Share this page
sulale ya fice daga gidan, Gidan Malam ya wuce suka had'e da ya Sheikh a sashen Malam din sukayi ta hira. Da dare Hajiya ta tara su Baba Usman a falon ta maganar zuwa neman auren AK da take son suje a gobe ta fara gabatar musu, Dukan su daga iyaye mazan har matan kowa ya nuna farin ciki da jin dadin shi na had'in auren a bayyane, bayan an gama tattauna akan auren su AK maganar Moon shima Abba Ahmad ya sako hajiya bata katse mishi hanzari ba har sai da yakai karshen zancen shi da cewa maneman auren Moon d'in zasu iso gidan a gobe dan ya kirasu cewa ya iso k'asar dan haka gara suzo a tsaida komai daya kamata, "Suwa ke neman aure Maimunan?" Hajiya ta tambaya, Gyara zama yayi dan yasan anzo inda yake tsoro azo din, "Hajiya dama munk'i shaida miki ne mukace sai munzo sai a gabatar da komai a gaban ki, Wannan yaron d'an gidan Malam Sulaiman na unguwar malamai d'an yayan su Mukhtar mijin Jiddan ki shine yaje har can Lagos da zancen yana neman auren Maimunatun Brigadier uban matar shi ne kuma yaje mishi neman auran shida abokan shi mutum biyu cikin su harda tsohon abokina, To dai tun lokacin nace musu su d'an dakata har in iso k'asar saboda in gabatar miki da zancen kafin isowar su" "Masha Allah sai dai kuma ban gane dogon kwatancen naka ba naji kace d'an yayan Mukhtar, wai mijin Jidda na kake magana ko wani daban?" "Eh shi dai Hajiya" "Ikon Allah to waye yayan nashi ni ban gane shiba" Shiru yayi yana kallon gefen da Baba Usman yake zaune wanda ya fuske abinshi kamar bai san akan me suke magana ba, "Hajiya shifa yaron shine mijin da Allah yasa ya auri Meenal a shekarun baya" "Ohh wai kana so kace min Sufyaan dai Sarki wanda aka aura ma Meenal ya saki shine ya dawo neman auren Moon yar uwarta kuma?" Cacaca falon ya haura da surutan mata har baka gane abunda suke cewa, dan a karkace zancen ya shiga kunnuwan su, Gyara zama Hajiya tati dan taba kowa damar tofa albarkacin bakin shi, Abba Ahmad shi dai da yaga surutan yak'i karewa shi ya tsawata musu da cewa, "Dan Allah kuyi ma mutane shiru ku barmu mu tattauna abunda ya taramu anan" Shirun sukayi suka koma jimami k'asaยฒ inba rainin wayau ba taya ma ya auri Meenal yanzun kuma ya dawo yace Moon yake so ai wannan sam ba maganar da hankali zai d'auka bane, Sufa matan sun natsu ne dan sun san cewa babu ma ta yanda za'ayi Hajiya ta goyi bayan al'amarin amma wai sai suka jiyo muryar Hajiya tana cewa, "Aiko dai indai Sarki ne Maimunatu kam ta more miji dan Wallahi samun miji irin shi dai yanzun sai an tona, dan haka suna isowa babu b'ata lokaci su gabatar da komai kawai ayi batun sa rana dan haka sai ka kirasu ka sheda musu suzo da shirin su" Duka jama'ar falon da kallo irin na mad'aukakin mamaki suka dunga binta, Anya wannan Hajiyar da suka sani ne kuwa? Umma ce ta gaza shiru tayi magana cewa, "Hajiya tsohon mijin Aminatu fa ake magana taya kuma za'ace Maimoon ta aure shi, in auren za'a mata ai gara a bata dama ta fad'i wanda take so sai a aura mata in ma babu ga d'an yar uwata nan Lukman tun bata kai haka ba yake kwakwa a kanta" Sai da Hajiya ta k'are mata kallo tsaf kafin tace, "Shi auren Sarki da Moon d'in akwai ta inda Allah ya haramta shi a musulunce ne?" Shiru falon yayi wannan Karon ma Umman ce dai ta amsa da cewa, "Amma Hajiya kusancin yayi yawa kuma Ana barin halak kodan kunya" "To nidai na riga na gama magana Moon dai Sarki ta zab'a a matsayin miji in baki sani ba ni na fad'a miki yanzun dan haka shi zata aura, shi dan yar uwarki tace bata son shi