan kunga yanda ta koma a gaban Hajiya dad'e duniya zakuyi zaton duk abubuwan da take fad'a gaskiyar su kenan bawai shirya su tayi ba, dan gaba d'aya ta juye ta koma kallar tausayi,
Meenal da tun d'azun kallo d'aya tama Sultanan ta d'auke kanta ta maida kan wayanta da suke chat da Ya Sa'eed wanda yake tambayan ta akan goben zata koma zaria ko sai anyi bakwai ne,
Jin wasu soki burutsun da tsinannun aljannun tsakar daren da suka hau kan sultanan suka sa ta hauka takeyi ne hakan ya sa Meenal d'in jan wani irin dogon tsakin daya fita da k'ara kamar zata cire harshenta,wani irin bak'in ciki mad'aukaki ne taji yana neman rufe ji da ganin ta, sai takeji kamar gizone maganganun na sultana ko kuma dai kila Sultanan ta shawo wasu kwayoyin da sukafi k'arfin kanta ne ko kuma dai aljannun gareta da gaske.
Bata tsaya ba Ya Sa'eed amsar tambayar shiba ta mik'e tsam daga inda take zaune jin surutan yana neman wuce abunda kwalwarta zata iya d'auka,
Zufa taji yana neman lullub'eta duk da ac da fankan da suke ta aiki a falon, d'aki ta shige kai tsaye dan tabbas tana buk'atar watsa ruwa masu sanyi a jikin ta k'ila ko zata dawo dai dai, Kai itafa sai takejin kamar ma dai aikin shedanu ne suka sa kunnuwan ta jiyo mata maganganun da ta tabbata k'ila ba haka Sultanan ta fad'e suba, inba haka ba taya ma sultanan da kwata kwata yaushe ma tasan Taubashin da har zata wani rikice da kukan cewa shi take so harda wani rok'on Hajiya akan ta taimaka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 59 Chapter of 92