dan haka babu mai mata dole, ku kuma jini da kyau maganar nan ta tsaya iya nan bana son in dunga jin wasu k'ananun magana suna tasowa a bayan fage, dama can Allah yayi cewa Moon ce matar shi tun farko wanda kuma duk yace zaiyi jayayya da hukuncin Allah to ya shirya shida Ubangijin shi, ba kuma Moon ba duk wata yar data isa aure ina bukatar ganin magabatan wad'anda ke neman su kafin kubar garin nan". Tana gama kora musu nata jawaban ta haye sama abinta ta barsu suna k'ara cakalkala zancen, A daren Abba Ahmad ya kira Brigadier sukayi magana shi kuma ya tabbatar mishi da cewa insha Allah zasuyi k'okarin isowa Zaria a gobe, wannan kenan, A daren Meenal Sultana da Safiyya matar Yusuf suka dawo gidan na Hajiya dan AK ya shaida ma Meenal cewa karsu sake suce zasu kwana a unguwar malamai su dawo gida su kwana, Bayan dawowar su har sunyi wanka sun kwanta suna hira tsakanin su ya kira wayarta akan ta fito ta same shi yana jiran ta, tana tura baki tana komai haka nan tasa hijab ta fita badan taso ba dan Wallahi yau ba karamin gajiya tayi ba, Bashi a falo dan haka sai ta bude kofar falon ta fito dan har yanzun akwai hayaniyar a gidan tasan kila yana farfajiyar gidan, Koda ta fito bata lura dashi ba sai ji tayi kawai ya jata zuwa bayan wata k'aramar bishiya dake kofar falon, "Waiyo Allah na wanene kai miye haka" take fad'a tana son kwacewa, Juyo da ita yayi yana dariya, "Kedai matsoraciya ce wallahi, yanzun nan ke fisabilillahi da ban kira ki ba haka zaki kwanta kuma har ki iya yin bacci abinki bayan kin san yau uni nayi da yunwar son ganin fuskar ki, da ace Sultana bata d'auki hoton kwalliyar ki ta turamin bafa da shike nan kin sha dani,ai dai kema kin san hakan bai dace ba nina fa" fa d'a yana lankwashe kanshi a gefen kafad'ar shi, "To kaima ba kana cikin naka abokan ba! Shi yasa ai ban kira ka ba saboda kar in dame ka" "Waye yace miki zaki dameni ne?" "Ba kowa" "To fad'amin kinyi kewa na yau" Murmushi tayi tana d'an rausayar da kai gefe, "Allah nidai gani nikeyi sam kamar baki wani damu dani ba" "Na damu dakai mana" "Tsaya kiga hotunan da Sultana ta tura min" ya fad'a yana nuna mata hotunan a cikin wayar shi, "Kinyi kyau amma dai gaskiya ni bana son kina goga wannan abun a bakin ki in zaki fita koda ko inda zaki shiga babu mata" "Me?" Ta tambaya tana d'ago kanta ta kalle shi, Shi kuma sai yakai yatsar shi dai dai bakinta a jikin hoton, "wannan jan abun da kika goga a bakin ki nike magana" "Wai jambaki? Baiyi min kyau bane? To amma ai yau kowa yace nayi kyau" Ta fad'a a shagwabe, "Eh ai nima saboda kyan da kikayi yayi yawa shi yasa nayi magana dan bana son inga kin shiga waje idanu sunyi miki yawa inba haka ba kuma lallai zaki fara yawo da facemask" Dariya ma ya bata dan haka ta dara "Waima facemask ana zaune kalau kaima ai kana da kyau me yasa baka sawa idan zaka fita?" "Ina sawa mana kece dai baki gani ba" "To nidai zanje in kwanta kaga dare yayi" "Ke yanzun nan fa kika fito" ya fad'a yana riko hannun ta, "To ai na gaji da yawa ne yau" "Ok tunda kin gaji saiki zauna a gida gobe basai kinje ko ina ba" "Tab lallai ma bikin Meelat nefa" "Eh bikin nata fa so kike insa miki ido kiyi ta ba kanki wahala shike nan bazaki huta ba, kinga nima duk yau haka nike ta jina kamar banda lafiya kuma nan d'ina sai k'aikayi yakeyi" Ya fad'i hakan a yayin da yakai hannun ta d'aya gefen fuskar shi dai dai wajen dimple din shi, "Me yake damun ka to? In sosa maka?" Ta tambaya ta kallon shi da tausayi a fuskar ta, "Ai ba sosawa akeyi ba" "Me akeyi?" Jawota yayi zuwa gaban shi kafin ta ankara taji Sautin muah a gefen nata fuskar, Kwacewa tayi tana kai mishi duka, "Allah nidai ban yarda ba ai nace maka bana son haka amma baka ji," "Ok ok sorry to zoki rama to shi kenan" Daga bayan su sukaji tafi na tashi RAF RAF RAF, "Kai amma AK kaf shekarar nan banga mara kirki kamar ka ba, Yanzun nan dama ashe tsabar munafunci har budurwa gareka shine mu bamu da labari, wacece ita? To yau dai Allah ya tona maka asiri anyi walkiya mun ganka, Wallahi Musty baka kyauta min ba daka kasa kirana tun tuni ka bani labari ni kuma in tattaro kayana in dawo nan in tare ayi komai a gaba na" "Kai dallah ai da ace a lokacin na fad'a muku karyatani zakuyi amma yanzun da Allah yasa kaji kuma ka gani kaga kaima sai kaba wasu labari, yanzun dai muje ciki dan Allah ka wani zo duk ka tsorata min Ya"cewar Musty, "Kan uba wallahi ban wucewa sai naga ko wacece" wayar Shi ya ciro ya fara musu hotuna duk da cewa wajen babu haske sosai, Shi kuma AK ganin haka sai yaja Meenal din ya maidata bayan Shi ya boye, "Faisal zanci uban ka in baka dena d'aukar mu hoto ba, Matar tawace kake son d'auka ka watsa kowa yagani?" Yan hannun Meenal din yayi sai da suka kai bakin kofar falon ya bud'e ya tura ta, "Wuce ciki sai da safe" Shi kuma Faisal cewa yayi "haba AK wannan ai wulakanci ne bazaka bar yarinya ta gaisheni ba haka akeyi duk kabi ka wani boyeta to yanzun ya za'ayi idan na ganta gobe in ganeta? Kai dai d'an iskane wallahi kuma wallahi kowa sai yaji zancen nan haba ashe Shi yasa ka barmu a waje ka shigo ciki wato kazo duba lafiyar fulawar ka". Juyawa yayi da gudu zuwa inda sauran abokan su suke yana basu labari su kuma kamar masu jira haka suka taso AK gaba akan cewa lallai fa ya kira musu ita ta fito ta gaishe su su ganta, Shi kuma yace musu uban kuturu yayi kad'an, Ya dai sha sharri ba kad'an ba kowa da abunda yake cewa wasu na fad'in wai Allah yayi ya samu aljanar data aureshi ta rabu dashi da kyar wasu kuma na cewa, wai hala dai bashi ita akayi dan sun san da wuya ace shine ya ganta yace yana so, Sanda Yusuf ya zauna ya fara basu labarin badakalar da aka sha kafin ya furta mata yana son ta koh kasa zama a cikin su Ak yayi dan haka suka hauro kamar zasu cinye namar Shi d'anye. *Ummiee ce*[10/3, 3:49 PM] Ummiee Zaria: โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ *BOOK 2* *PAGE 41* Washe gari kasawa AK yayi ya tsare tun asuba yake jiran saukowar Meenal k'asa, dan haka tana saukowa koh gaisuwa bai tsaya sun yi ba yake ce mata, "Amma da wuri zaku fita daga gidan nan yau koh?" "Eh ina kwana!"ta bashi amsa, "Lafiya lau ya gajiyar ki" "alhamdulillah" "Idan zaki fita yau ki d'auki abubuwan da kika san zaki buk'ata dan bana son yawon nan tsakanin nan da can unguwar ki zauna a can d'in kawai idan an gama bikin kya dawo ni kuma in ina son ganin ki zan biyoki can d'in kindai ga yanda gidan nan ya cika da maza ni kuma bazan yarda kiyi ta faman shige da fice a gaban su ba," Allah mai iko dafa itace tace mishi zata je can d'in ta tare ta tabbata sai yayi tsalle ya dire kafin ya kafta mata kashedin cewa Shi sam bai yarda da hakan ba, amma gashi yanzun a sauk'ake ya sallama ta ai ita hakan ma gaba ta kaita, dan haka bata tsaya jayayya ba sai kawai ta amsa mishi da cewa "to" "Zo muje ki gaishe dasu Abba" ya fad'a yana jan hannun ta suka fice daga falon na Hajiya zuwa sashen su Abba Ahmad, kai jama'a AK dai sam ya manta da wani abu wai Shi kunya domin dai can yaje gaban iyayen shi wai yana gabatar musu da Meenal din a matsayin sirikar su, Shi bai san da batun zaman da akayi a gidan jiya ba dan lokacin baya gidan dan haka saiya kama rokon Abba Ahmad din cewa dama su yake jira suje su nemo mishi auren ta. Da wurin suka wuce kamar yanda ya buk'ata ba tareda tarin abokan shi wadanda sukaci burin son ganin ko wacece Yarinyar da shi d'in wa kwarema ba, wannan rana dai ko ina ya zama busy gidan Hajiya suna ta shirin zuwa d'aurin auren Musty da neman auren AK kuma da zasu gabatar a gidan Malam bayan an gama d'aurin auren ga kuma shirin tarbar bak'in su wad'anda zasu taho neman auren Maimoon da sukeyi, A gefen Sarki koh koda ya shiga gidan Malam yaso ne dama ya same Shi yayi mishi bayanin Neman auren da za'aje mishi ayau sannan kuma yaso ace batun neman auren nashi ya fitane ta bakin Malam d'in ta yanda basai anyi ta surutai akan hakan ba sai dai kuma koda ya shiga bai iske Malam ba wai yayi sammakon zuwa kano wajen wani d'aurin auren shida Ya Sa'eed amma Baba Adamu da Baba Auta su suna gida, Abune da bazai yuwuba wato yace zai kai batun ga Baba Auta duk da cewa yasan bazaik'i zuwa ba amma shi dai yana jin kunya gaskiya, dan haka bayan sun d'an tab'a hira shida Sheikh sai ya wuce sashen na Baba Adamu bayan gaisuwa sun d'an tab'a hira dashi dan gane da aikin Sarkin dama fannin kasuwancin su kafin Sarkin ya gyara zama ya fara korama Baba Adamun abunda ke tafe dashi, "Baba wato dama aure nike so in k'ara!" "Ah ah masha Allah kaga jarumi to yanzun fa ya ake ciki?" Adamun ya tambaya yana taya shi murna "Eh to da yike ita Yarinyar ita da iyayen ta dukan su a Lagos suke zama, ni kuma ganin idan na kawo maganar nan wajen ku kamar zan baku aiki na tashin da zakuyi kuje har can sai kawai naje ma Baba Brigadier da maganan shine shi kuma ya d'auki abokan shi suka je can gidan su Yarinyar suka samu mahaifin ta domin neman izini,to baban dai tun lokacin ya sheda musu cewa yayan shine waliyin ita Yarinyar kuma shi ba anan Nigeria yake zaune ba, dan haka sai ya had'asu da yayan nashi sukayi magana akan idan ya shigo sai suzo nan agabatar da komai daya dace, to jiya dana shigo gari naje can family house din su munyi magana da kakarta ta kuma shaida min cewa in za'aje atafi da komai na neman aure dan so take asa rana gaba d'aya," "Masha Allah kace yar Babbar gida ka nemo mana to ai bashi da komai mu ai hakan ya mana badai kai ka riga ka shirya ba?" "A shirye nake duk yanda suka yanke yamin," "Ina ne family house din nasu?" "Iyalan gidan Prof Abdul Khareem ne wanda ke tudun wada" "Prof mahaifin Mommyn ku tanan gidan kake nufi?" "Eh shi nake nufi" Jin jina kai Baba Adamu yayi kafin ya kara jefo mishi tambaya cewa, "Kuma su can d'in sunsan cewa kaine ke neman auren yarsu?" "Eh sun sani dan dafarko ma ita Yarinyar taki saurarena amma da mukaje can gidan wajen Baban ta shi ya fahimce mu kakar suma kuma ta bada goyon baya" "Wai kana so kace min Hajiya tasan da cewa kaine ke neman auren jikarta a karo na biyu kuma harta amince?" Baba Adamu ya fad'a cike da mamaki "Eh ta sani, itama Meenal ta sani dan itace ma tayi min jagora wajen yar uwar nata" "Ah to masha Allah dama ai amincewar nasu shi mukafi buk'ata, tashi kaje insha Allah za'a gabatar da komai yau basai gobe ba karka damu dasu iyayen ka na nan kuma ni zan musu bayanin komai da kaina," Su Brigadier sun iso shida abokan shi su biyu sai, kuma shida kanshi ya zauna da Malam Sulaiman ya mishi bayani akan dalilin su na zuwa garin, ba k'aramin kunyar abinda Sarki ya aikata Malam Sulaiman yaji ba, ta ina ake haka fisabilillahi ka taso Baban matar ka tundaga wata uwa duniya ya taho har Zaria nema maka aure, shi dai yace babu inda zashi dan haka sai ya wakilta kanin shi Lawal da kuma Baba Adamu suka kwashi juna su biyar zuwa gidan Hajiya, Sun samu tarba na girma da mutuntawa a wajen su Abba Ahmad babu b'ata lokaci kuma suka gabatar da komai daya dace na neman aure tun daga kan kud'in gaisuwar uwa da uba goro da cingum komai da ake buk'atar shi a wajen sun gabatar dan haka aka tsaida rana nan da wata uku idan Allah ya kaimu da rayuwa, Sai bayan da komai ya kammala kafin shima Baba Usman ya bijiro ma da Baba Adamu zancen son zuwan da sukayi can wajen su ayau dan su nema ma AK auren Aminatu suma, Sun d'anyi maganganu dan ya shaida musu cewa Malam baya nan amma tunda har Allah yasa su sunzo nan ai basai sun basu wani wahala ba kuma tunda dai har su yaran sun dai daita a tsakanin su zaiyi ma Malam bayani idan sun tashi zuwa sai suzo suma kamar dai haka da duk wani abun buk'ata na sanya rana shi dai ya basu Meenal duk da cewa dama Meenal din tasu ce. To an dai watse taro cike da tarin farin ciki na murnar arzikin da ake shirin kullawa, tare dukan su suka wuce wajen d'aurin auren ana gama wa kuma su brigadier suka juya basu kwana ba duk da cewa Sarki yayi musu tayin kwanan, A gurguje..... Gefen Amarya da k'awayen ta lafiya lau sukaci gaba da gudanar da shagulgulan bikin su an d'aura auren Jamila da Angonta Mustapha da rana bayan an sauko daga masallacin juma'a da yamma aka gudanar da kayatacciyar walima wanda ango da amarya suka halarta tareda abokan su, anayin sallan magrib kuma angwaye suka kawo mota suka kwashi Amarya da kawayen ta zuwa GRA gidan amarya anayin sallan ishsha'i kuma suka k'ara kwasan su bayan an k'ara shirya amaryar zuwa wajen dinner, sai da aka kwashe yan uwa kaf kafin Amarya da kawayen ta suka fita daga k'arshe gaskiyar yan magana da suke cewa ko wacce mace ranar auren ta ana k'ara mata kyau domin dai wani irin kyau mai d'aukar hankali Meelat ta tsatso a wannan ranar, a cikin wad'anda suka zo d'aukar amarya har da AK sai dai shi ya shaida musu cewa ba d'aukar Amaryar Musty yazo ba ah ah shi yaxo d'aukar nashi amaryar ne tunda har ubanta yace ya bashi ta riga ta zama nashi kuma yanda kuraye sukayi yawa a wajen gara ya kula da kayan shi, Sultana da Maryam ne suka rik'o Meelat tareda wata yar uwar su Meelat din suka fito da ita Musty dake cikin motar da zasu saka amaryar da kanshi ya fito ya tari abinshi ya janye ta zuwa cikin motar, AK dake cikin nashi motar ne shima ya fito a sanda ya hango Faisal na k'okarin sa Sultana da Meenal su shiga cikin motar shi, Gaban Meenal din yasha fuska a d'aure yake cewa "ina kike shirin zuwa da wannan kwalliyar na fuskar ki" "Me kwalliya na yayi yanzun kuma?" "Amma ai nace miki bana son kina goga wannan abun a bakin ki a sanda zaki shiga cikin mutane koh?" Hankacin shi ya ciro daga cikin aljihun rigar shi, "Nidai dan Allah karka goge min ina son abuna a haka" ta fad'a tana tura baki, "Aminatu" wata daga cikin kawayen su dake tareda Maryam a wajen motar Sadeeq ta kirata, dan haka saita juya da sauri tabar wajen tana mishi gwalo, shi kuma sai ya k'arasa wajen Faisal suna magana, K'awar nata ce ke tambayan ta bayan ta k'arasa inda suke, "Friend amma dai wannan yayan ki ne koh?" Ta tambaya tana nuna mata AK, "Eh Yayana ne" meenal ta bata amsa, "Yana da mata?" Ta k'ara tambaya, "Ah ah" "Oh saurayi ne kenan bashi da mata?"ta k'ara tambaya tana gyad'a kai, "Eh saurayine" meenal ta k'ara amsa mata, "To dan Allah friend kid'an gabatar dani a gunshi mana wallahi nidai ina son shi yamin shine dai dai kalar mijin da nike son aure" ta k'asa fad'a tana karye wuya alamun rok'o, Fuuuu Meenal ta wuce tabar wajen a fusace zuwa wajen da motar AK yake tana isa ta bud'e bayan motar ta shiga ta kullo k'ofar motar da k'arfi a fusace, Sultana ce ta k'arasa inda Yarinyar take tana dariya ta dafa kafadarta take cewa, "Ke baki san shine mijin da zata aura ba shine zaki wani kirata kice kina son mijinta, gaskiya dai baki kyauta ba"tana gama fad'ar hakan ta wuce abinta ta shige motar Faisal, Shiko AK ganin da yayi ta wuce su a fusace da kuma yanda ta bud'e bayan motar ta shiga hakan ne yasa ya juya zuwa wajen motar shima ya bud'e bayan ya shiga ya sameta tana ta faman cika tana batsewa, "Ya akayi ne? Meya sameki?" Sai da ta watsa mishi harara mai lafiya tana turo baki tace "duk ba kai bane," "Ni kuma mai nayi?" "Eh ai haka zakace da ace baka fito daga cikin motar ka shiga cikin yan mata ba ai da bazata ganka ba balle harta wani cemin wai tana sonka" ta fad'a tana kauda kai gefe, Murmushi yayi ita kuma Sautin murmushin nashi ne yasa ta juyo taci gaba da masifa, Shidai bai kulata ba hartayi ta gaji ashe wai shirun da yayi mata kuma yayi laifi dan haka sai kawai ta kama murfin kofar da niyyar bud'ewa ta fice, Fincikota yayi ta fad'o cikin jikin shi kuma yasa hannu ya kulleta gam a jikin nashi, "Yi hakuri to naji nayi laifi in ma kince karmuje can d'in ai sai muyi zaman mu basai munje ba" "Tab duk wannan kwalliyar da nayi ne zan wani zauna a mota bikin Meelat dina akeyi fa" "Oh dama kwalliyar badan ni akayi ba kenan anyi ne dan wasu su gani, ai kin tunanin ma d'azun nace a goge jan bakin nan kika k'i" Mutsu mutsu ta fara a jikin nashi tana son kwacewa, "Nidai kabar min kwalliya ta kuma kana ganin duk sun wuce fa" Sakin ta yayi da sauri ya fice daga motar ya zagaya gefen direba ya zauna bayan ya gyara rigar shi data fara yamutse wa sakamakon mutstsukan data sha a wajen Meenal, "Anan zaki zauna ko zaki dawo nan ne?" Ya tambaya batareda ya waigoba ya kunna motar, tsallakowa ita kuma tayi batareda ta fita ba ta dawo gaban motar, Tissue ta yago bayan ta zauna ta goge jan bakin dake bakinta sai da ya fita tass kafin ta maye gurbin shi da lips glows ta d'an k'ara goga hoda kad'an ta kuma gyara zaman d'aurin kanta, da gefen ido yake kallon ta harta gama basu yi tafiya mai nisa ba suka isa inda ake gabatar da Dinner d'in koda suka isa amarya da ango sun shige babu wasu mutane sosai a waje, Bude kofar shi yayi yafita kafin ya zagaya ya bud'e mata nata side din ya mik'a mata hannun shi ta kama ya fito da ita, gefe ya maidata ta jingina da jikin motar shi kuma yasa kanshi cikin motar wani chain ya ciro a cikin dashboard ya fito dashi a hannun shi sai da ya maida kofar motar ya rufe kafin ya riko hannun ta na hagu ya mak'ala mata chain din da aka k'awata shi da wasu irin duwatsu masu gyalgyali, d'ayan chain din dake tare dana hannun ta makala a nashi hannun shima sai kuma ya cire wani d'an karfe k'arami dake matsayin mabud'in chain din ya saka a cikin aljihun shi, "Menene wannan d'in?" Ta tambaya, "Idon ma tambayi kin d'auka zan barki hannu sake ne in mun shiga kiyi ta yawo idon kowa a kanki?" "Wai shi yasa kasamin ankwa a hannu? Kai dan Allah yaya to haka zamu shiga ciki mutane suna kallon mu kuma fa harda yan gidan mu a ciki" "Eh haka na yanke kinga

Chapter 77 of 92